Header Ads
Showing 72001 words to 75000 words out of 171869 words

Chapter 25 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1069

Ads at the middle of Article

ciro maganane bakyajin shakkan tambaya kowace irice" Na ƙyaɓe fuska sannan nace.


"Yaya duk wani abunda yake faruwa a gidanmu nakeso naga yadaina komainya gyaru"


"Kin ɗauki hanya Habiba budurwatace" yafaɗa kai tsaye na tsaro ido haɗe dayin fiƙi-fiƙi na kalleshi amma babu alamun wasa bansan dariya ta kwacemin ba saida nayi mai isata shima ganin bazan tsayaba yasa ya tayani har muka tsagaita saida muka gama dariyar kuma sai yace.


"wato ke dariya ma nabaki marmeyy dagaske nake Habiba budurwa tace" nasake darawa ni tunda nakema ban taɓaji yakira sunan anty ba sai yau.


"Budurwa tace lokacin muna makaranta dukda soyayyace irinta yarinta amma alokacin zuciya tana rudata ina ganin kamar har zan aureta. Dukda shekarunmu ɗaya ajinmu ma ɗaya toh amma ita soyayyar farko tanada zafi kwatsam sai naji wai zatayi aure zance yazo ya tabbata mahaifina zata aura dafarko bata saniba amma dana sani na sanarda ita ta nuna batama sanniba duk soyayyadda mukayi tatashi abanza itafa mahaifin nawa takeso shi zata aura. Baba baisan wacecec ita agareni amma banida tabbacin idanya sani zai iya fasa aurenta shiyasa ban sanar dashiba kar zafin yamin yawa amma har ƙasa na tsugunna ina roƙonsa yafasa auren bai fasaba, alokacin bawai tsabar soyayya ke ɗawainiya daniba ina tunanin tayaya rayuwa zata kasance ace yau mahaifina shine yake auren yarinyarda nayi soyayya da ita. Bazan iya juraba hankalina bazai ɗaukaba gashi alokacin narasa mafita aure kuma yinsa za'ayi babu fashi nayi kuka nayi kuka tun kafin auren soyayyarda nakeyi mata ta juye zuwa ƙiyayya ba ina damuwa akan cewa Baba zai auremin masoyiya bace ina damuwane akan Baba zai auri wacce nataɓa soyayya da itane."






ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




"Nashiga tashin hankali ƙunci da baƙin ciki gabaki ɗaya bana cikin nutsuwata alokacin bazan iya misalta yanayinda nake ciki ba hakan yasa naji bazan iya zama waje ɗaya ina kallonsu matsayin ma'aurata ba hankalina bazai ɗaukaba inaga zuciyata bugawa zatayi bazan lamunci ganinta da mahaifina suna zaune matsayin ma'aurata ba dukda cewa babu wani burbushin soyayyarta a zuciyata. Kawai na yanke shawarar nabar musu gidan gabaki ɗaya nadawo nan da zama ban daɗeba wani abun yasake faruwa Mummy ma tabar gidan a case ɗinsu da Mummy nasan akwai laifin Mummy aciki amma haushin yarinyarnan danakeji yasanya sam banmaga laifin mummyn ba, bawai ina faɗan hakan dan don zuciyata ba amma auren yarinyar nan da Baba yayi yana ɗaya daga cikin abubuwanda suka tarwatsa mana gida. Nidai anyimin naji babu daɗi shiyasa na yanke shawarar da zarar na girma bazan auri ƙaramar yarinya ba koda kuwa hakan ba haramun bane kawai neman zaman lpy ne" bayan yagama magana na nisa sannna nace.


"Amma daka sanarwa Baba alokacin may be da hakan bata faruba, kuma dama Allah yarigada ya rubuta cewa sai Baba ya aureta akwai zuri'a a tsakani and Anty ta canja sosai yanzu sam batada matsala A halin yanzu Baba yana buƙatar haɗin kanmu gabaki ɗaya kayi haƙuri komai yawuce ka ɗauketa matsayin matar mahaifinka dukda nasan hakan abune mai wahala amma kadaure"


"Da nayi hakan abaya amma banyiba nakasa tsayawa na fahimci Baba Amma nima ai basu fahimcrni ba kuma lokacinma dana tsaya nayi duba harda yarinta tunda ko'a yanzu na fahimci itaɗin bawai sa'ar aurena bace saboda tsirarrune daga cikin mutane suke samun sa'ar auren masoyinsu na farko wanda sukayi yarinta suka taso tare ni komai ayanzu yawuce a wajena kawai ina fata komai yadawo dai-dai a mazauninsa. sannan Kwana biyu zakiga ina yawan takura miki akn zancen mayafi inada dalilina bawai inayin hakan bane danna takura miki ba kina ɗaya daga cikin dalilan da yasa kan ahalinmu yadawo yanason haɗewa dan Allah marmeeyy ko nan gaba ko wani abun zai faru wanda zaisa kiji ba'ayi miki dai-dai ba dahar zaisa jiki bazaki iya jurewa ba har yakai ki saɓawa Baba kiyi hakuri ki nusarda zuciyarki ki taushi kanki karki bijirewa umarninsa. Baba yanada hope akanki karki karyarda yardarsa, yasanya yaƙininsa akanki fiyeda duk ƴaƴanda ya haifa saboda ke kaɗai kika tashi domin share masa hawaye kafin muma kika sanyamu a hanya dan Allah marmeeyy karki karya wannan yaƙinin da Baba yake dashi akanki saboda zai cutar dashi hakan saiyafi masa zafi fiyeda duk wani abunda ya taɓa faruwa a rayuwarsa. Kisani duk wani abunda kikaga Baba ya yanke akanki toh yayi hakane dan hakan shine yaga yafi dacewa da rayuwarki"


"In sha Allahu yaya nafaɗa ina sakin murmushi" shima murmushin ya maidamin Aysha wacce zuwanta kenan alokacin da nayi murmushin shima ya maida ta saki tsakinda ya sanyamu duka muka juya muna kallonta saida ta maida kanta gefe cikeda jin haushinmu tace.


"Ana nemanka" daga haka bata ƙara faɗin komaiba tajuya tayi ciki muduka muka miƙe mikabi bayanta sai da mukakai wajan 12:00am a wajan saboda a cikin gidane anata hira da raha amma gabaki ɗaya banajin daɗin zaman wajan saboda Aysha dake aikamin harara da wasu daga cikin ƴan Uwansu ni sam banason rikici dana haka ban kulata ba banaso na tashi kuma azargi wani abun. Dan haka na maida hankalina kan maryam mukacigaba da hira har aka tashi. Ana tashi muka shige ciki ashe har maryam ta lura irin harararda suke aika mana. Ina shiga nakira Hamma a waya dannasan yana zaman jirana saboda katse wayar nayi kamar yanda nayi tunani kuwa hakanne dan Hamma na zaune yana jiran kirana.
yana amsawa nafara dabashi haƙuri ya nisa kafin yayi magana.


"Baby yakamata kudawo gaskiya danni nagaji inaso naganki idan kuma bazaki dawoba zan biyoki abuja dan dama su Ummi sun kusa dawowa saina zauna najira dawowarsu" Nima nayi missing ɗinsa sosai kuma inaso naganshi hardasu Mama da Da anty dakuma ƙannena Amma banaso yazo nafiso kamar yanda yace Su Ummi suna dawowa zai sanar musu suzo su samu Baba maganar aurenmu gara ayi hakan. Cikin sigar kwantarda hankali nace.


"Hammana nima inaso naganka yazamemin dole nadawo acikin kwanakinnan gobe in sha Allahu zanyiwa mummy magnar dawowa duk yanda mukayi da ita zan sanar dakai"

"Yawwa gara dai baby danni na gaji da zamanki acan" murmushi kawai nayi mukacigaba da hira har sannan mukayi sallama. Washe gari dayake babu waani event baccinmu mukasha da safe bamu muka fitoba sai wajajan 12 gabaki ɗayanmu a falon Mummy muka zauna muna hira Anty fadeelah ta lurada yanda nida Aysha muke share juna dannima na ɗebeta na watsar ko yanda take bana kallo tanaso tayi mana magana batayiba har mukayi sallar azahar muka dawo Alokacin cousins ɗinsu suka shisshigo mata da maza masu bala'in jida kansu. Suna hirarsu basa sakamu aciki gara mazan akan matan. Muna zaune ya Ahamda suka shigo shida Yaya Habibu ina jiyo ɗaya daga cikin ƴan matan tana taɓo Aysha tana faɗin. Ga brother ɗinkinnan yashigo danake faɗa miki kuna kama sosai amma wallh yafiki kyau dan Allah ki amsamin lambar wayarsa. Yaya Habibu take nufi dan dama shida Aysha sunfi kowa kyau agidanmu su sukayi kama da Baba dukda itama yafita kyau na ƙyaɓe baki iraina ina faɗin ƙwalelenki bazaki yimin wulaƙanci ba kice kinason yayana" Maryam ma sai harararta takeyi dan taji abunda take faɗa. Su ya Ahamd suka ƙaraso ciki sunata tsokanarsa ango. Na gaidashi da fara'a ya amsa yana zama kusada ƴan uwansa maza. Aka gaidashi sai bayan sun ɗan taɓa hira sannan yace.


"Au marmeeyy kinga namanta ansamu wayarki sai dai ta fashe layin kawai aka cire amma Ansai wata" na kalleshi ina masa kallon tuhuma inaso na gaskata abunda yake faɗa dan nidai nasan wancan mutumin yaɗauki wayata yaya akayi tazo hannun Ya Ahmad? Kodai Yaya Ahmad yanada masaniya akan Mutumin canne? Toh idan mutumin yaɗauka yabawa sucurities su kuma suka nemi Ya Ahmad ɗinfa? Wata zuciyar ta tambayeni na sauƙarda ajiyar zuciya. Shikuma ganin irin kallonda nake masa yasanya yasha jinin jikinsa ya kauda kansa sai yake kallon kamar ta fahimci wani abunne. Toh bama anan gizo yake saƙarwa wayarda Hammood ya aiko abata tayi tsada sosai anya bazata zargi wani abunba kuwa?".






ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Amma yaya zaiyi? Dole yabata wayarda mijinta yasaya mata tunda yanada hakki ya saya mata abunda yaga dama. Kuma ya tabbata ita kanta zataji daɗi idan taga wayar dukda yasan zata zargi wani abun. Jaka ya miƙomin yace.


"Ga sabuwar wayarki nan saiki buɗe kigani" na amsa cikeda murna ina faɗin.




"Yaya kaika siyamin? Murmushi kawai yayi bai amba dan bazai iyayin ƙarya ba. nafara masa godiya.


"Nagode sosai Allah yasaka da alkairi ya ƙara buɗ... Maganata ta ƙaƙare alokacin na ƙarasa ciro wayar na zaro ido da mugun sauri na ɗaye ledar naduba ciki tabbas wayarce aciki ƙirar Samsung latest Version ɗinda sukayi releasing kenan na tsaya ina kallon wayar da mmaaki ina kallon ya Ahamd shikuma yaƙi kallona. Kusan kowa aɗakin idsnuwansa yana kan wayar gabaki ɗaya cikin wajan harshi kansa ya Ahamd babu wacce wayarsa takai wannan amma bawai danta fi ƙarfin sayansu bane. Wani mugun tsakinda Aysha tajane ya sanyi juyawa na dubeta naga tana harara na. cikin ɓacin rai take faɗin.




"Zaku fito ku faɗi abunda yake ɓoye inbanda rashin gaskiya zai saya miki wannan wayarda koshi kansa baida kamarta za'a tsaya ana renawa mutans hankali" natsaya ina kallonta kawai da mamaki ban fahimci abinda takeso tace ba amma gabana faɗuwa yakeyi ƙirjina yana bugawa saboda nakasa gane abunda take nufi. A hasale nace.


"Me kike nufi? Kefa kwanakinann naga kina nemana da magana bansan mena miki ba kikejin haushina dan nazo cikinku ba hakan yana nufin zan ɗauki wulaƙanci ki faɗamin duk abunda kikaga dama ba"


"Da wani yasa kizo cikinmun? Angama bikin ai saiki tattare kitafi tunda nan cikin ƴan uwanmu ne ba naki ba inbanda azabar shishhigi da cusa kai wai uwarda ta haifemu ma tafi sonki akanmu" yaya Ahamd ya daka mata tsawa cikkn ɓacin rai. Ni kaina raina yakai ƙololuwa wajan ɓaci hawaye yafara zarya a idanuwana shi kansa yaya Habibu kawai yayi ƙoƙarine yayi controlling kansa. Ina miƙewa na ɗaga wayar hannuna na daidaici ƙirjinta na maka mata da ƙarfi saida tayi ƙara. Cikin kuka nake faɗin.


" akan wannan kike gayamin magana koh? toh ki riƙeta ina faɗin haka nabar wajan" anty faɗeela baƙin cikkn abunda aysha tayi ya maimayeta takasa cewa komai Ya Ahmad yanaji kamar ya rufeta da duka dan takaici" cikin jin zafin yanda na maka mata waya ta buɗe baki zatayi magana anty fadeela ta make bakin.
Tna kuka take faɗin.


"Bagashi ba ta gayamin magana babu wanda yamata magana amma ni ina faɗa mata dukanku kunji haushina nice wacce muka fito ciki ɗaya daku amma ita kukafiso" a hasale anty fadeelah tace.


"Banza kema ki gyara halayanki su dawo irin nata mana kiga ko baza'a soki ba" tana faɗin haka tatashi tabi bayana nikuwa ina komawa ɗaki harna fara kuka sai naga menene ma amfanin kukan da zanyi harme yafaru haka da zanyi kuka dan haka na share hawayena na zauna kawai ahaka tashigo ta sameni ganin bana kuka ko ƙoƙarin haɗa kayana da niyyar tafiya sai hankalinta ya kwanta tana zuwa ta zauna gefena tana rarrashi. Nace mata ni babu abunda yafaru tunda na rama daban rama abunda tamun bane shine zan zauna nayita jin zafi araina amma banda yanzu dana rama. Daga nan har muka fara hira muna dariya itadai tanata mamakin wani irin hali nake dashi haka da sam ban iya riƙo araina ba."


Mummy tashigo tasamu abunda yake faruwa dan ya Ahmad ya kirata tayiwa Aysha magana idan shine yace zaiyi mata magana yanaga zai fara karyata tukunna. Dataji abunda yafaru ranta yayi masifar ɓaci dan haka tasa aka kiramu nida anty fadeelah da sauran wanda suke wajan abun yafaru duka ta haɗamu. dake kusan kowa yana tsoronta har yayyunta maza shakkarta suke bare ƴaƴansu.
Saida tafara da faɗa sosai.


"Dan Ahmad ya siyawa marmeeyy waya shine kike tada jijiyar wuya kuɗinki ko nasa? Idan yaga dama ya cire kaff dukiyarsa yabata yanada damar yin hakan kuma babu wanda zai tuhumeshi tunda nasan kuma marmeyy ta cancanci fiyeda haka har zaki mata gorin gida wai tatafi. Toh kema zakizo kitafi tunda ba gidan ubanki bane sai ki koma gidan naki uban nan ni kaɗai nakeda iko nida ya kasance gidan ubana ba na ɗaya a cikinku ba" sannan kuma ta sauƙo tana faɗin.


"Nasan zakuga kamar nafison Marmeyy akanku ku yarana dana haifa a cikina ni kaina banida wannan amsar banta tabbacin da marmeeyy daku waye nafiso amma abu ɗaya nakeda tabbaci shine kaff cikinku babu wanda ya fahimceni kamar yanda marmeeyy ta fahimceni babu wanda yakemin uzuri kamar ynda takemin babu wanda yasan ciwona sai ita ban tsugunna na haifeta b aamma abunda yakamata wanda na tsugunna na haifa Yakamata suyi itace takeyi toh ina laifi dan na bata matsayin abunda na haifa? Tunda nabar gidan mahaifinku cikinku babu wanda yataɓa tunkarata da maganar ko maganar mahaifinku amma ita tayi ta fahimci ciwon aita kaɗaice ta kalleni ba irin kallonda duniya takemin ba. Ko ɗaya a cikinsu babu wanda yataɓa tarɓata da murmushi saboda kuna tsorona inada zafin hali amma ita kullum saita yimin murmushi a cewarta inada hali mai kyau. Dan haka idan damaijin haushi acikinku toh yaji amma acikinku da marmeeyy bansan wanda nafiso ba kuma karna sakejin wani abun yataso. gabaki ɗaya jikinsu yayi sanyi Muduka muka bata haƙuri ya Ahmad ya amshi wayata ya bani."




Banyi amfani da wayarba na sanyata a cikin akwatina kawai na ajiye.




Da Dare Kuwa nasamu Mummy da maganar tafiya hankalinta yatashi tana tunanin ko abunda yafaru ne ya sanya nakeson tafiya nace mata dama ana gama biki mukayi akan zamu koma. Saboda Maryam su Umminta sun kusa dawowa Tace toh zatayi shawara tasaka mana ranar tafiya saita sanar dani ahaka muka tsaya da maganar nakira Hamma na sanar masa yanda mukayi da ita. Yayi murna danya matsu yaganni bayaso muyi saɓani dan shima abujan zaizo week ɗinda zamu shiga saboda dawowar su Ummi kuma zai jirasu kaman na 2days anan. Bayida tabbacin ko yazo nan mu haɗu shiyasa yafiso nadawo kafin lokacin tafiyar.






ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




A gidansa yasamu Nawrah tana zaman jiransa Baiyi mamaki ba dan dama yayi zaton hakan. Baibi takanta ba ya wuce Shashinsa bata bishi ba dan taga alamun a ynzu bayason hayaniya kuma dama shi kaɗai keda access da part ɗinsa. Aranta ta ƙudirta cewa bazata tafi ba Dole idan yafito zaiyi mata ƙarin bayani akan abunda yake faruwa. Yana shiga ya dannawa wajan lock yanda ko knocking tayi bazai jiyota. Har yanzu bai shirya basu amsaba daga ita har mum ɗinsa ajiye wayarsa yayi yashiga wanka yana fitowa ya ƙwanta dama already yayi sallah tareda mutanensa kafin yakaiga shigowa ciki.
ransa fesss idan yatuna cewa Yanzu Zaynab tazama mallakinsa sai yasaki murmushi ahaka Har bacci ya ɗaukeshi. Bashi ya sauƙo daga part ɗinsa ba sai bayan wajan 11hours abunda baiyi zato ba shi ya taras mum ne agidansa ba kasafai tafiya zuwa wajanda yakeba kmar yanda bai wani damuda itaba hakama itama bata damu dashiba kodan rashin damuwar tasamo asaline daga wajanta tunda sam bata damu ba yaranba har saida yaronta yazama wani a duniya alokacin sannan tafito takeson nunawa duniya itace mahaifiyarsa wanda shikum yaƙi yabata damarda zata shiga jikinsa sosai itakuma saita ɗauki hakan ta alaƙantashi da bambamcin al'ada dakuma addini dake tsakaninsu atunaninta alaƙarda take tsakaninsu zata gyarune da Zarar ta aura masa wacce takeso daganan zai dawo jikinta alƙarda take tsakaninsu kuma taƙara girma anan zai dawo yanajin maganarta. Ko dangin mahaifinsa bazata yarda ya aura ba bare kuma baƙar fata wacce ita batayi musu kallon cikakkun mutane.


Bayan ganinta saida yasha jinin jikisa saboda halin mitarta Amma yajaa yadake dake dama shi namijin duniya ne abune mawuyaci gane yanayinda yake ciki ya ƙaraso yaɓoye duk wani mamakin ganinta ya isa yazaun a kujera fuska babu yabo ba fallasa yayi mata barka da zuwa ta Amsa sannan cikin tuhuma Tafara magana da harashen turanci.


"What is happening. Word is spreading that you are getting married Ko akwai ƙarin bayani da Zakamin gameda haka?" Murmushi kawai yayi baice komai ba mum tace.




"Mood Say something. Speak up"
Ajiyar zuciya yasauke yatashi ya nufi fridge yadauki ruwa mai sanyi ya ajiye agabanta haɗeda sakar mata murnushi. Tarasa gane wane irin murmushine mood yakeyi haka danshi ba ma'abocin murmushi bane bare ma ita wacce dama jininsu bai haɗuba. Batareda ya tsaya ya sauraresu ba yayi ficewarsa gabaki ɗaya yabar gidan kwananta biyu a ƙasar bata sake sanyashi a idanuwanta ba Mood ya bar ƙasar gabaki ɗaya saida tagaji dakanta takoma ƙasarta wayarsu kuwa kosun kira bata shiga kamar wanda aka datse layinsu gabaki ɗaya itada Nawrah a layinda zasuna kiransa dan sam baya shiga. Wannna abunda yayi yasake tabbatar musu da abunda sukaji gaskiyane dan Mood baya ƙarya duk rashin daɗin abu bazai iya cewa ba haka bane gara yayi shiru.
Mum bata bar ƙasar ba har saida ta tabbatar ta nunawa Nawrah hanyarda zata samo musu amsa wajan mahaifinsu.



Shim Nawrah tun kafin tazo nan tayi- tayi yafaɗa mata yaƙi danya kasance mutum mai riƙe amana tunda yayiwa mahafin Marmeeyy alƙawarin bazai sanarwa kowa ba tofa bazai faɗa ba danshi riƙon alƙawari yana ɗaya daga cikin sanannun halayansa. Duk wani abinda akace alƙawari toh angama tashi dan zai iya bada rayuwarsa akan hakan. Ko ita nawrah batada masaniya cewa mahaifinta yayi alƙawari dan da bazama tafara tunkararsa da cewar tanaon tasani ba danko kasheshi za'ayi bazai faɗa ba.


Itama Nawrah tagaji da zaman jiransa tatafi abunta dan batada tabbacin lokacin da zai dawo zai iya tafiya babu wanda yasan yanda yake his whereabout remain secret har sai randa yadawo dan kansa dagashi sai masu yimasa hidima yake tafiya.


_____


Bayan 2days dayiwa Mummy magana ta shirya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads