Showing 135001 words to 138000 words out of 171869 words
Chapter 46 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
tambayeta yanda nake tace ita tunda tazo gidan sau uku taganni kullum ina ɗaki. Dake baya wuni a gida bai sanda hakanba. Nakira Maryam muna video call yashugo. Maryam tanajin muryarsa tace.
"Toh ga masoyi yashugo matar Hammood sai aje ayi attending ɗinsa idan Angama a kirani dan kune hajiyoyi yanzu ban isa da kiran ƙasarnan taku ba" ban kaiga bata amsa ba ta datse. Sannu nayi masa ya ƙaraso ya zauna.
"Kinci abinci?" na jijjiga masa kai.
"why? Bakison cin abinci kuma bakyson fita killum kina ɗaki wannan gidanki ne idan baki sake ananba a'ina zaki sake?"
"Babu"
"Okay" ki zauna da Nawrah zatana ɗebe miki kewa kingani yanzu ina busy koh?" na jijjiga kai.
"A'a"
"Bakyason zama da itane?" saida natsaya nayi nazari sannan nayi magana.
"Ni bance ba naga kai kanka ɗan uwanta baka zama da ita baka kula da ita"
"I'm busy shine dalilin"
"No meyasa koda kana busy baka rasa lokacin da zaka waremin?"
"Saboda you're my wife and banason kiyi zaman kaɗaici"
"Wannan fa ba dalili bane, tazo wajanka zataga kamar ka shareta ne koni danake gefe na lura kamar bakason mu'amala da mutane"
"Zama da kowa bayamin daɗi Ke kaɗai ce kawai nakejin daɗi idan ina tare dake.
"menene dalili"
"Saboda ina sonki"
"wannan bashi bane dalilin. Dalilin shine saboda ka saka a ranka tun dama can zakaji daɗin rayuwa dani da zaka bawa sauran mutane irin damar daka bani na gane wane ne kai lokaci guda da zakasha mamakin yanda zakaji daɗin zama da mutane. Ni inajin daɗin zama da ƴan uwana yanda idan bana cikinsu nakanji kamar duniya bazatayi daɗi ba nadawo wajanka da saka ran samun farin ciki wajan naka ƴan uwan amma meh?" kai baka sakewa da ƴan uwanka a tunanina idan ka ɗaukeni ka kawoni nan ƴan uwanka zasu zama nawa har naji daɗin rayuwa nima. Amma Bahaka ba kaima kanka baka samu sakewa da ƴan uwanka ba bare ni danazo daga baya kawai zanyita zama cikim kaɗaici ne" nafaɗi hakan hawaye na gangara akan fuskata. Hannunsa yasa yana sharemin hawayen fuskata. Allah yagani yawan kukana yana damunsa danko yana farin ciki yakanji ɗaci aransa yarasa abunda zaiyi nadaina kukannan.
"Kina tunanin samun kusanci da ƴan uwana da zanyi shi zai basu kusanck dake?" na jijjiga kaina.
"Toh idan hakane zan samu kusanci dasu sosai yanda zakiji kaman kina gida, dan Allah ki taimaki rayuwata kidaina kuka idan kika sake zubda hawaye kinamin nuni da bakison nayi winning cup ɗinnan. Hawayenki are my weakness" dasauri na share hawayen dan banaso naji yayi zancen rashin winning cup ɗinnan.
Yana zaune a wajan ya turawa kitchen saƙon abunda yakeson su dafamin muna zaune har aka gama suka sanar dashi muka fita sai yana zune harna gama cin abincin na shirya Nawrah ta saƙƙo. Yayimin sallah ma akan akwai abunda zai fita yi nayi masa sallama na haura sama. Wajan Nwrah yabi tana zaune.
"مرحبًا Mood حبيي" Da murmushi ɗauke A fuskarsa ya shafo kanta.
"حبيتي Zan fita for wani lokaci take care okay?" ta gyada kai tana mamakin Mood da yakan tafi yabarta a gida sai dai idan tagaji da zama takoma gida. Har yakai ƙofa tace.
"Mum Will be here by 7pm"
"Okay I'll be home by then in sha Allah" mamaki ya kashe Nawrah dan tasan halin Hammood haka kawai idan yasan mahaufiyarsu zatazo yakan ƙi dawowa dan gangan wani lokacin kuma yadawo sai ɗaya idan yafita bazata sake ganinsa ba har sai tagaji dan kanta takoma kuma sam bayaso tazo yanda yake. Amma yanzu wai shine yake cewa zai dawo gida kafin isowarta ma bayan yasan yamata laifi dole zasu ƙwashi ƴan kallo." Hammood yafara canjawa dam da sam bahaka yake ba baisa sake wai ahakanma itace suke shiri dan babu yanda ya iya ta ita ko sun ɓata sai sun shirya."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Bayan Magrib Mood ya dawo gida yasamu Mum bata iso ba. Bayan ya shiga ɗakinsa yayi wanka ya shirya sannan ya fito zuwa ɗakina dan yasan ina zaman dana saba da iya yiwuwa tun fitarsa ban leƙo ba.
Kashe AC ɗakin nayi bayan ɗakin ya ɗauki Sanyi kamar yanda nasaba dai doguwar riga ce a ajikina kaina babu ɗankwali na kama gashin dake yanada cika sosai ina shirin cire rigar jikina na zauna da ƙananun kaya naji shigowarsa godiya nayi ga Allah da ban kaiga cire rigar ba Shi haka kawai sai yana shiga ɗaki batareda ya nemi izinin shiga ba
ƙananun kayane a jikinsa farar T-shirt da Short trouser bai ƙarasa guiwa ba farar tafarsa sai sheƙi da yalli take kamar wanda aka yita da dutsen lu'u-lu'u yayi matuƙar kyau sosai sai dai tunda na kalleshi sau ɗaya na kawarda kaina wata irin kunya ta rufeni nasaba yimasa kallo a yanayin dayafi haka ma tunda ina kallonsa da gajeren wanda na ƙwallo A TV banyi tunanin haka zanji idan naganshi a fili ba.
lumshe idanuwa na nayi a lokacin daya ƙaraso ya zauna kusa dani a kullum ƙamshin turarensa sabunta yakeyi a hancina nakanji kamar alokacin nafara shaƙarsa kuma akoda yaushe naji sai ya sauƙarmun da nutsuwa duk da ya kasance a halin yanzu nima irin ƙamshin da nakeyi kenan amma nasa danakeji a jikinsa yafimin daɗi. Sauƙar ɗumin hannunsa danaji akan wuyana ya sanyani buɗe idanuwa Na sauƙesu akan kyakkywar fuskarsa saida na Shaƙi numfashi Izuwa cikin cikine a raina nake yiwa Allah godiya daya mallakamin Hammood a matsayin miji ko a mafarki bantaɓa tunanin mallakar mutum kamarsa ba sai gashi baga wayona ba ba dabara ba Allah yabani shi kuma yayi ikonsa akansa ya sanya yakeyimin soyayyar da ni kaina bana tunanin ina yiwa kaina. Fuskata tana kan tasa ina ƙarewa kyakkyawar fuskarsa kallo nakasa cewa komai.
"هل اشتقت الي"
(kinyi kewa tane) naji zazzaƙar muryarsa a cikin kunnena, na lumshe idanuwa na nasake buɗewa akansa sanna ajiayr zuciya ta biyo baya. Sai asannan na ɗauke idona daga gareshi bawai dan idanuwana sun gaji da kallon fuskarsa ba.
Rumgumeni yayi ajikinsa tsam dan atunanina kewarsa nayi yasa nake masa irin wannan kallon kuma tunanin bai bashi ƙarya ba. Luff nayi a faffaɗan ƙirjinsa ina shaƙar ƙamshin turarensa tsabar daɗi sai nakeji kamar wanda bacci zai ɗaukeni. A kunnena naji kuryarsa.
"I missed you More Rouhii, I whish Babu wani abunda nakeyi na zauna dake nabaki farin ciki" Na raba jikina da nasa na kalleshi. A fili nace.
"Kai kaɗaine ke kalaman soyayya batareda murmushi akan fuskarka ba kuma kalmar ta ratsa mai sauraro sannan su zauna a mazauninsu" Baisan abunda na faɗa ba kawai yana bina da kallo akwai wani abu guda ɗaya daya lura dashi game dani. Akoda yaushe yayimin wata kalma ta soyayya wacce bazan iya bashi amsa ba nakanyi da yaransa bazaiji ba. Koda a zahiri bai fahimci abunda nafaɗa ba jikinsa yakan bashi abu mai kyawu na faɗa.
"My mum will be here soon. Inason ku gaisa idan bazaki takura ba Will you please?" na kalleshi da mamaki. Maman nashine yake roƙona mu gaisa? Lallai Hammood shi wani irin mutum ne? Wace irin alaƙa ke tsakaninsa da mahaifiyarsa? Ko baki bai kaiga furtawa alamu ya nuna babu alaƙa mai ƙarfi da kyau tsakaninsu. Ban bashi amsa ba dan banga abunda zance ba shima bai sake cemin komai ba.
"Zan sauƙa May be ta iso" kai ja gyada masa kawai ya miƙe yayimin peck a goshi ya fice. Yana sauƙa kuwa yasamu ta iso. Da murmushi kwance a kyakkaywar fuskarsa wanda hakan ba sabonsa bane. Dan Hammood shi sam bama abocin dariya bane amma idan yayita takan fitarda duk wani sirrintaccen kyawunsa ta'iya yiwuwa ya lura da hakan shi yasa bayayinta. Akoda yaushe idan suka haɗu Mum ita ke ƙarasawa gareshi tayi hugging ɗinsa amma a wannan karon shine ya isa gareta da mamaki yayi hugging ɗinta yana mata barka da zuwa. Ita dai Hammood ya cikata da mamaki matuƙa ga wani yalwataccen murmushi dake kan fuskarsa. Kodan yasan Nawrah ta faɗa mata zancen Matarsa bayaso tayi masa faɗa ko yaya zaiyi saita masa faɗa dan zaizo ya maida yarinyar yanda ya ɗaukota shiyasa bata taho Hannu haka ba tazo masa da wacce takeso ya aura idanna zata bar masa ita anan saita barta daga baya aɗaura aure duk kuwa da sanin halayansa da tayi a wannan karon ya zama dole Hammood ya biyeta ba iya ta biyeshi kamar yanda aka saba ba. Yaro shine mai bin Mahaifiya amma ita itace kebin Hammood a duk abunda yakeso Amma banda wannan karon. Ta rafa cikinsa da nata fuska babu Annuri tace.
"Where is She?" Ya Haɗe rai sosai yadawo Hammood ɗinsa datafi sanin dan yagane wacce take tambaya.
"Who? Ya tambaya cikeda rainin hankali" caraf Nawrah ta kama.
"Your wife"
"Ki huta yanzu zamuyi magana yafaɗa fuska a haɗe yabarsu a palourn"
Har akayi isha'i bai shigo gidanba yana neman hanyar da zai ɓullowa Mum ɗinsa.
Nikuwa yana barin ɗakin nayi wanka na fito ɗaure da alwala dake naji kiran Isha'i saida nayi sallah sannan na shirya cikin doguwar riga mai kyawun gaske
Lipgloss kawai na shafa na gyara fuskata na saka hula ina zaune zaman jira shigowarsa. Saida Kyawawan Awa biyu suka shuɗe sannan naji shugowarsa ɗakin yanda na ganshi nayi tunani ya shigone yayimin sallama zaije kwanciya.
Ƙarasowa yayi ya zauna fuskarsa Babu walwala ina game a wayata na ɗago na kalleshi zama yayi ƙasa kusa dani.
"Wai zaman ɗaki baya damunki" na gyada masa kai.
"Meyasa kikeson saka manyan kaya? Suna miki kyai amma kina takura kanki" na girgiza masa kai alamun ni basa takurani.
"Kinajin kunya nane?" ban bashi amsa ba tunda yasani ai bai kamata ya tambaya.
"Thi is Your Home kina saka kaya the way you want kidaina saka manyan kaya idan ba fita zamuyi ba" Nanma kai na gyada masa.
"Zaki ƙwana ɗakina?" naji tambaya asam da sauri na kalleshi ni yake kallo Babu murmushi ko alamun wasa a fuskarsa. Girgiza kai nayi.
"No zanfi jin daɗi anan"
"Mum ta iso I'm sorry Amma bansan yaya zata ɗauki lamarinba. nafiso Ki zauna kusa dani Hankalina zaifi kwanciya" Alamun damuwa ƙarara da bayyana akan fuskarsa.
"Muje mu gaisheta"
"No idan bakyaso karkije kiyi zamanki"
"Inaso shiyasa nace muje"
"Ya Rouhi nace miki bansan Yaya Mum zata ɗauki maganar aurenmu ba"
"Koma Yaya zata ɗauka ai ita uwace tanada ikone yasa hakan Kabarta ta gudanarda ikonta aynda taso"
"Banason abunda zai ɓata miki rai domin na tsamoki daga cikin danginki na taho dake ƙasarda ba taki ba da saka ran zan baki farin ciki banason alƙawarina ya fara karyewa daga yanzu"
"Ni nace baka bani farin ciki ba? idan nace haka ban zamto daga cikin mata masu karamci ba. Na lura tun zuwana babu wani abunda kakeyi sai ƙoƙarin farantamin"
"Bazaki barni ba idan mum ta faɗa miki magana?"
"No bazan tafi ba mu aurenmu Ba'a tafiya haka kawai da zarar an faɗi maganar da bata gamshemu ba aurenmu shine abu mai muhimmanci a rayuwarmu inaga yanda kuka ɗauki aure da Bambamci da yanda muka ɗauka abun har bai kai kayi tunanin zan tafi nabarka ba. Kowace mataltakalar jarabawa in sha Allahu zamu haura dakai a tare idan takama mu sauƙo haka zamu sauƙo atare idanda iko Hannunmu na riƙe dana juna dan tallafawa junanmu" da mamaki kawai yake kallona yana nazarim kalamaina tareda sanyasu a miazani yana aunasu yana ajiye kowacce a muhallinta. Idanda rubutawa nayi zaice ƙwafa nayi dan zancen hikima ne daya wuce ace mace mai shekaruna ce take furtasu zancene da ake jinsa bakin macen data cika shekaru sannan tazama malamar hikima.
"Shekarunki nawa?"
"20 nabashi amsa.
"No you're 19"
"Ashe kasani kake tambaya" nafaɗa cikin harshen hausa"
"Kalamanki si beyond shekarunki hankalinki yawuce girman jikinki, ina tsoron rasaki dan a kullum kina zuwamin da bazata da suke sakawa nake ƙara sonki inada rauni sosai a fannin soyayyar ki"
"Tun a tafiyar farko menene ya jawo hankalinka kafara sona da har kake tsoron Rasani? Menene dalilinka na mun irin wannan soyayyar"
"Babu komai bana buƙatar dalili a yayinda zan faɗa soyayya sannan kuma bana buƙatar wani abun jan hankali kafin na fara soyayya komai yafaru a yanda a yafaru alokacin daya kamata ace yafaru kuma babu dana sani gameda abunda yafaru sai godiya da yakamata kullun ina yiwa ubagiji Mahalicci daya mallakawa zuciya abunda take da burin mallaka abunda take ƙwana da tashi dashi a cikinta" kalamansa sun narkamin zuciya da nake tunanin babu wani abunda zai zo ya iya daskarar da ita.
"Zaki koma ɗakina daga Yau though We're leaving in 2daya" kamar wata sakowa na girgiza kaina alamun amincewa kamar wacce aka sakawa raƙumi akala.
"Lets meet her and don't be afraid I thought zaki tafi kibarni da barazanarta tunda You're not zan kareki tako wace hanya"
"Shhh she's your mother banda ta ko wace hanya akwai hanyarda tafi ƙarfinmu mubita da addu'a Ai babu abunda yafi ƙarfinta" daɗi yakeji sosai aransa ganin Marmeeyy zata tayashi yaƙin ayanzu yasake samun ƙwarin guiwa haɗeda saka ran samun nasara.
Na miƙe ganin yasa shina miƙewa muka fice yasan tana zaune a ƙasa tana zaman jiransa hakan yasa kai tsaye ya nufi can.
Jin takun sauƙowarmu ya sanyasu ɗagowa sai dai ya tareni dan nice a baya gabaki ɗaya bata ganina. Fuska babu fara'a kamar yanda shima tasa Babu fara'a.
Muka ƙarasa sauƙa ranta yakai ƙololuwa wajan ɓaci dataganni batayi tunanin bayan Baƙar fatar harda yarinta ba me hammood yake tunanin yaje ya auro wannan abin? Ita ɗan kyawun da Nawrah tagani ma ita bata gani ba. Riƙo hannuna gam yayi ina taso na raba hannuna da nasa dan kunyar da nakeji.
"Wannan itace matar taka? Mum tafaɗa cikin ɓacin rai. Alokacin taja hankalin matashiyar matar da take zaune akan dining ganin Hammood ya sanyata sauƙowa daga dining ya nufo wajanmu da takun takaminta ɗass-ɗass hakan yasa najuya wajanta ina kallonta. Takamine mai uban tsini a ƙafarta da doguwar riga wacce ta kaɗan ta rufe mazaunanta. Kuma ta kamata tamm-tamm gefe da gefan cikinta a waje suke har zuwa bayanta kusan rabin breast ɗinta a waje suke daga hips ɗinta zuwa breast kamar an hura balan-balan kayane a jikinta amma marabarta da tsirara kaɗanne. baturiya ce tanada kyau sosai dan fuskarta kamar wata ƴar tsana. Ta zuba gashin ta gefe. Na ɗauke kaina dam haka kawai naji takaicin kallonta. Tana zuwa ta shige jikin Hammood tayi hugging ɗinsa tsamm wani baƙin ciki ya sakani sake hannunsa da sauri nan da nan zuciyata tafara bugawa da sauri-sauri."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Ya matuƙar girgiza da jinta jikinsa duk da ba wannan bane karo na farko akoda yaushe idan haɗuwarsu ta kasance hakan take Masa amma wannan karon yasha bam-bam, zuciyarsa tanata zillo daga ƙirjinsa kamar zata faɗo tsoro da fargaba suka samu muhallin zama acikin zuciyarsa. Sida ya juya gefensa sannan yasamu cikekken dalilin tsoronsa nasa. Tsoro yashige saboda kasancewtaa a kusa dashi baisan Yaya zan ɗauki lamarinba dasauri ya juya gareni yan kallona raina yayi masifar ɓaci sai inaji kamar zuciyata zata ɓalle ta faɗo ƙasa dan baƙin ciki. Wata irin harara da sakar masa ga mamakina murmushi yayi kamar wanda yakeson yin dariywa wa hararar tawa.
Shikuwa ganin Hararar sai yaji daɗi aransa har yanzu baida tabbacin ina sonsa ko akasin haka amma yanzu yagani koda bana Sonsa yanzu nafara ɗaukar hanyar yin hakan kishi ƙarara yagani cikin ƙwayar idanuwa na. Raba jikinsa yayi da nata ya batareda ya sake bi takanta ba ya dawo bayana ya sanya hannu ya rumguneni.
"You look cute when you're jealous" abunda ya raɗamin a kunne kenan fuska sake. Raba jikina nayi da nasa batareda na kulashi ba dan har lokacin raina a ɓace yake wajan Mum na wuce na zaune ƙasa da kujerar da take zaune cikin girmamawa da ladabi na gaisheta. Ta kalleni Bata kulani ba taba ƙaremin kallo. Babu abunda ta hanga face nutsuwa da girmawaa sani darajar Manya a tattare dani. Cike da izza da nuna ƙyanƙyami tafara magana.
"Me kike tunanin kanki da zaki auri Hammood? Kinsan matsayinsa a duniya? Ke mecece taki matsayin? Who the hell do you think you are? In banda abun kunya me shiga family ɗinmu da kikayi zai jawo mana? Ko nawa kikeso zan baki amma ki fita a harkar Ɗana kibarshi ya auri dai-dai dashi. Dan baki kai darajar takalmin da yake sakawa ba."
matuƙar ɓacin rai Hammood yashiga idonsa har rinewa yayi cike da zafin zuciya yace.
"Mum stop, ba laifinta bane ai nine na ganta naji ina sonta bam tsaya ba har saida na mallaketa idan da wanda zaki faɗawa magana ba kowa bane nine"
"No Hammood bakina bai taɓa furta mummunan kalma akanka ba kuma a kan wannan abun da bazan faɗa maka ba. Bazan bari tazauna a ahalinmu ba