Showing 150001 words to 153000 words out of 171869 words
Chapter 51 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
da dare za'ayi tun safiya Hammood yabar gida ko ganinsa banyiba ana saura 1hour afara match muka hallara a cikin fili gabaki ɗayanmu kamar kullum wajan kallon match ɗinmu na musamman ne muna zaune anata shiga fili match saura 30minute za'a dakata da shiga. Wani labarabe yashugo wajanda muke bayan ya nemi izini ya shugo kai tsaye wajena yaje yabani waya na amsa ina karawa a kunne nayi shiru daga cikin wayar Hammood yace.
"Rouhii kina jina?" dasauri na amsa.
"Kibi wannan mutumin kizo wajena yanzu ina jiranki kinji?" kamar yana kallona nayi nodding head ya kashe wayar na miƙa masa wayar ya amsa matar Ya Ahmad kawai nayiwa sallama kuma da hausa itama ban faɗa mata yanda zanje ba. Bana takura kaina idan su mum suna waje nace sai nayi yaren da sukeji yaranda nafiki kawai nakeyi. Sunaso susan yanda zanje amma babu halin tambaya barinma Lina da Mum wanda sunada tabbacin wajan Hammood zanje.
Ƙyerarren wajena wanda aka yishi dan zallan players wajen wanda aka musu kamar na hutawa temporary accommodation ne mai tsarin gaske bayida Girma mutumin yana kaini bakin wajan ya juya nikuma nashiga ɗan ƙaramin bed ne aciki kuma anyi musu shine dan hutawa. Yana tsaye Yarigada ya shirya cikin kayan ball har takalmi akwai a ƙafarsa. Na ƙarasa na zauna jikin gadon.
"Bakayi late ba kuwa? Baifi saura 55minute ba afara wasa naga kuna halarta dawuri" ya kalli agogon dake jikin bango sannan ya juyo gareni.
"Eh nayi latti Atleast yanzu saina sake ɓata wani 15minute tareda Abun ƙaunata" nayi murmushi kawai nima inajin sonsa araina. Tsawon 2minute muna zaune babu wanda ysake cewa komai kuma dama hakan sabonmune ni ina kallon bambamcin yare dake tsakaninmu ne yajawo hakan.
"Rouhii kinyi shiru kina shiga lokacina bazan samu Goodluck kiss bane?" kaina yana ƙasa nace zaka samu"
"Okay kiss me" na maƙe kafaɗa,
"No kai kayi"
"nafiso kiyi da kanki naki yafi daɗi" Murmushi kawai nayi na sake yin ƙasa da kaina. Hannuna yakama ya ɗagoni ya manna jikina da nasa wuyana yasanya hancinsa yana shaƙar kamshin dake fita alokaci guda kuma naji sauƙan lips ɗinsa akan wuyana dasauri na maƙale wuyan saida naji tsikar jikina ta zuba ya sanya hannu ya kama waist ɗin ya haɗe fuskata da tasa saida na tattaro jarumtata kafin na ƙarasa masa abunda yake shirin yi, cikin nutsuwa nafara kissing dinsa dafarko tsayawa yayi kawai yana ƙarɓan saƙon danake aika masa sai daga baya sannan yafara maida mun martani mun ɗauki tsawon lokaci ahaka kafin muka daina kissing juna amma har lokacin lips ɗinmi na manne dana juna muna sauƙe numfashi. Wani irin sonsa da ƙaunarsa yake yawo a cikin jikina wanda yasa tsikar jikina sai zubawa takeyi zuciyata tana bugawa da ƙarfi laɓɓana sun kasa ɓoye abunda yake cikin zuciyata da gangar jikinsa saida suka wanzar dashi izuwa kunnuwan Hammood.
"Ina sonka Hammood, أحبك, I love you" duk yaranda na tabbatar yanaji saida na bayyana masa soyayyata dashi" a bazata yaji waɗannan kalmomin da baiyi zaton samunsu da sauƙi hakaba ya ɗago haɓana yana ƙarewa fuskata kallo yanaso ya tabhatar cewa nice na faɗi hakan batareda ya nema koya tilastamin ba dan raɗin kaina kawai na faɗa"
"Zaynab" ya kira sunanna ayayinda yakasa ɗauke ido daga kaina, a hankali na buɗe idanuwana akansa yasaka ƙwayar idanuwansa cikin nawa ya tabbatar da abunda nake faɗa daga zuciyata yake lips ɗinsa ya ɗaura akan nawa amma ba kissing ɗina yakeyi ba kawai yana motsasu ne ahaka nagane abubda yake faɗa sakeni yayi ya rumgumeni a jikinsa batareda yace komai ba sai dai bugun zuciyarsa ya tabbatarmin da halinda yake ciki. Mun ɗauki tsawon lokaci ahaka munwuce 15minute dayace saida akayi knocking anzo nemansa sannan ya sakeni har bakin ƙofar yanda muke ya rakani sannan ya juya yakoma zuwa ɗakin da suke taruwa kafin afara wasa.
Muna zaune har aka fara shugowa filin Aka fara wasa. Cikeda ƙwarin guiwa Hammood yakw buga wasa kana ganinsa za'a fahimci tsantsar farin ciki da nishaɗi dayake ciki Final ce wasan amma zance kusan kaff match ɗinda yabuga a worldcup itace tazo masa dasauƙi. Cikin lokaci ƙalilan sukayiwa wanda suke wasa fintinkau tun alokacin aka fahimci wanda zasuci cup ɗin wannan tun kafin atafi Fisrthalf kenan. Bayan andawo ana tunanin wasa zata canja salo sai zafi da salon su Hammood da ƙara ya riƙe wuta yaƙi basu damar da zasu samu taɓuka wani abun haka kawaima Hammood ɗan wasane na gaske bare da dalili. Ba ana tashi muka dawo gida ba saida muka tsaya mukaga Hammood ya amshi cup ɗinsu da Hannunsa Yau muda su Mum gabaki ɗaya babu bambamci kowa murnarsa yake batareda damuwa da wanda yake kusa dashi ba. Muna zaune ciki Hammood yasamu ya suɓule yazo cikinmu muna zaune muka nemeshi cikin ƴan uwansa players muka rasa saijin shigowarsa muka wajan Mum ya fara wucewa ya rumgumeta cikeda murna Nawarah ma tabishige cikinsu suna rumgume da juna saida ya sakesu sannan yayiwo wajena Lina bata bari ya ƙaraso ba ta rumguneshi tana ihun murna bansan sanda tsaki ya suɓucemin ba na haɗe girar sama da ƙasa raina yayi bala'in ɓaci hankalin Hammood yana kaina yayi saurin raba jikinsa da nata yana yaƙe bayaso yabata kunya cikin mutane. Yayi wajan da nake dasauri na juya baya hawaye na shirin zubamin kamoni yayi ta baya ya rumgume yana bani haƙuri ƙin kulashi nayi naƙi juyowa kuma saida ya sakeni ya juyo dani Gareshi har lokacin fuskata tana turɓune.
"Banace kiyi haƙuri ba Rouhi?"
"Kullum haka kake faɗa kace bazaka ƙara ba kuma kana ƙarawa kasanfa abunda kakeyi babu kyau"
"I know in sha Allah daga yanzu bazan ƙaraba" murmushi nayi ya mannani jikinsa ashe duk abunda akeyi Yaya Habibu na video dayake wayata tana hannunsa har indai za'ayi match ita yake amsa suna Video call da Maryam. Mum taɓe baki kawai takeyi ranta yaɓaci tana ganin abun takaici tsaki taja. Pictures kawai muka ɗauka da Hammood yabar cikin wajan yakoma wajan players ƴan uwansa duk da haka mun ƙara kusan 1hour wajan har saida aka kusa kiran asubahi kafin muka tafi najira saita nayi sallah sannan na ƙwanta bacci mai daɗi ya ɗaukeni inajin yau nacika burina. Kiran Sallah azahar ya tasheni a bacci banyi nayi wanka kafin nayi alwala nayi sallah nafito wajansu Ya Ahmad nasamu har suna shirya kayansu hankalina yatashi sosai.
"Ya Ahmad yanzu tafiya zakuyi?"
"Me zamu jira Marmeeyy in sha Allah gobe zamu tafi tunda abunda ya kawomu angama sai gida kinga cikinta girma yakeyi sosai karta haihu ƙasarda batamu ba gara gobe mukama Hanya dama visa ɗinmu ta 30days ce. Kamar zanyi kuka inata roƙonsu. Matar Ya Ahmad dake zaune tana jinmu sai alokacin ta amshi zancen.
"Me zamu zauna muyi toh marmeeyy saimu baku space keda mijinki kusamu lokacin juna kinga dama bakya bashi kulawarda ta dace yanzu yanda akayi tsawon lokaci ana abu ɗaya kulawarki kawai yake buƙata domin jiki yayi tsami ya huta da matarsa sai wani zubin kuma"
"Anty dan Allah menene hakan? Keda zaki bawa Yaya shawara ku ƙara ƙwana biyu kece kike zancen tafiya yanzu?"
"Kefa marmeeyy na lura sam bakyaso ma ayi zancem kibawa mijinki kulawa koni nan mai tsaohon ciki babu abunda na ragi mijina dashi wallh gara ki ware a idonki ma kai masa hari ake bare, idan kika lailaye kayanki yanda yake sonki nan ko kallo basu isheshi ba wallh" Ya Ahmad yayi shiru yana jinmu yanajin daɗin faɗan da takemun ya lura lamarina saida jan kunne sosai. Yana gama haɗa musu kayan ya fice yabarmu zaune tana tamun faɗa. Ganin yafita yabata damar yin zurfi cikin maganar duk da dama shiya faɗa mata view ɗinsa akana zamanmu.
"Bansaniba amma jikina yana bani kamar baki sakewa Hammood jiki ya mallakeki matsayin matarsa ba idan Hakane kuwa kina gabb da tafka asara idan kina tunanin ta yanda nagane Marmeeyy kwata-kwata babu shaƙuwar ma'aurata a tsakaninmu ko hannunki ya taɓa saiki riƙe ƙwacewa wani lokaci ma ki buge duk abunda kike muna hankalce dake, gara ki gyara idan wannan labarin yaje gida ba Mama ba Har Mummy da kike kallon tana lallaɓaki ƙaniyarki zataci. Bari kiji ba ina fallasa miki asirin aure bane wani lokaci yazama dole afaɗa miki danki gane wallh tsufan ciki baisa nadaina bawa yayan ki hakkinsa ba koda sau ɗaya kuwa ko raina bayason hakan. Yakamata ace yanzu kigane yanda rayuwa ta dosa Hammood fa ba dutse bane namijine shi idan kikaƙi barinsa samin nutsuwa tattare dake bakisan halin da kike jefa shi ba bakisan wace irin wahala yake sha jafin ya iya jurewa ba bakisan kema kanki kina jefa kanki a cikin wani haline idan baki saniba" Idona na ciko da hawaye nace
"toh ni Anty waini nace miki haka?" Tayi murmushi.
"Marmeeyy wanda ya rigaka ƙwana ai zai rigaka tashi kedai ki gyara" miƙewa nayi nakoma ɗakina nayi la'asar daganan nakoma bacci sai daff magrib natashi ina zuwa ɗakimsu Wayam babu kowa babu kayansu nakira layin da ake samunsu yaƙi shiga.
Kiran Hammood nayi wanda alokacin yake shiga bai amsaba ya ƙaraso ciki.
"Yaya Ahmad basanan kuma kayansu ma bayanan shine abunda na faɗa masa daga shigowarsa ina shirin fashewa da kuka. Shi yasan sun tafi kuma yasan basu faɗaminba Ya Ahmad ya buƙaci hakan domin yasan zanyi rikici idan suka tashi tafiya.
Daƙayr Hammood ya rarrasheni nayi shiru bayan naaan cewa suntafi ne. Cikin rarrashin yacemun sunada dinner na celebration zanje? Nace bazanje ba babu yanda baiyiba nace bazan jeba. Shima dan yazama masa dolena amma da fasa zuwan zaiyi.
Tun 9 yashirya yafita bashi yadawo ba sai 2am lokacin ina bacci bai tasheni ba shima ya ƙwanta yagama da ticket da komai kafin yashugo da Sassafe zmaubar ƙasar."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
7:00am jirginmu zai ɗaga. tun kafin akira sallah yatashi shida kansa ya shirya abunda muke buƙata wanda zamuyi tafiya dashi sannan yayi raka'atanil fijr bayan ankira sallah ya tasheni yawuce Masallaci yayi sallah yadawo har lokacin ina ƙwance kuma bayan yatasheni kafin yafita amma baccin da nakeji ya hanani tashi. Zama yayi gefen yanda nake ƙwance cikin sanyayyar murya yafara magana.
"Rouhii tashi kiyi sallah kinji saiki koma idan lokacin tafiyarmu yayi ni zan tasheki" a hankali na buɗe idona na sauƙesu akansa. Na maida na lumshe lokacin kusan 6:00am na buɗe ido dakyar nayj toilet saida nayi wanka sannan nayi alwala nafito na gabatar da sallah. Ina kan sallah yafice bayan na idar Ban koma bacci ba saboda lokaci yaja ina tunanin koda na ƙwanta bazan wuce 30minute ba lokaci zaiyi. shashinsu Mummy ya nufa kai tsaye suna zaune su uku harda Lina. Ticket da passport ɗinsi ya kai musu dake suna Hannunsa ya Mum da Lina su UK Zasu wuce kai tsaye Nawrah kuma Kuwait. Mum ta dubeshi.
"Lina da Nawrah zasu bika Ba gida kowannensu zai koma ba" Nawrah tayi saurin cafewa.
"No Mum nidai I'm going Home nayi missing Abie ninace ya yankemin ticket na can" Mum ta kalleshi
"Tunda Nawrah zata tafi kutafi da Lina"
"No Mum please, dan Allah kibar wannan abunda kikeyi Babu yanda Lina zata bimu ni bama gida zan wuce ba zan kai matata gidane taga Mahaifanta and Mum dan Allah kidaina ƙoƙarin ala dole saikin haɗani da Lina ni bana sonta sonda nake mata kawai na kasancewarta ƴar uwata Mum ni banason irin wannan abubuwanda kikeyi. kwanakin baya abu kika sakamin cikin drinks saboda Lina a sonki da ita kinaso ki cutar da ɗanki, Mum ki tsaya daganan dan Allah idan so kike ki sameni ki samu kusanci dani nayi miki alƙawarin daga yanzu zaki samu kusanci dani fiye da kowane irin lokaci a rayuwarmu idan kinaso nazo yanda kike akai-akai zanna zuwa idan kinason abu kawai ki faɗanun zanyi amma abun bazai shafi matata ba zai tsayane a zallan kaina nine ɗanki please Mum kibarmu muyi rayuwarmu" yafaɗa fuskarsa Babu alamun wasa. Mum me take buƙata Banda wannan? Iyakacin abunda takeso kenan samun kusanci da ɗanta amma tayaya zuciyarta zata amince da wannan zaɓin nasa a matsayin matar ɗanta? Bayan tasan sam wannan zaɓin bai dace dashi ba. Saida tayi tunani ta auna ta murza sannan tayi magana.
"Is okay zan tafi da Lina kuma bazata sake shiga rayuwarka ba Just keep your words nima zanyi keeping nawa" murmushi yayi ya rumguneta yana mata godiya. Yana fita lina ta dubeta.
"Mum me kike nufi da zaki tafi dani bazan sake shiga rayuwarsa ba? Ko kin faɗi hakanne saboda ganin idonsa?"
""No lina abunda nakeso daga gareshi shine kusanci kuma yayimin alƙawarin sanun hakan" dariya Lina tayi.
"Hakan bazata yiwuba saboda yanzu nakejin ina ƙara son Hammood"
"Lina Umarni nake baki dole zaki barshi zuwa lokacin da zamuga gudun ruwansa duk da nasan Hammood keeps his words baya saɓa alƙawari" tsawa Lina da dakawa Mum.
"Dama na nemi izininki kafin nafara sonsa? Bana bukatarsa domin dainawa saboda ban nemeshi da zan fara ba dama ba komai zaki iyamunba danna mallakeshi You're useless i dnt need you anymore, I'll find my way" Nawrah ranta ya ɓaci ta dakawa Lina tsawa lina ta mata kallon banza ta tattara kayanta ta ɗauki passport ɗinta tabar wajansu. Dama Lina ba kunya gareta ba kuma Mum tasan da hakan amma a ƙoƙarinta na sai lallai ta sanya Hammood yadawo gareta ta yarda da Lina gashi tun ba'aje ko'inaba tafara nuna mata hali.
A zaune yasameni akan sallaya ya ƙaraso ya zauna shima akan sallayan ya jawoni jikinsa.
"Mutafi koh rouhi? Time ɗin tashinmu yakusa. Kai kawai na gyaɗa masa yayi magana akazo aka fitarda kayanmu duk ina ƙwance a ajikinsa. Hijab ne ajikina Jalbab wanda na samesu a ɗakin kuma inajin daɗin sakasu. Yace natashi mutafi ahaka muka fita da wananan Hijab ɗin domin ɗinkin yayi masa baya nuna kowane shape na jikina. Tunda yaga yanda sukayimin kyau ahaka kuma suka suturta haliytar jikina ya sanyawa ransa sune abunda zan saka aduk lokacinda zamu fita dashi.
Tun daga ƙofar Masauƙinmu ƴan jarida ne damƙam tun kafin na ƙarasa wajansu naja jalbab na rufe fuskata zallan idona ake kallo dan banason camera ɗinnan. Da jami'an tsaro aka rakamu filin jirgi bansan ina zamuje ba nidai kawai ina biye dashi.
Saida muka sauƙa wata ƙasa mukayi hutun 3hours sannan muka wuce wajanda zamuje Da baodygyrds ɗinsa a bayanmu ko'ina muka tsaya saboda tsaro naga har wasuma aka ƙaro dayawa yanda aka buga worldcup ɗinnan yayi winning dole a tsaurara masa tsaro. Har P.A ma bansan yaya akayi ba bayan sauƙarmu a garin farko naganshi acan sai muka cigaba da tafiya dashi Wata ƙasace bansan sunanta ba dake komai nawa yana wajansa bare na karanta ajiki kuma hawai mun tsaya a ƙasar da muka fara sauƙa bane saida muka ɗauki ƙaramin jirgi kafin muka wuce can Wani island mai masifar kyau da ɗaukar hankali ruwan dake wajanma kawai abun kallo ne ya subhanallah kamar wajanne ake kira Maldive Island amma banda tabbaci tunda ban taɓa gani banda a hoto ba Zagewa nayi ina zuba ƙauyancina a wajan son raina har tsayawa nakeyi sai Hammood ya zauna ya jirani nagama kalle-kalle kafin muƙara gaba. wata hanya mukabi muka fara tafiya kawai sai gamu a ƙasan ruwa Ƙanƙame Hammood nayi sosai sabod tsoro daya kamani ganin kifi suna shawagi a samansmu murmushi kawai yayi ya ɗaukeni domin naƙi buɗe idanuwana suna kulle Gamm.
Masauƙinmu anan yake Bodyguards suna ƙarasawa damu kowannensu yakama nasa wajan amma akwai guda biyu wanda suke tare damu sai dai ba'a cikin wajanmu ba.
A kan bed ya sauƙeni ya zauna yana kallona a hankali nafara buɗe idona ajiyar zuciya na sauƙe kamar ance na kalli sama naga kifi suna shawagi a samanmu ihu nasake sakawa na kamashi Dariya kawai yake yana shafa bayana naƙi buɗe idona na kalli sama sai ahankali-ahankali nake buɗewa ahaka harna samu na buɗesu gabaki ɗaya. Dake lokacin garin da yanda muka baro akwai bambamci sai kawai mukayi saloloin da suka wucemu. Alokacin aka kawo mana abinci babu abunda na iyaci aciki dama yayi tunanin hakan shiyasa yayiwa P.A list na abubuwan da zai sayamin a wancan ƙasar friuts kawai nasha nakoma na ƙwanta saida aka kawo kayanmu kafin naci wani abun. Babu yanda Hammood yafita yana tare dani dagashi sai gajeren wando ko arzikin Singlet bai samu sakawa ba.
Wayarshi ya kunna yana kallo inason zuwa kusa dashi nima nayi amma banaso naje kusa dashi a yanda yake haka gashi ba Volume banajin abunda yake kallo raina kawai yanata azalzalata inaji kamar pics ɗin ƴan mata yake kallo da yayi shiru haka na saƙa na warware yafi abunda yafi shikuna ya maida hankalinsa kan waya haushi da takaici yanata damuna, Ashe sama ba keɓewa mu kaɗai yazo muyiba yazone ya maida hankali akan wayarsa.
Zuciya ta ɗebeni na tashi zuwa wajanda yake na fauce wayar. Nakai Kallona akan abunda yake kallo. Pictures ɗinmu ne wanda muka ɗauka jiya Yaya habibu ya tura masa yake kallo yana tsaye akan pictures ɗina kusan dance ma ni yake kallo. Murmushine ya suɓucemin na kalleshi inason na dake na ɓata rai amma murmushin yaƙi barin fuskata kallon Fuskata yake shima amma nakasa gane yanayin da ke kan fuskar dakuma abunda yake tunani. miƙa masa wayar nayi ina cin magani ina magana.
"Meyasa bazaka kalleni ba tunda gani kusa dake kake kallon hotona"
"Kin amince na kalleski kenan? Kece Rouhii rikicinki yayi yawa yanzu zan iya kallonki kice nayi laifi gara na kashe ishirwata akan pictures ɗinki" na girgiza kai.
"No bazaka yi kaifi ba" murmushi