Showing 21001 words to 24000 words out of 171869 words
Chapter 8 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
ganinsa ai ba ƙasarmu ba kawai duk ƙasar dayaje saiya rikita ƙasar tunda anyi ittifaƙin babu wanda yataɓa kafa record ɗinsa a yanzu fa shine matshin dayafi kowanne sanuwa a duniya ni bansanma abunda zai kawoshi ƙasarnan ba"
"May be personal issue ne shiyasa ba'a buga dalilin zuwannasa ba" nabashi amsa.
"Eh toh amma inagako shugaban ƙasa yakeda issue dashi zai iya binsa har ƙasarda yake ammma bansaniba basu sanar a media ba" canja zancen mukayi da wani zance daban."
***********
Wani katafaren gini ne mai Hawa biyu kusan gabaki ɗaya ginin da glass akayishi, gini yayi masifar haɗuwa gabaki ɗaya shape ɗin gidan curve yabada daga nesa kyallinsa kawai ake kallo, cikin katafariyar harabar gidan ansake wani katafaren ginin wanda yake kamada ma'aikata sai gefe filin kwallo ne wanda shima aka tsarashi, cikin wannan gini Kama da ma'aikata akwai wani Babban office aciki mai girman gaske yana ɗauke da set ɗin kujeru har guda biyu. Cikekken Balarabe ne matashi kyakkyawan gaske yanada tsayi sannan kuma baida jiki sai dai yanada murɗaɗɗan jiki bazai wuce 30years ba kansa cike take da kwancecciyar suma baƙiƙirin tayi luff yanada dara-daran idanuwa ƙwayar idanuwansa fararene tass yayinda tsakiyan eyeball ɗin yaci baƙi sosai fatarshi har wani tarr takeyi yanada haske sosai cikin larabawanma shi mai haskene, zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun yana duba wasu takardu yagama sanya hannu ya miƙawa mutumin dake zaune a kujerarda take facing ɗinsa ya amsa sannan cikin harshen larabci yadubi wannann mutumin Personal Assistant nasa yace.
"Idan mungama zamu iya tafiya" Mutumin yayi murmushi cikin harshen larabcin yace.
"mood sir kanada tabbacin samun abunda zakaje nema? Kamar yanda kafaɗa bazaka taɓa dawowa batareda cika burinka ba, sanya ran cikar burinka yasa kaja tsawon wannan lokacin ka daidaici lokacin daya dace dan aiwatarda ƙudirinka, ina fata Allah yacika maka ƙudirinka duk da abune mawuyaci ace kamar yanda kake wannan ƙudirin yakasa cika" Murmushi yayi saida gefen kumatunsa suka lotsa Ya furzar da iska mai zafi a bakinsa ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗaura kan ɗaya ya jingina ya lumshe idanuwansa ya buɗe hannaye akan saman kujerar yasake furzarda iska mai zafi, mutumin nan cikin harshen turanci yasake cewa.
"are you nervous? jijjiga masa kai kawai yayi alamun eh. Mutumin yace.
"don't be sannnan ya canja harshe zuwa larabci yana faɗin.
bana tunanin a duniya akwai wani wanda zasu ƙi baka aure bana tunanin a duniya akwai macen da zataƙi aurenka, kanada kuɗi kyau suna da komai na maore rayuwa meyasa bazata soka ba?" sai alokacin ya ɗago ya gyara zamansa yace.
Idan har zata soni saboda wannan qualities ɗin menene bambamcinta da sauran matan? Kamar yanda soyayyarda nake mata ta kasance ta daban inaso itama ta kasance ta daban" Ya miƙe yace.
" Zamu iya tafiya yafaɗi haɗeda fara yin gaba wannan P.A nasa yabishi abaya dama an rigada anshirya masa motaci guards ɗinsa suka suka buɗe yashiga sannan suka rufe suma suka shiga dasu aa tada motocin sai airport. Dama da Jirginsa na musamman hakan yasa da gabaki ɗaya guards ɗinsa duka suka tafi."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
✔️Ote
Comment
Follow
share
To be cintinued
Zaynab Alabura
*BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
PAGE 11
Gabaki ɗaya airport ɗin cike yakeda jami'an tsaro tako ina tun kafin isowarsa fans ɗinsa suna bakin airport wajan babu masaka tsinke wasusunma sun wuni zubur a wajan suna jiran isowarsa tunda ba'a sanarda specific time ɗinda zai iso ba. Bayan magrib jirginsa ya sauƙa daga sauƙan jirgin ma'aikatan gidan TV da masu hotuna wanda dama sun daɗe awajan suna jira suka fara aikinsu tun daga fitowarsa suke ɗauka duk wani moves nasa. Har ma'aiakan wajan kowanne damuwarsa su ganshi wasuma su samu Autograph nasa amma hakan bamai yiwuwa bane saboda tsananta tsaro da akayi a wajan, su kansu masu tsaron wajan idanda zasu samu dama badan aikin dayake gabansu da sai sun ɗauki hoto dashi. Ma'aikatan gidan TV sunaci gabada aikinsu kusan kaff manya manyan mutanen da suke cikin garin harda shugaban ƙasa saida sukaje taryarsa tun daga isowarsa suke taka masa har yakaiga fita a filin jirgin motoci suna jiransa a harabar ƙofar airport ɗin yana fita gabaki ɗaya wajan ya karaɗe da ihun fans saida jami'an sukayi da gaske kafinnan suka iya hana mutanen zuwa kansa domin irin ihu da murnar da sukeyi yafita a hayyaci, Hannu kawai yake ɗaga musu suna sake rikicewa har yakaiga shiga mota wasu dag acikin ƴan jaridun suka rakashi har masauƙinsa dayake wasu daga ciki live suke ɗauka nan da nan labari yabazu agabaki ɗaya kafar sada zumunta."
****
Bayan dawowar Baba daga masallaci sallar isha'i nahaɗa shayi kamar yanda nasaba nakai masa, nasamu yana canje canjen tashoshi har yakai tasharda suke labari akan isowar babban ɗan wasan ƙwallon ƙafa Hammood ina kallon tasharda yakamo nasamu waje nazauna muka fara kallon ana nuna irin mutanen da sukayi cincirundo zuwa wajan ganinsa abun sai wanda yagani, Baba yace.
"kai wannan bawan Allah. Allah yasaka masa farin jini shifa duk ƙasarda zaije haka ake taryansa da zarar yasaka ƙafarsa a ƙasa toh duk wani mutum mai muhimmanci ya biyo bayansa harsai yafita" murmushi nayi nace.
"Baba ai ita gabaki ɗaya duniyar takoma hannun footballers komai nasu shine akan gaba su suke juya komai" baba yace.
"tabbas haka yake Allah yasa mudace" na amsa da Amin. Kowacce tasha abunda ake nunawa kenan da zarar angama nuna na tasha ɗaya natashi na koma ɗakinmu naso nayiwa Baba zancensu Anty fadeelah amma sanin cewar baida cikekken lafiya kuma bansan abunda zaije yazoba yasanya ban sanar dashiba amma yazama kamar dolene na sanar dashi amma saina daidaici lokaci kafinnan duk da kasancewar bamuda wani lokacin tsayawa gabaki ɗaya kwana biyu tabasu"
Ina zuwa ɗaki naɗauki waya nakira Hamma. Duk azatona yadawo dake tun safe da mukayi waya bamu sake ba kuma ya shaidamin cewa yana gama abunda yakaishi zai juyo koda kuwa da dare ne dan yayi missing ɗina yanaso ya kasance zuwa safiya shine zai kaimu school. Bugu biyu ya ɗauki wayar. Muna gaisawa nace.
"Hamma kardai baka dawo ba?" Murmushi yayi mai sautin danake iya jiyowa yace.
"Yaya akayi kika gane?" cikin yanayin rashin jin daɗi nace.
"Oh hakan ya tabbata kenan?" sannan na amsa tambayarsa nace.
" jikina kawai yabani"
"uhmm ban dawoba gabaki ɗaya garin babu masaka tsinke ni fitarma wahala nake ganinta. Zuwa asubahi zan fice lokacin ƙafa batayi yawa ba"
"yanzu muka gama kallo nida Baba yanda jama'a suka taru a zahiri bazakace akwai wannan jama'ar agarinba" Hamma yace yanzu dai zuwa asubahi zan taso bayan kunfito daga lacture ɗin kishirya ganina Ina dawowa zan shigo school ɗinku munyi hira sosai Allah-Allah nakeyi washe gari tayi dan ina muradin ganinsa kwana biyunda nayi ban ganshiba sai nake ganin kamar wanda nayi wata guda banganshi ba mun raba sare muna magana dashi a waya sannan mukayi sallama washe gari nakira maryam bace mu haɗu a makaranta kawai basai tabiyominba. ni kaɗai nawuce makaranta inata zumuɗin dawowar Hamma jira kawai nakeyi rana tayi kamar yanda ya faɗamin na jirayi ganinsa. Ganin ɗaukin da nakeyi ya sanya Maryam tace.
"waike babe zumuɗin me kikeyi haka? Gabaki ɗaya farin cikinki yakasa ɓoyuwa wani abunne yafaru?" jijjiga kai nayi nace.
"me kika gani?" ni ba wani zumuɗin danakeyi" ta taɓe baki sannan tace gayawa makaho" Dariya nayi kawai nace.
"ke Da'allah Hamma ne yake hanya kuma yacemin daga can nan zaiyiyo shinefa nake ɗaukin ganinsa kuma kinsan dama dole zanyi"
"Uhm lallai babe bakida wayo kamar ba ranar muka gama magana dake akan abunda yakamata kiyi da wanda yakamat kibari ba idan kuma soyayyarki da Hamman harta isheku ne kinaso ku rabu toh" Duka nakai mata ina faɗin.
"banason iskanci wani irin ta isheni kuma? Ni nace miki haka?"
"eh toh mana Babe kinsan cewa ana bibiyar rayuwarki amma gashinnan kincewa Hamma yazo school kuma kinsan tunda dai ba ɗaukanmu zaizo ba kinsan za'a gane abunda ya kawoshi kina kallo ko wajan cin abinci muka canja a wajan cin abinci sai anbimu da takeaway ina kike tunanin zaki shiga baisan kin shiga ba?" kema kinsan karshen zancen wace irin haɗuwace da bazaku iya haƙuri sai antashi idan yazo ɗaukanmuba wannan baza'a zargi komai ba" jikina yayi sanyi lallai wannna mutumin tsoronsa da tsoron abunda zai iya aikatawa zai hanamu rawar gaban hantsi. Jiki asanyaye nace
"toni yanzu me zance masa? Idannace masa yafasa zuwa yanzu sai ransa ya ɓaci kinsan kuma banaso" Miƙamin hannu tayi tace.
"Bani wayarki" na miƙa mata ta shiga message ta tubuta saƙo sannan ta tura saita miƙemin tace.
"Gashinan yanzu bazaizoba" zaro ido nayi na amshi wayar ina faɗin.
"me kika tura masa nashiga uku" saida nashiga saƙon nagani sai kuma na sauƙe ajiyar zuciya. Kallo kawai maryam take bina dashi taja tsaki tace.
"na rantse babe kinada kayan takaici garafa tun wuri kishiga taytayinki soyayyar da kike yiwa Hamma tayi yawa ga wani bala'in tsaronsa da kikeji aikuwa zaki wahala har indai namijine da zarar ya fahimci hakan zai juyaki kamar ƙosai amai" cikeda jin haushinta nace.
"menene laifi danna nunawa Mutumin danake ƙauna irin Soyayyar danake masa?" Banjira amsarta ba cikeda takaici natashi nabar mata wajan."
Sai Yamma liƙis muka tashi dam tun kafin mutashi munyi waya da Hamma yasan lokacin so kafin mugama ya iso farin cikin danayi aganinsa kamar wanda akayimin wata babbar kyauta. A hankali yake tuƙin motar yanayi muna hira Maryam tayi tsaki cikin ranta yafi sau goma koda wasa bata bari yafito fili ba sanin halin Hamma sam baya ɗaukar raini. Ahaka har muka iso suka sauƙeni nayi mata sallama tacika fam ko kulani batayiba. Ko ajikina nashige gida."
ina shiga ɗakin Mama nawuce nacire kayana na ajiye jaka sannan nafito nayi ɗakinmu, Anty fadeelah nasamu tana shirya yakanta dama Aysha ta daɗe da shirya nata Dasauri na ƙarasa wajan ina faɗin.
"Anty fadeelah menene hakan? Wai kema kayan kike shiryawa? Banace kibani kwana biyu ba in sha Allahu zan shawo kan komai" Anty fadeelah tace.
"marmee bakisan mummynmu bace tunda ta ƙudurta aranta cewa saimun koma toh dole saimun koma babu wanda ya isa ya hana hakan ko baki fahimta bane? Yanzuma ta sanar mana cewa jiya da yau ta ɗaga mana ƙafane kawai saboda yanayin yanda garin Abuja yake Amma mummynmu ba mace bace wacce zata janyewa maganarta"
"Anty fadeelah dan Allah kubani kwana ɗaya gobe kawai zansan yanda zanyi" cikeda ƙufula Aysha tace.
"waike me kika sanine? Me kika sani gameda mummynmu? Kinsan wace irin matace ita kuwa?" me kike ɗaukan kankine da kike tunanin zaki iya jaa da maganarta? Toh ko Babanmu dayaja da maganarta baiji da daɗi ba kuma har yau yana kan rashin jin daɗi. jaa da maganarta kamar tarwatsa farin cikin rayuwarki baki ganewa?" Abunda Babanmu ya aikata mata kenan ya sanya ya tarwatsa mana ahali daya bita a yanda take kuma yanda takeso da mungirma gaban uwarmu da ubanmu, shi kanshi Baba bai isa da Mummynmu ba bare keh" maganganunta sunmin zafi ƙwarai dagske dan haka rai aɓace nace.
"har ita wacece mummyn taku da kike haɗata da babanmu? Kike nunawa tafishi ƙarfin iko da komai? Kin ɗauko laifin duk wani abunda yafaru kin laƙaba akan mahaifinmu? Shin itace ya kamata tabishi a matsayinta na matarsa daya aura yakawota cikin gidansa ko shine yakamata ya bita" Dariya sosai Aysha tasaka tace.
"gidansa? Toh lallai bakiji dakyau ba, Mummynmu itace mai gida kuma itace mai iko da komai kuma dole abita" raina yakai ƙololuwa wajan ɓaci dan haka nace.
"koma wacece mummynku koma mai take gadara dashi toh nayi alƙawarin dawo da ita ƙarkashin mafinmu" azafafe tayiyo kaina tana faɗin.
"harke wacece da zaki faɗi haka akan Mummynmu?" nima dake idona ya rufe nayi kanta ina faɗin"
" kema harke wacece da zaki aibatamin Babana" Anty fadeela tayi saurin shiga tsakaninmu tana daka mana tsawa amma bamu saurareta ba jin hayaniya tayi yawa ya sanya Mama da Anty suka yiyo ɗakin dsauri.
Mama tana kallon abunda yake faruwa tayi saurin Zuwa ta fincikeni ta zubamin mari cikeda tashin hankali take magana tana faɗin.
"Marmee hankalinki ƙalau? Ina zaman zamana kikeso ki jawomin masifa" anty tace kubarmu muji da abu ɗaya mana mahaifinku tunda yayi fitar asubahi har yanzu bai dawoba gashi wayarsa bata shiga" jin zafin marin da tayimin ga wannan abunda Anty tafaɗa ya sanyani ficewa raina amatuƙar bace nayi shashin Baba dake dama baicika rufe falonsa ba idan zaifita sai kawai nabuɗe bashige aciki na zauna nasha kukana babu wanda yabiyo bayana har wajajan sha biyu na dare ina zaune naji sallamar Baba kai tsaye ɗakinsa ya nufo bayan ya tabbatrda matan gidan sunji shigowarsa ina bakin ƙofa yazo ya taras dani ganina ahaka yasan akwai abunda yafaru dama duk lokacin da akayimin wani abun ɗakinsa nake zuwa. Amma yau yafi bada ƙarfinsa akan rashin jinsa da ba'ayi gabaki ɗaya aranar bane ya sanyani zama a ɗakinsa ina kuka ga fuskata gabaki ɗaya ta kumbura. Nadubeshi cikeda kulawa muryata harta shaƙe saboda kuka nace.
"Baba kana lafiya? Ina kashiga?" ya ƙarasa shigowa ciki yayi murmushi irin nasu na manya yace" lafiyata ƙalau wani abune ya taso na fice sassafe kuma bazai yiwu nabar wayata a kunne ba shiyasa."na sauƙe ajiyar zuciya dai-dai lokacin Anty da Mama suka shigo. Baba yace.
"marme jeki kwanta fuskarki tayi wani iri babu komai da zarar kinyi sallar asubahi kizo zamuyi magana na amsa da.
"toh" sannan nafice ina tunanin wace irin maganace Baba yakeso muyi dashi da asubahi, Banbi ɗakin Mama ba dayake fushi nakeyi da marinda tayimin nawuce ɗakinmu banbi takansu ba nayi wajan wayata in dubawa naga missed call ɗin Hamma dake dare yayi sosai banbi takan kiran ba na kwanta Bawani bacci nayi sosai ba saboda abubuwada suke cikin kaina asubahi tanayi natashi nayi sallah inajin dawowar Baba daga matsallaci natashi natafi ɗakinsa sallama nayi yacemin na shigo na zauna bayan na gaisheshi ya amsa. A hankali nace.
"Baba" yace.
"Na'am Marmee akwai wani abunne?"
"Nisawa nayi nace Baba wata alfarma nake nema awajanka"
"Wace" irin alfarma kenan Marmee?"
"Baba bazan faɗa makaba saika yarda zakayimin" Baba yayi murmushi irin nasu na manya yace.
" Toh faɗuwa tazo dai-dai ta zama kenan nima inaso na roƙi wata alfarma a wajanki banaso na yanke huknci akanki kamar yanda nayi abaya yazo ya tarwatsamin gida gabaki ɗaya banaso na maimaita kuskuren danayi abaya"
"Baba kaifa ubane wace alfarma kuma bayan kai mai bani umarnine nawa bine kawai daga yanzu karkaji komai karkaji shakku akaina a duk lokacin dakaji zaka yanke hukunci akaina bakada buƙatar shawara dani kai tsaye kayanke saboda kanada cikekken iko akaina kuma zanyi maka biyayya ɗari bisa ɗari saboda inada yaƙinin bazaka yanke hukuncin da ba dai-dai ba akaina" Baba cikeda jin daɗi yace.
"naji daɗin wannan zancen Allah kuma yayi miki albarka kuma in sha Allahu bazan yanke hukuncin da zakiyi dana saniba. Yanzu ina jinki ki faɗamin wace alfarma ce kikace zaki nema a wajena nima nayi miki alƙawarin yimiki komenene faɗamin inaji" Na nisa kafin nace.
Baba kafin na faɗa maka abunda yake tafe dani ina neman alfarmar ka faɗamin ainihin abunda yafaru a gidannnan da dalilin daya janyo rabewar kan gidanmu gabaki ɗaya. Wacece mummy kuma wani irin hali take dashi da kowa yakejin tsoronta harda kai kanka daya kamata ace kaine wanda kake bata umarni tanabi?" Baba yayi shiru kamar bazaiyi magana ba Harna cire rai da zaiyi magana sai kuma naji yace.
"SHEKARUN BAYA*
ZAINAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
PAGE 12
SHEKARUN BAYA (bari mu tsunduma cikin labarin tsundum)
kyakkyawan matashine wanda gabaki ɗaya illahirin makarantar Abubukar tafawa ɓalewa babu wanda yakaishi kyau sannan kuma yanada ilimi matuka da gaske a wannan lokaci anyi ittifaƙin kaff samarin makarantar babu mai kyawunsa a shekarun baya ɗalibanma gabaki ɗayansu basuda yawa so tantance irin wannan lamari abune mai sauƙi.
Ƙyawunsa yasa daga lacturers mata har ƴan makarantar basu ƙyaleshi kowwacce da taga fuska sai tayi Ƙokarin buɗe abunda yake zuciyarta. Har malamai mata sunsha bayyana masa ra'ayinsu akansa wasun sunzo da niyya mai kyau wasu kuma sun nemeshi da fasiƙanci agabaki ɗaya babu wanda yayi nasarar samun kansa, wata hanya ɗaya da Allah ya fissheshi yanada ƙoƙari sosai koda Malamai sun tunkareshi da wata mummunar niyya yaƙi tofa basuda damar da zasu kayardashi saboda makaranta ta shaida ƙwazonsa da zarar hukumar makaranta taga ya faɗi zatabi diddigi tayi bincike. Matashi mai kamun kai da nutsuwa haƙuri da sanyin hali sannan ga girmama nagaba dashi hakan yajawo masa farin jini wajan malamai da dama kuma baida ƙuiwa wasu daga cikin malaman idan ayyuka sunyi musu yawa sukan kirashi su sakashi a ƙanƙanin lokaci yake gama musu aikin wannan matashi Ba kowa bane sai Muhammad Muhammad Dani.
Muhammad Dani iyayensu su Huɗu