Header Ads
Showing 171001 words to 171869 words out of 171869 words

Chapter 58 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1093

Ads at the middle of Article

yanda banyi Hammood yabarni na tafi da ƴan uwana ba amma yaƙi. Su Mummy kanma ganin irin kulawarda ake bani yasa basuyi maganar tafiya ba. Har Mum ɗinsa yanzu sona take tunda taji nice dalilin dawowarta rayuwa cikin yaranta."


Hutu Hammood yaɗauka yadawo gida gabaki ɗaya yana kula damu tunda nake bantaɓa ganin soyayya irin wacce Hammood ke yiwa yarinyar dana haifa ba. Bayan 5month da haihuwata Hammood yafara zancen na sake samun ciki shareshi nayi kamar banji yayi zancen ba baisan nikanma planning nake namu na gargajiya yanda bazai gane ba. Saida yarinyarshi tayi 6month kafin yabarni naje gida Baba yasake sabob gini ƙatoton gida kai girman gaske kowa da shashinsa kuma komai equal yayi musu ya ɗaukawa kowacce mai aikin da zata dinga yimata hidima ya ginawa hajiyarsa ma shashinta wanda yafi na kowacce mace girma tunda mahaifin Baba yana zuwa lokaci-lokaci. Sai a wannan zuwan nawa Baba yabani sadakina ƙin amsa nayi nace mishi nabar masa ya fara business dashi, shawara suka zauna sukayi da Yaya Ahmad akan business ɗin da zasu fara dake zuwana naje musu da morethan 20 cartons na dabinon campanyn Abie nabawa Baba shawara adinga shigo masa dashi ya buɗe ƙaton store ana jibgesu da ƙananun shaguna na sayarwa hakan akayi kafin lokacin tafiyata yayi an tsara komai yazama shine Distributor na ƙasa baki ɗaya, sannan Baba suka haɗa business da mahaifinsa yana aiko masa kayyyaki daga wajansa suma aka buɗe musu shaguna manya-manya. 2weeks Hammood ya ishemu da ƙulafuci nadawo."


Bayan tafara wayo aka ƙaro wacce zata tayani kula da baby bayan Nanny ɗinta da aka kawo tun tana jaririya duk da mafi akasari ma nike kula da yarinyata ban yarda da koda yaushe yarinya tana wajen nanny ba suka sake ƙaro wata hakama dana haihu gidansu Hammood aka nemo wacce zata shayrda yarinya nikuwa nace bansan zance ba ni zan shayrda kayata dama basu shawarci Hammood ba dan bazai bari wata ta shayr masa da yarinya ba, saida akayi tsawon shekaru biyu ina amfani da Planning na gargajiya kuma yana dakyau domin yayimin sosai, Hammood yafara damuwa wai sai dai muje asibiti aduba har yanzu shiru. Nayi kicin-kicin na ɓata rai nace. "Menene asibiti kuma Allah na tuba kenan bamu yarda da hukincin ubangiji ba? Babu yanda zani daka ganni Allah zai kawo" ganin bai samu goyon bayaba yasa yabar maganar nima nadaina amfani da maganin gudun tonon asiri."


Sunan Hammood sai ƙara shahara yake a duniya yayinda ɗaukaka da buɗi na ubangiji tako'ina suke zuwa masa an ɗauki tsawon shekaru har izuwa yanzu ankasa samun wanda yakai Hammood bare ya wuceshi."


Ina zaune a ɗaki ina kallon wasu kayyyaki da Nasa aka sayo na babie yashigo, na ɗaura idanuwana kan kyakkyyawar fuskarsa nan da nan naji nutsuwa tana shigana, a hankali yazo ya zauna yadubeni cikin muryarsa mai daɗin sauraro yace. "Barka da aiki Rouhi fatan kina lafiya?" yayi maganar cikin yaran hausa A hankali na dubeshi sai wani kyau yake ƙarawa gashi nice dai natashi cikin hausawa amma hausarsa tafi tawa daɗi kodan ya haɗu da yanayin zazzaƙar muryarsa ce. Ya riƙe hannuna yana murzawa. "Rouhi kinsan abunda ya kawoni kuwa? Na jijjiga kai "Nazo nayi miki cikine da yardar Allah" zaro ido nayi "dan Allah kayi haƙuri masoyi yaushe-yaushe na haihu? Yara uku cikkn waɗannan shekarun yanzu kana son wani babu daɗewa dan Allah kabari na huta" yayi murmushin da yake ƙara masa kyau, "Yara goma kan ai sai an jajirce kuma Rouhi ke ina wani ruwanki da maganar baki daɗe da haihuwa ba? Haihuwa na biyu dana uku ko naƙuda bakiyi ba kuma babu laulayi sai dai haihuwa kawai, idan kinason kigama dawuri kifara haifan 2-3 lokaci guda" na girgiza kai "A'a ni gaskiya ban yardaba" "Okay toh ni yanzu kibari ki haifi mai kama dake sakk sai ahuta" na ɓata rai na miƙe zanbar ɗakin ya kamoni cakk ya ɗagani bai direni ko inaba sai kan gado hayewa kaina yayi, na murguɗa masa baki "kaifa ka dage saikamin cikine naga Alama nikuma ban shirya ba" ya sumbaci bakin toh dama shirya masa ake? Ai zuwa kawai yakeyi kiyi addu'a Allah yabamu masu albarka nace "Amin" daga nan wasan ya canja salo muka lula wata duniyar da mu biyunmu kaɗai muke iya kai junanmu. And We lived a happily ever after."








ALHAMDULILLHI ALLAH YAKAWO YAU ANGAMA BIBIYATA YAKEYI WAYE SHI KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFEMIN ALLAH YABAMU IKON RUBUTA ALKHAIRI SAIMUN HAƊU CIKIN LITTAFINA NA GABA *DA UBA AKE ADO* In sha Allah zakuji daɗinsa fiyeda Bibiyata yakeyi, Nagode sosai da nuna ƙauna da kulawa gareni."








PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads