Header Ads
Showing 63001 words to 66000 words out of 171869 words

Chapter 22 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1082

Ads at the middle of Article

Hajiya akwai abincin da akayi order ankawo mu kaiwa su Ya Ahamd. Duka muka miƙe muka fice saida mukabi wajan Hajiya muka ɗauko abincin sannan nufi wajansu. mukayi sallama suka bamu izinin shiga sannan muka shige dukansu suna zaune a palour muka ajiye suma inajinsu zancen Hammood sukeyi. Ya Ahmad yace su Aysha suje su ɗauko musu cups da plates mukuma mu zuba musu wanda zai iya ciyiwa acikin takeawaye ɗin.
Box na Snacks na buɗe na fara jera musu akan a box ɗaya Babba akan carfet. Ya Ahamd ne yasake dawo da hirar Hammood da sukeyi yace.


"amma hammood ɗinnan yanada nutsuwa koh? Dannaga kaman cikin footballers ɗinnan yanayinsa yafita daban. yanyinsa yanuna yanada nutsuwa" Ɗaya daga cikin abokanansa ne ya amsa yace.




"Eh sosai ma yanada nutsuwa kasanfa shi ba irin rayuwar celebraties yakeyi ba. Da ace wanine yasamu wannan ɗaukaka daya samu aida ba haka ba dan yanzu haka ina tunani kaff celebrities na duniya yafisu yawan mabiya a zahiri da kafar sada zumunta. Duk wannan ɗaukaka da Allah yabashi at his young age amma rayuwarsa a nutse yake yinta gwanin sha'awa bayida wani mummunan hali" Ya Ahmada ya sauƙo kan carfet ɗin yaja box ɗin gabansa sannan yafara faɗin.


"Kunsan na taɓa haɗuwa fa dashi nayi noticing hakan nida kaina komai nasa a nutse da tsari ko maganarsama a tsari yake yinta kuma da alamunsa bai cika magaba ba" Kamar wanda aka tsomo bakina aciki nace.




"Ya Ahamd dan Allah dagaske kuma kunyi magana dashi? Meyasa baku ɗauki photo ba?" Bai amsa tambayata ba yace.


"kinaso ki ganshi ne?" dasauri na gyaa masa kai yace.


"kibari idanya sake zuwa ƙasarnan zan kaiki ki ganshi" cikeda murna nace nagode. su kansu Friends ɗinsa sunyi mamaki da Yaa Ahmad yace ya ganshi. nan suka fara zolayarsa shima yazama celebraty. Duk wanda ya Haɗuda Hammood shima abun kallo ne. ɗaya daga cikinsu ne yace.


"Mutumina daga nemi autograph na mutuminnan da kasha ƙwana" kana zaune zakaji daga wata ƙasa wani hamashaƙin masoyinsa mai kuɗi yasiya a kuɗin tashin hankali. Dariya kawai Ya Ahmad yayi musu. Shikansa a lokacin daya fara haɗuwa da Hammood yaɗauka irin shirmen mafarki ne. Saida akwa ƙwana aka tashi yayarda ba mafarki bane. Har yanzu wani lokacin yana tsoron kada yafarka yaga ashe duk tsawon lokacin da aka ɗauka mafarkine. Alokacinda Baba yake faɗa masa zancenda Hammood yazo dashi ya daɗe sarewa rayuwar duniya. Ya tabbata rayuwa cike take da abun al'ajabi kuma yasan wannan ba komai bane sai wani ikon ubangiji. Shi kaɗai ya isa ya aikata wannan lamari ya sanya soyayyar marmeeyy acikin zuciyar mutum kamar Hammood. Su maryam suka dawo da plates ɗin da cups harda spoons muka serving ɗinsu sannan muka fice.


Bayan munfita abokin Ya Ahamda wanda yaketa shigemin yacewa ya Ahmad


"Yaahhh Dani nifa ina ciki da wannan ƙanwar taka yaya za'ayi dan Allah kabani ita wallhi aurenta zanyi. Ahmad yace.


"Ka makara"


"Kunyi mata miji kenan?" Kai tsaye yace masa Eh" Yaya habib yana jinsu baice komai ba amma shi baisan anyi mata mijiba. Yana tunanin Ya Ahamd dai kawai bayaso yabawa abokinsa ne. Baici abinci ba ya faki idanuwa ya sulale yatafi wajan Maryam.
Itama muna shiga tafice wajansa nikuma na shiga ɗaki saida muka wuce 11pm muna waya da Hamma sannan mukayi sallama. Har lokacin Maryam bata dawo ba dan haka nafice zuwa ɗakin Mummy nasami tana cire kayan da zata saka tana waresu kowanne da sarƙoƙinsu da gyalesnu na zauna na na tayata muka cire wasuma saita sanyasu na canja nace yafi dacewa da ɗayan dariya kawai takeyi idan nayi hakan. Har wajan 12:am ina wajanta. Muna hira sai dariha takeyi nace.


"Mummy" tace


"Na'am marmeeyy"


"Mummy kinada kirki"tayi murmushi da alamu taji daɗi sosai tace.


"Marmeeyy abakinki na farajin wannan kalamr kowa cewa yake banda kirki ko ba'a faɗamin hakan a idona ba yanayi ya nunamin. Har ƴaƴan cikina kuwa"


"Allah dagaske nake Mummy kinada kirki amma tunda kowa yana cewa baki dashi ni kaɗai kawai nagani ta iya yiwuwa na fuskanceki ta wata fuskar ce. kokuma yanda kika mua'amalanceni daban da yanda su kike musu Mai zai hana sauran ma ki canja mu'amala dasu? Ta'iya yiwuwa ma sai sunfi ganin kirkinki akan ni yanda nake gani" ta kalleni kawai batace komai ba. Nasake cewa.


"Mummy" ban bari tayi maganaba nace.


"Dan Allah Mummy kidawo gidanmu mucigaba da zama tare zaifi daɗi dan Allah mummy kinji"


"Marmeeyy agabaki ɗaya mutanen duniya ke kaɗai kikeso nadawo gidanku"


"Baba ma yanaso kidawo" nabata amsa.


"Babanku bayaso nadawo da yanaso daya nemi hakan"


"Mummy Baba yacemin yana tsoron rasaki nahar abada ne shiyasa yakasa nemanki. Yana tsoron ki aikata abunda kika faɗa nacewa idan ya yarda ya nemeki batareda ya aikata abunda kikace yayiba zai rasaki na har abada. Tsoron hakan yasashi kasa zuwa yanda kika amma duk da hakan bawai dalili bane. Nasan kinfaɗane kawai a lokacin da zuciyarki tayi zafi. Koda sau ɗaya daya nemi ki koma nasan zaki koma saboda mu mata munada rauni kuma zuciyarmu tanada saurin sauƙa na tabbata da yazo na tabbata zaki yafe masa. Amma kema dakin nemeshi koda sau ɗayane nasan tsoronda yake zuciyarsa zai gushe" Mummy ta runtse idanuwa kawai tana nazarin kalamaina. Dakyar ta iya buɗe baki tace.


"Marmeeyy shekarunki nawa?"


"19yrs" nabata amsa ta jijjikai A cikin zuciyarta tana tunanin yanda yarinya ƴar shekara sha tara zata kasance mai hangen nesa kamar haka afili kuma tace.


"Dare yayi kije ki ƙwanta gobe kitashi dawuri" nace toh nayi mata saida safe nafice.




ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Mummy zata iya cewa tama manta da waɗannan kalamanda tayiwa Baba sai yanzu da aka tuna mata. A zahiirin gaskiya za'a ganta tana cikin farin ciki da walwala da jindaɗi amma abun bahaka yake ba tana cikin kaɗaici rashin walwala kewar mijinta da rashin jin daɗi. yanda take jida kanta ne kawai zai hanata neman Baba su dai-dai ta a halin yanzu bayan Marmeeyy ta fama mata yanda yake mata ciwo. Amma a yanzu ta ƙudirta cewa koda sau ɗaya Baba yazo ya nemeta zata koma ɗakinta ne kawai ta ƙarasa rayuwarta acan. bakamar yanda abaya take tunanin ko yazo saita bashi wahala ba. Ita bata taɓa tunanin cewa Baba zai iya shareta ya fita harkarta na tsawon wannan lokacin ba. Kuma tun daga wancan lokacin Iya tsawon rayuwarta tarasa wanda zai zauna ya faɗa mata gaskiya sai wannan ƴar ƙaramar yarinyar itace wacce tafara nuna mata tagyara alaƙartarta da mutane sannan tabata shawarar takoma ɗakin mijinta.


Ajiyar zuciya tasauƙe taƙwanta tana tunanin maganganun marmeey. Ta lura shi kansa Baba ya yarda da hankalin yarinyar tunda har yana zama da ita ya faɗa mata damuwarsa. Tunda Marmeeyy tazo sai takeji kamar wanda damuwarta tazo ƙarshe kamar wanda zatayi mata maganin damuwarta. ta wani fannin kuma tanaji kamar wanda take sake taso mata da ciwon abunda yawuce abu ɗaya dai data sani shine tunda marmeeyy tazo gidaan tafita a cikin kaɗaicin rashin abokin da zata zauna ta faɗawa damuwarta sai takeji kamar akwai wani wani shashi da nuna cewa itama mutumiyar kirki ce. Ita kanta wasu lokuta takanji ajikinta cewa halayanta basuda kyau. Zuwan Marmeeyy yasa ta fuskanci wani ɓangare acikin zuciyarta da batasan tana dashi ba.


Ɗan kwanakin da sukayi yasa tayi discovering good side nata da batasan tanada shi ba. aranarda sukazo harsu Aysha ta lura ƙamewa sukayi cikin tsoro suna jira tayi musu faɗa babu ɗaukin ko murnar ganinta sam a fuskarsu bayan shekara biyu dasuka ɗauka basu ganta ba amma marmeeyy cikeda ɗaukin ganinta fuska yalwace da fara'a ta taryeta.


lokaci na farko a rayuwarta tasamu wanda ta fahimceta ta fahimci abnda yake cikin zuciyarta batayi mata irin kallonda kowa yake mata ba. Ajiyar zuciya tasauƙe tarasama wane yanayi take ciki kamar ranar saida taraba dare tana tunani bacci na ɗaukanta aka fara kiraye kirayen sallah."




Washe gari sassafe muka tashi kamar yanda nasaba tun zuwana nashiga na gaida Mummy. Abun yana bata mamaki ganin sassafe ina tashi wajanta nake nufa na gaisheta. Abunda yaranta basu iyaba kenan ko ince bata koyarda su ba. Lokacin suna wajanta sukan ɗauki tsawon kwana biyu bata sanyasu a idanuwanta ba. gara ma yanzu taga sun canja. Da safiya koda basu shiga ɗakinta ba suna gaisheta idan sun haɗu.


Breaskfast dukanmu muka haɗu munayi tana gani ɗaya bayan ɗaya saida Mama ta kiramu. Anty fadeela tafara kira nice ƙarshe. Abun yabata mamaki yanda taji suna magana da mama cikeda shaƙuwa da sakewa wanda ita kanta data haifesu bata samu hakan a wajansu ba. Bayan mun kammala breakfast ɗaki muka koma mukayi wanka muka shirya gida gabaki ɗaya yacika anata shirin ɗaurin aure. Bayan antafi sallar jumu'at aka ɗaura aure muna zaune da Mummy da wasu Friends ɗinta a palour muna shirya abunda za'a bawa wanda zasu kawo amarya saiga ya Ahamd yashigo. Matan da suka palourn suka fara tsokanarsa ango-ango ya Ahamd murmushi kawai yakeyi yasha manyan kaya kana ganinsa kaga angon gasken sai sheki kayan yakeyi yana zuwa ya durƙusa gaban Mummy wacce take ganin kamar fara'arsa hartayi yawa. Saida yaje kunne ya raɗa mata cewa Baba yana waje. sannan ta fahimci murnarce ta haɗu masa biyu harda ta ganin mahaifinsa wajan auransa. Wanda ita kanta tayi yaƙinin cewa bazaizo ba sai gashi kuma yazo. Bata taɓa tunanin hakanba Saida yanayinta ya canja taso ta birkice sai kuma ta dake ta maida miyau sannan tace kashiga dashi palournka idan babu kowa ina zuwa.
Ya Ahmad yayi mamaki sosai yanda Mummy ta amsa tana zuwa a lokaci ɗaya a zatonsa fushinda takeyi da Baba yayi yawa da zaisa bazata taɓa kula shi ba. Yajuya yana mai cikeda farin ciki ya nufi wajan Baba.


Tare sukazo da Alhaji habibu atare ya shigar dasu palourn Baba. Mummy ta dubemu dukanmu muna zaune hankalinmu yana kan kyaututtukan damuke haɗawa tace.


"Kutashi ku tafi wajan Ahmad Ku gaisa da Babanku" tafaɗa jiki a sanyaye sannan tayi ƙoƙari ta fuske. Su kansu sauran mamaki suke dan basuyi tunanin zaizo ba nikuwa danasan Baba na tabbata zaizo tunda mukayi wannan maganar dashi. Muka miƙe dukanmu tana zaune babu alamun zata tashi muka fice.


Muna fita tatashi tayi ɗakinta ta sake kayan jikinta haɗeda sake sarƙa da zabbe da canja gyale da takalmi ta feshe turare da ƙofar baya tabi dan gani takeyi kamar ta cutarda jin kanta har indai tafita kowa yaga ƙwalliayrda tayiwa mjjinda ya rabuda ita tsawon shekaru.


Muna shiga da murnar ganin Baba na ƙarasa da sauri dan nayi kewarsa sosai duk da kasancewar muna waya kullum na zauna akan carfet agaban kujerarda yake ina musu sannu da zuwa. Ya dafa kaina yana faɗin.


"Yawwa marmeeyy sannu Yaya hidimar biki?"


"Alhamdulillhi" na amsa. Na gaisheda alhaji Habibu batareda ya amsa ba yafara faɗa yana faɗin.


"Ke zaynab hankalinki ƙalau da zaki saka wannan gyalen? Kefa yanzu ba yarinya bace. Kull karki kuskura ki fita da wannan gyalen koda wasa karki sake" cikeda ɓacin rai nadubi gyalen jikina. Medium veil ne sai dai yanada shara-shara kuma mu duka irinsa muka saka amma baiyi musu magana ba. Kuma duk cikinsu sun girmeni amma yana cewa niba yarinya bace. Kodai baisanma shekarunmu bane. Bansan meyasa kwanannan sukemin haka ba har gyalenda bai kai wannan ba ina sakawa basa magana zai yanzu. naturo baki idanuwana suka cika da hawaye na haɗe rai sosai kota kansu ban sakebi ba inaji suna gaisardasu suka amsa. Alokacin Mummy tashigo bayan tsayuwarda tayi a ƙofa na tsawon lokaci tanaji kamar ta koma dakyar tadaure tashigo. Da sallama tashigo saida gaban Baba yafaɗi ya daure ya amsa sallamar sannan ya ɗaga ya kalleta itama shiɗin take kallo ajiyar zuciya su dukansu suka sauƙe. ta ƙarasa ta zauna ta gaisheda Alhaji Habibu ya amsa fuska sake. Ta gaisheda Baba. Karo nafarko data taɓa gaisheshi kenan. Sai abun yayi masa wani iri saida yayi jimmm saida taɗan kalleshi sannan ya amsa haɗeda yimata Allah yasanya alkhairi.
Ta kalleni tace.




ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya


"A'a marmeeyy yanaga ana kumbura fuska? Waya taɓamin marmeeyy ta?" ta gefen ido na kalli Alhaji Habibu danshi sam baya ɗaukan wargi baya wasa irinna kakanni. Tana ganin hakan ta fahimta sai taja bakinta tayi shiru.


Alhaji habibu yafara musu nasiha munajin hakan muka sulale muka barsu. Yayi musu faɗa sosai sannan ya roƙi Mummy takoma ɗakinta. Bayan yagama yace zai fita su haɗu da mahaifin Mummy yakira Ahmad yayi masa jagora. Yabarsu su biyu aɗakin.


shirune yabiyo bayan fitarsu aɗakin na daƙyar Baba ya iya daurewa yayi gyaran murya sannan yace.


"Mummy (kamar yanda yake faɗa mata abaya) ya bayan saduwa"


"Lpy" tabashi amsa.


"Fatan kunanan lpy" Ta kalleshi idonta ya ciko da hawaye bata iya bashi amsa ba. Ganin haka yasa yace.


"Subhanallahi mai kuma yafaru?" ta dake sosai sannan tace.


"Komai ma yafaru kana tambaya wai fatan munanan lpy. Inaji babu amfanin tambayar nan"


"Meyasa zakice haka kuma"


"Tsawon shekaru baka damu kasani ba Daka damu kasani daka kira koda sau ɗayane kaji lafiyarmu" tana magana hawaye yafara zarya a kumatunta tacigaba da faɗin.


"Ko baka kira danni ba yakamata kakira dan yaranka kaji lafiyarsu. Shekara goma sha ɗaya fa ba ƙwana goma sha ɗaya bane ko ba ƴaƴan mutane nataho dasuba zaka kira kaji lafiyarsu bare ƴaƴanka na cikinka. Koda bazaka iya aikata abunda nafaɗa maka ba wanda kai kanka kasan nafaɗane cikin zafin zuciya amma ai alokacin zaka iya bani haƙuri kayi ƙokari duk yanda zakayi kayi ka hanani tafiya. Kokuma ina tafiya kabiyoni ka dawo dani. Nasan bazakazo danni ba yanzu haka ma nasan dan auren ɗanka kazo. Hakanma mungode dan banyi tunanin zaka samu halarta ba" tana magana cikin raunin zuciya tana fitarda abunda ya daɗe yana damunta.


Baba ya nisa shima duk yanajin bbu daɗi ahalin yanzu babu wata maganar kare kai ko kinyi kaza kinyi kaza dan haka kai tsaye kawai yace mata.


"Ki yafeni Kiyi haƙuri nasan na ruguza gidana da kaina dan haka yanzu ina roƙonki kiyi haƙuri kidawo ɗakinki domin mu gyara abunda yaɓaci. Ina nufin mu maidashi kan hanya dan rayuwarmu ta bayan gabaki ɗayanta bata kan hanya. Yanzu na ɗauki alƙawarin jan ragamar gidana nazama jagora in sha Allahu zanyi muku jagora har gidan aljanna"
Mummy ta sanya hannu ta share hawayenta tace.




"Shikenan yawuce Allah yayafe mana baki ɗaya" ya amsa da amin.


"kin yarda zaki koma ɗakinki kenan?" ta gyada masa kai a fili yace Alhamdulillhi a zuciyarsa kuma yana tunanin lallai Mummy ta canja danta bashi mamaki da tayi saurin saƙƙowa bai zaci samun hakan da wuri ba amma kamar yanda tafaɗa shekara sha ɗaya ha ƙwana sha ɗaya bane.


Alokacin ta aika akawo masa abun taɓawa dan dama kafin tafita saida tabi kitchen tabada saƙon abunda za'a kawo. Aciki harda ruwan shayi da tuwo miyar kuɓaiwa yaji manshanu datasa akayi masa sanin cewa yafi sonsa akan kowani irin abinci. Dama already akwai tuwo da miyar stew da akayi. Tana basu umarni suka kaɗa zallan kuɓaiwa aka haɗo da Non sugary natural made drinks Suka kawo.


Aƙasa suka zauna aka baje abincin sunaci suna hira dariyarsu kawai ake jiyowa. Sannan Mummy ta roƙi Baba akan kar yafaɗawa yaransa cewa ta yarda zata koma dan ta lura cikinsu Marmeyy kaɗai keson takoma. Baba ya yarda cewa canjawar Mummy harda aikin marmeeyy ajiki. Ƙaramar yarinyace amma akwaita ta iya tsara zance na hikima har indai kalamine kam Allah yabata.




Alhaji habibu acan haƙuri yabawa mahaifin Mummy sannan yace ayi haƙuri takoma ɗakinta.
Ga mamakinsa shima mahaifin mummyn haƙuri yake basu sannan yace har indai ta amince takoma kawai.


Yayanta dayake zaune yace.
"Ai bawai sai anjira ta amince ba kabata umarni kawai takoma ɗakinta sufa yanzu ba yara bane abun kunya suke yiwa yaransu. Yanzu idan ƴarsu ta tattaro tadawo gida bayan an aurarda ita sai suce zasu mata faɗa?


Jikin mahaifin Mummy yayi sanyi danshi kansa abunda yayi kenan tunda Mummy tazo gida ko sau ɗaya bai taɓa mata faɗa ba. Shima fushin yayi kamar yanda tayi sai daga baya daya lura cewa abun bana ƙarewa bane shine ya sauƙo. Dafarko yayita neman hanyarda zaiyiwa Baba magana yazo yatafi da matarsa amma baiyi hakanba saboda yanaso yayi yanda bazata ganeba dan yasan idanta gane tabbas zatayi fushi shikuma bayason fushinta kasancewar ita kaɗai Allah yabashi mace sai maza guda biyu.
Alhaji Habibu yace.


"Abi komai a hankali kasancewar su yanzu ba yara bane yakamata abarsu su ƙara tunani tunda yanzu hakama natafi nabarsu ita da shiɗin nasan zasu sasanta kansu" yayan Mummy yace.




"Tunani a tsawon shekarunnana kowani irine ai sun ƙareshi dan dai nasan ku kanku sun gaji da zamanta ahaka itama idan dai bawai zuciyar ƙashi takedashi ba nasan yanzu ta sauƙo" mahaifin Mummy yace.


"Kamar dai yanda yace abi komai a hankali toh abishi a hankalin idan abun ya gagara sai mushiga ciki barema nasan bazai gagara ɗinba" Ahaka suka tsayarda maganar Bayan Baba yagama dakanta ta rakoshi ya gaida mahaifinta hakan ya tabbatar musu da babu wata matsala komai ya dai-dai ta. A wajan shima Alhaji habibu yaci abinci tareda mahaifin Mummy sannan sukayi sallar la'asar aka kiramu mukayi sallama ana ganin Babanmu za'a fahimci yana cikin walwala itama mummy haka farin ciki yagaza ɓoyuwa a fuskarta. Bayan mungama sallama suka kama hanya. Bayan Mummy tasaka ancika musu boot da tsaraba na mama dana Hajiya saina Alhaji habibu ma nasa daban. Bata bada na anty ba baisan ko har yanzu fushi takeyi da ita ba.


Suna tafiya mukayi shiri muka tafi walima. Bayan angama walima aka ɗauko amarya. A wajan Ya Ahmad aka ajiyeta dayake yanada girma.


Da dare za'ayi dinner munata shiri danso mukeyi mufi kowane lokaci ɗaukan wanka wannan dinner ta dabance har Mummy zata halarta.


Dake

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads