Showing 90001 words to 93000 words out of 171869 words
Chapter 31 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
yayi aure amma bawai dan kyawun matar ba"
"Hmm ke ai wanda suka ganshi sunce yafi kyau ido da ido. Kinga abunda kakeda tabbacin bazaka taɓa samunsa ba har mutuwa aiba laifi bane dan nayi mafarki idan bansameshi ido da ido ba barni nasameshi amafarki"
"Kinada gaskiya fa cewar ɗaya daga cikinsu wallh koni dazan samu nayi mafarkin aurensanma aida buƙatata tabiya" Kallon mahaukata kawai nake musu dan nasan zallan haukane data sanya suji Hammood Zai iya auren ɗaya daga cikinsu idanda taɓin hankali to babu mamaki idan sunyi tunanin hakan. Naji ana cewa harda ƴar gidan minister acikinsu dukansuma ƴaƴan manyane amma ba hakan yake nuni da ko samun ganin hammood zasu iyayi ba.
Neman hanyarda zasu samu ganinsa suka fara sai kiraye kirayen waya sukeyi ko akwai wanda yakeda connection da wani da zai sama musu ganinsa ko daga nesa amma basu samu ba.
"Uhmm kinga ni ko following ɗinsa mafa banayi" cewar wata daga cikinku.
"Gaskiya bakiyi ba yanzu ki ɗauko wayarki ki danna masa follow pics ɗinsa kawai zasu sauƙar miki da nutsuwa. Ta ɗauki wayarta tashiga insta a lokacin tayi fallowing suka shiga sai kallon pics ɗin suke suna yabonsa kamar wasu tsoffin mayu. Nidai ƙyaɓe baki kawai nakeyi sunaban haushi. Inaga kaff cikinsu babu wacce takaini son Hammood may be su fans ɗin kyawunsa dakuma ɗaukakarsane amma ni fans ɗin wasansa na ƙwallo ne tun bansan menene kyau da ɗaukakab anake kallon ball ɗinsa yake burgeni amma bazanyi irin wannan mutuwar da sukayi akansa ba.
"Lallai celebrity ɗinnnan sunaji da kansu kiga followers ɗinsa thousand of millions amma shi ƙwata-ƙwata 11people yake following"
"11 dai koh? Cewar ɗayar"
"no 11 suka dinga musu ta nuna mata daga ƙarshe ta ɗauki wayarta itama ta duba"
"kinga ashe yanzu yasake following ƙwata-ƙwata baifi 30minute da following ɗin account ɗinba barina shiga muga ko wacece"
"Wai wai wai kinga bama wata sannanniya bace ga sunan kamar Marmeeyy iyye lallai wannan tataki sa'a may be friends ko ƴar uwarshi ce gashi account ɗin babu hoto waɗannan followers ɗinma data tara may be bayan yayi following ɗintane fans sukabi. Kingansu hubdred thousands ne kawai"
"bari kiga zuwa gobe zata tafi millions" ina jinsu dana gajida jin hirarsu na miƙe danna gaji da sauraro kuma ya Ahmad ba shigowa zaiyi yanzuba da alama. Ina tashi naji sallamarsa alokacin fara'ata ta faɗaɗa na amsa sallamar ina faɗin sannu da zuwa Ya Ahmad.
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin
Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba
Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔
Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo
Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍
Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝
Yayi murmushi dan yaji daɗin ganin yanda nasaki raina gashi harna zauna cikin mutane ana hira dani.
"Iyyeh lallai Marmeeyy wato anshirya ganin bazata kenan gashi ansaki rai sai hira akesha toh Alhamdilulillhi hakan yayi kyau ai kinga yanzu muma zamuji daɗin ganinki hankalinmu zai ƙwanta" Mummy wacce muryarsa ta sanyata fitowa ta amshe zancen.
"Aikuwa kaga Marmeeyy ta saki ranta tayi ƙoƙari kaima saika cika alƙawari" dariya kawai yayi ya gaisheta. Anty fadeelah tace.
"Alƙawarin menene kayi mata?" Caraf na cafke zancen.
"Yace zaiyi surprising ɗina zamu fita zuwa jimawa" owoh toh idan zaku fita saiku sauƙeni naduba jikin Aysha dan banjeba yanzuna mummy ta matsa naje na dubata nifa bangama dalilin zuwa wannan dubiyar ba batada wani amfani tonon asiri kawai ake musu duk wanda yaje yadawo baya rasa abun faɗa.
"Toh ai an sallamesu yanzu daga nan nake kuma nabari suna jiransa yazo ɗaukansu ne sai dai na kaiki gidanta saimu wuce nabi na ɗaukeski bayan na sauƙe Marmeeyy"
"Ka sauƙeta kuma Yaya" naɗauka idan kakaita kuka dawo saimu wuce tare"
"Uhmm ku shirya bayan la'asar zamu fita. Zan tafi harda Antynku itama saita duba jikin Ayshan. Barina shiga wajan Baba tukunna yanzu Marmeeyy tashi ki buɗe ƙofar baya ta wancan falon Baba (Alhaji habibu) zai shigo munyi waya dashi lokacin nakusa isowa gidan yace shima yakusa isowa. Ke kuma fadeelah jeki kira Mama kice ta samemu aɗakin Baba. Dukanmu miƙewa mukayi dan aiwatarda abunda ya sakamu. Saida nabi wajan Baba zan karɓi keys ɗin ƙofan a palour na sameshi zaune akan kujera na shiga sa sallama na gaisheshi ya amsa yana kallona gabaki ɗaya na zabge amma sai dai kuma yaga walwala a tattare dani fiyeda yanda yaganni jiya. Har nazo zanfita yakira sunana na juya na dubeshi ganin yanason yayi magana saina juyo nafara dawowa.
"Yanzu kije ki buɗe ƙofar kafin kufita da yayanki kizo zanyi magana dake" murmushi nayi sannan Amsa da.
"Toh" Nafice naje na buɗe ƙofar yayi dai-dai da isowar Alhaji na isa na gaishe dashi sannan nayi masa iso har ƙaramin palourn Baba. Anan muka taradda Baba da Ya Ahmad Baba yana kallonsa ya miƙe tsaye yanayi masa sannu da zuwa cikin dalabi Baba ya gaisheshi yaya Ahmad ma ya gaisheshi alokacin mama ta shigo ganin mahaifinta yasa tasan Babban lamarine ya tarasu. Har zan fita Baba yace nayiwa Mummy da Anty magana na amsa sannan na fice.
A palour na samu Mummy ayanda nabarta da wasu daga cikin ƴan uwanta na shaida mata saƙon Baba sannan nawuce dan kiran Anty. Itama anty na kirawota nakoma ɗakin Mama nayi sallan azahar sannann na shiga nasake wanke dayake ana ɗan zafi agarin wannan karon doguwar riga nasaka na yafa ɗanƙwalinta na zauna ina jiran lokacin sallan la'asar yayi gabaki ɗaya lokacin kamar baya tafiya haka nake ganika kawai jikina yake bani wani babban Albishir Yake shirin yimin.
Zaune suke a gabaki ɗayansu palourn bayan sun gaisheda Baba (Alhaji habibu) Sannan yafara magana Toh Alhamdulillhi tsawon shekara da shekaru name buri da fatan Allah ya nunamin ranarda zanga iyalan Muhammad sun haɗe a waje ɗaya hakan bai yiwuba sai yau da dalili yayi dalili. Dalilim Aysha kuma dalilin marmeeyy na taraku anan ne danna sanar daku dalilin dayasa aka canja sure zuwa man aysha bayan kuma shi yaron saurayin Marmeeyy ne wannan abun yafaru batareda mun sanarwa kowanne daga cikinku dalili ba dagani sai mahaifin yaran sai yayanu Ahmadu gashi zaune shima kafin faruwar hakan akwai wani abunda yafaru wanda hakan shine Babban dalilin dayasa aka canja auren marmeeyy yadawo man ƴar uwarta Aysha bamu muka buƙaci hakanba mahaifin yaron suka nemi wata a cikinsu tunda hasu samu wacce sukazo nema ba. Naga baby dalilin da za'a hanasu sure kawai danya nemi ƙanwarta hakan yasa nabasu auren Aysha. Saboda its fadeeala akwai yaronda take zuwa wajanta itace ayshan dama batada manemi. Watannin baya da suka wuce yanzu haka ana neman shekara da faruwar wani lamari. Akwai wani yaro ɗan ƙasar Kuwait ɗan wasan ƙwallon kafa wanda nasan bazaku kasa jin sunansa ko'a bakin yara ba sunansa Hammood rana atsaka kawai Muhammad yafita sallar asubahi yadawo yasamh ana jiransa a ƙofar gida ana nemansa a gidan gobnati. Yayi mamamkin neman tunda shi ko aikin government bai taɓa yiba bare ajega siyasa. Toh sai suka ɗaukeshi suka tafi dashi anan yasamu wani labari wanda farkon jinsa hankalima bazai ɗauka wai shi wannan yaro Hammood shine yakeson Marmeeyy yanason aurenta yataso yazo gun daga can ƙasarsa neman izini a wajanmu toh shine daya sanarda abunda yazo dashi Governor da kansa ya aiko a ɗauko Muhammad aje dashi can toh alokacin basu samu wani ƙofa a wajan muhammad ba danshi yanda ya sanar dani dafarko hankalinsa bai kama zancenba. Akwai wani abokin shi muhammad ɗin dake yanzu senator ne sai suka biyo ta ƙafarsa sai yazo man dashi yaron wajan muhammad ɗin. Tun daga wannna lokaci yaron kullum sai yazo na yana neman auren Marmeeyy har saida ya kusan yanayin ƙasarmu dayake ya kasance babban mutum da wanda akeji dashi a duniya gabaki ɗaya mutane kala-kala suka ringa biyo sahu akan abawa wannan yaro auren Marmeeyy toh mudai dafarko zuciyarmu bata yarda da lamarinba amma ana tafe hankalinmu yafara ƙwanciya da irin ƙaunarda yake yiwa Marmeeyy mudai anan yaranmu da kuma al'adarmu abune mawuyaci asamu wanda zai iya yiwa mace wannan ƙaunar da yakeyi mata baiyi duba da matsayinka da dukiyarsa kowani mataki daya taka a rayuwa ba shidai hankalinsa yana kan marmeeyy gabaki ɗaya ya zuba waɗannan abubuwa a gefe yasanya neman aurenta agaba daga ƙarshe mun amince zamu bashi auren marmeeyy bayan tsananta bincike yarone mai hankali da matuƙar nutsuwa a tarihin shahararsa da rayuwarsa ba'a taɓa kamashi da wani mummunan hali ba. Bambamcin al'ada yare dakuma ƙasa bazaisa mu hanashi aure bayan nagartarsa ba. Duk wasu sharruɗanda namiji zai cika dan cancantar auren ƴa mace toh wannan yaro ya cikashi bamuda dalilin da zaisa mu hanashi aure bayan yarda da mukayi da irin sonda yake mata mahaifinsa cikekkekn ɗan ƙasar kuwait ne soja wanda yakai matakin Field marshall yana zaune a ƙasar kuwait da iyalansa sannan a bincikenmu ya nuna baya tareda mahaifiyar yaron saboda mahaifiyarsa baturiya ce. Alokacinda yadawo sun dawo tareda mahaifins sannan na amince masa nabashi auren Marmeeyy ambashi aurenta bisa yaƙininda mahaifinta yake dashi akan yarinyar nacewa kowane irin hukunci yayanke a kanta bada izininnta ba zata amshi wannan hukunci hannu bibbiyu. A lokacin mahaifin yaron ya nemi a ɗaura auren yaronsa da Yarinyarmu toh mun yarda an ɗaura auren ita Marmeeyy da Shi yaron batareda ɓata lokaci ba a wajan inda yayanta Yayi mata waliyyi sannann kuma muka nemi cewa karsu sanarwa da duniya wannan auren wato yatsaya a iya kanku dan wannan aure ba ƙaramin lamari bane da kai tsaye za'a fitarwa duniya abunda yake faruwa suma kuma sun amince da hakan ba fata mukeba amma saboda tsoron abunda zai biyo baya mun nemi ayi register auren tareda sanya hannun kowanne daga cikinmu. Mahaifinsa da kansa yayiwa hukumar aure magana aka bugo certificate kowa ya sanya hannu sannan suka bar mana shi nan a hannunmu yayinda su yaran suka fara rayuwa tare zasu karɓi kayansu su tafi dashi can su adana a wajansu mudai hankalinmu ya ƙwanta da wannan aure kuma munada dalilin dayasa ku iyayensu mata bamu sanar daku ba. yanzu da lamarin yazo ahaka yazama mana dole mu sanar daku dan itama kanta yarinyar a ranar yau zatasan cewa akwai aure akanta. Bance kowacce a cikinku ta sanarda itaba kubarshi shi mijin nata dakansa ya sanarda ita aurensa dayake kanta. Sannan abu nagaba abunda mukeso daku shine sanyawa wannan aure albarka dan anrigada anyishi bayan bincike da kiyaye ƙa'idoji. duk abubuwanda yakamata su sani gameda abunda yafaru da wanda suke son yafaru an sanar dasu. Har sadakinda suka biya saida aka nuna musu da certificate da komai. Sannan ya ƙarashe da Idan akwai mai magana muna saurarenku" mummy ce tafara magana.
"Kai Alhamdulillhi! Alhamdulillhi! Allah mungode maka kai amma wannan ai abun farin cikine dama wani hanin ga Allah baiwace dukda kasancewar Allah yafara bata abunda ya cancanceta kafin ya ɗauke wani daga gareta. Idan ana samun miji fiyeda Hammood Marmeeyy ta cancanceshi domin marmeeyy daban take a cikin ƴaƴanda muka haifa gabaki ɗayansu ita zinariya ce da Allah ya jefo mana ita acikin zuri'a. Wannan lamarine da bamu kaɗaiba gabaki ɗaya ƙasarnan zatayi alfahari da hakan kun rigada kun yanke hukunci daya dace mu bamu da abun cewa fatanmu kawai Allah yabasu zaman lpy yasa wannan aure ya amfani al'umna gabaki ɗaya" su duka suka amsa da Amin Antyma da mama gabaki ɗayansu hakan sukace. Baba yayi murna ganin yanda su dukansu suka amshi abun hannu bibbiyu ba kamar yanda yayi tunanin bazasu amshi abun da garaje ba.
Kiraye-kiraye sallar la'asar da aka fara ya sanya Alhaji Habibu yayi musu sallama ya tafi Baba ma yacewa Ya Ahmad suje suyi sallah sukayi alwala sannan suka fice."
Ana kiran sallah natashi naje nayi sallah sannan na gyara fuskata nasaka man baki da kajal sannan na ɗauko hijabi na ɗaura akan doguwar rigarda nasaka. Na suri jaka da takalmi ina shirin fita Mama tashigo ɗakin. Fuskarta babu yabo babu fallsa sannan bata nunamin komaiba tace nadawo na zauna. Ita aurenda akace anyimin bai dameta ba sannna kuma bataji bataso ko wani rashin daɗi akan hakan ba bawai dan ko mijinda akace an auramin ya kasance ɗaya acikin miliyan ba bawai danya kasance yanada kuɗi da ɗaukaka ko wata shahara ba itadai yanzu abunda takeso shibe samun ƙwanciyar hankali da nutsuwa ma ƴarta har indai auren Hammood zai kawowa ƴarta ƙwanciyar hankali da nutsuwa toh mai zai hanata yin maraba da shi? alokacin da Marmeeyy tarasa Hammood taji zafi sosai ta ƙullaci Baba amma yanzu ta fahinta ashe ya rabata da azurfa ne alokacin daya sama mata zinari. Tabbas marmeeyy tayi babbar sa'a dukda ita Mama batasan wasu ƴan wasan ƙwallo sosai ba amma tasan shaharar wannan bawan Allah. Jikina har rawa yakeyi ina kallon Mama data nutsa tunani.
"Mama! Please mana Yaya Ahmad fa yana jirana kuma hakanma sai nabi ta wajan Baba kafin muwuce" nafaɗa cikeda shagwaɓa saida tayi murnushi dan ta kwana biyu bataji nayi shagwaɓa ba.
"Marmeeyy kinsan Albishir ɗinda yayanki zaiyi miki ne naga kinata ɗauki da zumuɗi"
"A'a bansaniba kawai jikina ke bani wani Babban lamarine ke kinsani ne? Faɗamin idan kinsani? No barshi ma karki faɗa tunda aka kai wannan stage ɗin gara nagani da idona" Murmushi Mama tayi.
"Duk ke kaɗai dai kince nafaɗa kince nabarshi toh nabarshi, naga kaman kin sake jikinkk ƙwana biyunnan kin cire komai aranki ne?" ta jefomin tambaya.
"Eh nacire" nabata amsa kai tsaye.
"ko meyasa?" tasake jefamin tambaya.
"Saboda shiɗin mijin aysha ne kuma dama nafaɗa miki inaji tun baya da zarar anyi auren zan cire komai araina" jijjiga kai tayi na gamsuwa da maganata"
"a kullun cikin miki addu'ar alkhairi nake duk abunda kikaga baki sameshi ba Allah ya amshi addu'ar mahaifiyarki ne ya kaudashi daga hanyarki" duk kuma abunda kikaga ya faru toh inaso ki tunkari wannan lamari gadan-gadan dan addu'ar mahaufiyarki ta karɓu kenan Allah ya baki alkhairi sannan ki buɗe zuciyarki" tafaɗa haɗeda ɗaura hannunsa akan zuciyata. Nabi hannun da kallo sannan nadawo da idona akan fuskarta. A kullum ina miki addu'a Allah yabaki miji nagari wanda zai soki ya ƙaunaceki fiyeda yanda uwa takeson ɗanta wani lokacin nakance har indai hakan bamai yiwuwa bane toh Allah yabaki koda kwatanƙwacin irin sonda uwa takeyiwa ɗanta ne. Ta'iya yiwuwa Allah ya amshi addu'ata tun kafin ki haɗuda Hamma shiyasa da Hamma yazo rayuwarki ya cireshi yabar miki irin mijinda mahaifiyarki take miki addu'a inason kafin ki yankewa wani abu hukunci ki tsaya kiyi nazari kinada hangen nesa da tunani mai kyau na tabbata tunaninki zai baki abu mai kyau Tashi kije yayanki yna jiranki" nayi wani tunani akan maganganunda Mama take faɗa amma nakasa gane komai daga ƙarshe kawai nayi mata sallama har nakai bakin ƙofa nadawo.
"Mama ƙwnaaki kin faɗi wata magana wai Baba yafison Mummy akanki, kina zaune da Baba kin kasa fahimtarsa inaga a duniya idan aka cire mahaifiyarda ta haifeshi baida wani abunda yakeso sama dake komu ƴaƴansa baya sonmu kamarki ke kina zaune dashi kin kasa fahimtar hakan aamma mu ƴaƴanki mun fahimta" baki tasake sannan tayimin danƙwalo.
"Ƙaniyatki kenan Marmeeyy maras kunya" ina dariya nafice nabarta a wajan tana auna maganganuna.
A ɗaki nasamu Baba da Ya Ahmad bayan nashiga na zauna nace.
"Baba gani"
"Okay marmeeyy dama bawani abun bane zan baki hakuri gameda abunda yafaru sai yau naji ƙwarin guiwar tunkararki" na sunkuyarda kaina sai nkejin wani iri babu daɗi hawaye suka fara sauƙa akan kumatuna. Idon Baba yaga hawayen yacigaba da bani haƙuri." na girgiza kaina.
"Haba Baba dan Allah kabari kana sani jin wani iri karka sanya nadawo ƴarda bata gari ba wanda bazata iya farantawa iyayenta ba karka sanya najibkamar ban cancanci zama ƴarku ba har indai zaka tsaya bani haƙuri akan wannan lamarin. Shin wai Baba bankai ka yanke duk hukuncin da kaga dana akaina bane? Nifa da bakina na faɗa maka duk wani hukunci dakaji yayi dai-dai dani a rayuwa ka yankeshi kai tsaye. Bazan taɓa bijierewa umarninka ba kuma zan amshi kowani irin hukunci daka yanke akaina hannu bibbiyu kainefa ka haifeni Bani haƙurinda kakeyi zaisa naji kamar bibiyar danake maka takasa wacce yasa kaji idan ka yanke abu akaina yakamata kabani haƙuri banga abunda bazan iya sadaukar dashi akanku ko wani ɗan uwana ba.
"Shikenan Allah yayi miki albarka" shine kawai abunda yasake faɗa dan yanajin bayida wata kalma da zata nuna irin farin cikin dayake ciki face yayi mata albarka sannan idan yazo sallah yayi addu'a ya roƙi Allah ya kareta sannan yayi masa godiya da azurtashi da ƴa kamar Marmeeyy" Muda Ya Ahmad duka muka amsa da Amin. Jin shiru ya tabbatarmin da Baba yagama maganganunsa. Nadubi Ya Ahmad.
"Muje koh? Yanzu kusan huɗu da rabi lokaci yaja"
"Oh kin shirya kenan? Eh nashirya kai kawai name jira"
"Anya kuwa tafiyarnan matafi da wannna shiga Marmeeyy?" nadubi kayan jikina dakyau sannan na ɗago na kalleshi batareda nace komaiba.
"Kije ki canja kaya ya" na miƙe dasauri nayi ɗakin Mama 5minute nadawo na canja a palour na sameshi harda Mummy su Anty fadeelah gabaki ɗaya sun shirya.
"Au wai kin shirya kenan Marmeeyy? A'a jeki canja kaya" na kalleta kamar zanyi magana sai kuma na juya saida na canja kaya say uku na huɗunne nasaka wani riga da skirta wanda ya kamani sosai wanda ya Ahmad ya hanani sakawa a bikinsa nasaka hijab akai dannasan zaiyi magama idanna saka gyale.
"kayan yayi amma jeki saka gyale" mummy ta umurta na kalli ya Ahmad yabani yamin alamu da kayi nakoma ɗauko gyalen nasamu Mama tana fitowa miƙamin zobena tayi wanda