Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 171869 words

Chapter 24 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1086

Ads at the middle of Article

kallo fiskarsa nakeyi ba Cikin harshen turanci nace.


"Idan kanajina idan nayi magana respond idanba hakaba zanyi tafiyata"


"Okay" shine abunda yafaɗa.


"Sunanka" nafaɗa kai tsaye kamar mai bashi umarni. Ya nisa sannan Yace"


"You'll know soon" da hausa nace.


"bazaka faɗaba kenan?


"Mood" kawai ya yace dan yanda nayi maganar yagane cewa zan iya tafiya.


"Mood! Mood! Mood! Na nafaɗa inata nanatawa nakasa gane wane irin sunane wannan"


"Okay zan iya tafiya yanzu?" Kawai na tambaya. Da tambayoyi dayawa a raina amma banida lokacin yinsu dan bazanyita tsayuwa da mutuminda bansanshiba a wajanda babu kowa."


ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya



"No please stay" shine abunda yafaɗa naja numfashi nasamu kaina dayin abunda yace na buɗe mota na zauna gabaki ɗayana a waje nake amma ina zaune a cikinta. Shirune yabiyo bayan Zaman na tsawon lokaci. Naja ɗan siririn tsakinda bazai iya jiyoni ba banga dalilin zamanba tunda babu wani abunda muke faɗa sai zallan kallona da yakeyi wanda banida tabbacin yana iya kallon nawama sosai sabida duhun dake wajan. Ina zauna inata tunanin dalilin da zaisa nabi son zuciyarsa na zauna sai asannan nagano dalilin zamana awajan shine dan banaso nayi masa gardama saboda dagani saishi a wajan kuma bansanshiba bansan kamanninsa ba. Bare idan wani abun yafaru na iya bayani. Gara nabishi ayanda yakeso tunda naga alamun idan nayi hakan zamu wanye lafiya. Amma raina yana faɗamin har indai shine yake zuwa wajan Baba na tabbata bazai yimin komai ba. Toh idan kuma bashine wanda yake zuwa wajan Baba bafa? Wata zuciyar ta jefomin tambaya Ajiyar zuciya na sauke alokacin da zuciyata ta gajida saƙawa da warwarewa amma nakasa samun nutsuwar zuci. Idan bawai nasamu amsa ba hankalina bazai kwanta ba kuma Tunda gani gashi babu wata hanya da zanbi nasan hakan face na tambayeshi nasake sauƙarda ajiyar zuciya a karona bbu adadi. Har alokacin idanuwansa suna kaina Fuskarsa tana kallon tawa muna facing junanmu alokacin wata iska tafara kaɗawa yayinda take busamin ƙamshin turarensa mai cikeda wani sihirtaccen daɗi mai sanyawa zuciya nutsuwa. Na shigarda Kaina cikin motar sannna na ƙwanta na lumshe idanuwa a hankali yanda zai iya jiyoni nace.




"Do You know My father?" na jefa masa tambaya.


"نعم"
"Ohhh sorry yes" iska na furzar sannan na ɗan sake shige ciki na tayarda kaina sannan cikin harshen turanci nace.


"Sir nifa musulmace karkayi tunanin cewa ban iya larabci ba" saida yaɗan murmusa saboda maganar tabashi dariya baice komaiba. Asannna nasake jefo masa wata tambaya.


"هل قبلته؟"
"(Did you meet him)"


"who?"


"Baabna mana" yasan abinda Baba yake nufi akowani irin yare ana iya kiran mahaifi da Baba dan haka tsoron karna tafi nabarshi ya sanya yayi saurin faɗin.


"Yes" shiru kawai nayi ina mamakin daya haɗuda babana meya faɗa masa' wasa gaske duk wani zatona yanaso ya zamo gaskiya akan mutuminnan. Haka muka sake zama a wajan na tsawon lokaci bamu sake maganaba na maida idanuwana na lumshe bansan lokacin da muka ɗauka ahaka ba shikuwa kallona kawai yakeyi yana samun nutsuwa acikin zuciyarsa danshi Zamanda nayi a wajan kawai ya wadatar dashi koda bance masa komaiba. Ganin alamun nagaji da zaman wajan yasa yace.


"You can go" na ɗago kaina kamar wanda dama nake zaune akan ƙaya na ɗauki jakar kuɗin Ya Ahmad na fito daga motar nafara tafiya a hnakli. Kamar yanda nake tafiya a hankali haka shima yake tafiya a hankali a bayana. Da duhu a wajan sosai dakyar nake iya ganin yanda nake takawa gashi kayan yaɗan kamani shikuma yanabin bayana ina tafiya gabaki ɗaya cikin rashin kuzari ƙafafuna sai neman harɗewa sukeyi haka suka harɗe suka kusan yadani nayi gefe zan faɗi ya canja gefenda yake izuwa gefen da nake ƙoƙarin faɗuwa na faɗi a jikinsa yazame min madogara na rufe ido ina ƙoƙarin jina a ƙasa timm saina jini a jikinsa dasauri na buɗe idanuwana nayi saurin raba jikina danasa. Na juya nacigaba da tafiya idanuwana sun rufa bana ganin yanda nake takawa. Flash light ɗin wayarsa ya kunna yana haske footsteps ɗina ahaka nacigaba da tafiya da taimakon hasken da yake haskemin. Zuciyata ke karantamin son ganin fuskarsa na tabbata da zan juya dasauri idanna shammaceshi zan iya ganin ko wanene shi a wannan hasken, Dasauri na juya dan ganin fuskarsa amma kafin na juya ya kashe hasken bayan yin wani murmushi abun yabashi dariya sosai. Yana ganin yarinya ƙarama nason wai tayi masa wayo. Ƙyaɓe fuskata nayi cikin rashin jin daɗi bansan yaya akayi harya lurada jiyowata ya kashe hasken ba dukda banyi yanda zai gane ba, na juya nacigaba da tafiya ya maida flashlight ɗin ya kunna tunda muke fara tafiya bamu haɗuda ko mutum ɗaya ba kamar yanda nazo haka. a hankali muke tafiya harya sadani da ƙofarda zata kaini cikin wajan. Naja natsaya cakk shima ya tsaya sannan ya kashe hasken na juyo kamar wanda zanyi magana sai kuma nakaza cewa komai. najuya nashige ciki bansake waiwayowa ba.
Ina shiga gabaki ɗaya wutarda take wajan takawo na sauke ajiyar zuciya na daidaita nutsuwata sannan nashige ciki. Ga mamakina ina shiga na hangi Ya Ahmad yana wasa da kuɗi kamar bashi bane yacemin kuɗin hannunsa sun kusa ƙarewa. Jikina duk bbi kuzari na isa gareshi na miƙa masa kuɗin da key ɗin motarsa ya lurada yanayinda nake ciki amma saiya share kamar bai ganiba. Ina miƙa masa nabar wajan. Wajan zamanmu nayi har yanzu maryam bata dawoba na zauna da jakkunanmu duka a wajan ina buɗewa naga ƙaramar wayata sai alokacin na tuna nayi wurgi da babbar wayar alokacinda naji alamun mutum a atsaye a kusa dani. Inaso nafita na dubata amma bazan iyaba dole saina jira maryam idan tadawo ta rakani. Ina zama baifi 30minute ba tadawo. Ko kulata banyiba saboda haushinta danakeji. Saida ta lallasheni tacemin ta dawo bata ganniba shine tasake komawa, naduba time na daɗe a waje sosai dukda naga tsayin lokacin amma banyi tunanin nakai haka daɗewa ba.
bayan mungama pics da ya Ahmad ya kiramu akan muje sainace ta rakani na duba wayata.
Haka mukaje muka gama dubanmu amma babu komai a wajan muka dawo bamu daɗe da dawowa b aala fara tafiya muna cikin waɗanda suka fara barin wajan.


Anasa wajan kuma ina shiga ciki ya koma wajanda muka tsaya ya tattara wayata data fashe dama muƙarrabensa na jiransa a can wani waje daban yabisu wajan suka nufo masauƙinsu, P.A nataso yayi masa magana Akan yanayin yanda ya haɗuda ita Shi abunma gabaki ɗaya dariya yabashi saboda yaga soyayya a wajan manya baitaɓa kallon yanda ake soyayya haka abu kamar wasu dodanni. yana tunawa kawai ya fashe da dariya shi kaɗai. Mood ya ɗaga ido ya kalleshi cikeda tuhuma dan baisan dalilin dariyarba amma jikinsa yabashi dashi yakeyi, ganin mood na kallonsa yasanya ya shanye dariyarsa amma tana cinsa a ciki.
Har suka isa masauƙinsu babu wanda ya tanka wani bayan P.A yagama ajiye masa duk wani abunda zai buƙata domin asubahi zasubar ƙasar yagama yazo zai fita bayan yayi masa sallama Mood ya kirashi yazo ya tsaya yana jiran mood yayi magana ya nuna masa waje yabashi umarni
ya zaune. p.A yazauna yana kallonsa.
MOOD Yaɗanyi nazari haɗeda kaɗa kai ga dukkan alamu akwai abunda yake damunsa ya nisa sannan ya ɗan zoɓo daga kujerarda yake yana duban P.A yace."






ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya


Girgiza kai yayi ya fasa faɗin abunda yakeda niyya P.A yana ƙunshe da dariyarsa dan yaga alama ogannasa yanason ya zauce. Komawa yayi ya daidaita zamansa ya haɗe fuska kamar wanda yake ɓoyen wani abin sannan yabashi umarni daya tafi. P.A yatashi Harya kusan zuwa bakin ƙofa yasake dawo dashi yace yazo. Yadawo yazauna kamar yanda yayi datsu sannan yadubi ogannasa yana jira yayi magana. Yasake zoɓowa daga kan kujerar kaɗan sannan yaja iska ciki haɗeda yin nodding kansa ya kalli P.A cikin tuhuna da harshen larabci yace.


"Dariyar me kayi datsu?" saida P.A yasake wa dariyaar dan ganin yanda Mood ya susuce gabaki ɗaya a haɗuwarsa na farko da ita. Ranarda akace Ta dawo hannunsa kuma gabaki ɗaya baisan wani irin hali zata shiga ba. Yanzu ashe iya tambayarda yakeso yayi masa kenan yaketa gabas da Yamma. Mood Ya haɗe rai sosai Baice komaiba. Ganin haka yasa P.A ya gintse dariyarsa yaci murr shima sannan yace.


"Yanayin yanda ka haɗuda ita da hanyar da kabi wajan haɗuwa da ita ne abun dariya"


"Kamar Yaya?" ya jefo masa tambaya.


"Ita mace ai ba'a mata haka Mood sir maimakon ta kamu da soyayyarka sai kuma ta kamu da tsoronka. Tayaya zakaje mata kaamr wani dodo ko maras gaskiya. Yanzu Allah kaɗai yasan abunda ta ayyana a ranta game dakai" zaro ido yayi yace.


"Me kenan ba?"


"Wannan ita kaɗai tasani tunda ga yanda all'amari ya kasance" mood ya ɓata rai sosai ya buga table ɗin dake gabansa yace.


"Duk kasanda haka mai yasa baka sanarda niba kabari naje mata ahaka?" P.A ya kunshe dariyarsa kawai dan yaga yanda Mood yabi duk ya kiɗime kamar wanda yayi wani abun ba dai-dai ba.


"yanzu yaya za'ayi?"


"Yanda za'ayi shine gaba ka gyara karka ƙara zuwa mata ba'a Hammood ɗinda tasani ba be confident karka tsorata ka zama namiji itafa yanzu matarka ce kanada kowacce irin halastacciyar dama akanta. Kaje mata a matsayinka inada tabbacin zata amsheka, ita soyayya ba'a haka akeyinta ba, mace ba'a zuwa mata ahaka. Inada yaƙinin soyayyar da take maka matsayinka na celebrity datake so zaisa tasoka a matsayin miji bazaka taɓa samun soyayyarta ahaka ba zata ɗaukeka matsayin wanda ka takurawa rayuwarta kabarta na wani lokaci kafin ka dawo mata a matsayinka na Hammood ba'a matsayin ɓoyeyyen masoyi ba. Mood yayi shieru yana nazarin maganganun P.A tabbas abunda yafaɗa gaskiyane sai yanzu yake ganin wautarsa kuma ga dukkan alamu ta tsorata sai dai ya lura tanada ƙarfin zuciya dahar ta iya tsayawa ta saurareshi tayi ƙarfin halin tsayawa tayi masa tambayoyi akansa lumshe idanuwa yayi yanajin muryarta a kunnuwansa mai daɗi data sake sauƙar masa da nutsuwa yanajin sonta yana ƙaruwa acikin zuciyarsa komai nata yana burgeshi dai-dai da sauƙar numfashinta, yana tuno lokacin da ya rufe mata baki alokacin dataso yimasa ihu alokacin yashiga yanayinda tunda yake bai taɓa tsintar kansa a makamancin yanayi kamar wannan ba. Wannan lokaci ya tsaya masa arai yaƙi tafiya sai sake zuwa yakeyi a idanuwansa kamar a lokacin abun yafaru har P.A yagama magana ya tsaya yana kallonsa baisanma yagama ba gaanin haka ya sanya ya tashi yafice saboda yasan halin Mood fiyeda kowa.




Muna komawa gida bamu jira kowacce a cikinsu ba muka shiga domin kwanciya. Tun lokacinda ya manna jikinsa da nawa nakejin ƙamshin turarensa ya baibaiye gabaki ɗaya jikina dan haka ina zuwa wanka nashiga na daɗe a toilet ina dirza gabaki ɗaya illahirin jikina danji nakeyi gabaki ɗaya ƙamshin ya gama kamani tako ina amma ƙamshin bai fitaba haka na haƙura nafito.
Ina fitowa nasamu Maryam tana zaune tana jirana ganin nafito itama tashige bayan tagama tafito tashirya tazo ta kwanta sannan take cewa.


"babe Naji ƙamshin turare mai daɗi a jikinki ko toilet da kikayi wanka saida naji ƙamshin yanzu haka inajin ƙamshin wani irin masifaffen ƙamshine mai sauƙarda nutsuwa da kasala a lokaci ɗaya a'ina kima samu wannan turaren?" na dibirbirce nakasa cewa komai tacigaba da faɗin.


"Tun muna Hall nakejin ƙamshin banyi zaton a jikinki bane sai bayan nadawo daga wajan Yaya habeeb nakejin ƙamshin a jikinki a'ina kika samu wannan turaren?" nayi mata banza kamar banjita dan banda amsar bata saida tasake magana nace mata.


"Keh nima bansaniba Ya Ahmad ya aikeni motarsa na ɗauko masa aika sai... Sai maganar ta ƙaƙaremin nakasa ƙarasawa bansan wani irin kallo zatayimin babidan nace mata mutuminda bansanshi bane ya haɗa jikina danasa anan nasamu wannan ƙamshin Ajiyar zuciya nasauƙe.


"May be abokin yaya Ahmad ke amfani dashi amma gaskiya turaren yahaɗu" ahakan kawai nabita saboda inaso maganar da ƙare ahaka amma abun ya tsayamin arai sam yaƙi barina nasamu sukuni ganin haka ya sanya na ɗaga waya nakira Hamma Bugu biyu ya ɗauka kamar wanda yake jiran kirannawa yana amsawa nace.


"Amincin Allah ya tabbata agareka Hammana" daga cikin wayar naji sautin murmushinsa mai ɗauke da farin ciki.


"Amin babyn Hamma yau Hammanaki harya cire rai dajin muryar babynsa gani ina kwance amma bacci yaƙi ɗaukana"


"Hamma nima ai kasan bazan iya baccinba koda na kwanta shiyasa nakiraka dukda dare yayi kuma ina tunanin kayi bacci"


"Bazan iya bacci ba baby. Kwana biyu da bakya ɗaukan wayata bana iya bacci nashiga wani hali please bby karki sake yimin horo da rashin jin muryarki"


"In sha Allahu bazan sakeba Hammana kayi haƙuri" haka muka daɗe muna hira sannan mukayi sallama lokacin Maryam harta daɗe dayin bacci. Nima ban ɗauki wani lokaci ba na ƙwanta baccin zuciya cikeda soyayyar Hamma."




Asubahi jirginsu Mood yabar ƙasar zuwa Abu-dhabi
Ji yayi kamar yazauna yasake kwanaki ko zai samu yasake kallonta yasamu kansa a yanyinda yasamu a jiya da daddare tun baibar ƙasar ba yake missing ɗinta irin abunda yakeji akanta bai taɓajin makamancinsa ba. Wani lokacin yakan zauna yana tunani har indai haka kowane masoya sukeji akan abunda sukeso wasunsuma suzo basu samu soyayyar ba abun tausayawane shi kansa yanzu daya mallaki abunda yakeso yanajin fargaba taradadi da faɗuwar gbaa.




Bayan muntashi munyi sallar asubahi muka koma saida muka kai 10:00am bamu tashi ba saboda wajanmu babu hayaniya sau 2 mummy tana zuwa dubamu ko munfarka."


ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya


Baba tunda yakoma gida bai sanrda su Mama yabda sukayi da Mummy ba yafiso sai sun tsayarda magana dan har lokacin Mummy bata sanr dashi lokacin dawowarta ba. Yasan halinta sarai da iya canja ra'ayi dukda wannan karon bayaji zata canja ra'ayi dan yaga danasani da tsananin son ta koma ɗakinta a tattare da ita tacire duk wani girman kai jijjida kai isa da gadara ta tsaya sunyi Sulhu su fahimci junansu yaga abunda bai taɓa kallo ba atattare da ita yana saka ran ta canja kenan yana fata kar wani abun yataso abaya. Shi ba wannan bane yafi damunsa kamar yanda akayi auren Ɗiyar Mama (Marmeeyy) batareda sanintabba yana ganin kamar baiyiwa baiwar Allah mai hakuri da kawaici adalci ba . Kawai dan mahaifinta shine wanda ya ƙarfafa akan kada ya sanarda ita harya samu gwarin guiwa amma zuciyarsa takasa nutsuwa yasan idantaji koda daga baya zata fahinceshi tayi kasa uzuri kamar yanda tasaba amma bayaso taji babu daɗi aranta yasan babu wata mace da zataso ace an aurarda ɗiyarta batareda saninta ba dukda kuwa burin kowacce mace shine ta aurarda ɗiyarta. Zaibi umarnin mahaifinta tunda shima mahaifi yake a wajansa bazai sanarda itaba har lokacinda ya kamata tasani Amma har zuwa lokacin zuciyarsa zata kasance cikin rashin daɗi."




Saida Muka tashi muka shirya sannan muka nufi palour. Mummy na zaune da su anty fadeelah muka shiga muka gaidata ta amsa cikeda farin ciki tana faɗin.


"Marmeeyy antashi kenan nashiga dubaku keda maryam gabaki ɗaya kuna bacci kutashi kuje kuyi breaskfast gashican an anshirya" muka miƙe muka nufi wajan breakfast muna gamawa muka dawo. Aysha tasha murr bansan mena mataba tun jiya nake ganin tana shamin ƙamshi nima na ɗebeta na watsar. wunin ranar haka nayishi hankalin nakan wayata gashi banda Maryam babu wanda yasanda zancen ɓatar wayar dan itama cemata kawai nayi ta ɓata amma jikina yana bani shine ya ɗauki wayar dan kaf cikin wajannan babu wanda wayar zatayi masa wani abun.


Da Yamma akayi buɗar kan Yaya Ahamd da amaryarsa a harabar tsakar gidan sunyi kyau sosai bayan isha'i kuma za'ayi suya night(barbecue) tun Da yamma aka fara shirye-shirye mukuma bayan isha'i muka shirya cikin Abaya tawa data maryam iri ɗaya Babu makeup a fuskarmu amma munyi kyau.


Bbu wani african time 8. Aka fita wajan babu masu kida zallan photographers ne sai ƴan uwa da abokan arziki anata hira ana raha anajin daɗi an zazzauna da gashashun raguna a banƙare duk da sauran kayan marmari da drinks serve your self duk wani abunda kake buƙata dakanka zakaje kaɗauka. Harsu Mummh sunfita wajan yayinda akayi hira dasu da da sauran Ƴan uwa nikam naja gefe ina waya da Hamma sai sani nishaɗi yakeyi ana cikin event Ya Ahmad leƙa yaga baiganniba tun jiya yakeso ya fahinci abunda yafaru bayan fitata amma naƙi bada ƙofa yanzu haka rashin ganina sai yakeji kamar gameda abunda yafaru jiyane yasa banzauna cikin mutane ba dan haka yatashi yafara nemana nikam baisan Hammana harya gogemin duk wani abinda yafaru a kwakwalwata da soyayyarsa banyi auneba naji zamam mutum a gefena dasauri na ɗauke wayar a kunnema shikuma baima lurada wayarda nakeyi na datse wayar haɗeda ajiyeta a gefena, na sakar masa murmushi haɗeda faɗin.


"Yaya angama kataho nan?" ya girgiza kai sannan yace.


"A'a naduba kine naga banganki ba akwai wata matsalace gabaki ɗaya yau naganki wani daban" naɗanyi murmushi sannan nace.





"Subhanallahi Yaushe faruwar hakan kenan?"


"Jiya da dare wajan diner"


"Karki damu zan saya miki badai waya ba?" Na jijjaga kai sannan nace.


"Nagode yaya Allah yasaka da alkhairi" Amin ya amsa.


"muje ciki koh?" Yafaɗa yana ƙoƙarin tashi nace.


"Uhmm Yaya" na'am yafaɗi sannan yakoma yazauna yana saurarena dan yaga alamun magana zanyi. Abunda ya daɗe yana damuna wanda kullum nake burin sani yau zan daure na tambayeshi.


"Yaya menene atsakaninka da Anty naga gabaki ɗaya ka tsaneta ko gaisuwarta baka amsawa wanda kuma a zahiri ba haka kake ba kai mutumne mai sauƙin kai da saurin fahimta, wannan tsanarda kayi mata yawuge ace kawai dan Baba ya aureta kodan ta dalilinta Mummy da Baba sun samu matsala jikina yana bani akwai wani abun aƙasa koda Baba yabani labarin abunda yafaru a gidanmu nayita neman dalilin tsanar acikin labarin na rasa" murmushi yayi yafara magana.


"Marmeeyy meyasa bakya jin tsorin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads