Showing 48001 words to 51000 words out of 171869 words
Chapter 17 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
a serious tone" na kalleshi nace.
"Sosaima Baba kaima ai yana birgeka"
"Yana burgeni kuma yanada nutsuwa"
"Uhmm, Uhmm, Uhmm ɗinda nake faɗi ya sanya Baba yace.
"Marmeeyy akwai magana ne?"
"uhmm dama Baba maryam ce Umminta da Abbanta zasu tafi Umrah kuma zasu ƙwana biyu shine tace na roƙeka ka tambayi abbanta tadawo nan gidan da zama saboda mu samu muyi karatu cikin ƙwanciyar hankali" Ga mamakina sai naji Baba yace.
"Shikenan ai babu damuwa zanyiwa mahaifinnata magana saiki bani numbernsa" nayi murna sosai alokacin nabawa Baba numbern Abba yacemin zai kirashi zuwa safiya suyi magana.
ina komawa ɗakin Mama kai tsaye ɗakinmu nawuce saboda exam ta gabato yanzu kusan koda yaushe karatu kawai nakeyi wanka nashiga saboda yanayin zafo dayake garin. Nafito daga wanka idona yakai kan zoben dake hannuna natsaya kallonsa inaso natunano yanda naga makamancin irinsa a ƙwanakinnan gabana yayi mummunan faɗuwa."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Duk yanda naso nayi tunani nakasa tunano yanda naga makamancin wannan zoben ajiyar zuciya na sauƙe kai tsaye nashiga tunani idan zan iya tunawa tsawon wata biyu kenan bansamu saƙo daga wannan number mai turamin saƙo ba, to ko lpy? Ko wani abunne yafaru? Kokuma ya haƙura ne? Rashin samun amshoshin tambayoyina yasanya naji gabaki ɗaya babu daɗi nayi tagumi ina tunanin to ko wani abunne ya sameshi? Na sake sauƙe ajiyar zuciya akaro na biyu shin to ko wani abunne ya sameshi? Nayi zaton ya haƙura ne ya daina amma alamu bai nunashi acikin mutane masu sarewa ba. Wannan yanda yakeda jarabar naci bazai taɓa jaa baya ya haƙura da abunda yakeso ba. to koma meyasa zan damu dashi? bayan abunda nake nema ne ya samu yadaina damuna kamar yanda nake buƙata, na sake sauƙe wata ajiyar zuciyar. Saina samu kaina dayin addu'ar Allah yasa yana lpy. Uhmm koni maima ya dameni da zancen wannan mutumin?" na tambayi kaina. Ahaka anty fadeelah tashigo ta sameni ta zauna bakin bed sannan tace.
"Marmeeyy karatun kenan?" na ɗago na kalleta na zumɓuro baki bance komai ba tasake faɗin.
"Hamma ne ya sakaki tunani koh? Yasa kin kasa karatu toh aikuwa gara yabarki kiyi karatu" na yatsina fuska nace.
"Babu ruwan Hamma wani tunanin nakeyi can daban"
"Wani yashigo rayuwarki bayan Hamman kenan?" na zaro ido haɗeda faɗin.
"Rufamin asiri kar wani yaji labari" tayimin harara tana faɗin.
"ai gaskiya na faɗa dan duk wanda ya kalleki a lokacinda na ganki zai fahimci hankalinki yana wani wajan daban"
"kinganni ni tunanin exam ma nakeyi ko kaɗan hankalina bai kaiga Hamma ba" nafaɗi hakanne dan gujewa ta sake ɗauko wani abin. Ta jijjiga kai sannan tace.
"Bikin Ya Ahmad yanata ƙaratowa wai dagaske kike zakije?" Na jijjiga kai alamun tabbatarwa sannan nace.
" sosai ma kuwa"
"Marmeeyy baƙya tsoron mummynmu ba lallai ta ƙarɓeki ba kasancewarki ƴar babanmu abune maisauƙi tahuce haushin mahaifinmu akanki"
"Kuma ai ƴaƴan babanmu ne tunda ta amsheku nima zata amsheni sannan nifa bada niyyar zama zanje ba zan dawo gidan mahaifina bayan bikin yayana zan dawo gidanmu kinga ai bazata ƙi karɓan baƙin da sukaje mata biki ba nikuma gayyar Yaa ahmad nema ba nata ba. Kudai da kukejin bazakuje ba saboda kunajin tsoro ku zauna idan mundawo zamu baku labarin yanda bikin ya kasance"
"Uhmm" Kawai tafaɗa tana mamakin ƙarfin hali irinna marmeey. Amma tasan al'amura bazasu tafi dai-dai da Mummy ba."
Ɗaukan littafina nayi nafara karatu ban daɗe dafara karatu ba kiran Hamma yashigo na ajiye littafin gefe muka hau waya bamu mukayi sallama ba sai da 12:00am tayi muna sallama na ƙwanta bacci.
---------
Sun buga wasan ƙwallo sun dawo cikeda tarin nasarori dama bayan dawowarsa ya shirya zuwa wajan mahaifinsa.
Ƙwana biyu kawai ya ƙara ayanda ya tsara suka shirya tareda nawrah suka nufi wajan mahaifinsu a ƙasar Kuwait.
Dake tafiyar jirgi bawani nisa bane tsakanin Abu dhabi da kuwait ba tafiyar 2hours takaisu har cikin gidan mahaifinsu.
Gidane mai girman gaske yafi ƙarfin akirashi da anguwa guda wanda mutanenda suke rayuwa a cikinsa su kansu basusan kansu ba gidane wanda yake ƙunshe duk wani abunda ɗan adam zai buƙata akwaishi acikin wannan gida hatta da asibiti da filin jirginda helicopter ɗinsu yake tashi. Su Hammood kuwa koda isarsu a main airport suka sauƙa lokacin ɗan ƙaramin jirgi na mahaifinsu yana jiransu suna sauƙa suka tashi izuwa gidansu. Duk wannan gida mallakin mutum ɗaya ne amma shi kansa baisan yawan mutanenda suke rayuwa a wannan gida ba.
Suna sauƙa wajanda jirgin ke sauƙa akwai motocinda suke jiransu da zasu kaisu cikin gidan" saida sukayi tafiya 15minute acikin gidan kafinnan ta kaisu zuwa ainihin kan gidan tako'ina suka ratsa sojojine suke tsaran gidan tun daga farkonsa har ƙarshensa. Suna isa aka buɗe musu ƙofa suka shiga ciki babbar ƙofarda zata kaika cikin gidan mai masifar tsayice tafi tsayin mutum biyu daga nan sai wani tangamememen palour wanda aƙalla kujerun ciki sun kai 5set kowanne ɓari da nata. Wani balarabe kyakkyawa wanda bazai wuce 55years ba yake sauƙowa daga faffaɗan matakalarda take yalli kamar wanda aka yita sa diamon komai na gidan tangamemene komai an yankeshi da girma. Suna haɗa idanuwa da wannan mutumin ya sakar masa murmushi shima murmushin ya sakar masa yana ƙarasowa ya buɗe masa hannu. Ya ƙarasa yayi hugging mahaifinsa. Cikeda ƙauna da ɗumbin soyayya mahaifin yayi masa peck a gefen kumatu shima ya mayar masa sannan yace.
"مرحبا بك في البيت حمود حبيبي "
(welcome Home Hammod).
شكرن يا أبي
(thank you father) Nawrah dake gefe tacika tayi Famm mahaifin baima lurada ita a wajanba har saida yaji takun tafiyarta tana shirin barin wajen.
Saida yayi dariya dan yasan rikicinta sannan yace.
أنا آسف ياحبيبتي تعال وعانقني
( I'm sorry my dear come hug me)
Ta kaɗa kai tayi wani gefen batareda ta jiyo ba ya furzarda iska haɗeda girgiza kai yana dariya yasan halinta sarai mugun zafin kaine da ita. A kujerunda sukafi kowannen kyau da tsaruwa a cikin falon suka zauna. Mahaifin yace.
"Kacika alƙawarinka Hammood naji daɗin ganinka sosai" Shima yace.
"Naji daɗin ganinka nima" Suna zaune a wajan suna tattaunawa har aka kira magrib Dagannan suka tashi sukayi sallah basu shigoba har bayan isha'i. Mahaifin yasa a sanarda gabaki ɗaya iyalansa akan tare zasuyi dinner. da Hammood dan haka 8:30pm tayiwa kowannensu wajan cin abinci. Hakan kuw akayi kafin 8:30pm dukansu sun hallara Har Nawrah da Hammood. Sai mahaifinsu da wasu mata guda biyu ga dukkan alamu matansa ne sai yara mata guda uku da namiji guda ɗaya. namijin shine yashigo a ƙarshe bazai wuce 13years ba gabaki ɗayansa. Dukansu ƙannen Hammood ne amma iyayensu daban waɗannan mata da suke zaune a wajan sune suka haifesu kowacce yaranta biyu. Suka fara dinner cikin ƙwanciyar hankali amma affan ya damu Hammood sosai yayi murna da ganinsa dan haka zuba kawai yakeyi ko a kujera ata kusa dashi ya zauna ƙanwarsa ta zauna akai ya tasheta ya zauna kafin sugama yayi musu selfie yafi sau goma. Mahaifin dariya kawai yakeyi shiyasa yakeson Hammood yazo gida basa samun damar zama haka da iyalansa sai idan Hammood yana nan, saboda kowa na ɗaukin zama da cin abinci dashi. In bayanan kuwa ya tabbata wasu daga cikin iyalansa sukan iya months ko hanya bata haɗasu ba."
ZAYNAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI)*
Har matan mahaifinsa ma kowacce burinta ace da jituwa a tsakaninsu saboda yanda mahaifinsa kejin maganarsa. Bayan sun gama dinner sai aka zauna palour aka taɓa hira alokacin affan yashima yayi video yasake wani haka yakeyi dama koda yaushe Hammod yake gari aikinsa kenan.
A hankali da ɗai-ɗai dukaninsu suka fara watsewa har suka watse duka saura Affan shi kaɗai. Dawayo mahaifin ya koreshi yace.
"Habibi اترك اخاك حمود ليستريح (Leave your brother alone to rest)" yatashi badan ransa yasoba yayi musu sallama yafita. Suka tashi suka tafi can waje wajan wani shaƙatawa lamuben a wajan sai ruwa da akayi mishi wani design da dutsina wajan yayi kamada beach. Suka zauna idanuwansu nakan ruwanda yake zubowa. Yanayin wajanma kawai zai sauƙarda nutsuwa da kwanciyar hankali.
"Yaya ka sameta?" Shine tambayarda mahaifin nasa ya jefo masa.
"Tana lafiya" yabashi amsa.
"I need more explanation" mahaifin ya faɗi.
"Dafarko dai ina kallonta sai naji na ƙara sonta" mahaifin saida yayi dariya sannan yace"
"You got my approval" dan dama yace yaje ya ganta har indai bayan yaje yaji ani abun nata baiyi masa ba ko yaji bata ƙwanta masa araiba toh bazai amince da auren ba. Hammoda ya ɗaura da faɗin.
"Inason komai tattare da ita ina shagaltuwa da kallonta alokacinda take magana sannan alokacinda nafara ɗaura idanuwa na akanta nasamu nutsuwarda bantaɓa samun makamanciyarta ba. Bantaɓa jin irin wannan soyayyar ko alabari ba sai akaina. Babu wani sabo da mukayi da ita batama san ina sonta ba amma dana tafi nabarta na tsinci kaina cikin kaɗaicin da bantaɓa tsintar kaina aciki ba. I get used to living alone but not anymore. Moreover i see my world in her eyes" Saida Abbie ya nisa sannan yace.
" i am hapy for you yarona ya samu abunda yakeso nayi maka alƙawarin mallaka maka ita kota wani irin hali" ya girgiza kai haɗeda yin dariya yace.
"Abbie barni nazama namiji na tinkareta na samu soyayya kamar yanda ordinary people suke samu"
"Hammood Habibi you're not ordinary person. Kayi amfani da damarka alokacinda Allah yabaka. Dama yabaka ne danka moreta" Dariya kawai yayi batareda yabawa mahaifinsa amsa ba. Mahaifin yace.
"Your mum sai yaushe zaka rarrasheta harta amince?"
"Just leave her kasan Mum bazata taɓa amincewa ba. She's not the type to give up easily"
"ka rarrasheta she's still your mum"
"bayan yarinyar tazo gidan saina rarrasheta ta amince. Amma banda yanzu zata iya ruguza komai kasan hakan tunda kafi kowa sanin halinta" Baban ya jijjiga kai yace.
"Hakan yayi amma yazama dole bayan lokacin kayi mata biyayya ka sanya ta amince"
"Toh" shine abunda yafaɗa kawai. Danshima ya ƙudirta hakan amma sai bayan aure.
"Yaushe zaka koma ganinta?"
"Nan sa 1month ko three month i guess. I missed her" Abbie yayi murmushi kawai yanajin daɗin zama da sukayi da ɗansa yana masa expressing feelings dake cikin zuciyarsa yana faɗa masa cikinsa wanda abaya sam baya iyawa. Yawanci zaman kurame sukeyi sai dai mahaifin yayita hirarsa yana amsawa sama-sama. Shikam dai zaice yaji daɗin wannan tatayyar Hammood da wannan yarinya ko babu komai ya samu kusanci sosai da ɗansa gashinan yanzu a 2months ya ganshi har sau biyu idan abaya ne saisu doshi shekara basu haɗuba yakance aiki yayi masa yawa sai dai shi yatashi yaje ganinsa amma yanzu gashi yana cewa yazo ya amince kuma yazo ɗin har suna zaune suna hira cikeda sabo.
Suna zaune nawrah tafito ta samesu dayaks tasan nanne wajan zaman mahaifin nasu da dare kai tsaye nan za'a ganshi. Zama tayi a cikinsu sukaci gaba da hira. Abbie yacewa Hammood.
"Wannan zuwanne nawa ko sai wani?"
"duk yanda kayi" yabashi amsa.
"okay idan kaje saina biyoka a baya kona baro saika dawo duk yanda ta yiwu dai" Nawrah dake sauraronsu tace.
"Ina zakuje"
"Ganin surikar gidannan" abbie yabata amsa. Tayi insisting akan lallai itama sai anje da ita zataje ta ganta. Hammood yace.
"La nawrah habibty not know kibari saita amince dani tukunna sai kije mata matsayin ƴar uwa" da rashin fahimta Nawrah tace.
"What? Banganeba har yanzu bata amince dakai ba me take ɗaukan kanta?" abbie yayi dariya yasam zafin kan nawrah sannan yafara lallashinta.
اهدأ النورة حبيبتي"
"(Calm down Nawrah Habibty) Yayanki fa na miji ne karki duba matsayinsa dole saiya jajirce har indai yana son zama da mace ya ajiye matsayinsa agefe ya saka aramsa shi ba kowa bane sannan mace za ƙwantar da kanta tayi masa biyayya iya iyawarta ta sama masa farin ciki. Alokacinda ya ajiye rawanin sarautarsa alokacin zata naɗa masa rawanin a fadarta. Ke macece nasan kinsan hakan so ki barshi ya nemo soyayyarsa ta hanyarda zai iya" taɓe baki tayi dan maganar bata zauna mata akai ba kuma tasan halin abbiensu Hammood ko batunda yazo masa bamai kama kai bane bazaiyi wani tunani ba saiya amince. Bata daɗeba tayi musu salmama ta koma ciki. Tana shiga jikinta har ɓari yakeyi takira layin Mum ɗinsu bayan ta ɗauka ta shaida mata abunda yake faruwa cikeda ɓacin rai. Mum tace.
"Hakan yayi kyau sosai tunda yarinyar bata karɓeshi ba tukunna komai zaizo mana da sauƙi naji daɗin wannan labarin yanzu haka ki sanya ido kiga abunda zanyi amma sai kinmin abu ɗaya duk yanda za'ayi kiyi kutafi tare sam karki barshi yatafi shi ɗaya yayi kyakkyawan tsaro akan yarinyar nan ta tsohe duk wata kafa da zamusan yanda take wanann karon mu nuna masa muma munada wayo. Babu yanda za'ayi yana sananne a duniya ya auri wacce zamuji kunyar munata yanzu haka da zuwa gobe kisan yanda zakiyi ki shawo kansa yayarda kutafi tare idan bai amince ba cikin guards ɗinsa dole zamu samu wanda zai mana aiki" cikeda jin daɗin mahaifiyarta ta nema musu mafita sukayi sallama.
Hammood basu tashi a wajanba saida dare ya taba Sannan ya koma shashinsa an gyara ko'ina an canja komai according to his taste. Wanka yashiha yafara yi sannan yadawo ya zauna alokacin yaji wata irin kewarta a duk lokacinda yayi maganarta aranar haka zai tsunduma cikin kewarta.
"Wayarsa ya ɗauko ya tura saƙo".
-------------
Ina zaune saƙo yashigo wayata saida gabana yayi mummunan faɗuwa saboda nasan daga yanda saƙon yataho."
ZAYNAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
(WAYE SHI?)
Lokacin munagama waya da Hamma kenan dan kusan raba dare mukayi muna waya saboda washe gari zaiyi tafiya kuma zai zama busy ba lallai musamu lokacinda zamuyi waya ba. Ina shirin ƙwanciya saƙon yashigo wayata saida nasamu mummunan faɗuwar gaba sanin ta yanda saƙon ya fito. Kamar bazan duba saƙonba sai kuma na janyo wayar dan zuciyata bata iya jure share saƙon nashiga cikin message ɗin sai naga saƙo kamar haka. (Did you missed missed me?) dasauri na ajiye wayar gaban yanata bugawa nace wannan bawan Allahn duk wata hanya da zaibi yabawa mutum mamaki ya santa. Tayaya akayi yasan nayi tunaninsa? Na saka wayar a silent na ajiyeta gefe na ƙwanta bacci maimakon bacci ya ɗaukeni sai kuma nashiga tunani. Yazama dole da zarar nagama wannan exam ɗin nan nabawa Hamma damar fitowa da kowa zai sanshi iyaye su shiga magana. Idanba hakaba wannan mutumin da batasan waye shi ba zai iya fitomin ta hanyarda banyi zato ba. Da wannan tunanin araina nayi bacci."
Tun daga wannan lokacin ban ƙara samun saƙo daga gareshi ba kuma hakan ya samamin nutsuwa sosai danna tabbatarda lafiya qalau. Na kauda hankalina gabaki ɗaya yakoma kan Hamma dakuma exam dayake ƙaratowa Maryam bata sake tunamin tanason zama gidanmu ba nima ban sanarda ita yanda mukayi da Baba ba ganin Baba bai bani wani feed back ba may be koya manta kokuma mahaifinta bai amince ba. Hakan yasa bansake tuna masa zancen ba."
Yau yarage saura 3week bikin Ya Ahmad mukuma saura saura 1week mufara exam. Yanzu bama shiga school sosai saboda kowani lacture yayi covering ko Hamma bamucika samun haɗuwa dashi ba ko waya baya kirana da dare sosai sai yace nayi karatu.
Karati nayishi harna gashi dan haka nataso nafito palour yanda najiyo muryarsu Mama, anty, Anty fadeelah da Aysha. Daga lokacin dawowarmu ɗakin mama zuwa yanzu ba ƙaramin shaƙuwa bane tashiga tatsakanin su Mama dasu Aysha ba. Kulawarda suke samu wajanta ko wajan Mummynsu basu sami kamarta ba, ko abu Mama zata saya idan batada kuɗinda zata saya mana gabaki ɗaya toh takan haƙura ne. Anty ma yanzu suna gaisheta kuma tana masawa sannan Ana zaunawa ayi hira gabaki ɗaya. Ina fitowa Mama tace.
"Marmeeyy angama karatunne?"
Na zauna kan carfet nace..
" bangama ba Mama kawai na gajine shine nafito nahuta karatun duk babu daɗi"
"Gara kina hutawa ai ƙwaƙwalwar saita samu huta idanba hakaba idan stress na karatun yayi yawa sai kiga kinayi yana zubewa ana tufka da warwara"
"Ainagani dan saina gama idanna dawo baya sai naji kamar bansan komai ba dan haka ban sake ɗaukan littafi sai gobe" Aysha tace.
"Da'Allah ba'ace kizaƙe dayawa ba meye laifin da daddare? Yarinya da a Atbu kime dakin gane kurenki" harararta nayi nace.
"Keda kike Atbun ai naga kin gane kurenki" dama kusada ita nake zaune ta sanya Hannu ta dungure kaina tana faɗin.
"Kekam dai kinjiwa rashin kunya daɗi" mama tace.
"Make bakin zaki ringa yi zata shiga hankalinta ai maras kunya. Idan ta'isa tayiwa Yayanta Mana (Habibu)" Aysha tace.
"Aishi zansa yamata duka yanda bazata sakemin rashin kunya ba"
"Idan kunyi haƙuri ma ana gama Exam zan kama hanyata nabi Yaa Ahmad bazan dawo ba sai kunnemeni" na faɗa na dake. Anty fadeela wacce sai lokacin tasaka baki tace.
"Aikuwa zakije ki haɗu da dai-dai dake dan Mummy Aya ce ingaya miki" mama ta danƙwaleta da hannu ta rufa bakinta tana dariya itama Aysha dariyar tasaka harda ƴar ƙwafarta.
Muna zaune saiga Yaya Habibu yashigo da sallama haɗe da Ƙatuwar trolly a hannunsa saida yakaitta ƙofar shiga ɗakin Mama sannan ya ajiye muduka muna binsa da kallo bamu kaiga tambaya ba saiga Maryam nan tashigo da sallamarta Hannunta ɗauke da ƴar ƙaramar trolley sai jakan Hannunta. Dasauri natashi da murnata nayi kanta ina ihu zanyi hugging ɗinta ta tureni gefe tana faɗin.
"da Allah matsa ko meye ruwanki dani? Keda bakyaso nazo?" wanda sukeso naso ai gashinan sunyi magana nazo" ban kaiga tanka mata ba mukaji muryar Umminsu tana faɗin.
"Nima matsamin a hanya kona tureki kema" nayi gefe ina faɗin.
" sannu da zuwa Ummi"
"Yawwa sannu Marmeeyy " maryam tayi ciki mama tana faɗin.
"Marmeeyy bazaki karɓi kayan hannun Maryam ɗinba?"
"Batta tashigo da kayanta nafaɗa ina zaunawa Ummi ƙaraso ciki Mama tanayi mata barka da zuwa. Ta zauna suka gaggaisa. Dama tun ranar walimar sauƙarmu da suka haɗu basu sake