Showing 102001 words to 105000 words out of 171869 words
Chapter 35 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
ma marmeeyy an done kiyi mafarki mai daɗi" kwanciya nakoma nayi ina murmushi ina tuna mafarkin danayi.
"Marmeeyy bar baccin man please kitaso kizo muna jiranki idanba so kike ki fasa zuciyarmu ba" Alokacim Maryam tashigo ciki tana faɗin.
"Babe wallh yanzu kam dolema kitashi dan bazan sake jiraba kuma haba wannan wane irin baccine aike kamata yayi ace yau murna ya hanaki bacci" tana shigowa tayi arba dani ido buɗe. Dasauri ta haye gadon.
"Kai Alhamdulillhi naji daɗin tashinki haba bacci yaƙici yaƙi ƙarewa mu kanmu bamu iya bacci ha saboda ɗauki amma ke kin zauna baccinki kawai kikesha" Da mamaki nake kallonta.
"Ke kuma meya kawoki nan sassafe haka?"
"Bangane meya kawoni ba? Anan nakwana toh Kuma jiya da daddre har magana namiki tsabar baƙin hali kikaƙi kulani yanzu kinzo kina cewa meya kawoni kaji zancen shirme" Zaro ido nayi ina kallonta da sauri na fara neman wayata dan tabbatarda abunda take faɗi." akan dressing mirrow naganta dasauri na miƙe na ƙarasa wajan na ɗauka ina dubawa naga akashe take dasauri na danna switch na kunnata zuciya sai bugu take ina jira takawo sukuwa suka tsuramin ido kawai sun kasa cewa komai.
Wayar tana Kawowa nasaki ƙara na yarda gefe dan ganin pic ɗina dana Hammood a face ɗin wayar. Zaro ido nakeyi ina sauƙe numfashi kenan jiya dama ba mafarki nayi ba? Ya Ahmad yacika alƙawarinsa kenan yakaini wajan Hammood nikuma nayita masa shirme naɗauka mafarki nake na ƙarasa. Tunowa da shirmenda nayi ya sakani sakin ihu haɗeda sanya hannuwana bibbiyu ina dukan kaina. Wani irin haushin kaina da takaici nakeji. Nasan shima kansa yanajin haushina a shirmenda nayi jiya, kukan takaici nasaka dan baƙij cikin abunda nayi.
Maryam ta taso ta ɗauki wayata dana wullar itama ganin fuskar wayar ya sanyata ihu anty fadeela ta amsa tagani nan danan suka cika ɗakin da Ihu mutamenda suke cikin gida suka shigo.
"Menene yake faruwa?" suka haɗa baki wajan tambaya.
"Pic ɗin Marmeeyy da Hammood wallh shine Hammood ne yeahhh" mama ta girgiza kai ta juya gareni da nake kuka.
"Ke kuma menene abun kuka?" ban bata amsaba Mummy tayi sallama tashigo tana ganina zube aƙasa ina kuka ta ƙaraso wajena da sauri.
"A'a marmeeyy mekuma yafaru?" na ƙara ƙarfin kukan nawa ina shure ƙafa"
"Ko kiyi shiru kifaɗa mana abunda yafaru kona makeki" mama tafaɗa aƙufule. Na share hawayen haɗeda rage karfin kukan sai jan zuciya kawai nakeyi"
"Menene faɗamin ko marmeeyy ta? Meya sameki wani abun yafaru dakene?" cikin muryar kuka nafara magana.
"Mummy kingani Ya Ahmad ne yamin alƙawari duk ranarda Hammood yadawo nigeria zai kaini naganshi toh ranar sai yacemin yanada surprise ai kuna wajanma toh ni bansan menene ba. Sai jiya ashe wajan Hammood yakaini. Nikuma ganin Hammood yasa na ɗauka mafarki nake tunda banyi tunanin cewa zansamu ganinsa cikin sauƙi haka ba kuma haɗuwarma mu biyu kacal wane muhimmanci nake dashi da Hammood zai waremin lokacina ni kaɗai bayan manyan mutane da suka cancanta su ganshi suna neman ganinsa basu samuba. Toh ni naɗauka mafarki nakeyi wallh Mummy shirme kawai nayita masa jiya har cewafa nayi ina sonsa atunania tunda da an tashi bacci shikenan komai yawuce. Dana shiga ruwa nayi wanka har wanka nayi a masauƙinsa na canja kayana da wanda ya kawomin wallh Mummy duk na ɗauka mafarkine har taɓashi saida nayi atunanina tunda mafarki nake ban aikata komaiba. Toh shine yace muɗauki hoto duk amafarkin yayi saving a walpaper na har yadawo dani gida aƙofar gidannan ma yam..." Shiru nayi nakasa ƙarasawa ina tunanin yanda zancewa iyayena Hammoood yamin peck a goshina bayan baya ɗaya daga cikin muharramaina."Toh tohh shine fa yanzu kawai ina farkawa naga maryam agidanmu kamar yanda naganta jiya da dare. Kuma ina duba wayata naga pic ɗinda muka ɗauka A jikin wayata gashinan hakan yana nuni da ba mafarki nakeyi ba kuma ga kayanda nasaka nazo dashi ajikina ma" ina ƙarasa faɗin haka na fashe da kuka.
"Yanzu ke shirme kikaje kikayi masa? Allah ya kyauta ya shiryeki Marmeeyy" ina cikin kukan nace.
"mama dan Allah tayaya zanyi tunanin ba mafarki bane harfa cewa yayi yana sona a a wajan" idanba mafarki ba mai zanyi tunani tayaya zanyi tunanin Hammood zaice yana sona" juyawa tayi tafice ta takaicin abunda nayi mummy cikin rarrashi tace.
"Toh ya isa kinji idanda wanda yakamat Hammood ya warewa lokaci toh kece idanda wanda ya cancanci lokacinsa toh kece. kinfi kowa kusanci dashi a ƙasarnan gabaki ɗaya. Nan gaba zaki samu kusanci dashi wanda aduniya babu wanda Allah yabawa damar samun wannan kusancin ke"
"Mummy ban ganeba fa"
"Bayan yana sonki babu abunda ya faɗa miki?" Har zan girgiza kai sai natuno wani abun.
"Uhmm yace wai nice wacce nafi kowace mace kyau a idonsa"
"Bayan wannan babu wani?" na girgiza kai.
"Na manta sai dai idanna tuna na sanar dake"
"Okay toh tashi kiyi wanka kici abinci. Saiku fito naji Babanku yace za'ayi aiki" kai na gyaɗa hawaye nabin fuskata.
"Menene kuma Marmeeyy"
"Mummy halan yanzu yanajin haushina saboda shirmenda nayi masa koh?"
"No bayajin haushinki Ta iya yiwuwa hakanma ya nishaɗantar dashi maza tashi kishirya" namiƙe jiki babu ƙwari.
Dukansu suka fice yazama saura Nida Anty fadeelah da maryam a ɗakin. Anty fadeelah ta miƙomin wayata.
"Kingani buɗemin na tura pics ɗinda kuka ɗauka" na amsa na buɗe na miƙa mata.
"Barina fita nafara nunawa mutanen waje tukunna" tafaɗa tana kama hanyar fita abubuwanda suka faru sunata dawomin na kalli Maryam wacce take kallona da mamaki ɗauke a fuskarta.
"Babe Hammood fa shine mai turamin saƙonan"
"Nasani ai" Na zaro ido.
"Yaya akayi kika sani?"
"Ya Ahmad ya faɗamin jiya shine dalilin zamana da kana anan nakira Ummi na faɗa mata anan zan ƙwana bazan iya haƙuri zuwa gobe ba nabari kizo kibani labarin abunda yafaru kika dawo kika shareni daƙyar na iya bacci"
"Wato Ya Ahamd yasan Hammood shine ɓoyeyyen masoyi?"
"Iyi yasan yana bibiyarki amma baisan shine ɓoyeyyen masoyi ba"
"Lallak biri yayi kama da mutum" sai alokacin wasu abubuwanda ya Ahamd yakeyi suke dawomin har lokacinda yasaka na ɗebo masa kuɗi amota naje na haɗu da Hammood tabbas ko shakka babu mutuminda na haɗu dashi Hammood ne dan muryarsu ɗaya har yanayin jikinsu sannan a wancan lokacin yacemin sunansa Mood Acikin Hammood za'a cire Mood sannan kuma ƙamshin turaren ɗaya komai ɗaya ya tabbata Hammood ke bibiyar rayuwata. Amma duk soyayyata da Hammood meyasa wancan lokacin nakasa gane shine? To tayaya ma zan iya gane Hammood ne bayan ko ayanzu ƙwaƙwalwata daƙayr take ɗaukan lamarin. Ajiyar zuciya na sauƙe da sanyin jiki.
"Wai menene Babe? Ko wani abun yafaru ne? Ɗatsu kina zancen bayan kunzo gida kuma yamiki sai kikayi shiru.
"Babu abunda yafaru" sake cemin yayi yana Sona.
"Nikam danaji kin ƙaƙare kin kasa faɗa saina ɗauka kiss yayi miki"
"Allah ya sauwaƙa"
"Allah ya sauwaƙa koh? Ai naga bashi kaɗai yafara ba Hamma ya rigashi. tunda ranar ina ganin wajan event ɗin dinner ɗinsa ƙoƙari kawai yake ya haɗe bakinku waje ɗaya. Kuma bana tunanin wannan shine karonsa na farko akwai lokacinda mukaje gida su Ummi na umra naga kinfito kinata kuka na tambayeki kikaƙi faɗamin Kukayi faɗa daga sai daga baya muna abuja kuka shirya. Harni yayita kira yana cewa nabaki waya naƙi saboda jikina yabani a akwai abunda yayi miki kika shiga tashin hankali. Aranar kwana kikayi bakiyi bacci ba sannan bakiyi karatu ba gashi atlast kinyi carrying course ɗin. Sai a abuja kuka shirya. Duk mai hankali dayake tsakaninku yaga abunda yafaru yasan akwai abunda yamiki bare nida nazauna dake nasan bakida fushi. Sannan idona yazo ya ganemin abunda yake shirin yi a wajan event na bikinsa dan rashin kirki"
"Ke yayankine fa kika faɗa masa haka"
"Aysha ƴar jaraba tashiga hannu madallah" tafaɗa tana dariya na ɓata rai.
"Kekam maryam kin iya wulaƙanci wallh"
"Menene na wulaƙanci aciki keba Allah ya fissheki ba? Da wannan kayan kunyar dake za'a ƙareta kiyi kwanan asibiti tun baki haihu ba kin farke an ɗinke"
"Hmm lalli Maryam bakisan itama Aysha dan baya sonta yasa baiji ciwon aikata hakan akanta ba yabi da ita batreda tausayi ba. Ai duk yanda soyayya take akwai tausayi"
"Nidai koma menene wallh naji dadi anyi maganinta"
" Toh bari kiji wallh ba'a dariya wa motar gawa kina hanya ke bamusam yaya zaki kasance ba"
"Ahirr wallh babu abunda zai kasance wannan abunda sukayi ai tonawa kai asiri ne Ummi fa ko haɗa ido bata iyayi da Hamma"
"Allah ya kyauta" shine kawai abunda nafaɗa.
"Wai meya farune lokaci guda kika sauƙo Marmeeyy? Saida nayi taraddadin faɗa miki wannan abun saboda nayi tunanin zaki shiga tashin hankali" na jijjiga kai.
"A'a ni hakanma shine yaƙara cireminshi araina saboda nasan yayi nisa agareni"
"Kinyi nisa a gareshi dai koh Marmeeyy? Kefa yanzu ta Hammood ce a duniya wanda zasu iya bige hammood su mallakeki basuda yawa"
"Hmm" nafaɗa namiƙe.
"Kinga bari nayi wanka na shirya muje muga wani aikine a waje. Gobe yazama dole muje makaranta tunda yanzu mu mundawo ƴan duniya rabonmu da makaranta tun friday"
"Ai mubari sai wanj sati kawai gobe fa friday"
"Koma satuarday ne haka zamu shiga" nafaɗa nashige toilet. Nadaɗe a cikiin toilet ina tunanin abunda yake faruwa mai ƙarfinda ƙwaƙwalwa sai tasha wahala kafin ta iya ɗauka.
Na shirya cikin riga da zani acikin kayana nabawa Maryam tasaka dan batazo da kayaba muka fita wajan aikin. Babu kowa a cikin gida da alamu ba'a fara aikinba Maryam tatafi neman su Anty fadeelah nikuma na shige wajan Baba a palourn baba na samesu Mama da Baba sai Mummy ta anty yaciro kuɗi da alamu yana basu na wani abunda za'a saya ne.
Na gaisheda Baba shine wanda bamu haɗuda shiba dama ya amsa da fara'arsa.
Yaji daɗin ganina cikin walwala idanba idonsa ba sai yake ganin jiya da yau kaɗai nafara fike ramarda nayi.
"Mummy amma kindawo kenan koh?" na tambaya alokacin da nake ƙoƙarin tashi nabar palourn danna basu sararin ƙarasa maganarsu.
"Nadawo kenan Marmeeyy bazan sake tafiya ba har indai masu gidan sun amince da dawowata kuma sunce na zauna karna tafi" Mama ta washe baki.
"Dagaske kike Mummy kai Alhamdulillhi dan Allah kizauna karki tafi. Wallh tunda bikin yazo ina taraddadin ranarda zakice zaki tafi saboda zamanmu yayi daɗi sosai fiyeda na wancan lokacin. Yanzu duk ahunda yafaru abaya a maidashi yawuce kawai girma kamamu yakeyi mu rungumi yaronmu mu ƙarasa rayuwarmu atare"
"Nima sai yanzu na fahimci hakan zaman yafi daɗi kodan yanzu kun saki jiki danine. Nima kuma nasake ziciyata? Zaman da mukayi abaya sam baida daɗi yanzune idan zamuyi zama zamuyishi cikin aminci"
"Allah ya zaunar damu lafiya gabaki ɗaya ya kauda duk wata fitina da zata taso konan gaba" anty tafaɗa su duka suka amsa da Amin.
"Allah yayi muku albarka gabaki ɗaya ya ƙara haɗe kawunanku" Baba yafaɗa. mama ta kalleni ke tashi kitafo da Allah ana magana.
"A'a haba mamansu nifa dalilin Marmeeyy nadawo gidannan idan kikace zakina mata irin wannan hantarar sai nakoma yanda nafito"
"A'a haba dai itada zata tafi tabarmu kwannan gabaki ɗaya" Cewar anty.
"Aiko tunda zata tafi can waje mai nisa sai ayita lallaɓata har murabu lafiya"
Mama tana jinsu batace komaiba Na miƙe nafice dan ban fahimci abunda suke nufi ba. A harabar gidanmu na samu su Anty fadeelah harda maryam Amma ita tana gefe da Yaya habibu da sauran cousins ɗinsu Anty fadeelah nayi sallama na zauna.
"Marmeey zonan" yaya habibu dasuke zaune da Maryam a kujerun gefe yafaɗi. Natashi na isa wajan ban kaiga zamaba yafara magana.
"Marmeeyy manya Jiya ai banyi bacci ba nace barina tsaya naga dawowarki saiga Hammood naganshi ido da ido ya kawoki ke kuma daga kawoki gida harda Wuce gona da iri? Naga abunda kukayi ai Shegiya Ba Hammood ba ko koma waye kika gani ai bai kamata ki biye masa har yakai hannu ya riƙoki ba daga ƙarshe ina kallo yayi miki peck a kumatu. Idansu al'adarsu kenan ta larabawa ke al'adarkice da tarbiyarki haka dan ubanki? kuma bani kaɗai ba Baba ma yaga abunda yafaru dan baiyi bacci ba sai da kuka dawo yaga shigarki cikin gida sannan yace na kulle ƙofa" nayi narai-nari da ido jin cewa Baba ma yaga abunda Hammood yayi.
"Ai bakiyi kuka bama wallh sai Baba ya kirani yace na dakeki tukunna zakiyi kuka da gaske"
"Eh Marmeeyy lallai wuyanki yayi ƙwari wato har ƴan rungume-rungume kukayi" cewar Maryam.
"Allah ya isa wallh Maryam ni nace miki haka?"
"Zakija Allah ya isa dakyau alokacinda na dakeki"
"Metayi za'a daketa?" Ya Ahamd ya tambaya wanda shigowarsa kenan yafito amota yaji yaya Habibu yana zai dakeni.
"Ya Ahamd bakasan abunda yarinyarnan tayi ba dagaka kaita wajan Hammood saita wuce gona da iri ta manta da tarbiyar da aka bata"
"Me tayi haka na mantawa da Tarbiya Habibu?"
Toh gashinan nabiya harda na jiya
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Hawayenda nake riƙewane suka zubomin.
"wallh Yaya Ahmad banyi komaiba kawai ya rakoni nan ban ankara sai naji.." nayi shiu nakasa ƙarasawa hawaye suna zarya akan fuskata.
"Riƙo hannunta fa yayi daya sake hannun kawai sai yayi mata peck a forehead nata, sa'arsa ɗaya Hammood ne da wanine ai tamolo zanyi dashi wallh kuma Baba mafa yagani"
"KaCe Baba yagni?"
"Eh dan inada tabbacin yaga shugowarsu bayan yatafi yace na rufe ƙofa"
"Toh Baba yagani Habibu baiyi magana ba ai kaima da kaja bakinka kawai kayi shiru koh?" kai kasan dole akwai dalilin dayasa Baba baiyi magana ba.
"Nima nayita tunani haka danna ɗauka sassafe zai kirani nayita tamolo da ita"
"Toh taso nan kaji " yafaɗa yana riƙo kafaɗarsa suka bar wajan. Nazauna a gefen Maryam naƙi kulata.
"Wai yaya babe kika zauna kina cin magani nice fa yakamata nayi fushi datsunnan na tambaya ko kiss yayi miki kikace A'a" Saida na banka mata harara.
"Bake kikace wai munyi rumgume-rumgume dashiba bayan kuma ni bai rumgumeni ba"
"Toh meyema aciki? Hamma ma ya tsotsi baki bare Hammood" dasauri na buga mata mari a bakinta taji zafi kuwa saifa takama wajan.
"Babe kinada hankali kuwa? Kinji abunda kike faɗa kiwa? Amma kinsanni kinsan kalar tarbiyata ko hannuna bana bari namiji ya riƙe na Hamma ma tsautsayine kuma yanzu idan waɗannan ƴan bala'in sukaji fa suje su faɗawa Aysha yaya zataji idan tasan wannan abun yataɓa shiga tsakanina da Mijinta"
"Toh banza shine zaki dakeni haka da zafi da ƙarya nayi?"
"Toh nidai naji gaskiya kiyi shieu kidaina faɗa kar wani yaji na shiga uku kowa ɗaukan ƴar iska zaimin idan nace babu abunda yataɓa shiga tsakanina dashi babu wanda zai yarda dan haka ki rufamin asiri"
"Shikenan nayi shiru yanzu yaushe zaki sake komawa wajan Hammood?"
"Uhmm ke zanso nasake komawa amma wallh yanzu dana dafka masa shirme banason ganinsa kunya zanji"
"Ke nifa ban waniha shirme acikin abunda kikayi ni dukda bana kallon ball amma ace yau gani ga Hammood sai nayi yafi abunda kikayi. And ba Hammood ba zallah only to discover that shine ɓoyeyyen masoyi Kai Babe wallh irin murnarda nake ciki bansan iyakacinta ba dan Allah kiso Hammood babe ba irin soyayyarda kike masa yanzu ba irin soyayyarda kike yiwa Hamma. Hammood ya cancanci fiyeda haka dan Soyyayrda yake miki bata wasa bace. Har indai zai doke Ɗaukaka. Shahara. Kyau. Dukiya. Asal. Yare. al'ada yazo gareki yayi imagine rayuwa dake kaɗai. Toh zai iya doke komai na duniya ya rayu dake" tana magana idona yakan zobenda jiya naga irinsa sakk a hannunsa sai dai nashi yafi nawa faɗi da girma sannan babu stone akan nasmdk.
"Maryam"
"Na'am Babe?"
"Kinsan wannan zoben Hannun nawa shine ya aikomin? Jiya naga irinsa a hannunsa ba jiya ba babe a school ɗinmu lokacin danace miki ƙamshin danakeji najishi a wajan Baba har kikace ai ba llallai yazama mutum ɗaya ba? Toh Mutum ɗayane Hammood ne kuma yanzu nake tunani tabbas a wannan lokacin Hammood yazo ƙasarnan shine karonsa nafarko daya fara zuwa"
"Babe Hammood yaje yasamu Baba kenan? Hakan yana nufin tun tsawom lokaci Baba yasan Hammood yana sonki? Hakan shine dalilin fasa aurenki da Hamma"
"Hmm Babe wallh sai yanzu abubuwa suketa faɗamun amma zan tambayi ya Ahmad naj..
"Marmeeyy manyan mata wai kije inji Baba" yaya Habibu yafaɗa yan ƙarasowa wajan. Tashi ɗaya idanuwa na sukayi zuru-zuru hawaye suka ƙara cikasu. Saida yayi dariyar mugunta sannan yace.
"Ke kije kiji daɗinki Baba ma bai kalli abunda yafaru shiyaba shigarki gida kawai yaji ashe ya kirani" na sauƙe ajiyar zuciya amma har lokacin idanuwana suna zuru-zuru.
Na juyaga Anty fadeelah. Da cousin ɗinsu da suke kallona kamar wacce aranar suka taɓa kallona gabaki ɗaya naga jikinsu yayi sanyi rawar kan duk tasauƙa.
"Anty fadeelah zoki rakani dan Allah"
"Babu yanda zani jeki abunki idan faɗannema kisha kayanki ke kaɗai" jiki a sanyaye fuskar tausayi na nufi ɗakin Baba. Abunda nayi tsammani bashi na taras ba dan Baba cewa yayi nakira ƴan uwana mugyara palour tunda baƙi sun sauƙa aciki sannan Hammood zaizo yakamata ayi masa snacks. Nayi narai-narai da idanuwa.
"Baba yauma zuwan zaiyi?"
"Eh marmeeyy zuwa zaiyi ko bakyso yazone?" na jijjiga kai.
"Kawai jiya nayi masa shirme ne shiyasa yau banason haɗuwa dashi Allah yasa wajanka zaizo sai nazauna a ɗakin can na leƙeshi baisanma ina kallonsa ba."
"Kayya aikuwa ba wajena zaizo ba wajanki zaizo Marmeeyy" na sauƙe numfashi.
"Wallh Baba nina ɗauka duk mafarki nakeyi shiyasa nayita shirme"
"Iko sai lillahi Marmeeyy mafarki kuma?" cewar Ya Ahmad"
"Wallh Yaya"
"Yau idan yazo sai kice masa kefa jiya kin ɗauka mafarkine"
"Aina gaya masanma. Abunne yaya sai ahankali wallh banyi tsammanin ganin da Hammood ba natashi tun banda wayo a TV muke kallonsa shida Baba bantaɓa tunanin ganinsa ahaka ba sai ranarda kayimin alƙawarin haɗamu idan yazo toh ni banyi