Header Ads
Showing 168001 words to 171000 words out of 171869 words

Chapter 57 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1090

Ads at the middle of Article

kallo kamarsu ɗaya sakk da Hammood sai dai shi akwai girma a jikinsa nayi ƙasa da kaina, "Me kikeson sanar dani? Please tell me zanyi farin ciki sosai kuma in sha Allah ko menene zan yi miki" nayi ƙasa da kaina ina tunanin ta yanda zan fara maganar saboda inaso ya fahimceni sosai "Abie bani nakeson magana dakai ba shine yakeson magana dakai amma ya juyo dashi kaina inaga bazai iya faɗa bane amma zaifi kyau da zai faɗa daga bakinsa" Abie ya nutsu sosai saboda ganin tawa nutsuwar "Karki damu Habibty Faɗa daga bakinki can ɗaukeshi kanar shine yafaɗa" kaina yana ƙasa nace, "Mum, Mum yakeso tadawo tacigaba da zama a matsayin matarka a gidannan yanason neman alfarma a wajanka kayi masa wannan alfarmar har indai hakan bazai zama takura a rayuwarka ba, koda Mum tayi maka laifi yana nema mata yafiya a wajanka matsayinsa na ɗanta, nima ina neman alfarma Abie dan Allah kayi hakuri ka maida Mum tunda kaga har yanzu batayi aure ba ta iya yiwuwa bata buƙatar wani yashugo rayuwarta ta'iya yiwuwa tsawon lokacinnan kai kawai take jira, ta'iya yiwuwa Hannu kawai take jira ka miƙa mata ta riƙe" Abie ya kalli Hammood wanda yake pretending kamar hankalinsa na wani wajan ba akanmu yake ba, "Habibty kinsan Mum ɗinku wane irin addini takeyi?" dasauri na gyaɗa kai "Nasani Abie kuma nasan hakan bazai hanaka sake zama da itaba saboda abaya kazauna da ita kuma ahakan, idanma kanaso tadawo musulunci Abie ka jawota kusa dakai ka kyautata mata iyakar kyautatawa ka nuna mata halaye masu kyau da ɗabi'u na kwarai na tabbata waɗannan kawai sun isa suja ra'ayinta" Abie ya jijjiga kai yakai kallonsa wajan Nawrah ga mamakinsa kuka takeyi hawaye wani banin wani akan kumatunta jikinsa ya ƙara sanyi sosai ya kalli Hammood, "Tun yaushe kake da wannan saƙon gareni?" sai alokacin Hammood ya kalleshi "Tun ranarda Mum tasa ƙafa tabar gidannan" "Meyasa kaɗauki tsawon lokaci baka sanar dani ba? Da ace ka taɓa faɗamin abunda yake ranka koda sau ɗaya da Mum ɗinku bata ɗauki tsawon lokaci bata gidannan ba da bakuyi rayuwa Babu itaba" Nawrah wacce kuka yakeson cin ƙarfinta tace.


"A kullum ƙoƙarinka abie shine kabamu rayuwarda zamu manta da mahaufiyarmu baka taɓa tambayarmu ko munason sake rayuwa da itaba ko A'a ko yaya mahaifiyarmu take tayaya zamu ƙi son rayuwa da ita? tsawon Shekarun na rayu da kewarta abie kuma har yanzu inason sake rayuwa da ita anan gidan amma bazan takura maka ba kuma bazan roƙeka ba abie idan kaji kanason sake rayuwa da Mum kayi, idan bakaso kada ka takura kanka karka damu tsawon shekaru bamu rayu da itaba yanzu ma zamu iya ƙarasa rayuwarmu ahaka" tana gama faɗin haka ta miƙe tabar wajan. abie ya sauƙe ajiyar zuciya ya kalleni "Nagode Habibty Allah ya miki albarka idanba ace keba bazan san abunda yake ran yarana ba in sha Allah zan dawo musu da Mahifiayarsu suci gaba da rayuwa da ita" Nima Godiya nayi masa Hammood ma yayi masa godiya mukayi masa sallama muka wuce ciki, muna shiga na zabga masa Harara"Amma ai bahaka mukayi dakaiba cewa kayi zaka masa magana menene zakace masa nine nakeson yin magana dashi?" ya jawoni jikinsa "Sorry Rouhi nasan zaki fahimtar dashi fiyeda yanda ni zanyi shiyasa naso ki fahimtar dashi da kanki" na ɓata rai sosai, "Shikenan ai" "Sorry kimin afuwa Gobe in sha Allah nayi alƙawarin fita dake yawo" jin zamuje yawo yasani nasake ina walwala. Godiya kawai yakeyi kamar ba Hammood daya nuna da zamansu tare da akasin haka duk bai dameshi ba."


Washe gari ni dashi zallah ya ɗaukemu fita amma yarufe fuskarsa da Face-mask zaga wajaje mukeyi dama tunda mukazo bamu fita ba, wani mutumi mukaci karo dashi mai kamada Baba sakk a cikin shago da mukaje sai dai shi ya manyanta sosai na nunawa Hammood shi shima kansa yayi mamakin kamannin muka saya abunda yakaimu muka wuce.






Satinmu Biyu a gidan Abbie kafin muka ɗauki haramar tafiya daƙyar na lallasheshi muka wuce wajan Mum. Wannan karon Babu yabo babu fallasa bata dai shiga harkata amma idanna gaisheta tana amsawa gabaki ɗaya Hammood a takure yake a zamanmu wajanta saima ni nafishi sakewa, Muna wajanta Abie yazo neman aurenta ranar taci kuka kamar zatayi yaya dakyar tayi shiru Babu ɓata lokaci ta amince masa saboda itama batason ɓata rayuwarta a zama ita kaɗai, mun baro wajan Mum cikeda Murna dakuma ɗaukin abunda yake faruwa.


Shaf namanta da zancen wannan mutumin da muka gani saida ranar muna waya da Baba na tuna.


"Baba nikam ranar naga wani mai kama daki sosai a kuwait wallh Baba sakk amma shi ya manyanta sosai a wani shago da mukaje nida Hammood" nan da nana naga damuwa akan fuskarsa dake video call mukeyi yace yana zuwa yatashi ya ɗauko wani hoto ya nunamin" A tsorace nace Shine Baba wallh wannan mutumin sai dai kawai ya manyanta yanzu amma shine kamarku ɗaya sakk dashi Baba yace."Ina Hammood? Bani shi muyi magana" natashi nafito dasauri na nufi wajansa saboda naga hankalin Baba atashe yake, na miƙa masa wayar ya amsa ganin Baba yasa ya zauna suka gaisa. Basu waje nayi bansan abunda suka tattauna ba.


Bayan kamar 2weeks dayin wayarmu da Hammood yacemin zamuje Nigeria Murna kamar zanyi Yaya. A satin muka shirya tafiya amma nasha wahala bantaɓa tafiya da nasha wahala irinta ba muna sauƙa sai zazzaɓi hakan yasa Hammood yakaini gida kawai, dake shi hidimarsa Da Baba kawai yazo yi suka gama bincikensu akan abunda ya kawosu. Bayan kwana 2 Muna zaune ɗaki zazzaɓin ya sauƙa banmaje asibiti ba Baba ya aiko yana neman kowa nanda 2hours har anty fadeelah da Aysha sunzo da Yaya Ahmad dukanmu sai da muka haɗu har hassan da hussain koda kuwa ƙananune saida Baba yace aje hardasu. Harda Hammood cikin palourn Baba da Hajiya da ƙannen Baba da Alhaji Habibu, duk da Hammood bazai fahimci abunda za'ace aciki ba amma kasancewar yasan komai da za'a faɗa a wajan Baba yace yazauna ayi dashi. An gaisa Alhaji Habibu yafara magana.


"Nasan zakuyi mamakin abunda yasa aka taraku anan kamar yanda kuka sani mahaifin Babanku abokina ne na tsawon lokaci sai dai Rana ɗaya aka nemeshi aka rasa kamar yanada rana ɗaya dama yazo, ina nufin kakanku ba daga nan yake ba rana ɗaya kawai aka tsince shi kasancewar mutanen daa can da karamci wanda suka sameshi suka riƙeshi kamar sune mahaifansa idan bawak sun faɗa ba baza'a taɓa sanin cewa basu suka haufeshi ba sai dai kuma kalar fata data bambamta. lokacin baifi ɗan shekara goma sha ba a lokacin da aka tsinceshi baisan kansa koshi waye ba baisan daga yanda yake ba, anguwarmu ɗaya kuma lokacin muna kusan sa'anni yasa muka tashi atare bamu damu da farar fatarsa data zarce iyaka ba tunda munji da hausa yake magana tsawon wannan lokaci babu yanda zai kawo mana cewa ba daganan yake ba, kuma babu wanda yazo nemansa, aka sanya masa suna Muhammad aka sakashi a makaranta Bayan wasu shekaru sai Allah ya haɗasu da Hajiya gatanan akayi aure, aurensu gabaki ɗaya bai ɗauki tsawon lokaci ba bayan haihuwar yara uku aka nemeshi aka rasa ya ɓata ɓat kamar zuwansa babu bincike da ba'ayiba amma ko labarinsa babu shekaru kusan arba'in sai kawai ranar Marmeeyy taje can garinsu mijinta taga mai kama da mahaifinta sakk ta nunawa mijinta kamar ta manta da zancen saita yiwa mahaifinta magana yayiwa mijin magana bincike yayi bincike aka gane cewa mahaifin Babanku ne wnda ya ɓace tsawon lokaci shima bayan an tuntuɓeshi tabbaci ya nuna yayi zama A nijeria tun yana yaro kuma mahaifinsa ma'aikacin lafiya ne da yake zaune anan da iyalansa tun a wancan lokacin bayida lafiya yasamu taɓin ƙwaƙwalwa Rana ɗaya suka nemeshi suka rasa kamar yanda rana ɗaya yadawo garesu bazai iya tuna yayi aure kokuwa baiyiba amma shi kansa dayaga mahaifinku kamanninsu bai musa cewa babanku ɗansa bane mun shirya in sha Allah zamuje gareshi nida Mahaifinku da Ahmad mijin Marmeeyy ya shirya mana tafiya idanma takama muje harda matarsa zamu tafi da ita haka ubagiji yake lamarinsa wata rabuwar idanya ƙaddara tahar abada ce wata kuma sai dai aɗauki shekaru amma za'a sake haɗuwa. Allah ya ƙaddari zamu sake ganin mahaifinku Allah ya sada fuskokinmu da alkhairi su duka suka Amsa da Amin. Sukayiwa Hammood Godiya sosai."




PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA




Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.






Bayan mun fito gabaki ɗaya kowa mamaki yake al'amari irinna ubangiji. Bayan munsamu keɓewa muna zaune nida Aysha da Anty fadeelah aysha da dubeni.


"Marmeeyy wallh Shawarwarinki sunyi amfani kinga yanzu Hamma ya rage sosai bakiga har nayi auki ba?"


"Eh tabbas kinyi auki sosai wallh amma kinsan wani abu nifa yanda na lura Hamma harda rashin tausayi fa yanzu ta'iya yiwuwa harda soyayyarki datayi masa kamu yana jin tausayin shiyasa yake ragar miki, Ni kinga Hammood ko yaya na nuna banaso ƙyaleni yake yaushema yasamu kaina dawuri nabarshi da shan lime da lemon kullum?" Aysha tace"Lallai Marmeeyy bakida kirki wallh Allah ya shiryeki na amsa da"Amin" Anty fadeelah tana jinmu ita dai tayi shiru tana tunanin kowa da tasa abincin wani gubar wani, ita nata mijinma kwata-kwata bata gane yanayi mu'amalarsa batasan ko Dan tana sabon shiga wa lamarin bane yasa. Amma itama idan ankwana biyu tagama gane komai bataji canji ba zata ajiye girma agefe ta nemi shawarata. Wuni mukayi ranar gidan da farin ciki Baba ma kan ganinsa zakasan yana cikin farin ciki dama yanaji aransa wata rana nice wacce zan haɗa masa kan farin cikin gidansa gabaki ɗaya."




Muda Hammood muka fara gaba saboda a cikinsu akwai wanda Visa ɗinsa bata samu ba, Kuma Hammood yanada match da zai buga a wannan time ɗin. tun isarmu kuwait naga ina yiwa Hammood magana yana shashsareni ban kulashi ba saboda isar safe mukayi saida dare yashigo kwanciya sannan na sameshi, "Masoyi me nayi maka kake shareni? Idan laifi nayi maka saika sanar dani bawai kazauna kana fushi dani ba" kallona yayi baice komaiba zaiyi hanyar toilet nasha gabansa na langwaɓar dakai, "Please mana masoyi zaka sakani cikin damuwa fa" ya kamo Hannuna muka zauna, "Kema fa shareni kikayi Rouhi tunda mukaje nigeria ko neman yanda nake bakyayi gabaki ɗaya kin fita harkata gashi natashi ramawa wuni guda kin susucemin kiyi tunanin yanda naji a kwanakinnana anya bazaki daina zuwa nigeria ba kuwa?" na zaro ido, "Rufamin asiri masoyi wallh ba haka bane naga hankalinka gabaki ɗaya yanakan abunda yakaika canne banaso na takura maka amma idanna shareka nasa kaina a'ina" kawarda kansa gefe yayi yanason yimin sakalci na juyo da kansa ya kalleni zaiyi magana caraff na haɗe bakina da nasa. Saida Hammood yasan yau na shirya faranta masa dan ba ƙaramar gara ya ɗeba ba, tare muka shiga wankan a wajan wankan ma saida aka ƙara ruwa ɗaya. Washe gari kuwa sassafe na matsa masa cewa saiya kaini naga mahaifin Babanmu. Yakaini naga tarairaya a wajansu ya sake aure yanada yara guda biyu Abun mamaki suma murnar ganinmu suke, a ƙasar Hammood yabarni yatafi buga match ɗinsa zuwa lokacin gabaki ɗaya Visan su yazama ready. Baba Hajiya Alhaji Habibu Ya Ahamd da ƙanwar Baba ɗaya akazo dama ɗayar tarasu. A familynsu kamar wanda ake biki haka aka taru ashe family ne suke dashi masu yawa. Saboda gudun kokonto a azuciyar mutane Babansa kam shi ya yarda da Baba ɗansa ne a bugun farko, akaje akayi DNA test ya fito 99.9% su Baba basu daɗe acanba aka sake jaddada aurensa da Hajiya sannan suka koma harda itama." bayan angama wannan Hammood ya ɗaukeni muka koma gida.


Inada Ciki 3month amma ni bansan dashi ba shima Hammood baisan dashi ba ko yawu bantaɓa tofarwa da sunan ciki ba, Sai ƙirjina da suka ciko naɗauka yana tafiya da sahun ƙibar danayi, sai wata jaraba dagani har Hammood muka ƙara wanda shi kansa yana Mamakin abun, sai cin dabino kuma sosai ina zaune saina tashi da box guda dama tunda Abie ya fahimci inaso koda yaushe store ɗinmu a cike yake dashi, saida abunda yake cikina yafara motsi kafin nasan da zamansa ranar ihu na dinga yi gashi Hammood baya gida a tsorace ma'aikata suka kirashi ya dawo shima dana sanar masa ya masifar razama likita aka kira aka fara gwaje-gwaje harda scanning nan ya gano abunda yake cikin tun daga nan Hammood yadaina fita gabaki ɗaya kullum yananan yana kula dani kamar wata ƙwai. Shida kansa yakira Mum da Abie harda Baba ya sanar musu, kusan kullum daga gidansu Har namu cikin kira ake aji lafiyata data abunda yake cikina, Aysha ta haihu ta haifi mace aka saka mata sunan Mama. ana haka aka saka bikin Maryam da Yaya Habibu tunda aka sanar dani na ɗaura niyyar zuwa lokacin cikina yashiga 7month Sai da lokaci yayi Hammood Ya hanani zuwa kuka na dingayi amma ya ƙeƙeshe idanuwansa yace bani zuwa. Nayi fushi nadaina masa magana amma yanakan bakarsa na bani zuwa Ko zama yanda yake na daina ina kallonsa sai naji zuciya tana hantsiloni wani lokaci har zama nake nayi kuka tunda nake bantaɓa tunanin akwai ranarda Hammood zance masa ga abunda nakeso yace a'a ba, ban taɓa tunanin a irin sonda Hammood yakemin akwai lokacinda zaiso wani abu fiye dani tunma abun baizo duniya ba. shi dai ya zubamin idanuwa kawai nayi borina nagama ganin borina bayida lokacin ƙarewa, banida niyyar sauƙowa daga fushina yasa yaje Neman sulhu Ina zaune a ɗaki yashigo natashi zanbar wajan ya kamo Hannuna raina a ɓace ina kallon gefe sai hura hanci nake, ganin yanda nake hura hanci dakuma titsetsen cikina yasa shi yin dariya, gabaki ɗaya haushi ya cikani ina fushi shikuma yanamun dariya. A hankali ya jawoni zuwa cinyarsa bai damu da nauyin da nayi ba.


"Rouhi har me yayi zafi haka? Me yayi zafi da zakiyi fushi har haka da Hammood ɗinki? wannan hukuncin yayiwa Hammood tsauri dayawa Tsawon kwana uku ba kenan bakya kulani ko nayi miki magana shareni kike" na lula tunani wai dama 3days nayi ina fushi dashi? A tunanina nayi zaton nakai 1week ana abu ɗaya inaga ni nama fishi jin jiki da fushin tunda lokacin tsayi yayimin shikuwa harya riƙe kwanakin da nayi ina fushi dashi, "Rouhi ki yafeni amma bazan iya barinki kiyi tafiya ba bayan aiki tuƙuru danayi kafin samun cikin nan, bazanma iya barinki ki tafi ba inaso kamar yanda nafara rainon cikina na ƙare abina" yana fara bani haƙuri na sauƙo saboda ni kaina naji jiki. A ranar dana shiga hannunsa saida ya kusan tayarmun da haihuwar cikin wata bakwai dan wuni nayi da ciwon mara, dama tunda cikina yafara girma Hammood yake ɗagamun ƙafa bai cika kusantata ba sai sa'i-sa'i. Cikina yana wata takwas aka fara shirye-shiryen buga worldcup tare muka tafi dashi kwanamu 2 a can saiga Aysha da Hamma Maryam da Yaya Habibu ya Ahmad Hammood yaje biya yasamu yabiya nasa shida matarsa shiyasa zuwansu baiyi ɗaya ba. Suma bayan ƙwana 1suka iso gabaki ɗaya tunda aka fara worldcup ɗinnan cikin farin ciki nake daga na ƴan uwana kusa dani yaya Habibu da Maryam anashan soyayya kamar babu gobe kuma still soyayya suke da Nawrah duk da ta girme masa, zaga maryam suke yafice itama tafice suje hira saisu dawo daban-daban kamar kowanne da tafiyarsa, wannan karon Mum da Abie sukazo tare kallon match sai dai Ba hotel ɗaya muka sauƙa dasu ba. Ana gobe za'a fara match Hammood yace nafaɗa masa abunda zan bashi wannan karon idan yaci cup kamar wancan karon nace masa duk wani abunda yakeso. Aka fara match cikin sa'a har aka kai final. Baifi saura 1hour afara buga final ba naƙuda ta tasomun banfi 30minute ba gabaki ɗaya da haihuwa da naƙudar kuma ban wani wahala ba na haifo yarinyata kyakkyar gaske itaba bahaushiya ba itakuma ba balarabiya ba ana ganinta anga ruwa biyu dagani harshi tafimu kyau, Hammood saida yaje asibitin yaganni nida Baby ya tabbatar muna lafiya kafin ya nufi filin buga match a faɗinsa nabashi kyauta tun kafinma yaci cup ɗin zaiyi iya bakin ƙoƙarinsa yaci cup. Cikeda sa'a da nasara suga buga wasa bai wani tsaya celebration ba yataho asibiti suma sauran duka asibitin suka nufo ko'ina acike yake wani Babban ɗaki aka sakani mai haɗeda kujeru da komai ciki da palour duk a asibitin. Gabaki ɗaya ƴan uwana danasa suna cikin ɗakin kowanne fuska ɗauke da fara'a ana ganinsu za'a fahimci suna cikin farin ciki, Hammood shima yashugo ciki kai tsaye wajena yawuto saida yasake tabbatarwa lafiyata ƙalau yayimin peck a gefen lips ɗina yayi wajan abie ya amshi babyn. Bakinsa kamar gonar auduga fara'a kawai yake. Tako'ina sumbatar yarinyar yake ina binsu da kallo cikeda sha'awa. Saida na ƙwana asibitin kafin aka sallemu da Hammood muka kwana duk da babu masu zaman jinya amma bazai iya kwana a wani wjaanba. Bayan kammala komai a garin kai tsaye kuwait muka wuce ƴan uwan Baba sunata zuwa kallon Baby, kusan kaff gidanmu aka taho suna harda Ummi Mama daƙayr tazo sai dai bata yarda tazauna agidansu Hammood ba dayawansu Ma gidansu Baban babanmu suka sauƙa sai dai abie ya nuna rashin jin daɗinsa yana ganin barema wanda bai sansu ba bai taɓa ganinsu ba yabasu muhalli a cikin duniyar gidansa bare ƴan uwana wanda yanzu suma suna masa matsayin ƴan uwa tunda jini yahaɗa.


Babu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads