Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 171869 words

Chapter 20 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1096

Ads at the middle of Article

Ahmad yake bata zama dan bayajin tsoron disgracing ɗinta gaban kowa. harda Yaya habibu a tafiyar. Mu bamusanma dashi za'a tafi ba sai ganinsa mukayi ya shirya ya fito. Muka shiga motar dukanmu muna baya sai Yaya habibu yana zaune agaba.
Addu'a Baba yasanya mukayi sannan yayi mana sallama nan da nan naji idanuwana sun fara cikowa da hawaye dan tunda nake bantaɓa tafiya nabarsu ba koda sau ɗaya ne kullum inanan ina naniƙe da iyayena. Idona taciko taff na runtsesu inajin wani iri acikin zuciyata kamar wacce zantafi nabardu gabaki ɗaya. Har muka ɗauki hanya addu'a nakeyi acikin raina idona suna lumshe ban buɗesu ba. Ina jiyosu har suka fara hira. ban buɗe idanuwana na ba har saida naji ƙarar wayata ina dubawa naga Hamma batareda na amsa ba najira ta katse na sanyata a silent na maida jaka. Anata hira bansaka baki ba sai can yaa Ahmad yace.


"Wai ina marmeeyy ce ko bacci tayine?"


"Ganinnan" nabashi amsa.


"Naji bakinne ya mutu muɗus. Kardai duk san tafiyar abakine?"


"A'a Yaya kasan nifa bantaɓa tafiya ba"


"Tooh kar amin amai amota" yafaɗa hankalinsa yana kan tuƙinsa. Tunda muka fara nisa ya lura da wata mota a gabanmu ɓaka siɗik wanda taɗan bamu tazara kaɗan. Bayan kusan 30minute ya gano wata a bayanmu motocin ba iri ɗaya bane amma jikinsa yabashi tafiyarsu ɗaya kokuma yace tafiyarmu ɗaya atakaice. Ta bayanmu bata zo ta wuce ba dukda bawani gudu muke ba, ƴat tazara tabada a tsakaninmu. ta saita speed ɗinta dai-dai da namu namu yanda tazarar bazatayi yawa ba sannan kuma kusancin bazaiyi yawa ba. Ta gabanmu kuma batayi nisa damu sosai ba. sunyi abun atsari yanda baza'a fahimci komai ba amma Yaa Ahmad dake yasan komai dole zai fahimci wani abun.
Murmushi kawai yayi dan ya tabba wannan motar tare muke tafiya dasu. Yayi tsammanin hakan sai yaji abun ya matuƙar birgeshi dan koshine a matsayin Hammood zai bawa abunda yakeso tsaro na mamaki wanda idanba ikon Allah
ba babu wani abunda zai iya tunkarar abunda yakeso. Hankalinsa ƙwance yake tuƙinsa har muka kusa isa Abuja."


__________




Ƙarfe uku na dare jirginsu ya sauƙa a Abuja cikin sirri dan babu wanda yasanda hakan. Ko ma'aikatan filin jirgin manyan kawai sukasan da sauƙar kuma angargaɗesu da kar kowa yasani dan haka bbau wani yasani daga ƙofar filin jirgin motaci sukazo taryansu aka wuce dasu masauƙinsu.


Yariga mahaifinsa sauƙa danshi sai awajan asubahi ya sauƙa dama shi yake jira tafiyarsu da bambanci.shi daga Abu dhabi yazo mahaifinsa daga kuwait kuma lokacin tashinsu ba ɗaya ba so dole aka samu bambamcin lokaci dama shi isowar mahaifinsa yake jira so yana isowa jirginsu yatashi zuwa bauchi Acan sukayi sallar Asubahi.


Abhie yana sanardashi cewa Nawrah ta matsa sai yazo da ita. Baizo da itaba saboda bai fahimci amfanin zuwannta a yanzu ba yayi mata alƙawarin next zuwa da ita zaizo amma yanzuma yasan halinta da taurin kai ba lallai idan ya amince ta zauna ɗinba. Murmushi kawai moood yayi sanin cewa sassafe Marmeeyy zatabar garin koda tayi gigin zuwa bazata haɗuda itaba dan yasan damuwarta ta ganta ne kawai, shikuma ba yanzu yayi niyyar nunawa duniya itaba yasan wacece Nawrah da zarar da santa ta kowa ya santa. Yasan yanda rayuwarsa take akan idon mutane ko kaya yasaka sai an faɗi kuɗinsa har turarenda yake shafawa mutane sunsan kuɗinsa. Amma wannan karon lamarin ysha bambam. Ya barwa mutane abunda yaga damar su sani amma banda wannan itaɗin sirrinsa.




ZAYNAB BAWA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




A lokutan baya aryuwarsa baiyi tunanin akwai abubuwa masu muhimminanci wanda muhimmancinsu har yakai bazai iya fitowa duniya ya nuna musu ba sai yanzu daya kamuda soyayya a cikin zuciyarsa. Yana Masifar sonta da kishinta wanda yasa bazai iya jurar ganin ta ɗaura pics ɗinta a social media ba. Aranarda taɗaura pics ɗinta batareda niqab da Hijab ba ji yayi kamar zaibar duniya dan baƙin ciki. Yanzu yasan yanda ake tallali da ɓoyen abunda akeso. Kuma shi koda nan gaba bayida ra'ayin fitowa ya nunawa duniya suffar rayuwarsa da matarsa wato yana nufin kamar yanda celebraties suke ɗaura matansu da rayuwarsu su nunawa duniua shi bazai iya ɗaura musu ita su gani ba. Marmeeyy tasa ce shi kaɗai batareda fans ɗinsa da sauran mutanen duniya ba. Zai killace abarsa ya bata kulawa. Amma yanzu lokaci baiyi ba da zai sanarwa da duniya da zamanta alokacinda zai yi hakan toh yanada tabbacin yanada ikon da zai iya kareta kota wace hanyace yana nufin alokacinda tadawo ƙarƙashinsa yana kallonta kusa dashi.


ƙarfe 12:00pm tayi musu a cikin gidan Baba dayake dama Baba yasan da zuwannasu dan haka yayiwa Alhaji Habibu magana. Mahaifin Mama kenan shi kaɗai suka taryesu.


A wancan lokacin da Mood yazo wajan Baba yaɗauki week guda yana jigila amma Baba yaƙi yarda ya amince masa da bashi auren Marmeeyy. Baba kuwa yayi hakane bawai dan bai yarda da Halayansa da soyayyarsa ba. Celebraties gabaki ɗaya rayuwarsu a fili take. Barinma footballers ko shaye-shaye player yakeyida neman mata ansani saboda su kansu ƙungiyar ƙwallon sunada nasu ƙa'idojin. Duk wannan shirmen basa ɗaukarsa. Soyayya kuma har indai zai tsalleke kaff matanda suke gabansa celebreaties da masu faɗa aji a duniyar baki ɗayanta yazo neman auren Marmeeyy wacce a anguwarsu ma ba wanda ya santa sai ƴan tsirarrun mutane toh lallai soyayya takai a kirata soyayya. Tun zuwansa na farko ya yanke shawarar bashi auren Marmeeyy amma dole saiya gwada masa muhimmancinsa ƴarsa. Yasan komai ya nema a rayuwarsa yana samunsa cikin sauƙi amma yanaso ya gwada masa banda ƴarsa dole saiyasan darajarta kafin yabashi aurenta.


Saida yayi shawara da Yaa Ahmad. Dafarko ya Ahmada kamar almara yaɗauki abun dukda yasan Baba bazaiyi masa wasa ba har saida yaga Mood da idanuwansa. Bayan sun haɗu Ya Ahamd yabashi goyon baya ɗari bisa ɗari yasake ƙarfafa masa guiwa akan hukuncinda ya yanke.


Daga nan Baba ya yankewa zuciyarsa da zai bashi aurenta tunda ya fahimci abune mawyyaci yasamu wanda yake sonta kuma zai kulada ita kamarsa. Tun aranar farko ya fahimci hakan. Shiyasa tin ranar Ya roƙi alfarma a wajanta saboda zai yanke hukunci akanta. Alokacin zuciyarsama bata gama tsayawa hukuncin daya yanke ba amma magana da Ya Ahmad yasa ya tsayarda zuciyarsa waje ɗaya. Yasan duk yanda akaje akazo zai amincewa aurenne. Tun alokacin wancan zuwan Baba ya amince masa yayi alƙawarin bashi aurenta shiyasa yakoma cikeda ƙwarin guiwa amma sai dai shima Baba ya nemi alfarmar karya nuna mata kansa kamar yanda bata sanshi ba suyita tafiya ahaka har sai lokacinda Baban da kansa ya bashi umarnin hakan. Mood Ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari dan shima kansa yaga ƙarancin shekarunta sosai. Ko wannan zuwan kafin suzo saida suka sanarda Baba. Dan haka ya rigada ya shiryawa zuwan nasu. Suna zauna sun tattauna sosai akan maganar har suka kaiga matsaya a amma sai washe gari zasu gama yanke magana. Baba da Alhaji Habibu ganin abun sukeyi kamar amfarki kamar wani almara gani yakeyi kaman zai tashi a bacci yasamu mafarki yayi. Ace yau waɗannan mutane sune gidansa neman auren ɗiyarsa.






5hours ta shigar damu garin abuja. Lokacin da muka isa rana tayi ana shirin kiran azahar. Muna shiga garin Abuja waɗannan motocin da suke biyedamu kowacce takama tata hanyar ba Hanya ɗaya sukabi Ba dan ɗaya ta riga ɗaya fara tafiya kuma sunyi hannu riga hakan yasa Ya Ahmad yafara kokonton ko dama tun can tafiyar ba ɗaya bace kawai shine yayi tunanin haka ganin yanda muke tafiya ƙafa da ƙafa.


Gidansu Mummy dake maitama muka nufa. Gidane ƙayatacce nai kyawun gaske wanda zan iya cewa bantaɓa kallon gida mai kyawunsa ba. Gate uku ne kafin isa cikin gidan kuma kowanne sai anyi tafiya kafin aje ɗaya. Tsararren gidane sosai wani shashi muka nufa kusan duk sashin gidan iri ɗaya ne. Yana isa dai-dai parking lot dake jikin gidan yaja ya tsaya. Tun kafin mushigo Cikinsu Aysha da Anty fadeelah yagama ɗuran ruwa ana kallonsu za'a fahimci suna matuƙar tsorace. Saida Ya Ahmad yayi magana sannan naga sun fara ƙoƙarin buɗe ƙofar muka fita dukanmu. Muna fita wasu daga cikin ma'aikatan suka taho wajan motar aka buɗe musu boot suka fara shiga da kayan. Yaa Ahmad yaja hannun Yaya Habibu suka barmu a wajan.


Aysha ce tayi ƙarfin halin juyawa tabar wannan part ɗin ta nufi na gefensa ganin anty fadeelah ta rufa mata baya sai muma muka bita.


A palour muka samu wata dattijuwa a aƙalla zatakai 75years tana zaune a kan kujera da wasu wanda bazasu wuce sa'anni da itaba. Muka shiga da Sallama suka amsa.


Matan kana kallonsu zaka tabbatarda cewa manyan matane dan tsufarsu bata hanasu yin kwalliya da kayan alatu ba. Hannu da wuya duka sunsha zinari sai yalli sukeyi.


Muka isa ciki matar dana kallonsu da saki fara'a tana tarɓanmu. Muka zauna muna gaisheta ta ansa da sakin fuska gabaki ɗayanmu kamar tasanmu duka.




"Yaushe kuka sauƙa?" cewar wannan matar


"Yanzunan ma" Aysha tabata amsa.


"Baku shiga wajan Mummynku ba kenan?" ta tambaya. Anty fadeelah tace.


"bamuje ba ni wallh ma tsoro nakeji. Hajiya tana fushi damu koh?"


"Ni ina nasani ne? Kunyi mata laifine?" kunsan halin mumynkubai ba'a iya predicting yanayinta" .


"kutashi kushiga ciki ku huta sannan kuzo kuje wajanta koma fushin takeyi ai yanzu idanta ganku zata sauƙa" muka shige ciki ba mu muka fitoba sai ana daff da la'asar. Part ɗin Mummy muka wuce kai tsaye. Babu kowa a palour muka zaun anan bamu daɗe da zamaba mukaji footstep tana sauƙowa gabaki ɗayansu naga sun miƙe jikinsu har kyarma yakeyi tana sauƙowa idanuwanta suna kanmu.




ZAYNAB BAWA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Bazaki iya tantance irin kallonda take mana ba har taƙarasa sauƙowa fuskarta babu fara'a sannan kuma bbu alamun ɓacin rai atattare da ita. Idonta yana kanmu taƙaraso ta tsaya kamar bata sanmu ba amma idanuwanta yana kanmu, Muna haɗa idanuwa da ita na sakar mata murmushi ta tsayarda idanuwanta akan fuskata dake ƙunshe da murmushi.


"Marmeeyy" tafaɗa cikin sanyayyar murya ayayinda tasaki fuskarta ta ɗaura annuri akan fuskar. Na ƙarasa kusada ita da fara'a ina faɗin.


"ina wuni Mummy?" Ta amsa tana kamo kafaɗana tace"


"Lpy Marmeeyy yasu mamanku?"


"lpynsu ƙalau" nabata amsa. Ta ja hannuna muka zauna tana faɗin.




"Marmeeyy angirma kinyi wayo sosai kin zama budurwa sai dai kamanninki basu canja ba duk yanda naganki zan ganeki" nayi murmushi ina gyara zama a gefenta. A lokacin suka ƙaraso Suna gaisheta ta amsa batareda ta kallesu ba. Muka zauna a wajan tana yimun tambayoyi amma ko sau ɗaya bata sako Baba aciki ba.


Tsawon lokaci muna zaune a wajan muna hira tasake fuska sosai ni duk wani abunda ake faɗa akanta ban ganiba dan hira take yimin sosai kosu Aysha bata kulasu kamar yanda ta maida hankali akaina su naga wani shassharesu ma takeyi. Gabaki ɗaya kuma ɗari-ɗari sukeyi da ita kamar wanda suke tsoron ta sanya musu duka.


Ana kiran sallar la'asar Mummy tafara miƙewa ta kalleni tace.


"Marmeeyy ina aka ajiye kayanki?" nace.


"Bansaniba mummy anshiga dasu dai tun farkon zuwanmu" Alokacin takira masu aiki ta tambayesu yanda suka kai kayan. Suka shaida mata ɗakinsu Aysha. Anan tace su maida kayana ɗakinta anan zan zauna har sai ranarda natafi. Su aysha Abun yabasu mamaki ganin yanda Mummy ta karɓeni abunda basu taɓa tunani ba kenan. A'iya zamansu da itama basu taɓa kallo tasake dawani hakaba.


Su Aysha suka tashi kowacce tatafi ɗakinta. Mukuma mukabi Mummy kamar yanda ta buƙata. A ɗakunanta guda biyune a ɗaya daga aciki aka saka kayanmu. Mukayi sallah sannan muka fito.




Bayan magrib aka fara shirin tafiya tea party wanda matar Ya Ahmad ta shirya.


Mummy tasaka an shirya mana kayanda zamu sakaa wajan tea party ɗin. Sai dai kayanda aka kawo gabaki ɗaya banajin zan iya saka kowanne aciki. Gown ne gabaki ɗayansu wanda shape ɗinsu yabi jiki sannan gabaki ɗaya gefensu a tsage yake tun daga ƙasa har zuwa Guiwa. Hakan yasa dagani har Maryam muka yanke shawarar bazamu jeba dan gabaki ɗaya wayewarmu bata kaiga saka wannna kayanba. Anfara tafiya Mummy tashigo taganmu zaune. Ta ƙarasa shigowa tana faɗin.


"A'a marmeeyy anata tafiya fa Yaya baku shirya ba?" kai tsaye nace.


"Riganne Mummy takama jiki kuma a tsage take tundaga gefe har ƙasa" Mummy tace.


"Kayya Amma zaku iya sakawa tunda Event ɗinkune zallan na yara gasu Aysha can sun shirya" Dasauri na girgiza kai nace.




"Ya Ahamd zaiyi magana" Da mamaki Mummy take kallona tana tunanin wane Ahmad ɗinne zaiyi magana. Idan wanda tasanine ko ita kanta bata taɓa yin wani abun ya nuna mata ba dai-dai tayiba duk da kasancewar rayuwarta tacika da abubuwa marassa dai-dai dayawa amma bai taɓa nuna mata hakan ko a fuska ba. Mamaki yaƙi barinta haka tadaure tace.


"Toh ku sanya abaya ku tafi da ita" nɗan turo baki haɗeda furzarda numfashi nace.


"Mummy kibari kawai zuwa gobe. May be ba wannan dressing sukeso wajan event ɗinba idan muka sanya mukaje kinga mun ɓata musu" mummy tayi shiru kawai tana kallona tana mamakin yanda nafito nake faɗa mata abunda yake raina ba kamar yanda kowa yake mata ba da zarar tafaɗi abu shikenan babu kai musawa ko dai-dai ne ko akasin haka. Yanzu haka tasan su kansu su Aysha kayan baiyi musu ba amma dayake tace su shirya suje haka suka shirya batareda sun nuna ransu bayaso ba.


"Kuyi zamanku idan kun gama kufito kuyi dinner" shine abunda tafaɗa tayi ficewarta. Kai tsaye wajansu Anty fadeelah tawuce tasamesu sun shirya amma basu kaiga fitaba. Da alamunsu dukansu suna takure a cikin kayan. Batareda sakin fuska ba tace.


"Idan kuma kayan baiyi muku ba you can change to Abaya or something kokuma ku haƙura da zuwa idan kunso" da mamaki suke kallonta basuyi zaton fitowar kalmar daga bakinta ba. Tsayawa kallonta sukayi ta haɗe rai tace


"zaku iya tafiya idan kunso" Dasauri Anty fadeelah ta girgiza kai tace.


"A'a zamu haƙura da zuwanma gabaki ɗaya" mummy ta kalli Aysha dasauri Aysha ta jijjiga mata kai alamun itama tafasa zuwa. Mummy ta taɓe baki tawuce tazauna sukuma suka Shige ɗaki dan canja kayan.


Mummy tana ficewa na miƙe nashige wanka. Ina fitowa Ameerah tace.


"Babe Hamma ya kiraki kina wanka" na sauƙe ajiyar zuciya jikina yayi masifar sanyi duk zafin zuciyata yanzu yaci ace na sauƙo haka dan Hamma yayi dana sanin abinda ya aikata. Kafin nakaiga jikin bed yanda wayata take ajiye wani kiran yasake shigowa na zauna a gefen bed ɗin Nakai hannuna na ɗauki wayar gabana yana faɗuwa amma babu yanda zanyi haka nayi picking nakara a kunnena, daganan ina iya jiyo sautin ajiyar zuciyarsa. Nayi shiru bance komai ba. Cikin sanyin Murya yace.


"Baby kina jina?" uhmm na amsa sannan nace.


"Ina wuni?"


"lpy baby bakiga messages ɗina bane" shiru nayi hakan yasa yagane nagani kawai na shareni.


"Baby kiyi haƙuri dan Allah ki yafemin kinji? Bazan sake aikata makamancin haka gareki ba plesae baby" Nasauƙe ajiyar zuciya sannan nace.


"Yawuce"


"thank you baby nagode"


"shiru kawai nayi yanata jana da hira nikanma kunyarsa nakeji har maryam tayi wanka tafito lokacin nafara amsa masa magana. Murmushi kawai tayi dama ita ajikinta tasan dole za'a shirya tunfa Hamma yana matuƙar sona nima haka. Harta shirya ni ina zaune ina waya saida Mummy aiko a kiramu kafin nayi masa sallama natashi na shirya nasaka kaya nayi sallah sannan muka fita. A palourn ƙasa mika samu mummy muka ƙarasa wajanta. Muna zuwa nace.


"Sannu da Hutawa Mummy"


"Tayi murmushi sannna tace.


"Yawwwa Sannu Marmeeyy. Menene sunan Ƙawar taki?"


"Maryam" nabata amsa. Ma sha Allah kawai tace sannan ta maida hankalinta a kan wayarta da wasu mutane kusa ita da alamun tana zaɓen kayane.


Alokacin su Anty fadeelah suka fito Kai tsaye muka wuce wajan cin abinci Bayan mungama dukanmu muka dawo palour. Mummy kam waya kawai takeyi akan shirye-shiryen bikin mukuma hankalinmu nakan TV.
Alokacin wani matashi ya shigo.




ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya

Ya ƙaraso ciki cikin ladabi da girmamawa ya gaida Mummy ta amsa sannan tfara faɗin gasunna. Waɗannan yaranane sune zakayi musu ɗinkin amma dole yazama zuwa gobe za'a samu dan a Event ɗin gobe za'ayi amfani dashi wanda nasa aka tura maka dafarko kenan ba. Sauran kuma zuwa jibi banaso a samu matsala. Tayi magana cikeda bin umarni shikuma ya amsa dasauri sannan yace.


Wani irin style za'ayi musu?" bata bari mumyi magana ba tace.


"inaga kaman dukansu ayi musu doguwar riga koh?" saika gwadasu ka ɗauki measurement nasu. Su Aysha harsun miƙe. nace.


"Nikam Mummy basaiya gwadani ba zan tura masa measurement nawa kuma yayimin riga da skirt kawai. Mungode Allah yasaka da alkhairi yaƙara buɗi" baki buɗe suke kallona dan sunsan mummy bata faɗan abi ayi mata musu Amma ga mamakinsu sai sukaga tayi murmushi tace.


"Okay kayi mata nata riga da skirt ɗin. Kukuma sauranfa tafaɗa tana kallonsu" Aysha tace.


"Nima riga da skirta ɗin nakeso"


"kefa" Mummy ta tambayi maryam.


"nima haka" tafaɗa anty fadeelah kuma tace itakam abar mata doguwar rigar. Measurement ɗinsu kuma Mmy tace yabari zata aika masa dan taga alamun basason gwadawan kawai bazasu iya faɗa mata bane.


Alokacin yayi Mata lissafin kuɗin duka tana kaya dana ɗinkin. Idan zaiyi mata ɗinki design da colour na kayan kawai take tura masa saiya saya ya ɗinka ya kawo mata. Yana gama mata lissafi kawai tayi masa transfer yatafi."


Sai wajan 10:00pm masu event suka dawo. Lokacin mukanma harmun shiga kwanciya. Maryam tana zuwa ta ƙwanta bacci nikuma nahau waya dayake
mun ƙwana biyu bamuyi ba. Wajan 11:30pm Mummy tashigo ɗakin inajin alamun shigowarta nayi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads