Header Ads
Showing 165001 words to 168000 words out of 171869 words

Chapter 56 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1101

Ads at the middle of Article

aranar zan koma akwai abunda ya tsareshi amma zan tafi aranar" daƙyar na roƙeshi ya ƙaramin 4days Zan cika 2weeks kenan ganin ta iya yiwuwa yasamu time yazo ɗaukana a lokacin yasa yayi haƙuri yabarni. ana gobe zai iso.na shirya zuwa gidan Anty fadeelah Maryam ta rakani mukaje tun 12am sai wajan la'asar Mukabar gidan zuwa gidan Aysha.


akwance muka sameta itaba zazzaɓiba amma wai batajin daɗi anan mukayi la'asar Maryam tashiga kitchen tayi mana girki Hamma daya shigo ya samemu sake fita ma yayi. Asyah taci abinci firr taƙi wai bazataci ba na dubeta.


"Wai ke Aysha meyake damunki ne? Kince babu yanda yake miki ciwo amma bazakici abinci ba"


"Kamar zatayi kuka tace wallh ni Marmeeyy aurenne yafita akaina zan koma gida kawai abu yaƙici yaƙi ƙarewa kullum aiki guda ɗaya" nagane abunda take nufi sai tabani tausayi cikin sigar lallashi nafara bata shawara.


"Kiyi haƙuri amma ni inaga kamar harda tsanar abun da kika sakawa ranki kinƙi sake jikinki kullhm ciki tsoeo kike inaga wannan kaɗai zai sanya miki tsanar abun amma da zaki gwada daurewa kizama jaruma kuma kema kina bada gudumawarki zaki samu sauƙi sosai" hawayen kan fuskarta suka ƙarasa gangarowa, "Ke dai kawai Marmeeyy saboda naki mijin bahaka yake ba shiyasa kike maganar dauriya amma ina wani dauriya da zanyi fisabilillhahi?" cikin tausayawa nace toh mai zai hana ya yana yawan shan lemon ko lime ku ajiye drinks ɗinsu sa'i-sa'i zakiga yarage" abubuwan da Hammood yake sha a duk lokacin danaƙi bashi haɗin kai na faɗa mata shima yana rage zafi dasu da wasu ƴan dabarun da baza'a rasa ba. "Marmeeyy kina ganin isan nayi hakan ba wata jarabar zan ɗebowa kainaba", "Babu wata jaraba ki gwada ki gani" abubuwan danace mata yasha tun kafin mutafi ta kirashi ya sayo Maryam ita muna maganar ma jaa gefe tayi tana waya da Yaya habibu."


A daren ranar Hammood ya iso ƙwana 1kawai muka ƙara muka kama Hanya naci kuka kamar raina zai fita. Ba abu dhabi muka wuce ba kai tsaye kuwait muka sauƙa."




PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.




Isar cikin dare mukayi amma duk da haka munsamu tarɓa sosai sai dai Hammood bai yarda mun gana da mutannen cikin gidanba yace sai zuwa safiya, duk da kasancewar gidan kamar safiya haka yake ko'ina tarr hasken fitulu ga sojoji sunata shawagi ko'ina tareda ɗai-ɗai kun mutannen gidan ina kallon gidan ina sauƙe ajiyar zuciya ina ganin gidan Hammood wata duniya amma ga duniya guda
anan ina tunani koshi kansa mai gidan baisan yawan al'umma da suke rayuwa a cikin gidanba, Kai tsaye Masauƙinmu muka nufa kamar yanda ya buƙata dake akwai gajiya a jikina muna isa na cire kayan jikina na shiga wanka ina fitowa nabi gado na ƙwanta. Kafin Hammood yayi nasa wankan ni har bacci ya ɗaukeni. Ya zauna gefen gadon da murmushi ɗauke a kyakkyawar fuskarsa ya dafa jikina yana kallona, a hankali ya motsa lips ɗinsa yafara magana.


"Rouhii هل أنت نائم?" (Are you sleeping?)" cikin bacci naji muryarsa yana magana a hankali na motsa batareda na farka ba nayi sounding "Uhmmm" "Rouhi tashi kiji wani abu" cikin baccin na maƙe kafaɗa saboda baccin baiyi nisa sosai ba, "Rouhi please mana wai haka zaki barni batareda kin kula dani ba?" yayi magnar yana sauƙe numfashi mai ɗumi, "Masoyi dan Allah kabari kaga nagaji Kuma bacci nakeji" nayi maganar idona yana rufe "I know Rouhi it won't take time nima agajiyen nake kawai zan rage abunda ya tarumun ne 15days fa" na turo baki "Gaskiya 5 minute nabaka inaso nakoma bacci" Hmm kawai yayi sounding saboda yasan ba abune mai yiwuwa ba. Hannunsa yakai zuwa cikina yana shafawa.


"Rouhi har yanzu banyi ajiya bane?" na buɗe idanuwana suka sauƙa akan kyakkyawar fuskarsa ya sakarmin murmushinsa mai ƙayatarwa, lumshe ido nayi na sauƙe ƴar ƙaramar ajiyar zuciya inajin Sonsa da ƙaunarsa a cikin zuciyata."Kaida kayi ajiya baka saniba ni tayaya za'ayi na sani" "Zaki sani mana tunda wake nabawa ajiyar" na lumshe idanuwana kawai inaji yanda ya yake yawo da hannunsa a cikina, daga nan yayi sama da hannun zuwa Kirjina na lumshe ido ina amsar saƙonnin dayake aikamin shikuma idanuwansa yana kaina yana bina da wani mayen kallo, hayewa kaina yayi gabaki ɗayansa numfashinmu yana dukan na juna na nishi kawai nakeyi ina shaƙar ƙamshin turarensa a hankali yake yana shafa fatar jikin da tayi laushi tayi luwai-luwai sheƙi kawai take, Bansan dalili ba amma a hankali yake bidani kamar wata ƙwai bangane dalilinsa nayin hakanba saida yazo sai shigeni Ihune kawai bansaka masa ba. Yayi amfani da damar daya samu wajan sauƙe duk wata gajiye dake jikinsa akaina hakan yasa washe gari saida nayi baccin safe sosai sannan na tashi nayi wanka shima ashe bai fitaba ya jirani tukunna muka shiga ciki. Kamar yanda Hammood yafaɗa lamarin haka yake babansa yana matuƙar ƙaunata da hakan ya gaza ɓoyuwa nan da nan kawai yake dani hakama ƙannen Hammood idan suka isheni da surutu Hammood har koransu yakeyi. Nawrah kuwa sau ɗaya muka haɗu koda muka haɗu bataji tamin magana ba nima banbi takanta ba. Muna zaune da wata yarinya da bazata wuce 10yrs ba itama ƙanwar Hammood ce mata su 3 nagani babbarsu gabaki ɗaya bazata wuce 16yrs ba sai wani ɗan 13yrs namiji da wannan sai ƙanwarsu wacce bata kaisu ba toh gabaki ɗaya jinina yafi haɗuwa da wannan Nimlah kusan tunda nazo a wajena take wuni.


Muna zaune Hammood da abie suka shigo na nemi waje ɗaya nazauna nadaina hirar na nutsu domin inajin kunyar abie sosai, shima ya lura da hakan amma sai yadinga jana da Hira saboda yanaso na sake dashi, Hammood ya ƙaraso wajan da muke ya tsugunna cikeda kulawa yace.


"Rouhi kina lafiya? Bakyajin takura azamanki? Akwai abunda kike buƙata if you need something ki sanar dani" ya jeromin tambayoyi batareda yajira nabashi amsar ko guda ɗaya ba.


"Babu komai Dabino kawai nakeson ci" caraf a kunnen Nimla yayi murmushi bai kai ga bani amsaba Nimlah ta cafke, "Habibty zomuje nakaiki wajanda zaki samu dabino akwai company su anan" dariya nayi ina kallonta yanda tayi magana cikeda yarinta "Campany kuma?" "Or Sorry factory" sai alokacin Hammood yayi magana.


"Habibty jeki ɗauko mata dabino kawai kinji?" ta jijjiga kai please Habiby muje Wajan tagani please" abie dake tsaye yace.




"Mood Habiby idan zataso zuwa wajan ka kaita tagani mana? Zaman waje ɗaya bazaiyi mata daɗi ba" Ya kalleni yanaso yaga inason zuwa ko a'a na jijjiga masa kai dasauri, ya shafo kaina kamar wata ƙaranar yarinya "Okay muje" miƙewa nayi dasauri Nimlah ma tamiƙe tana murna. "Zaki iya tafiyar ƙafa ina" ya tambaya alokacinda muke ƙoƙarin fita, kai kawai na gyɗa masa muka fice a hankali muke tafiya mu 3 harda Nimlah mun wuce wajaje da dama duk yanda mukaje sai Nimlah ta faɗamin wajan. Ashe wajan bawani nisane sosai dashiba tun kafin mu gama ƙarasawa na hangi dogayen bishiyoyin dabino a jere a layi kowanne tsakanin bishiya akwai pond dogo wanda ya daɗa ƙayata a wajan, munyi tafiya mai tsayi amma bamu ƙure bishiyoyin ba sannan bamu daina ganinsu ba har saida muka kai wajan wani Gini wanda ma'aikata sanye da kayayyaki suke fitowa ga manya-manyan motoci da ake ɗaura boxes aciki. Muna isa ƙofar wajan ma'aikatan suka fara ɗiban gaisuwa kamar suma wanda suke marmarin ganin Hammood ga dukkan alamu Hammood yakan daɗe bai leƙa wajanba manager na wajan gabaki ɗaya yazo ya gaishemu sannan yayi mana iso cikin wajan muna ganin yanda ake sarrafa dabinon ko nace ina gani saboda su sun saba gani, dabino ne kala-kala wasu a boxes wasu a containers kowanne da tambarin Campaynyn babansu ajiki wasu dabinon ɗanyu wasu masu danƙo ayanda na fahimta wajan masarrafa ce wanda ake sarraba nau'ikan dabino ta hanyoyi daban-daban a watsa shi izuwa duniya. Guda 1 kawai naɗauka nasaka a bakina muka fito, Hammood yasaka wani yaraka Nimlah gida mukuma muka ƙarasa wajan wasu kujeru da aka ajiyesu cikin tsaruwa da ƙayata idon mai kallo, samawa kansa wajan zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun sannan ya miƙamin Hannu akan nima nazauna, na saka hannuna cikin nasa ya zaunar dani akan cinyarsa. Yakoma ya jinguni tareda miƙe ƙafafunsa nima jinginuwar nayi na miƙe ƙafafuna akan tasa.


"Masoyi" na kira sunansa cikin siga mai kamada lallama ko lallashi ko son wani abu daga gareshi, idanuwansa yana lumshe ya amsa da"Uhmm". "Masoyi please don't get angry inaso muyi magana" yayi ƙaramin murmushi"Rouhi dama ina fushi ne?" "No amma kana canjawa a lokacin da mukayi maganar" "Okay toh i won't me kikeson faɗamin" Saida nayi shiru ina tunanin ta yanda zanyi maganar ya fahimci nufina sosai, "Masoyi dan Allah ina neman alfarma nasan karayu tsawon shekaru cikeda kaɗaici duk kuwa da soyayyar da kake samun wajan mahaifinka amma kaso soyayyar Uwa ka rayu da ita nasan bazaka ƙi abie su Rayu da Mum ba despite abubuwan da suka faru, a zahiri yanda gangar jikinka da mu'amalarka suke nunawa ba hakan bane wannan yasa abie ko yanada niyyar sake zama da Mum zaiga bai samu fuska a wajanka ba kuma itama ko tanason komowa zataga bazata samu fuska a wajanku ba, duk wannan yafaru dalilin abubuwan da suke kallo a zahiri zai hanasu ɗaukan wani matakin dawo da rayuwarsu tare, amma ni nasan ba haka yakeba a wajanka kanason Mum tadawo rayuwa tareda abie saboda zamanta da take ita ɗaya nasan baya maka daɗi" idanuwansa yana rufe kuma baza'a iya predicting yanayinda yake ciki ba yayi magana Cikin muryarsa mai daɗin sauraro.
"Yaya akayi kikasan ba hakan bane bayan ga abunda na nuna a zahiri cewa bana buƙatar kusancinsu rayuwa ahaka tafimun daɗi" na juya ina kallon kyakkyawar fuskarsa idanuwansa a lumshe saida na sumbaci lips ɗinsa na ɗaura Hannuna saitin zuciyarsa da take bugawa da sauri sannan nayi magana. "Wannana a zahiri kenan ni kuma ba zahiri nake kallo ba ba ina kallon abunda yake ƙunshe a cikin zuciyarka ne, sai alokacin ya buɗe idanuwansa akaina dake nima shi nake kallo idanuwansa suna cikin nawa nacigaba da magana, "Bazakayi mamaki ba ace zuciyar da nakeda muhalli mafi girma a cikinta bansan abunda yake gudana a cikinta ba? Kana tunanin akwai abunda zai gifta a cikinta batareda nasani ba bare abunda yake zaune a ciki yana damunta tsawon shekaru idan hakan ta kasance yazama yana kulada abunda yake mallakina yanda ya dace, kumani bana cikin wannan sahun duk wani abu daya zama mallakina inayi masa rikon da bana tunanin duk ƙarfin mutum zai iya yimasa kwatankwacin wanda nayi saboda nima da zuciyar nake riƙe shi" na canja maganar ta sigar zolaya ina faɗin. "Shiyasa tun wuri kada kabawa wata mace ƙofa tayi ƙoƙarin shiga zuciyarka saboda tana Hannuna kuma nasan duk wani abunda yake faruwa a cikinta" yayi murmushi sannan ya furzar da iska mai cikeda damuwa sannan yace "Yanzu yaya za'ayi inaga kaman lokaci ya ƙure aikoh? Tswon shekru ashirin da basa tare wane zama kuma zasu yi yanzu? Its too late Rouhi kawai kibarsu sucigaba da Rayuwarsa zan jure tunda na jure shekarun baya ma when i was a little boy a lokacin nema nake buƙatarsu atare kusa dani". "No is not masoyi ko kwana ɗayane ya rage musu a duniya let them live together na wannna ƙwana ɗayan kaji idanma bazakayi tunanin kanka ba think of nawrah bance ba amma tanajin daɗin rayuwa ahaka? Tana samun kulawa yanda yadace? Sam fa ita batama fita tunda mukazo sua 1 muka taɓa haɗuwa da ita" "Okay toh yanzu yaya za'ayi?" "Kaje kasmu abie kace masa kanaso yadawo da auren Mum kansa zai dawo dashi" "Toh kawai ya amsa with cconfident""Amma ke zaki rakani" na zaro ido "Nikuma masoyi" "Ehem naga kinfini son Mum tadawo ai" na girgiza kai "Mahaifinka nefa" "kema mahaifinki ne ai" "Bahaka nake nufi ba masoyi" "Toh kawai afasa" na girgiza kai "No zan rakaka amma zan tsaya sai kayi magana ya jijjiga kai, "Okay hakan yayi" muka zauna a wajan na awanni sannan muka tashi muka fara tafiya zuwa ciki ina saƙale da hannunsa cikin nawa na ƙwantar da kaina a kafaɗarsa, "Rouhi Kin gaji na ɗaukeki?" "Masoyi nifa ba ƙaramar yarinya bace" ya zare hannunsa cikin nawa ya tsugunna a gabana yanamun alamun nahau bayansa" "Zan iya tafiya da ƙafata" nafaɗa ina ƙoƙarin wuceshi ya kamo ƙafata "Banason gardama Rouhi nasan kingaji zoki hau" "juyowa nayi nahau bayan a miƙe na ƙwantar da kaina a faffaɗan gadob bayabsa na lumshe ido ahaka muka isa har zuwa masauƙinmu. Bayan sallar isha'i muka fita cin abinci dukanmu tunda mukazo a wajanmu mukecin abinci amma Yau abie yace yanaso muyi diner gabaki ɗayanmu tare na shirya cikin doguwar rigar atampha nayi kyau sosai. tunda mukayi aure nadaina saka atampha sai yau kawai naji sha'awar hakan. Hammood kallona kawai yakeyi saboda nayi masa kyau sosai wajan da aka shirya zamuyi dinner nan muka nufa ina tafiya. Munsamu ƙannen Hammood da Nawrah da matan Babansu duka sun iso abie kaɗai bai iso ba, waje daban muka nema nida Hammood muka zauna, dayaga Abie har lokacin bai isoba yatashi ya tafi neman abie inajin Ɗaya daga cikin matan abie cikin harshen larabci tana magana da ɗiyarta wacce take 16yrs "Kalar zaren baiyi kama da zanin ba" tafaɗa suka fashe da dariya har suna rufe baki, Ban kulaba amma tabbas jikina yabani dani suke na sake haɗe rai, sukaci gb da maganarsu da larabci ina tunanin basuyi zaton inajin abunda suke faɗa ba saboda koda zuwana da turanci suka tarɓeni nima saina bisu ahakan, saida Nawrah tabari sun gama Gulmarsu itada ƴarta sannan tayi magana da turanci, "She speaks 94% fluent arabic Arabic better watch what you are saying kafin abie da mijinta suzo su ɗauki mataki akanku" tayi magana hankalinta nakan waya, sub tsorata da maganar ta amma sai matar ta dake Dariya sosai tayi "Tanajin larabci dakyau kuma tana mayarwa toh tayaya? Oh sorry ashe she's a muslim ba laifi" Nawrah tasan magana takeson yaɓa mata saboda mahaifiyarta ba musulma bace kuma ba yanzune farkon hakanba koda yaushe ita wannan tana yawan yaɓa mata magana shiyasa ma bata shiga harkarsu sam ko yanda suke bata zuwa idanba Abie ya buƙaci hakanba, Cikin ɓacin rai tace. "Oh speaking fluent arabic yazama requirenent da za'ayi considering mutum Muslim kenan?" Shiru sukayi saboda su san zata yaɓa magana zuwa gaba, adai-dai lokacin abie da Hammood suja shigo Hammoid ya nufoni ko kaɗan ban bashi fuskar da zai gane wani abu yafaru ba toh Mahaifiyarshi ma tayimin bandamu ba bare matar mahaifinsa.


Zama mukayi akan dining ma'aikata sukazo suka fara serving mutanen wajan banjira sunzo kanmu ba natashi nafara serving Hammood nayi nasa da nawa nazauna, nakasa cin abinci saboda kasantuwar Abie awajan dakyar na iya kai spoon ɗaya bakina Ganin hakan yasa Hammood ya tsaya da kaiwa abincin bakinsa ya ɗebo ya miƙa zuwa bakina, a hankali na girgiza kaina, Nawarh wacce take kallonmu sai muryarta mukaji,"Ai bazata iyaci ba yanzu Ummi da salima suka yi magana maras daɗi akanta da Mum kuma tanaji a idanuwanta sunaji kamar bata dace da aurenka ba Mum kuma akan addininta Ummi take habaici" dasauri na ɗago ido ina kallonta bantaɓa tunanin Nawrah zata sake tada maganar ta faɗawa Hammood ba itama ni take kallo tanaci gaba da maganarta ko ajikinta."




PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.






Ba Hammood kaɗai ba Har abie ransu yayu mummunan ɓaci yadubi Ummii cikin ɓacin rai yafara maganganu dake tana tsoronsa kamar mutuwa yasa tafara bashi haƙuri. Hammood kuwa iska kawai yake furzarwa yanajin ransa yana masa zafi ba abunda sukayimin kaɗaiba harda Mum data sako ciki ya ɓata masa rai. abie yace mani zasu bawa haƙuri bawa shiba haka suka juyo suna bani haƙuri kai kawai na gyaɗa musu alamun nayi. Shima Abie haƙurin yake bani kunya ta sakani sunkuyarda kaina, dinner ɗinda ba'ayiya ta daɗin rai ba kenan da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai suka fara watsewa yazama saura nida Nawrah da Hammood sai abie kawai.


Hammood ya dubi Abie"Abie tanason magana dakai akwai abunda zata faɗa maka" da mamaki na kalli Hammood ya ɓata rai yaƙi kallon yanda nake. Abie yayi murmushi "Me kukeson faɗamin?" Hammod yace"Takeson faɗa maka dai abie gata ga tambayeta" Sai kallonsa nake inason ya kalleni yaƙi na mintineshi ta ƙasan dining yace "Auchh abie kaga ta mintsineni kuma ita tace tanason magan dakai" Abie dai dariya yakeyi nayi shiru nayi ƙasa dakai nakasa cewa komai, "Zaynab Habibty" Abie yakira sunana a hankali na ɗago na kalleshi sai yau na ƙare masa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads