Showing 30001 words to 33000 words out of 171869 words
Chapter 11 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
bata umarni shima bashi umarnin akeyi. tacigaba da karatunta tana zuwa makaranta amma a ɓoye mijin yake ɗaukar ɗawainiyarta wata rana ma idan Mummynta bushi iska takance ita takeso tayi aiki dan haka bazata makarantarba, haka take haƙura da zuwa makarantar ta zauna tayi mata aiki, ganin hakan bai hanata karatunba ya sanya Mummy ta tashi rikici akan dole sai dai tabar karatun baza'a ɗauki nauyin karatun wata da dukiyar mahaifinta ba, shikuwa yace bazatabar karatu ba dan itama Mahaifinta yanada rufin asirinsa danshima ɗan kasuwane yanzu har takai takawo daga ƙasar waje yake shigoda kayyaki a wannan lokaci kuwa masu shigowa da kaya daga ƙasar waje sai mai ƙarfeffen jari ba kamar wannan lokaci bane da shigoda kaya daga ƙasar waje ya yawaita ba. Amma duk arzikinsa not to compare with baban Hajiya zaynab yayi masa fintinkau ya wuceshi fuu da aniya. ya gwada mata mahaifinta shi yafara ɗaukan nauyim karatunta kuma shi yake ɗauka har yanzu dan haka baida right ɗin hanata karatu tunda ya aminta da karatunta tun farko, itama idan tanada ra'ayi bazai hanata ba takoma. Tace ita bazata koma karatu ba tunda a yanzu babu abunda zata nema a duniya bata samuba. Ahakaz zancen ya mutu bata sake ɗagashi ba."
Haka suke rayuwa harta samu juna biyu Mummy batasan da zancen cikinba Har saida yafito itama lokacin tanada nata cikin had yafi na Amarya girma. Amma ita nata kowa yasan dashi itakuma amarya babu wansa yasani dake ba laulayi takeyi ba.
Ganin tanada juna biyu ya sanya Mummy ta sassauta mata gabaki ɗaya tadaina shifa sabgarta. Hakan ya sama mata sauƙi ba kaɗan ba tasamu ta ƙarasa rainon cikinta cikin salama gashi dama ya haɗu matada karatu. mummy tafara haihuwa aka sanya mata Aysha.
daga baya itama amarya ta sauƙa aka sanya sunan mahaifinta Habibu. ya hanata yin tsarin iyali saboda yanason yara itama Mummy adole takeyi bada son ransa ba. Watanta biyar da haihuwa tasake samun juna biyi shima saida yafito kafin aka gane dan ita sam bata laulayi wannan karon mace ta haifa Aka sanya mata sunan Mummy yayi hakane dan kawai ya faranta ran Mummy ko zata sauƙo suyi zaman lpy da Mama hakan kuwa yayi aiki dan tayi matuƙar jin daɗi kuma tayi mamaki dan har tana tambayarsa.
"Kuma mahaifiyarta ta yarda kasaka sunana?" yace.
"Ta yarda sosai ma kuwa itace ta daɗa ƙarfafamin guiwa akan nasaka sunanki ai tana ganin girmanki sosai" wannan abun yasanya Mummy ta watsarda kaff makaman yaƙinfa akan Mama tana nunawa yarinyar soyayya matuƙa wanda tayi mata laƙani da marmee tace tunda ita Mummy yabita ko wannan marmee ce haka ake gaya mata kowa marmee yake cemata.
Saida Mama tayi shekara taƙwas gaba bata sake haihuwa ba bayan haihuwar Marmee itakam Mummy dama ta sayarda haihuwarta kuma tunda ta haifi Aysha ta aika da Babbar ƴarta da fadeela Abuja wajan mahaifanta Ahmad kam mahaifinsa ya roƙi tabar masa shi anan, hakan yasa gabaki ɗaya yaran basusam junansu ba. Ahmad anan yake karatu yana ajin ƙarshe a secondary alokacin Mama ta haifi sadik. A wannan lokaci ana zaman lafiya matuƙa agidan Saboda Mama nayiwa Mummy biyayya itama Mummy darajar Marmee yasa ta sauƙo ta maida Mama ƴar uwa amma har lokacin jiji dakanta da gadara sunanan dan akomai saita nunasu."
Suna cikin wannan sama mai cikeda Daɗi Baba yazo musu da maganar ƙara aure zai auri yarinyar abokinsa. Abokin baida lafiya ya roƙeshi ya auri ƴarsa saboda mahaifiyarta tarasu bayaso yamutu yabarta batareda yasan tana hannu na gari ba alokacin yarinyar gabaki ɗaya bazata wuce sa'ar Ahmad b sunanta Habiba. Dafarko Baba yaso yaƙi zancem saboda first born ɗinsama ta girmeta bazata wuce shekara sha takwas ba amma ganin kamar itace alfarma guda ɗaya da zai iya yiwa mahaifinta yasa yayarda. Yaga tashin hankali matuƙa kan auren yarinyarnan dan wanda yagani abaya wajan auren anty ba komai bane wannan karon gashi yaransa sun girma hat Ahmad durƙusa ƙafarsa yayi yana kuka yana roƙon mahaifinsa Akan kar ya auri wannan yarinyar idan auren yakeso yacanja dawata yarinyar haka dai ya shafawa idonsa toka yacigaba da zancen auren tunda dama mutane dayawa sunce masa dole sai yayi haƙuri da irin abubuwanda zai gani yarufe idanuwansa kafin yiyuwar wannan lamarin.
Ahmad ganin mahaifinsa baida niyyar janyewa akan zancensa yasa ya yanke shawarar barin garin rana ɗaya ya tattara yakom abuja wajan mahaifan Mamarsa."
Ranar ɗaurin aure bayan anɗaura ƙanwar Baba Halima tarasu wajan haihuwa wannan mutuwa da girgiza shi shiyasa koda akayi auren amaryar bata gane kansa ba har zuwa lokacinda mutuwar ta sakeshi ya fawwala komai ga Allah, itama anata wajan anyi auren bada daɗewa ba mahaifinta ya cika kowa yaje mata ta'aziyya amma banda Mummy babu yanda bai roƙeta ba taƙi zuwa hakan yasa ya ɗauki fushi da ita bai taɓa yimata hakaba sai da yayi wannan auren shikuma yayi hakanne danta gane kuskurenda tayi."
Dafarko amaryar tashigo ta feleƙe ganin itace Yarinya acikinsu sam taƙi takuwa awajan Mummy kamar yanda ake taka kowa. Gani takeyi tunda gidan mijinta ne itama dole tayi abunda takeso batasan dawar garinba.
Mummy na matuƙar jin Haushin Habiba dan haka tafara fito mata da halaye shikuma anasa wajan tausayin Habiba yakeyi kasancewarta babu Uwa babu uba kuma ƙaramar yarinya.
Itadai Mama nata ido kawai tana kallon abubuwanda yake faruwa tana daga gefe shikansa yasan kaff cikin matanda babu maiyi masa biyayya da jin maganarsa kamar Mama hakan yasa takeda wani matsayi aransa ya lura ita kaɗaice ke tausayinsa da gudun ɓacin ransa."
Ya lura itama Habiba sam batajin Magana duk wani abinda ya hanata saita aikata kuma idan Mummy tayi abu saita tanka hakan yasa zaman lafiya yafara ƙauracewa gidan a ƙanƙanin lokaci yafara danasanin ƙaea aure.
Anyi hutu dan haka Baba ya buƙaci da akawo masa yaransa suyi hutu awajansa kowa yayarda zai taho hutu banda Ahmad. tsanarda yake yiwa aurenda mahaifinsa yayi tayi yawa wanda shi kaɗai yasan dalilin hakan.
A hanyarsu ta zuwa sukayi accident Babbar ƴarsu ta rasu Mummy kamar zatayi hauka saboda ta rasa ɗiyarta. A garin aka ƙaraso da gawar aka wanketa aka kaita makwanci har akayi wannan abun Habiba bata fitoba, kowa hankalinsa yana tashe dan haka babu wanda ya lurada ita sai bayan an kaita andawo Har akayi ƙwana uku batayiwa Mummy ta'aziya ba Baba ma mutuwar tashiga jikinsa matuƙa dan har rama yayi. Yana lurada cewa Habiba bata fitowa wajan kraɓan gaisuwa da yaje ya sameta cewa tayi itama ramawa tayi abun yabashi mamaki aiko batayi ta'aziyya dan Mummy ba zatayi danshi mahaifin yarinyar yayi mata faɗa sosai kuma yace taje tasamu Mummy tayi mata gaisuwa.
Itakuma taƙi zuwa tace itama lokacinda mahaifinta yarasu batayi mata gaisuwa ba ganin ana zaman makoki ya sanya Baba bai tada zancenba.
Ana gama zaman makoki Mummy tace sai dai Baba yazaɓa ko ita ko Habiba dan idan zata zauna agidan Habiba bazata zauna mata agida ba idan kuma Habiba zata zauna toya tabbatar ita zatabar gidan kuma da yaranta karya saka ran zata dawo har sai Habiba tabar gidan, wannan zancen yazo agaɓa da bayyanar cikin dayake jikin Habiba dan haka Baba yakasa yanke shawarin abunda zaiyi kamar da wasa rana ɗaya Mummy ta tattare yaranta da duk wani mallakinta tabar gidan kuma ta tabbatarwa Baba da cewa kar yazp nemanta har ranarda Habiba tabar gidan idan kuma ya nemeta batareda Habiba tabar gidanba toh ko yaƙi ko yaso aranar sayya yanke igiyar aurensu gabaki ɗaya" Wannan lamari ya girgiza Baba dayasa jininsa yahau ya kwanta jinya kusan abunda ya mallaka saida ya ƙare a jinyarsa a hankali yafara samun lafiya wannan jinya ta sanya Habiba tashiga hankalinta danta tsorata sosai gani takeyi kamar wanda zai mutu idan ya mutu kuwa itace asirinta ya tonu dan haka tayi mugun sanyi tun daga wannan lokacin yasa sam ba'ason ɓacin ransa. Mummy kuma ganin Baba bai nemeta ba ya sanya ta ɗauka ya zaɓi Habiba akanta dan haka ta ɗauki tsanar duniya ya ɗaurawa Habiba.
Bayan Habiba ta haifi wannan cikin dayake jikinta haihuwa ɗaya tasake yi wanda haifi ƴan biyu Mama ma haihuwa ɗayia ta ƙarayi. Sau dayawa mahaifin Mama ke taimaka musu da wasu abubuwan.
Wannan dalilin yasa gidan suka taso basusan juna ba kuma kansu arabe.
Back to cikin labari.
ZAYNAB ALABURA.
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
Jikina yayi masifar sanyi jin wanann labarin koda wasa babu wanda yataɓa bamu labarin abunda yafaru agidanmu sai yanzu Baba shida kansa dayaji zai bada kuma ya bada tausayinsa ya kamani sosai amma tabbas akwai kuskurensa acikin faruwar wannan lamarin dukda nima a sanina bantaɓa kallon mutum mai sanyin rai irinnasa ba. Na ɗaga idanuwana na kalleshi na sakar masa murmushi tabbas ko a yanzu da mahaifina yake cikin shekaru na hamsin da wani abun yanada matuƙar kyawunda kallo ɗaya ya ishi bayyana kyawunsa ko mu cikin ƴaƴansa babu wanda ya ɗauko kamanninsa sak Yayana Habibu ne ma yake kamanni dashi sosai amma mu duka sai dai ace gawani abunda muka ɗauko nasa kama da mahaifiyarsa yakeyi sakk hakan zamuce tunda mu bamusan mahaifinsa ba. Cikeda ladabi nadubi Baba nace.
"Baba har indai bazanyi laifi ba zan iya yimaka gyara akan abubuwanda suka faru?" saida ya murmusa sannan yace.
"Nasan nayi kuskure akwai abubuwanda da hannun agogo zai juya baya dana gyarasu amma yanzu lokaci yawuce bana tunanin akwai Abunda zai iya gyara lamarinan amma ina jinki bazanƙi taki ba ta iya yiwuwa akwaita hanyarda zakibi ki gyara" ina jinki.
Nisawa nayi sannan nace.
"Baba komai zai iya dawowa dai-dai ya zauna a muhallinsa amma ba irin yanda daa can yakeba saboda abaya abubuwa basa zaune a muhallinsu ba Baba koma wacece Mummy koma waye mahaifinta bai kamata kabata damar daka bataba komai ta mallaka kaine mijin itace matarka bana tunanin akwai wani yanayi daya kamata ace ya canja hakan. Akoda yaushe kazama kaine mai iko da gidanka ba mace ba aduk lokacinda akace macece ke iko da gida toh tabbas za'a samu matsala. Koda sau ɗaya daka fito ka gwada mata kaine kake aurenta bazaka ɗauki abubuwanda takeyiba nasan tana sonka dole zata risina amma kawaicinda kakeyi mata ya sanya take ganin kamar tazama maka dole zata juyaka ta yanda taso kuma ka bita har wasu suke kallon tsoronta kakeji. Ni banaso naga mahaifina a matsayin matsoraci inaso naga mahaifina a matsayin mai iko da faɗa aji wanda ya isa da gidan da ƴaƴansa da matansa gabaki ɗaya ko Dabba kake kiwo Baba yakamata ace data ganka tasan kaine mai gidan bare matanda Allah ya rigada ɗauraka akansu Allah da kansa yabaku daraja acikin suratul baƙara Allah yace.
"wa lirrijjaali 'alaihinna darajat" وللرجال عليهنّ درحة"
yafaɗa acikin alqur'ani yabaku daraja ya ɗauka muku nauyi a kafaɗarku ya baku iko akan iyalanku
Sannan kuma ya ɗauraku akanmu cikin suratul nisa'i Yace "Al rijalu Qawwamuna alal nisa'i" ya dauraku akan mata to take care of to look after' duk yanda aka ambaci Qawwamun ana nufin ruler shugaba Allah da kansa ya kiraku da Qawwamun yana nufin the one incharge, You're the protector kaine ginshiƙi wala Allah mahaifiyarka ƙanwarka matarka ko ƴarka. Ita mace gabaki ɗaya rayuwar a ƙarkashin wani take dafarko mahaifinta daganan saita koma hannun Mijinta sai kuma ɗanta idan ta girma. yanzu haka kana zaune amma itake juya maka yaranka yanzu wannan lokacin yawuce Baba kaiya kamata ace ka isa da yaranka ka sanyasu subi umarninka" tunda nafara magana Baba yake kallona harna ida sannan yace.
"Marmee shekarunki nawa?"
"Sha tara" nabashi amsa ya jijjiga kai yace.
"Nasani kawai ina sake jaddada shekarunne banyi tsammanin za'a samu wannan basira a shekarunki ha ni aganina komai ya rigaa ya ɓaci bazai taɓa dawowa muhallinsa ba aganina komai yadawo muhallinsa shine zai dawo da ahlina gabaki ɗaya. Sai kika nunamin dawowar al'amura muhallinsu wani gyarane amma ba itace dai-dai da samun farin cikiba yanzu tawace hanya kike ganin za'a gyara komai akan dai-dai?"
"Na nisa nace yanzu zaka fara da abunda ya tunkareka acikin gidanka shine farko Mummy nason Su anty fadeelah su koma a yau ko gobe, sun gama haɗe kayansu sun shirya yanzu umarninta suke jira da zaka jeka ka samesu kuyi magana ka fahimtar dasu sannan ma ɗaura da umarninka akai yna baka yarda su tafi ba da ka ɗauki hanyarda al'amura zasu dawo muhallinsu wanda tun abaya yakamata a ajiyesu amma yanzuma bai ɓaci ba za'a iya ajiyesu. Sannan Baba mai yasa koda sau ɗaya baka taɓa bin Mummy ba?" baka tunanin Hakan dakayi shine yasake zurfafa lamarin?" Baba ya furzarda iska sannan yafara magana.
"Wato waɗannan Yaranma so take ta sake ƙarɓesu? Tayi gangancin aikominsu dan haka banajin zan iya maidasu zanyi kamar yanda kikace zan zama mai iko acikin gidana mai faɗa aji bazan barsu su sake tafiya ba. sannan zancen binta kuma da ban yiba dalilin alwashinda taci. Bazan iya sakin Habiba ba saboda alƙawarina da mahaifinta shiyasa ban bitaba dan karna sake rikita lamarin.
Kince kina neman wata alfarma wajena inaso ki faɗamin wace alfarma ce nikuma zanyi miki Na murmusa sannan nace.
"Na rigada na faɗeta kuma kayarda zakayi banason rabuwa da ƴan uwana akaro na biyu bansansu ba ban taso dasuba amma inaso na rayu dasu" Baba ya jinjina kai yace.
"Allah nagode maka wannan shine alfarmar da kike nema? Wannan kamar kaina zanyiwa alfarmar amma tunda hakane na ɗauka alƙawarin in sha Allah bazan barsu su tafi ba, dama kullum inaji ajikina ta dalilinki kan ahlina zai sake dawowa ya haɗu kamar yanda ya haɗu abaya ta dalilinki. Kuma yanzu alamu sun fara nuna hakan Allah yayi miki albarka. Yanzu zan fita amma kafin na fita zanbi muyi magana dasu sannan akwai wani abunda yake faruwa wanda abaya naso na faɗa miki amma yanzu ganin cewa zaki iya karɓan kowane hukuncin dana yanke akanki yasa zan yanke hukunci da saran zaki amshi kowane irin hukunci" Batareda kawo wani tunani acikin rainaba nace.
"Karkaji komai Baba kowani irin hukunci na yarda ka yanke akaina"
"Allah yayi miki albarka" na amsa da Amin yace zaki iya tafiya kiyi shirin makaranta yanzu zanje na samesu zan fita ta iya yiwuwa nakai dare irin jiya idan baku ganni ba karku damu" naso na tambayeshi abunda zai fitayi dan jiyama hankalinmu yatashi kuma shi bai saba fitanba amma ganin bai sanarda abunda ya fitarda shiba ya tabbatarmin bayason asasnine nikuma bazan takurashi ba dan haka na can miƙe nayi masa sallama nafice"
Banbi ɗakin Mama ba dayake har yanzu ban sauƙo a fushin da nakeyi da itaba. Nashiga ɗaki nayi wanka na shirya zuwa makaranta sukuma sun ijiye kayansu kamar jira sukeyi gari yagama wayewa su tafi ko kuma akwai wanda suke jira zaizo ya ɗaukesu duk cikinsu babu wanda na kula na lanƙaya jakata ina shirin fita mukaji sallamar Baba saida muka amsa muka bashi izinin shiga sannna ya shigo. Ban tsayana nace.
"Baba nikam nawuce makaranta" Yace.
"Dawo ki zauna zanyi magana da ƴan uwanki agabanki. Nadawo na zauna acan gefensa suka gaisheshi tukunna ya nemi kujera ya zauna yana kallon jakarsu yace.
"Har kunyi shirin tafiya kenan? Zaku tafi batareda kun faɗaminba badan ƴar uwarku ta sanar daniba toh sai dai acemin bakwanan" su dukansu suka sunkuyarda kansu Baba yacigaba da faɗin.
"Ko bakwajin daɗin zama danine da zaku tafi?" su duka suka girgiza kai yace.
"Macece matsalar? Nasan bazan iya baku abubuwanda kuke buƙata kamar yanda kuke samu acanba amma zanyi iya ƙoƙarina a matsayina na mahaifi naga na tanada muku abubuwan buƙata a rayuwarku. Shekarun baya da bakwa tare dani babu yanda na iyane yanzu kuma inajin akwai abunda zan iya a matsayina na mahaifinku nace kuzauna ku rayu tare dani da ƴan uwanku kuskurenda yafaru abaya bazai sake faruwa ba bazan sake yarda ƴaƴana su fita agidannan da sunan komawa wani wajan rayuwa ba, ko Mummynku ta kiraku kuce mata ni mahaifinku nace bazaku tafiba. Koda zata tsoratar daku kar wacce a cikinku da yarda tafita bada izinina ba. Kuma daga yanzu dukanku ku tattara ku koma ɗakin mamarku da zama Acan zaku zauna Har Allah yasa na ɗagaku daga gidannan na kaiku gidan mijinku.
Idan Mummynku nason ganinku ta biyoku gidan mahaifinku ta ganku dan babu wacce zataje ko'ina acikinku" Sun rasa murna zasuyi ko akasin haka dama sam basason tafiya amma basason mahaifinsu yashiga matsala saboda su."
Baba yana gama faɗin Haka yace. Zaki iya tafiya nagama magana ta Anty fadeelah ce tace.
"Kayi haƙuri Baba in sha Allahu babu yanda zamu sake tunanin komawa" Baba yace.
"Babu komai Allah yayi muku albarka" muka amsada Amin. sai bayan yafita natashi nafice ɗakin Mama nafara zuwa na gaisheta babu yabo babu fallasa nayi mata sallama ina shirin juyawa naji tace.
"Marmee" na jiyo na dubeta fuskata babu fara'a tace.
"Zonan ki zauna" nadawo bazauna ina jira tafaɗi abunda zata faɗa.
"Fushi kikeyi dani Marmee?" ta jefomin tambaya saida na haɗe rai sannan nabata amsa da faɗin.
"A'a" tayi murmushi tace.
"Yaro man kaza fushi kikeyi mana, inbanda yarinta wayake fushi da mahaifiyarsa?" nan da nan idanuwana suka ciko nafara magana ina mai ƙoƙarim fashewa da kuka nace.
"Mama daga zuwanki fa kika mareni bakisan abunda ya haɗamu ba kika yanke hukunci kinsan yaya naji araina kuwa? Niba zafin dukan da kikamin bane ko nagwada baki isa hukuntani ba haka bane. Itace ta cancanci hukunci alokacin magana tafaɗa akan mahaifina nikuma bazan iya juraba" ina maganar nakasa ƙarasawa saboda yanda kuka yake ƙoƙoarin ƙwacemin tajawoni tasaka kaina akan cinyarta tana rarrashi tana ɗan bubbuga bayana har nayi shiru sannan tace.
"Marmee banason fitina ne bakisan wacece mahaifiyarsu ba yanzu wwannan dalilin saiki jawo mana nida mahaifinki masifa amma kiyi haƙuri nikaina marinda nayi miki ƙwana nayi ina tunaninsa"