Showing 24001 words to 27000 words out of 171869 words
Chapter 9 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
kawai suka haifa a duniya Mahaifinsu babban manomine. shine Babba awajansu sai sauan ƙannesa Mata gabaki ɗayansu. mahaifinsu tun suna ƴan ƙanana aka nemeshi aka rasa Har ila yau ba'asan yanda yakeba.
Wasu daga cikin gonakin mahaifinsu aka sayar mahaifiyarsu takama kasuwanci take kulada yaran har karatunda zasu zai fara ma sayarda gobar akayi ana biyan Aka ɗauki ɗawaniyar karatunsa dashi har gashi yanzu yazo aji biyar."
*********
motace ta tsaya ɗan gaba da yanda suke da abokanansa, cikeda izza da isa ta dubi wata ƙawarta dake zaune a gefenta tace.
"fita ki kiramun shi" ƙawayen gabaki ɗayansu suka saka shewa suna faɗin.
"eh lallai yau Hajiya Zee an ɗauki shawara kenan tsawon lokaci guda ana abu ɗaya yau dai rana tayi" Ganin yanda ta kimtse fuska ya sanya su duka sukaja bakinsu sukayi shiru sanin halinta abune mai sauƙi yanzu ta disgasu a wajan. Wacce aka aika ta buɗe murfin motar tafita ta isa zuwa wajanda suke zaune tayi musu sallama sannan tace.
"Hajiya zee na son ganinka" tafaɗa haɗeda yin pointing ɗin Muhammad.
"Ni" yafaɗa asanda yake nuna kansa da yatsarsa.
"Eh tana jiranka" tafaɗa haɗeda juyawa ransa yaɓaci amma sanyin halinsa yasa murmushi kawai yayi haɗeda girgiza kansa. Nan abokansa suka fara faɗin.
"haba mutumina kaje mana kasan wacece Ita kuwa? kaff gayun makarantarnan sun gwada sa'arsu akanta amma har yanzu babu wanda ta kula kaje kaji abunda tazo maka dashi" bada son ransa ba sai dan yanda sukayi masa caaa yasa yatafi tana kallon ya iso wajan tadubi ƙawayenta sun gane abunda take nufi dan haka dukansu suka fice a motar. Tsayawa yayi abakin motar yayi mata knocking. Da yanayin maganarta yanda tasaba tace.
"ƙofar motan a buɗene" kallonta yayi na seconds ganin batada niyyar fitowa yasa yabuɗe yashiga tunda shi baida zafin randa zai iya kaucewa yabar mata wajan. hand bag ɗinta ta ɗauka taciro wani littafi ta miƙa masa kallonta ya tsayayi bai karɓaba dan bai gane abunda take nufi ba. Cikeda gadara tace.
"lissafi zaka koyamin test muke dashi kuma ban iya ba" ganin yanda take magana cikeda izza kamar wacce take bashi umarni ya sanya yayi murmushi mai cikeda takaici, takirashi zuwa motarta maimakom ta gaisheshi ko sannu tace batayiba saita fara da bashi umarnin ya koya mata lissafi. Cikeda mamaki yace.
"Kinsanni? Koni nasanki?" yatsine fuska tayi tace. baka sanni nima bansanka ba kawai naji ance kana yiwa mutane tutorial akan abubuwanda basu ganeba nikuma bazan iya shiga cikin kowasu irin mutane na zaune ba shiyasa na nemi kamin nawa ni kaɗai idan takama na biyaka ne zan biyaka ko nawa kakeso just name your price" yayi murmushi mai cikeda takaici yace.
"idan kinaso na koya miki kije ki zauna cikin mutanenda bakyaso ɗin yau da ƙarfe huɗu shine zan iya haɗawa na koya muku tare" yana faɗin haka yakama ƙofar zai buɗe tayi saurin dannawa ƙofar lock ya juyo da mamaki ya kalleta jin ta garƙame ƙofar. Yana mata kallon tuhuma dan haka ta haɗe rai kamar wanda akayi mata dole tafara faɗin."
Honestly nifa bana ganewa ne idan bawai ni kaɗai akayimin dalla-dalla ba acikin mutane bana fahintar abunda ake koyarwa" Saida ya ƙare mata kallo itakuma ta kauda kanta gefe tana ciccin magani tace.
"kuma wannan abunda na faɗa maka babu wanda yasani sai kai kaɗai dan haka ka koyamin kuma kar kowa yasani" jin yanda tayi magana cikeda umarni yasa yayi murmushi yace.
"Okay maa" yanayin yanda yayi maganar saida ya sanyata takusan yin dariya amma saita dake hannu ya miƙa mata ta bashi littafin ya amsa ya fara nuna mata cikin lokaci ƙalilan tace tagane yace ta gwada masa tabi ta gwada masa kamar yanda yayi mata.
Zai tafi tace.
"Toh yanzu idan inason ganinka ka sake koyamin a'ina zan sameka?"
"A'ina yau kika sameni? Kullun inanan idan bawai lactures nake dashiba ko wani abun" ta yatsine fuska sannan tace.
"Ka sakamin phone number ɗinka inaga kaman zaifimin sauƙin nemanka"
"Banida waya ya faɗa alokacinda yake ficewa" ta taɓe baki kawai saida ya isa wajan zamansa sannan ƙawayenta suka shigo motar ta tada sukayi gaba. Suna tafiya suka fara tambayarta yanda sukayi ta taɓe baki haɗeda farfara ido tace.
"kuna tunanin kai tsaye zan fito na faɗa masa ina sonsa? Inaga you're mistaken nice fa Hajiya Zainab banajin kun manta halina sai dai ganganci shida kansa zan sashi ya faɗa sannan yazo da ƙafarsa ya faɗamin yana sona kuma hakanma saina garashi kafin na amshi soyayayrsa" ta faɗa fuskarta babu alamun wasa. Nan da nan suka fara wasa mata kai itakuma tanata hura hanci ita adole tafi ƙarfin tace Masa tana sonsa."
Shikuwa anasa wajan abokanansa sunajin wai karatu tazo ya koya mata sai murnarsu takoma ciki sunso ace tazo masa da soyayyace su samu abun bragging akai."
**********
Tun daga wannan lokaci ya daina zaman wannan waje saboda ya lura rainin hankalin yarinyar yanada mugun yawa sai tazo tayita yimasa gadara akan abunda roƙonsa ya kamata tayi. Itakuma nata wajan yanzu tana neman mafita ne tunda baida waya a wannan lokaci bakowane yake iya affording waya ba ita gabaki ɗayanta ma wayar bata wadatu a hannun al'umma ba sai gidan wane da wane ko ɗan wane ko ƴar wane.
Yau kam sanyawa tayi amata jiransa tun daga bakin gate ɗin makaranta da zarar anga yashigo asanar da ita hakan kuwa akayi mai achaba yana sauƙeshi a ƙofar school dake sun saba da masu tsaran gate ɗin yasa bai nuna IDcard ɗinsa ba yabisu suka gaisa kawai yashige. Tana tafiya yaji Horn abayasansa ya waiga kawai sai yaganta tana zuwa dai-dai shi ta tsaida motar tace.
" shigo" murmushi kawai yayi dan isarta ta kai akirata da isa.
"Barshi kawai nagode i can trek" yafaɗa hankalinsa yana gaba. Cikeda gadara tace.
"kashigo kai kayi alƙawarin koyamin lissafi and i look for you Everywhere. but you're no where to be found, you just vanished. Tayi maganar cikeda iyaye da ƙwainane Cikeda zolaye yace.
"did you look for each an every corner?"
"Yes i do tafaɗa tana ƙara jaddada masa"
"you look All over. the entire surface of everywhere"? Yafaɗa ya tsaya kallonta yana jiran amsarta.
" ehem naa,,," sai kuma tayi shiru data fahimci zolayarta dakuma shan cikinta yakeyi." dariya ya saka itama saida ta murmusa yace.
"dama inada muhimmanci har haka? dakewa tayi tace.
"Kashigo mutafi" batareda ƙara yin wata gardama ba yabuɗe yashiga, tace.
Kayimin alƙawarin zaka ringa koyamin karatu amma bana ganinka kuma lokacin exam yakusa yanzu haka muna tests"
"bamu haɗu bane yasa ban koya miki ba"
"Yanzu mun haɗu saika koyamin" yanzu saura 10minute nashiga lactures amma nayi miki alƙawari da zarar angama zan koya miki"
"toh amma yaya za'ayi a sameka?" kizo department ɗinmu, konazao bansan yanda zan sameka ba ga wannan ta ciro ƴar ƙaramar waya tace. Zan kiraka da zarar kunfito ka faɗamin yanda zan sameka nazo na sameka" yaƙi karɓa tace kace kawai bazaka koyaminba idan kuma zaka koyamin ka ƙarɓa idanka gama na kiraka ya amshi wayar bai ƙarasa department ɗinsu ba ta sauƙeshi ya ƙarasa da ƙafarsa."
Bayan yafito yayita jiran kiranta har kusan 20minute amma shiru, kuma ya faɗamin lokacinda zai Fito, abunda bai saniba tana zaune cikin motarta tana kallonsa bataso yaga kamar jiransa takeyi shiyasa bata kiraba. Sai can takira tazo ya koya mata da zata tafi taƙi karɓar wayar tace duk lokacinda take buƙatar ya koya mata karatu da ita zata kirashi."
Wasa gaske shaƙuwa mai ƙarfin gaske tashiga tsakaninsu koda bata nemeshiba yanzu kullum yashiga school shi yake nemanta."
Wacece Hajiya Zainab?"
ZAYNAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
PAGE 13
Zainab wanda ake yiwa laƙani da Hajiya zainab Ta kasance ƴar garin Abuja mahaifanta suna zaune acan. babanta ɗan siyasa ne. yana riƙe da babban muƙamin gomnati (Senate president) Yaran mahaifanta ukune kacal a duniya sauran biyun duka mazane itace ƙarama acikinsu daga can mahaifinta ya turota karatu Bauchi bayan nuna sha'awarta nason karatu agarin Bauchi, duk wani jindaɗi na rayuwa ya tanada mata gida na musamman ya saya mata ya ajiye mata motocin da zata ringa zirga-zirga dasu, sannan ya zuba masu sanya masa idanuwa akan tarbiyarta dukda kasancewa tanada masifar jijji dakai ga girman kai yasan abune mawuyaci ta ɓata lokacin wajan kula samari dan ko samarin Abuja basa gabanta.
Matsayinta da matsayin mahaifinta yasa takecin karanta babu babbaka ta taka wanda taso tayi abota da wanda taso kuma ta samu duk abunda taso hatta da ƙawayenta yasa take wainasu yanda ranta yakeso
da takasu son ranta bbu wanda zai iya fitowa yanuna mata ba dai-dai take yiba sudai tunda tana sake musu abunda suke buƙata (kuɗi) to koma menene tayi a wajansu dai-dai ne.
Ana hakane ta ɗaura idanuwata Akan muhammad ta rikice da ganinsa amma ko ƙawayenta sai take nuna musu kamar abun bai dameta ba. Kullum zancensu ɗaya taje ta Sameshi har shawara suke bata akan ta sakar masa kuɗi nan da nan zai narke akanta amma ita tana gani kasawane a matsayinta tace tana sonsa kai tsaye sai dai tabiyo ta wata hanya daban."
Shine tayi amfani da hanyar karatu dan cimma muradinta akansa gashi nan dai toh muradinta zai cinmu? Kokuwa bazata kaiga cimma muradintaba?.
*****
Miƙewa yayi yace.
"Toh mungama darasinnmu nayau zan iya tafiya idan anbani izini" dasauri itama ta miƙe tace.
"da naiman izini kakeyi a wajena daba miƙewa zaka fara yiba zaka fara tambayane idanna baka umarni saika tafi" murmushi yayi yace.
"Toh agafarceni gaba zan kiyaye amma yanzu inason na ɗauko yara a school" Tafiya tafarayi tace.
"muje"
"muje ina?" ya faɗa yana zaro ido.
"yanda zakaje taafaɗa sannan ta ƙarasa wajan motarta, tsayawa yayi baibitaba ganin baya tahowa ya sanya ya juyo tace.
"what are you waiting for muje mana" girgiza kai yayi yace.
"ƙannena zanje ɗaukowa a school duk lokacinda banida abunyi ni nake ɗauko so bazai yiwu muje tare ba kiyi zamanki kawai na hutasar dake"
"Nima ƙannena ne dan haka kabarni muje tare" baisan dalilin dayasa bayson yimata musu ba kodan dama gabaki ɗaya shiba maison jayayya bane. Dan haka yabita ya ayanda takeso ɗin yana isa dai-dai yanda take ta miƙa masa key ɗin motar haɗeda faɗin.
"Drive" yana amsa ta wuce seat ɗin mai zaman banza ta zauna tana jiransa ya shigo ya tayarda motar suka nufi makarantar yaran. Koda suka isa sun samu anrigada an tashesu dan haka yana ganinsu ya ƙarasa wajanda suke yayi parking suna kallonsa suka ƙaraso su huɗu Babbarce ta gaishesu ta juya dake dama ita tana ajin ƙarshe a secondary itaba lokaci ɗaya suke tashi ba amma duk aka tashesu saita fito dasu sukan ɗanyi jira na lokaci saboda idan bayida abunyi shi yake ɗaukansu ya wuce dasu gida idan taga ya jima baizoba saita tsara musu abun hawa saitaga tashinsu sannan takoma ciki, wacce tabita tana junior sai kuma ƙaramarsu tana ajin ƙarshe a primary, dake matan suna gidan abokin mahaifinsu yasanya suka kasance su huɗu saboda ya haɗasu ya sakasu makaranta da ɗiyarsa wacce itama ƙaramarce bazata wuce sa'ar wanda take primary ɗinba.
Suka shiga yakaisu har zuwa ƙofar gida ya ajiyesu sannan yace bari ya kaita saiya hau abun hawa yadawo ahanya ta dubeshi tace.
"su dukansu ƙannenka ne?" ya girgiza mata kai taace.
"bani labarinka toh bansan komai gameda kai ba" ya juya ya dubeta sannan ya maida hankalinsa ga tuƙinda yakeyi yafara magana.
"Wannan ukun da kika gani sune ƙannena ɗayar yarinyar ƴar abokin mahaifinane kuma itace yarinyarda zan aura" saida gabanta ya faɗi ta dubeshi tace.
"Amma dai wasa kake koh? Wannan ƙaramar yarinyar?" tayi maganar tana duban fuskarsa taga babu alamun wasa sai tashiga taytayinta amma abun ya dameta cikin ranta kamar zatayi haƙuri sai kuma taji bazata iyaba tace.
"Yanzu kai soyyaya kakeyi da wannan yarinya ƙarama ko wasa kakemin?" girgiza kansa yayi yace.
"eh toh. farko da wasandai yafara amma yanzu yawuce wasa yarinyar abokin mahaifinane kamar yanda na faɗa miki. bayan rasa mahaifinmu shine ya ɗauki ƙannena nikuma ina tare da mahaifiyata toh dafarko ina yiwa yarinyar wasa har mahaifinta yashiga maganar da cewar ko bayan ransa batada mijin saini mutumne mai karamci matuƙa" Jin wannan maganar yasa gabaki ɗaya tarasa abunda yake mata daɗi cikeda ɓacin randa yakasa ɓoyuwa tace.
"Yanzu kana nufin kana sonta kenan?"
"Eh inasonta yanzu nake ƙara fahimtar hakan Amma ai kamar yanda kika gani tayi ƙarama so yanzu babu batun soyyaya harsai ta girma" daganan bata ƙara cewa komaiba dan ranta gabaki ɗaya yayi mata babu daɗi shirune yabiyo bayan tattaunawarsu. Yabi ƙwatancen datayi masa yakaita har ƙofar gida. Itakam batamasan sun isoba saboda yanayinda take cike.
"Mun iso" yaceda ita bata jishi ba yace.
"Madam mun iso ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta dubeshi kamar zatayi magana saita fasa yace.
"Akwai wani abunne?" harda buɗe baki zatayi magana saita tuno wacece ita bazai yiwu da buɗewa namiji abinda yake cikinta ba saita sauya zancen da faɗin amma akwai tazarar shekaru a tsakaninku, bambancin yayi yawa. Cikeda rashin damuwa yace.
"Atamu al'adar aiba komai bane hakan am just 23 itakuma yanzu take 11yrs bambamcin 12years ne which is normal ana yawan samun hakan" jiki a sanyaye takama handle ɗin ƙofar zata fita yayi saurin dakatarda ita da faɗin.
"Dakata madam nine zanfita ko kin mantane?"
"Idan kafita ame zakaje gida toh kaje da ita inada wacce zanhau gobe" Ya buɗe motar sannan yace.
Da ame nake zuwa gida karki damu ina taran achaɓa yanzu zai kaini gida yana faɗin haka ya fice.
Aranar zaynab Batayi bacci ba maganarda sukayi ta tsaya mata arai, ashe ita tanata holoƙon banzane atunaninta tana gini ashe ginin nata ƙwata-ƙwata baiyiba bare aje matsayin rushe shi. Amma dukda hakan yanda takeji da kanta dakuma gadarar ita wacece bazai taɓa yiwuwa tafito ta bayyana masa abunda yake ranta ba, har yanzu tana bakarta nacewa dole sai dakansa yafara bayyana mata abunda yake ransa a yanzu dai ta janye maganarta tabaya datace saita garashi kafin ta amsa izuwa yanzu yana zuwa mata da batun soyayya zata amshe.
******
Shaƙuwa mai mugun ƙarfi tashiga tsakaninsu A yanzu koda yaushe ga ganshi tofa tare zaka gansu da ita mutane har suna faɗin soyayya sukeyi amma banda anasu wajan dan sunsan ko kalmar so bata taɓa shiga tsakaninsu ba. Ana haka lokacin gama makarantarsu Muhammad yayi anata shirye shiryen gamawa amma babu wani alamun zai gwada mata yana sonta.
yana zaune cikin abokanansa wayarsa tafara ruri dake ita tabashi wayar kuma lambarta kaɗai aciki yasanya yanaji yasan itake kiransa. Saida yafita acikinsu sannan ya amsa Cikeda bada Umarni tace.
"Kazo gida ka Sameni" shiru yayi bai bata amsaba saida ta ɗaga wayar taga ko ta katse ne ganin bata katsena ya sanya ta maida wayar kunnenta tace.
"kan jina?"
"ina jinki amma bazan iya zuwa gidanda kike ke kaɗai ba ki fito saimu haɗu ko a school dan yanzu haka ina school ɗinne, kabani 30minute tafaɗa sannan ta katse wayar.
"Saida ta ɗauki 1hour kafin ta iso" tazo har yanda yake ta sameshi, sukaje can wani waje suka zauna sannan ya kalleta yace.
"wani abunne yafaru? Naga kin buƙaci nazo gida na sameki"
"magana nakeso muyi dakai"
"uhum ina jinki"
"Ka kalleni dakyau inaso zanyi maka wata tambaya ce" Ya kalleta yace
" na kalla"
"Banida kyau ne" ta tambaya.
Ganin alamunta babu wasa yasa shima bai ɗauki lamarinda wasa ba yace.
" kina dashi wani abunne?" Ta ɓata rai sosai sannan tafara faɗin.
"inada kyau. Inada kuɗi. Inada ilimi. Kuma inada wayewa dan meyasa har yanzu bakace kana sona ba?" tafaɗa cikeda tuhuma. shima ya haɗe rai yace.
"ke me yahanaki cewa kina sona?"
"Saboda zai taɓamin jin kimata" tabashi amsa taɓe baki yayi yace.
" shikenan so bai kai soba har indai akwai maganar jinkai aciki" Shiru tayi tarasa yanda zatayi tace.
"zan iya sauƙarda jiji dakaina da komai nace maka ina sonka amma inaso kasani dole akwai sakamakon da zai biyo bayan kalmar soyayyata. Ko kaƙi ko kaso har indai kabari na furta maka kalmar so to saika aureni wannan shine sakamakon kalmar Dan soyayyata bazata taɓa tafiya a banza ba kota ƙarfin iko saina saka ka aureni dan haka ka zauna kayi tunani kafin kabari kalnar so tafito abakina dan idanta rigada tafito babu jaa dabaya" Murmushi yayi yana mamakin kalamanta komai saita nuna ita mai iko ce komai saita sako gadara da isa da jijji dakai aciki.
"Banajin akwai zancen aure tsakanina dake tunda ko ba'a faɗa mikiba kinsan kinwuce sa'ar aurena ko mahaifanki baanji zasu bari na aureki"
"Mahaifana kakeji?" shikenan kabani kwana biyi kaga abinda zan iya. Cikeda rashin damuwa yace.
"Nabaki.
"Gobe zantafi Abuja idan na isa zan nemeka"
"Allah yakaimu ya kaiki lafiya kawai ya faɗa" dan yasan idanta tafi ba lallai bane iyayenta su barta tadawo idan sukaji zancenda taje musu dashi."
Washe gari sassafe tashirya tawuce Abuja."
Muhammad baisan abunda yake faruwa ba acikin ƙwana biyunnan saita tasan yanda tayi ta shawo kan mahaifanta dukda bawani wahala tasha wajan jawo ra'ayinsu ba dan mahaifinta yana ganin har indai mutum yacika qualities ɗinda yakeso so beside dukiya ko komai mai sauƙine yanada arziki wanda yana tunanin har zuriarsa ta ƙare bazasuyi talauci so toh menene amfanin dukiyarsa idan bai bawa yarsa da mijinta ba?"
Yayi na'am da zancenda takawo masa dan haka