Showing 60001 words to 63000 words out of 171869 words
Chapter 21 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
saurin cusa wayar ƙasan pillow ta ƙarasao ciki ta kalleni tace.
"Marmeeyy bakiyi bacci ba?"
"Yanzu zan ƙwanta nabata amsa" tazauna gaban dressing mirror tacire zobbunan hannunta da Sarƙoƙin wuyanta ta zuba a ma'ajiyarsu. Ina kallonta ta baya har saida tagama nace.
"Mummy" tajuyo ta kalleni tace.
"Na'am Marmeeyy" Saida naja numfashi sannan nace.
"Mummy meyasa baki tambayi Yaya Baba yake ba?" naji kin tambayi kowa amma bandashi" Alokaci guda fuskarta ta canja kamar wanda akayi mutuwa ta turnuƙe ta ko mai tatuno kuma saita ɗan saki fuskar ta kalli fuskata tana nazarinta tace.
"Marmeeyy meyasa kikayimin wannan tambayar?" naga shi bai damu daya san Yaya nake ba. Ni mai yasa zan tambayi yanda yake? Ko Mmamanku da kikaga na tambaya koda yaushe saita aikomin da saƙon gaisuwa idan Ahmad yaje. Babanku kuma bai taɓa tambaya ta ba. Bai damu daniba. Bbu wani dalilin da zaisa nima na tambayeshi. Dasauri nace.
"karkice Haka Mummy Baba yadamu dake sosai kuma yace na gaisheki Baba kullum yana tunaninki yana tbayarki alokacinda bakyanan shine yabani labarinki harna sanki tunda banida wayo lokacin da zan iya saninki. Baba yana zancenki sosai.
Ta haɗiye wani yawu mai ɗaci tace.
"Marmeeyy kefa yarinya bazaki ganeba"
"Mummy karki ɗaukeni a matsayin yarinyarda bazaki iya faɗawa damuwarki ba. Ni ƴarkice koda ban sama miki mafita ba amma zafinda yake zuciyarki zai ragu. A idon mutane you look strong kamar babu wani damuwarda take damunki. Amma yau kaɗai naganki nasan deep down cikin zuciyarki akwai abunda yake damunki" Ta kalleni tanason gaskanta abunda nake faɗa.
"Marmeeyy Yadamu dani tsawon shekaru meya hanas.... Sai kuma tayi shiru sannan tace.
"Marmeeyy i am 50yrs old and you. You're not up to 20 bazaki fahimci komai ba lets not talk about that okay ki ƙwanta kiyi bacci. We'll talk in the morning"
"Toh" kawai nace sannan nayi mata saida safe tatashi har takai bakin ƙofa nasake cewa.
"Mummy" ta juyo batareda tace komai ba tana kallona da alamu tana jira nafaɗi abunda nakeson faɗa nace.
"Mummy bakya frin ciki. You're lonely not only that kina cikin ƙunc. tayi murmushin ƙarfin hali kawai tace.
"Dare yayi marmeeyy banace zamuyi magana da safiya ba?"
"Toh saida safe" nafaɗa cikeda tausayinta. Matarda kowa yake yiwa kallon mai zafin kai da ɗagun kai da isa da izzah. A kallona da ita ni banga duk waɗannan abubuwam ba. Ina kallonta rauni nagani atattare da ita. haɗeda ƙunshi da kaɗaici wanda mutanenda suke rayuwa da ita suka kasa fahimtar hakan.
bayan tafita naɗauki wayata naduba naga ya kashe kiran da alamun tun lokacin dayaji shiru ya datse kiran. Bannemeshi ba n ƙwanta bacci shima haka bai nemeni ba.
Tunda mummy tashiga ɗakin takasa bacci tanata tunanin wace irin yarinyace marmeeyy tsawon shekaru tasan cewa duka mutannenda take tare dasu basa taɓa iya gaya mata gaskiya. Kullum abunda tace shi sukeyi ko sunaso ko basaso. Mutanenda suke tareda ita basuda zaɓi sai nata. Basuda ikon yin abu sai wanda tace. Akaro nafarko ansamu wacce ta iya fitowa ta nuna mata zaɓinta instead of abunda ta zaɓa mata. ta fuskanci ƙuncinta da damuwarta.
Tunda tabaro gidan Baba ko iyayenta babu wanda yasake mata maganarsa babu wanda ya iya tunkararta da maganar kai tsaye. Ko iyayenta zuba mata idanuwa sukayi suna tunanin hakan shine farin cikinta tunda ita tazaɓi barin gidan tsawon shekaru babu wanda yataɓa tunkararta da maganar Baba har ƴaƴanta na cikinta.
Dama haka tana faruwa? Asamu wacce zata fahimceki fiyeda ƴaƴanda kika haifa a cikinki. Ranar bacci ɓarawone kawai yasace Mummy amma taraba dare cikin tunani."
Washe gari bam tashi ba sai wajan 11:00am tunda natashi gabana yake faɗuwa bansan dalili ba.
Tun tashina naji ana neman yaya Ahmad ba'a ganshi ba wayarshima gabaki ɗaya bata shiga. Mummy kam dama tunda yadawo basu haɗuda shi ba dan bai shigoba. Ga abokannasa da suke wani garin sun fara isowa.
Mummy ma tayi Friends nata sun fara isowa harda ƴaƴansu dake aranar za'a fara event wanda iyaye zasu iya halarta.
Mummy tace mu shirya muje wani spa Muyi gyaran jiki. anan za'ayi mana komai agama muka shirya mai lalle da kitso muka tafi saida aka fara mana gyaran jikk sannan dakai akayi kitso Dake kaina nada cika sosai tsayinsa ma baida yawa sai cikar yasa aka daɗe ba'a gamamin kitso ba. sai dai kitson yayi kyau sosai dan ƙananu akayi an daɗe ba'a gama ba ba'a taɓamin kitso ƙananu kamar haka ba.
Lallenma ba'a cika hannun sosai ba amma yayi kyau.
muna zaune a wajan still gabana yana faɗuwa haka na daure cikkm zuciyata inata addu'a.
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Ƙarfe sha ɗaya tayiwa su Abhie da Hammood acikin gidan Baba. Kamar jiya Baba Ya gayyaci Alhaji habibu awajan. Ana cikin zaman Ya Ahmad ya iso dama Baba yafaɗa masa ya yanki ticket na jirgi yazo shiyasa yana tashi yataho anata nemansa ba'a sameshi ba. Alokacin suka bada sadaki da zinari kamar yanda sukeyi a al'adarsu basa biyan sadaki da tsabar kuɗi. Alokacin Abhie ya nemi alfarmar a ɗaura auren gabaki ɗaya.
Jikin Baba yayi sanyi sosai dan baiso hakanba yayi shiru kawai yana kallon Alhaji Habibu da Ahamd yana jira yaji abunda zasuce dan shi dai idan anashi wajenne bazai amincewa aure yanzu ba koba komai yakamata asake ɗaukan lokaci aga yanda lamarin zai tafi.
Abhie yayi hakane dan yana ganin idan har yazama silarda Hammood ya mallaki abunda yakeso toh shaƙuwarda take tsakaninsu zata ƙara ƙarfi.
Mood bai taɓa tunanin mahaifin nasa zaiyi haka ba amma har indai zasu amince shi zaifi jin daɗin hakan fiyeda kowa kuma hankalinsa zai ƙwanta ya mallaki abunda yakeso.
Baba yayi shiru tsawon lokaci yaƙi cewa komai. Alhaji habibu ya dafa shi yace.
"Amsarka suke jira" Baba ya nisa cikeda damuwa yace.
"Banida tacewa Abba ku yanke shawarar kawai idan kun tsayar saiku faɗa musu duk yanda kukayi dai-dai ne. amma nida nafiso saita ƙare karatunta kafin ayi magana. Alhaji Habibu yace.
"Har indai wannan ne babu damuwa inaga bazasuƙi amincewa ta gama karatunba koda bayan auren. Akwai abubuwa dayawa danake hangowa wanda aganina yin auren shine Babbar maslaha. Amma zamu basu zaɓinmu sannan zai batta anan har zuwa wani lokaci" Baba ya jijjiga kai sannan yace..
"Shikenan Abba har indai hakan yayi maka amma inada sharaɗi ɗaya. Bazasu sanarwa da kowa zancen auren ba zai ɓoye abun har zuwa lokacinda zata koma hannunsa da zama"
"Hakanma yanada amfani" cewa alhaji habibu.
"aɗaura abatta anan ɗinma wata damace ta zaisa muƙara fahimtar al'amura. Sannan ko mahaifiyarta karka sanarwa kasan mata yanda muka fahimci lamarin ba lallai su su fahimceki haka ba. Yanzu zai kaji wanj zancen akeyi daban. Idan lokaci yayi nida kaina zanyi mata bayani yanda zata fahimta. Itama yarinyar sai asanya idanuwa akanta sosai. Itama idan tasani bamusan yanda zatayi reacting ba amma idan aka bari aka dai-daici lokaci komai zaizo da sauƙi in sha Allahu inaji ajikina babu komai gameda wannan lamari sai ɗumbin alkhairi. Ka saki zuciyarka ka miƙa komai ga Allah in sha Allah kowa zaiyi alfahari da wannan aure"
Hammood gabansa sai faɗuwa yakeyi dan baisan abunda suke tattaunawa ba amma fuskar Baba ta gwada masa kamar bazai amince da Zancen auranba.
Duk shawararda sukayi da yaran Hausa sukayita dan haka basusan abunda suke tattaunawa ba. Bayan sun gama tattaunawa Alhaji Habibu ya sanar dasu shawararda suka yanke da sharaɗinsu. Nan da nan suka amince. Baba ya miƙawa Ya Ahmad sadakin yace yayi mata waliyi. Da mamaki Ya Ahmad yake kallon Baba danshi yaɗauka Alhaji habibu ne zaiyi waliyyin. Zaiyi magana Baba ya katseshi yace.
"Waa take dashi daya wuceka Ahmad? Kayiwa ƙanwarka waliyyi Allah yasa hakan shine alkhairi. Suka amsa da amin sannan Ya Ahmada yace sunjirashi 15minute ydawo da dabino. yabada auren marmeeyy Shikuma Hammood shi ya ƙarɓi aurensa da kansa.
NOTE: mace ce take buƙatar waliyi itace wacce dole waninine zai bada auranta. Mahaifi ko yaya ko ƙani ko wani ɗan uwa har ɗan cikin mace yana aurarda ita. Wato ɗa yana iya aurarda uwarsa. Shi dama namiji wakili yake nema wanda zai wakilceshi amma zai iya amsar aurensa da kansa.
A lokacin aka ɗaura auren. Wata irin ajiyar zuciya Mood ya sauƙe wanda gabaki ɗayansu saida suka kalleshi ya runtse idanuwansa yanajin wani irin sanyi da daɗi da bai taɓa jin irinsa bai. Yau burinsa yacika. Godiya kawai yake yiwa Baba har saida yabashi tausayi baisan wani irin so Hammood yake yiwa marmeyy ba. Amma yana mata so matuƙa wanda baki bazai iya faɗarsa ba. Da hankalinsa bai ƙwanta da ɗaura auren ba amma dayaga halinda Hammooda yashiga bayan ɗaura auren sai yaji abunda yayi shine dai-dai.
Abhie yadafa kafaɗasa yace.
مبروك ابني"
(congratulation my son). Yayi murmushi kawai ynajin wani sanyi yana ratsashi a cikin jikinsa. Yanajin daɗi bai taɓa tunanin haka akeji alokacinda aka mallaki abunda akeso ba sai yau daya mallaki abu mai muhimmanci a gareshi.
P.A ma dake zaune yayi mishi barka ya amsa shima kasa yaji daɗi sosai na cikar burin mai gidannasa.
Aranar Abhie zai koma yaso yaga Marmeeyy amma batanan. koda tana nanma ganinta bazai yiwu ba tunda an rigada an amincewa baza'a saarda ita ba har sai lokaci yayi. Hammood kuwa bazai koma ba sai yabi yaganta dan Haka bai sanya ranar tafiya ba.
Bayan sun tafi Ya Ahamd ya dawowa Baba da akwatin zinaran daya bashi. Baba yace bazai karɓa ba ya ajiye a wajansa. Sanin cewa baida taƙammenmen wajanda zai ajiye yasa yashiga ɗaya daga cikin ɗakunan da Baba baya amfani dashi ya ajiye ya kulle sannan yatafi da key ɗin.
Har cikin gidan Babu wanda yasan da zuwannasa kamar yanda acan abuja ma basusan da tahowarsa ba.
-----
Angama mana gyaran jiki munyi kyau sosai barinma Maryam da Aysha dama sunfimu kyau. Sai dai kitso dake duka nafisu cikar gashi nawa yafi kyau. A wajan aka biyomu da kayanda zamu saka dan a shagon zammuyi make-up. Bayan angama makeup muka shirya cikin kayanmu da aka kawo mana ɗinkin. Skirt ɗina ya matseni sosai saboda inada hips kusan yafi komai Girma a jikina gashi skirt ɗin yazauna kamar wanda aka zanashi a jikin. Ko skirt ɗin sauran bai kamasu kamar yanda nawa ya kamaba. Tunda dukansu nafisu Hips harda ɗan cika ma. yanda kayan yabi jikina baida maraba da doguwar rigar pitted gown dan dai-dai da rigar itama bin jiki takeyi. Daƙayr nake numfashi a cikin kayan.
Mai makeup taɗaura mana head dukanmu munyi matuƙar kyau. Amma nikam ina takure acikin nawa kayan. Ganin yanda nakeyi yasa Anty fadeelah tayi ƙwafa tace.
"Aini dama jinki kawai nakeyi marmeeyy da wannan uban hips ɗinnaki yaushe zakice a miki riga da skirt? Aynda nasan halinki wannan kayan saiya gagareki sakawa" nidai bance komai ba dana sanin ɗinka riga da skirt ɗin kawai nakeyi amma harda laifin tailor ɗinma dannasan measurement dana tura yafi wannan may be yayimin kallon raini yasanya ya rage.
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Mummy taturo driver ya ɗaukemu ya maidamu gida Har lokacin Ya Ahmad bai dawo ba. Abokanansa da suka iso suna part ɗinsa sunata jiransa. Muna shigowa Mummy tace muzauna muci abinci anfara tafiya wajan evnt. Nidai ban iya tsayawa naci abincinba dan gani nake kamar wanda zan ɓata kwalliyata, Mummy bazata halarci wajan event ɗinba . Friends ɗin Ya Ahmad da suka iso suka shigo domin gaida mummy. Mummy tace mu kawo musu abinci da drinks saimu tafi tare tunda kusan duk ƴan aikin wajanta ta aikesu. Ɗaya daga cikinsu yace.
"Ai shiɗinma tun zuwanmu har yanzu bayanan wayarsa kuma bata shiga" cikin halin ko inkula Mummy tace.
"Duk yanda yashiga nasan kafin afara event zai dawo" kamar wanda aka turoshi kuwa sai gashi ya shigo tareda Yaya Habibu. Mummy tace.
"Yawwa kun ganshi ba" wajan abokanansa yayi suka fara gaisawa sannan yayi wajan Mummy.
Sama-Sama suka gaisa sannan yace akawo masa ruwa mai sanyi yasha. Mu muna can gefe muna zaune muna jira su gama mutafi Mummy ta kirani tace nakakawowa Ya Ahmad ruwa. Namiƙe ina faɗin Ya Ahmad ina kashiga tun safe ana nemanka. Batareda najira amsarsa ba nawuce na ɗauko masa ruwa da drinks na yi wajanda suke zaune. Tun kafin na ƙarasa idanuwan abokanansa yake kaina kamar zasu cinyeni ɗanya. Yaa Ahmad ya kalleni idanuwansa suka kai kan kayanda yake jikina. Ya ɓata rai sosai yace.
"Marmeeyy wannna wani irin kayane a jikinki?" na kalli jikina na turo baki nace.
"Me yayi" yaya habibu yace.
"ƙaniyarki yayi maras kunya"
"Yaya tailor ɗinne yarage measurement da nabashi shine kayan ya matse" yajijjiya kai yace.
" toh amma dai badasu zakije wajan event ba koh" nayi narai-narai da idanuwa nace.
"Yaya toh damai zanje"
"Marmeeyy ki rufa mana asiri kicire wwannna kayan idan bazaki cire ba rashin zuwanki shi yafi mana alkhairi" yafaɗa gabaki ɗaya nida Mummy muka zuba masa idanuwa. Cikeda tuhuma Mummy tace.
"Wai meyasa kasawa yarinyar nan idanuwa? Haka jiya taƙi zuwa wajan event saboda tsoronka a dama haka kake mata yanzu bikin naka ma bazaka barta ta sake ba?" da mamaki yake kallon Mummy yanda take backing Marmeey ya tabbata kosu Aysha yake yiwa faɗa bazata saka baki ba amma ta hayayyaƙo masa akan marmeyy. Shikuma ya faaɗi hakanne saboda yasan irin sonda Hammood yake mata kuma ya tabbata idonsa yana kan duk wani abunda take yi. Yasan yanda larabawa soyayyarsu take tafiya da masifaffen kishi barinma so irin na Hammood daya fita daban. Allah kaɗai yasan abunda zai iya aikatawa akan soyayyarta. Amma ganin Mummy nason ta fahimci wani abun yasa yace.
"Ina sauran suke kuma ku taso naga kayanda kuka saka. Dukansu suka taso yace.
" kingani koh marmeeyy duk cikinsu Babu wanda kayansu yakama kamar naki. Kije ki canja kokuma na hanaki zuwa bikin gabaki ɗaya har agama event dan dai bazaki fita ahaka ba" Na ɓata fuska sosai nace.
"Yaya kainefa farkon aure agidanmu yanzu dan Allah idan banje wajan bikinka ba bikinwa zanje"
"Ni bani bane farkon aure kije ki saka gyale" ban fahimci abunda yake nufi ba dan haka ban kai hankalina wajan ba. maryam ta ƙunshe dariyarta dan ta hango yanda kayan zaiyi da gyale. Idanuwana suka cika da ƙwalla bawai nasaka gyalen dayace nayi ba sai dariyarta naga sunamin. Ina shirin fashewa da kuka nace.
"Yaya kaga dariya sukemin" yace.
"Dukanku ku ɗaura gyale akan kayanku kokuma bazaku jeba. Kuma sauran kayanku dake wajan tailor gara ku kirashi tun yanzu karya muku irin wannan ɗinkunan ko bazaku saka su ba" Mummy tace.
"Kinga Marmeeyy rabu dasu karki ɓata ƙwalliyarki" muje anemi gyalenda zaki saka" nayi wajanta muka shiga ciki dama tana business na gyalluluka da takalma harda jakankuna acan na nemi gyale da takalminda suka shiga harda ƴar ƙaramar jaka. Saima hakan danayi yafi ƙyau. Nafito dukansu Mummy suma ta fitar musu da nasu. Ina fita Ya Ahamda yace.
"Bakiga kinfi kyau ahaka ba?" naturo baki nidai bance komai ba. Yaciro dabino a wani ɗan kwali daga aljihunsa ya miƙamin na amsa da murnata baiyimin wani bayani akaiba na jefashi ƴar ƙaramar jakata. Saida Ya Ahamd yayi wanka ya shirya sannan muka fita dan tafiya a motar abokanan ya Ahamd muka tafi. Daga nan muka wuce gidan amarya muka ɗauketa tukunna muka wuce wajan event. Matar Ya Ahamda kyakkyawa ce sosai. Kuma tanada son mutane Anyi event lafiya angama muka dawo gida. Dake mungaji sosai acan yasa muna dawowa sallah kawai mukayi muka ƙwanta. Dan munci abinci wajan event.
Dake munƙwanta da wuri sassafe muka tashi dan gidan yafara cika.
Yauma anyi event angama lpy lau event yayi daɗi sosai. Mummy ce tabamu kuɗinda Zamuyi masa manni.
Biki yana buguwa kuma yana daɗi sosai.
Wani labarine wanda gabaki ɗaya ya hargitse kowacce ƙasa wanda har yanzu aka kasa samun sahihancin labarin.
Tun jiya Mood ya canja bio ɗinsa na social media da wani tambari wanda acikin celebrities masu aurene kawao suke amfani da wannan tambarin duk wani celebrity da akaga yasaka wannan toh tabbas yana da aure lamarin yaja hankalin Al'umma lokaci guda aka buga a gidajen jaridu tareda tambayoyi masu tari yawa. Gidajen TV da radio da sauran kafafen yaɗa labarai. Duk wannan budirin da akeyi bansamu labari ba har saida nahau instagram kowane page na duba maganar kenan amma babu wata gamshesshiyar amsa dm ɗinsa kamar zai fashe da messages ko masu kulada social media ɗinsa basuda lokacin bin waɗannan messages bare shi da saiya samu lokaci yake dubawa.
Gabaki ɗaya Hammood yaja yayi buru da al'amarin kamar wanda bashi dakansa yaɗaura abunba. Ya ɗaura yaja gefe ya nutsu waje ɗaya yabar masoyansa da kace nace. Wasu daga cikin masu haukar sonsa harsun fara rikici saƙon barka da taya murna kuwa a lokacin baisan adadin shigowarsu ba. Koda zai ɗauki tsawon wata biyu yana replying saƙo batare da hutawa ba bazasu iya maida saƙon da suka samu duka a wannan lokaci ba. Su kansu masu handling social media nasa basusa takamammen bayani akan abunda yake faruwa sudai kawai sunga yahau yayi uploading abu Kuma basuda tacewa ko damar tambaya su dai kawai suna aikinda aka ɗaukosu suyine."
ZAYNAB BAWA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Ajiyar zuciya nasauƙe alokacinda na gaji da duba lamarin dayake faruwa. Nasauƙe wayar ina faɗin.
"Wata tayi wuff da wannan aljanin"
"Waye kuma aljani?" maryam ta tambaya.
"Hammood mana ɗan wasan ƙwallo wanda ranar muke hiransa. Kinmanta har nake cewa Su dama ƴan wasan ƙwallo basu cika auren sanannu ba sukayimin musu firr bagashi ba"
"Toh yanzu waya aura?" ta tambaya.
"ni ina nasanine? Ai bai faɗa ba"
"kun haɗa kanku da aiki" cewar Aysha dan ita tatsani wasan ƙwallo. Muna hirar Mummy tasauƙo tace muje part ɗin