Showing 6001 words to 9000 words out of 171869 words
Chapter 3 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
hankali sai musan yanda za'ayi" Girgiza kai yayi yace.
"Baza'ayi hakaba Mamee tayi kokari taci jarabawar ne danta faranta min nima ya zamenin kamar dole na faranta mata dole mamee zataci gaba da karatunnan ta farantamin nima zanyi mata haka kyautatawar da zanyi mata kenan"
"Amma tayaya? Tayaya zaka iya daukan nauyin karatun yara uku?" Karki damu Allah zai kawo mana hanya, shiru kawai tayi amma tausayinsa ya cikata tasan baida halin daukar nauyin karatun yaran gabaki dayansu, yanzu haka zaije ya takura kansa ne gashi ba cikekken lafiyane dashi ba, sai takeji inama ace Mamee tafadi wannan jarabawar dan tananne kadai zai samu sauki, kiran Sallar magrib da aka fara yine ya sanyashi mikewa yashige ciki yayi alwala yafito yawuce zuwa masallaci."
Ban tashi daurawa Baba ruwan shayinba saida aka kira isha'i saboda nasan idan yafita sallar magrib baya shigowa gida sai yayi Sallar isha'i bayan nagama najuye a flask ina jiran shigowarsa na mika masa ruwan shayin. Dauka nayi nakai masa bayan naji shigowarsa wannan ka'idane kullum sai Baba yasha ruwan shayi idan banice na dafa masa ba toh matansa ne zasu dafa sukai masa.
Da wayar Mama nakira maryam na shaida mata cewa nima na haye jarabawar domin jiya tun tana tsokanata har itama kanta tadawo ta damu. Ganin yanda nashiga damuwa yasa itama tashiga damuwa amma dake nayi zuciya yasa harna taho ban kulata ba.
Maryam tayi murna sosai kamar yanda nayi ihu haka itama najiota cikin wayar tana ihu tana fadawa mahaifiyarta kashe wayar nayi dan kada mucinyewa mama kudin wayarsa. Mintuna kalilanta biyo da kira cikin sigar zolaye tace.
"Kai ashe dai babu rabon za'ayi miki aure da karancin shekaru" tsaki naja sannan nace.
"Kefa maryam baki iya samun abuba wallh shiyasa wata rana har banaso nabaki labari banza"
"Malama kina sake zagina zan kashe wayata" cikin halin ko inkula nace.
"Toh kashe mana dama ni nasaka ki kirani" mtsewww taja tsaki takashe wayar bin wayar nayi da kallo Afili na furta.
"Lallai maryam bakida mutumci" na ajiye wayar gefe ko mintuna biyu bata bada a tsakani ba tasake danna kiran ina kallon wayar yashigo kamar bazan amsaba sai kuma na amsa ina ciccin magani.
Mukaci gaba dayin wayar daga karshe dai muka sake yin fada kowa tayi fushi ta ajiye wayar.
Sabbin Uniform Baba yakara dinkamin saboda sati daya kawai suka bada zamu koma aji duk wani abunda za'a bukata kafin sati Baba ya tanadarmun dashi.
Sati yana cikawa muka fara daukan darasi a makaranta.
Baba ya aika Yaya Ahmad ya sayawa fadeela da Aysha form na polytechnic amma Aysha tace. Ita nursing takeso ko degree Baba yace. Sai dai tajira wata shekara. Hakan akayi danta gwammaci ta bata shekara guda ta yarda zata jira, dake lokacin ina cuku cukun biyan JAMB kawai sai Baba ya biya mata. idan lokaci yayi zata zana.
Ina zaune adaki ina duba littafaina Baba yaturo akirani babu bata lokaci natashi natafi shida Mama nasamesu a falonsa nashiga da Sallama su dukansu suka amsa, bayan nayi musu Sannu da hutawa na zauna gefen Baba,
Ganin ana buga kwallo ya sanya nasan dalilin kiranda Baba yayimin na zauna muka fara kalla Mama har gyangyadi tafara dan bata iya kallan kwallon. saida aka gama sannan Baba ya dauko wani abu a leda ya mika min dake ledar mai ruwan garau ce ina kallo na fahimci menene aciki amma na bude dan tabbatarwa,
Wayace sabuwa dall a fankonta android Baba ya siyamin, ihu nasaka saida mama tatashi daga gyangyadin da takeyi cikeda bacin rai take fadin.
"Yau nikam wannan shashanci ya isheni ke yaushe zakiyi hankali? Da zarar anci kwallo kin cikawa mutane gida da ihu kenan?"
"Mama kingani ba kwallo akaci ba Baba ne ya saimin waya" da mamaki mama ke kallon wayar Hannuna sannan tajuya tadubi Baba tace.
"A'ina kasamu kudi kasai mata waya Alhaji? Dan Allah saboda karatun yarinyarnan kada ka sanya kanka cikin damuwa da waya da babu waya zatayi karatunta" Murmusawa yayi sannan yace.
"Shekarun Baya kenan ai yanzu lokaci ya canja idan babu wayar bazata samu damar yin karatun ba"
"Amma!" Baba ya daga mata hannu sannan yace.
"Nasan zaki tambayi yanda nasamu kudi daya dga cikin gonakina nadauka na bada hayarta ta shekara biyar daganan harsu gama karatunsu zan sami kudinda zanna biya musu hankali kwance"
Jikina yayi sanyi matuka jin cewa saida ya jinginarda gonarsa kafin yasamu kudinda zai biya mana karatu. Toh wannan Bawan Allahn dame zamu saka masa?
Komawa nayi na zauna jiki a sanyaye nace.
"Baba Allah ya saka maka da dumbin alkhairai masu yawa Allah yabiya maka bukatunka yasaka maka da aljanna"
"Amin" ya amsa cikeda jin dadi. Mama dake tanason korata a wajan tace.
"Kinfasa zuwa karatun da kikace zakije ne?" Kai na girgiza mata dasauri nace.
"Banfasa ba"
"Toh naji baki tambayi Babannaku ba" Baba yace.
"Karatu Zataje ta?"
"Eh itada kawarta amma naji batayi maganarba"
"Shikenan tajeta Allah yabasu sa'a" na amsa da "Amin" sannan nafice. Ina shiga daki na ɗauki wayar Mama na kira Maryam tace Zatzo ta daukeni. Minti talatin ta iso nayi musu sallma muka fice karatun 2hours kawai mukayi Maryam ta matsa sai mun wuce gidansu dake ban tambaya naki amma danaga tayi fushi tana faɗin.
"Tunda muke dake baki taɓa zuwa gidanmu ba amma ni naje gidanku sau babu iyaka Allah har indai yau bakije gidanmu ba toh bankara zuwa naku gidan"
"Duk mai yayi zafi haka? muje amma bazan daɗe ba tunda kinga ban fadawa Baba ba"
Murna sosai Maryam tayi dake dama driver yana jira kai tsaye muka wuce gidansu dake unguwar fadaman mada anan garin bauchi,
Gidansu ya haɗu sosai gidane Babba tsararre mai hawa biyu tun daga wajan gidanma abun kallo ne bare awuce zuwa ciki, a yanda maryam take mu'amala faram-faram da mutane baza'a taba dauka dukiyarsu har takai hakaba sai dai dama daga yanayinta zaka gane sunada hali.
Mai gadi ya bude mana gate muka shigr bayan minfito a motar kai tsaye ɗakin mamansu muka fara shiga muka gaidata, tanada fara'a sosai cikeda Murna take faɗin.
"Yau wace rana Mamee tazo gidanmu kullum saijin labarin Mamee amma ban taɓa ganinta ba" dariya kawai nayi muka wuce ciki ta falonda muka ratsa zamu wuce muka riski wani Saurayi zaune yana danne-danne a laptop ta company apple dake gabansa,
batareda ya juyo ba Yace.
"Harkinyi karatun kenan?"
"Eh mungama shine muka taho gida"
Murmushi yayi mai sauti wanda yasanyani satan kallonsa iya gefen fuskarsa nake kallo amma hakan bai hanani gane kamanninsa ba, kyakkyawane sosai na karshe duk yanda nake kallon kyawun Maryam nasa ya zarce nan fatarsa har wani tarr tayi sai sheki takeyi kamar madara gashi yanda yake tafiyarda laptop na gabansa cikin tsari da nutsuwa gwanin ban sha'awa saukarda idona kasa nayi na tattaro nutsuwata da sanyayyar murya nace.
"Ina wuni" batareda ya dago ya kalleni ba ya amsa maryam taja hannuna mukabar wajan, ɗakinta muka shiga shima da ɗan karamin palour da saitin kujeru sai kuma uwar dakin da saitin gado kamar dakin amarya kayanda aka zuba mata adakin amaryarma idanba yar masu hali ba bazata samu kamarsa ba.
kwanciya nayi kan bed ɗin ina maida numfashi maryam ta kalleni tana faɗin.
"Sannu" ita a tunaninta gajiya nayi yansa nake maida numfashin abunda bata saniba shine tunda nayi arba da Yayanta bugun zuciyata ta sauwa."
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
✔️Ote
Comment
Follow
share
To be cintinued
Zaynab Alabura
*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023
*بسم الله الرحمن الرحيم*
BY
ZAYNAB BAWA
PAGE 5
Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?
Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073
*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*
INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!
TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).
WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!
BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*
****
Ajiyar zuciya na sauke ta kalleni tace.
"ina zuwa" ɗan karamin fridge dayake dakin ta nufa tadaukomin ruwa da lemo ta ajiye gefen gadon tace.
"Tashi kisha ruwa" banbi takan ruwanda takawo ba
na miƙe zaune wayarda Baba ya siyomin na ciro ajaka na mika mata dama already nafaɗa mata Baba ya siyamin wayar ina mika mata ta jonata a chargy tafaramin setting dinta,
Instagram da whatsapp ta budemin tadaura pic ɗin data daukeni mai nikab akai. Mikamin tayi tace nayi following wanɗanda nakeso ina karɓa nafara following ƴan wasan kwallon kafa (footballers) Da mamaki maryam take kallona duka takaimin tana faɗin.
"Ke ana folllowing mutanen arziki ke kina shirme" mtsww naja tsaki sannan nace.
"nikuma kinga ai mutanen tsiya nayi" karban wayan tayi tafara searching abubuwa tana nunamin tana faɗin.
"Kingani irin waɗannan ake following kina mace menene ya haɗaki da ɗan wasan kwallo kuma?" Fauce wayata nayi nace.
"Yan wasan kwallon dai su nayi niyya kuma su zanbi. naga wayata ce ba taki ba? ƴan wasan kwallon kaff sunmafi kowa yawan followers"
Bata sake kulani ba nikuwa naci gaba da dannawa pictures dinsu likes, aɗakin ta ɗauko mana abinci takawo mukaci tafita da kwanukan sai wajan Yamma kafin muka tashi tafiya muka fito dan yiwa umminsu Sallama a falon da muka barshi muka taras dashi sai dai da alamu ya tashi danya canja kaya. Munzo daff zamu fita muka tsinci muryarsa yana faɗin.
"Kujirani zan kaiku" toh kawai maryam ta amsa amma abin yabata mamaki dan datsu babu yanda batayi ba yace bazai kaitaba tunda shi ba driver dinta bane amma yanzu bata tambaya ba yana fadin tajirashi yakaita.
Wajan Umminsu Maryam muka wuce danyi mata Sallama Kudi taɗauka tabani naki karba babu yanda batayi na karɓa ba naki bayan hakama ban faɗa agida zanje gidansu naryam ba kuma mama idan taga kudin sai tayimin faɗa, Umminsu Maryam bataji daɗin yanda naki karban kuɗin ba amma nima babu yanda na iya saboda yanayin gidanmu,
Muna zaune a falon munajiransa yashigo Bai kalli yanda muke yace.
"Muje" Nan danan zuciyata tafara bugawa da sauri-sauri jin muryarsa danayi a hankali na daga kaina na kalli fuskarsa farine sol kyakkyawa yanada dogon hanci da manyan idanuwa kana kallonsa kaga sakk bafulatani kamarsa ɗaya sak da Umminsu, Yanada tsayi kuma siririne, Cikin harshen fulatanci naji yana yiwa Umminsu magana itama ta maida masa da harshen fullancin amma naji ta ambaci sunansa Abubakar abunda na iya ganewa kenan acikin abunda suka faɗa bayan sun gama maganar Ummi ta juyo ta dubeni tace.
"ki gaishe da Mamanku" na amsa sannan mukayi mata sallama muka fice. Kafin mu karaso harya isa gaban motarsa yashiga mu kadai yake jira. Maryam ta bude min bayan motar nashiga tarufe sannna ta shiga gaba, tunda muka fara tafiya baice komaiba tuƙinsa kawai yakeyi cikin nutsuwa ganin yanda maryam ta nutsu duk kuwa da rawar kanta ya tabbatarmin da cewa bayason hayaniya saida muka hau titi sannan naji yace.
"ina zamuyi?" yayi maganar ne batareda ya kalli ko daya daga cikinmu ba.
"Kobi" Maryam tafaɗa sannan tayi masa bayani yanda zai gane. tunda muka fara tafiya nake satar kallonsa amma shi gabaki ɗaya hankalinsa ba'a kanmu yakeba. Yanda kikasan bai sanda mutane acikin motar ba. Sa'i-Sa'i maryam take jiyowa tanamin magana ina bata amsa. A dai-dai ƙofar gidanda ta faɗa masa yayi parking motarsa,
Muna isa nayi masa godiya da kayi kawai ya amsa na fice. Inajiyo maryam tana cemasa zataje ta gaida mamana juyawa nayi naga ko ita zai bata amsa sai naga itanma da kayin yabata amsa fitowa tayi muka wuce ciki tareda ita suka gaisa da Mama sanin yana jiranta yasa bata daɗe ba tafito suka wuce."
2YEARS LATER (Bayan shekara biyu)
Sanye nake da farin Uniform ɗina. ɗinkine wanda aka yishi na zamani yayi matukar zaunawa yamin kyau sosai yasha guga dagani har uniform ɗin sheƙi mukeyi. a shekara biyunnan da suka wuce nayi matukar kyau nayi cika har tsayi saida naƙara izuwa yanzu na cika ƴan mata wacce za'a kalla akirata da ƴan mata, baƙar jakace schoolbag maƙale a bayana duk wasu takadduna suna cikinta, muna sanya ƙafarmu cikin school ɗin wayata tayi ƙara. Inajin ƙarar shigowar Saƙo wayata saida gabana yafaɗi. Maryam ta dubeni tace.
"Saƙon koh?" Kai kawai na gyaɗa mata cike da damuwa nace.
"Wallh Babe Yanzu har banaso wayata tayi ƙara har indai nashigo school saina tsinci kaina da faɗuwar gaba" Maryam tace.
"ni abunda yake damuna mun kasa gane waye mai wannan saƙon mai kuma saƙon yake nufi" Nisawa nayi cikeda tabbacin abunda zan faɗa nace.
"inada Tabbacin namijine yake wannan saƙo, saƙone ake yinsa da ƙunshasshiyar manufa, saƙon yana nuni da kumshesshiyar soyayya, ina tunanina yana bayyana soyayyarsa gareni kuma ga dukkan alamu BIBIYATA YAKEYI toh amma WAYE SHI? me yake nema a wajena? Wace irin manufa yake da ita akaina da tsawon shekara biyu yakasa Bayyana kansa gareni?" Dafani maryam tayi tace.
"Khair in sha Allah karki damu inaji ajikina koma wanene yake BIBIYAR rayuwarki toh alkhairine Babu wani abun akasin haka ki kwantarda hankalinki kinji?" gyada mata kai nayi danni dai gaskiya yanzu abun yana damuna dafarko bai dameni kamar yanzu ganin lokaci kawai jaa yakeyi amma har yanzu yaƙi bayyana agareni. Nisawa nayi nace.
"tashi mutafi class kawai kar muyi latti" Dariya maryam tayi tace.
Yawwa Babe tashi mutafi ki share wannna mutumin dannaga yanaso ya maida minke baya" tafiya nafarayi ina faɗin aiya ma maidani bayan, biyoni tayi tana faɗin.
" ko zamuje ayi mana tracing na numbern?"
" Share kawai idan yagaji zai bari"
"Uhm Uhm fa babe shekara biyu tsawon lokacine da idan barine yaci ace yabari. Har indai zakina takura kanki da tunani gara muje ayi amma ni inaji ajikina alkhairinr kidaina matsawa kanki ko wanene shi wata rana zai bayyana a gaban idanuwanki"
"Hmm kawai nace nashige Class."
Bayan gama lactures ɗin lacturen yazo dai-dai zai fita yatsaya yakira reg no na yace mai Reg no ya sameshi bayan yagama lacture, jikina sai ɓari yakeyi domin bansan abunda nayi ba tunani babu irin wanda baizo rainaba,
Yana gama lacture yafita babu yanda banyi Maryam tazo ta rakani ba haka taƙi jiki aɗarare natafi office ɗinsa can na tadda ba wani abun bane ya sanya yake nemana details dina zan cika wanda za'a fara biyanmu, nacika nafito, Maryam tana kallon nafito ta tsareni tana tambayata abunda yacemin ƙin kulata nayi data dameni nace.
"Da kika matsu kiji abunda yacemin mai yahanaki biyoni? Sai dai kije ki tambayeshi abunda yacemin" tasan halina sarai bazan fada ba hakan yasa ta ƙyaleni dan haushinta nakeji da taƙi rakani yanzu da ace wani abunne haka zan shanye baƙin cikina ni ɗaya.
Sai wajan magrib kafin muka gama abunda zamuyi a school ɗin kusan yanzu koda yaushe tare muke tafiya da maryam itake saukeni wata rana ma sai tabi ta ɗaukeni tukunna, amma yau tunda haushinta nakeji na ƙudirta cewa bazan bita ba.
Abaya take bina amma naki saurarenta a bakin gate na makarantarmu mukaci karo da motan Hamma kamar yanda maryam ke faɗa masa ya buɗe motan yana zaune aciki amma ƙafafunsa suna waje yana danne-danne a waya ina kallonsa bugun zuciyata ya sauya tashi daya naji fushinda nakeyi yana neman kaucewa, ganin naja na tsaya ya sanya Maryam tayi sauri ta ƙaraso dai-dai yanda nake tana faɗin wai bana baki haƙuri ba?
Jin maganarta ya sanyashi ɗagowa ya dubemu batareda ya kulamu ba yashige motar ya maida murfin ya rufe mungane abunda yake nufi dan haka batareda na kulata ba na isa wajan na buɗe motar nashiga, itama ta ƙarasa tashiga yaja muna cikin tafiya Maryam tadubi Hamma tace.
"Hamma kaga Mamee fushi takeyi dani tun ɗatsu nabata haƙuri taƙi haƙura" Kamar bazai kulaba sai can kuma yace.
"Kukam ai kullum acikin faɗa kuke. Menene ya haɗaku?"
"Hamma wani lecturer nefa yace taje office ta sameshi dannaki rakata shine fa" yayi sauri ya taka burki gabaki ɗayansu suka razana. Ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya tayarda motar sukaci gaba da tafiya kamar bazai ƙara cewa komaiba sai can kuma yace.
"Me zatayi masa a office daya kirata?"
"nima bansaniba na tambayeta taƙi fadamin" tunda suka fara zancen sai yanzu tasaka baki tace.
"Details ɗinane bai cikaba shine yakira yace na rubuta masa"
Uhmm kawai yace amma jikinsa yana bashi akwai abunda zaiyi da details ɗin idanba hakaba ai sai dai takai aɗaura mata a portal. Suna sauƙeni nafita nayi masa godiya itako ko kallonta banyiba.
Wajajen ƙarfe tara wayata tafara ruri lokacin ina zaune cikin ɗakinmu ina duba littafaina, Ganin baƙuwar lamba ya sanya na ɗauka nayi shiru saida naji Sallama daga cikin wayar sannan na amsa, Sai akaci gaba da magana.
"Nasan baki gane waye ba dan nakiraki babu izini Sunana Salman nine wanda ɗatsu kika bawa lanbarki" cikeda rashin fahimta nace.
"ni banbada lambata ma kowa ba"
"kidaiyi tunani dan nidai nasan da hannunki kika rubutamin" shiru