Showing 78001 words to 81000 words out of 171869 words
Chapter 27 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
akwai cartons na drinks da ruwa tun auren Ya Ahmad da sukaje aka cika musu butt din mota dashi Alhaji Habibu mahaifin Mama kawai iya wand . zaiyiwa iyalnsa tsaraba ya deba dake yanada ciwon sugar bayashan carbonated drinks sauran duka Baba yadawo dasu ya bawa matan ya ajiye saurn dake shima ba gwanin shan zaki bane.
Baba yana zaune Mama tashiga wajansa da mamaki take kallonsa yaya Baka shirya ba? Ya kalleta.
"Oh wai dawuri zasuzo?" Haka nake tunani dan Umminsu ta kirani ina tunanin tafiya biyu zasuso da neman iri" saida gaban Baba yafadi dan yanajin haka yasan Zaiyi wuya idanba Marmeeyy bace. Yadaure yace.
"Tofa wace kenan cikin yaran?" Sai sunzo dai maji dannima haka aka sanar dani" hmy
"Toh Allah yakawosu barina kira Baba (Alhaji Habibu) na sanar dashi bai kyautu suzo su sanemi ni kadai ba.
" Eh hakanma yayi Allah ya taimaka ya amsa da amin"
Alokacin yakira Alhaji Habibu ya sanar dashi. Yanata Allah-Allah Alhaji Habibu ya iso kafin isowarsu saboda idan ya kasance Auren Marmeeyy akazo nema zaifi kyau ace yana kusa danshi zaifi yimusu bayani yanda zasu fahimta sosai.
Kafin Alhaji Habibu ya iso su Abban Hamma da mahaifinsu dawasu daga cikin yan uwan Abbansu sun iso. Ana gaggaisawa Alhaji Habibu ya iso shima. Batareda bata lokaci b suka sanarda abunda yakawosu. Bayan shaida musu da akayi yara sunason junansu. Baba yaji Babu dadi matuka dayasan akwai wanda Marmeeyy takeso da bazai taba aurarada itaba shiru yayi yakasa magana.
Alhaji Habibu ne yayi musu bayani hadeda basu hakuri bai fito kai tsaye ya fada musu anyi mata aure ba amma ya fada musu da sadakin wani akanta ita kanta yarinyar bata saniba yakara basu Hakuri. Mahaifin Abbansu ne yafara magana.
"Babu damuwa Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Amma kaya kam munzo dasu bazamu koma dasu ba mu a al'adarmu ba'a fita da kayan aure adawo dasu. Dan hakw idn kanada wata yarinya koda kanwarta ce sai abashi mu mika sadaki kamar yanda mukazo da niyya anyi niyyr kulla zumunci Allah har indai akwai yanda za'ayi toh kar afasa"
"Amma baka ganin su yaran bazasu so hakanba?" Cewar Alhaji Habibu.
" Ai tunda itama wannan an karbi sadakin ta batareda saninta b suma hakan za'ayi inada tabbacin yakini da kuke dashi akanta shiyasa suka yanke hukunci bada saninta ba. Suma wadannan ku sanya wannan yakinin akansu ina fata bazasu bamu kunya ba dan sun samu tarbiya. Inbanda yanzu zamani ma da yara suka kwallafa rai a soyayya ba dacan ina akasan wata soyayya aure akeyi batareda Sanin junaba kuma muyi hakuri mu zauna"Kowa a wajan ya aminta da shawarar da mahaifinsu Abba ya bayar na hada auren Hamma da Aysha Baba shikansa yaji dadin hakan amma jin dadinsa yana yankewa kasancewar baisan yanda yaran zasu dauki zancen ba." Dake Bbbane sosai dan har Alhaji Habibu ya girma ya sanya babu gardama duka mutanen wajan suka amince aka karbi sadaki na Aysha da Hamma. Dake azumi saura 2weeks hakan yasa aka saka auren sallah da sati biyu. Duk wani abun al'ada alokacin sukazo dashi. Dama sun gama shrinsu na komai dan haka aka saka rana bayan Sallah da sati biyu. Yara kuma zasuzo suga juna."
Anrabu cikin aminci da mutunta juna basu wuce gidansu Hamma ba gidan Mahaifinsu Abba suka wuce zasu tattauna. Mahaifinsu yaja musu kunne barinma Abba akan kar wanda yasake yafadawa iyalansa dalilin fasa auren har Ummi dashi kansa Hamman dan yasan iyayenta bazasu yanke hukunci su karbi kudin aurenta batareda saninta ba babu wani kwakwaran dalili. Dan haka kada ayi musu katsalandan abarsu su sanarda ita da kansu. Kowanne a cikinsu ya aminta da hakan.
Ummi kuwa batasan yanda abun ya kaya ba kawai wucowa tayi gidanmu.
Tunda naji muryarta na kule adaki dama tunda bakin suka iso ban fitaba. tareda Maryam sukazo ina jiyota tana tambayar Mama wajena Mama tace mata ina ciki. Tashigo tasanemi zaune akan gado ta dan maki kafadana hadeda fadin.
"Amaryar Hamma yane? Yaya da zaman tunani karki damu lokacin zaizo dawuri. Nayi yake kawai dan na lura Maryam batasan Yaya akeji ba idan akace anzo maganar aurenka baza iya biyeta muyi shirmen ba dan haka na koma na kwanta. Sai tsokanata takeyi amma ban kulata ba saida taga banda niyyar yimata magana saita mike tace.
"Kitashi toh Ummi na palour sai kije ku gaisa" sai alokacin na tuna dole zanje na gaisarda Ummi dan haka na mike na fice palour. Na zauna can gefe na gaisheta ta amsa da fara'a nakasa sakewa da ita kamar yanda nasaba dan haka nakoma ciki. Maryam ma tashigo da jaka cikeda kaya da Ummi tabata ta shugomin dashi anty fadeela ma sai murna takeyi t biyomu ciki Aysha na makaranta. Saida Ummi tayi kusan 2hours a gidanmu kafin tatafi. Bayan la'asar ana daff da magrib Baba ya taramu a palournsa gabaki daya anan mukag harda Alhaji Habibu bayan mungaisheshi Alhaji Habibu Kai tsaye yatafi kam abunda ya tara mu. jiri naji yana debana alokacinda naji yana fadin.
"Dan haka anmaida sadakin kan Aysha in sha Allahu bayan Sallah da sati biyu za'a daura auren. Ke Aysha saikiyi kokari karki zuba mana kasa a idanuwa dan mun rigada mun amince musu kuma yrda da tarbiyarmu yasa sukaso iri wajanmu mukum munga kece yadace abashi auren yasa muka ynke wannan hukuncin" Ga mamakin kowa sake wajan kai tsaye Aysha tace.
"Toh" Anty fadeela ta kalleta da masifar Mamaki takasa hakuri tadubi Baba wanda yake kallon wani wajan dan bayasan ganin yanayinda zan shiga.
"Baba meyasa zakuyi haka? Hamma fa saurayin Marmeeyy ne meyasa zakuyi haka idan aka bari kowa Allah zai kawo mata wanda zata aura amma dan Allah karku raba Hamma da Marmeeyy"
"Kiyi mana shiru baku zaku fada mana abunda ya dace ba mu zamuga abunda yadace mu yanke hukunci tunda wacce aka yanke hukunci akanta ta yarda ta amince toh Alhamdulillhi Allah yamata albarka"
"Kaina yana kasa nakasa dagowa dan banaso kowa ya fahimci halinda nake ciki wani irin daci nakeji acikin zuciya ta. Anki a fahimceni nida aka yiwa musayar masoyi sai ita wacce dama tun lokacin dayazo danaga irin kallon da take masa jikina yabani akwai wani abun data tsara aranta Allah yasa ba ita tasamu Baba da maganar ba Allah yasa ba itace wacce tanemi ajuya lamarinba. Aysha tafara bani tsoro yanzu. Saurin girgiza kaina nashiga yi dan banaso zuciyata ta yarda da cewa itace ta sanya aka juya lamarin yadawo haka. Amma idanba hakaba mai yasa baza'ace Anty fadeelah ba? Bayan itace Babba a cikinmu idan aurenne itace yakamata tafara. Anty fadeela wacce ranta yakai kololuwa wajan baci idanuwanta har hawaye sukeyi tayi saurin mikewa tabar dakin. Mama takasa cewa komai amma har cikin ranta takejin zafin abun. Bayan angama zaman na riga kowa fita adakin kai tsaye dakin Mama na wuce ina zuwa nashiga toilet narufo wani irin kuka mai sanya kuna acikin zuciya nakeyi na dade a ciki bbu wanda yashigo in tunanin irin rayuwarda naso ginawa da Hamma yanzu da Yar uwata zasuyita ina tuna haka sai kuka yasake kwacemin. Bansan abunda yadawo da Maryam ba muryarta naji suna magana da Mama nayi saurin goge hawayena na fito amma hawayen yaki barin bin kumatuna inajin shigowarta dakin na bude nafito duk yanda taso muhada idanuwa naki. Na nemi waje na zaun har tagama maganganunta injin itama kamar kuka takeyi ban kalleta ba.
"Babe kiitashi kije kiyiwa Baba magana nasan zai fahimceki Hamma yakawoni yana cikin tashin hankali yayita kiran wayarki ba'a dagawa menene dalilin wannan sauyin lamarin? Na girgiza mata kai alamun nima bansaniba. kitashi muje Hamma yana waje dakyar na iya bude bakina nace.
"Maryam kije zamuyi waya" ganin bazata samu hankalina ba yasa cikin tausayawa tatfice ta sanarwa Hamma bazai samu ganinaba alokacin ba tana sanar masa yahau kirana a waya ina kallonta har tayi iya rurinda zatayi ta katse yasake kira idona yana kan wayar wannan karonma ban daukaba dan bansan abunda zance masa ba.
Shi atunaninsa in amsa wayar zaiyimin bayani yanda zamu shawo kan lamarin
Amma sam bazan iya hakan ba zan jira naga yanda Allah zai sake juya lamarin batareda nayi abunda zan sabawa ahalina ba. Hawaye yakebin fuskata sosai Mama tashigo tasameni ahaka. Tausayina yakamata sai taji bazata iya jurewa ba.
"Marmeeyy kiyi hakuri zanje nasamu Babanku dan yafison mahaifiyarsu hakan bai bashi dalilin da zai cutar dake ya musanya abunda kikeso ba zan iya hkuri akan komai amma Marmeeyy babanku yakaini makura"
"Nayi murmushin karfin hali kawai Mama macece mai masifar hakuri shekara ahririnda biyu aurensu da Baba tun tasowarmu bamu tabaji ta fadi wata kalma akansa ko ta nuna ya bata mata raiba. Na riko hannunta haededa fadin.
"Kibari Mama tsya muga abunda Allah zaiyi" fuskata kawai ta shafa tafuce batareda tace komaiba.
Anty fadeelah kuwa tadauna yiwa Aysha magana dan tayi-tayi akan taje wajan Baba tace masa batason auren taki cikin rashin kunya take cemata.
"Oh ni maras kunya kenan koh? Mai sabawa mahaifana ita mai biyayya kisaka akara ganin bakina. ina zaman zamana Allah yakawomin hanyarda zan rama abunda tayimin auren Hamma na fashi"
" Marmeeyy yar uwarkice amma karfi dayaji kin dawo da ita makiyarki kina kishi da ita. ita kuma matsayin yar uwa tadaukeki banga abunda ta miki har haka da zaki dauki tsana ki daura mata?" Tun daga wannan maganar Anty fadeelah ta dauke mata wuta tadaina kulata.
Kwana biyu Mama bata sakewa Baba ba nikam ina shiga wajansa na gaisheshi iya kokarina nakanyi dan boye damuwata amma damuwa kam ina cikinta gashi sam naki yarda naji muryar Hamma dan bansan abunda jin muryarsa zai tasomunba.
ZAYNAB ALABURA
:Wannan Littafin na kudine kibiya 300Naira ta asuusn bankina domin samun damar yin karatu cikin kwanciyar hankali. 0003075326 JAIZ BANK ZAINAB M BAWA
Kira da message kala-kala Ga dukkan alamu yana cikin tashin hankali yayita kiaran waya ko message kalamanda yake aiko dasu ya nuna yana cikin matsanancin tashin hankali nikum nakasa daukam kiran banason jin muryarsa dan bansan abunda jin muryarsa zai tasomunba. ina matukar son Hamma banyi tsammanin haka nake sonsa da kaunarsa ba saida wannan abun yafaru lokuta da dama ina zaune sai dai naji hawaye sunabin kumatuna. Duk wata hanya da Hamma zaibi ya hadu dani yabi amma abun yaci tura dan ata wajena na toshe kowacce irin hanya da zata hadani dashi wayarsa ma nadaina dauka sam har yagaji yadaina kira nasan kuma fushi yayi shi asonsa musamu hanyarda zamubi mu nunawa iyayenmun munason junanmu hakan yana nufin sabawa hukuncin iyayennmu nikuma bazan iya hakanba zan jira naga hukuncin ubangiji yanda zaiyi damu.
Ana haka aka koma makaranta banaso nayi missing lactures dan bansaba hakan ba. Haka na shirya naje yiwa Baba yabani kudin transport ina hanya Maryam ta kirani tana hanya nace mata nima ina hanya muhadu a school. Gabaki daya na canja duk wanda yaganni sai yasan ina cikin damuwa. ana gama lactures nacewa maryam zantafi dan sai kusan bayan la'asar aka gama najira ta maidani nace mata zan koma dakaina. Data matsa nace idan akace zan ringa binta a yanzu zan ringa jin babu dadi tayi hakuri sai bayan wani lokaci. Ta fahimceni dan tasan ina cikin wani yanayi."
Kusan 10days da faruwar lamarin babu wani kwakkwaran bayani kan abunda yafaru daga wajan iyayenmu sudai kawai sunce mana an canja lamari hakan yana nufin sun nuna ikonsu akanmu. Lamarin babu sauki kamar yanda nake tunani saboda a kullum tunanina shine gyara kullum kokarina saka mutane a hanya Da abun yajuyo kaina sai naga babu sauki kamar yanda nake tunani amma yazamemin dolena na yi hakuri nadauki komai dasauki najira naga hukuncin ubangiji akaina.
Baba yashiga tashin hankali sosai dayasa wannan abun zai kasance ahaka da bai amincewa su Hammood ba yanason Marmeeyy yanason faranta mata kamar yanda take kokarin farantawa kowa. Gashi Mama sam ta canja masa yanda take sakewa dashi abaya yanzu ba kamar hakaba har yanzu bata fito tace masa komaiba yaso ace tayi masa magana zaiyi mata bayani yanda zata fahimceshi idan takama ya bayyana mata komai zai bayyana mata dan sam bazaiso fushinta ba tun aurensu basu taba samun matsala ba saboda hakurin ta koda ansamu matsalar ita a wajanta bata daukansa a matsala daganan shikenan sai komai yawuce. Amma yanzu yaga sauyin yanayi yasan dole ankaita makurane
data kasa danne damuwarta.
Ya Ahmad ke kwantar masa da hankali hakan yasa ma Yaya Ahmad yashirya dawowa a cikin satin. Ina zaune a daki kamar yanda ya zamemin jiki daga makaranta sai zaman daki ana saura kwana 1 adauki azumi mukaji shigowar Hamma ya tattaro batareda ya sanarwa kowa ba. ina jiyosu suna gaisawa dasu Mama a palour harda amaryarsa.
Saida suka dan dade da shigowa kafin na mike dan banajin dadin jikina a hankali nafita palourn daga ta ciki narike labule na gaidashi. Ya dago ya kalleni cikin tausayawa daga jin muryarta yasan ina cikin damuwa. Ya amsa na kauda kaina gefe dan banason kallon tausayawar dake fuskarsa zai sakamin rauni ya karyamin zuciyata. Na gaisheda matarsa ina kokarin komawa ciki Anty tashigo Yaya Ahmad ya kawarda kansa gefe Ya gaisheta a hankali ita batamasan da ita yakeyi ba saida yasha murry yasake maimaitawa. Bakinta har rawa yakeyi ta amsa naji dadi sosai araina sauran mutanen dakin Mamakinsu yaki boyuwa na koma ciki saida zasu tafi yace muduka mushirya zamuje mu share gidan tunda akayi jere ba'a sake gyarashi ba sai dai kawai Yaya Habibu yana zuwa akai-akai yana duba gidan.
Amota duk hirar da akeyi bansaka bakiba hankalina yana window inajin Aysha sai hirarta take zubawa kamar wacce takeyi da gayya dan naji haushi. Kuma naji haushin raina yayi daci sosai amma ban kalli yanda takeba bare tagane hakan su kansu wanda take sakasu cikin hirar bawani kulata sukeyi ba Anty fadeelah dama basa magana sai Ya Ahmad dayake kallon tsantsar wauta da shirmen abunda takeyi matarsa ce kawai take kulata dan ita batasan dawar garinba. ana isa suka fara fita sannan nabi bayansu. Gidan baiyi wani kura sosai ba muka fara aiki cikin gaggawa muna cikin aiki Ya Ahmad ya leko yakira sunana nadaga na kalleshi batareda na amsa ba.
"Zo kiji" shine abunda yafada sannan yafice na ajiye mopper hannuna nabi bayansa. Akan kujerar dake dayan palourn da muka fara gyarawa ya zauna na isa na zauna akan wacce take kusada nasa.
"Marmeeyy naji abunda yafaru kuma banyi bakin cikin hakan ba saboda inada tabbacin Baba bazai canja miki masoyiba face ya samo miki wanda ya ninkashi. Sannan kuma na tambayeki watannin baya nace miki kina soyayya kika cemin A'a meyasa?" Dakin sanar dani tun wancan lokacin da abun baizo ya kwabe hakaba. Munason farin cikinki kamar yanda kike kokarin faranta mana amma yanzu Bakin alkalami ya rigada ya bushe Marmeeyy kiyi hakuri inada tabbacin akwai alkhairai masu yawa a gaba" na sunkuyarda kaina kawai inata kokarin hana hawaye sakkowa kan kumatuna. Na dago bayan naci galaba akan hawayen na sakala murmushin karfin hali.
"Ya Ahmad kaifa kacemin Duk wani hukuncin da Baba zai yanke a kaina natsaya na fahimceshi. Tayaya zanki jin maganarka? Karka damu na fahimceshi na zubawa sarautar Allah idanu kasan dai kawai lamarinne bazai goge araina ta dadi ba sai a hankali. Na tabbata anayin aurensu zan dainajin komai inada yakinin bazanji komai akan mijin yar uwata ba" Murmushi Ya Ahmad yayi dama yasan za'ayi hakan dam Marmeeyy batada matsala.
"Allah yamiki albarka yadawo miki da ninkin farin cikin da kike tunanin kin rasa" cikin raina ma Amsa da Amin. Bamu zauna gidanba muna gama aiki ya maidamu gida.
Ankama azumi cikin yarjewar ubangiji wannan ayayinda nikuma ma dukufa Addu'a ina gayawa Allah damuwata a kankanin lokaci nafara jin saukin abunda nakeji."
Anata shirye shiryen Sallah nikam nazuba musu idanuwa akan duk wani abunda sukayi dai-dai duk wani abunda akeyi bandani iyakaci idan aka kawomin nayi godiya nakarba. Mama, Baba da duk sauran wanda sukasan yanayin mu'amalata da mutane abaya yanzu suna cikin damuwa danko hira nadaina zama anayi dani bawai dan bazan iya zama cikinsu ko akwai abunda yake damuna yasa nake haka ba duk yanda na zauna Sai Aysha tazauna itama ta yabamun maganganu bana kulata yawanci Anty fadeelah ke amshe maganar ta yaba mata maganganu itama harda gori take mata tace saurayin da take haukar akansa ko lamabr wayarta bayi da ita bare asaka ran wata rana zai kirata.
Akayi sallah angama Lpy daga nan aka shiga hidimar biki daga gidanmu har nasu Hamma bawani shiri akeyi ba ita kanta Ummi batason auren amma babu yanda ta iya saboda zancen daga sama yake. Maryam tabata labarin irin Abubuwanda Aysha ta dinga yiwa Marmeeyy a Abuja sam taji yarinyar bata kwanta mata araiba. Koda tajewa Abba da maganar yanuna mata shima babu abunda zai iya tunda shima mahaifinsa ya yanke wannan hukuncin.
Mama dafarko kamar bazata fara wani shiri ba sai taga rashin dacewar hakan ranta bayaso haka ta zage tafara hidima. Duk wani abu kafin Baba yayi saiya shawarce ta. Ya Ahmad ne yayi mata furnitures shida ita sukaje suka zaba. Dan rashin kunya tazo akan mu rakata zaben furnitures tayi hakanne danta cusa mana haushi arai. Nikam dama tasan ba zuwa zanyiba Anty fadeelah ma taki zuwa daga ita sai Mama da matar Ya Ahmad suka tafi. Dama Baba yabawa Mama kudin kayan Kitchen da Sauran wasu abubuwan. Daga wajan sayayya gidanta kai tsaye aka wuce dashi dan angama komai aka zubasu sai biki saura 1week za'ayi jere.
Idan nace banshiga tashin hankali da karatowar wannan lokaci ba nayi karya. Kawai tafiya nake ina rayuwa amma hankalina baya jikina ido nakebin mutane dashi ina kallon ikon Allah wai Hamma Wanda nashirya rayuwata dashi shine wanda zai auri yar uwata duk yadda naso daurewa haka nake zama nayi kuka wasu lokutan bana iya shiga mutane da lokacin bikin ya karato nadaina zama agida. A school nake wuni zubur ko banda lactures haka Maryam take jirana har sai lokacin da natashi tafiya kafin itama tatafi. Kullum cikin