Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 171869 words

Chapter 32 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1095

Ads at the middle of Article

tunda ta amsheshi bata sake baniba yanzu kam ta fahimci daga yanda zoben ya fito dan fitata nazari take tayi tasan dole shi kaɗai yakeda wannan ikoj yin hakaa akan zobe zallah. Na amsa batareda musu ko tambaya ba nasaka Nawuce na ɗauko gyalena turare Mummy tabini dashi kamar wanda zatayimin wanka har saida naji yahaumin kai duk sanyin ƙamshinsa.


waje dukanmu mukayi anan naga ƙawayen aysha cousin sis ɗinta suna shiga mota tareda Yaya habeeb dama tunda aka fara biki Baba yabawa Yaya habibu mota a hannunsa. Wannan uwar rawan kai itace ya shiga gaba a lokacin a abuja ta nuna tana sonsa har mun taɓa jiyota tana faɗawa aysha.


Na taɓe bakina na buɗe baya na zauna dake harda matarsa zamu tafi Anty fadeelah ma tashigo baya haɗeda wasu cousin sis ɗinsu. Matar Ya Ahamd tashiga gaba suma suka cika wancan motar muduka muka nufi gidan Aysha."


ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin


Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba


Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔


Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo


Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍


Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝
-------


Acan muka samu Maryam dan tunda naga ya Habibu zai tafi na tabbata saiya sanarda ita taje.


Da alamu itama zuwanta kenan bata daɗeba muka iso. Da sallama muka shiga ciki Aysha taba zaune akan kujera jikinta da sauƙi sosai dan ahaka bama za'ace akwai abunda yake damunta ba. Ya Ahmad da Ya habibu basu shigoba suna daga waje muma muka ƙarasa ciki muka zaune. Aysha batayi tsammanin ganina a gidanba dan naga hakan daga fuskarta data ganni kuma sakta yatsine fuska. Murmushi nayi Aysha kenan adakeni a hanani kuka ni itace ke kishi dani bayan masoyin nawane bata iya ɓoye haushin da takeji aranta ako'ina nunashi takeyi. Bayan nayi mata yaya jiki bansake bin takanta ba. Dan naga daƙyar ta amsa. Ƙawayen suka fara zolayarta ta yatsibe fuska tana faɗin.


"uhmm kedai bari aini naji jiki banɗauka haka yakeba mutum ace babu haƙuri" kallonta nake da mamaki yanda take ƙoƙarin fitarda sirrinsu itada mijinta ko tanayin hakanne danta bani haushi?" toh idanma hakanne batayiwa kanta dabara ba. ga anty fadeelah ka matar ya Ahamda sannan ga maryam awajen kota manta maryam ƙanwarsa ce oho ayi mutum sam babu wayo ƙannen bayansa Sun fita gane dai-dai da rashinsa. Namiƙe ina faɗin.


"Toh Allah yaƙara sauƙi bari natafi kema Maryam Yaya habibu yana jiranki fa" ta miƙe dasauri dan itama maganganun Aysha suna shirin ƙure mata tunani.


" sai kundawo cewar Anty fadeelah na amsa mata sannan nafice. Ita Aysha a tunaninta maganganunda tafara ne ya sanyani barin wajan. Muna fita harabar gidan motar Hamma ta danno kai ya tsaya yafito suna gaisawa da Ya Ahmad muka ƙaraso wajan tun daga nesa dana ganshi gabana yake faɗuwa amma haka a daure na ƙarasa dan ahalin yanzu inaso komai da komai da ƙarfi da arziki na yakiceshi araina. Muna ƙarasowa ya Ahmad yace.


"Kinfito"


"Eh"


"toh muje koh" na gaisheda Hamma ina kallon gefe saida ya kalleni na ƴan wasu lokuta sannan ya sam muryarsa da sanyi sosai ban yarda mun haɗa idanuwa dashi ba na juya wajan Yaya habibu.


"Yawwa kinga wannan yarinya wacce tayi zancensa a abuja har take cewa yayi mata abata lambar wayarsa? Wallh yau a gaban motarsa tazo sai hira yake mata ingaya mikk gara ki taka musu burki" maryam ta ɓata rai sosai ta kalli Yaya habibu. Yafara girgiza kai yakasa magana. Da dukkan alamu ta ƙulu sosai. Nacewa a ya Ahmad mutafi. Sai alokacin yayi magana.


"Kaji munafunci kaga yarinyarnan tazo zata haɗamin makirci tayi gaba abunta yanzu da kika haɗe bomb ɗin daɗi kikaji? Munafuka" Hamma harya buɗe baki zaiyi magana dan yaji ransa ya sosu sai yatuna yanzu ba daa bane kawai yayi shiru yayi musu sallama yabar wajan yanata kallona kozan kalleshi nayarda mu haɗa idanuwa naƙi ƙarshe. Ƙin kallonsa danayi yasanya yafara tunanin ko haushinsa nakeji akan abunda yafaru da zai iya dayayimin bayani cewa bada sonsa hakan tafaru ba amma menene amfanin yimin bayani? Ya nunamin bayason matarsa kenan? bayan kuma aure yanzu ya rigada ya haɗa. Da wannan tunanin yashiga ciki ganin mutane ya sanya ya shige ciki baiso yasamu mutane a cikin gidanba dan a hannu yadawo."


"Kai dai faɗi gaskiya nima na lurada kai da yarinyar nan tunda aka fara bikinanna" Ya Ahmad yafaɗa bada alamun wasa ba. Yana gama faɗama yashige mota. Yabar Yaya habibu yanata rantse-rantse. Nacewa maryam tajirani idan sun gama karta tafi saboda tanan zamu dawo. Nima nashiga motar muka tafi. Ina kallo saida yatura wani saƙo kafinnan ya ajiye wayarsa yafara tuƙi.


Kafin mu isa yanda zamuje anfara kiraye kirayen magrib kai tsaye naga sunbar Ya Ahmad yashige damu ciki tako'ina jami'an tsaro sunata shawagi ya Ahmad ya tsayardani a bakin reception na wajan yace na ƙarasa ciki zaije yayi sallah idan ya idar kuma batanan zai shigoba zai turo akaini wajanda zanga surprise ɗinda ya shiryamin. Wajan akwai tsaro sosai bansan kodan bantaɓa shiga bane nake ganin tsaron wajan na musamman ne tunda nashiga ko mutum ɗaya banganiba dan banma shiga wajan reception ɗinba daga yanda ya ajiyeni na hangi masallaci ma'aikatan wajan mata sunata shiga wajan. Nashiga nayi alwala nima na gabatarda sallar magrib dake hadari yahaɗi agarin ga iska mai daɗi yasa aka haɗa Sallah da isha'i. Bayan mun idar ina zaune naga duk ma'aikatan da suke wajan mata sunfita dasauri Da alamu anbasu time ɗinda akeson su hallara a yanda zasuje nayi tunanin hakanne ganin yanda suke sauri su dukansu. Ina zaune a cikin masallaci message na Ya Ahamd yashigo wayata wacce zata Ƙarasa dake ciki tana ƙofar masallaci tana jiranki. Nayi mamakin yanda akayi ya Ahamd yasan ina masallaci.


Na ɗaura ƙwalina nafita a wajen an taradda wasu mata guda biyu ina fita suka fara gaisheni cikin ladabi ɗaya christian ɗaya musulma dukda ƴan matane amma sun girmeni feww da aniya hakan yasa nakasa amsa gaisuwar suka fara yimin iso acan gefe da ainihin main ginin guest palace ɗin mukabi ahaɗe suke da main ginin amma shi a gefe aka haɗashi daban step muka fara hawa amma step ɗinda muka hau baifi 10 ba steps ba muka riski ƙofar wajan ta glass ce ana iya hango komai dake ciki daga wajan. Tun daga wajan suka barni suka juya na danna ƙofar ta buɗemin na shiga ciki saida nakusa tsayawa yin ƙauyanci domin an ƙayata wajan matuƙa dagaske wajene akayi decoration ɗinsa matuƙa yahaɗu kujeru ne a gefe guda biyu da table sunsha decoration da candles gabaki ɗaya wajannma haske candles ne ya haskeshi sai cups guda 2 da kwalbar wani abunda bantaɓa kallon irinsa ba can gefe da wajan kuma Unique lixury italian chairs ne wanda sukayiwa wajan yazaa kamar living room. Harda madaidaicin TB a gafen can ƙasan wajanma gabaki ɗaya carfet ne samansa kuma fayau ana iya kallon komai duk yanda zan tsaye faɗa muki kyau da tsaruwar wajan abun bazai misaltu ba."


Ya Ahmad yana tabbatarwa nabar na isa wajanda Hammood yake yajuya yatafi dan ɗaukansu Anty fadeela suwce gida.




Tun safe Anty fadeelah bata kunna data ba tana kunnawa notification suka fara shigowa cikin notification ɗin harda wanda akace mata Hammood yayi following Marmeeyy gabaki ɗaya hankalinta bai kaiga marmeeyy ƙanwarta ba ita bama son ƙeallon kafa takeyi ba tun lokacin Marmeeyy batada waya tana afani da phone ɗinta wajan kalle kallen ƙwallo tayi mata following ɗinsu dayawa. Ta danna kan notification ɗin tashiga wajan tana faɗin.


"Kunga nima sun nunamin datsu kuka gama hiran wannan ɗan wasan ƙwallon ƙafan yayi following wata" alokacin wayarta tana loading zata kaita kan abun kenan tana buɗewa da pic din profile na Marmeeyy idobta yafara arba dake pic ɗinta tasaka mai niƙab wanda Maryan ta ɗaukesta shekara biyu a islamiyya har yau bata cireshi a ahaka baza'a iya bambamce idon bahaushiya ce kota balarabiya ba. Domin kuwa idonta kawai yafito a niƙab ɗin shiyasa ko ɗatsu da sukayi zancen basu gano bahaushiya ba ce.


shiga kan abun tayi ya tabbatar mata Marmeeyy ce Marmeeyy ƙanwarta gashinan awanni dayin following ɗinta amma followers ɗibta suntafi 5m ihu anty fadeelah tasaka suna tambayarta menene tace.


"Marmeeyy marmeeyyn mufa yayi following gashin followers ɗinta suntafi 5m"



"Bangane ba wace marmeeyyn? Wai mema kuke zance akai?" Aysha ta tambaya. Basu bata amsaba Maryam tashigo.


"Ya Ahmad yana jiranku yana waje yace dukanku kufito mutafi" saida Aysha taji gabanta yafaɗi daram.
Dan bataso mutane sutafi saboda taba kallon irin kallonda Hamma yake mata tun a asibiti ita yanzu tsoransa takeyi bataso aabarsu su kaɗai.


"Maryam ɗan duba page ɗin Marmeeyy na insta nagani" Maryam taciro wayarta taba faɗin ni nama kwana biyy ban leƙaba barina duba"
Ihu tasaka da saida Hamma yafito daga ɗakinsa rai aɓace yace.


"Ke lafiyarki kuwa?"
"Lafiya ƙalau Hamma naga followers na Marmeeyy tashi ɗaya suntafi 5M ne kumafa 2days daya wuce ko 2k bata kaiba"


"Ke Hammood ne Hammood nefa yayi following ɗinta" Aysha tayi murmushi sai kace abun al'amara dan tanason ƙwallansa kawai sai yayi following ɗinta akwai fans ɗinsa da suka takata suka shanye amma baiyi nasu ba" Harara anty fadeelah ta wurga mata.


"Toh ƴar baƙin ciki saiki ɗauki wayarki kiduba kigani gashinann" ta miƙe tana faɗin Ya Ahmad na jiranmu barina tafi inje nabasu albishir Marmeeyynmu tazama celebrity" Tatashi tafice tabarsu awajan suna confirming itakam Aysha batama ɗauki wyaarta ba dan tasan ɓata lokacinta kawai zatayi dan hakan ba dai-dai bane.


"Ke dagaske fa sistern kuce naga tana following ɗinku gabaki ɗaya kuma kuma kunayi" cewar ɗaya daga cikinsu cikin sanyin jiki.
Hamma kuwa suna faɗin aduba bai tsayaba yawuce ɗakinsa yaɗauki waya zai duba.


Ajiye wayarta Aysha tayi bayan tagama ganin abunda yafaru ta tabbatar mamince.


"Uhmm sai dai fa idan anyj hacking account ɗin ɗaya daga cikinsu dan hakanma bamai yiwuwa bane toh amfanin mema marmeeyy zatayi masa da zaiyi following ɗinta?" itadai Aysha har lokacin bata yardaba har suka tashi zasu tafi ta rakasu har harabar gidan duk da batajin daɗi amma tanaso taji ƙarin bayani ko akwai labarinda su Ya Ahmad suka samo.


"Ya Ahamd ashe kai ka daɗe da gani kenan?"


"Eh ai tun safe yayi following ɗinta" cewarsa Anty fadeela da Maryam sai murna suke yayinda sukuma sauran kamar anyi musu mutuwa.


Jiki a sanyaye sukayiwa Aysha sallama da faɗin toh mukam dai muntafi dama sallama mukazo miki.
Aysha ta marairaice fuska haba kukuwa ba cemin kukayi idan kukazo bikina sai kunyi sati ba.


"Ke aini wannan abunda naji ya ƙaramin kaimin tafiya dama tunda mukaji Hammmood ya diro ƙasa muka goge zancen sati da yauma fa zamu tafi amma bamu samu ticket ba amma gobe dolenmu mutafi muje ko muma idan muka shiga jerin fans ɗinsa zamu samu yaui following ɗinmu"


"Wai yazo nigeria dama?" aysha ta tambaya.


"Eh tun jiya yasauƙo" Ya Ahmad yayi dariya.


"Ai wai dama da kuka matsa saikun koma dalilin Hammood ne? To ai Hammood yana garinnan"


"Eh ai munsani tun jiya mukaga update"


"No i mean yana cikin garin bauchi yanzu haka marmeeyy nakai wajansa na dawo.


"Kai haba sai kace wani al'amara Hammood fa?" Yaya habibu yafaɗa yana dariya.
"Uhum shifa ai dai tunda kunga yayi following ɗinta yakamata kusan cewa zuwa wajansa abune mai sauƙi kubari idanta dawo zan nuna miku pics ɗinsu ko videos tare" nasan bazata kasa ɗauka ha idan har bai sanarda ita matsayin koshi wanenne a wajanta yau ba" Maryam da daka tsalle haɗeda sanya ihu tana faɗin.


"Yeeeehhhh ɓoyeyyen masoyi ya bayyyana" su duka suka juya suna kallonta da rashin fahinta harda Yaya Ahmad ɗin shi kansa.




Ƙamshin tuarenda ya tsaya mata arai shi hancinta yafara jiyo saida ta sauƙe ajiyar zuciya saboda tasamu nutsuwa a shaƙa ɗaya data yiwa wannan ƙamshin.




ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin


Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba


Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔


Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo


Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍


Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝






Da mamaki Ya Ahmad yake kallonta.


" me cikakce Maryam?" riƙe bakinta tayi tunowa datayi tayi kasassaɓa.


"Uhmm ammh dama akwai wani wanda yake yiwa Marmeeyy text awaya tsawon shekaru har yau bamusan koshi wanene ba shi naie kira da ɓoyeyyen masoyi"


"Ban fahimta ba. Further explanation please" Cikin jin daɗij abunda take shirin faruwa da ƙawarta ta zayyanawa Ya Ahmad komai. Jin shiru Aysha bata dawo ba yasanya yasa Hamma yafito ya samesu sunyi jugum kamar masu ɗaukan darasi maryam kuma sai zuba kawai takeyi musu.


"kunga har lacturern ma dama lokacin yafaɗa yace duk mutuminda zai iya sanya companyn layi su rufe toh ba ƙaramin mutumi bane mukam ma bamuyi tsammanin mutum ne kamar Hammood Ba duk wani kira message da zai shigo wayarta yasan dasu harfa message na whatsapp yashigo wayarta yasani tana ɗaura pics a insta zaisa a sauƙe mukam har muna cewa ma aljanine"


"Eh toh ta iya yiwuwa aljaninnne tayaya za'ace ɗan adam ke wannan aikin. Kokuma ace Hammmood ke wannan aikin akan wata yarinya wanda ƴan anguwarsu ma ba lallai sun santaba sai kace abun al'amara" cewar ɗaya ɗaga cikin ƙawayen Aysha cikin ɓacin rai.


"Barsu mana please ana maganarda hankali zai ɗauka" wacce take bibiyar Yaya habibu tafaɗa. Maryam dama tanada cikinta aikuwa ta amshe.


"Eh ai bazaku yardaba dayake baƙin ciki da hassada yayi muku katutu ƴan hassada kawai baƙin ciki zai kasheku kuwa Marmeeyyn nan babu abunda ta tsare muku amma kunbi kun sakata agaba. Toh nagaba yayi gaba in sha Allahu Hammood shine ɓoyeyyen masoyi bari Marmeeyy tadawo muji wanda bazaiji ba ya toshe kunnuwansa" Anty fadeelah ta amshe.


"Haba maryam ya isa haka barsu sufa masa mata hassada few days back suka gama mata fatan alkhairi suna cemata Allah ya maida alkhairi kiksan ko addu'arsu tana ɗaya daga cikin wanda Allah ya amsa" ta ƙarasa maganar da gatse.




"Barima nakirata yanzu mu tabbatar Tana faɗin haka tayi dialing numberta. Saida tayi ringing tagama ban ɗauka ba. Maryam bata jira taji na ɗauki wayarba tacigaba da magana.


"Lala lala Haram Wallh ko kusa ba addu'arsu bace tayi aiki yanzu ai sune masu buƙatar fatan alkhairi ba Marmeeyy ba itakam Marmeeyy Allah ya kashe yabata"


"Waike da kike wannan zancen kinata faɗin Allah ya kashe ya bata uwarme ya kashe ya bata? Nifa banma yarda wai Hammood yazo ganiba may be ma wani talakan balarabe ne mai kama dashi yake walahardaku" ya Ahamd ya ɓata rai yace ya isa haka kubar wannan shashancin kowacce a cikinku ta shiga mota mutafi. Duk wanda yakeda wani tunani cikinku keep it for your self babu wanda ya nemi yaji and Maryam sunanda Kika bawa Hammood ya dace dashi sosai (Ɓoyeyyen masoyi) kubar Aysha tashiga ciki kunga mijinta yafito." ya Ahmad shi yaga zuwan Hamma tun fitowarsa ganin suna magana yasa yaja yatsaya. Aysha ita tarasa abunda takeji gameda wannan auren kwanaki tabbas tasan ya Ahmad yace yataɓa Kallon Hammmood har Marmeeyy ta roƙeshi akan duk randa yasake kallonsa itama tanaso taganshi. To ko Ya Ahmad ne ya haɗasu dayake yasaba wariya tsakaninsu yasa aka canja masoyinta zuwa kanta ita kuma ya haɗata da Hammmood ɗin taso tatofa albarkacin bakinta ko zataji sanyi sai dai kuma da Maryam ake magana ita kuma batason wani abun ya haɗata da Maryam tunda yanzu a gidansu tadawo take rayuwa itama tanaso tasamu soyayya a wajansu.


"Ke Aysha kishige gida mijinki yana jiranki kukuma kuzo mutafi" Maryam tayi saurin shugewa gaban motar Yaya habibu Aysha tayi narai-narai da fuska.


"Maryam bazaki zauna ba? Naɗauka anan zaki kwana"


"A'a ba'anan zan ƙwana ba"


"Dan Allah to ki zauna idan dare yayi sosai saimu maidaki" Ta girgiza kai.


"Ni bama gida zanje ba zanje najira Dawowar Marmeeyy ne dan yau kona koma gida ban iya bacci" data sake magana Hamma ya amshe.


"Barta taje gobe dasafe saita dawo yanzu idanba tafiya tayiba hankalinta bazai ƙwanta ba" bahaka taso ba dan taso tazauna akan zasu kaita daga nan saita langwaɓe tace batada lafiya su ƙwana agidan tare. Maryam ta kalli Hamma ya ɓalla mata Harara dan haushinta yakeji tasan da faruwar duka wannan lamarin bata taɓa faɗa masa ba har lamarin yakaiga haka? Tabbas sai yayi mata hukuncin wannan abun dan lamarin ya ɓata masa rai ƙwarai da gaske. Yanzu dayasan akwao wani wanda yake bibiyarta har zai zauna tayita juyashi tace kar yaje yasamu iyayenta kuma yayarda? Da yasan da hakan toda yanzu wani zancen akeyi ba wanann ba.


Ɗayar budurwarnan sai hararar Maryam takeyi ga haushib maganganunda ta yaɓa mata gakuma shiga wajan Yaya Habibu da tayi ayau takeso komai ya daidaita a tsakaninsu. Kama murfin motar tayi ta gallawa maryam harara.


"Nan waje nane anan nazo saiki fita ki koma wajan ƙawarki data bari" hararar data mata Maryam ta rama. Motar kuma motar saurayinane dole ne zauna ayanda naga dama.


Ya Ahmad baibi takansu ba ya tada motarsa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads