Showing 45001 words to 48000 words out of 171869 words
Chapter 16 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
amsa duk wannan maganar da sukayi gabaki ɗaya da larabci suke yinta har suka gama."
---------
ƙwana biyu da dawowarsa amma gabaki ɗaya hankalinsa yana can yana tattare da ita yasaba zama shi kaɗai batareda kaɗaici ya dameshi ba amma wannan karon yana matuƙar jin kaɗaici duk da haka yasaba rayuwarsa amma wannan karon yanajin kaɗaicin na daban kamar bai taɓa rayuwa ahaka ba.
Duk da kasancewarsa bamai magana amma har ma'aikatansa sun fuskanci sauyin yanayi atattare dashi.
sati biyu jall yayi da da dawowa daga wajanta amma ji yakeyi kamar wanda yayi watanni bai ganta ba. P.A dake shine Wanda yasan komai nasa Shi kaɗai yasan dalilin canjawarsa.
Zaune suke shida sectery nasa na wajan aiki yagama shirya masa duk wasu shedule ɗinda yake dasu a month mai zuwa wajan aiki. Yagama sanardashi schedule ɗinsa na washe gari yayi masa sallama yafice zuwa nasa office ɗin. Sai lokacin P.A yashigo tunda dama shi duk wani abunda yashafi personal life ɗinsa shine akai. Ya zauna kujerarda suke facing ɗin juna. Mood yace.
"Akwai wani abunne? Dan yasan kusan duk lokacin daya shigo ya sameshi a lokacin aiki akwai abunda yake tafe dashi. Saaida ya matso kusa yayi ƙasa-ƙasa da murya kamar akwai wanda yake jiyosu sannan yace.
"Mood sir you miss her right?"
"Uhumm kawai yafaɗa."
Duk wanda yasanka a baya yasanka yanzu yasan ka canja. Bayan gama schedule ɗinka na wannan month ɗin lets go met her. You've been lonly for half of your life. Met her talk to her express your feelings. Komai zaizo dai-dai, Mood wanda dama a ƙage yake da maganar yace.
"Kana kallon hakanne mafita. I"ve been lonely tsawon lokaci and hakan bai dameni ba yanzu dana ɗaura idanuwana akanta hakan ya dameni sosai kullum ina azabtuwa a cikin zuciyata inaji kamar bntaɓa rayuwa irin haka ba" P.A yace.
"Nima nasanka tsawon lokaci mai tsayi amma bantaɓa kallonka a irin haka ba. Zan iya cewa nafi kowa saninka dukda ba halayanka duka nasani ba. Abubuwa dayawa da suka shafeka kabarwa kanka kai kaɗai. wanda kai kaɗai kake sharing abunda ya sameka yanzu lokaci yayi da kaima zaka sauƙewa kanka nauyin duk wata rayuwarka. kasamu wacce zata tayka ɗauka karkaji komai ka tunkareta da zuciya ɗaya komai zaiyi dai-dai. rayuwarka tana cike da soyayya takowani fanni wanda bakowane mahaluki zai samu makamancinta a rayuwarsa ba amma kaƙi budewa wannan soyayya ƙofar data dace wanda zata baka farin ciki maras mislatuwa. Atunaninka Rayuwarka cike take da farin ciki. Amma lamarin gaskiya kai kaɗai kake sharing kayanka da ace zaka bada wata ƙofar da zakuyi sharing farin ciki tareda wasu mutannen da zaka fahimci cewa kasamu asalin farin cikin daya dace wanda kakeyi a baya sam ba farin ciki bane" Mood yaja numfashi yayi murmushi kawai yakasa cewa komai dan yaji ƙamshin gaskiya a maganarda P.A yake faɗa. A idon duniya rayuwarsa cike take da soyayya amma a zahirin gaskiya yana buƙatar soyayayya wacce zata canja masa rayuwarsu izuwa wani yanayin daban. Ya koma ya jingunu da kujera ya lumshe idanuwansa kawai yana hasasho yaushe zai shiga rayuwarda yafara mafarkinta a ɗan fara soyyayarsa wanda abaya bai taɓa mafarkin shigarsa wannan yanayinba."
Wayarshi dake kan ɗan table tafara ruri yasan dole na gidane yake kiransa. A kasalance ya buɗe idanuwansa ya kalli wayar yaga Nawrah. Maida kansa yayi batareda yayi picking ba ganin haka ya tabbatarwa مساعد شخصي (P.A) bayason ɗaga kiran dan haka baiyi tunanin ɗauka ya miƙa masa ba.
Ba'a sake kiran wayar ba 5minute later yaji an buɗe ƙofar office ɗin yana buɗe idanuwansa a fili yace.
"Nawrah" Ta ƙafaso ciki مساعد شخصي(P.A) yana ganin shigowarta yatashi yafice a office ɗin."
ZAYNAB ALABURA.
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
P.A yayi mata barka da zuwa ta amsa sannan ya fita itakuma ta ƙarasa ciki ta zauna. Kallo take masa mai cikeda tuhuma ya sakar mata murmushi haɗeda faɗin.
"مرحباً حبيتي "
"Welcome My love). ta ɓata rai sosai sannan tace.
"Kana kallon kirana kaƙi ɗagawa" ya girgza kai yace.
"Ina aikine shiyasa" cikeda Shagwaɓa irinta mai neman rikici tace.
"Mood Habibi wani aikine haka yafi kiranda nake maka? Kawai bakason muyi magana ne dan Mum takirani ta sanarda ni. inaso naji bayani daga bakinka shiyasa nazo. Wai dagaske tafiyarda kayi just recently shine kaje neman aure? Dan Allah kacemin da wasane please" ya furzarda iska sannan yace.
"Bada wasa bane"
"Amma mood Habibi tayaya zaka auri ƴar africa? Wacce bata sanu aduniya ba? Koda tasanu a duniya ita na sa'ar aurenka bace"
"Babu ruwanku da matarda zan aura ni zan zauna da ita dan tayimin hakan kuma inasonta babu wanda zai hanani aurenta" cikeda Mamaki tace.
"Ka manta mu suwaye? Ka manta danginda muka fito? And kai kanka kamanta kai waye? You're Hammood mansour Kaine Celebraty na ɗaya akaff duniya abun kunyarda zaka jamana kenan? Mutumci zaka zubar mana" Ya runtse idanuwansa Bayason mata tsawa amma tabbas tana shiga huruminda ba nata ba. Ya buɗe idanuwansa akanta. Kamanninsu ɗaya sak dashi ko ba'a faɗa ba ansan ƙanwarsa ce.
"Nawrah" ya kira sunanta. Da mamaki ta maimait.
"Nawrah? Nawrah fa kace?" ya ɓata rai yace.
"Ehem" cikeda ɓacin rai tace.
"Mood Habibi yanzu akan wata can zaka kira sunana? Ka zaɓi sonta fiyeda mu kenan? Asiri tayi maka?. Ya ɓata rai sosai yace.
"Stop it Nawrah karki aibantamin soyayya ta"
"Nawrah" tasake maimaitawa al'ajabi yaƙi barinta Mood mai masifar sanyin rai da tausasan kalamai yau shine yake kiran sunanta bada laffuza masu daɗi ba? Kuma adalilin mace wacce batada wani amfani a rayuwarsa gabaki ɗaya. Saida ya runtse idanuwansa ya furzarda iska ya buɗesu sannan yace.
"Asif Habibty. but kidaina aibantata. Tanada hankali da nutsuwa sannan ina sonta sosai bazan lamunci ki aibantamin itaba bazan iya ɗauka ba"
"Wacece ita? Inaso nasan waccece let me talk to her ko nawa takeso zan bata saboda tarabu dakai. kai ba ajinta bane" ya jijjiga kai haɗeda faɗin.
"kuɗinki su huta She has a multi billionaire husband Therefore yours is nothing"
"Husband" tayi exclaiming.
"Uhum" yafaɗa cikeda jaddadawa.
"Kanabin bayan ta akan sistanka da mahaifiyarka."
"Ko ɗaya kawai ina ƙoƙarin ajiye kowa a mazauninsa ne"
"Okay toh inaso nasan waccece ita."
"لا (No) zaki santa alokacinda na kawota gidana" Yana magana cikeda rashin damuwa a fuskarsa amma can cikin ransa yanajin damuwar rashin karɓan zaɓinsa da ƴan uwan nasa sukayi"
"Mood Habibi" ta kirashi ya ɗago ya kalleta tace.
"bazaka janye maganar auren yarinyar nan ba?" Yayi noding head alamun tabbatarwa.
"Zan saka maka pressure da kai kanka sai kaji zaka janyewa maganar"
"Okay" kawai yace. Aransa yanaji ba pressure ba komai zaka saka sai dai tasaka amma bazai iya janyewa ba. Shi tun kafin ya tunkari wannan lamari saida yagama tsayarda zuciyarsa waje ɗaya yayi shirin tunkar koma menene zai biyo baya. Nawrah dama ya shiryawa rikicinta dan bayau Mum tasaba ba duk lokacinda takeso yayi wani abin kowa bar wani abun nawrah take aikowa ta saka masa pressure har saiya amince ko ya janye amma banda
Akan soyayyarsa sa sam bazai ɗauki hakanba daga wajan koma waye.
Cikeda baƙin cikin ƙin amince da ƙudirinta da yayi ta miƙe tace.
"I hate her " ya taɓe baki sannan yace.
"Dama dame soyayyarki zata amfanarda ita? Tunda ni ina sonta hakan yayi"
"Mooda Habibi ka sani zannemota kuma zansan waccece ita zatasan tashiga abunda yafi ƙarfinta" Ya haɗe rai sosai yace.
"Idan kika taɓata zakiga ɓacin raina kuma zan iya yanke alaƙarda take tsakaninmu" cikeda tsoro take kallonsa taga fuskarsa babu alamun wasa saima ɓacin rai kuma tasan halinsa tsaff zai iya yanketa. Muryatta na rawa na tsoron abunda yafaɗa tace.
"Mood Habibi nice fa 1 and only sisternka. Ya jijjiga mata kai alamun tabbatarwa yace.
"Itama itace kaɗai soyayyata, ki amince da ita idan kinso" Tajuya tafice cike da ɓacin rai. Tana tunani lallai wannan yarinya ba ƙaramin shiri tayi akan mood ba taji ta tsaneta tsana mai matuƙa bazata taɓa saurarawa duk wani wanda zai shiga tsakaninta da ɗan uwanta ba. Kuma dole saita rabasu ta nemo masa macenda tadace da ajinsa.
Ta fice tasamu P.A. Babu yanda batayi ba yafaɗa mata yanda yarinyar take amma yaƙi dan haka kai tsaye tawuce cikin gidan mood. Daga office bai dawo gida kai tsaye ba yafita yadawo bayan magrib ya sameta da mamaki yake tambayarta abunda tazauna yi danya ɗauka tatafi. Tace taɗauki hutu zata ƙwana masa biyu. ta nuna masa komai yawuce ta yarda da zaɓinsa ya yarda da ita sosai dan yasan halinta kamar yanda yakeyin abunda takeso haka itama takebin abunda yakeso abunda bai saniba shine ƙwantan ɓauna tayi masa. ta ɗaura niyyar rabashi da yarinyar nan takowani irin hali."
sai bayan 2week ya shirya tafiya ganin mahaifinsa yanada match in 2weeks time sai bayan ya bugata sannan zai tafi dan haka suka shirya cewa idan yatashi tafiya zasu tafi tare da Nawrah."
---------------
fitowarmu daga test kenan gabaki ɗayanmu muna zaune maryam tace.
"Babe har yanzu baki faɗawa baban bafa gashi time sai tafiya yakeyi"
"Bani nace miki zan faɗa masa ba? Kina zamanki zakiji abba yayi miki magana tace
"shikenan" fadeelah wacce yanzu ta maƙale mana ko ina zamu cikin school da ita sai taje tace.
"Me za'a faɗawa Baban? Maganar aurenku da Hamma ne?" Dan Allah karkuyi gaggawa har yanzu ban fidda ran cewa nice zan auri Hamma ba" naja tsaki sosai dan maganarta ta ɓatamin rai ban kulata ba tacigaba da faɗin.
" kece fa kikayimin shigar sauri yanda kika naniƙewa maryam har ta haɗaku da yayanta danni har yanzu ban yarda cewa ba ita haɗaku ba" Maryam ma ta ɓata rai tace.
"wani iskancine haka fadeelah? Toh banice na haɗasu ba kuma na faɗa miki tun ba yau ba sannan ba Marmeeyy ta naniƙemin ba nice na naniƙe mata saboda abubuwa da dama. Tsawon lokaci muka haɗuda ita kafin muka haɗu dake. Tun muna islamiyya tana A ina B har mukazo hadda tare anan muka sana daganan muka yanke shawarar shiga nursing school tare kowacce ta faɗawa iyayenta suka amince. Sannan ta daɗe sanin Hamma bata taɓa nuna interest ɗinta akansa ba har saida ya ganta yace yanaso dakansa sannan ta amince masa ina marta bata ta wannan fannin babu ruwanta da kowaye mutum ko gidan bukka kuke dashi wallh marmeeyy idan tana sonka tana sonka tsakani da Allah kuma yanzuma zancemda mukeyi inaso nakoma gidansu da zama har mugama exam ɗin wannan lokacin"
Ganin ran maryam ya ɓaci sosai ya sanya Fadeelah ta maida abun wasa tana faɗin.
"ke da'allah wasa nakeyi fa" Maryam tace.
"Nidai na faɗa miki" Inajinsu ko tankawa banyiba saboda banda abunda zance. Lacturer muke zaune muna jira har lokacin bai isoba dama shi kaɗai muke dashi ganin bai zoba ya sanya muka haɗa chapter munata hira acikin friends ɗinmu akwai maison wasan ƙwallo kamana dan haka muka ware mu biyu muna hirar ball muna zancen match ɗinda za'a fara bugawa next week. Tacemin.
"kinsan Hammood yazo ƙasarnan kwanaki?" Nace.
"Nasan zuwansa aiya haukata mana ƙasa gabaki ɗaya ya rikita gidan radio da gidajen TV" ina faɗi cikeda murna da nishaɗi.
"Hmm bawan Allahn nan yayi kinji. Wanda suka ganshi sunce Afili yafi komai yakafawa duniya tarihinda baza'a mance dashiba at his young age yakafa tarihi a wasan ƙwallo" taciro wayarta tana nunamim pics ɗinsa ina following ɗinsa amma bantaɓa ajiye pics ɗinsa ko ɗaya a wayata ba wani irin kyau yake dashi mai masifar hankali. Kyawunsa bai kama kainaba sam gani nake kamar wani aljani barni dai na kalli wasansa dan har shagala nakeyi
Idan ina kallon wasansa. Ɗaya daga cikin friends ɗinmu da muke zaune tana jiyomu tasako baki tace.
"Ƴan wahala wannan mutumin kuna ɓatawa kanku lokaci akansa wallh manya manyan celebraties sunyi sun gashi akwai wata mawaƙiya and tana film ɗin turawa ta mace a soyayyyarsa amma baisan tanayi ba million dollars take biya tashiga ganin wansansa kowani pics ta ɗaura sai tayi tagging ɗinsa. Ke kinsan celebreaties nawa suke hauka akansa?" nayi dariya nace.
ke da'allah ɗaiɗaiku cikin ƴan wasan ƙwallo ke auren celebraties Yawanci matansu basu sanu a duniya ba zakice na faɗa miki matarda zai aura babu wanda ya santa" tace.
"Da wuya fa ke Hmm ai ana show akan yagennan mukam ai sai ƴan kallo a insta muna dariya iya namu likes da comment comment ɗinma marassa amfani dan babu wanda zai dubasu" Nace.
ZAYNAB ALABURA
*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.
" kinganni banida lokacin comment akan abun celeberaties toh me yayi zafi? Iyakacina like idanba sa'a ba harna mutu bazanga ko ɗaya cikinsu ba"
"Haba zainab yada cire rai haka?" Nace.
"Ke rabani na riƙe Hamma na hannu bibbiyu shine babban celebrity na wanda banda kamarsa ke ni ko wannan Hammood da ake ganin kyawunsa kamar hauka ni awajena bai kaimin Hammana ba" Daga wajanda maryam take taja tsaki tace.
"Dama mana yaushe zai kai miki shi? Kowa yana amfani da abunda yake hannunsa kenan amma kika sake haɗasu Allah ya isama Hammood" Cikeda ɓacin rai nace.
"Kekam dai anyi banza wallh waya keƙin nasa?" Saida tayi dariya ganin ta cikani sosai tace.
"Ai gaskiya ce zaki haɗa ɗan larabawa da ɗan fulani" nace.
"Kaman a kunnen Hamma"
"Kifaɗa mana yau kika saba min sharri Shima kansa idan yaji zai yaji kunyar abunda kikayi" takaici yasa nadaina kulata kota sakoni cikin zance bazan mayar matada amsa ba.
Muna zaune kusan 2hours lacturer yayi waya akan bazai samu zuwa ba bamuji haushi ba danma mun zauna munyi hirarmu abunmu mungode Allah dan haka na miƙe nace.
"idan kinga dama kizo mutafi" tasan da ita nake tace
"bantashi sai Hamma yazo"
"aidai kya barshi yahuta ko? Tunda shi baɗan aiki bane" ta taɓe baki tace.
"Aishi ya maida kansa driver dan haka yacika ladansa" nace.
"ke dai na daɗe banga ƴar rainin hankali kamanki ba wai Hamma ne driver" Nakoma ma zauna ban kirashi amma Ita ta kirashi"
Kusan 40minute sai gashi ya iso.
Tare muka fita dukanmu kowa yakama gabansa maryam tace fadeela tazo mutafi saboda hanyarmu yazo ɗaya samu sauƙeta a hanya. hakan akayi fa biyomu muna tafiya muna hira ƙasa-ƙasa nida Hamma. Maryam tace.
"Hamma kaji babe wai kar akiraka yau abarka ka halan yau batason ganinka ne" Ya kalleni na ɓalla mata harara yace.
"Wai haka babynah bakyason ganina? Nayi narai-narai nace.
"Hamma ka yarda kenan? Yarinyar nan ƙarya takeyi cewa nayi fa banason ka walaha yau ka huta shine ta juya maganar"
"Baby wani hutu zan samu batareda na ganki ba? Ai ganinki shine samun hutuna karki damu koda yaushe kikeson samamin hutu ki kirani nazo naganki kawai wannan shine babban kwanciyar hankalina" Nace.
"Toh in sha Allahu Hammana" maryam ta gefe ta kallon reaction na fadeelah dama ta jawota ne dan tasan dole Hamma zaiyi abunda zai ƙure mata tunani dataji muna hira ƙasa-ƙasa kawai saita sako wannan zancen dan tasan dole zai yi maganarda zata maido da fadeelah hankalinta. Kamar ƙwai haka yayita lallaɓina muna tafiya hankali har suka kawoni gida ahakanma Saida muka tsaya mukayi hira sannan nayi musu sallama nafice.
Ina shiga gida da kusan 30minute saiga kiran Maryam ina picking dariyarta nafara ji tana faɗin.
"Babe ya kikaga idon fadeelah nayi hakane kawai dan tasan matsayinta wallh yarinyar nan ƴar rainin hankali ce saita faɗi magana saita wani waske tace wai wasa takeyi kuma bafa wasan takeyi ba kawai dai taga rai yaɓacine Allah natuba mai Hamma zaiyi da ita?" Dariyar nima nakeyi nace.
" kedai bakida dama wallh da tasan waye Hamma dama bata fara wannan haukar ba na tabbata da Hamma yasam cewa yarinyar nan tafaɗi abunda tafaɗa da saiya tsayar mata Wallh Hamma baya ɗaukan rainin hankali" Maryame tace.
"Batta yanzu zata shiga hankalinta tasan sonki yake na gaskiya bawai cusa masa kai akeyi ba"
Mun daɗe muna waya da ita sannan Mukayi sallama."
Har tsawon sati biyu banyiwa Baba maganar maryam ba tayimin magana harta gaji tayi fushi ta sauƙo dan tace banida niyyar tambaya mata Baba ne taga alamun banaso tazo gidansu.
A yau na yanke shawarar samun Baba amma saina fara samun Mama nayi mata magana Anty fadeelah tana wajan aysha kuma ta school. Dana gma yiwa Mama bayani Anty fadeelah tafara amsawa.
"Lallai marmeeyy bakida kirki duk yanda maryam ke sonki kawai ta tambayeki ta zauna agidanku na ƴan satikai amma kiƙi? Ai ana rama hallaci da hallacine" mama tace.
"Barta ni banga abun tsayawa tunani ba dahar zataƙi tambaya ba yarintar nan dai iya kyautatawa tanayi miki amma" Nace.
"Mama dan Allah ki tambayeshi"
"A'a-A'a jeki tambayeshi da da kanki da kinso tazauna aida tun wuri kin faɗamin na tambaya miki shi amma yanzu da lokaci ya ƙure kejiyi da kanki" Nayi fuskar tausayi sannan nace.
"shikenan bayan isha'i zan shiga nafaɗa masa Allah yasa yayarda" mama tace.
'Amin" Bayan yadawo daga sallar isha'i nashiga wajansa nasamu alokacin za'a fara haska wasan ƙwallon ƙafa nazauna muma kallo cikeda sha'awa nake kallon yanda Hammood yake sarrafa ƙwallon Baba ma yazauna ya nutsu yana kallo kamar mai nazarin wani abu. Bantaɓa kallonsa ya nutsu haka wajan kallon ball ba kamar yanda yayi yanzu Muna zaune har aka gama sannan Baba yadawo da hankalinsa gareni dake mun kwana biyu bamu samu zama irin haka ba. Yace.
"Marmeeyy Ball tayi daɗi koh?" nace.
"tayi sosaima kuwa Baba Hammood kwarrarrene wajan sarrafa ƙwallo" Baba ya jijjiga kai cikeda gamsuwa da abunda na faɗa. yace.
"Tabbas yana da ƙwarewa. Yana burgeki kenan? Yayi maganar in