Showing 66001 words to 69000 words out of 171869 words
Chapter 23 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
da dare za'a tafi mai makeup dakanta zatazo tayi mana. Ana sallar isha'i muka fara shiryawa dama su Anty fadeelah kam ta rigada tafara shiri har anyi mata kwalliya dake ita ba sallah zatayi ba."
"Hammood
ZAYNAB ALABURA
Assalamu alaikum barkanmu da sallah fatan munyi sallah lpy Allah ya karɓi ibada ya amsa mana addu'oinmu. Mun dawo hutun sallah in in sha Allahu zamu daura daga yanda muka tsaya.
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Gabaki ɗaya ma'aikatansa saida suka fahimci irin yanayi najin daɗi dakuma farin ciki da Hammood yake ciki basu taɓa ganinsa a yanayi makamancin wannan ba lokaci-lokaci yake sakin murmushi mai sauti akasin yanayinsa da abune mawuyaci kaji saurin murmushinsa koda yayi sai dai kawai ya motsa lips ɗinsa idan zaiyi murmushin. P.A wanda shi kaɗai yasan abinda ya faru yana sakin murmushi shima yake tayashi yasaki nasa murmushin.
Yau yashirya zuwa yaganta daga nan kuma zaibar ƙasar wayewar asubahin washe garin ranar dayake yanada abubuwan da zaiyi a satin dayawa.
Idan yatuna zai ganta sai ya tsinci kansa yanayin daɗi dakuma fargaba aduk lokacinda zai haɗu da ita irin yanayinda yake tsintar kansa ciki kenan. Shi kaɗaine zaune a ɗakin yayi nisa cikin tunani ƙarar wayarsa tadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula. Ya furzarda iska sannan yadubi wayar Sunan mahaifiyarsa ya bayyana akan wayar. Har tayi tagama bai amsa ba tun jiya daga ita har nawrah babu abunda sukeyi sai aikin kiransa shikuma yaƙi picking idan suka gaji da kira bai ɗaga ba daganan sai su fara kiran P.A Babu yanda basuyi ba amma P.A yaƙi basu cikekkiyar ko gamshesshiyar amsar tambayarsu. Shima kansa yagaji da amsa kiransu da yanada yanda zaiyi bazai amsa ba amma babu halin yaƙi ɗaga wayar kamar yanda Mood yakeyi sai dai koda ya amsa babu wani bayaninda suke samu.
Bayan wayar tagama ringing dakamar 9minute P.A yayi knocking a hankali. Ogannasa yabashi umarnin shigowa. Sai da ya saka katinsa ƙofar ta buɗe sannna ya murɗa yashiga. Ya ƙarasa har yanda Mood yake sannan ya tsaya. Mood ya ɗago ya kalleshi dan yasan magana zaiyi. Ganin haka yasa P.A yafara magana cikin harshen larabci.
"Mood sir baka ganin yakamata a sanarwa Mummynka da ƴar uwarka wannan maganar? Sun damu sunataso susan gaskiyar lamarin akan abunda yaketa yawo" Mood ya miƙe tsaye yafara tafiya sannan yayi magana.
"idan ina buƙatar sanar dasu zan faɗa musu da kaina yanzu get ready it's almost time for isha'i" P.A yagane abunda yake nufi dan haka yayi masa sallama yafita shikuma ya nufi toilet yadaɗe sosai a ciki kamar yanda yasaba sai da aka fara kirayen kirayen sallar isha'i sannan yafito ya shirya sannan ya tara gabaki ɗaya ma'aikatansa sukayi sallah sannan suka zauna dinner bai wani ci abincin sosai ba dan zumuɗi dayakeji tun jiya bai samu yaci abinci sosai kamar yanda yasaba ba saiya zauna sai yaji gabaki ɗaya murna da farin ciki sun cika masa ciki. Zama yayi wani ɗan lokaci baya jimawa yake duba agogo yagani ko time yayi. gani yakeyi kamar lokacinma yaƙi tafiya. Idan yaɗan duba time saiya saki ajiyar zuciya yana ɗan jijjiga ƙafa."
-------
Sai wajan 9:00pm muka gama shiryawa lokacin har anfara tafiya Amarya da angone kawai basu tafiba Munyi kyau sosai. cikin laces mai ɗan karan tsada da Mummy tasaka aka ɗinka mana mu mukayi anko.
Alokacinda muka fito lokacin angama yiwa amarya tata kwalliyar itama tayi kyau sosai an jejjera motoci ana jiran fitowar sauran masu tafiya.
A harabar gidan muka samu su Yah Ahmad yasha babbar riga yayi kyau sosai sunyi anko da amaryarsa. Muna isa dai-dai wajansu abokinsa yana ƙarasowa ya dubi Ya Ahmad yace.
"ku hanzarta mana lokaci fa yana wucewa ga motoci duka sun taru ku kawai ake jiran"
"Okay toh muje koh?" shine abunda Ya Ahamd yafaɗi. Yafara tafiya zuwa wajan motarda zasu shiga. Abokinsa yace.
"Ba wancan motar bace taku?" yafaɗa haɗeda yin pointing wata mota datake ɗan gefe kaɗan. Gabaki ɗaya motocin wajan masu tsada ne wanda ake yayinsu amma wancan dabance duk ciki babu wacce takamo ƙafarta. Ya Ahmad yaɗan dakata sannan yace.
"Au kaga na manta" sai yajuyo yakallemu yace"
"Marmeeyy kushiga wancan motar kutafi yafaɗa yana nuna mana motar dake can gefe. abokinsa yace.
"Dakata mana malam. Kamar bakasan yanda tsarinmu yakeba? Aƙa'ida amarya da ango suke shiga motarda tafi kowacce ko kamanta ne?" Ya Ahamd yayi murmushi sannan yace.
"Mutumina kar kaja magana kaga lokaci na tafiya." sannan yajiyo ya kallemu yace.
"Kuwuce kutafi"kamar wanda yatuna wani abun yayi saurin faɗin marmeeyy dawonan dasauri najiyo ya ɓata fuska yafara faɗin.
"Wato ke bakyajin magana koh? Wuce ki ɗauko mayafinki. Nayi narai-narai zanyi kuka yace.
"Wallh koki wuce koki fasa zuwa" na juya nadubesu dukansu babu mai gyale har amaryarsa bata saka gyale ba sai dai kawai yanayin ɗinkinta na amare ne amma ai itama da saiyace tasaka gyalen. Abokinsa yace.
"Haba mutumina na yau kaɗai dai kabar yarinyar nan na sake kana takurata wallh"
tsaki yaja nikuma ban kula ba na juya nafara tafiya idona tacika tamm da hawaye kaɗan nake jira na fashe da kuka. ina shiga na nemi waje na zauna banason hawayen ya sauƙo dan karya ɓatamin kwalliyata dan haka na riƙe hawayena na zauna kawai inaji kamar nafasa zuwa event ɗin gabaki ɗaya.
Ganin natafi naƙi dawowa ya sanya Maryam tabiyo bayana. Bayan tabar wajan Aysha ta dubi Ya Ahmad tace.
"Ya Ahamd ko a fili baka iya ɓoye bambamcin da kake nunawa tsakaninmu da Marmeeyy mune muka fito ciki ɗaya dakai amma kafi nuna kulawa akanta. Mu koyaya zamu fita baka damuba amma ita bazata fita ko yaya ba dan ita ta musammance kowa yafi sonta. Koda yake ba abun Mamaki bane tunda mummynmu uwarda ta haifemu tafi nuna mata kualawa dan kai kayi haka bai kamata muyi mamaki ba." Anty fadeelah tana ƙwabarta amma saida ta ƙarasa abunda take faɗa tana gamawa tabar wajan fuuu. Murmushi kawai ya Ahmad yayi. Anty fadeelah tace.
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Bafa murmushi zakayi ba kana gani yanda ranta ya ɓaci.
"ita waccar nayi mata faɗa akan mayafi ranta yaɓaci tana ganin kamar na takurata bana sonta ita kuma wannan banyi mata faɗaba tana ganin kamar ban damu da itaba me zanyi idanba murmushin fadeela?" anty fadeelah tace.
"abunda ta faɗa gaskiyane ai dukanmu ya kamata kayiwa faɗa mu canja ba marmeeyy ita kaɗaiba. Hakan yana nuna matsayin marmeeyy daban yake da namu. Ko kafi sonta kokuma mu kafi sonmu shiyasa baka takuramu. Amma idan akayi duba da yanda marmeeyy ke mu'amalantar mutane zan iya cewa kafi sonta. Dannima anawa wajan hakanne"
Ya kalleta da tambayar me nata wajan hakan yake nufi. Bai kaiga samun cikekken tunani ba abokinsa yasake faɗin.
"Kabar amaryarka a tsaye ga dukkan alamu tagaji kabar yarannan abar musu mota ɗaya su biyomu abaya" badan yasoba suka wuce suka barmu nida Maryam zallah dan Anty fadeelah tabisu
aysha kanma baisan yanda tayi ba.
Sai da nayi iya ƙoƙarina wajan hana hawayena zuba dan tabbas zai ɓatamin ƙwalliyata. Ahaka maryam tashigo ta sameni ta ƙarasa kujerar da zauna tana faɗin.
"Babe kefa ake jira kokin fasa tafiya ne?"
Na kalleta da zan iya zuciya danace nafasa tafiyar amma bazan iyaba banida wannan ƙarfin halin.
"Allah babe takurin ya Ahmad yakemin yayi yawa sai nakeji kamar nafasa zuwan kigafa kowa wajan babu mayafi amma haka yamatsa wai saina saka mayafi ko matarsa bata dashi gasu anty fadeelah da aysha nanma duk babu ni kaɗai kawai zaice nasaka"
"Babe nifa gani nakeyi kamar yafi sonki ne akan sauran yasa yake haka kokuma kinfi jin maganarsa kinsan fa kowa yana gadara da abunda yake iko dashine ni aganina karki saka wannan aranki" nayi murmushi sannan nace.
"Duk da haka fa wannan ba hujja bane muduka ƙannensa ne sai yayi hukunci ma kowacce a cikinmu"
"Nidai babe tashi mutafi kinsanfa bazasu zauna jiranmu ba idan kuma kinaso ayi babu mu toh" namiƙe nace barina ɗauko mayafi.
"ki ɗauko mana tare" tafaɗa nashige ciki sannan nadawo hannuna ɗauke da mayafai ƴan ƙananu muka yafa muka fice. Ango da abokanansa gabaki ɗaya suntafi saura wancan motarda ya Ahamd yace mushiga ɗazu. Kai tsaye wajanta muka wuce. Kafin mu isa motar aka buɗe ƙofa dasauri ya buɗe mana ƙofar baya cikeda girmamawa. Batareda mun lurada kamannin wanda ya buɗe ɗinba muka shige muna shiga yarufe sannan yashiga driver ya tada muka tafi. CHIDA EVENT CENTER shine wajanda muka nufa wajene ƙayatacce mai kyawun gaske. Harabar wajan kamar ba dare ba saboda yanda hasken fitula ya haske ko'ina. Tun daga wajema abun kallo ne izuwa ciki yanda akayiwa wajan decoration mai masifar ɗaukan hankali. Kyawun wajan ya ƙarawa mutane wajan kyau duk da cewa kana kallon mutanneda suke wajan za'asan bikin ƴaƴan manya ne.
kafin mu ƙaraso faɗa sosai Mummy taketa yiwa su anty fadeelah da aysha akan meyasa zasu tafi su barni bayan ni baƙuwace babu yanda nasani alokacin tasaka Anty fadeelah kirani saboda ita batada contact ɗina. Dayake ina kallosu yasa ban amsa ba na ƙarasa wajan. Ina zuwa aysha taja tsaki tabar wajan banɗauka dani takeyi ba nasan dai muna yawan haurawa amma yanzu ai babu abunda ya haɗamu dan haka na wuce wajan Mummy.
"Hankalina yatashi marmeeyy anbarku agida can bayan bakusan waje ba Ahmad bansan wane irin abun yakeyi hakaba sa'arsa ɗaya kun iso yanzu da saina ƙarasa har gaban amaryarsan naci ƙaniyarsa. Murmushi kawai nayi ta miƙa mana bandir na kuɗi nawa daban ta miƙawa maryam nata daban tace muyiwa ango da amarya liƙi. Natsaya ina kallon ikon Allah ko Baba samun irin wannan kuɗi wahala yake masa amma nan gashi an damƙa mana shi wai muyi liƙi. Can gefe danaga su aysha suna zaune muka ƙarasa amma sai naga ta kauda kanta dama suna zaune da sauran ƴan matanne sa'anninmu suma kamar wanda tafaɗa musu wani abun sai naga sun kawarda kai harda masu jan tsaki. Haɗeda yimana wani kallon ƙasƙanci. yanayin shigarmu da tasu iri ɗaya ce ganin irin kallonda muke mana yasa naja hannun maryam muka bar wajan muka zauna gefe Daga yanda muke zaune muna iya kallon yanda ake wasa da kuɗi abun. Ashe duk wanda akayi abaya wasane yanzune ake liƙi abokanansa ma kamar wanda sukayi taru suka ajiye suna jiran zuwan lokacin bikin.
Muna zaune aka kira ƙannen ango naga ƴan mata sun tattashi cikeda masifar jida kansu suka isa aka fara liƙi bantashi ba hakama maryam har suka gama kwasar rawansu suka dawo. Kusan 30minute muna zaune a wajan hancina yafara jiyomin wannan ƙamshin turare mai masifaffen daɗi da sauƙarda nutsuwa wannan ƙamshin ya tsayamin araina da duk yanda najishi bana iya mantashi duk ɗaruruwan mutane masu aji da suke wajan cikeda ƙamshinsu saida wannan ƙamshi yafita daban. Ajiyar zuciya nasauƙe saboda yau naji mai irin ƙamshin hankalina ya ƙwanta. Ina zaune naji Mc yana kiran Hajiya marmeeyy yanason ganin Hajiya marmeeyy afili ban kawowa raina ni bace har saida yace ango yanason ganin ƙanwarsa Marmeeyy a fili. Kasa tashi nayi inata rabe raben idanuwa suka mutane sun zuba ido suna son ganin ta yanda zan fito. Saida maryam ta matsa sannan natashi amma ahakanma tareda ita babu yanda batayi nasake ta ba naki sai da mukazo daff shiga filin tajanye hannunta tayi baya da sauri. Najuya ina kallonta gashi babu halin na fita tunda na rigada na fito har an haske ni na ƙarasa har wajanda Ya Ahmad da amaryarsa suke tsaye ƙafata tana rawa saboda idon mutane dayake akaina. Ina shiga narasa abunda zanyi sai kawai nacire kuɗin nahau musu manni. Alokacin Mummy tafito itakuma tafaramin Manni fuskarta ɗauke da farin ciikin da ita kaɗai tasan ma'anarsa tun tafiyarsu Baba nake kallonta ahaka.
Ya Ahmad ma yaciro kuɗi yanamin manni gabaki ɗaya sai mannin yadawo kaina. Mc yana faɗin.
"Uhmmm Hajiya marmeeyy ƴar gata autar Mummy. Allah yanuna mana naki auren kema musha biki za'ayi kallo ranar bikin auta" Aysha daga yanda take kamar zata fashe dan baƙin ciki. Sai take ganin kamar wanda suke abun da gayya. Ya Ahmad kanma datayi masa magana ko ajikinsa ya sake sai liƙi yake yiwa marmeeyy wato babu alamun zai gyara kenan dukda tasaka haƙuri magantu. Taja tsaki yafi a irga.
Mummy takoma tazauna sannan ya Ahmad ya miƙamin key ɗin motarsa haɗeɗa faɗin.
ZAINAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
"Marmeeyy kuɗin wajena ya kusa ƙarewa kuma namanta sauran a mota amshi wannan key ɗin kifita harabar wajan ki danna key ɗin motar zatayi ƙara saiki buɗe ki ɗaukomin" yafaɗi haka bayan yamin kwtaancen yanda motar take. na amsa sannan Najuya nayi wajanda muka zaune banga maryam Ba. Nakira wayarta taƙi amsawa. Nasan tatafi wajan Yaya Habibu dan haka kawai na shareta dan koda zan mata kiran duniya bazata amsa ba. Da tafiya tsakanin Hall ɗin zuwa parking lot ɗin danshi yanda yayimin kwatance bama a ainihin main parking-lot ya ajiye motarba tayi ɗan gefe da wajan kaɗan. Kamar wanda aka share wajan babu kowa babu masu zirga-zirga. Bayan nafito ƙamshin ya sake bayyanamin ga dukkan alamu mai wannan ƙamshin ya gifta ta wajan alokacinda na isa wajan mota naji ƙamshin ya kusantoni dayawa dayawuce ace giftawa kawai akayi ta wajan. Da dukkan alamu mai ƙamshin yana zaune ne a wajan. Adaidai lokacin wutarda ke wajan ta ɗauke gabaki ɗaya tadawo dim haka na ciro wayata dasauri na kunna flash light ɗinta amma dake wayar taji jiki batama da haske sosai. Na isa gaban motar dasauri na buɗe aikuwa naga jakar kamar yanda yamin kwtance na ɗaukota dasauri dan nafara jin tsoro-tsoro. Jin alamun da mutum a kusa dani ya sanya nayi saurin jiyowa aikuwa nayi arba dashi a tsorace na cillar da wayar zan saka ƙara fahimtar hakan da yayi yasashi ƙarasowa da sauri banyi auneba sai ji nayi ya haɗeni da jikin motar haɗeda sanya tausassan hannunsa ya rufemin bakina ayayinda taushin hannunsa da ƙamshin jikinsa ya sanyani lumshe idanuwa sai inaji kamar wanda bacci zai ɗaukeni. A hankali na buɗe idanuwana akansa. Wajan akwai duhu sosai sai hasken farin wata daya hasko wajan amma ba sosai ba dake kamawar watan kenan baida haske sosai amma hakan hai hanani kallo cikin idanuwansa ba shima idon ya zubamin ina iya jiyo bugun zuciyarsa kamar yanda shima yake jiyo bugun nawa zuciyar gabaki ɗayanmu bamusan yanayinda muke ciki ba ni gabaki ɗaya natafi tunanine tunanin yanda nasan fuskar dukda duhu ya ɓoye kamannin amma sai inaji kamar na taɓa kallonsa. Abu ɗaya nakeda tabbaci shine mutuminda yake zuwa school ɗinmu amma fuskarsa a rufe da facemask a wancan lokacin. yanzu kuma akwai duhu sosai a wajan amma Koda ƙamshinsa zan ganeshi. Kuma ganinsa yanzu anan ya tabbatarmin da cewa shine baƙonda yake zuwa wajan Baba. Yanzu na yarda na tabbatarda shi kaɗaine mai wannan ƙamshin. Ko a wancan lokacin dana ganshi school ɗinmu jikina yabani da wata aƙasa amma ganin bai bani wata ƙofa dazan zargi wani abunba yasanya badan nasoba nasakawa raina wani abun daban ke kawoshi. ahankali na sanya hannuna nayi ƙoƙarin tureshi amma ko gizau baiyiba ganin haka yasa yaraba jikinsa da nawa yaɗanja baya kaɗan. Ajiyar zuciya mai sauti na sauƙe daya sakashi murmusawa dukda shima nasa numfashin yana bashi a wahala a wannan lokacin. Daƙyar na iya tattaro nutsuwata dasauri sauri nace.
"Waye kai? Bibiyata kakeyi nasani Danba wannan bane karo na farko dana ganka ba" duhune a wajan amma kallona yakeyi da rashin fahimta dan bai fahimci abunda nake faɗa ba. Iska ya furzar gabaki ɗaya komai ya ɗauke masa baisan abunda zaiyi ba. Dama shiyasa yake taraddadin haɗuwa da ita dan kalmarda zai furta mata ba baisanta ba. Ganin yatsaya yana kallona kamar statue yasa nima na tsaya ina kallonsa. Dafarko na tsorata amma yanzu sam tsoro yafice araina tunda nagane cewa shine mutumin can. Na tabbata baida niyyar cutar dani dan da yanada niyyar hakan daya daɗe da cutar dani.
Ganin ina kallonsa ya sanya yayi baya a hankali yasake shiga cikin duhu yanda alamun tsayuwars kawai zanna kallo dan yanada yaƙinin idan naganshi zan ganeshi, zan gane cewa Shine Hammood baisan kuma yanda ƙwaƙwalwata zata ɗauki lamarinba. Na gyara jinginuwata jikin Motar ina kallon ikon Allah abunma ni saiya fara bani dariya. saida naɗan dara kaɗan har lokacin kallona yakeyi baisan abunda yabani daeiya ba. Tsawon mintuna muna ahaka shiru naja ɗan siririn tsaki sannan nace.
"Idan bazakayi magana ba ni zan tafi" nafaɗa ina ƙoƙarin barin wajen. Dasauri yace.
"انتظر"
Kamar wanda ya tuno wani abun kuma sai yace.
"Ohhh please wait" alokacin daya ambaci kalmar na larabci na tsaya da saida gabana yafaɗi domin muryarsa batayi kamada wanda ya iya hausa ba. Tabbas wannan muryar ba tamu tanan bace kawai jikina yafara bani cewa shine wanda yake yimin text da kalmar larabci wani lokacin da turanci. Sai yanzu tunanina yake dawomin cewa wannan mutumin dayake zuwa makarantarmu ga dukkan alamu ba ɗan ƙasarnan bane. Idan kuma ɗan nan ne toh ruwa biyune dan abune mawuyaci acikinmu asamu mutum mai hasken fata kamar nasa. Nasauƙe ajiyar zuciya. Sannan a nima nace.
"Me zan tsaya namaka? Bazakayi maganaba? Bakuma zaka nunamin fuskarka ba. Inada abunda zanyi aciki" nafaɗa alokacinda nake ƙoƙarin sake barin waje. Bai hanani har saida nakusan barin wajan gabaki ɗaya zuciyata taƙi samun nutsuwa nasan idan natafi batareda wata ƙwaƙwaran bayani ba zanbar kaina cikin tunani. Iska ya furzar ya sunkuyarda kansa yanajin babu daɗi. Ko kalma ɗaya da zatazo bakinsa yayi mata magana ya nema yarasa.
Jin takun takalmina ya sanyashi ɗago kansa ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallona na dawo na harɗe hannayena a ƙirji ina kallonsa dukda ba iya