Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 171869 words

Chapter 14 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1070

Ads at the middle of Article

dakuma matsayinsa yasa dole wasu abubuwan suke saka bashi mamaki gabaki ɗaya ya canja Akan ƙaramar yarinya yarinyarda bawani kyau ko kuɗi ko suna gareta cikin celebraties na duniya baki ɗaya yana daga cikin wanda yafi sanuwa babu yanda zaije bai samu macenda yakeso ba kowace irin mace a halin yanzu sai dai ya sauƙe class ɗinsa ya aureta amma bawai danta kai ba aganinsu saboda status ɗinsa yawuce tsarar kowace mace amma sai gashi yabasu mamaki mamakinda basu kaɗai ba da duniya da zatasan da wannan lamari ita kanta zata jijjiga tashiha firgici numfashi ya furzar sannan sannan yace. g


"أنا متأكد جدا"
(am very sure)" Ajiyar zuciya ya sauƙe ya ɗauki facemask yasaka ya ɗauki glass yasaka sannan ya ɗauko Facing caff ya rufe fuskarsa gabaki ɗaya yanda babu wanda zai ganeshi.


Ƙarasawa yayi ya ɗebi wayoyinsa sannan ya ƙarasa yabuɗe masa ƙofa yafita gabaki ɗaya ɗakunan floor ɗin dayake an kamasu morethan 50rooms gabaki ɗaya aka kamesu saboda tsaro dakuma rashin son hayaniya. Harya fita cikin harabar mutane babu wanda ya ganeshi ya ƙarasa wajan motanda ake jiransa motoci biyune kacal wanda shi ya buƙaci hakan gabaki ɗayama ba'asanda shigowarsa garinba kusan kowa ya ɗauka yana abuja dayake dai kods yaushe idan zuwa abujan takama yakanje yadawo har ila yau babu wanda yasan dalilin daya kawoshi sai ƴan tsirarrun mutane gidan tv da jaridu sunyi tambaya harsun gaji har yau babu wanda yasamo musu amsa. Kuma abunda yake kan bawa mutane mamaki shine daɗewar dayayi aƙasar da bai taɓa yi awata ƙasa haka kawai bawani aikine yakaishi ba.
Atarihinsa ma gabaki ɗaya bai taɓa zuwa ƙasarba baida friends a ƙasar nigeria sai zallan fans da yake dasu wanda shi kansa yaji mamakin ganinsuba lokacinda ya sauƙa a ƙasar ya kasance yanada masoya masu tarin yawa haka a ƙasar.


Yanayin yanda motocin suke tafiya baza'a taɓa zaton tafiyarsu ɗaya ba yanabin duk wata hanya da zaibi dan ganin babu wanda yasan da zamansa a garin."




Fitowarmu daga lactures kenan cikina sai ƙugi yakeyi danko karyawa banyiba dake sassafe na shiga school jan hannun Maryam nayi muka nufi wani eatery dake cikin school ɗin tunda muka doshi wajan hancina yake jiyomin saƙon kamshin da ƙwana biyu nasaba da jinsa. a tunanina inajin ƙamshinne saboda shaƙarsa danayi ƙwana biyu dayawa wanda yanzu haka ya gama kama gidanmu barinma shashin Baba tunanina ya canja a lokacinda nasaka ƙafata cikin wajan saboda yanda ƙamshin ya tunkareni gadan-gadan ko shakka babu akwai baƙon Baba acikin wannan wajan kokuma wani mai irin ƙamshinsa. Waige-waige nafarayi mutane daban-daban zaune cikin wajan can idona ya tsaya akan wani dake zaune can gefe gabaki ɗaya cikin wajan shine wanda yayi suiting wannan ƙamshin. sanye da fara jallabiya amma sai dai hula ta rufe fuskarsa bana iya kallowa na kai fuskata kan hannunsa saida gabana ya faɗi fari sol kaman a tsaga jini yafito abune mai matuƙar wahala samun mutum mai irin wannan hasken a nahiyarmu. Agogon dake ɗaure a hannunsa brand na Patek Philippe koda bansaniba nasan agogon mak masifar tsaɗa ne. Bansan kuma ko kwayun hannun bane ya ƙarawa watch ɗin kyau ba. Sai wani zobbe mai wani design wanda nakasa tunano yanda nasan zobben. danna waya yakeyi gabaki ɗaya hankalinsa ya karkata a kan wayar. Muryar maryam tadawo dani daga tunaninsa na wuntsila.


"Babe kije kiyi mana order nagaji wallh ga wani azabebben ƙamshi daya sauƙarmun da kasala tunda nake ban taɓa cin karo d ƙamshi makamancinsa ba"
Sai alokacin na tabbatar da cewa bani kaɗai kejin wannan ƙamshin ba. Ajiye bags ɗina nayi akan kujerarda da zan zauna. Ƙarasawa nayi wajan nayi making ordern daga yanda nake ina iya jiyo muryar wanda suke zaune tareda shi yana magana cikkn harshen labarci harna bar wajan nadawo na zauna banji yabashi amsaba.

Na zauna akan kujerar ina facing ɗinsu kauda kaina nayi daga garesu dan zuciyata tanata faɗamin something is off. Nadubi Maryam nace.


"Babe something is not right a cikin awajannan bakiji ƙamshinna ba? bantaɓa jinsa ba sai ƙwannan cikin gidanmu kuma yanzu najishi anan ina tunanin kamar mutum ɗayane da wanda yaje Wajan Bab. Maryam saida ta nisa tace.


"Naji mana babe ba yanzu nake miki magana ba? Nima bantaɓa jin irinsa ba amma kinsan turare dayawa a duniya bbu yanda za'ayi brand na turare su buga sample ɗaya idandai ba nawani celebrity bane sune suke amfani da turare su kaɗai so calm down. Mema zai kawo baƙin Baba nan? Nan fa school ce ɗai-ɗai ku wanda ba ƴan makaranta ba suke shigowa nan sai suma a irin waɗanda ke buƙatar wani snacks awajan ko wani abun" Nayi shiru kawai dannaga bazata fahimceni ba. Lokaci-lokaci nake kallon wajanda suke zaune ganin ko sau ɗaya bankamasu suna kallo naba yasa hankalina ya ƙwanta muka gama abunda zamuyi muka tashi na nufi wajan na biya kuɗin sannan nazo muka fice.


Bayan nafita ya dubeshi yace.


"Mood sir tafita ko zamu bita?" Ya girgiza kai da Mamaki P.A yace.


"Are you not going to talk to her?" ya sake girgiza kai yace.


"No. I love her even though i haven't met her. So whats the point of meeting her" P.A yace.


"Go met her express your feelings" murmushi yayi yace.


"it's a fantasy, hopes and a dream. It's sweet kuma it's a basics for actually wanting to meet her amma ba yanzu ba not now. Expressing feelings ga wanda gareta i am a totally stranger that would surely freak her out. if i met her bazan iya barin sonda nake mata ya ƙwanta cikin raina kamar yanda nayi alƙawari ba koda na seconds ne and Banason na fara rayuwa tareda ita batareda ta yarda dani da kanta ba. Yanzu abunda yake gabana what can i do to make her fall for me?" P.A yace.


" okay. Meet her first. Let her get to know you. Go on a few date. if things work out then it would be appropriate to express your feeling" Dariya yasaka kawai dan abun bai kama hankalin kansa ba ya miƙe yana shirin barin waje. P.A ybashi yana faɗin.


"Mood sir whats the problem?" Ya nuna masa hannunsa haɗeda faɗin.


"This. This is the problem. My skin colour. Yarena ƙasata everything about me is different from her shine kake tunanin muje date? How? Tayaya zata yarda da totally stranger sufita date"
P.A cikeda gundura da maganar yace.


"Mood sir whats the point of all this? She's already yo..... . Shshshhhhhh ya dakatar dashi alokacinda yayi arba da ita ta dawo cikin wajan. Saida ta kalli yanda suke wannan karon ita yake kallo amma bata kallon idonsa saboda yana cikin gilashi ta kauda kanta hankalinta na wani wajan ba tasu takeba dasauri ta ƙarasa wajanda suka zauna da ɗauki ƴar ƙaramar wayarta data bari haɗeda sauƙe ajiyar zuciya. Menene wannan Zuciyarsa ta tambaya a yayinda tayi arba da wayar hannunta. Nan ƙirjinsa ya fara bugawa dasauri me takeyi da wannan wayar? Badai waya takeyi da wani ba?" idanuwansa suka rufe nan da nan suka kaɗa bai ankaraba harta fice. Dasauri yabi bayanta shima yayi wajen."






PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA


*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*






Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.




Ina isa dai-dai yanda maryam take na tsaya ina haki saboda saurin da nayi. Ta taɓe baki tace.


"Wannan wayar ko rayuwarki iyakaci kin waani bi kin rikice kawai dan kin duba baki ganta ba" na mika mata wayar haɗe faɗin.


"idanba rayuwata ha to mecece? hamma nefa yabani. Ni da'allah riƙemin ki sakamin acikin jakata" ta amshi wayar haɗeda buɗe jakata dake hannunta ta saka a ciki tana faɗin.


" sai muje koh?"


"Babe bari na huta mana" na faɗa ina zama a kujerun a ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin garden ɗin. Ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ya sauƙe haɗeda sakin murmushi saida yaga na miƙa mata wayar kafin hankalinsa ya ƙwanta. Sai lokacin ya tabbatar wayar ba mallakina bace. P.A ya ƙaraso wajan yana faɗin.


"Mood Sir is everything okay?" ya jijjiga masa kai batareda ya ɗaga idanuwansa daga kainaba. P.A yakai idaonsa yanda Hammood yake kallo shima saida yasaki murmushi ganin yanda ƙura mata idanuwa itakuma sai zuba surutu takeyi. Maryam ta miƙe tana faɗin.


"Ni wallh kin isheni ke yanzu ba hali azauna dake saiki fara labarin Hamma. Kedashi gabaki ɗaya kun zauce soyayya Hauka ce" nima na miƙe ina faɗin.


"nida Hamman nawa ne zautattu? Toh wallhy zaki maimaita gabansa"


"ni rufamin asiri karkije ki faɗa masa Hamma idonsa ya rufe akanki yanzu sai yamin rashin kirki" Saida nayi dariya danjin daɗin yanda ta ambaci sonda Hamma yakemin sannan nace.


"Nima ai idona ya rufe akansa banaji bana gani"


"kin haɗu da aiki kuwa" shine abunda tace. Saida yaga wuce wata saita idanuwansa suka daina hangen yanda nake sannan yafara tafiya zuwa yanda motarsa take.yana isa suka ƙaraso suka buɗe masa yashige. A hankali suke tafiya idonsa nakan window gabaki ɗaya hankalinsa yana waje yana kallo da nazarin yanayin garin. Saida P.A yayi gyaran Murya sannan yajuya baya ya kalleshi gabaki ɗaya hankalinsa na wani waje yace.


"Sir kana ganin zaka iya jurewa? Idan bazaka iyaba it's fine dama kai ka ɗaukawa kanka wannan alƙawarin is okay you can break it" saida ya daɗe bai bashi amsaba kamar bazaiyi magana ba sabo da halinsa yasa P.A baiji komai ba dan dama shi bawai mai son magana bane har sai indai lokacin maganar tasa yayi ko maganar tazo masa akan gaɓa.


"is okay i can handle it" shine abunda ya faɗa P.A ya jijjiga kai.




Da Yamma Hamma yazo ɗaukanmu cikeda ɗaukin ganinsa na isa wajanda yake ina faɗin.


"Sannu da zuwa Hamma"


"Yawwa sannu babyna mai kuma yaci na ɗin nawa?" Na kalleshi da rashin fahimta nace.

"Na?" Ya lumshe idanuwa sannan yace.


"Uhum na! Hamma na. a waya kice Hammana a fili kice Hamma. Ya narke sannan yacigaba da faɗin.


"Babyna adaina cutar dani dayawa mana ana sassautawa wasu abubuwan ana cire kunyar nan" Maryam tayi gyaran murya alamun musan tana wajan. Ya juya ya kalleta ya haɗe rai yace.

"Ƴar sarkin rashin haƙuri bazaki iya jira mu gama bane?" ta tura baki tana faɗin Hamna kagafa yanda ka narke murya kana yiwa Babe Magana amma ni da ihu kamar zaka tada wajan?" ya haɗe rai haɗeda maimaita.


" Babe? Babe kikace koh? Toh yafita a bakinki ni kaɗai nakeda hurumin kiranta da Haka she's my babe ni kaɗai" ta fara ƙunƙuni ƙasa-ƙasa tana faɗin.


"Wallh baka isaba ai ƙawatace kuma tare ka ganmu" Jin tana magana yasa ya haɗe rai haɗeda faɗin.


"Me kike cewa?" Ta kumbura fuska tana faɗin.


" Babu abunda nake faɗa tashige mota" Mu duka muka shiga muma tafi.


Saida ya kawoni ƙofar gida ya tsaya sannan yace.


"Baby I'll miss you" gobe bazan samu daman zuwa ganinki ba ayimin uzuri" Nace.


"Nayi maka Hamma sai dai na daure sannan na ƙarasa na ɗin gaban yayi murmushi na juya ga Maryam nace.


"Babe sai gobe idan mun haɗu school karkizo ɗaukana zan taho" dana juya naga irin kallonda yakemin yasani saurin sauya zancen da faɗin.


"Oh sorry Maryam saida safe" ta taɓe baki tace.


"ke kikaji wajan"


"kema kinji" nabata amsa nafice nashige ciki. Girgiza kai yayi kawai yace.


"Maryam gara kibar faɗa mata magana gabana yanda ranki keso dan munyi aure bazan ɗauki ki rainamin mata ba kuma kidawo gaba. Tafice takoma gaban aranta tana faɗin. Idan haka yayyu suke dawowa bayan fara soyayya da ƙawa an haɗu da aiki."


An ɗauki tsawon ƙwana ukku kullum sai na gansu a wannan wajan da muke zuwa harna ɗauki niyyar canja waje amma saina fasa dan ina tsoron nasake ganinsu acan daganan hankalina bazai ƙwanta ba zanga duk yanda naje zasu iya bina so gara na zauna a waje ɗaya."




Wannan karon Ya Ahmad ya daɗe ba kamar yanda yasaba zuwa yayi ƙwana ɗaya yatafi ba kusan ƙwanansa goma kenan banga yana shirin tafiya ba koda yake ba sallama yakeyi ba sai dai muji kawai ya tafi.


Dawowata daga makaranta kenan naganshi yana cikin chinese canopy wajan shaƙatawar dake harabar gidanmu waya yakeyi cikeda nishaɗi sai murmushi yake sakewa akai-akai. maimakon nashiga cikin gida saina canja akalar tafiyata zuwa wajanda yake ina isa batareda sanin da wacce yake waya ba nace.


"Yaya kabani ita mugaisa" baisan sanda yasaki dariya ba haɗeda faɗin.


"Lallai Marmee wayace miki da mace nake waya?"


"Yanayinka ne ya nuna" batareda ya ɗaga wayar a kunnensa ba yace.


"wane yanayi nayi?"


"Sai murmushi kakeyi cikeda nishaɗi. murmushin fuskarka ya bambamta gashi zai tsinke flower kakeyi" na faɗa haɗeda nuna flower ɗinda ya tsinke yakai kallonsa wajan batareda ya sake mun musu ba yabani wayar na amsa muka fara hira dake itama mai surutu ce min ɗauki tsawon lokaci muna magana. Saida ya haɗe rai yace.


"Ke bani wayata" bankaiga miƙa masa wayarba naji tana faɗin Marmee zakizo bikinmu koh? Ihu nasaka ina faɗin biki? aure zakuyi" najuya wajansa ina faɗin.


"Yaya aure zakayi?" batareda yabani amsa ba ya amshe wayar yakai kunnensa yace.


"Zan kiraki ina zuwa" bayan sunyi sallama ya dubeni yace.




"Eh aure zanyi Marmee"


"Yaushe" nasake jefo masa tambaya.


"Ankusa baifi saura 2month ba"




"Dan Allah yaya zakaje dani?" saida yayi wani nazari wanda bansan na menene ba yace.


"Makaranta"


"Lokacin nagama" nayi saurin bashi amsa" saida yayi shiru sannan yace.


"Naji zanje dake" na saka ihu ina faɗin.


"promise" kai kawai ya jijjigamin. Nace.


"Ya Ahmad kaga dama ba'a taɓa biki agidanmu ba akanka za'a fara kaine farkon aure agidanmu"


"Anya kuwa" yafaɗi. Nace.


"iyi sosaima kagani bikinka sai wanda yagani da a garinnan za'ayi duk wanda nasani saina gayyacesu"


Ganin na cikashi da surutu yasa yace.


"Maemee yanzu kika dawo school baki gaji ba?" kije ki huta" nace


"Toh amma idanna gama zan dawo ka nunamin hotonta" ya gyaɗa kai kawai" ya lura tun abaya duk yanda yaso raba kansa da ƴan uwansa bai samu hakan daga wajan marmee ba danko bazai kulata ba saita masa magama da surutu har takai takawo shida kansa yakeyi mata magana. Babu sabo ko shaƙuwa tsakaninsu amma yana jinta cikin ransa tana ɗaya daga cikin mutannenda yakeso a rayuwarsa koda bai fito ya nuna ba amma marmee ƴar uwarsa ce wacce takeda matsayinda Wanda suka fito ciki ɗaya basu samuba. Baya mantawa lokacin tana yarinya ƙarama kullum tana wajansa. Ko anguwa zaije yakance saida ita sunyi wata iriyar shaƙuwa tashi ɗaya kawai akazo aka raba tsakaninsu. Wanda hakan yayi sanadiyyar da shaƙuwarsu taja baya amma yanzu ƙarfi dayaji tanaso ta dawo da ita. Kuma yanajin daɗin yanda take shiga al'amuransa. Harta juya zata tafi ya kirata.


"Marmee" na juyo nace.


"Na'am Yaya"


"Marmee kina soyayya ne?" gabana yayi mummunan faɗuwa kardai Ya Ahmad yasan soyayyata da Hamma" saida na dabirce sannan na tattaro nutsuwata nace.


"A'a meka gani?"


"Naga kinsan murmushin soyayya kinsan yanayinta gabaki ɗaya" Nayi murmushi nace.


"Au wannan? Ai a waya nagani"


"Okay jeki toh" nasakai nashige.


"Ina shiga saida na sanarwa kowa zancen auren Ya Ahmad" Anty fadeelah tana murna. Aysha tace.


"Meye naki na murna? Bayan kinsan ba zuwa zakiyi ba?"

"bangane bazan jeba"


"Eh bazakije ba mana"


"Kamar Yaya fa? Banganeba?"


"kije ma kiga yanda zaku kaya da mummy" nace.


"ku zauna karkuje amma nikam sai naje duk abunda zai faru yafaru"


"Mama tana zaune itada anty suna jinmu basu tankaba, natashi naje nacire uniform ɗina nadawo na zauna da plate ɗin abinci a hannuna. Muna zaune Ya Ahmad yashigo Mama tayi masa barka da fatan alkahairi" ya amsa cikeda murna da fara'a. Antyma tayi masa saiya share kamar baiji abunda tace ba."




Washe gari cikin Asibiti muke practical zamuyi da Wani babban likita, tsoro nakeji sosai dan har yanzu nakasa sabaw ada duk wani practical daya shafi threatre. Shigarmu aka kawo wani maras lafiya wanda za'a yankewa ƙafa, duk wani abunda akeyi ana yimana bayani. Hankalina bai tashiba saida naga anzo wajanda aka cire ƙafar cancak aka ajiyeta gefe. Luuuu nayi ƙasa na faɗi saboda firgicin dana shiga.




Awanshi biyi akaina cikeda damuwa. Ko numfashi mai ƙarfi baya Iyayi saboda gani yakeyi kamar zaita dani, a hankali nake sauƙe numfashi idanuwana a rufe luff zara zaran gashin idona suma sun ƙwanta sunyiwa ƙasan idon rumfa, duk kallonda yakeso ya ƙaremin ayau yayi. Yayinda zuciyarsa ke ƙara azalzala da soyayyata. Ganinsa haka Kusa dani saI zuciyarsa tasama masa waswasi aKan Alƙawarinda ya ɗauka" Nikuma Bansake sanin yanda kaina yake har bayan awa biyu buɗe idona nafarayi a hankali a lokacin ya silale yabar ɗakin. Na buɗe ido kawai naganni cikin wani ɗaki. Kaina yana jujjuyawa ina buɗe idanuwa harna fahimci yanda nake ɗayane daga cikin manyan ɗakuman dake asibitin baki ɗaya ba kowa ake ƙwantarwa a wajanba nikuma mai ya kawoni nan? Alokacinda hankalina ya gama dawowa jikina saina fahimci ƙamshin da nakeji. Zumbur na miƙe tabbas wancan ƙamshinne toh amma me ƙamshin yakeyi aɗakinda ƙwance?" nasauƙa daga kan gadona nafito acan gefe naga maryam zaune cikeda damuwa na ƙarasa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads