Showing 117001 words to 120000 words out of 171869 words
Chapter 40 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
da Hamma tataho gida ta ƙwana? Banida amsar tambayoyina dan haka naja bakina nayi shiru bata kulani ba nima banbi takanta ba tayi waje ina jiyota tana tambayar Mama abinci.
mama tace yana kitchen kishiga ki ɗauka.
"Yanzu fisabilillhi abincin nawa aka barmin a kitchen Mama? Nazo gida bayan ƙwanaki ko tattalina ba'ayi? Toh ni wallh yanzu zan shirya na koma gidana tunda abun hakane"
"Shirya ki koma Aysha dama Babu wanda yace ki ƙwana anan sia taurin kanki"
"Wallh Mama acan ina zaune ake dafamin a kawomin sai dai natashi nasamu wani lokaci Hamma ya biyoni dashi har ɗaki"
"Aikuwa dai gata yakusa ƙarewa dan kin kusa fara shiga kitchen kina girki" miƙewa nayi nafito nima naɗauki nawa abincin nashiga naci sannan na fito tsakar gida Wajan Baba nawuce na gaisheshi yacemin na kira masa matan gidan na shiga ciki na sanarda aikar Baba sannan na dawo ɗaki.
Su duka suna zaune a palourn Baba yadubesu
" Ƴan sayyyar da za'ayi agida na kayan abinci su cefene nakeso kuyimin list sai Habiba su Fita da Habibu kasuwa suje su sayo da kuɗaɗen da suke hannuna dan nasan yanda akayi bikinnan komai yaɗauko ƙarewa. Sannan ga wannan ya miƙawa Mummy. Kuɗin cefene ne na yau nasan har baza'a samu sayowa ba kafin ayi sayyayar gida gabaki ɗaya. Mummy ta jujjuya kuɗin tausayin Baba ya kamata a rana takan kashe ninkin hakan yakai sau 4 a wasu ƴan hidimominta kawai da bata ɗaukesu a komai ba ashe quatern abunda take kashewa ƙananun matsalarta sune cefenan gidan mijinta"
"Kabarshi Kawai zanyi amfani da kuɗin wajena akwak kuɗi a wajena" Baba ya jijjiga kai.
"A'a hakkina nake sauƙewa ki karɓesu a nemi yara suyi cefane a ɗaura abinci dawuri. Sai yaranki su tayaki dan gidan yanzu babu mai aiki" Iya adalcin da Baba zai iya mata kenan yace yara suyi mata aiki dan yasan bazata iyaba kuma shi bayida halin ɗaukan mai aiki Idan yace zai ɗauka kuma bazai yiwu ya ɗauka mata mai aiki ita kaɗai ba"
"Mummy kam ai yanzu baƙuwa ce abari muyi mata ko na wani lokaci ne kafin ta karɓi aikin"
"A'a abunda bazai ɗaure ba gara kar afara shi tun yanzu. Kubari yaranta dai suyi mata zuwa wani lokaci muga abunda Allah zaiyi" Mummy tayi shiru ita dai batasan tayaya zata fara aikin gida ba tunda tun farkon aurensu bawai yi takeyi ba tazo takoma gidansu masu aikinta kaɗai su 3 ne yanzu tayaya zata fara aiki? Bari dai tajira tagani yanzu yaran su fara aikin kwana biyu zata ɗauki maiyi mata aiki.
Ɗaki nashiga na ɗauki wayata anan nayi arba da jakar da Hammod yabani nabawa Baba. Saida naganta kafin na tuna ta batareda ɓata lokaci ba naɗauki jakar na isa zuwa ɗakin Baba na manta da matansa na ciki saida naga takalmansu A ƙofar ɗakin har zan juya sai naji Baba yana faɗin.
"Waye a baƙin ƙofa?" dake yaji footsteps ɗina kuma baiji shigowata ba.
"Nice Baba aika na kawo maka amma tunda kuna magana zan dawo"
"Shigo ki kawomin ai mungama maganar" toh nafaɗa haɗeda yin sallama nashiga ciki.
Na isa zuwa wajansa na miƙa masa jakar ya miƙa hannu batareda yace komaiba saida ta isa gareshi ya ajiyeta a gabanshi sannan yace.
"Menene wannan marmeeyy?"
"Aikeane Jiya yabani nabaka"
"Waye kuma yabaki aika ki bani?" Baba yayi tambayar kansa tsaye dan tunaninsa bai kawo masa Hammood ba.
"Uhmmm Hammood ne jiya yace nabaka nafaɗa ina sunkuyarda kaina"
"Toh" kawai yafaɗa haɗeda buɗe jakar saida gabansa ya buga ganin abunda yake ciki"
"Marmeeyy kikace shi yabaki kuma kibani?"
"Eh Baba nikuma ya bani wannan na miƙa masa ATM daya bani jiya saida na tashi sannan naga abunda yake ciki zaro ido nayi na kalli Baba da yayi shiru bazaka iya gane yanayinsa ba. Ya sanya hannu ya karɓi ATM ɗin ya dubashi sannan ya dawomin dashi na tsaya ina kallonsa danna ɗauka zai riƙene.
"Karɓi Marmeeyy wannan nakine shi yabaki kiyi amfani dashi matsayinsa na mijinki yanada ikon yabaki kyauta yaɗauki ɗawainiyarki idan yaji zaiyi hakan amma ni wannan kuɗin daya aikomin ne bansan dalili ba"
"Kyautatawa ce yayi maka matsayinka na mahaifin matarsa duk da dai abun ya zarce hankali" mummy tabashi amsa.
"Banƙi taki ba amma Kyautatawa da wannan kuɗin? Ke marmeeyy bayan yabaki baiyi miki wani bayani ba? Na jijjiga kai.
"Toh bari nakira Ahmad naji ko ya faɗa masa wani abun yaɗauki waya yakira ya Ahmad yafe yazo yana nemanshi nikuma ya miƙamin ATM ɗin.
"Ungo amshi wannan Marmeyy" na jijiiga kai.
"Baba ka riƙe a wajansa kawai ni babu abunda zanyi dashi"
"akwai abunda zakiyi mana Marmeey Bayan gashi yanzu haka neman kuɗi ake na shirye-shiryen gama makarantarku ga wasu expenses na rayuwa da baza'a rasa ba maza karɓi" na sanya Hannu na amsa na miƙe na fice. Baifi 1hour da kiran Yaya Ahmad ba sai gashi ya iso. Ya nuna masa abunda Hammood ya aiko masa.
"Baba ni baicemin komai gameda kuɗin ba amma inaga tunda yabata tabaka toh yana nufin yabaka kyautane"
"Kyauta Ahmad kadubi abunda name gani fa? Ba naira ba kuma ba dala ba"
"Eh toh Baba a namu wajan kam wannan kyautar tayi yawa ta zarce ƙa'ida amma idan akayi da la'akari da waye Hammood nawa albashinsa yake aduk 1hour ba abun Mamaki bane amma idan kanajin wani iri akai sai a ajiye aji ko zaiyi magana akai.
"Gaskiya fa ai hakanma za'ayi kawai Allah ya kyauta saida naji gabana yafaɗi wallh Ahmad ganin wannan dukiya yanzu fisabilillhi akwai mutane da zasu iya kyauta da dukiya kamar wannan ake samun talaka da zai ƙwana baici abinci ba? Wannan lamari Ahmad idan nace maka bai bani tsoroba nayi ƙarya sai nakeji kamar bazan iya bada Marmeeyy yatafi da itaba shakku ya ɗarsu a zuciyata.
"Karkaji komai Baba in sha Allahu babu komai sannan nazo na faɗa maka Hammood yayi announcin aurensa a kafafen sada zumunta gabaki ɗaya duniya ta kaure zancen kawai akeyi shiyasa nazo na saka Marmeeyy ta canja sunanta na Instagram data saka dan wasu sun santa abun zai watsu a duniya tunda mutane sun fara zargin wacce yayi following recently itace wacce ya aura. Baba naji daɗin sanarda aurensa da yayi a duniya gara komai ya fito fili domin yin abu a ɓoye babu daɗi."
"Eh toh nima zance naji daɗin hakan har naji hankalina yaɗan ƙwanta amma inace bai sanar musu wacece wacce ya aura ba?"
"A'a Baba bai sanarba daya sanar ai yanzu gidannan babu masaka tsinke kawai ya ɗaura a shafinsa ne sannan kuma nasan dole idan yabuga match ɗin da zaiyi this week ƴan jaridu zasu nemi sanin wacece wacce ya aura" Baba yasauƙe ajiyar zuciya.
"Allah Ahmad nima yanzu naji gara ya sanar da auren nasa danaga wannan uban kuɗi dayayi kyauta dashi. Gara asan da zancen kawai"
"Hakane Baba Allah yakyauta su duka suka amsa da amin" miƙewa yayi
"Bari nayi magana da Marmeeyy saina dawo muji yanda za'a ajiye kuɗin ko banki za'a kai?"
"Jeka dawo ɗin dai amma ai babu batun banki a wannan lamari"
Da sallama yashiga ɗakin Mama. mama wacce tashiga tana yimana magana akan mutashi mufara aiki ta amsa sannan tafito palour. ya gaisheta ta amsa tana tambayarsa wajan matarsa yace lafiya. yana kallom aysha dake zaune a palourn Mama.
"Anan ta ƙwnaa?" ya tambaya rai ɓace.
"Eh wai batajin daɗi ajiyan mukace takoma takirashi wai ya rigada ya ƙwanta itakuma tace tanaso tatafi da Marmeeyy saboda batajin daɗi tun jiyan naso ince maka ko zaka tambayi shi mijin marmeeyyn?"
"Babu wanda za'a tambaya Mama dan babu yanda Marmeeyy zataje duk da kuwa Hammood yabata izinin zuwa ko'ina har ranarda zata koma hannunsa. Garama ta shirya idan zan fita an ajiyeta a gida.
"Dan Allah Yaya Ahmad kayi haƙuri kabari yazo ɗaukana dan Allah sai kace wacce kuka gaji dani? Daga zuwana zakuce wani yazo ya ɗaukeni fisabilillhi"
"Toh yazo ɗin Amma babu yanda Marmeeyy zataje" kowa ya zauna a muhallinsa" sannan ya dubeni.
"Marmeeyy kihau ki canja User ɗinki na facebook da wani suna daban da baza'a ganeki ba komai da kikasan za'a iya ganeki dashi ki canja saboda wanda suka sanki" Dake wayar tana hannuna alokacin nashiga nafara canjawa nabarshi a zaynab kaɗai duk hotunan kai na cire har profile ɗina saida na canja. Tun auren Aysha sai lokacin nashiga insta millions of Followers nagani ga DM's kamar zasu kasheni dake Yaya Ahmad na tsaye sai na kashe datar muka gama magana yafita sannan na miƙawa Mama box sarƙan dake hannuna ta duba tace.
"Allah ya sanya alkhairi na amsa da amin" muka fita cikin gida nida Anty fadeela muka fara aiki alokacin Aysha tafito dake zaman ɗakin ita kaɗai ya isheta.
"Marmeeyy nikam nace Yaya akayi kuka haɗu da Hammood? Ko Ya Ahmad ya haɗaku?" Aysha ta jefamin tambaya.
"Eh" kawai na amsa mata.
"Hala faɗuwa ce tazo dai-dai da zama dan ina tunanin Wani bokansa dake bashi sa'a yace ya auri baƙar fata badai wata kyakkyawar gaske ba halan shine kawai da yaya Ahmad ya haɗaku sai yace yana sonki dan yasamu dai-dai buƙatarsa"
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
"Anya kuwa kinada hankali Aysha? Wa ƴar uwarki kike yiwa wannan fata? Toh idan boka yace ya aureta tsafi kenan yakeyi? Taɓabbiya kawai"
"A'a ni wallh bance haka ba ai bakiji nakira tsafi ba kawai ina nufin irin mutane masu neman sa'a a jikin mace sai kiji ance musu da auri kala kaza arzikinka zai buɗu amma ni na isa nace tsafi habawa A'a" tana magana ne dan duk da ƙular dani danta lura a halin yanzu shine kawai abunda zata iya ya ƙuntatamin idan ta ƙular dani zanji zafi. Nayi murmushi da saida ta tsaya kerere tana kallona tana tunanin me akayi na murmushi"
"Lallai bokan Hammood yayimin adalci tunda zaɓinsa ta jeho kaina har nake samun soyayya a wajansa ba shakka Hammood najin magana haɗin boka ne amma soyayya mai ƙarfi ta ƙullu. Wasu fa zakiga haɗin na iyaye ne amma san abun babu armashi soyayya takasa ƙulluwa a tsakani" Nafaɗa mata wannan maganar ne kawai ko zataji zafi koda sau ɗaya ne akan irin maganarda take yaɓamin.
miƙewa tayi kaina tana huci nima na miƙe.
"Wallhi kina dukana saina rama tunda ke ƴar rainin hankali ce kin ɗauka kowa tsoronki yakeji shiyasa ake barinki kina yaɓawa mutane magana. Kema kiji idan akwai daɗi ƙaryane Hamman sonki yakeyi? Koba haɗin bane amma har yanzu kin kasa samun soyayayrsa gara ni ko haɗin bokane Aysha duniya ta shaida soyayayr dayake min amma kefa? Ke kanki kin kasa shaida soyayya da mijinki yake miki" ganin abun yana shirin ƙwaɓewa yasa Anty fadeela shiga tsakani hayaniyarda akaji ya sanya mutanen gidan fitowa harda Baba kafin su ƙaraso cikin gidan ma kuka ya ƙwacemin Jin abunda nake faɗa ya sanya mama tayi kaina.
"Marmeeyy bakida Hankali ne? Ta ɗaga hanu zata ƙwaɗamin mari Baba yayi mata magana ta sauƙar. Kull karki taɓata. Ke marmeeyy meya faru haka kike yiwa yayarki rashin kunya?" Nasaka kuka nakasa cewa komai. Cikin zafin rai Mama tace.
"ba magana ake miki ba? Ai abun bazai wuce santa auri Hamma ba bakaji da kunnuwanka gori take mata akan Hamman baya sonta? (ki kasance mai son yan uwanki kada kitaba kullatar yan uwanki a wani dalili komai girmansa) marmeeyy kullum wannan maganar nake faɗa miki ashe bakiji magana taba? Ashe ban isa na faɗa miki kiji ba? Akan wani can daban kin ƙullaci ƴar uwarki Marmeeyy kinyiwa kanki adalci kenan?" mama take magana cikin zafin rai.
"Wallh Mama ba marmeeyy bace da laifi Aysha ce shaiɗaniya ummul aba'isin komai dake faruwa duk hanyarda Marmeeyy zatabi wajan ganin ta kaucewa rikicin Aysha tanayi amma abun ya gagara" Nikam kuka kawai nakeyi Mummy ta ƙaraso wajena ta fara lallashi ganin baza'a gane kan zancen ba idan ba an zauna ba ya sanya Baba yace muduka mu sameshi a ɗakinsa. A lokacin muka nufi ɗakinsa. Munsamu sun baje kuɗin shida Yaya Ahmad suna dubawa. Yaya Ahmad ya tattare kuɗin muka zauna saida Baba yayi nasiha sannan yadawo kaina yanamin faɗa.
"Marmeeyy banji daɗin abunda kika faɗawa ƴar uwarki ba koma me tace miki bai kamata ki yimata gori akan ta auri masoyinki ba kisani itama ba son kanta bane ni nayi mata auren dashi kuma tayi biyayya ta zauna" saida ya dasa aya sannan anty fadeelah ta amsa.
"Baba wallh ba laifin marmeeyy bane. Marmeeyy nazaune da kowa zuciya ɗaya ƴan uwanta duk so ɗaya take musu kuma bata ƙullatar kowa a cikinmu Baba tun kafin ka aurawa Aysha Hamma take sonsa dukda tasan cewa Hamma saurayin Marmeeyy ne danni nagani da idona hawa kafat sata zumunta takeyi tana ɗauko pictures ɗinsa. Kuma naan Marmeeyy ta fahinci hakan amma bata taɓa nuna mata tasani ba. Akazo aka juya aurenta kan Hamma wallh Baba naje na samu marmeeyy akan mu sameka mu roƙeka taƙi kuma tayi hakanne danta fahimci aysha tana sonsa tun alokacin tabar mata shi ko bata faɗa ba actions ɗinta ya nuna tunda taƙi taɓuka komai da zaisa su kasance tare da Hamma. tunda aka saka auren Hamma da Aysha marmeeyy tadawo abun dariya da zolaya a idon Aysha da ƙawayenta har habaici suke yaɓa mata duk da Mummy tayi musu faɗa tun a abuja wannan dalilin ya ƙarawa Marmeeyy damuwa aranta sannan kuma tadaina zaman cikin mutane dan idan Aysha tanana saita yaɓa mata magana. Duk wani abubda yafaru abaya wanda Baba ya kamata yasani saida fadeela tafaɗa sannan ta ɗaura. Ko yanzu Baba Marmeeyy batayi niyyar kulata ba amma cin fuskar yayi yawa idan bata tanka mata abun zaiyi tsamari cewa take wai boka yasa Hammood ya auri Marmeeyy. Toh yanzu dan Allah Baba idan bata faɗa nata baƙa itama ko sau ɗaya ba ina zataji daɗi aranta? Wallh marmaeeyy nada zuciya mai kyau ita dai Aysha da tasawa ranta jin ɗacin Marmeeyy babu gaira babu dalili wai Mummu tafison Marmeeyy akanmu kuma Mummy ita kanta tafaɗa yanda Marmeeyy ta ɗauketa mu data haifa ba haka muka ɗauketa ba. Kulawarda Marmeeyy tabata bamu bata ba. Ni bawai kare Marmeeyy nakeyi ba Baba ban kuma ce wai yanzu sam batason Hamma ba amma tun a baya batasan tanada Hammood ba ta ɗauki ɗamarar cireshi aranta bare yanzu data san Hammood tun ana ajiyewa ta ajiye Hamma wallh Baba ka ɗauki mataki kan aysha dan bataji sam zata raba maka gida". Kaf cikin wajan shieu akayi ana sauraron Anty fadeelah bayan tagama Baba yayi salati kawai yana jinjina girman zancen a ƙwaƙwalwarsa haka tana faruwa agidansa amma babu wanda ya sanr dashi?.
Yayi musu faɗa sosai wanda ko wannensu saida yaji tsoro dan bai taɓa irin hakan ba sannan ya dawo nasiha jikinsu sanyi matuƙa. Sannan yabawa kowannenesu haƙuri yace karya sake ji ko wani abun makamancin haka yasake faruwa Anty fadeela tazo ta faɗa masa zai ɗauki mataki. Aysha tunda take a rayuwarta bata taɓajin anyi mata shari'a nai adalci ba irin na yau dan Baba bai goyi bayan kowacce ba kuma yayiwa kowwcce faɗa dai-dai da lafinsa sannan yace kuma shi yaransa gabaki ɗaya yana sonsu babu wanda yace yafiso aciki sannan yace idan kuna tunanin anfi nunawa wasu kulawa a cikinsu ku kasance kamar yanda wancan yake ta iya yiwuwa sai anfi nuna muku kulawa akan wanda kuke tunani sannan yace su iyaye tsere ake a yayin kyautata musu bawai nuna fushi akan wanda ya kyautata ba. Kaff babu wanda jikinsa baiyi sanyi a cikinsu ba har iyayensu mata maganganun Baba sun ratsa su sannan ya roƙesu suyi zaman lafiya. Yakuma soke maganar zuwan Marmeeyy gidan Aysha dan jiya yafara tunanin barinta tatafi amma yau magana tatashi."
Su duka suka fita Zuwa ɗakinsu mukuma mukaje muka ƙarasa aikin abinci. Bayan mungama su Anty zasu shiga kasuwa na bisu.
Saida nafara checking balance a bankin dake kusada kasuwar Zeros ɗinne ban ganeba na cire kawai dan bazan tsaya irgawa ba muka shiga kasuwa kuɗinda Baba ya bada nace Anty ta ajiye muyi amfani da na hannuna. Wajan mai shimkafa mukaje zai auna mana nace.
"Anty tsaya kiga muyi amfani da wannan akwai kuɗi dayawa a ciki bansan ko nawa bane karmu auni shinkafar kawai mu sayai buhu" amincewa kawai anty tayi mukace abamu thailand buhu guda na miƙa masa Atm ya cire nace dubamin balance yaduba.
"Nawane aciki?
"Wallh hajiya toh dai ga kuɗin naki nan Bansan nawa bane ya kama ciki dan bantaɓa cin karo da zerorin kamar haka ba. Na kalleshi da alamu bawani dogon karatu yayi ba naɗauka ƴan kasuwa ai lissafinsu akai yake. nima danayi karatun ban tsaya lissafa zeron ba bare shi.
"Toh wama yadamu da zeron? Cire kuɗin buhu biyar nafaɗi" Anty ta kalleni ke Marmeeyy har buhu biyar?" shikuwa bai tsaya wata-wata ba ya danna kuɗin biyar ya miƙomin na amsa zansaka pin alokacinda nake hawa Anty amsa
"Anty ai shinkafa bata ɓaci idan takama goma saimu saya goman ma" Mai shagon ya washe baki.
"aikuwa kinga idan gomanne me zaifi a lissafe tubda kinga ko zero ta biyar bata motsa ba"
"Toh saka goman amma karka lissfa saimun haɗa da sauran kayayyaki" anty ta hanani haka naƙi haka kawai ina kallon mahaifina yana aunar abinci sa'i-s'i ace nasamu halin da zan hanashi auna ban hanashi ba. Komai dana tashi saya a na hauka na saya har gishiri muka gama lissafi ya cire kuɗinsa yabamu reciept da zummar zasu aika mana gida da kayan a abbar mota dan motar da mukazo da ita bazata ɗeba ba tun kafin mubar wajan mukaji kai shago yafice yaja bawa maƙwanta labari yana nunoni. Muka wuce wajan wasu abubun duk abunda na saya saida