Showing 105001 words to 108000 words out of 171869 words
Chapter 36 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt
zato ba ko wannan karon ɗinma na ɗauka ba haɗuwar kusa ba"
"Toh yanzu dai marmeeyy sai ashirya yana hanya a yi ƙoƙarin goge shirmenda akayi jiya"
"Toh in sha Allahu amma Baba Hammood yataɓa zuwa wajanka koh?"
"Yaya akayi kika sani koya sanar dakene?"
"A'a bai sanarda niba ina lokacin dana taɓa tambayarka baƙinda sukazo wajanka? Na kwana biyu inajin ƙamshin har a school ɗinmu sannan kaima Yaya kasan Hammood tunba yau ba" Dariya yayi yayi yana faɗin.
"Toh yanzu idan Hammood ɗin yazo ki tambayeshi da kanki mana"
"Kitashi kije bansan wani lokaci zai isoba hara ki shirya kafin yazo"
"Toh" nafaɗa namiƙe zuwa Waje nasamu su Anty fadeelah.
"Wai kuzo inji Baba mugyara gida za'ayi baƙo"
"Hammood Zaizo ne?"
"Eh" nafaɗa haɗeda juyawa" su duka suka biyo bayan a cikeda murna yau zasuga Hammood a acikin gida su Mama suka bamu aikinda za'ayi saida muka gama kimtsa palourn sannan muka shiga aikin cikin gida sai wajan la'asar muka gama. Saida mukahi sallar la'asar sannan muka shiga ciki.
tsefe kitsonda yake kaina nayi na taje kan yanada Cika sosai na gyarashi nasaka ribom nakama kan. Sannan nayi wanka na shirya cikin doguwar rigar lace wacce tabi duk illahirin jikina kamar wanda aka zanata. zan ɗaura kwali Maryam ta ciromin Mini veil.
"Bab yafa wannan kawai kibar kwalinan haka kuwa akayi dan ban saka ƙwalinba. Humrar da Mama ke amfani da ita na shafa. Harna shafa saina tuna lokacinda wannan abun yafaru tsakanina da Hamma dalilin shafa wannan humrarne. Toh amma ai Hamma ba Hammood bane.
Muka zauna zaman jira har akayi magriba. Bai isoba natashi nayi magrib.
"Babe bazaki tafi gida ba? Gashi har dare yayi Hammood bai isoba"
"Zantafi amma sai naga Hammood zan jirashi yazo Saimu tafi Yaya Habibu zai kaini"
"Uhmm" kawai nace ina zaune har aka kira sallah Isha'i nayi nazauna akan sallah ƙamshin turarena yafara sanarmin da isowarsa. Lumshe ido nayi na miƙe kan sallayar na ƙwanta. Ina shaƙar ƙamshin
daga yanda nake. Nasamu kaina da faɗuwar gaba gashi cikin zuciyata ina Allah-Allah naganshi.
kusan 30minute da shigowarsa Baba yakira wayar Mama ya sanar mata akan naje wajan Hammood yana zaune shi kaɗai.
"Marmeeyy tashi kije palourn Babanku kinada baƙo sannan ki kula karki sake yin shirmenda kikayi jiya"
"Toh in sha Allahu bazan sake ba" Na miƙe na suri
gyalena na dubi Maryam.
"Zo muje babe"
"A'a ba yanzu ba idan kikaga zai tafi sai kimin magana nazo mugaisa"
Tunda nayi Sallama ya amaa idonsa yake kan ƙofa nashiga ciki na nemi can gefe na zauna har lokacin idonsa yana kaina a hankali cikeda kunya na gaisheshi ya amsa. Yana taso na ɗago muhaɗa ido.
"هياً اجلسي هنا"
"(zoki zauna ana)
Yafaɗa yana nuna kusa dashi da hannunsa" na ɗaga idanuwana na kalli wajan ban tashi ba nasaka ƙasa da kaina. Inaso na ɗaga ido na kalleshi amma nakasa kunyar abunda nayi nakeji.
"Zaynab" ya kira sunana sai alokacin na kalleshi nayi arba da kyakkyawar fuskarsa yana sanye cikin jallabiya fara ƙal tayi masifar yimasa kyau amma sai dai yanda naganshi jiya da yau ya bambamta domin yau hancinsa yayi jajazir alamun yana mura. Ganin ya tsuramin idanuwa bayan yakira sunana baida alamun cewa komai yasa na sunkuyarda kaina A hankali nafara wasa da zoben hannuna.
"Zaynab هل أنت غاضب مني
(Fushi kike dani)" na jijjiga kai alamun A'a.
"Toh menene idanba fushi ba?"
"Abunda yafaru jiya naɗauka dagaske mafarki nakeyi ashe ba mafarki bane sai yau na tabbatar. Kayi hakuri da abunda yafaru"
Sauƙowa yayi daga kan kujerarda yake yadawo kusa dani.
"Jiya ranar farin ciki nace ban taɓa tunanin kasancewa dake kamar jiya ba nayi kwana farin ciki domin kin bani nishaɗi kuma na ƙara sonki a jiya kaɗai" na jijjiga kaina kamar wanda nakeson yin kuka.
"Please Stop Hammood tayaya za'a soyayya a tsakaninmu, ka manta kai wanene? Tayaya haka zata yiwu? Meyasa bazaka gane hakanba"
Babu damuwa a fuskarsaba ko alamun ɓacin rai da maganarta kamarma wanda yakejin daɗin abunda take faɗa.
"أنت لا تحبني؟
bakya sona kenan" na kalleshi idan nace banasn Hammood ai nayi ƙarya.
"Ina zuwa" shine abunda nafaɗi bayan na miƙe zanbar wajan. Zan wuce yakamo hannuna.
"Meyasa baki bani amsa ba" alokacin na kalli cikin idanuwansa wasu abubuwa nake kallo wanda bazan iya faɗin ko menen ba. Ina kallonsa ina ƙara kallon irin halittar da Allah yayi masa toh wai tayaya ma za'ayi yace ni yakeso? Bayan nasan yaga wanda suka fini sunfi miliyan bayan nasan kusan matanda yake zagaye dasu gabaki ɗaya sun fini.
"Meyasa baki bani amsa ba?"
"Amsar me zan baka bayan kasan amsar jiya ma aina faɗa maka nagama buɗe maka abunda yake cikina" yanzu ƙarya kakeso nayi?"
"Menene aibuna?"
"Babu babbar matsalar kenan shine bakada wani aibu kai daban ni daban" Hannunsa daya rike nawa na kalla.
"Kalli nan daga fatar jikinmu zakasan akwai bambamci tsakanina dakai. Kalli kalarka da tawa"
"Nasanda hakan amma ke kaɗai nakeso." lumshe ido nayi jikina yayi sanyi tayaya zan iya masa bayani ya fahimceni.
"تعال لنتحدث" (come let's talk) ya faɗa babu musu na dawo ma zauna.
"Don't say or do anything Just أستمع لي (hear me out) just listing untill I've said what I want to say and then you can make up your mind.
"Okay fine" I thought wata magana mai tsayi zaiyi sai naji yace
"أنت زوجتي زينب"
You're My wife.
PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."
ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya
Na turo baki danni bangane abunda yake nufi ba i thought ko Irin yanayin yanda samari idan sunso daɗin baki suke cewa ƴan matansu ne atunanina yanason tsarani da waɗannan kalamanne. Ganin ban fahimci abunda yake nufiba ya sanya yacigaba da bayani.
نحن متزوجون"
"We are married) You're my person Now and forever. Few months backs Anyi mana aure.
"Aure? Kamar you"re my husband" Ya jijjiga kai dan tabbatarwa.
"Yes I'm" yafaɗa cikeda tabbatarwa nayi shiru inata sauƙe ajiyar zuciya. Zancen yakasa kama ƙwaƙwalwata.
narasa yanda zanyi murna zanyi cewa Hammood yazama mallakina ko kuma damuwa zanyi? Na tabbata Ikon da kuma yarda da mahaifina yake dashi akaina yasaka yayimin aure batareda sanina ba. Tsawon yaushe na kasance a matsayin matar aure? Tsawon yaushe Hammood yake matsayin mijina? Kai anya kuwa Wannan abune mai yiwuwa Hammood fa? Hammood za'a ɗauramin aure dashi.
To meyasa Ma Hammood zai faɗa soyayya dani har takaimu ga aure? Wani irinso haka yakemin da zai tsallake duk wank ƙyaleƙyalen duniya da duk abunda yake gabansa ya mallakeni? Shin dama akwai irin wannan soyayyar a duniya? Ni atunanina duk zafin soyayya akwai dalilin da zasu sanya ayi hakuri da ita. Hammood kuma yatara wannan dalilan dayawa da zasusa ya rabu da soyayyata Mai yasa basu ja ra'ayinsa yayi haƙuri da soyayyata ba? Meyasa soyayyata ta rinjayesu basu suka rinjayeta ba? Kenan soyayyar tafi dalilan ƙarfi? Cikin sanyi jiki nace.
"Why do you hide the fact that we're married?"
"We were being vague about the truth saboda hakan Umarnin mahaifinki. I'm sorry"
Na lumshe idanuwa kawai nakasa cewa komai shikuma kallona kawai yakeyi yanaso ya rarrasheni dan yaga alamun kuka nakeson yi. Na tabbata Hammood gaskiya yake faɗa saboda wasu dalilai dayawa da yanzu nake tunaninsu da suka faru abaya. Nafarko Baba ya roƙeni alfarmar zai yanke hukunci akaina har nabashi damar yanke kowane irin hukunci. Ya Ahmad bayan an saka auren Hamma da Aysha ya roƙeni ko nan gaba naji Baba ya yanke wani hukunci da kaina na tsaya na fahinceshi saboda yaƙinin dayake dashi akaina yasa yayi hakan. Sannan ni kaɗai Ya Ahmad ke yiwa faɗa idan bansaka gyale ba hakan yana nufin tun wancan lokacin inada aure. Baban mahaifiyata. (Alhaji Habibu) yayita yimin faɗa daya ganni da ƙaramin gyale bayan duka wanda muka saka girmansu ɗaya kuma sun girmeni. Waɗannan dalilan kaɗai sun isa su saka na zargi wani abun amma banyiba Ya Ahmad, Baba, da mahaifin mahaifiyata sun sanda aure akaina tun wancan lokacin. wancan zuwan Hammood Akwai aurensa akaina kenan? Meyasa toh zasuyi tausata da bani hakuri bayan alkhairi suka aikatawa rayuwata? Meyasa shi kansa Hammood da yasan yafi ƙarfin matsayina yake bani hakuri?l idan da wacce yakamata tabada hakuri nice. bansan dalilin dayasa Hammood yakamu da soyayyata ba sai dai nasan dole zai kasance nice nayi wani abunda yaja hankalinsa gareni har yasanni ya kamuda soyayya? Toh yaushe kenan hakan tafaru?. Kuka na fashe dashi sosai wanda yasa hankalinsa tashi. Kallona ya tsayayi yakasa aikata komai sai can ya tuna abunda zaiyi ya lallasheni. Dawowa kusa dani yayi ya sanya hannu ya jawoni jikinsa a hankali yafara shafa bayana cikin sigar lallashi. Lokaci guda naji nutsuwa ta sauƙamin kukan na shirin tsayawa saboda ƙamshin da nake shaƙa tun bai furta ko kalma wajan rarrashin bama.
"Shhhh is okay"
"No is not nasan cewa jarabawace kawai soyayata gareka babu yanda ka iyane bawai dan ranka yaso hakan ba. Babu yanda za'ayi kaji daɗin soyayyar da kakemin. Bayan babu wani abunda yadace gameda soyayyar. Ta iya yiwuwa ka bayyana soyayyar ce saboda ya kasance babu yanda zakayi da zuciyarka ta rinjayi gangar jikinka I'm sorry nice yakamata nabaka haƙuri koma menene yafaru harka fara sona ni banyi da gayya ba mata nawa suka fini a rayuwarka wanda zakaso dama ace sune kafaɗa soyayyarsu baniba" Ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa yana saurarena. Dafarko shi kansa bai yarda soyayay bace har lokacin datafi ƙarfinsa ya zamana bazai iya jaa da bayaba bazai iya komai ba face fara neman hanyarda zai mallaki abunda yakeso kasancewa da ita kuma yasa ya fahimci hakan shine abunda yafi buƙata a rayuwarsa ya fahimci haske sosai data shigo rayuwarta toh tayaya ma za'ace baiji daɗin soyayyarsa gareta ba? bai taɓa dana sanin faɗawa soyayyarta ba bai kuma taɓaji da wata daban yaso ba itaba. Yacigaba da shafa bayanta.
"No zaynab the best things da suka faru dani a rayuwata is knowing you, being with you and loving you. zan sake faɗa you're the best thing that ever happen to me. zan faɗa hakan a zuciyata. I'll say it loud and let the whole world know. Zan faɗa a yayinda idona yake rufe. Zan kuma buɗe idona na faɗa. أحبك كثيراً Zanyi miki raɗa a kunne zan kuma bayyana a zahiri. I Love you. You are my best. Ina nufin my best out of all the best. أنت أفضل ما لدي. I never regret loving you ko sau ɗaya. And i never felt like da wata naso bakeba. Tunda kika kalli ke kaɗai nakeso zuciyata is attached to you only you zaynab hakan yana nufin gabaki ɗaya cycle na matanda suke tare dani babu wacce takai tasota sai ke. Ki sanyawa ranki isa hold yourself proudly with excellent posture. be more of you Be confident Zaynab. Nabaki assurance cewa kinkai nasoki har kin wuce hakan saboda i felt the luckiest a lokacin dana mallakeki" Nayi shiru ina ƙwance luff ajikinsa ina sauraron raɗarda yakemin a kunnena ko zuciyata ta ƙashi ce dole ta lanƙwasa da waɗannan kalamai nasa bayan kyaun fuska data halitta da shahara da Allah yabashi harda iya sarrafa harshe.
Miƙewa tayi zumbur a wajanda suke zaune jugum-jugum suna jiara abasu damar zuwa ganin Hammood. Ganin miƙewarda tayi da alamun wani abun yasa Anty fadeelah tace
"Rauda Ina kuma zakice?"
"Wallh nagaji bazan kuma iya jiraba dole zanje naga Hammood Haba toh sai dai idan bashi ɗin bane dagaske yasa ake hanamu zuwa ganinsa nifa dama bangama yardaba wallh abun yaƙi kama hankalina Hammood dai? Hammood fa?" saida ƙawarta ta tuntsure da dariya tace.
"Waishi fa sai kace wani abun almara Hammood the whole Hammood taɓ sai dai afaɗawa wani ai ko pic ɗin jiya bawai nagama yarda bane saboda akwai photoshop yanzu haka wani baƙauyen balaraben aka samu ake ƙarya akan Hammood"
"Kai hassada dai batayi ba wallh duk yanda aka samu burbushin hassada a cikin zuciyar mutum ansamu matsala wallh idan baku yarda ba meya hanaku tafiya Yau? Ba kunce yau zaku tafi ba?" anty fadeelah tafaɗa a hasale dan ƴan uwan nata sun fara hasalata kuma duk aysha tabasu ƙofa.
"Ƙure ƙarya' ƙure ƙarya muka zauna yi muga ƙwafƙwaf mutafi mubada labari musamu na ɗaurawa a media"
"Nifa ban yarda cewa abunma ƙarya bane sai danaji ɗatsu suna cewa wai yayi mata peck wannan zancen hankaline dan Allah? Ko yau aka haifemu ai baza'ayi expecting mu yarda da hakanba.
"Ke kingani ni zancen nanma ɓatamin lokaci yake natafi ganinsa pic ɗinsa ma na nemo akan wayata dashi zan shiga yanda zan masa kallon ƙwaf-ƙwaf" anty fadeelah takaici yasa bata hanata ba gara taje taganshi ko zasu samu sauƙin iskanci sai abunsun yayi kamar zai lafa kamar wanda ake zugasu saisu sake fitoda wani feleƙe gashi sunƙi tafiya dukda ƴan uwantane tagaji da zama dasu.
Har lokacin Rarrashina kawai yake nikuma nayi luff ina shaƙar ni'ima yayinda nakeji kamar wanda bacci zai ɗaukeni. Shima yaji daɗin kasancewarmu ahakan shiyasa bai sakeni da garaje ba yacigaba da shafa bayana a hankali da sunan rarrashi.
Kanta tsaye ta shigo palourn dayake sama banrufe ƙofa ba kuma dimun da'imun labulen palourn arufe yaktake
Dafarko kamar bata fahimci yanayin da muke ciki ba bakuma idonta yakai kan Hammood ba saida muka ɗago danjin shigowar mutum. Nayi mamamki danaji anshigo saboda nasan ƴan gidanmu bazasu taɓa shugowa ba. Amma mamakina saiya koma danaga itane dan nasan zatayi fiyeda haka ma. Alokacinda ta kalli pic ɗin wayarta ta dawo da idonta kan Hammood dake zaune muna manne da juna dan farko nayi niyar barin jikinsa idona yana sauƙa akanta na gyara zamana ayanda nake sai dai natashi daga kishingiɗar danayi ajikinsa.
Zubewa tayi akan guiwowinta yayinda numfashinta yake ƙoƙarin barin jikinta ta ƙwala ihu.
"Yeahhh Hammood Hammood wallh shine. Shine Hammood" Mama da suke cikin gida suka jiyo ihunta. Mummy ma tana zaune a ɗakinta tajiyo ihun salati tayi da sanarwa ubangiji.
"Yanzu wace maras jinne a cikin yaranann ta shiga wajansu? Gabaki ɗaya ta rikice tama rasa abunda zatayi gabaki ɗaya. ta ƙaraso wajanda muke.
"Hammood is that really you?"
"Ya jijjiga mata kai alamun tabbatarwa" shirme tafaryi tana masa tana haɗawa da ihu.
"Marmeeyy idan kungama selfie ki matsa nima muyi please. Oh my God I'm so excited" tafaɗi cikin murna. Na ɓata rai kamar bantaɓa dariya ba na murtuƙe.
"Haka yamiki kama da selfie mukeyi?" sai lokacin ta ƙare mana kallo tsaff da fahimci ba zancen selfie ake a Wajanba. wani yawu ta haɗiya ganin yanda ya tallafoni Jikinsa. Itakam tanaga ko yatsarsa tataɓa zatayi sati bata runtsa ba.
"Hammood if it's really you can i please have your autograph?"
"Sure" yafaɗa cikeda tabbatarwa tasaka ihu yeeahh yayimin magana tafice aguje. Alokacins ihunta ya ishi sauran su duka suka fito harda Maryam.
"Wallh wallh tallhy Hammood ne Hammood dai da muke kallo TV shine acikin can" ta nuna plaourn Baba.
Su duka suka ɗugunzuma ciki yayinda tatafi ɗauko abunda zaiyi mata autograph ɗin ajiki. Sanƙamo abunda zaiyi mata ajiki tayi tadawo ta gudu kamar wata mahaukaciya. Ta gudu ta wucesu basu kaiga shiga ba tashige ciki.
Alokacin yatashi yakoma kan kujera nima na canja wajan zama tashigo ta miƙa masa sai ɓari take kamar mazari. Takasa zaune takasa tsaye yana miƙa mata ga amshe haɗeda miƙo masa Hannu su gaisa. Zuciyata naji tayi baƙi Daga wajan da nake natashi na buge hannunta naci fuska.
"Idan kingama abunda kikeyi saiki fita muna magane ne" bataji haushin abunda na faɗa mata ba haka tafara roƙon ko rigarsa tataɓa. Aikuwa saida ta taɓashi tasake sakin ihu.
"Jaka" shine abunda nafaɗa a raina baƙin ciki da takaicinta ya cikani. Sauran sun tsaya a waje suna taraddadin shiga tukunna. Daga ƙarshe dai suka saka kai suka shigo. Wacce keson Yaya Habibu tana kallonsa sai ji mukayi luuu ta zube sharaf ta sume. Saida suka sanya mata ruwa tukunna. Daga ƙarshe kifa kaina nayi akan kujera ina jinsu sunata shirme saida Mummy ta kirasu a waya ɗaya bayan ɗaya tayi musu babu daɗi sannan suka fita rai baiso ba. Rauda wacce yayiwa autogrp suna shiga abunda tafara searching shine Autogrph ɗinsa a onine ta tabbatar nasanne. Rungumewa tayi ta ƙwanta sai surutan bazan takeyi. Bayan sun fita naji ya taɓani. suma abunsu shikuma hankalinsa yana kaina.
"You can get up they're gone" A hankali na ɗago kaina looking Embarrass bayan shirmen da nayi gashi sun ɗaura wani akan nawa wanda yafi nawa ma gara nima za'ace tunda da soyayya zaimin kallon hankali ta iya yiwiwa hakanma ya burgeshi amma sufa? Ni kaina sun bani haushi.
Nayi ƙasa da kaina.
"They're not my sisters ba ƴan uwana bane we're not related" saida yayi murmushi sannan yace.
"I know nasake ƙwantarda kaina haɗeda sauke ajiyar zuciya naɗanyi ƙara kaɗan dan abun idanna tuna sai naji kamar nasaka ihu.
"Don't worry I"m used to it. Kusan mutane dayawa haka suke tarɓata a yayinda muka haɗu shiyasa nace you're different the way u react alokacin a kika fara ganina bantaɓa kallon kamar hakanba a shekaruna danayi ina haɗuwa da mutane masuson ganina. It annoys me to see people reacting like that when they saw me but that was then yanzu i get used to been welcoming like that. Inason mutane suyi treating ɗina like a Normal human being ba kamar wani mutum na daban ba.
ووالدك اخوك وجدك
your father, brother and your grand father wajansu nafara samun wannan karramawar. Sai kuma ke aranarda muka fara haɗuwa" shiru yayi alokacinda murmushi ke suɓuce masa. Na zaro ido. Shikeann shirmenda nayi yake tunawa yana dariya. Nakoma na sake rufa fuskata.
Saida yasake magana sanna na ɗago. Idon nakan hancina da yayi jazir. Yatsa nasa akan hancina