Header Ads
Showing 120001 words to 123000 words out of 171869 words

Chapter 41 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1371

Ads at the middle of Article

na sayawa maryam da Anty fadeelah sai ɗai-ɗaiku da baza'a rasa ba. Anty ma taɗauki abunda takeso muka gama muka fito Yaya habibu yaja muka koma gida.


Ina shiga na cirewa Anty Fadeelah nata na bar nawa dana maryam. Mama tayita yimin faɗa akan kashe kuɗin danayi tana faɗin.


"Dan shirme daga yabaki ATM saiki kama ki kashe kuɗin ciki marmeeyy babu ko dan kawaici idan yaga kuɗinda kike kashewa fa?"


"Bazai gani ba Mama komai da layina ya saitashi" kuma dagasken bazia gani ɗinba domin komai da nata ya saida babu abunda zai shugo wayarsa.


"Dukda haka Marmeeyy wannan sayayyar tayi yawa"


"Hmm ai bakiga komai ba sai kayanda tayi sayyaya ya iso"


"Bayan wannan akwai wasu kayan kenan?"


"Suna hanya dan tun kafin mu taso anfara ɗaurasu a mota"


"Allah yakyauta" kawai Mama tace




Sai bayan kusan 2hours lokacin ana kiran la'asar kafin kayan ya iso. Mama batace komai ba amma abun yabata mamaki sai dai bazatace nayi laifi ba tunda mahaifina na taimaka.


Aysha takira Hamma akan yazo sutafi amma marmeeyy bazata jeba. Data tambayi dalili tace sai yazo zata faɗa masa. Muna zaune mukaji shigowar Maryam tacewa Aysha ta shirya yana ƙofar gida su tafi. bayan aysha tashiga ɗauko kayanta maryam ta dubeni.


"Babe kinsan wai mutumin zuwa yayi wajan Abba ai abasu ni su tafi dani? Sai kace wata ƴar tsana wallh nima gara Yaya habib yafito muyi aurenan muhuta bayan muntafi ki faɗawa Mama dan Allah.


"Kafin kitafi zan faɗa mata dai maras kunya"


"No dan Allah ki rufamin asiri ki bari saina tafi" naja tsaki nayi ɗaki kayanda na siya mana na ɗebo nata a bags guda biyu na miƙa mata.


"Menene wannan?"


"Idan kikaje kika buɗe zamuyi waya amma yanzu kije suna jiranki" amsa tayi tamusu sallama suka tafi. Tana shiga Hamma ya nuna mata ɗakin da zata zauna tashiga ta ajiye kayanta. Aysha taso su zauna ɗaki ɗaya da ita.


Anan tafara duba kayayyakin dana bata. Kayan sunyi mata kyau sosai tana gama buɗewa ta kirani.


Na ɗauka muna magana kenan Hamma yashigo fahintar cewa dani take waya ya sanyashi ƙarɓan wayan ya kara a kunne."


PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Bai bata damar da zata faɗamin ya amshi wayar ba ya karɓe yakara a kunnensa. nikuma a lokacin magana kawai nake banjira amsarta ba.


"Mama ai tanata faɗa wai naje na kashe kuɗi kumafa shi bayani yace nayi amfani dashi duk abunda zanyi nayi dashi komai nakeso karna tambayi Baba kinga ai dama yanzu duk wani hakkina yana wuyansa Kuma Baba yana buƙatar hutu" harna ƙarashe magana nayi shiru batace komai ba. Shikuma yatsaya yana auna maganata a ma'auni yana nazarori akan maganata.


"Babe kina jina?"


"Bata jinki Da Abubakar kike magana. karki kashemin waya ki tsaya muyi magana" Yafaɗa bayan ya tabbatar zan iya kashewa ɗin. gabana yafaɗi damm jin muryar Hamma mai zaiyimin daya amshi wayar? Wai meyasa Hamma baya kaucewa abubuwanda zasu jawo hatsaniya a tsakani? Mai yasa yakeyin wasu abubuwan da zasu shiga tsakanina da ƴar uwata?.


"Marmeeyy waye shi wannan da kika magana akansa?" batareda wata tsoro ba nabashi Amsa.


"Hammood ne?"


"Menene haɗinki da Hammood?" bansan dalilin dayaaa yake yimin tambayoyi ba dan dai nasan babu abunda zasu amfaneshi dashi amma yazama dole na tsaya nayi masa bayani dan naga alama Aysha bata sanar dashi komai gameda aurena ba, toh ko tanajin kunya tace masa Hammood ne mijina?"


"Mijinane shine dalilin fasa aurena dakai a yanda aka faɗamin an daɗe da ɗaura aurena dashi a lokacin da akazo neman aurena Baba yayi musu bayani shine suka nemi a maida auren akan Aysha. Kuma Aysha ƴar uwata ce duk wani dalili da zaisa ka soni Aysha tana dasu" ban kaiga gama maganataba ya katseni.


"Kina sonsa kenan?"


"Eh" nabashi amsa kai tsaye" saida yaji zufa sun keto masa dan baiyi tunanin zan iya faɗawa soyayya lokaci guda haka bayan rabuwata dashi ba.


"Marmeeyy kai tsaye kika amsamin kina son wani namiji baniba bakisan hakan zai cutar dani ba?" dama duk soyayyar da mukayi ƙaryace kenan tunda har zaki iya faɗawa soyayya a ƙaramin lokaci bayan rabuwata dake." na girgiza kai kamar wanda yake kallona.


"A'a wallh ba ƙarya bace Allah yagani har zuciyata nake tare dakai kuma na soka amma yanzu babu amfanin wannan son dole na fiddashi araina dan gudun faɗawa halaka kuma banga dalilin dayasa soyayyarda nake yiwa mijina zai cutar dakai ba bayan kanada taka matar kuma kalar soyayyar daka nuna mata bai cutar dani ba" yagane abunda nake nufi sai yayi shiru yana nazarin maganganuna.


"Hamma dan Allah daga yanzu ka ɗaukeni matsayin Maryam idan bazaka iyaba ka ɗaukeni matsayin ƙanwar matarka wanda hakan shi yazame dole karka jawo dalilin da zai kawo rashin jituwa tsakanina da ƴar uwata karka zama sanadiyyar raba zumunci na roƙeka dan Allah nidai ina son zaɓinda Allah yayimin yarage maka ka zauna da matarka Lafiya ka sota ka ƙauneceta ka gina rayuwarda gabaki ɗayanku zasuyi alfahari ku gina rayuwarku kicin aminci kamar yanda nake ƙoƙarin gina tawa rayuwar" Zama yayi a gefen gadon baisan lokacijda murmushi ya suɓuce masa ba. Tabbas yayi rashin mace mai nagarta ita Marmeeyy sam batajin nauyin sakin abunda yake bakinta har indai hakan shine abunda ya kamata ace tafaɗa.


"Toh Marmeeyy naji nagode in sha Allahu zanyi yanda kikaje har indai ta dalilina ne bazaki sake samun matsala da ƴar uwarki ba sannan zanyi duk iya ƙoƙarina wajan ganin nasota na ƙaunaceta kamar yanda kika buƙata" dariya nayi daga cikin wayar dan naji daɗin yanda Hamma ya ɗauki lamarin da sauƙi kodan dama da alamu yafara son Aysha sai dai yaƙi bawa kansa damar da soyayyar tata zatayi ƙarfi. Ya miƙawa Maryam wayar.


"Idan kungama kifito muci abinci muna jiranki" Aysha batasan fitowarsa ba taɗauka yana ɗakinta hakan yasa tana fitowa tawuce wajab Maryam a baƙin ƙofa ta tsaya jin yana waya tagama sauraren duk wani abinda zai faɗa sannan tajuya taje ta zauna. Yana ganinta ya sakar mata murmushi ya zauna kusa da ita cikeda kulawarda bai taɓa ƙwatanta mata irinta ba yace.


"Yaya jikin naki?"


"Dasauki"


"Toh Alhamdulillhi Allah ya ƙara miki lafiya" ta amsa da amin" cikin ranta kuwa tana tunanin wato koda ace marmeeyy ta sallami soyayyarsa yanajin maganarta dan bataji abunda tafaɗa ba amma tagane cewa tayi masa magana akan su zauna lafiya. Toh yanzu Marmeeyy ba dole ta nemi duk yanda zatayi ta raba kanta da Hamma ba? Tunda tasamu duka ɗauka. Saida Maryam tagama waya kafin tafito Aysha ta saki jiki da ita sosai.


Akai-akai Hammood yakemin message amma bai taɓa kira ba ko sau ɗaya ganin yatafi ya manta dani sai zallan message yasa nima na ɗebeshi na watsar ko tunaninsa banayi nasa kaina a zancen makaranta kawai tunda exam ƙaratowa take."


Rabarda za'ayi match ɗinsu gabaki ɗaya gidanmu da wanda suke kallo da wanda basa kallo saida muka zauna kalla. Bayan yaci ball ka kalli camera yayi murmushi haka kawai jikina yabani dani yake murmushin. Kuma hakanne yasan dole ina gaban tv ina kallonsa yasa ya aikomin aiken murmushi. Ina kallon ball ne amma hankalin akan Hammood yake ina tunanin komai na Hammood kalan burgewa ne na kalli March ɗinsa abaya dayawa kuma salon balla ɗinsa akoda yaushe burgeni yakeyi amma bantaɓa sanin salon yakai haka burgewa ba sai yau. Aka tashi a match sunyi nasara aranar na wuni da farin ciki. Har text saida na tura masa a lokacin yayimin relpay naɗauka zai kira amma baiyi hakanba inason jin muryarsa amma bazan taɓa iya kiransa ba idan bashi ya kirani ba. Bayan gama match ɗin ƴan jarida suka shirya hira da Player ɗin saboda tarin nasarorin da suka samu kowanne da lokacin da za'a zanta dashi. Bayan gama duk wani hira da Hammood abunda yashafi ball dakuma nasarar daya samu dalilin ball sai wani ɗan jarida ya jefo masa tambayar da mafi yawanci daga cikinsu suke son yimasa." bayan sunyi masa tambaya akan jita-jitan da take yawo akan yayi aure menene gaskiyar lamari. Alokacin ya shaida musu cewa yayi aure wannan dagaske ne sun nemi sanin wanda ya aura amma ya gwada musu wannan private life ɗinsa ne bayida niyyar nunawa matarsa a duniya kowa ya santa ita matarsa tasace shi kaɗai batareda duniya ba. bayanan da yayi musu Ya gamsar dasu amma duk da hakan akwai masuson sanin wacece ita.


Gabaki ɗaya wannan lokacin abunda yake yawo a kowace kafa ta sada zumunta kenan saida aka ɗauki tsawon lokaci ana zancen ni bansanma sunayi ba gabaki ɗaya na tattara hankalina na maidashi akan karatuna. Nadaina shiga kafafen sada zumunta gabaki ɗaya dan saƙonni nake taras dasu Ba adadi gabaki ɗaya mutane sun yanke hukunci cewa nice matarsa batareda sun samu tabbaci ba inaji ina gani account ɗina ya gagareni amfani sai gani sai bari."


Hamma yake kawo Maryam makaranta kullum sai takoma da kanta. Ranar kawai sai gashi tazo ita kaɗai bayan angama lactures munfita zuwa cafeteria. Muna zaune na dubi maryam.


"Yasu Aysha?"


"Aysha kam ai sai dai ki kirata ki tambayi yanda take ni tun jiya nabar gidan kuma bazan sake komawa ba Hamma baida kunya zaman gidan da nake ma babu amfani dan Hamma ba barinta zaiyiba kamar tsohon maye har korata yake ya aikeni aikarda babu gaira dalili ƙarshe ma sai yadaina Aikata Ina gidan yake komai danaga abu ya isheni nabar gidan jiya amma wallh inajin tausayinta kullum ƙarewa takeyi gashi sam batada kuzari. Aina faɗawa Ummi itadai da jininta baj haɗu dana Ayshan bace amma nace mata ta ɗaukota tadawo wajanta da zama"


"Allah ya kyauta amma Babe dakin daina cemata Aysha gatsau matar Hamma ce fa" yatsina fuska tayi.


"Bazan daina ba tunda kema ai Ayshan kike cemata kuma ko kema dakin auri Hamma Marmeeyy zance miki"


"Toh Allah ya shiryeki" ta amsa da amin.


"Babe wai yaushe Hammood zaizo ne?"


"Saina gama exams" Toh Allah yabada sa'a Babe ina tunanin yanda zanyi rayuwa kina wata ƙasa can daban" Shiru nayi mata dan nima bansan yaya wannan lokacin zai kasance ba toh dan haka mubar zancen muga zuwan lokacin.


Bayan 2weeks Aysha tayi miscarriage duka mukaje muka ganta daga nan aka dawo da ita gida tayi 2days sannan aka maida ta gidanta gabaki ɗaya ta rame ta zabge sai ƙashin wuya."


Cikin hikima ta ubangiji muka fara zana jarabawa a cikin sati biyu muka gama Alhamdulillhi kuma kowacce jarabawa tayi daɗi sosai dan karatun kawai mukeyi ga addu'a da kullum muke samu wajan iyaye.Hammood kullum shima yana cikin turamin sinƙin addu'oinsa. muka zauna muna jiiran result naji daɗin zuwan ƙarshen karatunmu duk da ni nasan bawai nagama bane inada outstanding course guda ɗaya. Kullum cikin taraddadin rabarda Hammood zaizo nake ina tunanin yanda zan tafi nabar dangina nafara rayuwa cana wajan wasu mutane wanda al'ada da yaranmu ba ɗaya ba idan natuna har kuka nakeyi."


PAID BOOK


Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab m Bawa JAIZ BANK Ko katin MTN ta wannna lambar 08161146563 shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."




ZAYNAB ALABURA


Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun banking Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya






Ganin halin da nashiga mama ta tausayin dan ko ban faɗa ba tasan abunda yake damuna bazia wuce tunanin barin gida ba ita kanta abun bai dameta abaya ba sai yanzu dataga lokacin tafiyar sai ƙaratowa yake. Kuma gashi tunda aka fara zance akan wannan lamari bantaɓa yimata maganar ba itama haka batayi minba jira take nafara mata zance kamar yanda nima nake jira tafara yimin. Cikinmu Babu wanda yasan abunda yake zuciyar ɗayanmu."




Muna zaune nida Anty fadeelah muna hira wayarta tayi ƙara tana dubawa taga Aysha. Amsa kiran tayi takara a kunne bayan sun gaisa naji Anty fadeelah tana faɗin.


"Subhanallahi Wane asibitin kuke?" bayan ta sanar da ita asibitin da suke tace.


"Toh barina sanarwa Mama" ta kase kiran ta kalleni.


"Wai Aysha fa ba lafiya suna asibiti yanzu haka"


"Subhanallahi Allah yabata lafiya toh ki faɗawa Mama sai muje mu dubata" ta sanarwa su Mama muka shirya gabaki ɗayanmu muka nufi asibitin 1month 2weeks kenan dayin ɓarinta amma tasake wani ɓarin dama ni dake rabona da ita tun wancan ɓarin da tayi tazo gida ta ƙwana biyu bayan ta koma tazo sau biyu ina makaranta harta tafi bamu haɗuba.


A wajanta muka samu Ummi da Maryam sai bayan munje kafin Ummi tatafi Maryam kuma muka zauna da ita Mama anty da Mummy suka koma sukabar nida Anty fadeelah da Maryam.


Lokacin da suka tafi tana bacci taba farkawa taga basanan ta fashe da kuka daƙyar muka rarrasheta tayi shiru takira Mama tana kuka akan tadawo Mama tace zata dawo amma sai Yamma. Da yamma kuwa Mama tadawo da abinci shikuma daga gidansu shima yakawo abincin. Mama bata kwana a sibitin ba suka tafi itada Anty fadeelah tace na zauna mu kwana tare banso zamaba tunda bawani shiri muke da Aysha ba amma babu yanda na iya. nida Maryam muka kwana wajan 9:00pm Hamma yashigo asibitin muka fice a ɗakin muka barsu zuwa wani waje daban. Ina gefe har Maryam suka gama waya da Yaya habibu sannan ta dubeni.


"Dan Allah Marmeeyy kimin wata alfarma guda ɗaya ki faɗa agida aturo Yaya Habibu kunya yakeji wallh kuma kinga zaman haka babu amfani kullum fa sai yace zai faɗawa mam ta faɗawa Baba sai yace yakasa wai sai yashiga yaji bazai iya ba yace nayiwa Ummi magana toh dan Allah ina aka taɓa yin haka? Ummii zan yiwa magana kenan tayiwa Mama magana? Kinga hakan ai baiyi tsari ba dan Allah kiyiwa Mama magana"


"Ke me ya hanaki mata magana? Sai nice zanyi mata magana?"


"Toh dan Allah idan bake ba wazan samu nayi mata magana? Saboda ina saka ran zaki taimaka shiyasa na miki magana" tafaɗa idanuwanta sun cika da hawaye.


"Toh naji idan muka koma zan faɗawa Mama saita samu Baba Amma kisani ba lallai ayarda da yiwa Yaya habibu aure kai tsaye bayan ƙarancin shekaru ga rashin aikin yi, shi kansa yasan da hakan shiyasa bai yarda yaje yasamu wani da zancen ba" tayi hugging ɗina tana faɗin.


"Ni in hardai zakije toh babu damuwa dan nasan Mama bazata ƙiba tana sona sosai"




"Allah yasa shine kawai abunda nafaɗa". Sai wajan 10 kafin yafita a ɗakin. Washe gari sassafe aka sallamemu shi yazo yakaimu gida dan jikin nata babu ƙwari sai Ummi tace yawuce da ita gida kawai.


Su Mama dama hakan sukaso dan jikin nata babu ƙwari amma bazasu iya tambaya ba sai sukayi shiru gashi kuma An kawota gida.


Harna manta da zancen da Maryam tayimin sai bayan ƙwana biyu kafin nasamu Mama nayi mata magana. Batacemin komai ba dan haka bansan abunda take nufi ba ban bawa maryam wani feedback ba sai bayan ƙwana uku naga Ansiyo goro Ashe da Mama tasamu Baba da zancen yace Yaya za'ayi yayiwa Habibu sure a yanzu? Bayan ƙarancin shekaru ai baida aikin yi. Amma zaiyiwa aikawa Alhaji habibu Magana. Da Alhaji habibu yaji abunda Baba yaje masa dashi sai yace. Babu komai tunda yagama karatunsa zai sama masa aiki kafin lokacin aure idan aiki bai samuba zai bashi jari mai ƙarfi yanda zai kama ƙasa dan haka yanzu babu damuwa akai tambayar kawai tunda tambaya ai ba itace aure ba daga baya sai ayi maganar aure. Baba ya anince da shawarar Alhaji habibu san haka cikin 3days ɗin aka siyo goro. Tunda nakira maryam na faɗa mata za'a kawo take ihun murna godiya kawai take surfamin. ankai tambaya. Ranar Maryam murna kamar zata goyani shi kansa Yaya habibu saida yayimin godiya.



Saida Aysha tayi sati ɗaya agida sannan yazo tafiya da ita har shiɗewa takeyi tsabar kuka sanna tace babu yanda zataje babu irin rarrashin da Ba'ayi mata ba amma tace bazataje ba magana har gaban Baba. Baba ya roƙi yabarta ta sake sati guda hakan akayi nanma da akazo tafiya da ita tace bazata jeba har faɗa Baba yayi mata tace batta zuwa ko'ina saida ran kowa ya ɓaci agidan. Baba ne yace su Mama su zauna da ita suji matsalarta. Daƙayr suka sanya tafaɗa musu abunda yake damunta. Mama tasamu Baba tayi masa bayani. Gabaki ɗaya sun rasa yanda zasu ɓullowa lamarin daga ƙarshe hakuri da Lallashi kawai akayita mata takoma sannan suka bata shawarwarin daya kamata ace sun bata mukanmu tausayi take bamu yanzu dan abun yana damunta kuma tasakashi aranta hakan yasa sai ramewa kawai takeyi.


Hammaood baizo Bayan mungama exam ba sai bayan Babbar sallah harda wata guda sannan ya turamun message akan akowani lokaci zan iya ganinsa babu wanda na sanarwa sai zallan damuwa dana sakawa raina bansaniba ashe ya rigada ya sanarwa Ya Ahmad da Baban shi kansa.


Ko Baba saida walwalarsa ta canja sannan sun shirya akan idan tafiyar tazo zamu tafi tare da Mummy da Anty fadeelah da Yaya Habibu zasu ƙwana biyu acan suga yanayin yanda wajan yake sannan kafin su dawo Ya Ahmad zaije ko bayan sun dawo dan Baba yadamu sosai yace

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads