Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 171869 words

Chapter 13 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1074

Ads at the middle of Article

bana iya amsawa ba. Sai faɗamin yanda zamu gudanarda rayuwarmu bayan aure yakeyi da Uhm da Eh kawai nake binsa" Baby kinsan abunda nafiso jikin mace" magana ɗaya yayi ya sanyani saurin faɗin.


"Hammmma!!! Ni bacci nakeji"


"Okay ba damuwa yi baccin gobe idan mun haɗu saiki saina faɗa miki ido da ido" na runtse idanuwana haɗeda sakin murmushi inajin kunyarsa da ƙaunarsa acikin raina nace.


"Hamma dagaske nake bacci nakeji" saida yaɗan ɗauki lokaci sannan yace.


" okay yi baccin Good night I love you"


"I love you too" na faɗa. Sai bayan nafaɗa tunanina ya kawomin abunda nayi. nayi saurin datse kiran tunda muke dashi ban taɓa cewa ina sonsa ba bawai dan banayi ba Sai dan matuƙar kunyarsa da nakeji. Shima kansa yasan inasonsa amma bai taɓa tunanin jin kalmar abakina a wannan lokacinba. Yayi murmushi haɗeda ajiye wayar. ni kaina banyi tsammanin zan iya faɗa ba ji nayi kawai ta suɓuce abakina" Murmushi nayi haɗeda rungume wayar nace.


"Ina sonka sosai Hamma na" Daga saman kaina naji Anty fadeelah tana faɗin.


"Iyyeh waye kuma Hamma? Lallai Hamma yayi kasuwa ya sace zuciyar wannan babysis ɗin" nayi kici-kici nace.


"Sace zuciya kuma? littafin Hausa fa nake karantawa shine yafito fili" ta zauna sannan tace.


"koba littafin Hausa ba? Nace.


"shifa"


"Happy littafin Hausa. lallai ma yarinyar nan kin rainamin hankali ina jiyoki cikin waya kina cemasa i love you too kika kashe sai murmushi kikeyi irin wacce ta daɗe da nutsawa a soyayya. Wai har shekarunki nawane da kikasan soyayya? Ke wallh da kina tareda Mummy dakin gane kuranki" Na sake kicin-kicin na haɗe rai nace.


"wai dama tsayawa kikayi kina sauraron wayata wallh babu kyau toh nidai babu ruwana" yanayin yanda nayi maganar saida yasakata murmushi tace.


"Yi abunki wallh kina samin miji kiyi aure ni kaina auren nakeso amma kinga Mummy ta nace sai nayi karatu haka nayita faɗuwa a jarabawa karatu ya gagara niga yanda hankalina yake can daban itama yanda nata ya karkata daban gashi ɗaya yaƙi yiwuwa Wai tana cewa ita bata samu ta ƙarasa karatu ha dan haka bazata yarda ƴarta tayi aure batareda tagama karatu ba. amma kingani yanzu muna dai-dai ta magana zan turoshi wajan Baba. Daɗin uba kenan" Cikin raɗa nace mata.


"waye shi"


"Wa fa? Ta tambaya


"Wanda zaki turo wajan Baban mana"


"ji yarinya da wayo ke kin faɗamin waye Hamman da kike waya dashine?" Na girgiza kai cikeda nishaɗi jin sunan Hamma kaɗai yana sauƙarmin da nishaɗi nace.


"Zan faɗa miki amma kiyi alƙawari bazaki faɗawa kowa ba"


"Nayi alƙawari bazan faɗawa kowa ba" Na jijjiga kai sannan nace.


"Yayan maryam ne ƙawata ya matsa zai turo amma nace yabari saina gama exam wannan semestern"


"ko meyasa" ta tambaya.


" zuwa lokacin nakusa ƙare makaranta kinga kar suna zuwa suyi maganar aure baba kuma baida kuɗi da karatunmu zaiji koda aure? Kinga yanzu idan sukazo bayan gama exam ɗina kafin ayi maganar aure nagama karatu zuwa lokacin nauyi ya ragu akan Baba"




"Lallai kinyi basira Allah yakaimu lokacin" nace.




"Amin" na ɗauko wayata na nuna mata pic ɗinshi tace.


"Kai ma sha Allah hamma ya haɗu ashe dole ki kwarewa soyayyarsa banga laifinki ba so abunki"
Nayi murmushi nace.


"Ai saima kin ganshi afili" cikeda jinjinawa tace.


"Au Allah" nace.


"wallh kuwa" Muna cikin ƙus-ƙus Aysha tashigo sai mukayi shiru muka canja zance ta taɓe baki haɗeda Miƙawa Anty fadeelah riga tace.


" gashi" ta amsa ta Canja zuwa kayan bacci sannan Muka ƙwanta."






-----------

Wani irin nishaɗi yakeji wanda bai taɓajin makamancinsa ba. P.A ɗinsa dake front seat ya juyo ya kalleshi saboda yanda yakejin sautin murmushinsa akai-akai. Shima murmushin yayi sannan yace.


"Mood sir" ya ɗago ya kalleshi batareda ya amsa ba yacigaba da faɗin.


"Bamu kaiga samun abunda ya kawomu ba amna kana cikin farin ciki ko meyasa?" Saida yayi murmushi sannan yace.


"وثق" trust
"صدق" Believe.




I believe and trust in Allah inada hope bazan bar ƙasarnan batareda cikar burina ba she'll be mine in sha Allah" P.A ya jijjiga kai yace.


"Babanta nada tsauri yaƙi yarda a tsaida magana bansan abunda yake tunani akanmu ba. Bayan irin mutanenda ya haɗu dasu a jiya banyi tsammani tun ajiye zaiƙi ba. Gashi yau katashi mukaje muka sameshi har gida amma magana bata tsaya. daga ƙarshema cewa yayi zaiyi tunani abashi lokaci kafin ya yanke hukunci"


"Eh yanada gaskiya barshi ya ɗauki lokacinsa I'll wait. har indai zai cikamin burina and atimes yanada sauƙin kai. Nunawa nayi inason cin abincinda yafito a hannunta ya sanya tayi akwai hope akan zaiyi tunani mai kyau. Tunda yace he's my biggest fan."
P.A yace.


"May be" danshi dai bai taɓa tunanin bazasu samu abunda sukazo nema a bugun farko ba saida ya leƙa yaga anyi jiya anyi yau abun tun yana bashi mamaki yafara bashi tsoro"





"Mood sir ina gani basai kaci abincin da ka saka akayi mata ba meyasa bazamuyi order wani wajanba?" Lumshe idanuwansa yayi ya jingina jikin kujera kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace.


"Ita kaɗai zuciyata ta yarda da ita" bayan hakan hai sake cewa komai ba har suka isa masauƙinsu.




8:00am mukeda lactures dan haka sassafe nashirya shiga makaranta Maryam ta kirani da zasu fito nace tabari zanzo dakaina. Tace.


"kinsan halin Hamma ai bazai taɓa yarda ba yanzu hakama ya shirya ni yake jira" ni dama nagama shiryawa dan haka nazauna ina jiran zuwansu. Da suka iso ta kirani nayiwa Mama sallama na fice Maryan harta koma Baya kamar yanda tasaba yanzu banso na sameta a baya ba da bayan zan shige dan yau kunyar Hamma nakeji. Suluf-suluf nashige na gaisheshi yana kallona amma sam naƙi kallon yanda yake murmushi yayi daya gane kunyarsa nakeji sai dai baisan kunyar ta menene ɗaya ba, ta sakin layin da yayi jiyane kota cewa da nayi ina sonsa.


A bakin gate na school ya ajiyemu Maryam ta fita harna saka ƙafata waje na juyo na kalleshi. Shima ni yake kallo dan haka nayi saurin yida kaina ƙasa nace.


"Hamma nayiwa Antyna maganarka.
yanzu agidanmu akwai wanda yasanda tarayyarmu" yayi murmushi yace.


"naji daɗi sosai nagode ahaka har Baba zai sani wata rana. Dariya kawai nayi ina ƙoƙarin fita yace.


"Bakicemin kina sonaba zaki tafi" Nace.


"Ai kasan inayi" nafaɗa hakan alokacinda nake ƙarasa fita. Maryam tana tsaye tana jirana ina ƙarasowa tace.


"Kukam dai sai gyaran Allah abu ba kunya sam ba tsoron Allah kuyita kallon juna kuna sakin murmushi gaban mutane aiko wanda bai saniba daya ganku zaisan kuna soyayya" Nace.


"kefa bakida Hankali idan bamuji tsoron Allah ba kinaso muji tsoronki ne?"


"Ke dai Allah yayi banza tafaɗa haɗeda wuce nima nabita abaya har muka ƙarasa lacture hole."


Zaynab Alabura


*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*






Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya.




Lacture ɗaya mukayi muka dawo gida kasancewar ranar friday ana tashi muka fita gate kawai kowacce tahau abun hawa batareda munjira anzo an ɗaukemu kamar aka sababa.


Da motar Yaya Ahmad naci karo a harabar cikin gidan, aɗakin Mama na sameshi da alamun isowarsa kenan ko wajan Baba bai ƙarasa ba nashiga da fara'ata ina gaidashi yace.


"Marmee har andawo daga makarantar?"


"Eh yaya lacture ɗaya mukayi yau Friday dama bamu cika daɗewa ba" yace toh Allah yataimaka bari nashiga ciki naduba Baba. Mama tace.


"Babanku yafita ɗazu amma yace bazai jimaba saƙo yasamu na gaggawa ayanda ya sanar dani" Yaya Ahmad yace.


toh barin fita kafin yadawo nima zan dawo" Dasauri nace.


"Yaya dan Allah bari nazo ka ajiyeni gidan Hajiya (Maman Baba) rabona da gidanta na daɗe bazan iya tunawa ba" yatashi yana tafiya yace.


"kiyi sauri" mama tace sai kiyiwa ƴan uwanki magana ina tunani tunda suka dawo ko sau ɗaya basu taɓa zuwa ba" nace.


"Toh" namiƙe nayi ciki nayi musu magana dasaurinsu kowacce taɗauki mayafi dayake dama sun gaji da zama Jiya ko makaranta basu fita ba hakama yau saboda tsoron abunda Mummynsu zata iya aikatawa. kaya kawai na canja nasaka Hijabi Nafito Mama tabamu mai da sinƙin sabulai sai abincinda tayi ta zuba a cooler tace akai mata dama akai-akai ana kai mata abinci. acikin mota muka sameshi.


"Abakin ƙofa ya sauƙemu yace ku gaisheta" da Mamaki nace.


"Yaya bazaka shiga ba? Aikuwa bazataji daɗi ba saida ya kalleni kamar mai nazarin wani abun sai kuma yace.


"Nafi shekaru ban leƙata ba nasan yanzu idan naje sai tayita mita nikums banaso" nace.


"Yaya kabarta tayi mitarta na lokaci ɗaya yashige gaba sai ka gyara kana zuwa ganinta akan lokaci. Amma yanke zumunci babu kyau" batareda wani tunani ba yace.


"muje toh" Daga baya Anty fadeela tace.


"Marmee hoo sarkin iya tsara zancen da magana kenan. idan kina zubo da zancennan na tabbata babu wanda bazai saurareki ba. Wannna bakin naki inaga babu wanda bazakicishi da zance ba zanso ki haɗu da Mummynmu naga ko bakinki zaiyi aiki akanta" Harararta Yaa Ahmad yayi yace.


"ke kifara haɗuwa da Mummyn kiga yanda zata kaya muku zaɓar rashin hankali ma a blacklist kuka sakata idan bazaku dawo ba kufito kuce mata bazaku
dawo ba mana amma yanzu mummy tana wuya daku yanzu haka ita ta turoni na tafi daku" Anty fadeelah taturo baki tace.


"wallh banzuwa ko'ina" yace.


"toh saiku gaya"


"Allah yaya dama mata dama ace idan mungaya mata zata yarda ta barmu ne saimu zauna yimata bayani" Aysha tace.


"Taɓ wallh ban binka. zama ka koma kamar yanda kazo kuma Babama yace ba yanda zamuje" yaja tsaki.


"mtswww uwar ƴan tsiwa komai bazaki faɗeshi da ladabi kamarna ƴar uwarki ba" Aransa yana mamakin wai Babane zaice su bazasu koma ba sai Babandai yadawo zaiji kanun labarin. Suka fice dukansu suka shiga cikin gidan.


Hajiya tasake aure bayan shekaru da ɓatan Babansu Baba amma bata samu haihuwa ba. Sunyi shekaru da mijin kafinnan Allah ya ɗauki ransa bai daɗe da rasuwa ba. babu yanda Baba baiyi akan zai ɗaukota gidansa ba yaran mutumin suka hana. Sunce suma tazama mahaifiyarsu tunda anyi zaman mutumci yazama dole su riƙeta, tana zaune yaran duk abunda suka yiwa mahaifansu itama sunayi mata. Babban gidane sosai shashi-shashi kowacce sun zuba mata ƴan aiki. Da sallama muka shiga dake nice agaba nita fara hangowa tana kallona tafara faɗin.


"Idonki kenan ja'irar yarinya ɗazu da ubanki yazo gaisheni nagama yimasa akan rashin zuwanki. ta iya yiwuwa ma shi yayi miki magana kikazo. Habibu ɗan arzkiki daga dawowarsa sansa huɗu acikin gidannan" na ƙaraso ciki ina faɗin.


"mukuma ƴaƴan tsiya koh?" tace.


"kyaji dashi ni dai bance ba ai fitinanniya" tana hango Yaya Ahmad wanda shi tagane tayi salati ta sanarwa ubangiji.


"Laha'ila ha illalahu Mahammadar rasulillhi Wa nake gani kamar amadu?" muka ƙarasa ciki Yaya Ahmad shidai murmushi kawai yakeyi" Tana kallonsu fadeela tace.


"waɗannan fa? Ƙannenka ne Ahmadu?" Yana amsa mata ta fashe da kuka tana faɗin bantaɓa tunanin zan sake ganinku kafin Allah yaɗauki raina ba. tana kuka tana faɗin.


"Amadu haka kukayi watsi damu kuka wulaƙanta zumunci. gara kaima idan anci sa'a ana ganinka amma banda waɗannan ta nunasu Anty fadeelah sukam sunbi uwarsu sunyi watsi da ubansu. Toh ingaya muku da uba ake ado zakuce na gaya muku sai an goranta muku rashin uba. Inbanda ku fitinannu waya ke ƙin ubansa uyumm. Uwarku ta hure muku kunne. Batayi muku huɗubar gaskiya. Idona idon uwarki saina faɗa mata Allah yayi mata abunda tayi mana a danginmu. Aysha data fara ƙuluwa tace.


"Ah ji matarnan" Yaya Ahmad yayi saurin taranta faɗin.


"ƙaniyarki Aysha, Hajiya kiyi haƙuri in sha Allahu zamu kiyaye" Hajiya tace.


"Kagani koh?" fitinianniyar yarinyar nan rashin kunya zatayimin" Natashi ina faɗin.


"kedai Hajiya idan kika kama mita bakyaji bakya gani. mu babanmu ba haka yake mana ba. Wallh kamanninki kawai ya ɗauka banda Azabar masifarki"


"Allah na tuba daya ɗauko halina mace ta juyashi? badai halina ba wallh. Kitchen ɗinta na nufa batareda naji ƙarashin faɗanba dan bala'i kawai takeyi takasa sararawa sai haƙuri suke bata amma kamar wanda suke zugata. Na ɗauko coolern kwacokam datake zuba dambun namanta na fito dashi na zauna tana surfa bala'i ina ina gefe ina ci " Aysha ta dallah mata harara hajiya tace.


"uwarki kika harara" nace.


"Ya Ahmad tashi katafi abunka tunda bazata daina masifa ba" Tanajin haka tayi shiru nacigaba da faɗin wannan mitar kaɗai Hajiya ta'isa ta hana zuwa wajanki kin sakasu gaba kinata faɗa. Sunzo kinyi faɗa basuzoba kice basu zoba kinyi faɗa wanne ɗaya kikeso subi?" Hajiya tace.


" shikenan ai tunda baza'a faɗa muku gaskiya ba nidai nafaɗa yarage naku ku ɗauka uba ba abun yasarwa bane. Saiki kawo Muku kisaka muku agaba aiko tunda dai banaki bane natashi nashiga kitchen ina faɗin Hajiya basai kinmin gori ba akan dambun nama inaji tana magana amma bana iya jiyota na ɗauko ƙananun unbreakable bowls na fito aciki na zuba na maida coolern kitchen.


Muna zaune hira tayi nisa harmun manta da mitarta Yaya ya miƙe yace.


"Hajiya ni zan wuce" Hajiya ta ƙyaɓe baki tace.


"Sai kuma wace shekarar Amadu?" yace.

"Jimawa ma zan dawo zanzo na ɗaukesu" Hajiya tace toh Allah yasa. Saida akayi magrib kafin yaya Ahmad yazo ya ɗaukemu tare muka shiga cikin gidan dashi. Ƙamshin turarennan ne yafara muna barka hakan ya nuna yauma Baba yanada baƙi. tare muka ƙarasa har ɗakin Mama Yaya yace.


"Har yanzu Baba bai dawo ba? mama tace.


"Yadawo yana tareda baƙi"


"Toh nikam zanje saida safe na haɗu"
Mama tace.


"Allah ya tashemu ya amsa yafita"


"Mama baƙin jiyane suka dawo? " Na jefa mata tambaya.


"Eh dannaji Naji gidan gabaki ɗaya yaɗauki irin ƙamshin jiya" tabani amsa.


----------




Baba ya gyara zamansa dakyau yadubi Yaya Ahmad. Murmushi yayi sannan yace.


"Ahmad kenan A tunanina Uba ne yake sanarda ɗansa ranar auren yaro bayan yaje ya tattauna da mahaifan yarinya amma naji kai kake sanarmin lokacin aurenka. Bansan kodan banida komai bazan iya yimaka komai a wajan bikin bane yasa kayi haka amma ko yaya mahaifi yake Ahmad mahaifine kana tunanin zanji daɗin wannan maganar ne?" Jikin Yaya Ahmad yayi sanyi ayanda yasan Baba bai taɓa tunanin danya cemasa anje an tambaya masa aure harsun bada rana zai ɓata rai ba. Lallai Baba ya canja sosai. Jiki a sanyaye yace.


"kayi hakuri Baba banyi niyyar hakan ba da zarar na sanarwa Mummy saita tura gidansu yarinyar sukuma ana zuwa suka bada rana" Baba ya jijjiga kai kawai zuciyarsa tayi masa babu daɗi sakenda yayi agidansa yayi yawa dahar aka kai wanan stage ɗin. jin Baba yayi shiru yasa Yaya Ahmad yace.


"Baba dan Allah kayi haƙuri" Baba yace.


"shikenan yawuce" amma idanda son rainane inaso ka zauna anan bazan tilasta maka ba amma idan zakabi umarnina inaso ka zauna anan garin kaida matarda zaka aura. Banason zamanka acan yakamata ace kaima yanzu kadawo cikin ƴan uwanka kayi rayuwa. Jiya da kukaje wajan Hajiya ta kirani tanata murna. Yakamata ka zauna anan bance dole ina nufin idanda umarnina zaiyi amfani. Yaya Ahmad ya sunkuyarda kansa Maganar gaskiya yanason garinnan amma akwai dalilin dayasa bayason zaman garin yanzu kuma ga Baba yanason ɗaureshi da jijiyoyin jikinsa yasan bazai iya kaucewa maganarsa kuma kamar yazama dolene ya faranta masa tunda yasan abunda akayi a neman aurensa ya taɓa masa kimarsa matsayinsa na uba, yasan ko dangin matar suma zasuyi mamaki ace Babu mahaifinsa a neman aurensa bayan yana raye. amma baisan yanda zasu kaya da Mummy ba idan taji" jiki babu laka yace.


"Shikenan Baba zan zauna anan ɗin in sha Allahu" Baba yace Allah yayarda yayi maka albarka. Ya amsa da amin."




""""""""


Sati ɗaya yayi kullum sai Baba yayi baƙi wannan ƙamshin ya zauna dimun da'imun acikin gidanmu."




ZAYNAB ALABURA
























*BIBIYATA YAKEYI*
*(WAYE SHI?)*






Ya daɗe acikin toilet yana wanka yayinda yayi amfani da duk wani bath-mist dayasan yana amfani dashi nan da nan ƙamshi ya karaɗe gabaki ɗaya floor na illahirin hotel ɗin. Yayin beard ɗin fuskarsa ya ƙwanta luff-luff sai sheƙi yakeyi Cike da nutsuwa ya fito daga wanka. Ya isa gaba mirror da aka jera mayuƙan da yake amfani dasu cikin nutsuwa ya shafe jikinsa da mayukan wanda ƙamshinsu ma wata duniyar ce. Ya isa jikin Cloth cupboard ya tura murfin yayi gefe ya tsaya yana kallon ciki kusan 5minute kafin yaciro sabuwar jallbiya wacce take cikin ƙwalinta da singlet itama sabuwa dall acikin ƙwalinta sai boxer shima yana cikin ƙwalinsa da 3quater jeans gabaki ɗaya singlet da Boxer stamp na sunansa ne ajiki ga dukkan alamu daga company ake buga masa tasa daban ko shine mamallakin kamfanin gabaki ɗaya. Ya shirya cikin farar jallabiya yayi matuƙar kyau sosai ya tsaya kallon madubi yafi 10minute gaban madubi duk wannan abunda yakeyi yana yine cikeda nishaɗi amma wani ɓangaren akwai tsoro cike aransa. Ya shafo sajen dake ƙwance a fuskarsa sannan ya sauƙe ajiyar zuciya ya fara tafiya zuwa gaban wani bell ya danna 3minute saiga P.A ɗinsa yashigo ganinsa a shirya yasa yace.




"Mood sir harka shirya zan iya sanarda tafiyarka yanzu?" yayi ajiyar zuciya kana kallonsa zaka tabbatar akwai abunda yake damunsa.


"كيف ابدو
(How do i look)"
yayi magana out of fear saida P.A yayi murmushi sannan yace.


"Kayi kyau sosai you
انت دائما تبدو وسيم
(always look Handsome)" ajiyar zuciya ya sauƙe yasake komawa ya kalli madubi sannan yadawo yadubi P.A yace.


"هل أنت متأكد؟"(are you sure)"
tun yana mamakin yanda boss nasa ya nutsewa soyayya harya dawo yadawo yadaina amma sanin waye Hammood

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads