Header Ads
Showing 84001 words to 87000 words out of 171869 words

Chapter 29 - BIBIYATA YAKE YI COMPLT Document by Zainab Bawa.txt

Ads the beginning of article before Image

05 Jun 2024

1097

Ads at the middle of Article

shekara biyu anshiga da uku kullum saƙonnk kawai yake aikon dasu. Bansan dalilin kiranba yasa bazan iya ignoring ba amma kafin na ɗauka nayi saƙa da warwara sunfi goma. Ina pjcking na kara a kunnena nayi shiru. Ba'ace komai ba daga wayar nima bance ba. Na maida idanuwana na lumshe wayar tanakan kumatuna saitin kunnena a hankali nake sauƙe numfashi. Bansan me yasaba sai nakeji kamar mai kiran yana saurarona daga numfashin danake fitarwa.


Daga yanayin yanda numfashina yake sauƙa yagane cewa ina cikin damuwa gabaki ɗaya sai yajishi babu daɗi Marmeeyyn da yasani mak surutuce da fara'a amma yajita shiru gashi tana jan bumfashi tana sauƙar dashi cikeda damuwa bazai iya sauraran hakanba dan haka ya datse kiran. 15minute bayan datsewar kiran naji sallamar Yaya Ahmad. Har yanzu wayar nakan kumatuna yanda take ban sauƙetaba koda naji datsewa wayar. Sallama yayi nabashi izinin shigowa dan bazan iya tashi jafita palournba sam banason haɗuwa da mutane. Tubda Ya Ahmad yake inbanda yarinta bai taɓa shiga ɗakin mama ba sai yau. Yashigo yazauna akan comfy bedroom chair dake gefen gadon Mama. Na gaisheshi batareda na tashi ba.


"Marmeeyy tashi ki zauna zamuyi magana" batareda na amsa ba na nemi mike zaune.


"Kina sonsa da yawane har haka?" nayi ƙasa da kaina ya fahimci abinda nake nufi zuciyarsa tayi wani iri yakasa cewa komai. Bayan wasu mintuna kafin yacigaba da magana.


"Marmeeyy kisan cewa kuma na yarda cewa Allah bazai ƙwace wani abu atare dake batareda ya canja miki da ninkinsa sau babu adadi ba. Mijinda nake mikk buri da fata shine wanda zai soki ya ƙaunaceki ya riritaki yaga kimarki da darajarki ya zame miki gata kamar yanda kika zamewa gabaki ɗaya ahlinki gata. Ina miki fatan mijinda zai soki aduk yanda kike mijinda zai fahimci kina cikin damuwa daga zallan numfashinda kika sauƙar basai laɓɓanki sun furta ba wanda zai fahimci damuwa acikin ƙwayar idanuwanki batareda taimakon kalaman bakinki ba. Na tabbata bazaki daɗe cikin wannan damuwar ba dan ayau na tabbata cewa Allah ya amshi addu'armu.
Yanzu kitashi kiyi wanka idan kingama ki kirani zan fita dake may be zakiji sanyi aranki daganan zan wuce nasamu Baba zamuyi magana akwai wani suprise da zan miki amma sai kinmin alƙawarin sakin ranki nayi murmushi sannan nace.


"Ya Ahmad karka damu kanka da saika farantamin kar kaje ka takura kanka kaga ranar haka kacire maƙudan kuɗi ka siyamin wayarda tafi ƙarfina idan kanaso na saki raina zan saka kasan kawai zanji babu daɗine amma yanzu zan tashi nayi wanka ma" murmushi kawai yayi ya fice natashi daƙyar nashiga nayi wanka.


A ɗakin Baba Ya Ahmad ya shaidawa Baba abunda yake faruwa badan ya ɗaga masa hankali ba sai dan yanaso yaɗaga maganarsa akan cewa ba yanzu zai nunawa Marmeeyy akwai auren Hammood akanta ba shi aganinsa tunda marmeeyy nason Hammood koda da son bana aure bane bazatai masa uwar shawo kaiba. Sannan yana ganin Hammood kaɗai zai iya cireta a wannan damuwar da take cikk ya ƙwantar matada hankali. Bai bar ɗakin ba har saida ya sanya Baba ya amince da zai Kira Hammood da kansa dan yazo ya bayyanawa Marmeeyy kansa."




Bayan na fito a wanka wadrope na buɗe anan idanuwan suka sauƙa akan kayanda nasaka ranar diner ya Ahmad na cirosu ƙamshinsu yana dukan hancina har lokacin kayan ƙamshin turaren wannan mutumin sukeyi dukda sun ƙwana biyu a ajiye tun ranar dinner bansake sakasu ba bansan dalili ba amma naji daɗin ƙamshin danya sanyamun nutsuwa kuma dama tun abaya ƙamshine mai saka nutsuwa. Daga yanda nasaka kayan na gane naɗan faɗa ban shafa komaiba na ɗaura ɗanƙwali na yafe gyale tunanin Ya Ahmad zaiyi magana yasa na canja zuwa hijabi wanda zai shiga da kayan na saka plat shoe na fito a plaourn mama naga matar Ya Ahamd ni banmasan shigowarta ba na gaisheta sannan nafice fitata tayi dai-dai da fitowar ya Ahmad daga ɗakin baba. Ficewa mukayi sai bayan azahar sannan muka dawo."




Da Yamma na kira Maryam nace ta shirya zamuje diner datse kiran tayi bayan 40minute kawai sai najita a gidanmu.


"Babe wai kinyi haukane? Dagaske kike wai zuwa zakiyi? Toh me zakije kiyi? Dan Allah ki haƙura kiji da abu ɗaya haba"


"Zuwa zanyi mana kuma tare dake toh mema zai hanamu zuwa?"


"Babe please stop kina ɓatamun raina Allah na tuba mai Zai kaimu? Kinaso kisake tada ciwon da yake damunkine? Gashi duk kinbi kinyi wani ƙashi kin rame abu bakyan gani" cikeda jin haushi nakai mata duka"


"Ji banza wallh bansan wulaƙanci nice babu ƙyawun ganin?"


"Toh ƙarya nayi? Kije ki kalli mudubi shi zai baki amsa"


"Mtswww naja tsakk na ɗebeta na watsar" tayi magiya ta gaji nasake tabbatar mata da zamuje diner babu fashi duk yanda taso tayi convincing ɗina akan kar muje naƙi biyeta daga ƙarshe ficewa tayi tabarni.


Sai bayan magrib aka ɗauki amarya amma gidan iyayensa aka wuce da ita kamar yanda al'adan ƴan garin bauchi yake saisun ƙwana ɗaya gidan iyayen miji idan aka gama biki sai akai amarya ɗakinta.


Mama da anty suka raka amarya sai Ummi tana kallon harda Mama akazo ta jata ɗaki ta tambayeta yanda nake sannan tabata labarin irin halinda Hamma yashiga har yanzu ta sanar mata bai ƙwantarda zuciyarsa ba. Mama ta shaida mata nawa wajanma hakanne amma yaya zasuyi iyaye sun rigada sun zartar da hukunci. Ummi ta tambayi Mama akan dalilin canjuwar auren Mama ta nuna mata bata saniba. Basu daɗe a gidanba suka dawo akabar zallan amarya da ƙawayenta sai ƴan manya guda biyu.


Dare yayi anata shirin tafiya saida kowa ya watse sannan na shiga nasake wanka lace na ciro wanda aka ɗinka mana a sallah na sanyashi powder kawai da lipstick nasaka na ɗaura ƙwali yazauna akaina ni kaina nasan bawani kyau zanyiba tunda fusk duk bbu annuri amma yaya na iya? Dole zanje ko ban daɗeba na dawo. Sai bayan nagama shiri na fita naduba kowa yatafi dagani Sai Anty fadeela wautarmu nagani lo yanzu da muka bari kowa yatafi waye zai kaimu? ɗakin Mama muka dawo muka zauna bamu daɗe da zamaba wayata tafara ruri Ina duba naga Maryam dasauri mayi picking ina ɗauka tace.




"kifito ina waje tana faɗin haka da datse kiran nayiwa Anty fadeela magana muka fita. Waje yayi kyau ya tsaru anarya na tayi kyau sosai ɗass da ita Babu Mummy a wajan da alamu bata jeba. Saida mukayi kusan 30minute da zuwa kafin aka sanarda isowar ango saida gabana yafaɗi rasss."




ZAYNAB ALABURA💕
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin


Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba


Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔


Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo


Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍


Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝


------





Ango yayi kyau sosai sai dai ya rame dan sam baida walwala ana ganinsa za'a fahimci hakan. Aysha tana kallonsa tafara sakin murmushi alokaci ɗaya haƙwaranta suka fito waje sai buɗesu takeyi dan murna ya isa zuwa wajan babu wani annuri a fuskarsa yana isa akacigaba da gudanarda shagali. Ƴan uwansa ƴan tsirarrune sukaje wajan ana kallon amaryar da angon za'a fahimci babu wata shaƙuwa atattare dasu. Nidai ƙasa nayi dakaina ina danna wayata dan duk lokacinda na ɗaga idanuwana na dubesu sai naji gabana yafaɗi.


ƙawayen amarya sai rangwaɗa akeyi a fili kamar za'a ɓalle. Shikuwa Hamma baisanda zuwana wajanba. Tunda aka fara event maryam tana zaune bata matsa ko nan dacan ba nayi-nayi tatashi tayi musu manni taƙi Haka na haƙura na ƙyaleta, wata daga cikin ƴan uwan Mummy da batasan abunda yake faruwa ba tazo tana mana magana akan mutashi muje wajan amarya muyi mata liƙi bata jira cewarmu ba ta mimkiƙar damu ala dole sai munje baya na kalla dan banaji zan iya zuwa wajan. Anty fadeelah ta dafani.


"Marmeeyy idan bazaki iya zuwaba ki zauna abunki ba lallai amma a shawarce dakinje wajan kin saki ranki kiyi musu liƙi fuska ɗauke da murmushi dan wannan makirar tasan cewa damuwarda take tunanin tasakaki aciki toh bakya cikinta. Marmeeyy inaji ajikina akwai tanadin da ubangiji ya miki fiyeda wanda kika rasa ki taho muje. Cikeda ƙwarin guiwa na nufi wajanda suke tareda Anty fadeelah da maryam wacce sai ƙunƙuni take.


Muna dayawa wanda muke tafiya wajan amma abunka da abunda rai keso kallo ɗaya idanuwansa suka sauƙa akaina ya tsareni da idanuwa yana tambayar kansa abunda nasoyi wajan. Ko makahone yaganni yasan ina cikin damuwa danna rame na canja bare shi masoyina tunda yasaka idanuwansa akaina bai ɗaukesu ba. Ban sake shayar dashi mamaki ba saida yaga na halarci wannan dinner. Anya marmeeyy tanada hankali kuwa? Shine abunda yake tambayar kansa dan yasan babu abunda zuwa wajan zai jawo mata face tayi hurting kanta.
har muka ƙaraso wajanda suke tsaye ban yarda na kallesu ba dan nasan zanji kamar zuciyata zata buga. Aysha wacce itama sai yanzu ta lurada zamana a wajan kawai tabini da kallon mamaki tana tambayar kanta abunda nazoyi mata a wajan dinner. Kallon Hamma tayi taga idanuwansa suna kaina ko kaudawa bayayi bai damu da kowa yaga irin kallonda yake yimin ba. Kallone mak cikeda So. Ƙauna, Tausayi, dakuma jin haushi, wani abu ya tokare zuciyarta dan taji haushi sosai saida fuskarta ta nuna. Daƙyar na iya ɗaga idanuwana na kallesu Muka haɗa idanuwa nayi saurin ƴin ƙasa da kaina dan bazan iya juran kallonda yake yimin ba.


Ba ƙasa nake kallo ba jikinsu kawai na tsurawa idanuwa kamar maison gano wani abun jikin kayanda suka saka. sauran sunata manni nikuma nakasa. Lurada yayi da yanda nake kallo yasa yakai hannunsa ya zagaye a waist ɗinta yayi holding ɗinta very tight haɗeda mannata a jikinsa. Saida gabana ya faɗi na runtse idanuwa na inajin zuciyata tana bugawa da sauri da sauri nayi baya na riƙe maryam gam-gam dan jiri nafaraji ganin abunda Hamma yake yiwa Aysha wanda nasan yayi da gayya ne. Shikuma anasa wajan kawai yanaso ya ƙure dauriyata ne yanaso yaga ƙarshen yanda zan iya kaiwa.


Wani irin murmushi Aysha tasaki mai sauti alamun jin daɗi ya hayyana a fuskarta ta ɗago idanuwa ta dubeshi hannunsa ne kawai yake riƙe ita dakuma jikinsa daya manna a nata amma fuskarsa nakan marmeeyy. Ganin yanda hankalinsa yake baisata jin haushi ba itadai tunda ya riƙeta taji daɗi su abunda zasu kalla daban abunda duniya ma zata kalla daban. Kowa zaiyi tunanin ya riƙeta ne cikeda shauƙi bayan shikuma yayi hakanne danyaga reaction na marmeeyy ita kanta Aysha tasan dalilin yin hakan amma ita koma yaya ne yayi mata daɗi zata jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya bayan kallonda mutane zasuyiwa lamari gashi ya ƙuntatawa marmeyy. Jida maryam tayi na riƙeta gam-gam rikon bana hankali ha yasa ta ɗaga dan ganin abunda yake faruwa idanuwanta suka sauƙa akan abunda Hamma yakeyi dasauri tajani mukabar wajan. Can kujerun baya ta nufa muka zauna.


"Marmeeyy kinga abinda nake faɗa miki koh? Har yanzu knason Hamma bai kamata kizo wajannan ba. Sakamakon bazaiyi daɗi ba" inajinta amma bana fahimtar abunda take faɗa. Daga nan har aka gama event ban sake ɗaga idanuwana na kallesu ba.


Ana gamawa mune farkon fita amma munsamu motoci sun tsattsare yanda mukayi parking so babu hali mu tafi yanzu gashi sun tsaya ɗaukan pics yanda babu mutane muka nema muka zauna a kafaɗar maryam na ƙwantarda kaina na lumshe idanuwa yanzu damuwata kawai naganni agida. Bamu daɗe da zama ba naji muryan Hamma akanmu Bansan yaya akayi yasan yanda mukeba dan wajan yaɗanyi baya.


"Zamu iya magana yanzu?" ya tambaya.


"Hamma menene hakan katafi please wallh batajin daɗi.


"Tashi kibarnan maryam magana zamuyi" ganin fuskarsa Babu wasa yasa ta ɗan matsa gefe"


"You ignored me, my calls, my messages, dakin kulani May be da munyi sorting out wannan matsalan marmeeyy meyasa zaki mana haka? Kina kallon halinda kika jefamu hakanma bai isheki ba kika bata numberna dan ki gwada baki damu daniba duk hakan baiyiba sai kinzo wajan event ɗin. Why marmeeyy bayan kinzo babu abunda kikayi sai huring kanki, ke kaɗai nakeso kuma ke keɗai zanso duk wacce ta aureni zaman haƙuri zatayi dani dan zuciyata tana wani waje daban" tunda yake magana sai yanzu na kalleshi nafara girgiza kai zuciyata tayimin nauyi.


"Please Hamma dan Allah kabar wannan zancen ka zauna da matarka tsakani da Allah ka kula da ita Aysha fa ƴar uwatace abunda yayi marmeeyy shi yayi Aysha kana tunanin zanji daɗi idan ka cutarda ita?"


"Bansaniba bansan ko bazakiji daɗi ba amma na tabbata bakiji daɗiba dana riƙeta dukda ta kasance matata" saida gabana ya faɗi daram daya ambaci matarsa nan zuciya tafaramin saƙa tunani yafara kai kawo. Kodai yaudarar kaina nakeyi bazanji daɗiba idan Hamma yaso aysha? Ko bazan samu sauƙin danake tunanin samuba yayinda Hamma da Aysha kamar yanda nake tunani. Ya jijjigani.


"Aduk lokacinda kika shirya zaman dani kika shirya tsaya dan ƙwatar soyayyarki zan jiraki inanan Hammanki yananan yana ƙaunarki bantaɓa cire rai da zamu rayu da junaba kuma har yanzu ban cireba. na jijjiga kai ayayinda kuka yakeson fin ƙarfina.


"Hamma karka maidani maci amana dan Allah wallh ka haramta a gareni tunda ka auri ƴar uwata" yana jijjiga kai ina jijjiga kai.


"Ban haramta agareki ba kidaina faɗin haka" yafaɗa haɗeda kamo kafaɗata ya jawoni jikinsa yana shirin haɗe bakinmu waje ɗaya. Maryam da take gefe tana kallonmu ta rufe baki dan taso tasaki ƙara alokacinda taga abunda Hamma yake ƙoƙarin aikata gani tayi idan tayi ƙarar mutane zasuyo wajan suga abunda yake faruwa kuma ta tabbata abubuwa zasu ƙwaɓe hakan yasa ta rufe bakinta da hannuwanta biyu. alokacinda naga abunda yake shirinyi kuma baida niyyar fasawa dukda turjewarda nakeyi sai dai lips ɗinmu yazo gaff zai haɗe waje ɗaya nayi amfani da tafin hannuna nasaka a tsakanin lips ɗinmu. Jin abunda yashiga tsakani dayasahi sakina yana kallona.


"Hamma dan Allah kaje ka riƙe matarka hannu bibbiyu ko sau ɗaya baka tsaya ka saurareni kaji dalilin fasa aurenba. Dalilin shine dan inada wanda nakeso bakaiba Hamma ni naje nasamu Baba nace masa akwai wanda nakeso mun haɗu dashi auren ya Ahmad tun alokacin hankalina ya karkata gareshi bazan iya gaya makaba saboda girmanka da nake gani yasa nasamu Baba dan Allah ka ƙyaleni kaje kaso ƴar uwata ka zauna na ita" ina magana ina kuka nafaɗi hakanne san kawai Hamma ya janye maganarsa da yayi akaina ya koma ya fuskanci ƴar uwata. Murmushi yayi na irin kinma rainamin hankaki.


"Karya kike marmeeyy wallh ƙarya kike ni kaɗai kikeso ni shaidane nasanda hakan ƙarya kikayi danna rabu dake. Do you have to go this far marmeeyy kawai danna rabu dake saiki furta kalmar rashin so agareni" nakasa cewa komai kawai na haɗe kai da guiwa ina kuka yatashi fuuuuu yabar wajan. Yana barin wajan Maryam tataso tazo tayita tafara rarrashina ashe duk abunda yafaru A idon Aysha tunda taga Hamma yafito jikinta yabata ni yake nema dan ta bishi abaya tacema masu hotuna tana zuwa.


"Kin kyauta marmeeyy dama abunda kikazo yi kenan koh? Kinzo kiyimin ruining wannan ranar na tabbata da bakizo ba da komai zaiyi armashi. Wallh marmeeyy bana dana sanin canja masoyinki yadawo kaina. Ina zaune da ƴar uwata shigowarki rayuwarmu kika sanya takoma tafi sonki akaina haka Ya Ahmad yazamana kamar kece kuka fito ciki ɗaya baniba. Hakan bai ishekiba uwarda ta haifesni saida kika maidata tadawo kanki. Me kika sani a zafin ƙwace masoyi danna ƙwace miki mutum ɗaya shine kike hawaye? Ki share hawayenki marmeeyy bakida komaiba. Asheni na kasance jaruma da kika rabani da kowa nawa kika dawo ƴar lale amma banyi kuka ba. Hakanma ban isa nayi magana ha kowa haushina yakeyi. Yanzu Allah ya ƙwato masoyinki yabani bada tsumi naba bada dabarata ba hakanma kowa haushina yakeji nayi ba dai-dai ba Marmeeyy ki adana hawayenki dasaura. a fusace maryam tabata amsa.


"Wanda yakeda baƙin hali da Hassada shiya kamata ya adana hawayensa ba marmeeyy mak zuciya mai kyau cikeda alkhairai ba. Aysha zata mayarwa Maryam saita tuna cewa itafa ƙanwar Hamma ne maida mata magana batasan abunda zai jawo ba sai kawai tayi shiru. Har tayi tagam nikam ko ɗaga idanuwa banyiba ganin anfara watsewa yasa maryam tace mutaso mutafi dan yanzu mota zata tafiyu. Anty fadeela tarigada tatafi dan haka maryam takaina ta sauƙe sannan tawuce gida.


Nima ina shiga ƙwanciya nayi saboda kukanda nayi ina ƙwanciya bacci ya ɗaukeni.


Tunda Baba yabawa Hammmood Umarnin yazo ya bayyana kansa agareni ya tsinci kansa cikin farin ciki zullumi dakuma taradddadi.


Ko ƙwana ɗaya bai ƙara akaiba ya sa aka shirya masa tafiya in 2days wannan karon ya shirya fuskantata a matsayin namiji kuma mijina wanda yakeda iko dakuma mallakina."


ZAYNAB ALABURA
Wannan littafin na kuɗine kibiya ₦300 ta asusun bankina Kamar haka 0003075326 Zainab M Bawa JAIZ BANK ko katin waya na MTN ta 08161146563 haɗeda shaidar biya




Assalamu alaikum yan'uwa da abokan arziki🤝🤝🤝
Ina mata masu fama da wadannan matsalolin


Matsalar haihuwa
rikicewar al'ada
ciwon mara yayi period
Fesowar kuraje ga gaba
Ganin farin ruwa mai wari yana fito maki
Kurajan gaba
Kaikayin gaba


Da dai Sauran wasu alamomi to yar uwa kinsan ko miye to ba wani abu bane face sanyi ne ya taro yayi maki yawa 😔😔😔


Toh masha Allah sha kuruminki Allah ya kawo maki sauki ga wannan addababai ciwo


Maganin da zaki sha kiyi garau da yarda Allah 🙌👍


Toh ga dama ta samu maza ki kira aunty zee mom mujahid Katsina akan wannan lambar wayar ki ce mata MAIJIDDA MUSAWA ce taba ki wannan number
ki na son sanyan magani
08162859027🤝


-------


Washe gari haka natashi fuskata a kumbure luhu-luhu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads