Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 149432 words

Chapter 1 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1351

Ads at the middle of Article

INTEESAR
Story & written by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}



*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.






Wannan kirkirerren labari ne,banyi tunanin rubutashi Dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni da niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.


*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*




page0️⃣1️⃣


Zaune take akan kujerar tsugunno Tana k'ara itace a cikin murhun wutar da ta hura,wata matashiyar budurwa ce ta fito daga cikin daki,ta karaso gaban mahaifiyar nata dai-dai lokacin da ruwan dake saman wutar ya fara tafasa, ta durk'usa ta ce,



"Umma sannu da aiki"




Murmushi umman tayi ta bude marfin robar dake gaban ta tayi garin Dan waken da ta kwaba,sannan ta ce,




"Yauwa sannu Inteesar"




"Umma barshi na tayaki jefawa"


"A'a ki barshi kawai nasan yanxun zaki je gidan Hajiya Fatima ne ko?"




"Eh umma kindan duk safiya idan bata ganni ba zata fara nema na wai lapiya har yanxun ban shigo ba?"


Murmushi umman tayi tare da cewa


"Ai na sani don tasha yo aike idan taga k'arfe goma tayi baki shiga ba,kice ina gaishe ta."


" To"
Ta ce tare da mikewa




"Bari to na tafi tunda nagama ayyuka na kuma kin hanani jefa dan waken."




Ta Mike cikin nutsuwa irin tata ta nufi hanyar fita gidan.mahaifin ta ta samu a zauren gidan yana karatun Al-qur'ani,
Durkusawa tayi ta gaishe sa ya amsa cikin sakin fuska.


"Abba zanje gidan Hajiya ta"


Kai ya gyada mata tare da cewa


"Ki gaishe ta Allah ya tsare a dawo lapiya"


Mikewa tayi ta ce,


"To Abba,insha Allah"
Kofar gida ta fita tare da karanta Addu'ar fita gida.


Kasancewar basu da nisa gidan a gaban layin su yakekan hanya.cikin nutsuwa ta karasa gidan cikin nutsuwa ta tsaya dai-dai gaban tangamemen gidan,buga gate din gidan tayi,mallam Ibrahim Mai gadin gidan ya karaso ya bude mata karamar kofar tashigo,
Durkusawa tayi cikin girmamawa ta gishe shi.


"Ina kwana Baba"


Murmushi dattijon yayi tare da cewa


"Dama nasan kece kika shigo yanzun,Kin tashi lapiya Inteesar?"


"Lapiya qalau Baba"


Kai tsaye ta karasa cikin gidan.A hankali ta tura kofar falon tare da yin sallama,dama bata tsammaci ganin kowa a falon ba.kai tsaye ta nufi falon Hajiya Fatima bakin ta dauke da sallama.jin motsi a kitchen ne yasa ta nufi kichen din,Hajiya Fatima dake wanke kayan ciki ne ta kalli Inteesar tare da sakar mata murmushi


"Yanxun nake zancen ki a zuciya ta 'yar halak ashe kina hanya"?
Murmushi tayi tare da durkawa har kasa ta gaida Hajiya Fatima


"Ina kwana mummy"?


"Lapiya qalau Inteesar yasu ummanki da mallam?"


"Lapiya qalau sunce na gaishe ki."


"To Ina amsawa"


Mikewa Inteesar tayi tare da kallon mufida dake fere dankalin turawa


"Mufida kin tashi lapiya"?


"Lapiya qalau Inteesar, Yauwa zoki tayani fere dankalin nan wallahi nagaji."
Kallon ta mummy tayi tare watsa mata harara


" wani aiki kikayi da zakice kin gaji?"


"Mummy har yankewa nayi fa da wukan nan baki sani ba?"


Gajeren murmushi mummy tayi


"Kece zaki yanke ba tare da kinyiwa mutane ihu da raki ba?"


Yamutse fuska tayi tare da cewa,


"Wash Inteesar Dan Allah zoki karasa Bari naje nasa spirit da plaster na dawo."


Batare da ta jira cewar mummy ba ta ajiye wukan ta ta fita da sauri Girgiza Kai mummy tayi ta ce,


" Dama ba son aiki kike ba Don ma ina tursasaki Amma duk da haka ba biyan bukata kidauki dogon lokaci baki gama kwakkwaran aiki d'aya ba."


Inteesar ce ta k'arasa gaban dankalin ta dauki wuka ta fara ferewa cikin kankanin lokaci ta gama,ta wanke tasa gishiri kadan ta soya tagama ta soya kwai ta dafa ruwan shayi da yaji kayan kamshi,ta kalli mummy tare da akin murmushi ta ce,




"Mummy ki barshi kawai Bari zan karasa"

"To Allah yayi maki Albarka bari naje nayi wanka"


Ta fita Inteesar taci gaba da aikin ita kadai,cikin kankanin lokaci ta gama ta zuzzuba a flask ta jera a dinning table sannan ta dawo ta tsaftace kitchen d'in, da kayan da suka 'bata,dai_dai lokacin Mufida ta shigo kitchen din tana murmushi.


"Inteesar sannu da aiki"


Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, Mufida tacigaba da magana

"Ke bari na fada maki gaskiya bawani yankewar da nayi kinsan bana son aiki aike gara kisaba da aiki don mace ce ke wata rana aure zakiyi kuma haihuwa zakiyi ki zama uwa."


Dariya tayi tare da cewa
"Ai insha Allah mijin da zan aura bazai zama mai ra'ayi irin na Dady na ba,don Dady baya son a dauko mai aikin da zata dinga dafa abinci sai dai mummy ce damu zamu dinga yi,baki ga gidan nan ga ma'aikata nan ba? suna aiki amma banda shiga kitchen?shi kuma nashi tsarin kenan baya cin abincin mai aiki,ni kuma mijin da zan aura sai na tabbatar ba irin tsarin Dady ne dashi ba ehe."Dariya Inteesar tayi ta ce,


"Allah ya shirye ki"


Tare suka fito kitchen din dai_dai lokacin da Dady da Mummy suka karasa dinning table din suka zauna,Inteesar ta durkusa ta gaida Dady cikin girmamawa


"Dady Ina kwana"?


Cikin sakin fuska ya amsa mata

"Lapiya Lau Inteesar ya k'ok'ari damu?"


Murmushi tayi tare da durkusawa da Kai kasa,mummy ma murmushi tayi tana jin son yarinyar har cikin ranta take kaunar ta, mi'kewa tayi tare da k'arasawa ta zauna akan kujerun da suke falon,
Dai-dai lokacin da wayar Dady ya fara ruri,kallon secreen din wayar yayi tare da murmushi ya ce,


Ga Muhammad muhdeen na Kira na a waya."


Take sai gabn Inteesar ya Fadi jin ya ambaci sunan muhdeen,a zuciyar ta tace Allah yasa mugun ba dawowa zaiyi ba,da na shiga uku.Dady ya d'aga wayar.






Daga alk'amin✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




Don k'arin bayani


09065327995




Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89




*INTEESAR*


Story & written by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.




Wannan kirkirerren labari ne,banyi tunanin rubutashi da cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.


*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*


Page0️⃣2️⃣


Daddy ya daga wayar tare da cewa


" son kana lapiya?yau satin ka daya a can,ko wani irin biki ne yakamata a ce angama,ga Asibiti nan yana jiran ka."


Daga d'aya bangaren muhdeen dake kwance saman lapiyayyen godo na alfarma,gyra kwanciyar sa yayi tare da cewa


"Eh mungama bikin Dady Amma Ina son kafin na dawo Nigeria zan biya kasar London Naga sumayya."


Dady ya katse shi ta hanyar cewa ba wannan lokacin,karka manta ankammala asibitin nan an zuba kayan aiki da ma'aikata tun last week yakamata ka fara zuwa ka ce zakaje bikin abokin ka a kasar Egypt zakayi kwana uku can ka dawo yanzun satinka daya sannan kace mun zaka je wata kasa?bazai yuwu ba."


Muhdeen yamutse fuska yayi Don yasan Halin mahaifin sa idan ya fadi magana ya fadi kenan.


"To shikenan Dady zan dawo gobe insh Allah."


Murmushi Dady yayi tare da cewa


"To 'Dan Albarka Allah ya tsare"


Ya mik'awa mummy wayar tare da cewa


"Ga mummyn ka"


Amsar wayar tayi tare da sallama


"Son ina fatan kana lapiya"?


Daga can bangaren ya
ce,
"Ina lapiya Mum fatan kema lapiya?"


Murmushi tayi tare da cewa


"Alhamdulillah kun gama bikin abokin naka me ka tsaya yi a Egypt har yanzun baka dawo ba?"


"Mummy na hadu da abokai nane da mukayi karatu tare duk sunzo,kuma kowa daga k'asar da yake shiyasa muka Dan zauna dasu don yanzun idan kowa ya watse mukan dad'e bamu haduba,amma insha Allah zan dawo gobe tunda Dady ya matsa da naso na biya kasar London naga Sumy na ta matsamun wai sai mazo."


Shiru mummy tayi kafin tace,


"Idan ka samu sarari kaje wani lokacin amma ka dawo yanzun.don idan ka tafi London din nan baka San dawowa sai an matsamaka."


"To shikenan tunda haka kuka ce"


Mufida ce ta kar'bi wayar ta ce


"hellow big bro shine ko ka nemeni a waya ko? Amma Asiya Tana gida da yanzun kace a bata."


Dariya yayi tare da cewa


"Autar mummy sarkin k'orafi to ai yanzun nake Shirin tambayar ki sai kikayi gajen Hakuri"


Tura baki tayi cikin shagwa'ba tace
Bawani Nan ai nasan kafi damuwa da Asiya akaina."


"Dariya yayi tare da cewa


"Karki manta kece fa auta gaba d'aya shalele,hidima ne sukayi mani yawa Amma kiyi Hakuri kinji?"


Kai ta gyad'a masa tare da yimasa sallama.


Mikawa Dady wayar tayi inda ya K'ara jaddada masa ya dawo bayan sunyi sallama ne mummy ta juya ta kalli Inteesar ta ce


" 'yata taso muyi breakfast mana"

Kai ta girgiza tana murmushi ta ce


"Mummy gida zan koma Umma Dan wake tayi shi zanci*


Dariya Mummy tayi tare da jinjina Kai


"Kedai Inteesar akwai son d'an wake to shikenan idan kingama ki dawo."


Mikewa tayi tare da cewa "To Mummy."


Kofar fita ta nufa da sauri Mufida ta ajiye kofin tea din da take Sha ta ce


"Lah jirani Inteesar bari na d'auko gyale na mu tafi nima d'an waken zanci"


Dariya Inteesar tayi Wanda har sai da wushiryar ta ta fito.


"To Ina jiranki kije ki dauko"


Bayan ta dauko ne suka tafi,Suna tafiya Mufida ta ce,


"kinji gobe Yaya Muhdeen zai dawo ko?"


" Wallahi nayi missing d'insa sosai"


Ta fadi Tana murmushi


Itako Inteesar tunda taji zai dawo kamar taji sak'on mutuwa don har ga Allah bata son dawowar shi saboda ya tsane ta,ba abunda ke hada ta dashi daga yadinga binta da mugun kallo sai kuma ya dinga galla mata harara indai Yana gidan nan bata da sake,ko gaishe shi tayi baya amsa mata sai dai idan akwai idan want wajen mummy ko Dady ko kuma Mufida.idan a gaban Asiya ne Kam baya amsa mata ko kallo bata isheshi ba.dayake Aasiyar ma basu jituwa da Inteesar.


Suka shiga gidan bakin su dauke da sallama.Umma dake cikin daki ne ta amsa masu,shiga sukayi suka gaishe ta.ta amsa masu cikin fara'a.


"Mufida yau kece a gidan namu?"


"Eh Umma naji Inteesar tace 'Dan wake kikayi shine nazo naci."


Cewar Mufida
Umma ta ce


"kema dai kina son 'Dan wake kamar Inteesar."


"To yana can nakai mata d'akin ta Don nasan sai ta dawo taci."


Mikewa sukayi suka fita suka nufi dakinIinteesar,suna shiga Mufida ta zauna kan katifar Inteesar dama d'akin Sai da tagyara shi fes tasa turaren wuta kafin ta tafi gidan Mummy
Plate Inteesar ta dauko ta zuba masu 'Dan waken tasa yaji da man kuli sannan ya yanka kabeji da cucumber da tumatur suka hau ci mufida nata santi,bayan sun kammala sun k'oshi mufita ta kishingid'a ta fara chatting'ita ko Inteesar fita tayi take ta fara Shirin 'Dora masu abincin rana.miyar taushe tayi sannan ta daura tukunyar tuwo,koda ta ahiga d'aki ta tarar mufida ta na barci murmushi tayi sannan ta fita,cikin kankanin lokaci tayi tuwon shinkafa zuwa karfe goma Sha biyu ta kammala komai ta tada mufida tace


"ki tashi har na gama girki gashinan idan zakici"


Mufida cikin yamutse fuska alamun barci bai ishe ta ba ta ce,


" me kika dafa?"


Kallonta Inteesar tayi tace tuw....."


Tun kan ta karasa ta ce


Wallahi bazanci tuwo da rananan ba."


Kasancewar Inteesar ma batajin yunwa kuma dama it ba Mai yawan cin abinci bane.ta ce.


"To tashi mu tafi"
Tare suka fito inda suka shiga sukayiwa Umma sallama suka tafi zuwa gidan su Mufida koda suka k'arasa Kai tsaye Inteesar ta nufi kitchen Don 'Dora abincin Rana.


Washe gari ranar da Muhdeen zai dawo kenan bayan sun gama breakfast mummy tasa Inteesar da mufida Sud'an Kara gyara masa d'aki.dama Shima ya hana ma'aikatan gidan suna shigar masa d'aki.
Koda suka shiga mufida zama tayi kan side drawer'intesar ta zage ta gayra d'akin ta goge ta wanke masa toilet sannan suka fita,dama d'akin Mummy da na su Mufida Maimuna mai aiki ke gyara masu da fallo


Kai tsaye Inteesar ta nufi kitchen Dan taga mummy ta shiga abinci lafiyayyu kala-kala aka shiryar don tarban Muhdeen bayan sun gama sunyi wanka karfe daya na Rana suka nufi airport dan tarban sa, Direban su biyu suka dauki motoci guda biyu inteesar bata so zuwa ba amma da mummy ta matsa mata dole taje, Mummy ta shiga bayan d'ayan motar Inteesar da mufida daya .


Suna Isa jirgin su na sauka,ya fito daga jirgin rik'e da akwatin sa da fara'a suka karasa Mufida ta rungume sa tana masa barka da sauka,bayan ta sake shi ya rungume Mummy tare da cewa


"Imiss you mum"


Murmushi tayi tare da cewa
" miss u to."


Inteesar ce ta kalleshi ta ce,
"Sannu da dawowa ya muhdeen"


"Wani kallo ya mata ganin idon Mummy ne ya sa ya amsa


"Yauwa"


Kai tsaye suka nufi motocin su inda Mufida ta dage sai motar su zai shiga haka akayi kuwa ya zauna gaban motar, da
Yana hada ido da Inteesar ta jikin madubin motar ya watsa mata harara,da sauri ta sunkuyar da Kai k'asa.




Daga alk'amin✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






Don k'arin bayani


09065327995




Love u ollFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89




*INTEESAR*


Story & written by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.






Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.


*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*


Page0️⃣3️⃣


Yana hada ido da Inteesar ta jikin madubin motar ya watsa mata harara,
Da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,Direba yaja motar suka bar airport d'in suka nufi hanyar gida,yayin da motar da Mummy ta shiga ya rufa masu baya.


Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu gate din gidan.bayan sunyi parking direban ya zagayowa da sauri ya budewa muhdeen mufin motar ya fito,yayin da Direban ya dauko kayan da muhdeen din ya dawo dasu daga cikin boot d'in motar,yayin da Mufida da Inteesar suka fito daga cikin motar,mummy ce ta riko hannun Muhdeen cike da son gudan jinin nata,langwa'bar da Kai yayi alamun gajiya.


Murmushi mummy tayi tare da cewa ,


"Ka gaji ko"


Kai ya gyad'a mata alamar Eh,hannun shi taja suka nufi kofar shiga part din,yayin da su Mufida suka rufa masu baya,ita dai Inteesar jikin ta duk yayi sanyi kamar an Jefi kaza da gishiri.


Kai tsaye Mummy ta raka shi har part d'insa,har bedroom suka shiga yayin da direban ya ajiye kayan a falon sa.
Mummy ta ce,


" kayi wanka ka fito Muna jiranka muci abinci."


kai ya gyad'a yayin da mummy ta fita taja masa k'ofar ta nufi folo inda ta samu Inteesar da Mufida, itama falon ta zauna fuskar ta dauke da murmushin farin ciki.


Cikin kankanin lokaci Muhdeen ya k'araso falon sanye yake cikin kananun Kaya farin Riga da bakin wando 3 quarter, Mufida ce taja hannunsa tana murmushi suka nufi dinning area din Mummy ma ta Mike tabi bayan su tare da cewa Inteesar ta taso suci abinci.


"Mummy bana Jin yunwa anjima zanci"


Mummy ta dakata tare da juyowa tana kallon ta da mamaki,Don tasan cewa tun suna girki take cewa Tana Jin yunwa amma yanxun kuma tace bazataci ba sai anjima.


"Ina ce yunwa kike ji sannan yanzun kice bazakici abinci ba,taso ko kadan ne kici .
Har ga Allah tana son cin abincin amma kuma tsoron Muhdeen d'in da takeyi ne yasa bazata iya zama dasu taci Abincin ba.mufida ce tace,


"Inteesar Dan Allah ki taso Mana
tana Shirin mikewa ne taji muryar muhdeen Yana cewa


"Ki kyaleta mana tunda tace bazataci ba ko zaki matsa mata dole ne?ba tafiku sanin cikin ta ba?"


Mummy bata Kara cewa komai ba taja hannun Inteesar din suka nufi dinning area din kujera taja mata kuje
ran dake facing d'in Muhdeen ta zaunar da ita kauda kansa yayi bayan ya jefa wata Mata mugun kallo,
Mummy ta shiga bude kulolin abincin ta fara zuba masa nasa.fried rice ne da yaji hanta da Koda,sai kuma farfesun kajin da Inteesar tayi masu,ta zuba masa juice din kwakwa da Madara Wanda Inteesar din ce ta hada.ta kalli Inteesar tace,


"'yata me zaki ci?"


Cikin sanyi ta ce


" ruwa kawai zansha"


Ba tare da mummy tace komai ba ta zuba mata jallop din cuscus ta ajiye mata a gaban ta tare da ajiye mata kofin juice a gaban ta,ta juya ta kalli Mufida ta ce,


"Ke kuma ki tashi ki zuba abunda kike so,
Kulan cuscus d'in a gaban ta.ta zuba a plate ta balle murfin robar ruwa ta zaba a cup Mummy ma nata ta zuba ta fara ci bayan ta zubawa Inteesar farfesun kajin.


Inteesar gaba d'aya ta kasa sakewa taci abinci yadda kowa ya sake yana ci,gabanta sai fad'awa yakeyi musamman irin kallon da Muhdeen ke jifanta dashi.


Shima kansa a cikin zuciyar sa ya rasa gane dalilin da yasa ya tsani yarinyar,shidai wulak'anta mutane ko kuma kyarar mutane ba dabi'ar sa bace, amma baisan dalilin da yasa ya tsani yarinyar ba.Gashi dai Kullun zata baro gidan iyayen ta taxo gidan su tana taya mahifiyar shi aikace-aikacen gida, gashi tana son dangin shi jininta ya had'u da autar su Mufida amma duk lokacin da yarinyar ta shigo gidan sai yaji gaban sa ya fad'i,ga kuma yawan mafarkin da yakeyi da ita kusan kullun,ko sumayya masoyiyar shi da suka kwashe shekaru biyu suna soyayya baya mafarki da ita sai wannan mayyar,sunan da yasa mata kenan mayya.


Yana cin Abincin sa yana tunani kuma gashi yaji dadin abincin sosai don gaskiya Inteesar ba baya bace wajen iya girki.ta kware sosai shiyasa Mummy kullun sai ta jira ta tazo kafin ta d'aura girki,don suna Jin dadin abincin ta sosai.


Mummy ce ta zuba mata ido tana nazartar yanayin ta


"Inteesar lapiya kuwa me yake damun ki?"


Daga kai tayi ta ce


"Lafiya qalau mummy"


"To meyasa bakici abincin kirki ba kinsaka abinci a gaban ki sai jujjuya cokali kikeyi
dakyar taci cokali uku tasha ruwa ta koma falo kan kujera ta zaina,
Mummy dai shiru tayi tare da binta da ido
suka cigaba da cin Abincin su
Muhdeen sai da ya koshi ya Kora da juice din kwakwa sanna ya Mike tare da cewa


"Mummy bari na

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads