Showing 78001 words to 81000 words out of 149432 words
Chapter 27 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
da gaske kafin kici abinci?to kiyi sauri zamuje mu fara cin abincin ki tabbatar kafin nabar wajen cin abincin ki kinzo."
Kai ta jinjina Mata
"To Gwaggo"
Hannun Muhdeen taja suka fita daga d'akin,dagan Inteesar ta shiga wanka
Daga Gwaggo har Muhdeen ba Wanda yaci Indomie, dukkansu kunun gyad'a da k'osai suka ci, Muhdeen ne ya kalli Gwaggo ya ce,
"Yanzun Gwaggo sai ki dinga nuna mani wariya akan 'yarki ko?
Murmushi tayi tare da cewa
"Wariyar me zan nuna maka.?"
"Nagani kinfi son Inteesar akaina"
Dariya tayi kafin ta d'ora da cewa
"Waye ya fad'a maki haka?"
"Ai naga kin fifita soyayyarta akaina ne"
"Waya fad'a maka haka?ai gurbin ido ba idon bane,karka manta kaifa shalele na ne kafi sauran jikokina soyuwa a cikin zuciya ta."
"Ada kenan Gwaggo amma a yanzun dai kam kinfi son yariyar can a kaina,tun ranar da kika zo kika kyallara ido kika ganta shikenan."
"Gaskiya ka fad'a yariyar ta shiga raina sosai,kuma naga dacewarka da ita sosai ba kad'an ba,kuma inaji a jiki na ita ce abokiyar rayiwarka ."
"Jiya bata fad'a maki abunda tayi bane?"
"Ta fad'a mani gaskiya shine na ce da ta tarar da Ishaq baya nan me yasa bata dawo ta sanar ba ta tafi?sannan wanda ka gansu tare ba kowa bane face Usman Wanda ya kad'e ta da mota a kwanakin baya,shine wajen dawowa shi da k'anwasa suka rage mata hanya."
"K'arya ne Gwaggo,k'arya take maki,ba wata k'anwarsa da ido na gansu suzo Ubasanjo complex ina tsaye tare da manager access bank,ita da zata zo gida mai ya had'a ta da complex?sannan zata zauna tayi ta wage masa baki kamar mara kamun kai da aurenta."
"To yanzun dai kayi hak'uri ba zata sake ba."
Da misalin k'arfe goma sha biyu na rana motarsa tayi horn a k'ofar gidan Muhdeen,mai gadin ne ya bud'e masa,bayan yayi parking ne suka fito, Jabeer ya gaida mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan sannan ya shiga gaba Maryam na binsa a baya.
Knocking sukayi Inteesar ce dake kitchen taji k'arar kofar,tazo ta bud'e ganin Jabeer ne yasa ta saki fara'a.
"Yaya Jabeer Kaine?"
Ganin Aunty Maryam yasa ta fad'ad'a fara'arta
"Oyoyo Aunty Maryam ashe yau muna da manyan bak'i, bisimillah ku shigo mana."
Kai Jabeer ya girgiza tare da cewa
"Ni yanzun zan koma Ina da aiki,anjima zanzo na d'auke ta, Gwaggo na ciki ne?"
"Eh amma tana barci."
"Ba damuwa idan na dawo sai mu gaisa."
Daga nan ya koma ita kuma Inteesar ta janyo hannunta suka shigo cikin falon ta zauna, kitchen Inteesar ta koma ta kawo mata abun ta'bawa sannan ta koma kitchen ta cigaba da aikinta.
Tana cikin aikinta ne a kitchen sai ga Aunty Maryam ta shigo tasa hannu wajen taya ta aiki,duk da Inteesar ta hanata kan cewa bata da lafiya,amma sam tak'i amincewa dole ta barta sukayi tare.
Bayan sun kammala ne Gwaggo ta farka fitowarta yayi dai-dai da kammalawarsu,da mamaki ta kalli Aunty Maryam ta ce,
"Wannan ba matar Jabeeru bace."
Murmushi sukayi dukkansu inda Inteesar ta ce,
"Ita ce Gwaggo,ya kawota lokacin kina barci yace idan ya dawo sai ku gaisa."
Aunty Maryam ta gaida Gwaggo ta amsa tana 'yar tsokanarta,daga nan Inteesar taja hannun Aunty Maryam tana cewa
"Aunty Maryam mu shiga ciki kiyi sallah ko?"
Tare suka shiga bayan Aunty Maryam ta d'auro alwala ta fito ne, Inteesar ta ahiga don yin wanka,bayan ta fito ne ta sanya kaya tayi sallah,sannan suka fita zuwa falo.
A dinning room suka samu Gwaggo tana cin white rice and chicken soup,zama sukayi inda Aunty Maryam ta tsiyayi ruwa Inteesar ta zuba mata abinci sannan ta d'ebi nata.
Da yamma ne Jabeer yazo ya d'auke ta suka tafi gida.
Da misalin k'arfe goma na dare ne Inteesar tana Sanya rigar barci da niyyar zuwa d'ayan d'akin ta kwana,sai ga wayar Gwaggo tayi k'ara,tana d'agawa raji muryar Muhdeen na cew wai ta sanar da Inteesar ta kawo masa coffee a d'akinsa.gabanta ne ya fad'i don tasan yau Bata da ma'buya.
Bata da wani za'bi dole haka ta nufi kitchen ta dafa masa.
Hijabi tasa har k'asa tare da k'ok'arin cire tsoron dake ranta,tura k'ofar tayi tare da shiga da sallama tana shiga ya mik'e ya nufi k'ofar d'akin tare da murzawa k'ofar key ya zare key d'in daga jikin k'ofar,gabanta ne ya fad'i ganin wani irin murmushi akan fuskarsa Wanda bata ta'ba ganin ya mata shi makamancinsa ba.
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love you oll😘😍
Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page4️⃣8️⃣
Hijabi tasa har k'asa tare da k'ok'arin cire tsoron dake ranta, tura k'ofar tayi tare da shiga da sallama,tana shiga ya mik'e ya nufi k'ofar d'akin tare da murzawa k'ofar key, ya zare key d'in daga jikin k'ofar, gabanta ne ya fad'i ganin wani irin murmushi akan fuskarsa Wanda bata ta'ba amfani yayi mata makamancinsa ba.
K'ok'arin dakewa tayi don kada yaga tsoronsa a cikin idanunta, durk'usawa tayi ta ajiye jug da kofin sannan ta mi'ke, ba tare da ta kalleshi ta ce,
"Ka bud'e mani k'ofa na fita?"
Kamar baiji abunda take fad'a ba ya shareta, ganin baida niyyar mata magana ne yasa tayi shiru don taga yana da niyyar shiga wanka yasa tayi shiru, da niyyar idan ya shiga wanka ta d'uki key d'in ta bud'e d'akin ta fice.
Kamar yasan niyarta, da zai shiga wankan sai ya shiga da key.
Tsabar bak'in ciki da takaici ji take kamar tayi kuka, tana nan tsaye ne ya fito d'aure da towel a k'ugunsa sai wani k'arami da yake goge ruwan kansa, kallo d'aya tayi masa tagansa d'aure da towel,gashin k'irjinsa da ya kwanta luf ta kalla ta kauda kanta da sauri tare da juya masa baya.
Jin alamun ya kammala shirinsa ne yasa ta juyo ta kalle shi, sanye yake da riga da wando na barci ya zauna bakin gadon.
"Ki zuba mani nasha ko ni zan zuba da kaina."
K'arasawa tayi kusa dashi ta durk'usa ta zuba masa ta saka suga dunk'ule uku, mik'a masa tayi ta mi'ke tsaye ta cigaba da tsayiwarta.
"Kin tsaya mani akai kamar wata dogariya"
Tura baki tayi tana magana ciki ciki
"Wannan bakin da kike tura mani shi idan kika shiga hannu na ko?"
"Ni ka bud'e mani k'ofa na fita."
"Ki fita Ina?ai kin shigo kenan sai kuma gobe, guje-gujen naki ya k'are?saboda kinsan baki da gaskiya shiyasa kike gudu ko?"
Ya k'arasa maganar yana kai kofin coffee a bakinsa.
"Ina kika je jiya? sannan waye naganki tare da shi jiya? sannan kuma meye tsakaninki da shi?"
"Jiya fa gidan rasuwa naje kuma an fad'a maka Mahaifiyar k'awa ta ce ta rasu."
"Da nace kije Ishaq Direba ya kaiki me yasa kika tafi?"
"Yana da mara lafiya ne ya tafi gida, shine ni kuma na tafi na hau abun hawa,amma Gwaggo tayi mani fad'a bazan sake ba."
"Waye na ganki tare a Ubasanjo complex?"
"Usman ne sunan sa."
"Yayanki ne ko kuma muharraminki ne?"
Kai ta girgiza alamun a'a
"To meye zaisa ki shiha motarsa alhalin gidan rasuwa na fito zan samu abun hawa ne sai yayi parking, nagansa da k'anwarsa suka matsa akan sai na shiga, bayan na shiga ne k'an war tasa ya sauke ta ne awani tsago, ni kuma ya kawo ni gida."
"Me kuka je yi uba sanjo complex?"
"Cewa yayi wai zai siya mani waya."
Wani irin kallo ya watsa mata sai da hanjin cikinta suka kad'a cikin tsananin 'bacin rai ya mik'e tsaye, tare da zuba mata ido.
"Wato saboda wancan ranar na kamaki kina waya da shi, na kar'bi wayar na 'boye shine kika fad'a masa ya siyar maki wata wayar ko?"
Kunnenta ya kama ya murd'e, k'ara ta saki saboda zafin da taji,bata san lokacin da ta shige jikinsa ba tare da rok'onsa ya sake mata kunne, wani irin shock yaji kamar an jona masa lantarki, gaba d'aya sai ya tsinci kansa a wani irin yanayi mai wuyar fassara,ya rasa dalilin da yasa kwanan nan duk lokacin da yayi niyar zai hukunta ta ko ya kad'aice daga shi sai ita sai ya tsinci kansa a wani irin yanayi,gaba d'aya jikinsa ya mace sakamakon k'irjinta da ya had'u da nasa,wani irin ajiyar zuciya ya sauke, ita kama duk ba ruwanta bata ma San halin da yake cikin ba, ita dai taji zafin murd'e mata kunnenta da yayi ne yasa ta shige jikinsa, ya rasa yadda zaiyi gaba d'aya yaji buk'atarta kawai yake yi, a hankali yayi mata magana kamar mai yin rad'a
" kina son na yafe maki?"
Kai ta gyad'a masa alamar eh
Sabon yanayin da ya riski kansa ne ya rasa ya zaiyi, duk da cewar ba wani abu da ya ta'ba shiga tsakaninsa da Inteesar, amma duk lokacin da suka kad'aice ita sai yaji wani bak'on yanayin da bai ta'ba jinsa ba, koda kuwa a tare da matarsa Sumayya ce wacce har sex yake da ita bai ta'ba jin irin yanayin a tare da ita ba, ya sanya harshensa a cikin kunnenta ya shiga wasa da shi a ciki, rufe idonta tayi sakamakon wani abu da taji yana mata yawa a jiki, sai da ya had'a ta da bango sannan yaja wani irin ajiyar zuciya, Wanda hakan yasa ta yi saurin rufe idonta,bakisa ya sa a kunnenta ya hura mata isaka,a kasalance ta d'ago idanunta ta kalle shi,sannan ta cire idanunta daga gare shi tare da tura mata baki, bakinshi yakai cikin bakinta ya fara tsotsa, gaba d'aya k'afafunshi sun kasa d'aukarsa, janye bakinta tayi daga nasa, shi kuma ba abunda yake buk'ata illa ya same ta don mararsa ta fara masa ciwo, janta yayi suka fad'a kan gadon, Hijabin dake jikinta ya cire ya shiga k'ok'arin'balle buturan gaban rigarta, rik'e boturan tayi ta hanshi damar cire wa,hannunsa ya zura cikin rigarta hankalinsa gaba d'aya ya gama tashi lokacin da ya fara shafar fatar jikinta gaba d'aya hanklinsa ya gama tashi saboda taushin fatarta.
Kuka ta saka masa tare da kiciniyar kwace kanta daga gare shi, cikin wata irin murya da bata sanshi da ita ba ta ji yana magana.
"Don Allah karki Mani haka Inteesar, wallahi ina cikin wani hali idan ban same ki ba komai zai iya faruwa dani, ki taimaka mani."
Ya k'arasa maganar yana cije la'b'bansa sakamakon mararsa dake masa ciwo.
"Banida abunda zan raimake ka da shi, ko ka mance ne na tuna maka?Kai da bakinka ka fad'a cewa me zakayi da wannan kucakar yarinyar, to me kucakar yarinyar zata maka yanzu?kai fa kace baka k'auna ta ka tsane ni to kenan jiki na ne kake so? Am sorry yaya bazan iya bada jiki na ga mutumin da baya k'aunata da tausayi na ba sai dai ya mori jiki na ba, so kake kawai ka mayar da ni abun biyar buk'atarka a duk lokacin da buk'atarka ta taso maka da zaran ka gama amfani na ya k'are a wajenka, to ni ba cingam bane da zaka 'bare kaci da zarar ka gama ka cillar dashi a kwandon shara, zan tsaya na jajirce dan ganin na kare martabar kaina, bazan tsaya lokaci guda wani mugu ya rab..."
Bata kai K'arshen zancen ba sakamakon jin da tayi ya yaga rigar barcin da ke jikinta, kalonsa tayi yadda idanunsa suka koma can ciki sun canza launi zuwa ja gabanta ne ya fad'i bata ankare ba sai ji tayi ya cafki na shanunta ya fara tsotsa kamar d'ayan kuma yana wasa dashi, haka yake tsotsan k'irjinta kamar jarinrin da ya kwana biyu baisha nono ba, zafin da taji sun fara mata ne yasa ta fara kokuwar k'watar kanta abun mamaki hawaye ta gani akan fusakarsa yana cewa
"Dan Allah kada kiyi mani haka,kada ki haramta mani abunda Allah ya halatta mani shi, yadda nake jin kaina zan iya mutuwa idan ban same ki ba."
"Idan ka mutu kwananka ne ya k'are yaya wallahi nima bazan iya ba."
Maganar da ta fad'a masa ne yayi masifar k'ona masa rai, sakinta yayi tare da nuna mata key d'in d'akin.
"Fita ki wuce kuma kada na sake ganin k'afarki a d'akin na, saboda kasantuwarmu a cikin d'aki d'aya shine yake saka Ni cikin wannan halin."
Mi'kewa tayi ta d'auki hijabinta ta saka, cikin sauri ta suri key d'in d'akin har ta murza zata fita taji muryarsa yana cewa
"Wallahi na rantse da Allah Wanda ba wani uban giji sai shi, matuk'ar na sake ganin k'afarki a d'akin nan da sunan kinzo barci, to fa ki sani ranar sai na amshi hakki na na aure da yake kanki, baza kibar d'akin nan ba sai na mayar dake cikakkiyar matar aure, idan kuma banyi haka ba to Ni ba Muhammad Muhdeen Sani bane, karki manta da wannan."
Aguje ta fita,shi kuma ya kifa cikinsa ga tsananin ciwon marar da yake ji duk ya ishe sa, sai cizon la'b'bansa yake,dakyar ya iya tashi ya ciro wani magani a cikin bedside drawer, ya d'auki goran ruwa a wajen ya had'iye maganin.
Ita kuma tana fita ta shige d'ayan d'akin dake kusa da nata,ruf da ciki tayi ta kwanta sai kuka take kamar ranta zai fita,yanayin da ta ganshi da alwashin da ya d'auka idan ya sake ganinta a d'akinsa ne yake tayar mata da hankali,gefe d'aya tasan halin Gwaggo muddin ta lura da bata kwana d'akinsa sai ta rakata har bakin k'ofar d'akin ba k'aramin aikinta bane, a haka dai barci ya d'auke ta.
'Bangarensa kuwa sai wajen mintuna talatin kafin yaji dai-dai, Dan maganin baya saurin masa aiki, wanka yaje yayo don dama duk da sanyin A.C dake d'akin sai da ya had'a zufa.
Bayan ya watsa ruwan ne yazo ya kwanta, ba jimawa barci ya d'auke sa.
Da asuba ya ya farka a k'urarren lokaci, don har za'a tayar da sallah hakan yasa alwala kawai yayi ya tafi masallaci,
Ita kuwa wanka tayi ta d'auro alwala tazo ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne tayi azkar kamar yadda ta saba, tana gamawa kuma sai ta tashi ta nufi d'akinta da sallama ta shiga Kallo d'aya Gwaggo tayi mata ta Gane cewa tasha kuka, ganin yadda idanunta suka kumbura sukayi jazir, duk'awa tayi
"Ina kwana Gwaggo?"
Bata amsa mata ba sai ido da ta zuba mata, ita Kam Inteesar batayi tunanin Gwaggo zata fahimci kukan da tayi ba.
"Dukanki yayi ne naga alamar kinsha kuka?,
Kai ta girgiza
"Banyi kuka ba Gwaggo,barcin da na tashi ne"
"Ni zaki rainawa haankali?nasan idon kuka nasa na barci, idan akwai abunda yake maki da baki so ki sanar dani dan Allah."
"Ba komai Gwaggo, hanaki yayi ki fad'a ko?zaizo ya same ni ina nan ina jiransa, tunda ke amana ce."
Gabanta ne ya fad'i tana Allah yasa kada ya sanar da Gwaggo idan ta tambaye shi, mi'kewa tayi ta cire hijabin ta Ciro wani kaya zata sauya,idanun Gwaggo ne ya sauka akan rigar da Muhdeen ya yaga gabanta, da mamaki ta kalli rigar amma sai tayi shiru kawai, Dan tasan Inteesar ba zata fad'a mata ba ko ta tambaye ta,
Yana kwance a d'akinsa Yana waya da Sumayya, inda yake cewa
"Kinga kibar wannan maganar kawai kizo gobe."
"Ya zan zauna gida d'aya da wannan tsohuwar why not ba zaka bari ta tafi ba."
"Kinga idan har kina sona kuma da gaske kinyi missing d'ina to ki bar London ki dawo gobe."
"Ok zan dawo zuwa jibi"
Acikin zuciyarta Tana mamakin shi da yace ta bari Gwaggo ta tafi yanzu ya canza magana, ta'be baki tayi dan bata san dalilinsa ba.
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll😍😘
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page4️⃣9️⃣
A cikin zuciyarta tana mamakin shi da ya ce ta bari Gwaggo ta tafi yanzu ya canza magana, ta'be baki tayi dan bata san dalilinsa ba.
Da misalin k'arfe goma na safe Inteesar ta gama duk ayyukan ta da zata yi na cikin gidan,d'akinsa ya rage kuma yana ciki ba zata iya shiga ba,hatta breakfast ta shirya masu ta jera a dinning table,ta sanar da Gwaggo cewa ta kammala amma Gwaggo Bata tashi ba,yau 'yan fad'a da take yi na rashin breakfast da wuri bata yi ba.
Wanka Inteesar tayi ta shirya cikin riga da siket na atamfa, d'inkin ya mata kyau kuma ya bayyana kyawun surarta da Allah ya mata, powder kawai ta shafa bayan ta shafa mai sai turare mai dad'in k'amshi.
Gwaggo ce da kanta yau taje d'akin Muhdeen don kiransa,samunsa tayi yana waya dan haka ya sallami wanda suke wayan da shi.
"Barka da safiya Gwaggo"
"Yauwa barka dai kaga na shigo maka d'akinku kai tsaye ko?to naga ita tana can ne nasan kai kad'ai ne shiyasa."
Ido ya zuba ba tare da ya ce komai ba,cigaba da magana ta yi
"Nace lafiya dai ko?"
Da mamaki ya kalleta don bai fahimci tambayar da take masa ba,ji yayi ta cigaba da cewa
"Naga alamar jiya akwai matsala tsakaninka da 'yar albarka."
Ido ya zuba mata yana nazari,kafin ya fara tambayarsa kansa cewa kodai Gwaggo la'be take masu ne?Kai ya girgiza Dan yasan da ace taji ba ruwanta da 'boye zata yi magana ne.
"Naga da ta shigo yau da safe gaban rigarta a yage take,kamar tayi kokawa da kura kaima ga shi na ganka kamar wanda ya tashi daga jinya,shin bata baka hakkinka na aure ne ko kuwa dai tana iya k'ok'arinta kaine jarabarka tayi yawa bata iya d'aukar nauyinka?"
Wani irin kallo ya watsawa Gwaggo wanda ita ma bata san ma'anarsa ba,don ita ba ruwanta da kunya ko wani 'boye-'boye,kauda kansa yayi gefe.
"Mtsww matsala ta da kai kenan,idan ana tambayarka kana wani kauda kai saboda mishkilanci,inda Jabeer ya fika kenan da shi na tambaya da yanzun ya bani amsa,amma kai