Header Ads
Showing 93001 words to 96000 words out of 149432 words

Chapter 32 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1388

Ads at the middle of Article

tayi tana tausaya mata ganin yadda ra rame.


Tana nan zaune sai ga Mummyn Muhdeen da Gwaggo sunzo, mik'ewa tayi da niyyar zuwa ta taro Gwaggo sai taji bazata iya ba saboda yanayin tafiyarta, bayan sun k'araso ne ta durk'usa ta gaishe su, Mummyn Muhdeen ta ce,


"Daughter ya kike fatan kina lafiya"


Sunkuyar da kai tayi ta ce ,


"Alhamdulillah"


Gwaggo ce ta mik'ar da ita tsaye ta ce,


"Tashi 'yar albarka, ya Kuna lafiya ina jikan nawa?"


Kafin ta yi magana ne Muhdeen ya shigo rik'e da hannun Mufuda yana cewa


"Gani nan kaka ta ya kike?"


Fuskarsa d'auke da tsantsar farin ciki, musamman da yaga Gwaggo ya tuna cewa ita ce silar aurensa da inteesar, ada haushin Gwaggo yake kan ta aura masa inteesar amma a yanzun yasan gata tayi masa, ta aura masa irin maccen da yake mafarkin samu, gashi tasan darajar miji bata masa gardama, murmushi yayi Gwaggo ta zuba masa ido ta ce,


"Kai kuma fara'ar me kake ne?"


Ba tare da ya ce komai ba ya durk'usa ya gaida Mahaukaciyarsa.


"Mummy ina kwana?"


Lafiya qalau son ya iyali da aiki?"


"Alhamdulillah"


Umma ce ta bud'e idanunta tare da kallonsu d'aya bayan d'aya, Inteesar ta k'arasa gabanta ta ce,


"Umma ya jikinki?"


Murmushi tayi tare da rik'e hannun inteesar ta ce,


"Naji sauk'i"


"Umma wallahi hankali na ya tashi sosai da naji baki da lafiya"


Murmushi tayi


"Ki kwantar da hankalinki naji sauk'i"


Muhdeen ne ya durk'usa ya gaida Umma ta amsa masa cikin sakin fuska tare da masa godiya, don an fad'a mata shine yasa a dawo da ita nan.


Jabeer ne ya turo k'ofar ya shigo da sallama, ganin Muhdeen yasa ya ce,


"Alhamdulillah, dama zan kira ka ne kazo ka duba wasu patients da suke buk'atar kulawarka."


Kallon mamaki Muhdeen ya masa ya ce,


"Da banzo Asibitin ba waye zai duba su, to nikam ina..."


Kafin ya k'arasa yaji muryar Mummy tana cewa


"Dama Dadynka nason ganinka, sau uku yana zuwa asibitin nan baya ganinka sai dai Jabeer, ka fara wasa da aikinka kana barin Jabeer da aiki shi kad'ai, don haka ka koma kamar da bana son rashin mauda hankalinka kan aikinka, ko kana da wani aiki ne bayan wannan?"


"Kuyi hak'uri Mummy za'a gyara"


Da misalin k'arfe d'aya na rana Inteesar da Mufida suka nufi masallacin da mata suke shiga suyi sallah, bayan sun idar ne kasancewar su biyu ne a cikin masallacin yasa Mufida cewa


"Wai ni me damunki ne naga kina tafiya a gwale kamar 'yar kaciya."


Kai ta girgiza alamar ba komai


"Akwai komai mana sai dai idan bai cancanci na sani ba."


"Haba Mufida kinsan ba abunda zan 'boye maki, ina tausayin kaina ne."


"Tausayin kanki kuma bayan naga Yaya na yana sonki"


"Injiwa ya fad'a maki yana so na?idan akwai waccr ya tsana nine?"


"Meye dalilinki?"


"Zan fad'a maki amma sirri na ne,kada Wanda ya ji"


Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,


"Yayanki baya so na ya tsane ni, tun ranar farko da ya dawo daga k'asar waje kik kira ni na gaishe sa naga tsanar da ya mani, dalili na ne ranar kema ya kore ki, duk da cewar kusan kullun Ina gidanku, idan na gaishe sa baya amsawa sai ya buni da harara, sai dai idan yaga idon mutane yake amsawa, akwai ranar da banida lafiya kika kira ni a waya nazo na gidanku wai Gwaggo na nema na, a ranar bansan yana nan ba naje zubar da yawu bisa rashin sani watsa masa, maruka biyu ya bani wanda ban ta'ba jin zafin makamancinsa ba, lokacin da yaga ba kowa falonku ni kad,'aice na kwanta saboda rashin lafiyar da nake haka ya kira ni d'akinsa ya saka ni wankin kayan a toilet nasa, zanyi amfani da washing machine ya Hana na wanke da hannu, sannan yasa ni na shanya kayan a rana sannan nayi gadin kayan a cikin rana har sai sun bushe, haka nayi sannan ya ce na goge su, hantara kala-,kala yake mani baku sani ba a cikin gidan, ki da aka d'aura mani aure da shi ya ce na d'auka zaman gidan kurkuku nake, a daren farkon da aka kaini ba irin cin mutuncin da baiyi mani ba, ya ce kuma sai ya sake ni, haka ya dinga bautar dani da ayyukan da suka fi k'arfi na, baya son na huta idan yaga na kwanta Ina barci ba aiki ba haka zai d'auko ruwan sanyi a fridge ya watsa Mani a jiki na, na farka a gigice, idan zan canza kayan zai hana a haka zasu bushe a jiki na."


Mufida ce ta fashe da kuka ta rungume ta a jikinta sannan ta ce,


"Shine baki fad'awa kowa ba?"


Kuka itama tasa ta ce


"Bzan iya ba ina jin tsoronsa ada haka da matarsa ta dawo nice nake komai a gidan na gurka mata abuncin da take son ci, sannan na gyara mata d'akinta da gadonta na wanke mata toilet d'inta."








Daga alk'alamin✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)






Don k'arin bayani


09065327995






Love you oll😘😍


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa.




*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*


Page5️⃣5️⃣


"Bazan iya ba ina jin tsoronsa ada, haka da matarsa ta dawo nice nake komai a gidan na girka mata abincin da take son ci, sannan na gyara mata d'akinta da gadonta na wanke mata toilet d'inta."


Tsuki Mufida ta ja tare da cewa


"Kina jin tsoronsa shine kika tsaya ya mayar da ke tamkar baiwarsa shi da matarsa, kika zauna kina masu bauta? baki da wanda zaki fad'awa ne ko da ace baki fad'awa kowa ba ai zaki k'watarwa kanki 'yanci ne, amma ki zauna kamar wata mara galihu? Ki ce kina tsoronsa yana da wutar saka ki ne?"


Dafe goshinta tayi cike da takaici tace,


"Wallahi inteesar ki bani kunya, haba mana idan nice ke wallahi koda a ce ban fad'awa kowa zan iya fad'a maki saboda amintan da ke tsakaninmu, ba abunda zan iya 'boye maki kema na d'auka haka ne a wajenki ashe yanzun bankai can ba kin sauke ni a mizanin da kika d'aura ni ada."


Girgiza kai inteesar tayi idanunta cike da k'walla ta ce,


"A'a Mufida wallahi ba haka bane, bamu 'boyewa juna komai wannan karan abunda yasa ban fad'a maki ba saboda ke k'anwarsa ce, zaki iya zuwa ki fad'awa mahaifiyarku kuma hakan zaisa ya sami matsala da iyayensa, ni kuma bana son a ce saboda ni ya samu matsala da iyayensa bazan so hakan ba."


"Aiko sai na fad'awa Mummy bazan zuba ido ina ganinki cikin damuwa da bak'in ciki ba, dole na fad'a asan abunyi domin rayuwa ba zata yiwu a hakan ba, domin kuwa ke ba baiwa bace."


Hawayen da suka cika mata ido ne suka samu nasarar zubowa ta ce,


"Kinga wannan maganar da mukayi tsakaninmu ne ki d'auke shi a matsayin sirri, don Allah ina neman alfarma a wajenki da kada ki fad'awa kowa maganar nan, kiyi mani alk'awari
don Allah."


Girgiza kai Mufida ta yi


"Gaskiya bazan maki wannan alk'awari ba, domin a wuri na wani abu ne mai kamar wahala."


Hannayenta biyu rik'o cikin nata ta ce,


"Kada ki damu yanzun ba kamar da bane, inteesar d'in da kika sani a da to yanzun ba ita bace, cin kashin da sukayi mani a da na d'auka to yanzun bazan d'auka ba na canza."


Murmushin takaici Mufida tayi tare da cewa


"Yaushe kika canza? ke d'in da na sani ce zaki iya canzawa? bank'i ba dai idan yanayi ya saki canzawa, idan kuma ba ya sonki ne gara a raba ku da ya dinga cutarki a banza a wofi, zaki samu mai sonki ya aure ki kiyi rayuwa mai dad'i, Ina fatan dai ba wani abun da ya shiga tsakaninki da shi na fannin auratayya ko? don a cikin labarin da kika bani banga alamar hakan zai iya faruwa ba ko?"


Kuka mara sauti ta saki tare da goge hawayenta ta ce,


"Mufida aikin gama ya riga da ya gama."


Da mamaki ta kalle ta


"Ban gane aikin gama ya gama ba, kina nufin a cikin wannan halin da kike ciki kika iya bashi kanki?"


Cikin muryar kuka ta ce


"Bani da za'bi Mufida, ko kece a cikin wannan yanayin da nake ciki dole ba yadda zaki iya"


Tsuki ta ja


"Dalla can gafara, har akwai wani yanayin da nake ciki da zan bari ya mori jiki na
irin wannan zamantakewar? shi fa ya ce baya sonki kuma zai rabu dake, wato idan ya ci moriyar ganga kenan sai ya yada koranta ko? idan ya gama dake ya mayar dake fanko sannan zai rabu dake ki koma gidanku, duk mijin da ya aure ki fanko ya aura, wallahi ka fad'a mani haka ne zan amince da kai kina abu kamar ba wayayya ba."


"Mufida wannan abun fa jiya ne ya faru, idan kin kula bana iya tafiya yadda ya kamata, kuma bani da za'bi yayi amfani ne da rashin lafiyar Umma ta ya d'auke shi a matsayin makami, bayan kin kira ni a waya kin sanar dani shine naje don neman izininsa, ya nuna mani idan ban amince da shi ba to bazan je na gaida Umma na ba, kuma ina son zuwa na ganta hankali na ya tashi bansan halin da take ciki ba, dole na barshi yayi yadda yake so."


"Aikin banza dan ya d'auki wannan a matsayin makami shine kika yarda da shi? ya same ki ne shiyasa."


Murmushin takaici inteesar ta yi tare da cewa


"Asalin samu kuwa, Mufida wallahi ya wahalar dani a daren jiya nasha azaba a hannunsa har na gwammaci mutuwa ta, tun ina gane komai har nazo bana ganewa ban k'ara sanin me ke faruwa ba sai tsintar kaina nayi a band'aki cikin ruwan zafi, ashe suma nayi tsawon awanni hud'u ya d'auka yana wahalar da rayuwa ta, tun k'arfe goma har k'arfe biyun dare."


"Koma mene ne kika jawo wa kanki, lallai namiji ma fa bashi da kunya."


Girgiza kai kawai tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba, inteesar dai zuba mata ido tayi tana ganin cewa lallai Mufida k'awa ta gari ce mai son farin cikinta, gashi dai Muhdeen yayanta ne amma bata goyi bayansa ba a matsayin d'an uwanta ba.


Hira suka d'an ta'ba daga nan suka mik'e suka nufi komawa d'akin da aka kwantar da Umma.




'Bangaren Sumayya kuwa bata tashi daga barci ba sai k'arfe d'aya da rabi, yunwa ne ya addabe ta sosai don tun lokacin da Muhdeen ya korr ta sai ta koma d'akinta ta kwanta, shine bata fsrka ba sai yanzun toilet ta shiga tayi wanka, bayan ta fito ne ta saka kaya ba zancen sallah ma, ta nufi kitchen don a tunaninta Inteesar ta gama girkin abincin rana.


Kai tsaye dinning room ta fara nufa, gani tayi wayam ba'a jera komai ba don haka ta tsaya a falo ta rik'e k'ugu cikin bala'i ta ce,


"Lallai ma yarinyar nan wato na tashi daga barci banga ta gyara mun d'aki na ba, kayan da na cire na zubar da su a k'asa suna nan har yanzun, toilet ma bata wanke mani ba,sannan nazo na tarar bata gama girki ba wato yunwa ta kashe ni ko?"


Girgiza kai tayi tare da k'walawa inteesar kira cikin masifa


"INTEESAR! INTEESAR!! INTEESAR!!!"


Jin shiru ne yasa tayi kwafa ta nufi kitchen d'in a fusace, tana shiga tayi turus tayi ganin kitchen d'in wayam ba alamar ma anyi girki, ranta a 'bace ta furta


"Lallai ma yarinyar nan wuyanta ya isa yanka, ubanwa ta ajiye da zai mata aikin da bata yi ba? lallai yau zanyiwa yarinyar nan wulak'ancin da ban ta'ba yi mata ba."


Kai tsaye ta nufi part d'in Inteesar, dan zuwa d'akinta, da k'afarta ta bankawa k'ofar duka, k'ofar ta bud'e ta shiga ciki tare da cewa


"Ke 'yar matsiyata ubanwa za..."


Dakatawa tayi da maganar da tayi niyar yi sakamakon ganin k'awatuwar d'akin inteesar d'in, kasancewar yau ne rana ta farko da ta fara shigowa d'akin, ganin furniture's masu tsada da aka zuba mata ga d'akin yasha gyara sosai komai na d'akin abun sha'awa ne, ta'be baki tayi tare da cewa


"Ina wannan ba iyayenta bane suka sayi mata wannan kayan d'akin, don ba suda kud'in siye mata su, bayan naji ance uban nata dankali yake siyarwa bazai iya siyen ko kwatankwacin kayan nan ba sai dai idan iyayen Muhdeen da suka had'a auren ne suka siye mata, ganin ba kowa yasa ta k'arasa bakin k'ofar toilet ta k'wank'wasa jin shiru ne yasa ta nufi hanyar fita.


Bata zame ko ina ba sai k'ofar d'akin Muhdeen,tura k'ofar tayi tare da shiga,har toilet ta shiga bata ganshi ba tambayar kanta tayi da cewa


"Ina yaje ne kuma?"


Idanunta ya sauka akan gyalen d'an kwalin inteesar dake gefen gado, sai kuma d'an kunnenta guda d'aya shima a saman gadon, gabanta ne ya fad'i Wanda sai da taji wani abu kmar dutse ya danne mata k'irji.


"Me nake shirin gani ne haka? me d'an kwalain yarinyar nan yake yi. d'akin nidai nasan bazai ta'ba nemanta ba don bai d'auke ta a mace ba, wata kila ta shigo gyara masa ne d'an kunnen ya fad'i ta mance d'an?"
kwalinta.


"To wai Ina my love ya je ne? d'an jim taui tare da k'arewa d'akin kallo tayi sannan ta fice ga uban yinwa da ke cinta kuma ita bata iya girka komai ba ki ruwan zafi ba zata iya dafawa ba, rasa abunyi tayi Dan haka ta nufi d'akinta wayarta ta d'auka wayarta number Muhdeen ta shiga kira yakai sau biyar tana kirnsa bai d'aga ba dan haka ta ajiye wayar ta shiga tagumi tana mamakin sauyawar da Muhdeen yayi daga jiya zuwa yau ya canza mata sosai da sosai, fita tayi tare da Kiran Direban gidan ta aike shi yayi mta takeaway ko zata samu abincin da zata ci.




Inteesar da Mufida suna komawa wajen Umma suka tare ta farka, da farin ciki inteesar ta k'arasa wurinta ta rungume ta.


"Umma na ya jikinki?"


"Da sauk'i kunyi sallar?"


"Eh munyi Umma"


Mufida ce ta ce


"Sannu Umma ya jikinki?"


Murmushi ta yi


"Da sauk'i Mufida"


Kallon gefen su Mummy tayi tare da cewa sannu


"Sannunku Gwaggo"


Gwaggo da Mummy suka had'a baki wajen amsawa, sai a lokacin idanunta ya sauka akan Muhdeen, tana kallonsa taga ya zuba mata ido yana kallonta tare da sakar mata lallausan Murmushi, da sauri ta d'auke kanta tare da tura baki, karaf akan idanun Ummanta sai dai tayi shiru tunda tana fama da kanta,Mama Huraira ce ta ce da inteesar


"Inteesar tunda kika zo banga kinci komai ba, kina ta zama da yinwa."


Murmushi ta yi tare da cewa


"Mama Huraira na k'oshi"


Muhdeen ne ya kalle ta ya ce


"Me kika ci da kika k'oshi? biyo ni mu tafi office d'ina kici abinci"


Kunyar mutanen da ke wurin ne ya kama inteesar, shi kuma baiga abun jin kunya a wurin ba, fita yayi ta zauna kamar bata ji me ya ce ba, Mama Huraira ce ta kalle ta ta ce,


"Ba kiranki mijinki yayi ba?"


Tura baki tayi ta ce


"Nifa na k'oshi"


Had'e fuska Mama Huraira ta yi tare da cewa


"Bana son gardama"


Dan haka dole ta fita, tsaye ta same shi yana jiranta, Dan haka suna fita ya rik'e hannunta yaja suka fara tafiya hannunsu sark'e cikin na juna sunyi kyau sisai, tayi k'ok'ari ta k'wace hannunta amma ina ta kasa da haka ta bishi suka dinga tafiya a hankali, duk inda suka wuce mutane sai an kalle su yadda suka dace da juna, kasancewarsa Doctor da aka sani yasa mutane ke ta gaishe su, ita dai ko amsawa bata yi, har office d'insa suka nufa suna shiga ya tura k'ofar ya rufe , wayarta ce ta soma ringing ta ciro daga cikin jaka ganin sunan Usman ne yasa gabanta ya fad'i, har ta katse bata d'auka ba sau uku yana kira bata d'aga ba,ganin yanayinya yasa ya gane akwai wani abu .


"Ya ana kiran wayarki baki d'agawa."


"Eh kiran baida mahimmanci ne."


Take sai ga wani kira ya shigo, duba sunan me kran yayi Usman, take ya murtuk'e fuska don ya tuna cewa Usman ne saurayin da ke son inteesar, lokacin da Mummy ta matsa ya je gidansu inteesar ya gaishe ta Usman ya kad'e ta da mota, kuma shine wanda ya ta'ba kama ta tana waya da shi bayan aurensu har ya amshe mata wata gaba d'aya, kuma shine ya gansu ya d'auko inteesar a gaban motarsa tana tayi masa dariya shima yana mata kallon soyayya, take yaji wani d'aci a ransa har idanunsa suka rikid'e suka koma ja, text message ne ya shigo wayar ya mik'a mata hannu tare da cewa


"Bani wayar nan"


Shiru tayi tare da zuba masa ido banu alamar tsoronsa a tattare da ita kmar yadda ta saba tsoronsa, don haka itama sai ta had'e fuska kamar yadda ya had'e nashi fuskar.








*Daga alk'alamin*✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)






*Don neman k'arin bayani*


09065327995




Love you oll😍😘


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.




*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*


Page5️⃣6️⃣


--------Shiru tayi tare da zuba masa ido ba alamar tsoronsa a tattare da ita, kamar yadda ta saba tsoronsa, don haka itama sai ta had'e fuska kamar yadda ya had'e nashi fuskar.


Fusgar wayar yayi daga hannunta dai-dai lokacin da sak'o ya shigo ya fara karantawa kamar haka.


"ASSALAMU ALAIKI YA SARAUNIYAR MATA, DAN ALLAH KI DAINA AZABAR DA NI HAKA, KINSAN HALIN DA NA SHIGA NA RASHIN GANINKI KUWA? YANZUN HAKA INA K'OFAR GIDANKU ANCE BA KOWA A GIDAN, DAN ALLAH KI TAIMAKA KI 'DAUKI WAYA TA KO ZANJI SANYI A ZUCIYA TA, DOMIN RASHINKI A RAYUWA TA TAMKAR JIRGIN SAMA NE BABU MATUK'I, I LOVE YOU."


Bayan ya gama karantawa ne ya kalle ta tare da cewa


"Wato har yanzun kina waya da tsohon saurayinki da igiyar aure na akanki ko?"


Murmushin takaici tayi ta ce,


"Igiyar aurenka yana wuyar matarka da ka baro a gida, dan ni ba igiyar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads