Showing 126001 words to 129000 words out of 149432 words
Chapter 43 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
tsani kyakkyawar mace,idan har naga mace ta haɗu ta ko ina bata da cikas wallahi sai naji na tsane ta musamman idan na fahimci ta fini ko akan hanya ne bana son ganinta ballantana wannan da ta aure mani miji."
Dariya Bashir yake ta ƙyaƙyatawa har Sumayya ta fara jin haushinsa, dan haka ta buɗe murfin motar ta fice ranta a ɓace.
Komawa tayi ɗakin ta tarar Salisu da Biliyaminu ne sai Mummy, zama tayi gefen gadon da Muhdeen yake tana cewa
"Allah sarki Allah ya tasarmun da kai ya baka lafiya."
Ta ƙarasa maganar idanunta na tara ƙwalla, gaba ɗayansu suka amsa mata da Ameen inda Mummy ta ce,
"Dan Allah ku daina masa kuka haka, jikinsa fa da sauƙi insha Allahu zai miƙe kamar baiyi ba."
Kuka ta sake rusawa tana cewa
"Mummy ta yaya hankali na zai kwanta? mijina yana cikin wani hali l."
A'a kinga wannan ba abunda tada hankali bane addu'a kawai zamuyi masa Allah zai bashi lafiya, nan dai Umma ta dinga kwantar mata da hankali akan ta cire samuwar dake cikin zuciyarta, ana haka ne Bashir ya shigo ko kallon inda yake bata yi ba, daga bisani suka fita zuwa wajen Jabeer, ɗakin ya rage daga Mummy sai Inteesar.
Shiyoyin sallar magariba ne, Mufida ta shigo hannunta ɗauke da basket da aka jera kayan abinci a ciki.
"Assalamu alaikum"
Mummy da Sumayya suka amsa mata
"Wa'alaiki salam"
"Mummy ya jikinsa?"
"Jiki da sauƙi Mufida"
"Allah ya bashi lafiya."
Suka amsa da Ameen, Mummy ce ta kalle ta ta ce,
"Baki ga Auntynki bace?"
Yamutshe fuska tayi tare da cewa
"Mummy ni banga Aunty na anan ba gaskiya."
Kallon gargaɗi Mummy tayi mata ba tare da ta ce komai ba, sanin dalilin kallon ne yasa ta kalli Sumayya murya ciki ciki ta ce,
"Ina wuni?"
Itama kanta Sumayya taji zafin abinda Mufida tayi mata, amma sai ta dake ta nuna hakan bai dame ta ba kasancewar a gaban Mummy suke,
"Lafiya lau Mufida ya kike?
Kauda kanta gefe tayi tare da cewa
"Lafiya"
Dan tunda suka je gidan Muhdeen da Gwaggo lokacin Sumayya na Amarya har tayiwa Gwaggo rashin kunya, tun daga wannan lokacin Sumayya ta fice daga zuciyar Mufida, ganin lokacin salla yayi ne yasa Mummy cewa zata tafi tayi sallah, Mufida ma tabi bayanta suka fice, sai a lokacin Sumayya ta samu dama ta kira Jumy take sanar da ita halin da ake ciki na hatsarin Muhdeen, daga can ɓangaren Jumy ta ce
"Anya ƙawa ta babu sa hannunki a hatsarin nan kuwa?"
"Na san halinki nasan abunda zaki iya aikatawa ."
"Dariya Sumayya tare da cewa
"Tabbas kinyi gaskiya ba abunda bazan iya aikatawa ba, amma ki sani wannan hatsarin masa ba saka hannuna a ciki, ai kinsan idan in son mutum bazan iya cutar da shi ba matuƙar kuwa kika ga na cutar da mutumin dake ƙaunata to haƙiƙa ya kainii bango ne wanda hakan shine masalaha."
Taɓe baki Jumy tayi tare da cewa
"Ba wata masalaha da sai an halaka wani, nifa nan da kika ganni duk iya shige da isakanci na wallahi bazan iya yin kisan kai ba."
"Hmmm ba'a kaiki bango bane wallahi da ankaiki bango da ba zaki daɗi haka ba, sannan lokacin da zaki aikata hakan ma ba zaki sani ba, nayi yunƙurin kashe Inteesar a baya ta tsallake rijiya da baya, amma matukar ta kaimu bango to fa wallahi bazata sha ba, don idan raina ya ɓaci ko zuciyata bana saurara duk abinda yazo gaba na aikata shi nake."
"To ki guji ranar da zakiyi nadama kuwa wanda lokacin nadamar ba zata maki amfani ba."
Maganganun Jumy ba suyi mata ba dan haka ta katse kiran tare da kiran lamabar wayar shila, bugu biyu shila ta ɗauka suka gaisa zancen da yayiwa Jumy ita tayiwa Shila, sai dai shila tunzura ta ta dingyi akan duk abinda ta ce zata yi, a haka sukayi sallama ta kashe wayar .
Sai da akayi sallar isha'i ne su Mummy suka dawo bayan sunyi sallar isha'i, Sumayya tana nan zaune bata tashi ta je sallah ba.
Da sallma suka shigo ɗakin ta amsa masu, a tunanin Mummy Sumayya bata je. sallah bane saboda kada a bar Muhdeen a ɗaki ba kowa dan haka ta kalli Sumayya ta ce,
"Sumayya tunda mun dawo idan zakiyi sallah ki tashi kije kiyi ko."
Dai lokacin Gwaggo da Inteesar ta suka shigo ɗakin, Sumayya ta miƙe tare da cewa
"Bari na tashi naje nayi sallah to."
Kai Mummy ta jinjina tare da cewa
"To sai kin dawo."
Daga nan ta fice Gwaggo ta raka ta da harara, Mummy tayi magana cikin sigar lallashi ta ce,
"Gwaggo don Allah ki fita harkar yarinyar nan, tunda yanzun dai bata sake wani laifi ba."
Gwaggo ta nuna Mummy da yatsarta manuniya ta ce
"Fatima ki kiyaye ni fa ki fita a ido na na rufe, saboda ba ke tayiwa na mi tayiwa rashin kunya da fitsara, ai idan mayar ya manta ai uwar ɗa bai ci ta manta ba, kina cewa wai bata sake wani laifin ba sannunki kenan, amma wannan yarinya duk inda kike neman kaba'ira takai."
Ita dai Mummy bata ce komai ba har Gwaggo ta ƙaraci sababinta tayi shiru.
Jabeer ne ya shigo da sallama gaishe da su Mummy da Gwaggo yayi yayinda Mufida ta gaishe sa,zama kusa da Gwaggo ya ce,
"Ke wannan tsohuwar ba zaki tafi gida ki huta ba?"
Kai ta girgiza
"Ina naga tafiya ga miji kwance ko motsi baiyi ba."
"Kada ku damu ina sa ran insha Allahu ya kusa farkawa"
Mummy ce ta kalli Mufida ta ce,
"Ki dubawa yayanki abinci mana"
Mufida ta tashi da niyyar zuba masa abincin yayi saurin cewa
"Am okay"
Dan haka Mufida ta koma ta zauna inda Jabeer ya cigaba da cewa
"Yanzun magana cin abinci Mummy."
Sumayya kuwa tunda ta fita da sunan zatayi sallah sallah ta zauna gefen masallacin, tana tunanin ta ina zata fara, dan ko sallar asuba barayi na ballantana azahar da la'asar, wayarta ta ciro ta kira number Bashir bugu biyu ya ɗaya
"Hello Sumy ya akayi ya farka ne?"
"Tukunnah dai bai farka ba tukunnah"
"Okay nan zaki kwana Asibitin ne?"
"Wace ni da kwana a Asibitin alhalin wannan fitina miyar tsohuwar na nan ai ba mu zama inuwa ɗaya, gida zan koma da safe na dawo."
"Okay ko nazo na taya ki kwana ne"
Da sauri ta furta
"What's"
Dariya yayi tare da cewa
"Wai sai na maye gurbinsu tunda baya nan ko?"
"Kasan me kake faɗa kuwa? kazo gida na ka kwana bayan ga mai gadin gidan da sauran ma'aikatan gidan zasu ganka ka kwana bayan abokinka baya nan? me zasauyi zato?"
Taɓa baki yayi tare da cewa
"To ke kizo mana ki same ni idan har ba nan zakai kwana ba ba wanda zai san inda kika kwana, su a nan zasu ɗauka gida kika je kika kwana su can ma gidan zasu ɗauka asibiti kika kwana ba wanda zai sani."
Shiru tayi tana nazari kafin ta ce,
"Shikenan sai nayi tunani amma idan kaji ni shiru to ka tabbatar a Asibitin zan kwana tare da mijina."
"Hmm ai naga dole zaki fi buƙatata saboda zanyi maki amfani a daren yau shi kuma fa meye zai tsinana maku?"
"Kaga kada fa ka zaƙe da yawa dan zaka iya fuskantar tirjiya daga gare ni, kuma duk son da nakeyi maka baikai wanda nake masa ba, i love him more than everything dan haka kada ma kayi tunanin haɗa kanka da shi dan ya fika ta kowace fuska."
"Kada ki nemi gaya mun maganar da zuciyata ba zata iya ɗauka ba."
Tsuki tayi tare da kashe wayar
Tashi tayi ta je ta jero dalilin da ake binta tun daga asuba har isha'i.
Bayan ta idar ne ta koma ɗakin ta samu suna cin abinci, Mummy ta kalle ta ta ce,
"Sumayya kin idar da sallar ko?"
"Eh Mummy"
Zama tayi ta fara daddanna wayar ta, Mummy ta kalli Mufida ta ce,
"Ki zubawa Sumayya abinci mana"
"To Mummy"
Daga nan ta janyo Basket d'in da aka jera abincin tare da ciro plate ta zuba mata abincin, ta haɗa mata da ruwan sha, karɓar tayi don dama yunwa take ji sosai.
Suna gama cin abincin ne Inteesar wacce rabin hankalinta na wajen Muhdeen ta lura da ya fara motsi yana juya kai tare da yamutshe fuska.
Cikin tsananin farin ciki ta ce
"Ya farka"
Gaba ɗaynsu suka maida hankalinsu ga Muhdeen, gani sukayi yana juya kai amma idanunsa a rufe, da sauri suka ƙara da wajen gadon Jabeer ya riƙo hannunsa tare da kiran Sunansa.
"Muhdeen sannu ko"
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya amsa da yauwa, Sumayya ta ce
"Sannu ya jikinka?"
Ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ce,
"Yauwa"
Sai a lokacin Inteesar tayi magana ta ce,
"Sannu yaya ya jikin?"
Jin saukar muryarta a cikin dodon kunne da yasa ya buɗe idanunsa da sauri dan tabbatar da abinda kunne da ya jiyo masa, idanunsa ne suka sauka akan nata yaga tana sakar masa murmushi, zuba mata ido yayi don tunda yake da ita bata taɓa yi masa murmushi ba sai yau, gani yake kamar ba gaskiya bane mafarki yakeyi dan haka sai ya miƙa hannunsa ya riƙo nata hannun, cikin muryarar da bata fita ya furta
"Inteesar kece?"
Kai kawai ta gyaɗa masa tana murmushi ba tare da tayi magana ba, sun kai mintuna biyu zuwa uku suna kallon juna suna sakarwa juna murmushi, kowa kallonsu yake yana murmushi saɓanin Sumayya wacce baƙin ciki da takaici duk ya ishe ta, ta gaishe sa amsawa yayi ba tare ba tare da ya ko kalle ta ba, amma daga jin muryar Inteesar ya buɗe ido ba shiri sai kallon juna suke kamar zasu haɗiye junansu, ƙoƙarin tashi zaune yayi yana cije leɓe har lokacin hannunsu na riƙe da juna, Gwaggo ce ta ce,
"Muhammadu ya jikinka?"
Kai ya jinjina tare da cewa
"Da sauƙi Gwaggo"
Nan ma Mummy da Mufida suka gaishe su ya amsa masu, Jabeer ne ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo da kofin shafi ya bashi daƙyar yasha sannan Jabeer ya bashi magani yasha.
Haka farin ciki ya lulluɓe zuƙatansu
Ganin ƙarfe goma tayi ne yasa yasa Jabeer ya ce su tafi gida shi yana tare da shi, hakan yasa suka tafi Gwaggo, Mummy, Mufida da Inteesar sukayi masa sallama zasu tafi, maraice fuska yayi alamar baiso tafiyarsu ba kuma duk saboda Inteesar ne, Mummy ce ta kalle shi tayi murmushi
"Son kada ka damu da sassafe zamu dawo."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa daga nan sukayi masa sallama suka tafi, Jabeer ne ya kalli Sumayya ya ce,
"Ke fa ba zaki tafi bane yanzun dare yayi."
Fuskarta ba walwala ta ƙarasa wajen gadon Muhdeen ta ce,
"Baby baka ganni bane?"
Murmushi yayi ya tare da cewa
"Ba kece kika fara mani magana bayan Jabeer ba? mun gaisa ai."
Cikin ƙunar rai ta fara magana
"Shine ko kallo ban ishe ma ka ba ko? amma daga jin muryar waccan bagidajiyar kucakar yarinyar ka maida hanakalinka akanta saboda tafini a wajenka ko?"
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Bakwai ta fiki a wajena bane a'a matsayinku ɗaya ne ba wacce tafi wata"
"Ba haka bane ka fifita ta a kaina mana, ki ta kaina ma baka bi ba sai da ta fita sannan ka kalle ni ka kuma kama hannunta ka riƙe kana kallon fuskarta kamar ka samu farin wata, me ta fini da shi da ka maida hankalinka akanta ka amsa mani."
Dade kansa yayi jin yana sara masa don baya son hayaniya, lura da hakan yasa Jabeer ya ce,
"Sumayya meye haka? mutumin da yake cikin wannan halin ne zaki saka a gaba kina damunsa da hayaniya? wannan ba dai-dai bane."
"Yanzun ne kasan ba dai-dai ba? lokacin da nayi masa magana bai kalle ni ba ya zubawa waccan 'yar matsiyatar ido me yasa baka faɗa masa wannan ba dai-dai bane?."
Muhdeen kam rintse idanunsa yayi tare da riƙe kansa dan maganar Sumayya ma ciwon kai yake saka sa.
Fita tayi fuuu kamar wacce zata tashi sama, wajen motarta ta nufa ranta a matuƙar ɓaci ga zafin kishin da take ji akan Inteesar ɗin, kai tsaye wayar ta ciro a handbag ɗinta number Bashir ta Kira, bugu biyu ya ɗaga kafin yayi magana ta ce
"Kana ina ne gidanka ko hotel?"
Yana kwance a kan kujerar mai zaman mutum uku ya ce,
"Ina gida ne ya akayi?"
"Lahira zatayi baƙuwa"
Cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa ya ce,
"Ban fahimci inda zancenki ya dosa ba."
"Am on my way"
"Till you come?"
Daga nan ta katse kiran ta tayar da motar tana ayyana yadda zata aiwatar da shirinta, tayar da motar tayi ranar Asibitin ta ɗauki hanyar gidan Bashir.
*Saura pages guda 10 na kammala book 1 insha Allahu, zamu shiga book 2 amma book 2 paid book ne idan kin siya ki karanta*
Daga alƙalamin ✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DON NEMAN ƘARIN BAYANI*
09065327995
Love you oll😍😘
Comments & shara
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne
Sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne.
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page7️⃣1️⃣
Daga nan ta katse kiran ta tayar da motar tana ayyana yadda zata aiwatar da shirinta,tayar da motar tayi ta ɗauki hanyar gidan Bashir.
Horn yayi mai gadin gidan ya leƙo ganin ita ce yasa ya wangale mata gare ɗin gidan ta shiga, bata ma tsaya yin parking da kyau ba ta fito ta nufi hanyar da zata sada ta da falon, tura ƙofar tayi ba tare da tayi sallama ba, ƙamshin turarenta ne ya tabbatar wa da Bashir ta iso,miƙewa yayi daga kwance da yake ya tashi zaune tare da ware hannayensa duka biyu, alamun tazo gare shi, ƙara sawa tayi tare da faɗawa jikinsa ya rungume ta, ajiyar zuciya ta sauke.
"Waye ya taɓa ki? ki kwantar da hankalin..."
Kafin ya kai ƙarshen zancenta ta katse shi da cewa
"Hankali na bazai taɓa kwanciya ba matuƙar tana raye, mutuwarta shine kwanciyar hankaalina."
"Wace ce?"
Wani tunani tayi dan haka bata amsa masa tambaya da yayi mata ba.
"Nace wace ce, mutuwarta ne kwanciyar hankali a gare ki?"
Ƙara tsuke fuska tayi
"Bai shafe ka ba."
"Ki faɗa mani wata kila ma akwai amfanin da zanyi maki."
"Babu wani amfanin da zaka mani a matsayinka na abokin miji na."
"Domin ina da yaƙinin zaka iya taimakonsa ta wata fuskar"
"Badai Inteesar kike ƙoƙarin kashewa ba?"
"Ba matsalarka bace"
"Idan ma ita ce tun yanzun ki fidda abunda ke cikin ranki, domin Inteesar she is innocent.."
"Me ye matsalarka da ita ce, naga matar abokinka ce, bayan haka nana tunanin akwai wata alaƙa a tsakanin ku"
Jinjina kai yayi tare da cewa
"Tabbas ba wata alaƙa a tsakanina da ita bayan ta matar aboki a gare ni, kuma ita ce matar da na fara tunanin mallaka a matsayin uwar ƴaƴa a gare ni."
Da sauri Sumayya ta miƙa daga jikinsa tana masa kallon mamaki, ya cigaba da cewa
"Tun kafin Muhdeen ya fara sonta nake sonta duk ƴan mata da nake da su da kuma waɗanda nake gani banaga wacce ta ta mallaki duk abinda make so a wuri ƴa mace ba sai ta, ita ce ta cika 💯 irin zaɓi na."
Taɓa baki tayi tare da jan tsuki, jin taja tsuki ne ya kalle ta ya ce,
"Kishi kike ne?"
"Allah ya sauwaƙe, akan mijina da make so kamar raina zanyi kishi, shi kaɗai ne nake kishi akansa saboda shine wanda nake haukar so, bayan shi banga namijin da ya isa nayi kishi akansa ba."
Dariya yayi tare da cewa
"Kina kishinsa har haka amma kika kasa killace masa kanki, kike fita kina waufantar da kanki ga wasu mazan da ba baki ba?"
Murmushin takaici tayi tare da cewa
"Ba laifinka bane laifi na ne da na baka kaina dole kayi mani duk cin kashin da kaga dama."
Ƙoƙarin tashi daga jikinsa tayi yayi saurin janyo ta jikinsa ya ƙara katse ta
"Am sorry"
Bata ce komai ba ta cigaba da ƙoƙarin ƙwatar kanta yayinda shi kuma bai sake ta b.
"Don Allah kiyi hak'uri Allah ya huci zuciyarki sarauniyar mata, banyi niyyar ɓata maki rai ba, ke ai baƙuwa ta ce dole na girmama ki, kuma na fahimci matsalarki Inteesar ce ko? to kiyi tunanin hanyar raba da Muhdeen yadda zai sake ta Ni kuma na aure ta, kinga Shikenan ke kin samu damar mallakarsa ke kaɗai Ni kuma na samu mallakar macen da nake mafarkin samunta a rayuwata."
Shiru tayi tana nazarin kalamansa, tabbas ba zata iya jure ganin Muhdeen da kowace mace na raɓarsa ba kuma tasan raba Muhdeen da Inteesar wani abu ne mai wahalar gaske, don ta lura da yadda yake tsaninin son Inteesar yanzun, ga danginsa suna sonta ba zasu taɓa yarda ya rabu da ita ba, mafita ɗaya ce mutuwar Inteesar, bata san lokacin da murmushi ya suɓuce nata ba har sai da Bashir yaji saurin murmushin nata, kallonta yayi yana murmushi.
"Kin amince wane shawara kika yanke?"
"Ka zuba ido kawai kayi jallo"
Daga nan ta tashi ta shiga bedroom ɗinsa kai tsaye toilet ta nufa, wanka tayi ta fito ɗaure da towel zama tayi ta shafa lotion nasa mai ƙamshi bayan ta gama ta juyo ta kalle shi taga yana kallonta yana mata murmushi yayin da ya haye saman gadon tare da jan bargo, ya rufe jikinsa, bayan ta gama ne ya ƙarasa jikin gadon tare da hayewa saman gadon ya shige cikin barhon itama, janyota yayi jikinsa tare da warware towel ɗin da ta ɗaura shima ya cire kayan jikinsa suka soma saɓon Allah kamar yadda suka saba yi.
Washe gari Inteesar na idar da sallar asuba tayi azkar ta nufi kitchen don haɗa breakfast.
Farfesun kayan ciki tayi wanda yaji kayan ƙamshi kamar yadda ta lura Muhdeen yana son shan farfesun kayan ciki da safe, don haka tayi shi Musamman saboda shi ta fere dankalin turawa da plantain ta soya da ƙwai sai ruwan shayi da yaji kayan ƙamshi, tayi kunun gyaɗa da bayan ta jiƙa wake ta wanke ta zuba tattatasai da albasa tayi blendin tayi ƙosai.
Koda Mummy ta fito ƙarfe bakwai ta tarar da Inteesar a kitcheen har