Showing 60001 words to 63000 words out of 149432 words
Chapter 21 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
bai sake zuwa ba sai dai kullun cikin kiran waya yake,dama tunda taji labarin an aurar da ita ta kashe wayan gaba d'aya,sai yanzun da ta kunna wayar Kiran Usaman ya sake shigowa tana ji tana gani har sai da ya mata 5 Bata d'aga ba sai kuka take you a haka har ta kwanta barci 'barawo ya sace ta.
Kamar yadda ta saba k'arfe hud'u na asuba ta farka,wanka ta tashi ta yi ta d'auro alwala tazo ta yi nafila kamar yadda ta saba,daga nan ta fara karatun al qur'ani kamar yadda ta saba,sai da loacin sallar asuba ta yi sannan ta tashi ta gabatar da sallar asuba,bayan ta idar da sallar ta yi azkar da addu'o'i sannan ta Fara ayyukan gidan kamar yadda aka kafa mata doka.
Da misalin k'arfe goma sha biyu na rana ya fito raga cikin d'akinsa,sanye yake da shadda sky blue sai hula neavy blue da ya sanya a kansa da bak'in takalmi a k'afarsa da tsadaddan agogo dake d'aure a hannunsa,ya biyo ta falon Inteesar zai wuce tana zaune tayi tagumi, Jin takunsa yasa ta d'aga kai ta kalle sa sai da ya k'araso ta durk'usa ta gaishe sa.
"Ina kwana?"
Ko kallonta baiyi ba ballantana ya amsa mata,ta cigaba da cewa.
"Ga breakfast na shirya can na shirya maka."
Nan ma shiru ganin yana k'ok'arin fita ne yasa ta ce,
"Adawo lafiya"
Dakatawa yayi tare da jefa mata mugun kallo.
"Wai ke wace irin mayya ce?kinyi magna d'aya ban amsa maki ba,ba sai ki kyaleni ba?"
Tsuki yaja tare da ficewa,wayarta ce ta soma ringing,duban wayar tayi ganin Mummy ce yasa ta sakin murmushi ta d'aga kiran.
"Assalamu Alaikum"
Daga can 'bangaren Mummy ta ce,
"Wa'alaiki salam Daughter ya hak'uri?"
Murmushi ta yi
"Alhamdulillah Mummy."
"Masha Allah"
'Dan jim ta yi kafin ta d'aura da cewa
"Daughter"
"Na'am Mummy."
"Kuna dai lafiya ko?"
"Lafiya lau Mummy"
"Ki fad'a mani gaskiya naji muryarki wani iri,idan akwai matsala ki sanar dani,kinsan Ni na haife sa idan akwai bunda ya ke maki wanda baki so ki sanar dani."
Sahiru Inteesar ta yi ta kasa magana,ganin kamar akwai want abu da Inteesar ke son 'boyewa yasa Mummy cewa,
"Ina son d'in ya ke"
"Ya fita yanzun nan."
Da zai fita ina ya ce maki zaije?"
"Bai sanar dani ba."
Shiru Mummy ta yi kafin ta ce,
"Ki shirya yanzun nan zan kira shi zai dawo ya d'auke ki,zai kai ki giadanku ki gaida Ummanki sannan ya kawoki gida na."
Cikin jin dad'i Inteesar ta ce,
"To Mummy Nagode sosai sai nazo."
Dagan nan ta kashe wayar ta ajiye a nan kan kujera,sannan ta nufi d'akinta cikin tsananin farin ciki.
Muhdeen kuwa yana tsaka da driving Mummy ta kirasa nayan ya d'aga a cikin bada umarni ta yi magana.
"Son ka koma gida ka je ka d'auko matarka ka tafi da ita ta gaida mahaifiyarta da mahaifinta kaima ka gaishe su,daga nan sai ku taho nan gidan."
Bata jira mai zaice ba ta katse kiran.
Dole ya juya akalar motar don kawa gida,dan yau da kansa ya ke driving ba kullun ya ke fita da Direba ba.
Koda ya koma gidan bata nan a falo don haka ya nufi d'akinta,ita kuma lokacin ta fito daga wanka kenan tana d'aure da towel iya rabin cinyarta ya rufe gashin kanta da suka jike da ruwa kafad'arta,tana goge suman kanta dai-dai lokacin da ya shigo d'akin da niyyar yi mata masifa,mutuwar tsaye yayi lokacin da yayi arba da ita,tundaga k'asan k'afarta ya fara kallon zara zaran yatsun k'afarta da suka sha zanen filawowi masu kyau,a hankali yake d'aga k'wayar idonsa har zuwa santala santalan cinyoyinta farare masu kyalli da d'aukar ido,surar jikinta masu Jan hankali ya ke kallo gashin ya zubawa ido kamar na wata ba'indiya hand dryer ta d'auko ta kunna ta fara busar da gashin kanta,bayan ta gama ne ta fara k'ok'arin zare towel d'in da ta d'auka ne ta hango shi tsaye ta cikin mirror,cikin zafin nama ta maida towel d'in ta d'aura tare da janyo dogon hijabinta ya saka,ta'be baki ya yi ya fara magana cikin muryarsa da ta sark'e ya ce
" ki same ni a mota."
Daga nan ya saka Kai ya fice daga d'akin,ita kuma ajiyar zuciya ta sauke tare da hanzarin shiryawa.
Yana fitowa falo wayarta dake saman kujera ta Fara ringing,kallon wayar ya yi yaga sunan wanda ya Kira ta,Usaman shine sunar da ya bayyana akan wayar,bai kula ba ya fice abinsa.
Yana zaune cikin motarsa ya na jiranta, danne-danne ya ke a wayarsa,ta k'araso sanye take da abaya kalar lemon green ta sa hula ba'ki a ciki kafin ta yafa gyalen,ta yi simple makeup tana ri'ke da posanta da wayarta a hannunta,bak'in takalmi flat shoe ta saka,abayar na d'aya daga cikin kayan da ya siya lokacin da suka tafi Dubai da Sumayya had'o lefe inda kayan suka burgesa ya za'besu ita kuma Sumayya ta ce bata son kayan duk abunda ya burge wani baya burgeta,shi kuma sai ya kawo wa k'annensa Asiya da Mufida Mummy ta cirewa Inteesar wasu daga ciki,son shi dama kayan sun masa.
Bud'e murfin motar tayi ta shiga tare da masa sallama,a zuciyarsa ya amsa sallamar,zama tayi ba tare da tayi magana ba,shiru yayi har tsawon mintuna goma bai ja motar sun tafi ba kuma bai ce komai ba,ganin bai da niyyar tafiya ne ya sa ta ce,
"Yaya na gama."
Shiru ya d'anyi kafin ya fara magana.
"Dama kina da baki shine kika zauna mani shiru a mota kamar kurma?"
Yaui maganar ba tare da ya kalle ta ba,zuba masa idanu ta yi tana mamaki wani irin mutum ne shi wannan?sai da fa ta masa sallama Bai amsa ba amma wai ya na cewa kamar kurma,shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.
"Bari kiji na fad'a maki wani abu d'aya,idan muka je gidanku ko gidanmu aka tambaye ki yanayin zamanmu kika kuskura ki ka sanar dasu halin da muke ciki da ke wallahi sai na lahira ya fi ki jin dad'i,ki nuna masu ba komai a tsakaninmu muna zaune lafiya cikin jindad'i,kuma bari kiji wannan d'ari d'arin da kike Dani ki ajiyeshi tun yanzun kuma a nan ki saki jikinki dani sosai ki nuna masu ba wata matsala a tsakaninmu,ki nuna muna jin dad'i da k'aunar juna,bari na fad'a maki meye ma sunanki?"
Kallonsa tayi tare da cewa
" sunana Inteesar"
Jinjina Kai ya yi tare da cewa
" koma dai wace ce na fad'a maki wallahi kika kuskura suka tambayarka kika sanar dasu zaman da muke yi dake,iya ka dai sai dai suyi mani fad'a,ke kuma idan muka dawo gidan nan Ni kad'ai nasan hukuncin da zan yanke maki,idan kunne ya ji jiki ya tsira,ina fatan kin gane?"
Kai ta jinjina tare da cewa
"Eh na gane"
"Good,sannan magana ta k'arshe naji Gwaggo wai zata zo nan gidan tayi 1 month to da zaran ta maki zancen ki nuna mata cewar ba sai tazo ba tunda kinzo ta ganki."
Da sauri ta kalleshi,dan Allah ya sani ba zata iya fad'awa Gwaggo haka ba,amma sai ta amsa masa da kawai.
Kunna motar ya yi tare da yin horn inda mai gadi ya wangale masa gate ya bar gidan.
Suna tafiya a gefen ya yi kwana ya tsaya a gaban wani tafkeken super market,yana gama parking yana k'ok'arin fita daga motar yaji an k'wank'wasa gilashin motar, sauke gilashin ya yi sai yaga shila k'awar Sumayya ri'ke da waya a hannunta, murmushi ta sakar masu tare da cewa
"Barka da warhaka amarya da ango."
"Shila kece ya kike?"
Kallon Inteesar ta yi tare da watsa mata harara sannan ta ce,
"Amarya ta ango ya cin amarci?"
Inteesar ta kalleta tare gaishe ta
"Ina wuni?"
"Lafiya lau ya kike"
"Alhamdulillah"
Harara ta watsa mata a fakaice tare da cewa
"Da alama amarya tasa an mance da Sumayya ko?"
Ajiya zuciya ya sauke
"Ba haka bane shila abun ne ya fi k'arfina ba yadda na iya ne,kuma ita da iyayenta sun d'auki zafi Amma na da few days komai zai dai daita."
Jinjina kai tare da yi masu sallama ta bar wajen,shi kuma fitowa ya yi ba tare da ya kalli Inteesar ba ya fita daga motar.
Bayan wani mintuna sai sai ji tayi ana zuba kaya a but d'in motar,karin aka rufe ya zagayo ya zauna ya ja motar suka bar harabar wajen.
Bai tsaya ki ina ba sai k'ofar gidansu Inteesar,ganin ya yi parking k'ofar gidansu ya sa ta sakin murmushi mai sauti,Wanda har sai da ya kuyo ya kalleta,cikin farin ciki tayi yun'kurin bad'e motar amma sa taji ya yi lock d'In motar,juyawa ta yi da niyyar masa magana sai ta ga ya had'e fuska ba annuri a fuskarsa,hakan yasa ta turo baki ta cigaba da zama cikin motar,sai da kwashe mintuna bakwai kafin ya ce,
"Ki shiga ki sanar da su tare muke."
Bayan ya yi unlock d'in motar,fita tayi ta nufi cikin gidan,tun a zauren gidan take kwalawa Ummanta Kira.
Umma! Umma!! Umma!!!"
Da sauri ta fito daga d'aki jin muryar tilor 'yarta,A guje Inteesar ta k'arasa jikin Ummanta ta rungumeta sai hawaye kawai ke fita daga idanunta
"Ummana nayi kewarki sosai,ta kwantar da kanta a kafad'ar Ummanta hawaye kawai ke tsiyaya daga idanunta,kusan mintuna uku suna a haka kafin Umman nata ta janyeta daga jikinta tare da Jan hannunta suka shiga cikin d'akin,Kan gadonta Ummanta ta zaunar da ita,zuba mata ido tayi ganin duk ta rame da alama bata cikin kwanciyar hankali,alamu sun nuna haka amma ko mene ne zata nemi Jin ta baki 'yarta, tasan halin da take ciki,don sanin cewa ba auren aoyayya bane na had'i ne.
"Umma ina kwana?"
"Lafiya lau Inteesar ya kike?"
"Alhamdulillah Umma"
"Ya mijin mai gidan naki?"
Sai a lokacin Inteesar ta tuna cewa yana waje.
"Umma muna tare ya ce nazo na sanar dake kafin ya shigo."
"In banda abunki shine da kika shigo baki sanar dani ba?"
"Farin cikin ganinki ne yasa na mance da shi,ina Abba ya tafi kasuwa ko?"
Murmushi Umma ta yi tare da cewa
Yana kasuwa amma idan zaki dad'e ne har zai dawo ya tarar dake,ki je ki shigo da mijin naki ko?"
Mi'kewa Inteesar tayi ta fice daga d'akin duk wanda ya kalli fuskarta yasan tana cikin farin ciki.
Yana zaune a cikin motarsa ya d'an kishingid'a,idanunsa a lumshe kamar mai barci,sallama ta yi masa a zuciyarsa ya amsa har sau uku tana masa magana amma shiru bai amsa ba.
A hankali ya bud'e idanunsa a kanta
"Dan tsabar iskanci da wulak'anci kika shanyani ina jirnaki ko?"
"Kayi hak'uri"
"Bari na fad'a maki abu d'aya mintuna talatin na baki kiyi a cikin gidanku,kada ki wuce haka,kina jina ko?"
Kai ta jinjina masa
"Dan Allah ka k'ara mani lokaci kaga Abbana baya nan koda awa d'aya ne ka k'ara mani don Allah."
"Bana son Musu umarni na baki."
Daga nan ta shige gaba suka nufi cikin gidan tana gaba Yana biye da ita a baya.
*KUYI HAKURI DA WANNAN BA LALLAI BANE NA DINGA MAKU POSTING WEEKEND DAN BANA SAMUN ISASHSHEN LOKACI*
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page 4️⃣0️⃣
Daga nan ta shige gaba suka nufi cikin gidan tana gaba yana biye da ita a baya.
Tun a bakin k'ofar zauren ya yi sallama,Umma ta lek'o ta amsa masa sallamar tare da ce masa ya shigo, takalminsa ya cire a k'ofar d'akin.
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaika salam"
Shiga cikin d'aki. Ya yi ya durk'usa k'asa
"Ina wuni Umma?"
"Lafiya lau Muhammad ya aiki,ya kuma hak'uri?"
Sunkuyar da kai ya yi tare da sakin murmushi
"Alhamdulillah"
Kallon Inteesar Umma ta yi tare da cewa
"Kawo masa ruwa mana"
Mi'kewa Inteesar ta yi ta ta fita waje ta d'auko kofin silba da murfin sa tazo ta bud'e randar k'asa ta d'ebo ruwan cikinta mai sanyi kamar na fridge,ta rufe kofin ta nufi d'akin a zuciyarta tana cewa nasan ma ba Shan wannan ruwan zaiyi ba,mutumin da ya saba da shan ruwan gora ta ina ma zai iya Shan wannan ruwan namu bari dai na kai masa.
Da sallama ta shiga d'akin inda ta ajiye masa ruwan a gabansa,itama ta zauna daga gefe.
"Muhammad ga ruwa kasha"
Murmushi ya yi tare da d'aukar bud'e murfin kofin ya d'auki ruwan ya sha,kallonsa Inteesar ta yi don bata ta'ba tunanin zaisha ba kasancewar shi muyum mai k'yank'ami,bayan yasha ne ya rufe kofin,kafin ya d'ora da cewa
"Abba baya gida ne?"
"Eh ya tafi kasuwa"
Kud'i ya ciro kimanin dubu a hamsin daga aljihunsa,ya ajiye a saman tabarmar sannan ya ce,
"Umma idan ya dawo a gaishe shi to sai na sake shigowa."
Umma ta nuna cewa yabar kud'in sunyi yawa ba za'ayi haka ba,ya nuna ba wani abu bane dan ya yi masu hidima,sallama ya yi ya fita inda Inteesar ta duba agogo saura mintuna ashirin cikin mintuna talatin da ya bata, ajiyar zuciya ta sauke tana tunananin cewa wata irin rayuwa ne wannan a ce a ce mace tazo gidan iyayenta ba za'a badi ta yini ba wai mintuna talatin ya bata.
A k'ofar gida kuwa wasu matasan samari su biyu Muhdeen ya gani sunzo wacewa ya kira su,but d'in motar ya bud'e kayan da suka tsaya ya siya a hanya ne ya ce su shiga dasu cikin gidan nan,buhun shinkafa ne da carton d'in taliya da makaroni,sai na semovita da maggi da galan man gyad'a da na manja,haka suka shiga nik'i -nik'i da kayan sallama suka yi Umma ta lek'o ganinsu nik'i -nik'i da kaya da mamaki ta tambaye su.
"Samari daga ina da kaya?"
"Wani ne da ya fito daga nan gidan ya ce mu shigo da kayan nan."
Da mamaki Umma ke kallon kayan har suka gama jidesu,ta juya ta kalli Inteesar ta ce,
"Inteesar mijin naki har da d'awainiya kuam?haba ai da baki badshi ya kashe kud'i da yawa haka ba ga kud'in da ya bamu ai d'awainiya ta yi yawa."
Inteesar dai bata ce komai ba,suka dinga kama kayan suna shigar dashi cikin d'aki.
Nan dai suka zauna suna firan bayan rabuwa,kafin Inteesar ta ankare har ta kwashe awa d'aya, lokacin da ta ankare gabanta ya fad'i rasss da k'arfi.
"Na shiga uku"
Da sauri Ummanta ta kalleta
"Lafiya me ya faru?"
Shiru ta d'anyi don bata son Ummanta tasan halin da take ciki kada ta saka damuwa a ranta,hakan yasa ta ce,
"Ina sauri ne Umma zan koma"
Da mamaki Umman nata ta kalleta
"Gida tun yanzun kuma? ba Zaki bari Abban naku ya zo ku gaisa ba?"
Murmushin ya k'e Inteesar ta yi
"Abunda ya sa zan tafi dama zanyi bak'i ne,lokacin da muna hanya ne suka sanar damu shine muka ce su d'an jira mu mun fita yanzun zamu dawo."
Ido Umman nata ta zuba mata,don Inteesar bata iya k'arya ba indai ta fad'i maganar da k'arya ce tsab yanayinta ke nunawa,hakan yasa Umma dai ta yi shiru Dan ta fahimci akwai abunda take 'boyewa,bata son k'ureta ne yasa ta dai yi shiru tare da cewa
"To shi mijin naki fa?"
"Yana jira na a mota"
Kai Umma ta jinjina ta ce,
"To shikenan tunda haka kika ce,zan k'ara mai maita maki zaman aure sai hak'uri ki k'ara hak'uri akan wanda kike da shi yi nayi bari na bari dan Allah kibi mijinki sau da k'afa ki zama mai hak'uri da juriya a gidan mininki.
"To Umma insha Allah"
Hawaye ne suka cika mata ido ta mayar da su day sauri ta nufi k'ofar fita ta fice,sai da ta Kai zauren gidan ta tsaya ta saki kukan da ya taso mata,sanna ta tsagaita tare da share hawayen ta fice gabanta na dukan uku uku ta fita waje,wajen motar ta nufa bud'ewa ta yi ta shiga bayan ta shiga ne ta rufe murfin motar,yana zaune waya ya ke da alama Jabeer ne ya kirasa a waya inda yake cewa.
"Badamuwa Jabeer,Kai da wa zakuzo goben ne?"
Daga can 'bangaren Jabeer ke cewa
"Nida Salisu ne da Bilyaminu,sai kuma Bashir dan har sunyi fushi ganin ko d'aurin auren baka sanar da su ba,na dai basu hak'uri sun ce gobe zasu zo suga amarya."
Shiru ya yi na d'an lokaci kafin ya d'aura da cewa
"Allah ya kaimu gaben sai kunzo."
Daga nan ya katse kiran ba tare da ya kalli Inteesar ba ya ce,
"Minti nawa na baki?"
Shiru ta yi kafin ta ce,
"Mintuna talatiin"
Jinjina kai ya yi
"Yanzun mintuna nawa kika yi?"
"Awa d'aya nayi wallahi muna fira da Ummana ne bansan lokaci ya yi nisa ba shiyasa."
Jin muryarta alamun ta yi kuka yasa ya kalleta
"Saboda baki son komawa yasa kike kuka?to ai da kin fad'a mata baki son zaman auren Kinga shikenan kowa ya huta,ko an fad'a maki nima son zama nake dake?ala dole ala lalurati yasa nake zaune dake,dama Zaki taimaka yanzun ki koma ki fad'a Mata cewar baki so na ba Zaki iya zaman aure da ni ba sai dai na sauwak'e maki,kuma yanzu. Idan mun tafi gidanmu ki fad'awa Gwaggo cewa baki sona ba Zaki zauna dani ba wallahi da kin burgeni,ki nunawa Gwaggo cewa ita da ta had'a auren tasa na sauwak'e maki wallahi da kin burgeni ni,don sai na maki Babbar kyauta amma da ya ke mayya ce ke kika lik'e."
Shiru ta yi tana jinsa bata ce komai ba.
"Koda ya ke nan ba da dad'ewa ba zan sake ki ne, saboda Sumy na bata son zama da kishiya,buri na Komai ya dai daita ta dawo gida na a lokacin ke kuma Zaki bar gidan don wuta da auduga basa zama waje guda."
Tana jin sa irin munanan maganganun da yake fad'a mata bata ce komai ba,tada motar ya yi ya yin da yake cewa
"Isakancin banza daga mintuna talatin ta barni zaune ina jiranta sai da taga damar fitowa ta fito."
Gyad'a Kai ya yi tare da yin kwafa
"Kinci sa'a ba a gida muke ba da ace a gida muke da kika karya Mani doka wallahi sai kin gane kurenki."
Ya cigaba da driving yana ta ta fad'a ita dai uffan ba ta masa ba,har suka k'arasa k'ofar gidansu inda ya yi horn mai gadin gidan ya wangale masu gate.
Bayan ya shiga ya yi parking ne ya kalleta tare da cewa,
"Ina fatan baki mance da abunda na fad'a maki a baya ba ki? matuk'ar kika nunawa Mummy da Gwaggo wani alamu na rashin jituwa ko