Header Ads
Showing 30001 words to 33000 words out of 149432 words

Chapter 11 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1386

Ads at the middle of Article

naga shiru-shiru Bata dawo ba na tambayi Mufida cewa ga Inteesar shiru,take cewa kila ta tsaya wajen mutumiyarta Gwaggo"


Mufida ta girgiza Kai tare da cewa,


"Nidai nasan bakiyin kukan ciwo sai dai idan 'boye mana zakiyi"


Asiya dake tsaye bakin k'kofar hannunta na rik'e da handle d'in k'ofa ce tayi tsuki tare da fad'in


"Amma kuma da naci kuke,tace bakomai ta a tafi a hakan mana haba da Allah.yauwa ni ba wannan ya kawoni ba,wace ce ta d'auki chargern wayata?


Azeeza ta ce


Nice Aunty Asiya na mance da tawa ce,na shiga ban ganki ba shine na d'auko"


Ta k'arasa maganar tana nuna socket d'in da tasaka charging.


"Okay badamuwa idan kin gama ki kawo mani"


Daga nan ta juya ta fice, Inteesar kwanciya tayi akan gadon ta juya masu baya.


'Bangaren Gwaggo kuwa ganin Inteesar ta fito 'bangaren Muhdeen Tana kuka yasa ta nufi 'bangaren nasa.ko sallama batayi ba ta tura k'ofar ta shiga.


"To shugaban mugaye na Africa,uban me kayiwa 'yar mutane ta fito tana kuka?"


Shiru yayi bai kalleta ballantana ya amsa Mata,bada Kai nake magana ba ka yi mani shiru?nasan dai yarinyar nan bazata ta'ba aikata wani abu da zaisa kayi mata azaba ba,sai dai idan kuskure aka samu,haka ranar ka akan ta watsa maka yayu a rashin sani ka kamata kahau yarfa mata maruka kamar Allah ne ya aiko ka,yanzun ma ka kamata kana jibga to a kunnen ubanka d'an banza mai k'irar yahudawa."


Ba tare da ya kalleta ba ya fara magana.


"A halin yanzun Ina cikin farin ciki,saboda haka kada ki ruguza farin mani cikin da nake ciki.karki manta nifa ango ne"


Harararsa tayi ta ce,


Dalla rufe mani baki ina angon yake,sai dai muna angon don ni banga cikakken ango anan ba,wata kila idan zakayi auren da ake kira aure zan ganka cikakken ango Amma yanzun angogo na gani.Dan zaka auri wananna tambad'ad'd'yar yarinyar zaka kira kanka ango.


Take ya murtuk'e fuskar sa don ya tsani a fad'i kalma mara dad'i akan Sumayyarsa.


Zata bud'e baki da niyyar tayi magana,yayi saurin dakatar da ita da fad'in.


"Gwaggo a halin yanzun kin riga da kin 'bata mani rai saboda haka kada ki tunzurani."


Ri'ke baki tayi tana kallosa.


Muhammadu duka na za ka yi ko me?na tunzura kan d'in,ko uwarka da ubanka za su ce kada na tunzura su ballantana kai.?"


Jabeer ne ya k'arasa gaban Gwaggo cikin sigar rarrashi ya fara magana.


"Allah ya huci zuciyarki Gwaggo kiyi hak'uri ki tafi kada ki biyewa Muhdeen don Allah kinsan halinsa."


"Halinsa na banza ba,yanzun ka fad'a mani gaskiya me yayiwa yarinyar nan?"don nasan ba abunda zatayi masa bak'ar zuciyarsa ce da mugun halinsa ne kawai."


Ahljiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa,


Gwaggo idan har nace ga abunda tayi masa nayi k'arya,nadai zo na tarar ya murd'e mata hannaye ya lan'kwasa mata su baya tare da toshe Mata baki wallahi iya abunda na sani kenan."


Jinjina Kai tayi


"To Allah yayi maka Albarka ya sauke matar ka lafiya ta Haifa maka d'anka namiji, mai sanin darajar mutane da neman albarka irinka."


Murmushi yayi tare da cewa,


"Ameen Gwaggo."


"Ni banma tambayeka ya jikin matar taka ba ko?anya ma zata iya zuwa bikin nan kuwa?"


Girgiza kai Jabeer yayi yana dariya ya ce,


"Ba zata iya zuwa ba Gwaggo saboda cikin nan yana wahalar da ita."


Kai ta jinjina tare da ake tambayar sa.


"Cikin nan nata wata nawa ne?"


"Wata biyar kenan Gwaggo"


"Auren KU watanni biyar kenan ko"


Kai ta jinjina tana dariya ta ce,


"Dakyau namijin gaske,ashe dai jikan nawa ba rago bane,aure wata biyar ciki ma wata biyar lokacin da kukayi watanni tara da aure lokacin cikinta watanni tara sai haihuwa kenan. Wato baka da wasa kana jefa k'wallo kenan ta shige raga lallai yaron nan ka cika namiji ba lusari bane kai.Ai dam..."


Muhdeen ne ya katseta ta hanyar cewa.


Ba'a irin wad'annan maganganun a gaba na,don na dad'e da sanin cewa baki san alkunya ba."


Kallon shek'ek'e Gwaggo tayi masa ta ce,


"Ubanwa yace dole sai ka saurare mu ka fita mana."


"Kuzo har cikin d'aki na sannan ku ce na fita? ai ba zamanin mulkin mallaka muke ciki ba.Koda yake dama ke nasan haka kike shine ma da ya biye maki."


Juyawa yayi ya kalli Jabeer ya nuna sa da hannu ya ce,


"Kai baka san waye Gwaggo ba ko? shiyasa har take tambayarka sirrin gidanka kake fad'a mata,sai ta dinga terere da sirrin gidan ka.Idan ka biye Mata cewa zatayi ka fad'a mata me ya faru a first night d'in ku,kaga jata ku tafi can d'akinta ku karasa zancen ku ba'a nan ba."


ya k'arasa maganar yana shigewa bedroom.Ta bishi da harara tana cewa,


"Ai sai dai ka shiga ciki,kuma saura kuma naga naka k'wazon jarumi ne ko kuma lusari."


Daga Nan ta fice daga d'akin tana sababi,Kai tsaye d'akin Mufida ta nufa nufa ganin Inteesar kwance tana barci yasa ta fita ko gaisuwar da su Azeema suke mata Bata amsa ba ta fice.




Washe gari gidan ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arziki ana ta shagulan biki.inda kowa yake cin abincin da ransa yake so yasa abunda ransa ke so.


Da misalin karfe hud'u na yamma ana ta Shirin zuwa reception kowa ya saka ankon material d'in da aka fitar saboda reception d'in kowacce tana shiga mitoci ana waucewa dasu.Su Inteesar kuwa suna cikin d'akin Mufida su hud'u. Mufida, Inteesar,Azeema da Azeeza.Sunci anko inda Azeeza ta tsantsara masu kwalliya sunyi matuk'ar kyawu sosai sai shek'i da k'amshi suke inda suka inda suka dinga fama da Inteesar akan ta dage lallai dole sai ta saka hijabi ita kuma ta dage,dakyar suka shawo kanta ta har ta amince zata saka gyalen.Gashi kayan sun bayyana tsantsar kyawun surar jikinta kowacce ta d'auki wayarta da posa d'inta suka fito.


Koda suka k'araso harabar gidan duka motocin gidan ba ko d'aya duk an tafi dasu tundaga Kan motar Mummy har Motocin Muhdeen ba ko d'aya .Domin duk an tafi wajen reception motar Jabeer kawai suka gani sai motar Asiya wacce fitowarta kenan daga cikin gidan ita da k'awayenta guda biyu,tana k'arasowa ta kallesu tace,


"Au kuma baku tafi ba?"


Mufida ce ta kalleta tace,


"Wallahi bamu tafi ba tunda gaki sai mu biki"


girgiza Kai tayi tare da cewa,


"Sai dai dukkanku motar ba zata d'uke mu duka ba,don ga friends d'ina guda biyu sannan ga ku hud'u kinga sai dai mutum d'aya ta hak'ura ta hau keke napep"


Mufida ta kallesu ta ce,


"Badamuwa ni zan hau napep ku ku shiga motar."


Kai Asiya ta girgiza


"A'a sai dai Inteesar ta hau napep don bazaiyuwu ba kibar su Azeeza baku tare."


"Gaskiya Inteesar ba zata hau napep ba."


'Daga kafada Asiya tayi alamun I don't care d'innan sannan ta kalli Mufida ta ce,


"Shikenan sai ku tafi daga ke har ita kuhau napep d'in."


Dai -dai lokacin Muhdeen ya fito tare da Jabeer,Jin abunda suke fad'a yasa Jabeer tambayarsu.


"Wace ce zata shiga napep?"


Mufida ta ce


"Motar ce bazata d'auke mu duka ba saura mutum d'aya."


Idanun Jabeer ne suka akan Inteesar ya zuba Mata idanu ba ko k'yaftawa,gaba d'aya ta tafi da hankalin sa ya kasa d'auke idanunsa akan kyakkywan surar jikinta.Muhdeen ya lura da kallon da Jabeer ke mata hakan yasa ya buge masa hannu Wanda yasa shi dawowa hayyacinsa.Muhdeen ya baibi ta kansa ba ya wuce ya shige bayan motar ya zauna.


Jabeer ya kalli Inteesar ya ce,


"Inteesar kizo mu tafi a motata"


Kallon Mufida tayi,sai Mufida tayi mata alamun taje ta shiga.Hakan yasa tabi baynsa inda ya bud'e Mata marfin gabar motar ta shiga ta zauna.Mufida kuwa suka shiga na Asiya.Cikin sanyi murya ta ce,


"Nagode"


Murmushi Jabeer ya sakar mata tare da cewa


"Bakomai Inteesar."


Muhdeen ne ya had'e fusaka ya ce,


"Motar da zaka d'auki Amarya da Ango ne zaka d'auki wannan kucakar yarinyar to aiko sai dai ta fita."


Jabeer ne yayi masa irin kallon nan na kayi kad'an sannan yace,


"Wallahi bazata fita daga motar Nan ba sai dai Kai ka fita."








09065327995Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89




*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*




Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.








Page2️⃣3️⃣




"Wallahi ba zata fita daga motar nan ba sai dai Kai ka fita."


Kallon mamaki Muhdeen yayiwa Jabeer don Bai ta'ba tunananin jin wannan maganar daga bakin Jabeer ba.


"Yanzun akan wannan yarinyar kake fad'a Mani magana?don kaga friends d'ina sau d'auki motacina zasuyi amfani dashi basoda nace zanbi naka kai ka isa ka fad'a mani mota?kaima kasan motocin da nake hawa sunfi naka, ballantana ka fad'a Mani magana"


Murmushi Jabeer ya ce


"Bakomai ai zakaranka rak'uminka,kardai ka 'bata ranka a banza a wofi don yanzun zamuje mu d'auko maka amaryarka tana zaune gefenka yayin da ni kuma Inteesar tana zaune a gefe na."


Banza dashi Muhdeen yayi bai tanka masa ba, yayinda Jabeer kan d'an ja Inteesar da fira,duk da ba wani biyeshi yakeyi ba idan daga eh sai A'a, a hakan har suka k'araso k'ofar gidan su Sumayya amarya nan suka tarar da d'aya daga cikin motocin Muhdeen a k'ofar Get d'in gidan,wanda abokin ango Bilyaminu ne ya tukota don d'aukar 'kawayen amarya.Bayan ansaka amarya cikin motar da ango ke ciki ne sauran k'awayenta suka shiga motar da Bilyaminu ya tuk'o,daya nan suka d'au hanya.Amarya kuma ta shiga Motar Jabir inda ta zauna kusa da angonta.K'amshin turarenta ne ya gauraye cikin motar murmushi suka sakarwa junansu .Jabir ne ya kalleta ta cikin mirror d'in dake cikin motar ya ce,


"Amarya bakya laifi"


Murmushi tayi tana fad'in


"Koda na kashe d'an masu gida"


Amsa ya maida Mata da cewa,


" A'a sai dai idan baki kashe ba,"


Share shi tayi kamar bataji abunda yake fad'a ba,ta mayar da idanunta wajen duban angon nata cikin tsananin k'unarsa ta sakar masa murmushi cike da son sa ta ce,


"Kayi kyau my heart"


Murmushi ya mayar mata


"Ai ban kaiki kyawu ba"


Inteesar ce ta bud'e baki ta gaishe ta


"Anty sumayya ina wuni"


Dai -dai lokacin da Jabeer yaja mota suka bar wajen,sumayya cike da mamaki da takaici ta ce,


"Wannan ba yarinyar nan bace, Inteesar?"


Jabeer ne ya bata yayinda idanunsa ke kan hanya yana cigaba da tuk'i ya ce,


"Itace mana dama kinsanta ne?"


Ba tare da ta bashi amsa ba ta cigaba da magana


"To me yasa ta biyo ku batabi sauran jama'ar sun wuce ba?dole sai motar da ango da amarya zasu tafi shi zata bi a matsayinta na wa?"




"A matsayinta na mutum 'yar mutuwa,jikar rasuwa,kakar jana'iza.kamar yadda babu Wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi tsoron sa."


Shiru tayi ta cika tayi fam cike da takaici. Kalaman Jabeer d'in kamar yana jirace da ita.Dama ta dad'e da zargin cewa Jabeer baya k'aunarta a tare da Muhdeen,kuma taci alwashin sai ta raba tsakanin su,bata gama tunanin da takeyi a cikin zuciyarta ba taji maganar Muhdeen yana cewa Jabeer


"Wai kai Jabeer me yake damunka ne? so kake sai ka gusar mana da farin cikin da ke cikin zuciyarmu ne? ya kake neman ka dinga gayawa mutane magana san ranka ne?ko ko don kaga an shiga motar ka ne zaka nemi gaya mana maganar banza?dama kace da abokaina su d'auki motocina suyi zurga-zarga dasu ne dan kaci mana mutunci? To yanzun kayi parking nan mu sauka mubar maka motarka,zansa yanzun a kawo muna mota,kana ta faman gayawa mutane magana akan wannan kucakar yarinyar."


Murmushi Jabeer yayi tare da cewa,


"Idan ko zaka kira Inteesar kucaka ashe ko duka 'yan matan duniyar nan kucakai ne.don idan za'a tara mata d'ari to dakyar za'a samu biyar biyar kamarta."


Ganin ransu yayi matuk'ar 'baci ne yasashi cewa


"Kuyi hak'uri wallahi banida niyyar'bata muku rai,ku gafarceni."


Ba Wanda ya sakeyiwa kowa magana magana har suka k'arasa wajen reception d'in inda aka gudanar da komai cikin tsari,inda amarya da ango suka zauna wajen zaman su aka rera masu wak'a aka rak'ashe aka lik'a nairori.bayan antashi ne, Muhdeen ya ce,shi bazai shiga motar Jabeer ba inda Salisu ya d'auke su a d'aya daga cikin motocin Muhdeen d'in.Inteesar kuwa dole ta sake bin Jabeer Don komawa gida.


Akan hanyarsu ta komawa gida ne, Maryam matar Jabeer ta kirashi a waya Wai tana son shan agwaluma dan Allah ya siyo mata.bayan ya gama amsa wayar ya juya ya kalli Inteesar sannan ya maida dubansa ga driving d'in da yake yi ya ce,


"Don Allah kid'anyi hak'uri zamu d'an biya wani waje na siyawa mata ta agwaluma sai mu biya nakai mata."


Da sauri Inteesar ta kalle shi tare da cewa,


"To amma da ka ajiyeni anan sai na samu napep na k'arasa gida don bazan iya binka gidanka ba."


"Saboda me kina tsoron kada na cutar dake ko?"


Shiru tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta da suka sha jan lalle.Batare da ya kalleta ba ya sake jefa mata wata tambayar.


"Zaki yarda ki rakani ko?"


Nanma shiru tayi tana tunani, ita dai yau ta fara ganinsa lokacin da ya k'wace ta a hannun Muhdeen.Sai dai taji Mufida ta kira shi da Yaya Jabeer,kuma tana yawan jin sunan sa a bakin Mufida ko ranar da tayi rashin lafiya da su Mummy suka zo gaisheta taji Mufida na cewa daga gidan Yaya Jabeer suke wai d'an wan Mahaifinsu ne.sai dai duk da haka baikamta tabishi gidansa ba to amma kuma yana da mata kuma taji sanda matar take fad'a masa ya siyo Mata agwaluma Amma ya dace ta bishi kuwa?dama tare da Mufida suke ba zata damu ba.


Tana cikin tunani taga ya d'auki wata hanya daban ,gani yayi yanayinta ya canza alamar Bata yarda dashi ba.Hakan yasa ya Ciro wayarsa bayan yayi parking a gefen titi.Lambar wayar Mummy ya lalubo ya danna mata kira, lolacin Mummy na zaune a d'akinta ita Mahifiyar Jabeer,kiran Jabeer ne ya shigo wayarta kallon Mahifiyar Jabeer d'in tayi ta ce,


"Kinga Jabeer ne ke kira na kodai ya kira lambarki ne bai shiga ba?"


'Daga wayar tayi tare da cewa,


"Hello Jabeer kun iso gida ne?"


Jabir ya Bata amsa da cewa


"A'a Mummy dama lokacin da zamu tafi reception ne naga su Mufida da tagwayen Aunty Maryam, so motar da zasu shiga bai d'aukesu ba hakan yasa nacewa Inteesar da bata samu wuri a motar ba ta shigo motata.Tunda ango da Amarya zan d'auka kad'a,to yanzun Angon ma a motarsa ya koma sai ni da Inteesar d'in mun kama hanyar dawowa Maryam ta kirani Wai tana son agwaluma,nacewa Inteesar bari na siye na Kai mata tunda munfi kusa da gidana,naga hankalinta bai kwanta ba tana tsoron na cutar da ita ne gashi yanzun magariba tayi ko zakiyi mata magana ko hankainta zai kwanta."


Murmushi Mummy tayi tare da cewa,


"Bata wayar"


Mi'kewa Inteesar wayar yayi tare da sakar Mata Murmushi,amsar wayar tayi ta Kara a kunnenta ta ce,


"Assalamu Alaikum."


Jin muryar Mummy yasa ta sakin murmushi tana cewa


"Ina wuni Mummy?"


"Lafiya lau Inteesar ki kwantar da hankainki Jabeer kamar yaya ne a wajenki,bari ya siye abunda zai siya idan yakai mata sai ku dawo gida kinji?.Abunda yasa baki sanshi ba lokacin da yake zuwa lokacin ki tafi gida shiyasa baki sanshi ba,ki kwantar da hankalinki Jabeer ba mutumin kirki ne.Allahnya kawoku lafiya."


"Ameen"


Inteesar ta amsa tare da kashe Kiran,Mik'awa Jabeer wayar tayi taga ya shagala da kallonta saurin kanye idanunta tayi ta sunkuyar da kanta k'asa.Ajiyar zuciya ya sauke tare da amsar wayar,key yayiwa motar suka d'auki hanya.Bayan yayi parking wajen me agwalumar ya juya ya kalli Inteesar ya ce,


"Kema zakisha agwalumar ne na siye maki."


Cikin sanyin Murya tayi magana


"A'a bana Sha."


Fita yayi yaje ya siyo ya dawo rik'e da leda cike da agwaluma,dan. Inteesar tayi mamakin yawan agwalumar a zuciyarta tana mamakin yawan agwalumar da mutum d'aya zata sha.Bayan ya tada motar ne sun d'anyi tafiya kad'an sai yayi parking a wani k'ayataccen wajen siyar da abinci.ya kalleta ya ce,


"Bari na d'anyo mana takeaway sai mu k'arasa gida."Ba ta ce komaiba ya fita yaje ya dawo da ledoji biyu a hannunsa,d'aya takeaway ne guda uku d'aya ledar kuma kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe danginsu chocolate da snacks da ice cream da Biscuits ne a cikin.Yana shiga ya tada motar sai gidansa ya nufa,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga da motar,bayan yayi parking ne ya fito ya bud'e mata yayi don ta fito sai ta mak'e kafad'arta alamar bazata fito ba ya k'ura Mata yadda take tura d'an k'aramin bakinta ne ya bashi dariya ce mata yayi


"To shikenan tunda ba zaki fito ba Ni zan shiga ciki kinji ana Kiran sallar magariba ni zan shiga nayi alwala sai naje masallaci na dawo sannan zamu tafi gida.kinsan lokacin sallar magariba gajeren lokaci ne dashi gara ma ki fito.Jin hakan yasa ta fito ,bayan motar ya bud'e ya d'auko ledojin yayi gaba tabi bayansa.


A falo sula tarar da Maryam kwance kan doguwar, kujera tayi rigingine ta d'aura hannunta akan cikinta.Jin muryarsa yasa ta mi'kewa zaune don dama agwalumar take jira tasha. Jin sallamar muryar mace yasa ta d'aga kai ta kalli Inteesar,gabanta ne ya fad'i saboda yanzun ta sauka a online kuma tagani a status Mufida ta d'ora videon reception d'in da sukayi taga inda Jabeer ya fito daga gaban motarsa ya zagayo ya bud'ewa Inteesar ta fito daga gaban motar sa yana kallonta yana murmushi.Tare suka shiga wurin tana gaba yana binta a baya.Har tayiwa Mufida reply da cewa wace ce nan tare da miji na?Mufida bata amsa Mata ba don ta sauka online.Zaubawa Inteesar ido tayi tana tunanin meye tsakaninta da mijinta da tun d'azu suke tare har yanzun ya kawo Mata ita cikin gida.


Murmushin yak'e tayi tare da cewa,


" sannun ku da zuwa"


Inteesar ce ta gaishe ta,ta amsa mata fusaka a sake ba yabo ba fallasa.Jabeer ya ajiye lesojin ka center carpet dake tsakiyar falon,ya kalli Maryam ya ce,


"Madam ya jikinki?"


Murmushi tayi tare da cewa


"Da sau'ki."


Ledar agwalumar ya d'auka ya ce,


"Bari naje na wanko maki su kafin ki Fara shansu hakanan."


Kichen ya nufa da agwalumar don wankewa, Maryam ta kalli Inteesar ta ce,


"Zauna mana baiwar Allah kinyi tsaye."


Inteesar tayi murmushi ta zauna Kan kujerar dake kallon Maryam,zauba Mata ido Maryam tayi tana kallon tsantsar kyawu irin na Inteesar kamar wata balarabiya,sai taji wani abu ya d'arsu a zuciyarta ta kasa gane kishi take da Inteesar ko meye?gashi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads