Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 149432 words

Chapter 12 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1401

Ads at the middle of Article

dai yarinyar ta burgeta amma meye had'inta da mijinta?ta sake duba wayarta taga yanda Jabeer ya fito motarsa ya zagayo ya bud'ewa Inteesar sai kallonta yake Yana sakin murmushi.Jin ya dawo ne yasa ta ajiye wayar ta fara shan agwalumar.kallon Inteesar yayi yace bari nayi sallah sai na maidake gida ko?"


Ya maida dubansa ga Maryam ya ce


" ta shiga ciki tayi sallah ga takeaway nan idan ta idar da sallah taci abinci zan maidata gida."


Daga Nan ya fice Maryam ta zubawa Inteesar ido kafin ta mi'ke dakyar tana yamutse fuska ta ce,


"Zo mu shiga ciki."


Ba musu Inteesar tabi bayanta har bedroom d'inta ta nuna Mata k'ofar toilet ta shiga ta d'auro alwala,Koda ta fito Maryam ta shimfid'a Mata sallaya ta aje mata hijab.Bayan ta Fara sallah sannan Maryam ta shiga ta d'auro alwala tana tafiya tana d'an dafa bango don jiri takeji.


Bayan sun idar da sallah,Maryam tace da Inteesar taje taci abinci kafin ya dawo,tace ita ba zataci abinci ba ta k'oshi.Shiru-shiru Jabeer bai dawo ba Inteesar ta kagara sai da har aka Kira sallar isha'i suka idar sannan ya dawo.A falo ya tarar dasu ganin yadda yadda ajiye ledar takeaway haka ya same shi ya ce,


"Me yasa bakici komai ba?"


Mik'ewa tayi tare da d'aukar posan ta ta ce,


"Na k'oshi,ka kaini gida kawai."


Yadda tayi maganar ne ya burgeshi ya zuba Mata ido yana murmushi,Maryam ta lura da hakan sai tayi gyaran muryar da yasa ya kauda idonsa akan Inteesar ya maida kan Maryam.alama ya mata Wai meye?Kai ta girgiza ta kauda kanta gefe,hakan yasa yacewa Inteesar ta zo su tafi.Sallama tayiwa Maryam suka fice.


Akan hanyarsu yayi parking dai-dai wani super market.kallonsa tayi ya kauda Kai tare da fita don kar ma ta tambaye shi,bud'e mata yayi tare da cewa


"Fito"


Kallon mamaki tayi masa tare da cewa


" me zamuyi anan kuma?"


"Turare zan siya"


Ya Bata amsa a ta'kaice,ta koma jefa masa wata tambayar ta ce,


"To ka maidani gida idan ka dawo ka siya,ko kuma kaje ka siya Ina jiranka a mota."


Kallonta yayi yana cewa


"Idan baki fito kin rakani ba bazamu bar nan wajen ba ko zamu kwana ne kuwa."


Jin hakan yasa ta fito suka jera dab da zasu shiga taji an Kira sunanta,gabanta ne ya fad'i jin muryar Wanda ya kirata.Juyawa tayi da sauri ganinsa tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu ya zuba Mata ido.








*DON K'ARIN BAYANI*


09065327995Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*






Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)








*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*






Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba.Idan suna ko hali yazo d'aya,to you gafarceni bada niyyar yin gakan nayi ba arashi mai kashe auran Wawa.






*GARGA'DI*




Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guii sarrafa mani shi ta kowace siga.








Page 2️⃣4️⃣


Juyawa tayi da sauri ganinsa tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu ya zuba mata ido.


A hankali ta furta sunansa


"Usman"


Murmushi ya sakar mata tare da yi Mata alama da tazo,kallon Jabeer tayi taga ita yake kallo ita da Usman.Cikin sanyin Murya ta ce,


"Yaya Jabeer don Allah ina d'an zuwa 2 minutes."


Kai kawai ya d'aga ba tare da yace Mata komai ba,take kuma fara'ar dake d'auke a fuskarsa suka gushe.Dai-dai lokacin ne wayar Jabeer ya soma ruri,ganin sunan Mummy ce ya saka shi sakin murmushi ya d'aga kiran.Jin muryar Mummy na cewa Ina suk tsaya da basu dawo ba haryanzun?


Inteesar kuwa har ta kusan k'arasawa kusa da Usman Jabeer ya kira Sunanta,juyowa tayi ta kalleshi.Cikin bada Umarni yace ta dawo,ganin fuskasa ba wasa yasa ta juya ta koma wajensa,tana k'arasawa ya ce,


"Mummy ta kira waya, ki wuce mu tafi."


Kai tsaye inda yayi parking ya nufa tana biye dashi, bud'e mata yayi ta shiga sannan Shima ya zagaya ya shige.Sauke glass d'in motar yayi tare da kallon Usman yaga idanunsa nakan su,jan motar yayi suka bar wajen super market d'inda basu shiga ba kenan.Usman bin motar yayi da kallo har ta 'bacewa ganinsa,a ransa yana jin babu dad'i, zuciyarsa cike da tarin tambayoyi,shin waye wannan dake tare da Inteesar? Ita da lokacin da ya ce zaizo gidansu ta hanashi ta ce wai ba'a barinta ta tsaya da saurayi,sai da yayi Mata dabarar cewa maganinta ne doctor ya ce a bata sannan ta yarda ta bari yazo gidansu. Kuma iya saninsa bata da wani yaya ita kad'aice a wajen iyayenta ballantana ace shi yayanta ne, yarinyar da Bata tsayawa da saurayi me zaisa a irin wannan lokacin wani saurayi ya kawota shopping?.Haka ya dinga yiwa kansa tarin tambayoyi sanin bashida mai bashi amsane yasa jin zuciyarsa jin ba dad'i musamman idan ya tuna cewa Inteesar zata k'araso wajensa kenan wannan saurayin ya kirata dan kada tayi magana da shi.Ita kuma sai ta biye masa ta tafi ta barshi,Take ransa ya kuma 'baci haka yaja motarsa ya bar wajen,dama ya gama abunda zaiyi yana shirin tafiya ne yaga Inteesar ta fito daga Motar Jabeer.


Jabeer kuwa akan hanyarsu ta komawa gida ne yake tuna irin kallon da Usman yakeyiwa Inteesar,da yadda yadda dinga sakar Mata murmushi babu abunda ya ke hangowa a cikin idon Usaman kamar tsantsar so da yake Mata.Take sai yaji kishi a cikin zuciyarsa.Kallon Inteesar yayi sannan ya maida hankain sa kan driving d'in da yake yi sannan ya jefa mata tambaya.


"Waye shi?"


Kallonsa tayi cikin rashin gane me yake nufi sanan ta ce,


"Yaya Jabeer me kake magana akai?"


"Raina mani hankali zakiyi?waye kika rabu dashi yanzun zakije gurinsa?"


Ya fad'i maganar cikin d'aga murya kamar Yana fad'a.kallon mamaki take binsa dashi yadda lokaci d'aya yanayinsa ya sauya kamar ba Jabeer d'in da sani d'azun ba.


Cikin sanyin Muryarta ta fara magana


"Shine wanda ya kad'eni da mota."


"Yaushe ya kad'e ki da motar?"


"Sati biyu da suka wuce,lokacin da zamu kai d'inkin bikin nan nida Mufida,naga wani makaho yazo kan titi sai na k'arasa don na taimaka masa ya tsallaka Dai-dai lokacin da motarsa ta kawo kai, shine tsautsayi ya gifta ya kad'eni."


Sake jefa Mata wata tambayar yayi da cewa


"Daga Nan kuma sai akayi Yaya?"


"Shine ya kaini asibiti ya biya kud'in komai sannan ya tafi."


Wani tambayar ya sake yi mata inda ya ce,


"Daga nan baku sake had'uwa ba kenan?"


"Mun sake had'uwa saboda yazo gidanmu bayan ya dawo daga tafiyar da yayi."


"Ya akayi yasan gidan ku?kuma meye dalilin zuwansa."


Tura baku tayi,don zuwa yanzun ta fara gajiya da yawan tambayoyin da ya ke mata ba.cikin k'osawa da tambayoyin sa ta ce,


"Lokacin da yaje asibiti ne ya d'auki wayata ya saka number sa ya kira,to anan ya samu number na shine yake kira na a waya,sau d'aya yazo gidanmu gaishe ni."


Bai sake cewa komai ba ya maida hankain sa kan driving d'in da yakeyi har suka k'araso. K'ofar gidan a waje yayi parking,da sauri ta riga shi fitowa Shima ya fito,tare suka jera zuwa cikin gidan.


A harabar gidan ya tararda Muhdeen da wasu abokan su zaune kan wasu kujeru suna tattaunawa.Ido suka zubawa Inteesar da Jabeer,wani daga cikinsu mai suna Bashir ne yayi magana ya ce,


"Tsarki ta tabbata ga ubangijin halittu,gaskiya Jabeer ya iya za'ben kyakkyawar mace mai kyawun sura da diri."


Salisu ne yayi dariya tare da cewa


"Ai wannan ba matarsa bace."


Bashir ya sake cewa


"To wace ce ita a wurinsa?kodai budurwarsa ce?"


"Bari ya k'araso ka tambaye shi don banida amsar wannan tambayar taka."


Kai tsaye Inteesar ta nufi cikin gidan, Jabeer kuma ya k'araso wajen su sallama yayi masu tare da mik'awa kowannensu hannu suka gaisa.Muhdeen ne ya kalle shi ya ce,


"Daga ina haka?tun d'azun nake jiran k'arasowarka sai yanzun?"


Murmushi Jabeer yayi ya shafi sumar kansa ya ce,


"Eh daga wajen reception na biya wani waje ne sannan na tafi gidana dawowarmu kenan."


"Kenan tun lokacin kana tare da wannan yarinyar?"


"Eh kana da matsala da hakan ne?"


Ta'be baki Muhdeen yayi tare da kauda kansa gefe.Bashir ne ya washe baki yana cewa,


"Ina ka samo wannan zazzafar yarinyar gaskiya ta had'u ta ko ina,tayi mun."


Jabeer ne ya had'e fusaka domin yasan halin Bashir da neman mata kamar bunsuru.watsawa Bashir mugun kallo yayi tare cewa


"Bari kaji Bashir wannan ba irin matar banzan da ka saba mu'amala dasu bane gara ma ka kama kanka."


Gyara zama Bahir yayi cikin d'aukar maganar da mahimmanci ya ce,


Ai wannan ba irin wad'annan can sauran 'yan matan bane,wannan idan na sameta sunnah zan raya don mace ce ta nunawa sa'a."


Gaba d'ayansu suka saka dariya banda Muhdeen da ko kallonsu bayayi.salisu kuwa harda tafi yayi don bai ta'ba Jin Bashir yayi maganar aure ba,sai dai ya dinga kawo matan banza a guest House d'insa.Sharholiyarsa kawai yake Bai ta'ba maganar aure ba sai da yaga Inteesar yau.


Jabeer ya kalle shi yana cewa


"Baka dace da Inteesar ba kwata-kwata,ai ko da girgiza kurna tafi magarya."


Daga Nan ya tafi ya barsu wajen.


Inteesar kuwa tana shiga falon ta tarar da Bak'i mata 'yan biki sallama tayi ta gaishe su,sannan ta nufi d'akin Mummy nan ta tarar da Mummy da mahaifiyar Jabeer sai k'awayen Mummy guda uku.Gaishe su tayi sannan ta nufi d'akin Mufida.


Da sallama ta shiga,suka amsa Mata suna tambayarta Ina suka tsaya ne haka?


"Lapiya kika k'i d'aukar Kiran wayar da nake maki?"


Cewar Mufida da ta zubawa Inteesar ido,Sai a lokacin Inteesar ta tuna cewa wayar na a silent take,ciro wayar tayi taga Miss call d'in Mufida har guda 5.


'Bangaren Usman kuwa Koda ya koma gida ransa a jagule yake,


A falo ya tarar da Ammynsa da Khadija suna kallon news,kallo d'aya Ammy tayi masa ta gane akwai abunda ya faru a can.Don ba yadda yadda yadda fita ba kenan,yanayinsa ya sauya,Khadija ce ta kar'bi ledar hannunsa ta ajiye agaban Ammy.don dama ita ce ta kirashi a waya ta ce idan zai dawo ya biya super market yayo mata siyayya kamar yadda yadda saba duk bayan kwna biyu.


"Lapiya kuwa naga yanayinka ya canza?ko akwai abunda ya faru ne?"


Murmushi ya k'ak'alo ya ce,


"Babu komai Ammyna bari na d'an shiga ciki na huta."


Bai jira cewarta ba ya shige ciki tabishi da kallo.




Washe gari ranar juma'a Gidan Alhaji sani ya cika mak'il da jama'a.'Yan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa,aga abinci nan kala-kala sai Wanda mutum yake so zaici ko yasha,komai sunyishi a wadace.


Da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren Muhdeen da Sumayya akan sadaki naira dubu d'ari biyar murna a wajen Muhdeen Ba'a magana.Haka 'bangaren amarya ma hakan take Dan tafi kowa murna.




Da misalin'karfe biyar na yamma aka tafi d'aukar amaeya don kaita d'akin mijinta Dank'arararren gida ne Wanda akashe naira wajen yinsa.Amarya ma iyayenta sunyi bajinta wajen yo mata order lafiyayyun furnitures.Tunda ga Kan kayan d'aki har zuwa kayan kitchen komai masu tsada ne na kece raini, d'akuna guda biyu aka zuba Mata kaya.




Da misalin k'arfe takwas na dare ana ta shirin zuwa dinner wanda za'ayi a JUSTICE IDRIS LEGBO KUTIGI dake daura da Government house a cikin garin Minna.


Mai makeup aka d'auko inda tazo ta tsantsara wa amarya lafiyyen kwalliya.Tayi kyau kam sai baza k'amshi takeyi tana kyalli,k'awayenta su Jummy sai kod'ata suke suna k'ara fasa mata kai.


A can gidansu Mummy kuwa anata shirin zuwa dinner inda nan ma Azeeza ta sake tsantsarawa Inteesar da Mufida kwalliya,sai faman kod'a kyawun da Inteesar tayi sukeyi,har suna cewa ma ai kila tafi amaryar kyawu.Nan ma sai da suka sha fama da ita akan sanya gyale ba yadda ta iya haka ta biye masu ta fasa saka hijabin da ta saba sakawa.Inda kyawunta da kwarjininta suka sake bayyana don ko mace ce ta kalleta sau d'aya sai ta sake kallonta ballantana namiji.












Maman Ihsan ce✍️


09065327995




Comment and share




Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*


Story & writing✍️


Zainab Abdullahi
(maman Ihsan)






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.








Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.








*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*








Page 2️⃣5️⃣


Kyawunta da kwarjininta suka sake bayyana,don ko mace ce ta kalleta sau d'aya sai ta sake kallonta ballantana namiji.




Ajere suka fito daga d'akin inda suka nufi d'akin Mummy.


Da sallama suka shiga d'akin, Mummy ce da Aunty Maryam sai Mummyn Jabeer,amsa musu sallamar sukayi Mummyn Jabeer ce tayi murmushi tare da cewa


"Masha Allahu'yan matana kunyi kyau sosai kamar kune amaren,Allah ya nuna mani ranar aurenku musha biki.Kai kyawawan 'ya'yana kuzo na rungume ku mana."


Ta k'arasa maganar tana bud'e hannayenta alamar suzo ta rungume su.Mufida da Azeema da Azeeza suka k'arasa suka shige jikinta,yayin da Inteesar ta tsaya tsaye inda take Don Bata san Mahaifiyar Jabeer ba sai sai shekaran jiya ta fara ganinta kuma gaisuwa ce kawai ke had'asu.Hakan yasa ita Bata k'arasa ta rungumeta ba,Murmushi ta sakarwa Inteesar ta ce,


"Zo mana 'yata ya kika tsaya can?"


Hakan yasa ta tako cikin sanyin jikinta ta rungumeta hakan yasa Mufida ta ciro wayarta tayi masu selfie su duka kowacce tana dariya.daga nan sukayi masu sallama suka ce zasu tafi dinner,nan Mummy ta ce da su Anty maryam su shirya lokacin fara dinner yayi.


Dama Direban Mummy ne zai kaisu Mufida idan ya dawozai Kai su Mummy.suna Isa harabar gidan wayar Mufida ya fara ruri dubawa tayi taga yaya jabeer ne,d'agawa tayi taji muryarsa yana cewa sun tafi dinner ne? tace suna gida yanzun zasu tafi,ya tamabayeta Inteesar, ta sanar dashi cewa tare zasu tafi ya ce wai Inteesar ta sameshi waje yana cikin motarsa zai wuce da ita dinner d'in.Daga nan ya kashe Mufida ta zubawa wayar idanu Tana mamakin me ya Jabeer yake nufi?baice suzo ya kaisu ba Wai Inteesar tazo wato daga shi sai ita kenan.Kallon Inteesar tayi ta ce,


"Tafiyarmu da ke ba d'aya bane,ya Jabeer Wai kije ya kaiki."


"Babu inda zanje ya kaini sai dai idan tare zai kaimu da ku."


Dariya Mufida tayi tana fad'in


"Ai bada mu ya ce ba ke kad'ai ya ce."


Kauda Kai Inteesar tayi ta dage bazata je ba.Jin shiru yasa ya sake kiran wayar Mufida ta shaida masa yadda sukayi.Sai gashi ya zo da kansa yace da Azeeza da Azeema su shiga motar haka ma Mufida yasa ta shiga daga nan ya ce da Ishaq yaja motar su tafi.Inteesar na gani motar ta fice tsabar takaici kamar tayi kuka.kallonta yayi yana cewa


"Kizo mu tafi lokaci na tafiya fa."


'Dago ido tayi da niyyar ce masa ta fasa zuwa,amma da ta kalli cikin idanunsa sai taji ta kasa masa gardama,haka nan ta bishi har suka fita Murfin motar ya bud'e mata ta shiga,ya rufe sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa.kasancewar haske ne gab d'aya kofar gidan yasa ya zuba Mata ido,domin tasaha kyau har ta gaji.tsawon mintuna biyu taji shiru yasa ta d'ago ta kalleshi,ganin yadda yadda ya zuba Mata ido ne yasa ta d'aga kai ta kalleshi,idanunsa ne suka sark'e cikin na juna da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa murmushi yayi tare da Jan motar yabar wajen.


Akan hanyarsu ta zuwa kuwa du yadda Inteesar taso share Jabeer hakan baiyuwu ba.Domim da ya dinga janta da hira yaga bata tanka masa ba sai ya dinga yi mata tambayoyi yadda dole sai ta dinga amsa masa.shima dama burinsa kawai yayi ta Jin muryarta.A haka suka k'arasa JUSTICE IDRIS LEGBO KUTIGI inda nan ne za'a gabatar da dinner party d'in, a harabar wajen wajen suka tarar da su Mufida suna jiran K'arasowar su Inteesar d'in yayinda Mufida sai d'aukar photo da video take kasancewar gurin haske ne ya gauraye shi tamkar da rana ne.Tana ganin K'arasowar su Inteesar ta maida d'aukar zuwa ga gurin motar yayinda Jabeer ne ya Fara fitowa yayi saurin zagayowa da nufin bud'ewa Inteesar ta fito sai dai kafin ya bud'e Mata tayi saurin bud'ewa ta fito tare suka k'araso wajen ta kalli Mufida tana murmushi ta ce,


"To sarkin d'aukar photo ko dare ma ba zaki bari camera ta huta ba?"


Jabeer dai ya nufi cikin hall d'in inda za'a gudanar da shagalin.


Hall d'in ya cika mak'il da jama'a 'yan uwa da abokan arziki wasu ta hanyar amarya wasu ta hanyar ango.Nan dai amarya da ango suka k'araso cikin shiga ta alfarma sunyi kyau sosai.Wedding goun d'in amaryar irin Mai sirrin hannun nan ne kamar singileti sai jan k'asa rigar take ta bayanta ya sauka yayinda fuskarta ke lullu'be da farin net gaban rigar anyita kamar breezier.Yayinda shi kuma ya saka fararen suit.


Su Hajiya Gwaggo kuwa tana ganin shigar ta Fara salati tana tafa hannu,Aunty Maryam dake zaune gefenta ne ta kalleta tare da tambayarta


"Gwaggo lafiya me ya faru?"


Rik'e ha'barta tayi tana jujjuya Kai tana cewa


"Oh ni,yau naga abunda ya isheni."


Anty Maryam ne ta same tambayar Gwaggo ta ce,


"Wai Gwaggo ne kike ma sallallami haka?"


"Wai ke mairo ke makauniyar ina ce?ki duba wasu 'yan isakan tsinannun rgar da wannan amaryar tasa,duk surar jikinta a bayyane,ki duba gaban rigar harda gidan da mamanta zasu zauna akyi su,gashi sun zauna ciki kowa na ganin shaidar su ga rigar ko hannu Bata dashi.Wani abun takaicin Wai matar aure kenan,tunda d'azu jama'a da yawa sun shida d'aurin auren su.Gab d'aya rayuwar yahdawa suka d'auko.shi kuma da yake mijin hotiho ne da baya kishin matarsa shine ya barta ta fito a haka,ace mutum sam baida kishi kamar Wanda yaci naman alade."


Aunty. Maryam ce da wasu k'awayen Mummy suka saka dariya.Nan dai aka Fara gudanar da komai cikin tsari inda aka wak'e ango da amarya,aka kira dangin amarya inda suka fito suka cashe sukayiwa ango da amarya lik'i.
Bayan dangin amarya sun koma ne aka kira dangin ango nan suka fito harda Mummy da su Anty Maryam da k'anwar Dady da Mummyn Jabeer da su Gwaggo da Asiyya da Mufida, Azeema, Azeeza hatta Inteesar sai da Mufida ta janyota Jabeer ma ya fito Nan aka shiga lik'e-lik'en nairori da raye- raye anci ansha sannan aka tashi kowa ya watse.


Da misain karfe goma da rabi na dare ne amarya tana zaune a Kan gado,sanye take da wani less golden yellow Mai ratsin fari a jikinsa doguwar riga ce dakyar k'awayen Mum d'inta suka lalla'bata ta yadda take saka,don ita ba ma'abociya Sanya suturar kirki bane.yayinda k'awayenta su Jumy da shila je zaune a gefenta suna ta mata tsiya suna tsokanarta.


Ango da abokansa ne suka shigo cikin d'akin.Muhdeen Ango Yana sanye da farar shadda da Babbar riga sai k'amshi ke tashi a jikinsa.Salisu na rik'e da ledar kaji da fresh milk a hannunsa,da sallama suka shiga d'akin Su shila ce

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads