Showing 117001 words to 120000 words out of 149432 words
Chapter 40 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
a kumbure, ga goshinta ya ffashe ya kumbura, ga jini da ya bushe a goshin nata,a hankali Jabeer ya furta sunanta.
"Sumayya?"
Maryam kam da ba don da Jabeer ya ambaci sunanta ba ba zata gane ta ba, domin Muhdeen gaba d'aya ya sauya mata kamanni, kamar ba Sumayya 'yar k'walisa ba, hawaye ne kawai ke tsiyaya daga idanunta k'arasowa tayi ta zauna kan kujera ta fashe da kuka.
Jabeer ne ya bud'e baki yayi magana ya ce,
"Sumayya ya naganki haka me ya same ki? gashi ma ko treatment ba'a maki ba, Muhdeen baya nan ne da ya barki haka ba tare da ya maki treatment ba?"
Sautin kukanta ta k'ara tana cewa
"Shine da kansa yayi mani haka."
Kallon Juna suka yi Jabeer da matarsa ya ce
"Ban gane shi yayi maki haka ba ta yaya hakan ta faru?"
Sunkuyar da kanta k'asa tayi, ta kasa magana, hakan yasa Jabeer ya gane cewa lallai Muhdeen ya gano abunda Sumayya ta aikata, dan haka ya ce,
"Kan abunda kika aikatawa Inteesar ne yayi maki haka?"
A hankali ta gyad'a kai almar eh
Tambayar kansa yayi idan har Muhdeen ya iya aikatawa Sumayya haka akan Inteesar, to tabbas yana son Inteesar, duba da yadda ya sauyawa Sumayya kamanni dan tayi yunk'urin kashe Inteesar, Sumayya da yake masifar sonta zai iya 'batawa da kowa kanta amma yau shine yayi mata mugun duka haka? kuma akan yarinyar da ya tsana a rayuwarsa yau ya illata masoyiyarsa akanta? me hakan ke nufi? Shin yanzun ya koma yana son Inteesar ne ko meye?.
Haka ya dinga sak'e-sak'e a zuciyarsa sanin ba mai amsa ne yasa ya kalli Sumayya tare da cewa
"Ina zuwa"
Tashi yayi ya nufi d'akinsa, ba jimawa ya fito da aid box yazo ya fara treatment nata, sai kuka take tana jin zafin goshinta, sai sannu suke jera mata gaskiya sun tausaya mata, Jabeer yayi mamaki dan bai ta'ba tunanin Muhdeen zaiyiwa Sumayya makamancin abunda yayi mata ba, bayan ya gama mata ne yayi mata allura, sannan ya kalle ta ya ce,
"Me ke tafe da ke"
"Ya kore ni ne ya ce nabar masa gidansa"
Jinjina kai Jabeer yayi tare da cewa
"Yayi dai-dai ko nine a matsayin da yake abunda zanyi kenan, na ga ma k'ok'ari da bai had'a maki da saki."
Da sauri ta d'aga idanunta ta kalli Jabeer jin abunda yake fad'a, ranta ya 'baci sosai da hakan, kamar ta maida masa martanin maganarsa amma sai ta gagara, don nema tazo yi kuma mai nema baya fushi, dan haka ta kwantar da murya tare da marairaice fuska ta ce,
"Dan Allah kada ka fad'i haka, wallahi nayi nadama Kan abuda na aikata, hakan ba zata sake faruwa ba, ina son ka taya ni rok'onsa da ya yafe mani ya barni mu cigaba da zamanmu, hakan ba zata sake faruwa ba."
Girgiza kai Jabeer yayi tare da cewa
"Sumayya wannan tuba da kika yi tuban muzuru ne, na tabbata sai kin sake aikatawa, sai dai idan ba'a 'bata maki rai ba, amma matuk'ar ranki ya 'baci to ba abunda ba zaki iya aikatawa ba, domin kuwa wannan d'abi'arki ce, shiyasa tun farkon auren Inteesar ba yadda banyi ba ya raba maku gida bai saurare ni ba."
Zamowa tayi daga Kan kujera ta durk'usa akan akan k'afarta ta fashe da kuka ta fara magana.
"Jabeer ka ji tausayi na mana wallahi idan Muhdeen bai yarda ya cigaba da zama da ni ba wallahi zan iya rasa rayuwa ta, shine farin ciki na walalhi zan kiyaye duk abunda zai kawo mana sa'bani, haka ta dinga kuka tana rok'onsa da kuka tare da alk'awari daban-daban har Jabeer ya amince zai saka baki akan maganar tunda tayi nadama, har ya amince zai kaita sukayi sallama da Maryam sannan suka fito suka nufi gidan Muhdeen.
Koda suka k'arasa mai gadin ya sanar da su baya ciki, wayarsa ya ciro ya lalubo number Muhdeen ya danna masa kira, jin ya d'aga ne yasa ya ce,
"Kana ina ne?"
Muhdeen dake driving ya ce,
"Sai yau ka tuna da ni?"
"Dama mancewa da kai aka ce nayi?"
"To yanzun dai mene ne?"
"Ina gidanka ne yanzun"
"Ni kuma ina hanya zanje gidan Dady ne, kazo gidan sai mu had'u ko?"
"A'a kadai zo nan dan maganar ba ta can bane."
"Me ke faruwa."
"Idan kazo zaka ji koma mene ne"
"Daga nan ya katse kiran ya maida wayarsa cikin aljihu, ya kalli Sumayya ya ce,
"Yana zuwa mu k'arasa ciki kafin ya zo."
Tana gaba yana binta baya suka wace zuwa falo.
*KUYI HAK'URI DA WANNAN*
*DAGA ALK'ALAMIN*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DON K'ARIN BAYANI*
09965327995
Love you oll😍😘
Comments & share
Comments & shareCanFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne.
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Pa6️⃣6️⃣
Tana gaba yana binta a baya suka wuce zuwa falo.
Zama suka yi suna jiransa ba jimawa ya k'araso tara da sallama d'auke a bakinsa, yana ganin Sumayya ya tamke fusaka tare da cewa
"Ke me na fad'a maki?"
Jabeer ne yayi magana ya ce,
"Dan Allah ka saura..."
D'aga masa hannu yayi alamar dakatarwa ya ce,
"Please Jabeer kada ka shiga wannan maganar, ka barta kawai halinta sai ita."
"Nasan girman laifin da kayi mata kuma na nuna mata kuskurenta, ta nuna tayi nadama dan Allah ka kar'bi tubarta, ko Allah da ya halicce mu idan munyi masa laifi yana yafe mana, ballantana kai bawan Allah, ka bata dama ta gyara kuskurenta insha Allah ba zata maimaita ba, nasan irin son da take maka kuma ba zata iya rabuwa da kai ba, don tasan idan ta sake hukuncin da zai biyo baya, kayi hak'uri dan Allah ko wannan dukan da kayi mata ai yakamta ace ka hak'ura ka huce haushinka."
Murmushin takaici yayi tare da cewa,
"Bazan ta'ba hucewa ba har sai Inteesar ta dawo cikin gidan nan matuk'ar bata dawo ba wallahi bazan ta'ba hucewa ba."
Da sauri Sumayya ta kalli Muhdeen jin kalaman da suke fitowa daga bakinsa,wani bak'in ciki da takaici ya lullu'be ta, ta d'auka fushin da yayi da ita na yunk'urin kisan Kaine, wanda ko akan waye zai d'auki mataki dan babban laifi ta aikata, amma yanzun ta fahimci cewa akan Inteesar ne yayi hakan, take ta tsinci Kanta a wani yanayi na tsananin bak'in ciki, ji tayi kamar ta kurma ihu tayi hauka, amma tuna halin da take ciki yasa tayi k'ok'arin danne bak'in cikinta kada su fahimta, a zubiyarta tana ayyana irin abunda zata aikata, tana magana ita kad'ai a tunaninta a zuciyarta take magana bata san maganar zuciya ce ta fito fili ba, jin muryarta sukayi tana cewa
"Kwantar da Hankalinki Sumy komai zai dawo dai-dai, kada wannan ya d'aga maki hankali kece zakiyi nasara."
Jin muryar Jabeer na cewa
"Nasara?"
Yasa ta gane cewa a fili tayi maganar, dan haka ta wayance da cewa,
"Eh mana ai mai hak'uri shine mai nasara."
Muhdeen ne ya kalli Jabeer ya ce,
"Jabeer a zahirin gaskiya bazan..."
Jabeer yayi saurin cewa
"Kada ka ce haka, na fahimci matsalarka, insha Allah zata gyara ka tuna baya da darajar iyaye da kuma soyayyar da ta nuna maka kayi hak'uri komai ya wuce."
Murmushin takaici yayi
tare da cewa
"Ba zata ta'ba canzawa ba, na san wace ce ita duk da yanzun ta wuce sani na, kuma ka sani ba abunda zai wuce har sai Inteesar ta dawo."
Danne bak'in cikinta tayi tare da k'ak'alo murmushi ta ce,
"Bakomai duk da hakan nagode Allah ya dawo da ita lafiya, tana ina ne?"
"Bai shafe ki ba, salon na fad'a maki kije ki k'arasa ta?"
Murmushi tayi ta ce
"Yanzun na Sumayya da ka sani a baya bace, wannan ta daban ce na sauya, ina son ka d'auki abunda nayi a baya kayi jifa da shi kada ka sake waiwayawa gare shi, hakan zaisa mu samu zaman lafiya."
Durk'usawa tayi akan gwuiwarta biyu ta fara magana
"Mijina ka yafe mani kuskuren da na aikata na tuba, ka gafarce ni hakan ba zata sake faruwa ba insha Allah."
Bud'e baki yayi da niyyar magana, Jabeer ya ce,
"Kada ka ce komai ka yafe mata dan albarkacin nabiyyin rahmati ."
Murmushi yayi tare da cewa
"Wato Jabeer kasan cewa duk fushin da nayi idan aka kira annabin rahama sai na hak'ura, dan ba za'ace annabi ba banyi ba, amma bakoma zaka iya tafiya."
Sallama Jabeer yayi masa ya tafiyarsa, yana fita ta fad'a jikin Muhdeen ta fashe da kuka ta fara magana
"Nasan zaka d'auke ni mace mara aji, mai nacin soyayya kada kaga laifi na zuciyata ce take assasa ni, I'm crazy about yor I love you more than everything."
Kuka ta dingayi sosai shima kansa yasan tana masifar sonta, wanda had'uwarsu ta farko ita ce ta fara nuna masa so kafin shi ya nuna mata, kuma yasan zata iya 'batawa da kowa akansa, amma duk da haka d'abi'arta baya sonsu, kallon fuskarta yayi ganin yadda ya sauya mata kamanni kuma ya kore ta amma ta kasa tafiya ta dawo ta nemi yafiyarsa, wanda bai ta'ba tunanin hakan ba, yadda take ji da kanta amma wannan Karan ta aje ji da kan a gefe saboda sonsa da gudun rasa shi, tausayinta ne ya kama sa cikin tausayi ya ce,
"Am so sorry"
"Ka daina sona ko?"
Murmushi yayi tare da cewa
"Ban daina sonki ba, kuma bazan ta'badainawa ba, halinki ne bana so, idan kika sauya bani da wata matsala da ke."
Goge hawayen fuskarta tayi tare da cewa
"To naji zan gyara, ita fa kana sonta?"
Ya gane abunda take nufi amma ya ce,
"Wace ce nake so?"
"Inteesar"
"Dukanku mata na ne kuma dukanku ina sonku."
'Daga kanta tayi daga k'irjinsa ta kalle shi da sauri, k'walla ce take k'ok'ari zubo mata na kishinsa, amma sai tayi saurin maida hawayenta ta ce,
"Kai da kanka ka sanar dani cewa kai baka sonta ka tsane ta, kuma nasan auren doke akayi maku daga kai har ita baku son juna, to yaushe ka fara sonta haka? dama saboda ita ce kayi mani dukan da kayi mani? saboda ita ce nemi raba ni da rayuwata?"
"Ba saboda ita bane, ko da ma waye kika aikatawa abunda kika aikata mata hukuncin da zan maki kenen, yakamata ki gane kuskurenki."
Jinjina kai tayi cike da k'unar rai ta ce,
"Yanzun idan ta dawo gidan nan tare zamu dinga sharing d'inka ni da ita?"
Jinjina mata kai yayi alamar eh kasa danne bak'in cikinta tayi ta fashe masa da kuka tana cewa
"Ai ba haka mukayi da kai ba, cewa kayi ko an d'aura maka aure da ita ba ruwanka da ita, baka d'auke ta mata a gare ka ba, na d'auka 'yar aiki aka kawo mani, amma shine yanzun zaka canza magana?"
"To yanzun maganarki zanbi, ko maganar Aah da manzonsa zanbi?"
Kallonsa tayi da idanunta da sukayi jazir tabce,
"Nidai na fad'a maka"
Addinina ya halatta mani auren mata hud'u, koda kike ganin Inteesar auren had'i akyi muna amma ai tana da hakki akaina, kuma idan na fifita ki aknta ko kuma na fifita ta aknaki Allah zai tambaye ni, ko kina son ranar gobe kiyama na tashi 'barin jiki na a karkace?"
Ba zata iya cigaba da saurarensa ba, dan haka ta ruga a guje zuwa d'akinta tana kuka, a tunaninta zai biyo ta ne kamar yadda suka Saba idan tayi haka ya bita shima a guje, amm ayau kam sai taga ba haka ba, ko a jikinsa ya fice a binsa, lokacin da taji tashin motarsa kukanta ya k'aru sosai
Pillows dake kan gadon ta fara d'auka tana jifa da su zanin gadon ma ta yaur tayi jifa da shi, ta mik'e ta nufi dressing mirror kenan ta tuna da zancensa, na cewa halinta ne baya so, don haka ta dakata ta tsaya tana nazari fasawa tayi ta kwashe pillows din da bedsheet ta d'ora Kan gadon don bata ma san yadda zata gyara gadon ta shimfid'a sabon zanin gadon ba.
A can gidan kuwa Inteesar tana cikin d'akin Mufida ta rafka tagumi, tunanin Ummanta kawai take yi, don tunda suka je asibiti dau d'aya ta gaida Ummanta bata sake zuwa ba, don bata san ya jikin nata ba ya kasance ba, ta dai san ance an sallame su tana gida, dan haka ta mik'e ta nufi falo don neman izinin zuwa gaida Mahaifiyarta.
Zaune suke Gwaggo ce da Mummy suna fira, Inteesar ta k'araso wajen tare da sallama, durkuwa tayi tare da cewa
"Sannunku"
Gaba d'ayansu suka amsa da yauwa, Gwaggo ta ce,
"Yar albarka kin fito?
Kai kawai ta gyad'a alamar eh, Mummy ta zuba mata ido tana murmushi ta ce
"Daughter ya dai kamar akwai magana a bakinki ko?"
Sunkuyar da kanta k'asa tayi ta ce,
"Eh Mummy"
"Me ke faruwa?"
Gwaggo ce tayi saurin cewa
"Ki dai kin gaji da zama da mu ne mu maida je d'akin mijinki?"
Tura baki tayi tare da yin narai da Ido kamar zatayi kuka, Mummy ta ce
"Kwantar da hankalinki ba zamu maida ke ba kinji?"
Kai ta jinjina cikin sanyin muryarta ta ce,
"To Mummy"
"Yauwa to ki fad'a mani akwai abunda kike buk'ata ne?"
Kai ta jinjina
"Dama cewa zanyi tunda aka sallamo Umma banje na gaishe ta ba, tunda tana gida muna kusa nake so naje na gaishe ta."
Gwaggo ta ce
"Akan wannan shine kike damuwa? ai uwa ba wasa ba, kuma ai ba nisa bane nan baya ne kije kawai amma dan Allah kada ki sanar da su halin da ake ciki kada hankalinsu ya tashi, kinga Ummanki ba lafiya ne da ita sosai ba, ki nuna mata daga gidan mijinki kika zo kika fara sauka nan sannan kika je gaishe ta."
Kai Inteesar ta jinjina alamr to sannan ta nufi d'akin Mufida, ba jimawa ta fito da hijabinta jar k'asa, sallama tayi masu ta tafi.
Ummanta na zaune tana wankin kayanta, Inteesar ta shigo da sallama, tana hangen Umma ta k'arasa a guje ta rungume ta, Umman nata tayi farin ciki sosai da ganin tilon 'yarta.
"Umma Ina wuni?"
"Lafiya lau wlh"
"Ya jikinki?"
"Jiki Alhamdulillah"
"Mummy tashi na k'arasa wankin"
"Ai na gama "
Inteesar ce ta dinga daukar kayan tana shanyawa akan igiyar shanya, a haka har suka gama.
A can gidan Mummy kuwa Inteesar na barin gidan sai ga Muhdeen yazo, bayan yayi parking ne ya gaisa da ma'aikatan gidan sannan ya nufi cikin gidan.
A falo ya tarar da Gwaggo da Mummy, gaishe su yayi sannan ya durk'usa akan kadarsa ya ce
"Mummy in wuni?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa masa, dubansa Gwaggo tayi tare da kauda kanta taji ya ce,
"Ina wuni Gwaggo"
"Wai yau Kaine ka gaishe ni? banza bata kai zomo kasuwa, abunda kake so na sani saboda matarka ka gaishe ni, kuma ta ba zata koma gidanka ba Dan haka kai kawo mata takardar saki."
Ji yayi kamar an soka masa mashi a kahon zuciyarsa, bazai iya jure maganar Gwaggo ba da haka ya mik'e ya nufi k'ofar fita ba tare da cewa komai ba, a harabar gidan ya had'u da Mufida ya kalle ta ya ce,
."Inteesar tana barci ne?"
Wallah nima yanzun na dawo gidan, kataf suka ju muryar mai gadin yana cewa
"Bata jima da fita ba"
Da sauri ya kalle shi
"What!? ta fita zuwa Ina?"
"Wai zata je gaida Mahaifiyarta da jiki"
Bai Kara cewa komai ba yaja motarsa yabar gida.
Inteesar tana gama shanya kayan Ummanta yaro yayi sallama ya shigo ya ce wai ana sallama da Inteesar, gabnta ne ya fad'i ta ce waye? yaron ya shaida mata cewa wani ne da mota yazo, ta ce ya ke ya sanar bata nan Umma ce ta ce ,
"Saboda me zaki ce haka, bayan kinsan idan ba mijinki ba ai ba Wanda zaizo nemanki, ko dai tare kuka zo ne ya tsasya jiranki waje?"
Rasa ba Umma amsa tayi don bata son ta fahimci halin da take ciki da mijinta, bata gama tunanin ba ta ju Umma na cewa ki tafi ki same shi."
Ba musu ta d'auki hijabi ta nufi k'ofar fita, gabanta ne ya fad'i ganin Usman zaune akan motarsa ya zuba mata ido yana sakar mata murmushi, a zuciyarta ta ce ya akayi yasan tana nan, k'arasawa tayi da niyyar idan ta je ta sanar da shi gaskiya an mata aure da wani.
"Ina wuni?
Murmushi yayi tare da cewa
"Bazan amsa gaishwar ba tsawo kwanki kina wahalar da ni, kullun sai na kira wayarki bata shiga, na kasa hak'uri tsawon lokaci banganki ba zuciyata ta kasa jurewa."
Dai-dai lokacin motar Muhdeen ya k'araso yana parking idanunsa ya sauka akan Inteesar da Usman, ji yayi jinsa da ganinsa sun d'auke na wucen gadi, Usman sai Murmushi yake sakar mata a fusace ya fito daga cikin motar ya nufe su, Inteesar na ganinsa sai da ta tsorata, amma ta daure ya Harare ta ya ce,
"Kina da hankalinki kuwa, kinsan abunda kikayi kuwa"
Kallonsa tayi ta ta'be baki ta ce,
"Waye kai a ina ka sanni?"
Juyawa tayi ta koma cikin gidansu, ya bita da kallon mamaki da al'ajabi, sannan ya kalli Usman ya tuna cewa shine wanda ya ta'ba ganin suna zance da Inteesar kafin tayi aure, kuma shine ya gani ya d'auko Inteesar a mota sunje ubasanjo complex tana zaune gaban motarsa suna sakarwa juna murmushi, rintse idanunsa yayi tare da bud'e su ya kalli Usman ya ce,
"Waye kai?"
Dariyar rainin hankali Usman yayi tare da cewa
"Wanda yazo akeyiwa wannan tambaya ba wanda aka tarar ba"
"Ina mai gargad'i a gare ka ka kiyayi matata."
"Wace ce matarka? Inteesar kake nufi? to ai naga ita wacce kake Kira matarka bata ma sanka ba bata san kanayi ba, isaka ne ke wahalar da mai kayan Kara."
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don k'arin bayani*
09965327995
Love you oll😍😘
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Idan har