Showing 48001 words to 51000 words out of 149432 words
Chapter 17 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
sai ta kasa tana tsoron abunda zai biyo baya kada aji mutuwar sarki a bakinta.Rarrashinta ta dingayi har tayi shiru ta nutsu,ganin bata ta'ab abincin da aka kawo mata bane yasa Mufida janyo abincin cikin hikama taja Inteesar har suka ci suka k'oshi sannan mufida ta kalleta tare da cewa
"2 minutes"
Hanyar fita ta nufa ita dai Inteesar ta zauna tayi tagumi,ba jimawa sai ga Mufida ta dawo da wani k'aramin akwati da kaya a ciki, kallon Inteesar ta yi ta ce,
"Wannan kayanki ne ki tashi ki watsa ruwa, Mummy ta ce na kawo maki kuma wai yau ni zan tayaki kwana."
Inteesar taji dad'in hakan mi'kewa tayi ta nufa toilet don yin wanka.
A can Asibiti kuwa misalin k'arfe biyu na dare Muhdeen ya fito daga d'akin tiyata Kai tsaye office d'insa ya nufa.Bayan ya shiga ne ya nufi bedroom d'in dake cikin office d'in,kayan jikinsa ya rage ya nufi bedroom ya watsa ruwa ya fito jallabiya ya saka ya k'ara gudun A C ya haye gado tare da janyo bargo ya lullu'be.
Washe gari ne da misalin k'arfe tara na safe, Muhdeen ya shigo gidan,da Sallama d'auke a bakinsa ya shigo falon,don dama yana so yayiwa Dady maganar zuwansa London saboda baisan halin da Sumayya ke ciki ba.Ba kowa a falon Gwaggo na d'akinta Mummy kuwa tana kitchen ita da Mufida, kitchen d'in ya shiga ya gaida Mummy yayin da Mufida ta gaida shi nan yake tambayar ko Dady na ciki, Mummy ta shaida masa cewa ya fita tun safe.Hakan yasa dole ya hak'ura inda ya ce zaije ya dawo anjima da yamma lokacin da Dady ya dawo.Har ya kai bakin k'ofa Mummy ta kira sa.
"Son"
Juyowa yayi tare da cewa
"Na'am Mummy"
Kafin ka wuce ka biya ka gaida Gwaggo sannan kuma Inteesar tana part d'inka can aka ajiye ta kafin ta tare a gidanka,itama ka lek'ata ku gaisa kafin ka tafi."
Shiru yayi kafin ya amsa da cewa
"To Mummy"
Baiso hakan ba amma ba yadda zaiyi,d'akin Gwaggo ya fara shiga bata nan amma sai yaji k'arar saukar ruwa a toilet,hakan ya tabbatar masa da cewa wanka take.
Part d'insa ya nufa ba kowa a falon,Kai tsaye ya shiga bedroom d'in.
Inteesar kuwa tana tsaye ta juyawa k'ofar baya,photon Muhdeen dake manne a bango yana murmushi ta zubawa idanu hararar photon take tana ta surutu ita kad'ai Bata San da shigowarsa ba shima baiyi magana ba,jinmuryarta yayi tana cewa
"Hmm kalli yadda yake murmushi a photo kamar bashine wannan mugun ba,mai bak'ar mugunta.Bazan ta'ba mancewa da marukan da kayi Mani a baya ba,kawai don kuskure da nayi bada sanina na watsa maka yawu ba Amma ka dinga marina wanda tunda nake a rayuwa ko mahaifina da mahaifiya basu ta'ba Mani irinsa ba.gashi banda lafiya lokacin haka ka sakani wankin kayanka a cikin toilet dinka duk da haka bai isheka ba sai kace na zauna a rana nayi gadin kayanka har su bushe na goge.Allah ya isan Mani mugu kawai ka banj wahala."
Kamar daga sama taji muryar mutum a bayanta yana cewa
"Ban baki wahala ba tukunna ki shiya shan wahalar nan gaba."
A firgice ta juyo ta kalle shi,wannan shine karo na farko da ta tsaya ta kalleshi da kyau,kyakkyawa ne ajin farko yana da matuk'ar kwarjini gashi da k'ira da cikar zati irin na cikakken namiji.cikin takunsa na k'asaita da tafiyarsa irin na lafiyayyan maza ya k'araso gabanta.
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don k'arin bayani*
0965327995
Love u oll😘😍
Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa.
Page3️⃣3️⃣
Kyakkyawa ne ajin farko yana da matuk'ar kwarjini, gashi da k'ira da cikar zati irin na cikakken namiji.cikin takunsa na k'asaita da tafiyarsa irin na lafiyayyan maza ya k'araso gabanta.
Gabanta ne ya tsananta fad'uwa ganin fuskasa a d'aure tamau ba alamun rahama,tasan halinsa sarai lokacin da bata zagesa ba ya suka k'arke ballantana da yanzun yaji tana zaginsa.Tsoro ne yakamata tuna wahalar da tasha a ranar da murd'e mata hannayenta tare da matse mata baki.
K'ara matsowa kusa da ita yayi har suna shak'ar numfashin juna,cikin tsoro ta bud'e baki zata yi magana ya d'aura yatsar sa d'aya a bakinsa tare da fitar da sautin shhhh. Hakan yasa ta kama bakinta tayi shiru idonta a k'asa Don bazata iya jurar kallon cikin idanunsa ba,don wani irin kwarjini ne dashi. Baya tayi da niyar guduwa tabar masa d'akin amma inaa kafin ta gudu ya damk'o hannunta.Nan take ta ce,
"A'uzubillahi mina shaid'ani rajim"
"Ke nayi maki kama da shaid'an ne da kike mani ta'awizi?"
Kamar zata yi kuka ta fara magana
"Nifa yanzun matar aure ce ka sakar mani hannu."
K'ara matse hannayenta yayi wanda saboda azaba sai da idanunta ya tara k'wallan azaba.
turo k'ofar d'akin akayi Mufida ce ba tare da sallama ba ta fara magana
"Inteesar Mummy ce ta..."
Bata k'arasa maganar ba ta tsaya turus sakamakon ganin Muhdeen da Inteesar da tayi tsaye yana rik'e da hannun Inteesar,sunkuyar da Kai tayi tare da cewa.
"Ku gafarceni na shigo maku Kai tsaye."
Daga nan ta juya zata fice taji muryar Inteesar na cewa,
"Yauwa Mufida gara da kika shigo ki fad'a masa cewa ni matar aure ce Kinga yadda yadda matse..."
Kafin ta kai K'arshen maganar ne taji ya daka wa Mufida tsawa.
"Get out in my room"
Da sauri Mufida ta fice a d'akin,don ta tsorata da tsawar da ya daka mata,maida dubansa ga Inteesar yayi yana cewa.
"Da kike cewa ke matar aure ce ni zaki fad'awa aure?to ki tantabara ce ke ni ba damuwa ta ba ce."
Murd'e hannayanta yayi da d'an k'arfi tare da cewa
" ni kika gama zagi ko? wato nine bak'in mugu ko?"
Kai ta girgiza masa idanunta na zubda hawaye ta ce,
"I'm sorry"
Gajeren murmushi ya yi yana cewa
"Sorry for your self"
Yana rik'e da hannayenta wayarsa ta Fara ruri zaro wayar yayi daga cikin aljihunsa,d'agawa yayi tare da cewa.
"Jabeer ya akayi ne?"
Jabeer yana shirin bud'e baki yayi magana kenan sai yaji muryar Inteesar ta cikin wayarsa tana kuka tana cewa
"Dan Allah yaya Muhdeen kayi hak'uri ka barni haka nan wallahi da zafi,ka tausaya mun haka."
ta saki k'ara lokacin da ya k'ara matse hannayenta.Jabeer kusa daga can cikin wayarsa yake Jin maganar Inteesar.Dariya ya kece dashi sosai har ya zauna daga tsayen da yake, shi a tunaninsa muhdeen sex yake da Inteesar da ya ji tana cewa akwai zafi ya barta hakanan ya ji k'aran da ta saki hakan yasa yakewa Muhdeen dariya.sai da ya tsagaita da dariyar kafin ya fara magana.
"Lallai namiji bashida kunya wato duk zagin yarinyar nan da kake kana cewa kucakar yarinya Allah ya kiyaye ka tsaneta yanzun ta tashi daga kucakar ne?ko kuma k'iyayya har ta juya ta koma soyayya ce? Hhhhj to kadai bi 'yar mutane a sannu kasan sabon shiga sa..."
Tsuki Muhdeen yayi tare da katse kiran,hannun Inteesar ya saki tare da hankad'ata ta fad'a Kan gadon tana sakin kuka.
Mummy da Mufida ya samu a dinning room suna Breakfast,Sallamar Mummy yayi tare da sanar da ita anjima zai dawo yana son magana da Dady.Nan Mummy ta nemi yayi Breakfast kafin ya tafi amma ya nuna a office zaiyi Breakfast,hakan yasa ta barshi ya tafi hakanan.
Fitarsa kenan sai ga Gwaggo ta fito daga d'akinta,k'arasowa tayi tana fad'in
"ina cikin band'aki sai naji kamar muryar Muhammadu ya shigo d'akina shin ya tafi ko yana nan?"
Mummy ce ta bata amsa
"Yanzun ya fita amma ya ce anjima zai dawo."
Kallon Mufida Gwaggo ta yi tana cewa
"Ya banga 'yar albarka ba?"
Mik'ewa Mufida tayi
"Bari naje yanzun na kirata dama lokacin da naje kiranta na sameta ita da yaya ne a cikin d'akin,yanzu tunda ya fita bari na koma."
Da sallama ta shiga d'akin,jin muryar Mufida ne yasa Inteesar saurin goge hawayenta,d'agowa tayi ta kalli Mufida tana sakar mata murmushi,da mamaki Mufida ta kalli fuskarta.
"Lafiya kike kuwa naga idonki kamar kinyi kuka?"
"Bakomai banyi kuka ba,barcin da na tashi ne yasa idanu na sukayi haka."
Murmushi Mufida tayi tana fad'in
"Tare da ke fa muka tashi barci idonki baiyi haka ba sai yanzun?koda ya ke bazan matsa maki tashi muje muyi Breakfast."
"Yauwa Mufida bari na tambayeki mana ."
"Ina jinki"
"Me yasa aka sauke ni a d'akin nan ne?wallahi banso zama a d'akin nan ba ga mai d'akin ya dawo ya sameni a ciki nifa gasky zan koma d'akinki ko na Gwaggo."
Dariya Mufida yayi tana cewa
"To ai ba inda Zaki zauna bayan nan nan ne yafi dacewa dake."
Tunawa tayi da cewa Kila fa haryanzun ba wanda ya fad'awa Inteesar cewa Muhdeen ne mijinta.Hakan yasa bata sake magana taja hannun Inteesar suka nufi hanyar fita.
Koda suka k'arasa dinning table kallo d'aya Gwaggo tayi mata taga idonta ya yi kama da na wacce ta yi kuka.Haka ma Mummy ta lura da hakan, Gwaggo ce ya fara magana.
"To 'yar albarka lafiya me ya sameki ne kikayi kuka?"
"Banyi kuka ba Gwaggona"
Mummy ce ta zuba mata ido
"Kada kiyi mana k'arya don ba d'abi'arki ba ce k'arya kada ki fara."
Shiru tayi tana nazari,don ita dama duk abunda zai janyowa wani 'bacin rai bata so,hakan yasa ta ce,
"Bakomai"
Kai Mummy ta girgiza
"Kodai da son ya shiga ya 'bata maki raine?idan ya maki abunda ba dai-dai ba ki fad'a mani a matsayina na mahifiyarsa zand'auki mataki aka sa."
Murmushin yak'e tayi
"Ba komai ya sani kuka ba kawai na tuno da Abbana da Umma ne yasa nake kuka"
Kai Gwaggo ta girgiza tana cew,
"Kiyi hak'uri kinji kowa haka akayi mata Umman taki mma haka Mata ."
Nan dai suka dinga Bata baki sai da suka dinga bata baki har ta hak'ura sukayi Breakfast suka gama.Bayan kammalawarsu ne Gwaggo ta ce Inteesar ta koma d'akin Muhdeen zata zo ta same ta,haka kuwa akayi Inteesar ta ka d'aki ba jimawa Gwaggo ta shigo hannunta d'auke da wani galam da kuma Babbar robar ruwa da wani abu a cikin robar.Inteesar na zaune saman sofa dake ckin bedroom d'i,gefenta Gwaggo ta zauna tare da ajiye su,kofin da ta d'aura saman Galam d'i ne ta d'auko robar k'arami ta bud'e tare da tsiyayo wani abu daga cikin gorar,mik'awa Inteesar tayi
"Kar'bi wannan yanzun ki shanye shi yanzunnan."
Kar'ba Inteesar tare da zubawa abun ido gashi kamar zuma Amma ga wani garin abu a ciki kamar garin magani a ciki.
"Gwaggo meye wannan kuma?"
"Zuma ce ta mata da tsumi,kar'bi kisha."
Kar'ba Inteesar tayi ta fara sha,dama ita akwaita da son zak'i to zak'in da taji ne yasa nan da nanan ta shanye shi tas.Kar'bar kofin Gwaggo tayi tare da zuba mata tsumin cikin kofin ta mik'a Mata, dai-dai lokacin da Mufida ta shigo d'akin,kafa baki Inteesar tayi ta fara sha sannan ta cire baki tana d'an yamutse fuska ta ce,
"Gwaggo naji wannan da d'an bauri bai yi zak'i kaman wancan ba,gaskiya ni ya isheni hakannan"
Ta k'arasa maganar tana mik'awa Mufida sauran tsumin kar'ba Mufida tayi zata shawa sai Gwaggo tayi saurin k'ar'ba ta mik'awa Inteesar tana cewa,
"Me yasa zaki bata?to ba irin nata bane,itama idan lokacin ta yazo zata sha ne amma ba yanzun ba."
"Yaushe ne lokacinta?"
"Lokacin da tayi aure kamar yadda kema kikayi."
"Gwaggo Wai kina nufin saboda nayi aure kika bani?"
"K'warai kuwa kayan mata ne gobe ma za'a kawo maki wasu,don Mummyn Mufida tasa akawo maki wasu."
Suna Jin haka sun san inda zancenaGwaggon ya dosa tura baki Inteesar tayi yayin da Mufida ke ta yi mata dariya.
"Nidai Gwaggo don Allah ku kyale ni wallahi bana so."
Fuska Gwaggo ta had'e
"Ke dalla gafara can ana nuna maki ga annabi kina rintse ido,akwai gatan da zamu nuna maki wanda ya wuce wannan ne?ko ba don shi jikana ba zanyi ba ko ba komai ni maiyi maki ne,Ballantana jikana nayiwa."
Ita dai Inteesar bata san inda maganar Gwaggo ya dosa ba,Don Bata gane nufinta ba.Turo k'ofar akayi had'i da sallama Mummy ce hannunta rik'e da food flask Aunty Abla na biye da ita a baya, Mummy ce ta mik'awa Gwaggo food flask d'in tana cewa,
"Kinga ma na d'auka sai gobe ne zata had'o da sauran kayayyakin ta kawo ashe ma Wai tunda an riga an dafa kazar shine ta fara kawo ta tare da sauran magungunan."
Aunty Abla ce ta gaida Gwaggo.
"Ina kwana Gwaggo"
"Lafiya lau Abla ya Mai gidan da yara duka?"
"Lapiya qalau suke Gwaggo."
"To masha Allah,amma kazar ce kawai ta samu?"
"Eh Gwaggo sauran Wai sai gobe zata had'o su,kuma ina da shwara Gwaggo matar nan k'awata ce munyi magana da ita idan ba damuwa da ankai Inteesar ta zauna a gidanta na sati d'aya yadda zata gyara ta ciki da waje,wallahi idan kika yadda na tafi da Inteesar gidanta na tsawon sati d'aya kawai wallahi sai kinyi mamakin canzawa da zatayi don Wallahi sai ta burge ki."
Jim kad'an Gwaggo ta yi tare da kllon Mummy ta ce,
"Fatima ya kika gani game da shawar k'anwar taki?"
Murmushi Mummy tayi tare da cewa
"Gwaggo nima nayi wannan tunanin,nariga ta a zuci ne ita kuma ta rigani a baki,nasan Hajiya Bilkisu k'awar Abla ce tun suna yara,sana'ara ce gyran amare da zaifi idan muka bari suka tafi tare don wasu ma tun biki na wata d'aya saura suke Kai yaransu gidanta."
Gwaggo jinjina Kai tayi
"To shikenan tunda haka kuka ce na amince ta tafi da ita d'in,amma fa ina ganin sai anyi fama da yarinyar nan, yanzun nake bata tsumi da zumar mata take ce Mani wai bata so mubarta hakanan."
"Karki damu Gwaggo zata kula da ita yadda yadda kamata ba zata barta hakanan kawai ba,ki tana so ki bata so sai anyi mata,ni kuma kullun zan dinga lek'awa Ina duba su.
Ta k'arasa maganar tana zama gefen Inteesar tana cewa
"Tare zamu tafi kinji daughter"
jinjina Kai kawai Inteesar tayi don bata son tayi masu gardama ne yasa ta yin shiru,amma ita har ga Allah bata k'aunar zuwa wani gidan gyaran da za'a kaita.
Mummy ce ta kalli Gwaggo tana cewa
"Yanzun taci kazar su tafi don ta ce sauri take zatayi bak'i."
Gwaggo ce ta bud'e flask d'in da aka zuba kazar ta mik'awa Inteesar,ganin gari-garin magani a jikin kazar yasa Inteesar ture baki, Gwaggo ce tayi Mata magana
"Zaki tsaya kina tura baki ko kuma zakici kazar ne ku tafi ko kuma zaki tsaya kina turawa mutane baki ne."
A shagwa'be ta fara maganar
"Wallahi Gwaggo na k'oshi ba wajen da zan saka kazar nan."
Jin hakan yasa Aunty Abla cewa
"Kada ku damu ku rufe mani flask d'in mu tafi dash,ko tana so ko bata so zata cimye shi tas."
Aunty Abla ce ta kar'bi flaak d'in ta rufe tare da kallon Inteesar ta ce,
"Tashi ki saka hijabi kid'ebi kayan sawanki na sati d'aya mu tafi."
Ba musu duk da a ranta bata so hakan ba amma bata da za'bi hakan ta mik'e ta d'auki hijab d'inta ta saka mummy ce ta ce,
"Kid'auki akwatin kayan da Mufida ta kawo maki jiya dadaddare kije dasu gaba d'aya."
Mufida ce ta janyo akwatin kayan gaba d'ayansu suka fita har harabar gidan,but d'in motar Aunty Abla Mufida ta bud'e ta saka akwatin kayan sannan ta bud'ewa Inteesar murfin motar gefen Aunty Abla ta zauna,sallama sukayi da juna sannan Aunty Abla taja motar tare da yin horn mai gadi ya bud'e mata suka fice daga gidan.
Lokacin da Muhdeen yabar gidan Asibiti ya koma,Kai tsaye office d'in Jabeer ya nufa yana k'ok'arin knowking ne Jabeer ya murd'a handle d'in k'ofa zai fito,ganin Muhdeen ne yasa ya koma ciki yana k'unshe dariya a bakinsa,zama yayi a sofa dake cikin office d'in Muhdeen ya tsaya tsaye ya zuba masa luhuluhun idanunsa yana kallonsa.Jabeer ne yayi k'ok'arin dakatar da dariyarsa ya ce,
"A mijin kucaka har ka gama kwasan romon amarcin ne? Dan Allah adai dinga d'aga k'afa kasan sabbin shiga sai a hankali sai ana tausaya masu,duk da nayi mamakin cika bakin da ka dingayi akan Inteesar sai dai abun mamaki a Rana d'aya ka zubar da makamanka,banyi tunanin haka da wuri ba fa nace ashe ashe kucakar yarinyar da ka tsana zatayi maka rana 'Dan iska jarababbe ranar har kana cewa ko Mata sun k'are a duniyar nan ba abunda zakayi da ita,Ashe har matan sun k'are banda labari."
Ya k'arasa maganar yana kecewa da dariya, Muhdeen ransa ne ya gama 'baci kuma shi Mai yawan magana ba gani yayi baida lokacin 'bata lokacinsa a kan Jabeer yasa ya mi'ke ya nufi hanyar fita.Da sauri Jabeer yasha ganansa tare da cewa
"Sorry friend dama na kiraka ne dan na shaida maka kana da patients suna jiranka"
Daga nam Muhdeen yasa Kai ya fice ya bar Jabeer na binsa da kallo.
A yammcin ranar ne Muhdeen ya koma gida dan magana da mahaifinsa,cikin sa'a kuma ya same su dukkansu a falo Dady, Gwaggo,sai kuma Mummy,da sallamarsa ya shigo falon,gaba d'ayansu suka amsa masa nan ya gishe da kowa da kowa harda Gwaggo yau cikin girmamawa ya gaishe da ita yana kwantar da Kai Dan kada tasa Dady ya hana shi zuwa London.Harda yi mata alk'awarin kawo mata magungunan ciwon k'afarta Wanda zata ji dad'i haka ya dinga kamfen a wajen Gwaggo don yasan ba k'aramin aikinta bane tasa Dady ya hana sa tafiya.
"Muhammad ya akayine ance kana ta zuwa nema na bana nan kuma baka sanar dani a waya ba."
Sunkuyar da Kai yayi
"Dady maganar ba Bata waya bace shiyasa."
"To Allah yasa lafiya ina jinka"
"Dady Sumayya ce ta tafi bansan inda ta je ba tun da taji an d'aura aure na da Inteesar ta saka k'afa tabar gidan har yau bansan inda ta tafi ba."
Da mamaki Dady ke kallonsa
"Subahanallahi shine tun tuni baka sanar da kowa ba sai yanzu?Haba Muhammad ai baikamata kayi shiru ba."
"Dady abunda yasa nayi shiru na d'auka zan ganta ne sai na shawo kanta mu cigaba da zamanmu,to gaba d'aya mun zaga garinnan inda nasan cewa tana da k'awa ko dangi ko wani Wanda yake da alak'a da ita amma ko ina bata nan."
Mummy ce ta ce,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,shine na aka tambayeka ka sanar da matarka kace eh."
"Wallahi Mummy na d'auka zan iya shawo matsalar ne,kuma na Kira number Dad da Mum d'inta duk basa shiga."
Dady ne ya ciro wayarsa a aljihu ya Kira number