Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 149432 words

Chapter 23 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1360

Ads at the middle of Article

aikin.


Da paart d'inta ta soma daga nan bayan ta gama ta nufi part d'in Sumayya,haka ta dinga bin falon da d'akunan da toilets na kowane da kitchen duka biyu dinnan area ko ina sai da ta goge su tas.


Dama can ba wani datti sukayi ba fes suke kuma ba amfani ake dasu ba ba kowa a ciki,amma don mugunta sai ya sata ta yi safe da yamma.


Bata gama ayyukan da ya saka ta ba sai k'arfe d'aya na dare,duk ta gaji sai hawaye ne kawai ke tsiyaya masu d'umi daga idanunta.wanka ta yi tare da yin addu'ar kwanciya barci ta kwanta, lokacin k'arfe d'aya da rabi na dare.


K'arfe hud'u da rabi na asuba ta farka wanka ta yi ta d'auro alwala,ta yi nafila da addu'a ta samun sassauci a rayuwarta, har aka Kira assalatu ta yi sallah da azkar tana son ta tashi ta yi ayyukan safe ne barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita ba tare da ta shiryawa yin barcin ba.


Misalin k'arfe tara na safe ya fito daga bedroom d'insa ganin bai ganta a kitchen ba kuma bata shigo ta gyara masa d'aki ba yasa ya nufi d'akinta.


Tura k'ofar ya yi ya ganta kwance saman sallaya da hijab a jikinta,alamun daga sallah ta yi barcin,fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi sosai ya 'balle murfin robr ya tsiyaya mata ruwa tun daga Kan fuskarta har zuwa jikinta, a firgice ta farka tare da fad'in


"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un"


Jikinta ne ya soma rawa don ruwan ya yi sanyi da yawa,gashi dama bata son ruwan sanyi ko wanka dashi batayi Amma yau ruwa mai sanyi kamar K'ank'ara aka kwarara mata a jiki,kuka ta fashe da shi mai cin rai,yatsarsa ya sa a baki tare da furta


"Shhhhhhp"


Ba shiri ta had'ye kukan hawaye na tsiyaya a idanunta.


"K'arfe nawa yanzun?"


Kallon agogon da ke manne a d'akin ta yi


"K'arfe tara da minti biyar"


"Shine kike kwance kina barci?"


"Wallahi bansan lokacin da barci ya d'auke ni ba."


"Tashi kije ki yi ayyukan da kika San ya wajaba a kanki."


Mi'kewa ta yi zata shiga toilet taji muryarsa yana cewa


"Ina zaki je?"


"Zan shiga toilet ne na cire kayan nan sun jik'e da ruwan sanyi, idan na ce zan barsu a jikina sanyi zai kamani ne."


"Ya kamaki mana sai me?ba sanyi ba ko k'ank'ara zai kamaki ya kamaki ba matsalata bace,don haka fita ki fara ayyukan da na saka ki."


Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki ta fita ya bita da kallon banza.








Daga alk'amin✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






Don k'arin bayani


09065327995




Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*


Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.






Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa,idan suna ki hali yaso d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi t,arashi ne mai kashe auren wawa.






*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*




Page4️⃣2️⃣


Haka ta fita kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki,ta fita ya bita da kallon banza.


A haka ta da jik'akkun kayan ta dinga aiki da su a jikinta,har suka bushe a jikinta ga sanyin da take ji ba yadda ta iya ahaka ta gama ayyukan gidan.


Kasancewar ba ya cin abincinta ya sa bata yi wani girki ba ta ruwan shayi kawai ta dafa ta sha,ta koma d'akinta lokacin rana ta riga da ta yi, wanka ta yi ta Sanya soguwar riga na atamfa wayarta ta soma ringing dubawa ta yi Usman ne daon haka Bata d'aga kiran ba har ya tsinke,wani tunani ta yi kodai ta d'aga ne tunda wannan auren ba mai d'orewa bane shi da kansa ya fad'a mata idan Sumayya ta dawo zai rabu da ita,don ba sonta ya ke ba tunanin hakan ne ya sa ta cewa bari ta d'aga kafin matarsa ta dawo ya ce zai sallame ta,d'aga wayar ta yi ta Kara a kunnenta.


"Assalamu Alaikum"


Daga can 'bangaren Usman da ke zaune a office d'insa ya saki ajiyar zuciya tare da furta.


"Wa'alaiki salam, har naji sanyi a Raina Inteesar azabtar da ni da kike ya yi yawa,baki san rashin ganinki da rashin jin muryarka ya hanani sukuni ba kullun da tunaninki nake kwana nake tashi,tunda muka had'u a sau uku nazo gidanku amma kika hana wai Abba ya hanaki,hakan ya sa na yi tunanin zuwa neman izinin zuwa zance a wurinsa."


Da sauri ta katse shi da cewa


"Kadai bari zuwa nan gaba kad'an amma ko ka same shi yanzun zai ce ka bari zuwa gaba kad'an ba jimawa,saboda haka idan olkaci ya yi da kaina zan sanar dake."


Hira suka ta'ba sosai na kusan mintuna talatinl,sai da ya ji ana knocking sannan ya mata sallama ya ajiye wayar,sannan ya bada izinin shigowa.


Ita kuma sanin cewa jiya abokan mijinta suka ce yau zasuzo ne ya sa ta mi'ke ta nufi kitchen don d'aura masu girki.
Jallop d'in cuscus ta da white rice and stew da ta ji naman rago,sai pepper chicken da tayi masu da farfesun d'anyar kifi da ta yi masu ga lafiyayyan juice na kwakwa da madara,ta had'a masu girkuna masu gidan ya cika da k'amshin girkinta ya cika gidan.


Komawa d'akinta tayi ta fad'a toilet ta sake sabon wanka sake ta shirya cikin doguwar riga na less d'inki bubu ya kar'bi jikinta,dama ita bata damu da kwalliya ba,don haka bayan ta shafa man shafawarta na wajen Hajiya Bilkisu, powder kawai ta shafa sai man baki,ta saka sark'a da d'an kunne,gasjin kanta ta tufke shi a tsakiyar kanta,zama ta yi baki gadon tare da d'aukar wayarta tana buga game.




Gidansu Inteesar kuwa koda Abbanta ya dawo kasuwa yammaci ne lik'is hannunsa d'auke da leda mai layin yellow da bak'i, Dankalin hausa ne a cikin ledan da sallama ya shigo gidan , Umma da ke zaune gaban murhun itace tana tuk'a tuwo ne ta amsa masa sallamar,sakin muciyar ta yi da niyyar tashi ta kar'bo ledar,hannu ya d'aga mata alamar ta barshi .


"Zauna ki cigaba da aikinki Umman Inteesar"


Murmushi ta yi tare da cewa


"Sannu da zuwa ya kasuwar?"


"Alhamdulillah an godewa Allah."


Zama ya yi kan tabarman da ke shimfid'e a k'ofar d'akinsa.


Bayan Umman Inteesar ta gama tuk'a tuwon ne ta tashi ta d'auki kofin silver da murfinsa ta d'ebo masa ruwa,a cikin randar k'andar k'asa me sanyi gabnsa ta ajiye tare da k'ara masa sannu da zuwa,bayan yasha ruwan ne ya mi'ke tare da cewa


"Bari na tashi nayi wanka na tafi masallaci, lokacin salla ya k'arato.


Mi'kewa ya yi yayin da Umma dama ta ajiye masa ruwan wanka a cikin tukunyar da suke dafa ruwan zafi,juyewa ta yi a cikin bokinti ta surkar masa da ruwan sanyi ta kai masa bad'aki ya fito daga cikin d'akinsa ya shiga band'akin


Bayan sallar isha'i ne bayan ta dawo daga masallaci yana zaune a Kan tabarma Umma ta kawo masa tuwo,ya ci ya gama ta ce ,


"Mallam Inteesar sunzo da mijinta d'azun da rana kana kasuwa."


Zuba ma Umma ido yayi fuskarsa d'auke da murna duk da bai ganta ba amma ya ji dad'in zuwanta gidan.


"Masha Allah da nasan zata zo da na bari sai na ganta kafin na tafi,suna dai lafiya ba wata matsala ko?"


"Wannan ne kuma ban sani ba mallam"


"Kamar ya baki sani ba da tazo me yasa baki tambaye ta ba ko awai wata damuwa."


Shiru Umma ta yi tana tunanin yanayin da taga Inteesar,ita ta haifeta tafi kowa saninta a duniyarnan,amma ganin yanayin da ta ganta ko shakka babu akwai abunda ke damunta,dalilin da yasa bata d'aga hankali ba tasan cewa wasu lokutan auren had'i idan har basa son junansu sukan sawa kansu damuwa da tunani saboda ba wannan ne a zuciyarsa ba,wannan dalilin yasa Mummy kauda ido.


"Mallam ta ce mani suna zaune lafiya."


Jinjina kai yayi


"Masha Allah"


Umma ta mik'e ta shiga d'aki ta fito hannunta d'auke da kud'in da Muhdeen ya bata mik'a masa tare da cewa


"Mijinta ne ya kawo muna kayan abinci masu yawa tare da kud'in nan."


Kallon kud'in Abba ya yi sannan ya kalli Umma ya ce,


"Harda d'awainiya haka?da baki kar'bi kod'insa ba"


"Nima banso kar'ba ba ajiyewa ya yi"


Yana zaune akan kujera Yana jiran isowar abokansa,wayarsa ta fara ruri,dubawa ya yi yaga Dadynsa ne,d'aga wayar ya yi tare da cewa

"Assalamu Alaikum"


Daga d'aya 'bangaren


"Wa'alaika salam Muhammad kana gida ne?"


"Eh Dady ina gida ina jiran su Jabeer ne zasu zo."


"Okay to ga Gwaggo nan ta shirya kayanta ta ce lallai sai dai na kira ka kazo ka d'auke ta zuwa gidanka."


Gaba d'aya hankalin Muhdeen ya tashi,don yasan zuwa sa masa ido kawai Gwaggo zata yi ba wai don ziyara ba,yanzun ya zaiyi da wannan tsohuwar ba,ta zame masa matsala,yana cikin tunani ya jiyo muryar Dady na cewa


"Ya kayi shiru lafiya kuwa?"


Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa


"Gani nan zuwa Dady"


Tsuki ya ja tare da d'aukar wayarsa kamar ya ba Direba ya d'auko ta,ya tuna kira Mahaifinsa ne don haka ya ta fi da kansa.


Yana driving akan hanyarsa ta zuwa d'aukota ne wayarsa ta soma ruri dubawa ya yi yaga Sumayya ce, ba shiri yayi parking a gefen titi ya amsa wayar cikin farin ciki.


"Hello Baby sai yau kika Kira ni tunda kika tafi sai ma kika sakani a blacklist ko?"


Jin sautin kukanta ya ke harda sheshshek'ar kukanta,rintse ido ya yi sakamakon jin sautin kukan nata.


Kinga kunga dan Allah ki daina kukan nan hakanan muyi magana.


"Ba dole nayi kuka ba tunda na tafi ba ka damu Dani ba ka mance dani saboda kana tare da wannan yarinyar da parents d'inka suka aura maka."


Kinga da kinsan irin zaman da nake yi da yarinyar nan a gidan nan ko?da baki fad'i haka ba,ni fa wannan auren ban d'auke shi aure ba tunda taso gidan nan wallahi ko kallo bata ishe ni ba zaman gidan nan dai-dai yake da zaman gidan wak'afi a wajenta."


Dakatar da kukanta ta yi tare da cewa


"Kana nufin ba abunda ya shiga tsakaninka da ita?'


"K'warai kuwa ko hannunta ba ta'ba rik'ewa ba ballantana wani abu ya shiga tsakaninka mu,kuma zaman da take a gidan nan ki d'auka 'yar aiki ce na kawo maki,zata kasance mai maki ko wani irin aiki da bin umarninki."


Dariyar mugunta ta yi tare da cewa to


"Gobe ma zan dawo"


Shiru ya ya yana nazari kafin ya ce,


"Dawowarki gobe akwai matsala ki bari sai bayan wata d'aya ki dawo?"


Sakin baki tayi cikin mamaki ta ce,


"Baby anya kuwa kana sona yanzun?"


"Ba abunda ya ragu cikin son da nake maki."


"To me zaisa ka ce na bari sai bayan wata d'aya na dawo alhalin ina nan na matsu na ganka kana cewa one month."


"Abunda ya sa kika ji na ce haka yau Gwaggo zata zo gidan nan kuma idan tazo sai ta yi one month kafin ta tafi,Kinga kuma zamanki da Gwaggo a gida d'aya akwai matsala,kuma kunga matuk'ar tana cikin gidan nan bazan ta'ba k'untatawa rayuwar Inteesar ba dole na d'aga mata k'afa bazan cutar da ita ba har sai bayan Gwaggo tabar gidan."


Shiru ta yi tana nazari kafin ta d'aura da cewa


"Bakomai amma gaskiya ka samu lokaci kazo na matsu na ganka kafin lokacin tafiyar Gwaggo ya zo."


Murmushi ya yi tare da cewa


"Karki damu zamuyi waya anjima."




Tana zaune a falonta tana tunanin yanayin rayuwar da take ciki,tana kuma tuna yanayin rayuwar da take ciki kafin aurenta.


Turo k'ofar aka yi taga Ishaq direba ne da akwati a hannunsa,tana kallon akwatin ne ta ji muryar Gwaggo na cewa


"Ina 'yar albarka take?"


A guje ta nufi k'ofar tana dariya,akan barandar shiga falon ne taga Gwaggo da Muhdeen, rungume Gwaggo ta yi da k'arfi kamar zata shige jikinta.


"Yar albarka bini a hankali k'afar ba lafiya"


Jin hakan yasa ta d'an sassauta tare da cewa


" Oyoyo Gwaggo"


"Okay wato ganin Gwaggo yasa kin mance da ni ko?oyoyon da ake mani ma yanzu ban samu ba saboda Gwaggo ko?"


Tsayawa ta yi tana kallonsa cikin mamamki,a zuciyarta ta ke cewa yanzun zai fara amfani da fuska biyu kenan.


A falo suka zauna inda Inteesar ta nufi kitchen don kawowa Gwaggo abun ta'bawa Muhdeen kuma ya k'udiri niyyar cewa bazai ta'ba barin wata k'ofa da zaisa Gwaggo ta gane cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da Inteesar ba,zai dinga nuna mata k'auna da kulawa,zai janyo Inteesar a jikinsa yadda zata sake dashi ta daina jin tsoronsa don burinsa ya cika.


Inteesar ce ta kawowa Gwaggo ruwa da lemu a faranti,kallonta Gwaggo ta yi tare da cewa


"Sannu da k'ok'ari 'yar albarka Allah ya nuna mani 'ya'yanku."


Sallama suka ji daga bakin k'ofar shigowa, Muhdeen ne ya amsa tare da basu izinin shigowa, Jabeer ne da Salisu da Bilyaminu sai kuma Baahir.


"Jabiru kune a tafe?


Dariy ya yi tare da cewa


"Eh mune Gwaggo, dama kina nan ne?"


"Yanzun nan nazo kuma wata d'aya zan masu a gidan nan,duk da cewar shi Muhammadu bak'in ciki yake da zuwa na ban damu ba,duk tsiyarsa Bai isa ya koreni ba tunda 'yar albarka na maraba da ganina."


Inteesar dama tunda taji muryar maza zasu shigo ne tayi saurin ta nufi d'akinta,sai gata da hijabi har k'asa,Su Salisu ne suka gaida Gwaggo suka zazzauna a kujera, Muhdeen ya dinga mi'ka masu hannu d'aya bayan d'aya suna gaisawa,Bashir ne k'arshe lokacin da Muhdeen ke mik'a ma Bashir hannu baima san yana mik'o masa hannun ba,gaba d'aya ya shagala da kallon Inteesar ko k'yaftawa baya yi, Muhdeen ya kalle shi ya kalli Inteesar da bata ma San yana kallonta ba hankalinta na wurin Gwaggo da take tambayarta su Mufida,had'e fuska ya yi tare da kallon Inteesar cikin bada umarni ya ce,


"Inteesar ki shiga d'aki"


Da sauri ta kalle shi tana kokonton sunanta da ya kira,don tunda take bata ta'ba Jin ya Kira ta da sunanta ba sai dai ya ce ke wata rana ma mayya yake kiranta amma yau karon farko ta ji ya kirata da sunanta da mahaifinta ya saka mata,Bata gama tuna ni ba ta jiyo ya maimata cewa ta shiga d'aki,take ta juya ta koma d'akinta,kowa dake falon zuba masa ido ya yi shi kuma fuskar nan tasa a had'e,yana tuna lokacin bikinsa da Sumayya ranar da Bashir ya fara ganin Inteesar yana ta yaba kyawun surarta da har yana kiranta da zazzafar yarinya wai duk neman matan banza da yake bai ta'ba ganin macen da ta mallaki abunda ya ke so komai a jikin mace ba sai Inteesar.


"Bros ya zaka kori amarya ita fa muka zo gani,ko gaisawa ba muyi ba ana muna rowarta."


Dariya sukayi Salisu ta d'aura da cewa


"Nima abunda na gani kenan,lokacin da mukayi auren mu ai da yazo zama ya yi suka gaisa da amaren mu,amma kunga shi rowar ta ya ke."


"Muhammadu mutumce fa ita ba akuya ba ce da zaka rufe a d'aki,wannan ai zalinci ne wallahi bani so takura,haka kawai zaka takurawa 'yar mutane."


Bai ko kalleta ba ballantana tasa ran zai amsa mata,


"Bisimillah kuzo muci abinci"


Jabeer ya tintsire da dariya tuna ranar da suka zo cin girkin amarya Sumayya,Salisu da Bilyaminu ma ta ya shi dariyar sukayi don suma abunda suka tuna kenan.


"Nidai wallahi tsoron cin girkin gidanka nake ranar farko da mukazo cin girkin amarya ba Wanda ya iya had'iye ko cokali d'aya gaba d'aya saboda k'warewar Hajiya Sumayya a iya girki."


Gaba d'ayansu suka sake dariya,hakan ya sosa ran Muhdeen matuk'a don haka ya zauna ya fita batunsu ko kallonsu Bai sake ba.


"Koda yake Sumayya daban Inteesar ma daban ,don Sumayya bata iya girki ba ba yana nufin cewa Inteesar bata iya ba,bari mu tashi dai bakinmu ya gaya Mana."


Gwaggo ta zubawa Jabeer idanu tana cewa


"Jabiru Wai kana nufin wannan yarinyar bata iya girki ba?"


Dariya ya yi don dama ya it's tsokana


"Ai Gwaggo idan ana sallah ba'a magana wato ranar da tayi muna girki wallahi gaba d'aya kamar an wanke kai,ni wani d'aci naji na ma kasa tantance want irin test abincin keyi gashi bai dahu ba,dukanmu ba Wanda ya iya cin ko cokali d'aya,na ce wannan girkin na masoya ne."


Ta'be baki Gwaggo ta yi tare da cewa


"Idan mace bata iya girki ba ki ai ba mace bace,dama sai da na guje masa auren ta amma bai saurare ni ba."


"Ya isa hakanan kun zauna Kuna ta cin mutuncin mata ta akan me?"


Mi'kewa Jabeer ya yi tare da nufar dinning area.


"To ina amarya ta zo ta zuba mana muji ya nata k'warewar take."


"Ba zata zo ba kowa ya zubawa kansa ya ci tunda ba cikinta zaku zuba ba."


Daga nan ya juya ya nufi d'akin Inteesar,tura k'ofar ya yi inda ya samu tana waya a cikin zancen nata ne ya ji tana cewa


"Haba Usman ka daina fad'in haka Usman wallahi nima ina cikin damuwa na yi missing d'inka sosai."


Gaban Muhdeen ne ta fad'i cikin tashin hankali ya furta


"What?"








Daga alk'amin✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






Don k'arin bayani


09065327995




Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*


Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.






Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kase auren wawa.






Page4️⃣3️⃣


"Haba Usman ka daina fad'in haka, Usman wallahi nima ina cikin damuwa, na yi missing d'inka sosai."


Gaban Muhdeen ne ya fad'i cikin tashin hankali ya furta


"What?"


A firgice Inteesar ta juyo ta kalleshi gabanta na tsananta fad'uwa,cikin sanyi da nutsuwa fuskarsa ba yabo ba fallasa,ya k'araso gabanta yayin da ya mik'a mata hannu alamun ta bashi wayar,katse kiran tayi kafin ta bashi wayar kar'ba yayi tare da cewa


"Waye shi?"


Shiru ta yi ba tare da tayi magana ba,ya sake tambayarta da cewa


"Na ce waye Usman?"


Shiru ta yi masa ta kasa cewa komai,zuba mata ido ya yi yana kallonta.


"Soyayya kike da wani k'ato da igiyar aure na akanki?saboda baki San darajar aure da martabarsa ba ko?."


Sanin cewa Gwaggo na cikin gidan kuma matuk'ar Gwaggo na gidan bai isa ya ce zai mata wani

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads