Showing 6001 words to 9000 words out of 149432 words
Chapter 3 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
don Allah da soyayyar ka annabi Muhammad S.A.W."
Jikin mallam Ali ne yayi sanyi domin duk taurin kansa idan aka had'a shi da Allah da mazon sa angama yace to
" Shikenan Allah yasaka da khairan."
Waigawa tayi tana neman Inteesar cikin murmushi ta ce,
"Ina Yar tawa take?"
Umma ce ta ce,
"Ta tafi islamiya"
Kai ta gyada tare da cewa
"Agaida mani ita"
Mikewa tayi tare da masu sallama tabar gida.
A cikin kwana biyu aka gama shiryawa Inteesar komai na makarantar an basu inda ta fara karatu class d'in su daya da Mufida jss 3 kullun direban gidan su mufida zai kaisu, Inteesar da wuri take shirywa Don idan ta idar da sallar asuba tayi azkar bata kuma kwanciya barci,zata hura wuta tayi wanke-wanke ta gyara d'akin ta da share tsakr gidan idan Koko zasusha ta dama idan kuma d'umame ne tayi kafin karfe bakwai ta gama ayyukan gidan nan ta karya karfe bakwai zata nufi gidan su mufida,kullun idan taje takan samu Mummy a kitchen tana had'a breakfast,haka zataje ta tayata su kammala,ko Mummy tayi ta fama da ita taci wani abun ko tea tasha amma sai tak'i.wata rana ma ita take taya Mufida shiryawa don idan ta Mufida ce sai suyi lettin zuwa school, Ita kuma Asiya tunda ba school d'aya suke ba bata bi ta kansu,ko gaisuwar Inteesar ma Bata amsawa sai dai idan taga idanun mummy,don kallo wulakanci take mata,don bata d'auko halin Mummy ba tana da kyamatar talaka gata mishkila ce,Dady ma ya nunawa Inteesar k'auna da kulawa,musamman da yaga matar sa da kuma autar sa Mufida suna k'aunar Inteesar Shima yake kaunar ta kamar shi ya haife ta,don ko abu zai siyowa yaran nasa guda uku yake siyo komai Asiya, mufida, inteesar.haka 'bangaren mummy komai tar take masu ko Kaya ne dinki ma iri daya ne take masu,haka takalma da d'an kunne,kayan kwalliya gyale ne kawai idan zata siya masu sai ta siyawa Inteesar Hijab kasancewar Bata saka gyale ko ansiye Mata zata a jiye shi ne,Abban Inteesar da Ummata ma takanas sukazo yiwa Dady da Mummy godiyar d'awainiyar da suke da 'yar su, Mummy tana son kowane lokaci Inteesar tana gidan ta,
Wata rana Da yamma Inteesar tana zaune a tsakiyar gidan su tana wanke-wanke.Mufidaa tayi sallama ta shigo da far'ar ta ta k'araso cikin Jin dadi take cewa Inteesar Babban yayan mu ya dawo kizo muje ki gansa,dama baki taba ganin sa ba.
Cikin Jin dadi tace,
"Haba da gaske kikeyi"?
Murmushi Jin dadi Mufida tayi kafin tayi magana ne umma ta fito daga d'aki tana kallon Mufida ta ce,
"Mufida kece a gidan namu?"
Durk'usawa tayi ta gaida Umma
"Ina yini Umma?"
"Lapiya qalau ya mutanen gidan?"
Cikin yanayin da take ciki na jindadi tace
"Umma Yayan mu ya dawo shine nazo Kiran Inteesar tazo su gaisa."
"Masha Allahwanda yake can kasar turai ko?"
Cewar umma
"Eh umma"
Da-dai lokacin Inteesar ta k'arasa gama wanke-wanke ta saka hijab Mufida taja hannun ta suka tafi tana sallamar Umma.
"Umma sai na dawo"
"To ki gaishe su."
Koda suka karasa gidan a falon ba kowa kowa yayi d'aki,dama sun Dad'e suna fira kasancewar da ya iso Mufida na barci bata sani ba ta farka ne ta gansa take sanar da aminiyar ta.
Kai tsaye part din sa suka nufa baya falo, knocking Mufida sukayi yabada izinin shiga.da sallama suka shiga ya na magana da wani a waya da alama abokin sa ne,yana tozali da Inteesar gabansa ya fad'i ya mik'e da sauri tare da cire wayar a kunnen sa,kallon mamaki yake mata,don tabbas itace yarinyar da yake gani cikin mafarkinsa ,nuna ta yayi da yatsa tare da furta
" kee!"
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DON K'ARIN BAYANI*
09065327995
Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashiubuta ta Shi dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to ku gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Page0️⃣7️⃣
Nuna ta yayi da yatsa tare da furta
"Kee!"
Inteesar cikin tsananin mamaki take kallon shi ganin yadda yake Mata kallon mamaki,alhalin ita bata ta'ba ganin sa ba,
Acikin zuciyar ta kuwa ta ce,
"Anya kuwa wannan mutumim Yana da hankali?duk yabi ya rikice har da tambayar ta Wai ni ce?alhalin ban taba ganin sa ba."
Muryar mufida ce ta katsae ta Jin tana cewa,
"Yaya lapiya kuwa?"
K'ok'arin dai daita nutsuwar sa yayi don kada su fahimci wani abu game dashi,sannan ya ce,
"Babu komai"
Murmushi tayi tare da kamo hannun Inteesar din ta ce,
"Yaya wannan itace Inteesar d'in da nake baka labari"
Kai ya gyad'a ba tare da ya kalle su ba.inteesar ce tadan durk'usa cikin girmamawa ta ce,
"Ina yini?"
"Lafiya"
Ya amsa Mata a gajerce ba tare da ya kalle ta ba,ta Kara cewa
"kadawo lafiya?"
Bai kalle ta ba,balle tasa ran zai amsa kallon Mufida yayi tare da yamutse fuska yace,
"Pls kud'an fita dan ina son na Dan huta."
Kwa'be Fuska ta tare da cewa
"Yaya Wai yau nice kake Kora daga d'akin ka abunda baka taba yi maniba?"
Jinjina Kai ta yi
" Koda kanajin barci sai dai idan nice naga alamun haka na fita? Kuma gani tare da k'awa ta sannan ko gaisuwar kirki baku..."
Dakatar da ita yayi ta hanyar daga Mata hannu,sanan ya nuna Mata kofar fita yace "please"
Rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka,taja hannun Inteesar suka fice daga dak'in,suna fita ya samu yayi ajiyar zuciya,don har ga Allah baiji dad'in abunda da yawa k'anwar tasu ba,amma ba yadda yadda iya dole yayi hakan ki zai samu sassauci, domin tunda ya kalli Inteesar gabansa yake ta lugude don ya girgiza da ganin ta.fitar nata shine samun sau'kin sa.
Bangaren su Mufida kuwa suna barin d'akin sa Kai tsaye d'akin Mummy suka nufa, Inteesar ce kadai tayi sallama Mufida kuwa idanun ta tab da kwallah suke,kadan take jiran tayi kuka, Mummy dake shirya kayan da mai masu wanki da guga ya kawo ne take shiya su a cikin wardrobe din kayana ta.
Juyowa tayi ta kalle su ganin su cikin wani yanayin yasa ta dakatar da abunda takeyi ta karaso bakin gadon ta janyo hannayen su ta zauna dasu bakin gadon tare da cewa,
"ku lapiya kuwa?me ya faru?"
Cikin shagwaba ta da muryar kuka take cewa,
"Wai daga mun shiga mu gaida Yaya Inteesar da bata San shi ba sai a photo nace muje ta gaishe sa,shine kawai harda korar mu ko gaisuwar ta bai amsa ba."
Ido Mummy ta zuba masu tare da yin tunanin ko me yasa yayi masu hakan?
"Kunga wata K'ila akwai abunda ke damun sa ne,kuma kun cika shi da suruta.ke mufida ai kinsan baya son hayaniya,wata Kila shiyasa ya Kore ku,Amma kada hakan ya dame ku kuyi hak'uri kunji?"
Ta karasa maganar tana shafar gefen fuskokin su
Mufida tayi saurin cewa
"Wlh ba hayaniyar da muka damesa dashi,ko gaisuwar kirki basuyi ba.
To naji ku saki ranku sai dai idan akwai abunda yake damun sa.cewar mummy kenan."
Mik'ewa tayi ta nufi d'akin sa,Murda handle din kofar tayi tare da yin sallama.zaune yake bakin gadon say yayi tagumi.jin muryar Mummy ce yasa ya amsa sallamar tare da amsa sallamar da tayi masa.
Murmushi ya k'ak'alo ganin mummy ta zuba masa idanu Tana karantar yanayin sa.
"Mummy sannu da shigowa"
"Yauwa "
tace tare da karasawa ta zauna saman side drawer.
"Son lapiyar ka kuwa ko akwai abunda yake damun ka ne ban sani ba?"
Murmushi ya k'ak'alo wanda iya fatar bakin sa ta tsaya,bata Kai zuci ba.
"Lapiya qalau Mummy kawai dai nagaji ne"
Kai ta girgiza tare da cewa,
"Akwai mana son,nifa mahaifiyar ka ce idan ma kana cikin damuwa ka sanar dani mana,kada ka boye Mani."
"Kada ki damu Mummy gajiya ce,I will be fine."
Mikewa tayi tace
"To shikenan tunda haka kace,amma baikamta ko Kori kannen ka ba,da suka shigo gaishe ka,musamman ma Inteesar da karon faroko kenan tasan ka,tazo kaishe ka sannan zaka kure su?"
Jinjina Kai yayi alamun gamsuwa
"To Mummy insha Allah hakan bazata sake faruwa ba,daga ta fita tabar masa dakin."
Haka rayuwa tayi ta tafiya yayin da Mummy da Dady da kuma mufida ke Kara k'aunar Inteesar,don har mommy taso a ce Inteesar ta dawo gidanta da zama gaba d'aya,amma ganin cewa ita kad'ai iyayen ta suka haifa kuma tana taimaka wa mahaifiyarta da aikace-aikacen gida gida yasa ta ha'kura.kullun Inteesar idan ta idar da sallar asuba tayi azkar Bata kuma kwanciya zata Fara aikace-aikacen gida,shara wanke kwanuka d'ora masu abun abun da zasuyi kalaci dashi wankin bandaki gyaran d'akunan gidan duk itace.kuma kafin karfe bakwai ta gama komai tayi Shirin zuwa school bayan ta gaida iyayen ta ta sallame su.kai tsaye zata nufi hanyar gidan su Mufida kullu taje zata 9tarar da ma'aikatan gidan nata aiki tunda kan Mai gadi da Mai bawa fulawa ruwa da masu sharar harabar gidan da masu goge windows kowa na aiki harda Mai wankin mota.sai da ta gaishe su sannan ta nufi cikin gidan,nan ta tarar da Mai aikin su tana goge-goge Mummy kuwa kullum tana kitchen Tana hada breakfast din mutanen gidan.Yayin da jummai ke girka na ma'aikatan gidan.don Dady bayason Abincin masu aiki.kullun sai Inteesar sai ta taya mummy karasa hada breakfast tajira mufida tayi breakfast sannan su tafi.
A bangaren Muhdeen kuwa sai K'ara tsanr yarinyar yakeyi a cikin zuciyar sa.har ita kanta Inteesar din ta fahimci hakan.cewa baya kaunar ta Wanda ita kanta ta rasa dalilin da yasa haka.don ko had a ido sukayi zai galla Mata harara ko ta gaishe sa sai dai idan a gaban mutanen gidan ne yake amsawa idan basu nan kuwa ki ta gaishe say sai yayi tsaki ko ya harare ta
Kwanci tashi asarar Mai rai.har muhdeen ya kammala karatun sa na likitanci ya dawo Nigeria inda Dady ya gina masa Babban Asibiti a nan cikin garin Minna.inda Jabir wato d'an yayan Dady zasu dinga tafiyar da asibitin a tare,don Shima abunda ya karanta kenan.
Bayan an zuba kayan aiki an d'auki kwararrun ma'aikata sun fara aiki ba dadewa ne Muhdeen Ya tafi kasar Egypt bikin Abokin saWanda sukayi karatu a tare.
*CIGABA LABARIN*
Washe gari Monday ne Muhdeen ya shirya da sassafe zai tafi asibiti,kai tsaye ya nufi kitchen,don a tunanin sa Mummy na cikin kitchen din.ya nufi kofar kitchen d'in Yana cewa
"Muummy da wuri yau zan fita a hada m"ani breakfast di..."
Kasa karasa maganar yayi sakamokon tozali da yayi da Inteesar dake kokarin zuba ruwan shayi a cikin flask.bayan ta gama soya dankalin da kwai.
Jin muryar muhdeen yasa ta juyo ta kalle shi tare da sunkuyar da kanta kasa tace
"Barka da safiya Yaya"
Tsuki yayi tare da niyar barin kitchen din
Dai-dai lokacin Mummy ta shigo,ganin ta yasa ya k'ak'aro murmushn dole ya kalli Inteesar din cikin sakin fuska yace
"Yauwa k'anwata kin tashi lapiya ko?"
Daga kai tayi ta kalle shi ciki mamaki,ganin Mummy ne ta shigo kitchen din yasa tasan dalilin amsa gaisuwar ta da yayi.
Don dama mummy tace ya dauke ta kamar Asiya da Mufida itama kanwar sa ce.murmushi mummy tayi tace
"Yau da wuri zaka tafi asibitin kenan"
Kai ya gyada tare da cewa
"Eh kinsan sati daya kenan banje ba saboda tadiyar da nayi,Ga aiki sunyiwa Jabeer yawa"
Kai Mummy ta jinjina tare da cewa
Hakane, Inteesar had'a masa breakfast ya tafi
Da sauri ya girgiza Kai tare da cewa
"No ta barshi kawai sauri nake idan naje can zanyi."
Ya fita daga kitchen din ransa a bace,Don yayi niyyar yin breakfast a gida ganin cewa Inteesar zata hada breakfast yasa ya fasa haka yayi masu sallama fita.
Mufida ce ta fito daga dakin ta cikin hanzari ta shiga kitchen din,ta d'ebi ruwan tea kawai sai slice bread da ta dauki guda biyu.a kichen din ta zauna tayi breakfast din suka tafi suna sallamar mummy don'ton dama yanzun already sunyi late.
Bangaren Muhdeen kuwa a office yasa aka kawo masa coffee,Yana zaune akan kujerar office dinsa ga tarin file a gaban say Yana shan coffee din a hankali wayar sa ce dake ajiye akan table din gaban sa ta Soma ruri duban yayi tare da murmushi Don yasan ita ce ke Kiran sa dai-dai wannan lokcin,murmushi yayi acikin zuciyar sa ya furta my Sumy daga wayar yayi ba tare da ya furta komai ba.
*LONDON*
Tana kwance saman gadon ta Jin yayi picking tace
"Morning sweet"
Daga can bangaren sa
"Kina lapiya"?
Lumshe idanu tayi sakamakon Jin muryar sa,sannan tace
"Lapiya qalau wlh kana inane yanxun?"
"Ina office ne,yasu Mum da Dad?"
Ya tambaye ta
Amsa masa tayi tare da cewa
" suna lapiya yanxun haka ma sune suka sa na Kira ka akan maganar da mukayi dakai kan cewa ka turo magabantan ka ayi maganar auren mu
Cikin Jin dadi yace Are you serious?Kai Amma naji dadin Jin hakan daga gare ki. Kinyimun albishir mai dadi da safen nan.ina komawa gida zan sanar da su Dady tunda dad dinki ya amince."
Murmushi tayi kafin tace,
"Kaima kasan duk abunda nace Ina so shi akaeyi mani,ban taba cewa Ina son Abu Mum da Dad suka ki mincewa ba Koda basa son Abu zasuyi mani don su faranta mani Rai."
Jinjina Kai yayi kafin yace
"Ai ke 'yar gata ce"
Knocking k'ofar akayi sannan yace mata
" Kinga I will call you when I'm done."
Bata fuska tayi tace,
"Oh Allah yanxun ba zaka iya Bari mucigaba da hirar mu cikin jindadi ba."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace,
"Karki damu zamuyi magana,"
Bai jira cewae ta ba ya katse kiran,sannan ya kalli k'ofar da ake knocking ya bada izinin shigowa.
Jabeer ne ya shigo tare da Mika masa hannu sukayi musabaha ya zauna kan kujerar dake facing din muhdeen.
Jabeer ne ya ce
"Wato ka shigo ko ka sanar dani ko? dan banda nurse Hauwa da take sanar sani."
Murmushi yayi tare da cewa
"Wallahi nabar gida banyi breakfast ba,Ina shigowa nasa aka kawo mani coffee Ina jiran idan na kammala na Kira ka ne sai kuma na samu labari mai dadi."
Ya Karasa maganar Yana sakin murmushi,Shima jabeer dtin yayi murmushi tare da cewa
"To Masha Allah wani abun farin ciki muka samu da safen nan?"
Fara'ar sa ce ta karu yacigaba da cewa
"Sumy ce take sanar Dani cewar mahaifin ta yace na turo magabata na a sa Mana ranar aure"
Take fara'ar dake Kan fuskar jabeer ya dauke,ya shiga damuwa nan take.domin yasan sumy sosai tunda dukkan su tare sukayi karatu a America tare,Sam bata da tarbiyya bata San darajar dan aadam ba.yadda kasan ba 'yar musulma ba idan kayi la'akari da shigar ta da dabi'un ta sallah ma Bata Dame ta ba,sunan ta kawai zakaji kasan cewa musulma ce.
Ido muhdeen ya zuba masa Yana karantar yanayin sa.kafinya ce
"Yadai bro lapiya?"
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wanna kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
Page0️⃣8️⃣
Ajiyar zuciya Jabeer yayi tare da kallon Muhdeen cikin kwantar damurya ya ce,
"Amma da zaka bi shawara ta daka rabu da Sumy baby domin bata dace da Kai ba"
Wani irin kallo Muhdeen ya watsawa jabeer tare da cewa
"Meye dalilin ka?"
Jinjina Kai jabeer yayi tare da cewa,
"Dalilai da yawa ma kuwa,
Na farko, yarinyar Nan bata da kamun Kai
Na biyu,Bata da tarbiyya
Na uku yarinyar bata San darajar d'an Adam
Shigar ta da dabi'un ta sunsha ban-ban da ta 'ya'ya masu mutun..."
Muhdeen ya daga masa hannu ta alamun dakatarwa
cikin bacin rai ya nuna masa hanyar kofa tare da cewa,
"Fice mun da ga office"
Kallon mamaki jabeer yayi masa yace
"Dan na fadi gaskiya shine kake korata?"
Cikin daure fuska muhdeen ya furta
"Dama na Dad'e da sanin baka k'auna ta da sSumayya,bansan me tayi maka da yasa ka tsane ta na lura da hakan tunda dadewa.kuma Bari kaji aure na da sumayya babu fashi baka Isa ka hanani auren ta ba."
Gajeren murmushi Jabeer yayi tare da cewa,
"To meye zaisa na tsane ta hakanan kawai?i ba ita na tsana ba halayyar ta ne kawai na tsana."
Tsaki muhdeen yayi
"Yaushe ka zauna da ita da har zaka fahimci halayyar ta?don kunyi karatu kasa daya makaranta d'aya shine har zaka fahimci halayyar ta?"
Cikin takaici jabeer yace,
"Ai ba sai ka zauna da mutum ba,kamannin mutum da halayyar sa da ayyukan da yake aikatawa ma yakan say ka fahimce shi ko wane irin mutumi ne."
Cikin Dan d'aga murya ya ce
"To koma dai manene abunda na sani kawai shine Tana masifar sona.kuma bazata aikata abunda zai 'bata mani rai ba."
Jabeer na ya daga kafad'a alamun bandamu ba,sannan ya furta
"Shikenan tunda haka kace,sai dai ina baka shawar ka nemawa 'ya'yan ka uwa tagari wacce zakayi alfahari da it...."
Cikin daga tsawa yace
"I said out"
Kai tsaye ya nufi kofar fita ya fice,yana mamakin abokin nasa da ya makance akan soyayyar Sumayya,tunsa yake da muhdeen bai taba d'aga masa murya ba sai akan sumayya.Bashi da Babban abokin da wuce Muhdeen ko shawara ya bashi yana karba amma yau Karan farko ya 'bata dashi akan mace.haka ya nufi office din sa ransa ba dad'i.
Shima muhdeen aikin da baiyi ba kenan,haka ya rufe office din nasa yabar jabeer da tulun aiki.
Ya nufi parking space ya tada motar say yabar asibitin.
Kai tsaye gida ya nufa. ya tarar da Dady a falo yayin da Mummy ta tsiyaya masa ruwa a kofi ta mik'a masa,da sallama ya Isa da mamaki suke kallon sa ganin lokacin da ya dawo ba lokacin dawowar sa ba.
Amsa sallamar sukayi yayin da ya karaso zauna a gaban su bisa center carpet.
tare da cewa,
"Barka da warhaka Dady."
Kallonsa Dady yayi bayan ya ajiye Glass cup din da yasha ruwa a saman center table d'in dake gaban sa.
"Yauwa barka dai Muhammad,lapiya Naga ka dawo dai-dai wannan lokacin?"
Sunkuyar da Kai yayi tare da Sosa keya
"Eh lapiya Dady,dama am... "
Sai yayi shiru ya kasa