Header Ads
Showing 114001 words to 117000 words out of 149432 words

Chapter 39 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1375

Ads at the middle of Article

wani tsoronsa ne ya shige ta, ko kallonta baiyi ba har ya wuce ta zai nufi d'akinsa ya tsaya ba tare da ya kalle ta ba ya ce,

"Kada ki sake kwana mani a gida, ki tattara naki ya naki kibar mani gida na."

Daga nan ya shige d'akinsa, kuka ta saki tana cewa

"Dan Allah kayi hak'uri ka gafarce ni wallahi bazan sake ba, kayi mani alk'awari na zamu rayu har k'arshen rayuwarmu ba zamu rabu da juna ba, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba dan Allah kayi hak'uri, soyayyar da nake maka ne ya saka ni cikin wannan halin.

Bai saurare ta ba ya shigewarsa d'akinsa.

A guje ta ruga d'akinta wayarta ta d'auka tana kuka, lamabar Jumy ta kira bugu d'aya ta d'auka, tana d'auka Sumayya ta fashe da kuka ta fara magana

"Jumy na shiga uku, Muhdeen ya kore ni ya ce nabar masa gidansa."

Cikin mamaki ta ce,

"What! akan me ya kore ki?"

Cikin muryar kuka ta fara magana

"Jumy ya gano gaskiya cewa nayi yunk'urin kashe Inteesar."

"Me kika ce? ta yaya ya gano gaskiya? ko dai bata mutu bane?"

Jinjina kai tayi kamar tana ganinta ta ce

"Ina tunanin bata mutu ba, kuma ta sanar cewa nice nayi mata wannan aiki."

"To yanzun ina ita yarinyar take?"

"Nima ban sani ba, amma da alamar ya sani tunda har yasan nayi yunk'urin kashe ta, kinga ta sanar da wani kenan, Jumy wallahi jiya na d'and'ani k'amshin mutuwa, kwana na ne kawai a gaba."

"To yanzun da ya ce kibar masa gidansa Ina zaki je? London zaki koma?"

"Ba inda zanje Wallahi, bazan ta'ba rabuwa da shi ba, ni da shi takalmin kaza mutu ka raba."

"Kada fa yazo ya wulak'anta ki."

"A shirye nake da na fuskanci ko wane irin wulak'anci daga gare shi, amma bazan tabu da shi ba."

Ajiyar zuciya Jumy ta sauke ta ce

"Shikenan, Allah ya bada sa'a."

Daga nan ta katse kiran ."

Tana nan zaune har tsawon mintuna talatin, turo k'ofar yaayi ba tare da ya kalle ta ba ya ce,

"Kada na dawo gidan nan na tarar da ke, don wallahi zaki sha mamaki a waje na."

Daga nan ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi,. kuka tan saki, domin Alah ya sani ba zata iya rabuwa da, gaba d'ya hankalin ta yatashi.

Wayar ce ta k'ara d'auka tare da Kiran shila a waya, labarin abunda ya faru tabbata, sannan ta cigaba da cewa

"Wallahi bana son rabuwa da shi, ya zanyi ya hak'ura ya barni, so nake mu cigaba da zaman mu, meye mafita?

"Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da dogon tunani ta ce,

"Ina zuwa k'awa ta zan kira ki"

Katse kiran tayi ta nufi k'ofar d'akinta da taji ana knocking.

Acan gida kuwa tunda Gwaggo ta shiga d'akinta Inteesar ta bita a baya, Gwaggo na zama Inteesar ta fad'a jikinta tare da sakin kuka, cikin tashin hankali Gwaggo ta d'ago ta tana cewa

"Yar albarka me ya faru kuma kike kuka?"

Cikin kuka ta fara magana

"Gwaggo kada ki mayar dani"

Kada mu mayar da ke Ina?"

"Gidan Yaya"

Murmushi Gwaggo tayi tare da cewa

"Akan wannan shine kike kuka? to ki kwantar da hankalinki tunda baki so ba zaki koma ba."

Cikin kwantar da murya tayi magana

"To kiyi mani alk'awari"

Dariya Gwaggo ta sake yi sosai ta ce,.

"Nayi maki alk'awari sai dai idan kece kika nuna kina kina son cigaba da zama da shi, idan ba haka ba ki d'auka aurenku ya rabu."

Dariya tayi sosai tare da cewa

"Ni ba abunda zaisa nayi sha'awar komawa gidansa, daga shi har matarsa basu da imani, kashe ni zasuyi idan na cigaba da zama da su."

"Ba zasu kashe ki ba sai dai idan kwananki ne suka k'are."

"Gwaggo kenan haka zancenki yake, amma ni kad'ai nasan wahalar da nake sha a gidansa."

"Dalla matsa ki bani waje, kinsan da haka shine na je gidanku tsawon wata d'aya baki sanar da ni halin da kike ciki ba? "

"Gwaggo yadda yake nuna mani so da kulawa, da nace zan fad'a maki ba zaki yarda dani ba, saboda wayau ne da shi,yasan me yakeyi shiyasa ya ya dinga mani abubuwan da yake dan ki yarda da shi "

"Shikenan yanzundai ba inda zaki koma."

Cikin jindad'i ta jinjina kanta alamar gamsuwa da maganar Gwaggon .

Sumayya na zaune tana jiran Kiran wayar sha ta shigo wayarta, sai kuwa ga Kiran nan ya shigo, da saurinta ta d'aga tare da cewa

"Yauwa k'awa ta naji kince mafita d'aya ce zaisa na cigaba da zama da Muhdeen me ne ne?"

Ajiyar zuciya shila ta sauke tare da cewa

"Nasan ko na fad'a maki ba zaki amince kiyi ba, amma nasan hakan ne kawai mafitar da zaisa ku cigaba da mallakar juna, idan kuma baki amince kinyi abunda nasa ki ba to lallai ba ke ba Muhdeen yafi k'arfinki kina ji kina gani."

"Kinga kada kiyi shakka akan komai don ba abunda bazan iya aikawa ba akan na cigaba da mallakarsa."

*DAGA ALK'ALAMIN*✍️

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)

*Don neman k'arin bayani*

09065327995

Love you oll😘😍
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a

*INTEESAR*

Story & writing by✍️

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan, duk abu d'aya, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kin shiga indai baki comments zan fitar da ke ne.

*GARGA'DI*

Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.

*SANARWA*

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.

Page6️⃣5️⃣

"Kinga kada kiyi shakka akan komai, don ba abunda bazan iya aikatawa ba akan na cigaba da mallakarsa."

'Dan jim Shila tayi kafin ta ce,

"Ki shirya ki tafi gidan Dadynsa da Mummynsa ki nuna nadamarki, sannan ki rok'e su gafara kin tuba ba zaki sake aikata abunda kika aikata ba, nasan suna da mutunci da karamci, ba zasu banzatar da ke ba, musamman idan suka ga abunda d'ansu ya aikata maki, nasan zasu kar'be ki hakan zaisa suyi masa maga..."

Tun kafin takai k'arshen maganar da zata yi Sumayya ta katse ta tare da cewa

"Bazan iya ba."

Sakin baki Shila tayi cike da mamaki ta ce,

"Lallai kuwa baki shirya zama da mijinki bane, kuma baki da wani za'bi da ya wuce ki nemi wad'anda zasuyi masa magana ya hak'ura, kinga sai ku cigaba da zama tare da shi, amma idan ba haka ba yadda ya zuciya da ke bazai saurare ki ba."

Nidai ki bani wata shawarar amma ba wannan ba, dan gaskiya bazan iya zuwa gidansu na sanar da su ba, dan ba k'aunata suke ba, musamman wannan kakarsa ta tsane ni sosai wallahi, dan haka nima na tsane ta."

Dariya shila tayi tare cewa

"Idan 'bera na da sata daddawa ma tana da wari, haka nan kawai ba yadda za'ayi dangin mijinki su tsane ki, sai dai idan halinki ne zai sa su tsane ki, nasan halinki fa kuma dangin mijinki suna da mutunci haka nan kawai ba zasu tsane ki ba, idan kika girmama su kika d'auke su iyaye suma zasu d'auke ki 'yarsu."

"Kingama? to shawarki bata yi aiki ba ki kawo wata."

"To kije ki nemi abokinsa Wanda kika san yana d'aukar shawaransa ki sanar da shi, kuma ki rok'e sa ya taya ki bashi hak'uri ya yafe maki."

Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawar shila ta ce,

"Yanzun kikayi magana mai kyau, zan nemi abokinsa Jabeer duk da shima ba wai jini na ya had'u da shi bane, amma zanyi amfani da shi wajen cikar buri na."

Sallama sukayi ta katse kiran.

Number wayar Jabeer ta lalubo zata danna masa kira, lokacin ya fito zai shiga motarsa ya fita kenan ya ji wayarsa na ruri, ciro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba, mamaki ne ya kama shi ganin mai kiransa a bayyane ya furta

"Sumayya?"

Zuba ma wayar ido yayi yana mamakin ya akayi ta kira sa, har wayar ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kiransa a ya d'aga, yana d'agawa yaji muryarta ta fashe da kuka, gabansa ne ya fad'i dan shi a tunaninsa wani abun ne ya samu Muhdeen, cikin tashin hankali ya ce,

"Subhanallahi Sumayya me ke faruwa? wani abu ne ya samu Muhdeen?"

Kai ta girgiza kamar yana ganinta ba tare da tayi magana ba

"Me ke faruwa ki sanar da ni mana."

"Jabeer kana ina ne?"

"Ina gida yanzun nake shirin zuwa Asibiti, akwai matsala ne?"

"Dan Allah ka jira ni gani nan zuwa."

"Okay ki hanzarta dan ina sauri."

Daga nan ya katse kiran ya koma cikin gidan zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, Maryam da ke zaune a dinning room tana breakfast, ta kalle shi ta ce,

"Kayi mantuwa ne?"

"A'a Sumayya ce ta kira ni wai tana son ganina, shine na dawo na jira ta."

"Lafiya take son ganinka?"

"Yadda naji tana kuka kam ba lafiya, akwai wani abun da ya faru."

Ta'be baki Maryam tayi tare da cewa

"Allah ya kyauta"

"Ameen ya rabbi"

Bayan ta kammala ta dawo ta zauna kusa da shi, suna d'an ta'ba hira.

Bayan kimanin mintuna talatin aka turo k'ofara aka shigo da sallama, dukkansu a zabure suka mik'e suka Zuba mata ido cikin mamaki, ganin yadda fuskarta a kumbure, ga goshinta ya ffashe ya kumbura, ga jini da ya bushe a goshin nata,a hankali Jabeer ya furta sunanta.

"Sumayya?"

Maryam kam da ba don da Jabeer ya ambaci sunanta ba ba zata gane ta ba, domin Muhdeen gaba d'aya ya sauya mata kamanni, kamar ba Sumayya 'yar k'walisa ba, hawaye ne kawai ke tsiyaya daga idanunta k'arasowa tayi ta zauna kan kujera ta fashe da kuka.

Jabeer ne ya bud'e baki yayi magana ya ce,

"Sumayya ya naganki haka me ya same ki? gashi ma ko treatment ba'a maki ba, Muhdeen baya nan ne da ya barki haka ba tare da ya maki treatment ba?"

Sautin kukanta ta k'ara tana cewa

"Shine da kansa yayi mani haka."

Kallon Juna suka yi Jabeer da matarsa ya ce

"Ban gane shi yayi maki haka ba ta yaya hakan ta faru?"

Sunkuyar da kanta k'asa tayi, ta kasa magana, hakan yasa Jabeer ya gane cewa lallai Muhdeen ya gano abunda Sumayya ta aikata, dan haka ya ce,

"Kan abunda kika aikatawa Inteesar ne yayi maki haka?"

A hankali ta gyad'a kai almar eh

Tambayar kansa yayi idan har Muhdeen ya iya aikatawa Sumayya haka akan Inteesar, to tabbas yana son Inteesar, duba da yadda ya sauyawa Sumayya kamanni dan tayi yunk'urin kashe Inteesar, Sumayya da yake masifar sonta zai iya 'batawa da kowa kanta amma yau shine yayi mata mugun duka haka? kuma akan yarinyar da ya tsana a rayuwarsa yau ya illata masoyiyarsa akanta? me hakan ke nufi? Shin yanzun ya koma yana son Inteesar ne ko meye?.

Haka ya dinga sak'e-sak'e a zuciyarsa sanin ba mai amsa ne yasa ya kalli Sumayya tare da cewa

"Ina zuwa"

Tashi yayi ya nufi d'akinsa, ba jimawa ya fito da aid box yazo ya fara treatment nata, sai kuka take tana jin zafin goshinta, sai sannu suke jera mata gaskiya sun tausaya mata, Jabeer yayi mamaki dan bai ta'ba tunanin Muhdeen zaiyiwa Sumayya makamancin abunda yayi mata ba, bayan ya gama mata ne yayi mata allura, sannan ya kalle ta ya ce,

"Me ke tafe da ke"

"Ya kore ni ne ya ce nabar masa gidansa"

Jinjina kai Jabeer yayi tare da cewa

"Yayi dai-dai ko nine a matsayin da yake abunda zanyi kenan, na ga ma k'ok'ari da bai had'a maki da saki."

Da sauri ta d'aga idanunta ta kalli Jabeer jin abunda yake fad'a, ranta ya 'baci sosai da hakan, kamar ta maida masa martanin maganarsa amma sai ta gagara, don nema tazo yi kuma mai nema baya fushi, dan haka ta kwantar da murya tare da marairaice fuska ta ce,

"Dan Allah kada ka fad'i haka, wallahi nayi nadama Kan abuda na aikata, hakan ba zata sake faruwa ba, ina son ka taya ni rok'onsa da ya yafe mani ya barni mu cigaba da zamanmu, hakan ba zata sake faruwa ba."

Girgiza kai Jabeer yayi tare da cewa

"Sumayya wannan tuba da kika yi tuban muzuru ne, na tabbata sai kin sake aikatawa, sai dai idan ba'a 'bata maki rai ba, amma matuk'ar ranki ya 'baci to ba abunda ba zaki iya aikatawa ba, domin kuwa wannan d'abi'arki ce, shiyasa tun farkon auren Inteesar ba yadda banyi ba ya raba maku gida bai saurare ni ba."

Zamowa tayi daga Kan kujera ta durk'usa akan akan k'afarta ta fashe da kuka ta fara magana.

"Jabeer ka ji tausayi na mana wallahi idan Muhdeen bai yarda ya cigaba da zama da ni ba wallahi zan iya rasa rayuwa ta, shine farin ciki na walalhi zan kiyaye duk abunda zai kawo mana sa'bani, haka ta dinga kuka tana rok'onsa da kuka tare da alk'awari daban-daban har Jabeer ya amince zai saka baki akan maganar tunda tayi nadama, har ya amince zai kaita sukayi sallama da Maryam sannan suka fito suka nufi gidan Muhdeen.

Koda suka k'arasa mai gadin ya sanar da su baya ciki, wayarsa ya ciro ya lalubo number Muhdeen ya danna masa kira, jin ya d'aga ne yasa ya ce,

"Kana ina ne?"

Muhdeen dake driving ya ce,

"Sai yau ka tuna da ni?"

"Dama mancewa da kai aka ce nayi?"

"To yanzun dai mene ne?"

"Ina gidanka ne yanzun"

"Ni kuma ina hanya zanje gidan Dady ne, kazo gidan sai mu had'u ko?"

"A'a kadai zo nan dan maganar ba ta can bane."

"Me ke faruwa."

"Idan kazo zaka ji koma mene ne"

"Daga nan ya katse kiran ya maida wayarsa cikin aljihu, ya kalli Sumayya ya ce,

"Yana zuwa mu k'arasa ciki kafin ya zo."

Tana gaba yana binta baya suka wace zuwa falo.

*KUYI HAK'URI DA WANNAN*

*DAGA ALK'ALAMIN*✍️

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)

*DON K'ARIN BAYANI*

09965327995

Love you oll😍😘

Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a

*INTEESAR*

Story & writing by✍️

Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

Idan har kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan, duk abu d'aya, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kin shiga indai baki comments zan fitar da ke ne.

*GARGA'DI*

Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.

*SANARWA*

Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.

Page6️⃣5️⃣

"Kinga kada kiyi shakka akan komai, don ba abunda bazan iya aikatawa ba akan na cigaba da mallakarsa."

'Dan jim Shila tayi kafin ta ce,

"Ki shirya ki tafi gidan Dadynsa da Mummynsa ki nuna nadamarki, sannan ki rok'e su gafara kin tuba ba zaki sake aikata abunda kika aikata ba, nasan suna da mutunci da karamci, ba zasu banzatar da ke ba, musamman idan suka ga abunda d'ansu ya aikata maki, nasan zasu kar'be ki hakan zaisa suyi masa maga..."

Tun kafin takai k'arshen maganar da zata yi Sumayya ta katse ta tare da cewa

"Bazan iya ba."

Sakin baki Shila tayi cike da mamaki ta ce,

"Lallai kuwa baki shirya zama da mijinki bane, kuma baki da wani za'bi da ya wuce ki nemi wad'anda zasuyi masa magana ya hak'ura, kinga sai ku cigaba da zama tare da shi, amma idan ba haka ba yadda ya zuciya da ke bazai saurare ki ba."

Nidai ki bani wata shawarar amma ba wannan ba, dan gaskiya bazan iya zuwa gidansu na sanar da su ba, dan ba k'aunata suke ba, musamman wannan kakarsa ta tsane ni sosai wallahi, dan haka nima na tsane ta."

Dariya shila tayi tare cewa

"Idan 'bera na da sata daddawa ma tana da wari, haka nan kawai ba yadda za'ayi dangin mijinki su tsane ki, sai dai idan halinki ne zai sa su tsane ki, nasan halinki fa kuma dangin mijinki suna da mutunci haka nan kawai ba zasu tsane ki ba, idan kika girmama su kika d'auke su iyaye suma zasu d'auke ki 'yarsu."

"Kingama? to shawarki bata yi aiki ba ki kawo wata."

"To kije ki nemi abokinsa Wanda kika san yana d'aukar shawaransa ki sanar da shi, kuma ki rok'e sa ya taya ki bashi hak'uri ya yafe maki."

Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawar shila ta ce,

"Yanzun kikayi magana mai kyau, zan nemi abokinsa Jabeer duk da shima ba wai jini na ya had'u da shi bane, amma zanyi amfani da shi wajen cikar buri na."

Sallama sukayi ta katse kiran.

Number wayar Jabeer ta lalubo zata danna masa kira, lokacin ya fito zai shiga motarsa ya fita kenan ya ji wayarsa na ruri, ciro wayar yayi daga cikin aljihunsa ya duba, mamaki ne ya kama shi ganin mai kiransa a bayyane ya furta

"Sumayya?"

Zuba ma wayar ido yayi yana mamakin ya akayi ta kira sa, har wayar ta katse bai d'aga ba sai da ta sake kiransa a ya d'aga, yana d'agawa yaji muryarta ta fashe da kuka, gabansa ne ya fad'i dan shi a tunaninsa wani abun ne ya samu Muhdeen, cikin tashin hankali ya ce,

"Subhanallahi Sumayya me ke faruwa? wani abu ne ya samu Muhdeen?"

Kai ta girgiza kamar yana ganinta ba tare da tayi magana ba

"Me ke faruwa ki sanar da ni mana."

"Jabeer kana ina ne?"

"Ina gida yanzun nake shirin zuwa Asibiti, akwai matsala ne?"

"Dan Allah ka jira ni gani nan zuwa."

"Okay ki hanzarta dan ina sauri."

Daga nan ya katse kiran ya koma cikin gidan zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, Maryam da ke zaune a dinning room tana breakfast, ta kalle shi ta ce,

"Kayi mantuwa ne?"

"A'a Sumayya ce ta kira ni wai tana son ganina, shine na dawo na jira ta."

"Lafiya take son ganinka?"

"Yadda naji tana kuka kam ba lafiya, akwai wani abun da ya faru."

Ta'be baki Maryam tayi tare da cewa

"Allah ya kyauta"

"Ameen ya rabbi"

Bayan ta kammala ta dawo ta zauna kusa da shi, suna d'an ta'ba hira.

Bayan kimanin mintuna talatin aka turo k'ofara aka shigo da sallama, dukkansu a zabure suka mik'e suka Zuba mata ido cikin mamaki, ganin yadda fuskarta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads