Header Ads
Showing 132001 words to 135000 words out of 149432 words

Chapter 45 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1394

Ads at the middle of Article

zo dubawa Asibiti?"


"Mijina"


Da sauri ya kalle ta tare da yin murmushi ya ce,


"Mijinki fa kika ce."


"Eh Mallam haka na ce,"


"Masha Allah na taya ki murnar auren da kikayi Allah ya sanya alkhairi."


Murmushin kawai tayi tare da cewa


"Nagode Mallam bari na ƙarasa, idan Maryam ta farka a isar mata da saƙon gaisuwa ta."


"Okay zata ji, muje na gaida mijin naki da jiki."


Zatayi magana kenan sai ta hango shi tsaye a ya jingina da bango ya zuba mata ido, sai da gabanta ya daɗi ganin irin kallon da yake mata fuskar nan tasa a murtuƙe ba sassauci a tattare da shi.


"Gashi can ma ya fito"


Mallam Auwal ya ɗaga kansa yana kallon inda take kallo, ganin Muhdeen yayi tsaye kansa an naɗe masa da bandeji idanunsa na kansu.


"Amma mijin naki accident yayi ko?"


Kai ta ta gyaɗa masa kawai, ƙarasowa sukayi gaban Muhdeen fuskar Mallam Auwal ɗauke da murmushi ya miƙawa Muhdeen hannu tare da cewa


"Assalamu alaikum"


Tsayawa Muhdeen yayi yana kallonsa kafin ya miƙa masa hannu fuskarsa a tamke, ciki ciki ya amsa masa sallamar, idan ba kin kalli bakinsa ba ba zaki san ya amsa sallamar ba, Mallam Auwal ya cigaba da cewa


"Ya jiki?"


Kai kawai ya ɗaga ba tare da yayi magana ba, Mallam Auwal ya sake cewa


"Allah ya ƙara lafiya ya kiyaye gaba."


Nan ma kai kawai ya ɗaga masa, ganin hakan yasa Mallam Auwal tunanin ko Muhdeen baya magana ne dan haka ya ce,


"Allah sarki baya magana ne amma yana ji."


Ita dai Inteesar shiru tayi bata ce komai ba, har Mallam Auwal yayi masu sallama ya tafi, bayan tafiyarsa da ne ya kalli Inteesar tare da cewa


"Waye wannan meye alaƙarki da shi?"


"Malami ne a school namu."


"To yanzun me ye haɗinki da shi kuma waye ya ce ki fita ballantana har ya ganki kuma daga ina kuke?"


Haka ya jera mata tambayoyi kallonsa tayi tare da cewa


"To wace tambaya zan amsa maka?"


"Dukansu zaki amsa mani."


"Maganar cewa meye haɗina da shi bani da shi bani da wata haɗu da shi, face a matsayinsa na musulmi ɗan uwa na kuma malamin da ya karantar dani."


Kallonsa tayi cikin ido sannan ta cigaba da cewa


"Maganar daga inda muke kuma ya ganni zaune ina hutawa shine yayi mani sallama, bayan mun gaisa ne ya sanar da ni cewa akwai wata classmate ɗina ce ba lafiya, shine na bishi dan na gaishe ta."


Saura tamabarka ɗaya na cewa me yasa n fita? to zaman me zanyi bayan kana buƙatar sirri kai da matarka shiyasa na fita tunda ku baku ji kunya ta ba, ai ni naji kunya na fita na baku waje, dan na lura kunya baya kuka bashi ba gaba ba."


Mamanki ne ya kama shi yadda ta tsaya tana gaya masa magana, ba tare da shakkarasa ba kamar yadda take yi wasu lokutan, kuma maganar da yadda take yinsa zaka gane cewa har da kishi ne,don cikin jin haushinsa take maganar.






*Daga alk'alamin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




*DON NEMAN ƘARIN BAYANI*


09065327995




Love you oll😍😘


Comments &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a




*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






Idan har kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, dan ko kinshiga idan baki comments zan fitar dake ne.




*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page7️⃣3️⃣


Mamaki ne ya kama shi yadda ta tsaya tana gaya masa magana, ba tare da shakkarasa ba kamar yadda take yi wasu lokutan, kuma maganar da yadda take yinsa zaka gane cewa har da kishi ne, don cikin jin haushi take maganar.


"Okay saboda haka ne yasa kika fita haka kike mani terere da jikinki? kalli kayan da kika saka yadda suka kama jikinki yaushe kika zama haka, ke da kina buduwa ma kullum cikin hijabi kike, sai yanzun da kina matar aure da yakamata ace kin ƙara killace jikinki shine kika fito haka ko?sai wannna mayafin wanda yake shara-shara da ajiye shima kawai kika yi kika fito haka nan, dan biada amfani."


Jabeer ne da ya ƙara so wajen ya ce,


"To Sarkin kishi."


Girgiza kai yayi tare da nuna jama'ar da ke harabar wajen da masu kai kawo ya ce,


"Jabeer ka duba ka gani cikin jama'ar da ke nan ta keto ta ta taho akasarin jama'ar da ke wajan duk idanunsu akanta, kowa kallonta yake yi da haka ta saba fita?"


Wani ne ya gifto zai wuce sai Muhdeen ya kalle sa ya ce


"Yauwa Mannir zonan dan Allah"


Wanda aka kira da Mannir yazo cikin girmamawa ya ce,


"Sannu yallaɓai ya jikinka?"


"Da sauƙi"


Cikin aljihun wandonsa ya ciro kuɗi ya miƙa wa Mannir ya ce,


"Ka tafi yanzun nan ka siyo mani manyan hijabai guda biyar ka kawo mani."


Karɓa Mannir yayi tare da cewa


"To yallaɓai"


Ya tafi Jabeer ya kalli Muhdeen tare da cewa


"Ai taɓa sanin cewa kana da kishi ba sai yanzun, na ɗauka baka da kishi sam a rayuwarka."


Kallon Inteesar Muhdeen yayi tare da cewa


"Ki shiga ciki"


Ba musu ta nufi room ɗin da Muhdeen yake ta shige.


Kallonsa ya maida ga Jabeer ya ce,


"Me yasa kake tunanin bani da da kishi?"


Dariya yayi tare da cewa


"Abunda a bayyane yake, ita Sumayya da take yawo da kayan da basu dace ba wanda kwata-kwata ba wanda zai ganta yayi tunanin matar aure bace fa? tunda nake ganinta ban taɓa ganinta da shiga irin ta mutunci ba, tun daga kan 'yan matancinta har zuwa aurenta, duk da cewar da tayi auren an samu sauyi amma duk haka banbancin kaɗan ne, me yasa ita Sumayya baka tilasta mata ta lulluɓe jikinta da hijabi ba? sai Inteesar da take shigar mutunci ce zaka saka a gaba? ai naga duka matanka ne meye banbanci?"


Gajeren murmushi Muhdeen yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa sannan ya cigaba da magana


"Kasan akwai banbanci tsakanin Inteesar da Sumayya, Inteesar tana da nazari, nutsuwa, hankali da kuma tarbiyya, yayinda Sumayya kuma tayi hannun riga da waɗannan abubuwan sam bata da su, domin Sumayya bata samu tarbiyya daga wurin iyayenta ba, haka ta tashi ba mai saka ta ba mai hana ta duk abinda taga dama shi zatayi na wanda zai ce da ita me yasa ko mai tayi dai-dai ne a wajen iyayenta su kansu basu isa da ita ba, kasan icce tun yana ɗanye ake lanƙwasa shi idan ya bushe bazai lanƙwasu ba sai dai ya karye, to Sumayya ma haka take kaima ka sani, Inteesar kuwa ta samu cikakkiyar tarbiyya daga wajen iyayenta tasan darajar mijinta, ɗan zama na da ita ko ita ce na ajiye na ce kada ta tsallake sa to baza ta tsallaka ba, tana mani biyayya da jin magana ta koda ranta bai so ba bata tsallake magana ta, shiyasa kai tsaye nake iko da ita saboda nasan na isa da ita."


Jinjina kai Jabeer yayi ya ce,


"Hakane, ne ta girko mana ne dan dama kasan nan Asibiti na kwana banyi breakfast ba, nasan Inteesar wajen iya girki ba daga baya ba."


Shiga cikin ɗakin sukayi inda Inteesar ta zauna da tazo yanzun ma nan take, kuma a kagare take da ta tafi tasan bazai barta ta fita haka ba dan haka ta tsaya jiran a kawo mata hijabi ta tafi, Sumayya kuma tana zaune bakin gadon.


Jabeer ne ya kalli Inteesar ya ce,


"Ƙanwata a bani abincin da aka kawo wa majinyaci naci ina son naci girkin nan naki mai daɗin gaske."


Dariya tayi tare da ƙara sawa tayi wajen Basket ta ce,


"Yaya Jabeer me zan fara zuba maka?"


"Me da me kika kawo ne?"


"Kunun gyaɗa da ƙosai sai shayi da bread da soyayen dankali da plantain da ƙwai, sai farfesun kayan ciki."


Murmushi yayi tare da cewa


"Masha Allah, ki bani kunun gyaɗa da ƙosai sai farfesun nan"


Cup ɗaya ta ciro ta zuba masa ta ciro plate ta zuba masa ƙosai, tana buɗe farfesun ƙamshi ya gauraye ɗakin Sumayya har tana haɗiyar miyau.


Bayan ta ajiyewa Jabeer nashi ta koma ta zauna ki kallon inda Muhdeen da Sumayya suke bata yi ba, dan sun ɓata mata rai, ganin ta zauna yasa Summary kallonsa ta fara Magana


"Baby wai ba saboda kai aka kawo abincin nan bane? naga ko zuba maka naka bata yi ba ballantana ni."


Kafin Muhdeen yayi magana ne Jabeer ya ce,


"Ai tayi mai wuyan tunda ta girka ta kawo ke sai ki zuba masa ai."


Kallon Jabeer tayi cike da jin haushinsa ta buɗe baki da niyyar maida masa martani ne taji muryar Muhdeen ya ce,


"Ki zuba ki kawo mani"


Kallon Inteesar tayi dan gani take kamar tafi ƙarfin hakan tunda ga Inteesar a wurin, taso a ce ita zata zuba masu ta kawo masu.


Tashi tayi ta je ta zuba ganin zata cika ne yasa ya ce ta barshi haka nan, sai ta nuna masa cewa ita da shi ta haɗa, dan haka yayi shiru bai ce komai ba, tashi yayi daga kan gadon ya nufi sofa dake ɗakin ya zauna, Sumayya ta kawo da ajiye a Centre table dake gaban Muhdeen, komai da aka kawo sai da ta zuba masu ta haɗa a plate kunun gyaɗa da ruwan shayi ta zuba a kofi biyu ita da shi, kallonta yayi tare da cewa,


"Ki zuba a kofuna uku"


Kallonsa tayi zatayi masa magana sai ta tamke fuska dan yasan halinta yanzun zata yi masa gardama, ganin haka yasa bata ce komai ba ta zuba tana jiran taga ikon Allah.


Zama sukayi zasu fara yin breakfast ɗin ya kalli Inteesar tare da cewa


"Zo ki zauna kiyi breakfast nasan baki ci komai ba."


Da sauri Sumayya ta kalle shi jin abunda ya faɗa, dan kwata-kwata ta tsani taga yana kula Inteesar kuma yanzun ta lura ya faɗa tarkon son Inteesar tsundum, amma baya yi tunanin zai haɗa matsayinta da na Inteesar ba, wai ita ce zaisa ta zubawa Inteesar abinci? takaici ne ya kamata sosai da sosai, kallon Inteesar tayi lokacin da taji Inteesar na magana tana cewa


"A'a yaya na ƙoshi"


Kallonta yayi


"Me kika ci?"


Girgiza kanta tayi tare da cewa


"Bakomai"


"Bana son gardama kizo kici abinci, "


Cikin sanyinta da nutsuwarta ta taso tazo ta zauna a cikinsu, wannan ne karo na farko da ta zauna a tsakiyarsu dan yin breakfast, ko can gida lokacin da take masu girki sai dai ta jera masu ta ajiye su ci tare amma yau da kansa ya ce ta shigo cikinsu.


Cikin jin haushinta Sumayya ke binta da kallo har ta zo ta zauna, kowa ya fara cin nasa banda Sumayya da baƙin ciki ya hana ta ci, ganin kallon da Muhdeen ke mata yasa ta fara shan kunun gyaɗa ita kuma Inteesar ruwan shayi kawai ta ɗauka take sha.


Gaba ɗaya idanun Muhdeen akan Inteesar yake ita kuma bata ma kula da kallon da yake mata bane, idonta nakan kofin shayin da take sha, Sumayya da idanunta ke kansa ne ta kula da hakan, yayin da take cike da takaici, miƙewa Inteesar tayi zata bar wajen ta jiyo muryarsa yana cewa


"Ina zaki je baki ci komai ba."


Cikin sanyin Muryarta ta ce,


"Na ƙoshi"


"Dawo ki zauna "


Sumayya ce ta kalle shi da sauri


"Haba Dear tunda ta ce ta ƙoshi dole ne? cikinta ne fa ba naka ba, idan ma bata..."


Kasa ƙara maganar tayi ganin kallon da ya jefa mata, domin tun ranar da ya gane cewa ita ce tayi yinƙurin kashe Inteesar ya mata dukan da sai da ta suma to tun daga ranar ne ta fara shakkarsa idan ta tuna ma takan ji tsoronsa dan haka koda taga kallon gargaɗin da yake mata sai tayi shiru.


Ba musu Inteesar ta dawo ta zauna, da kansa ya ɗebi soyayyan dankali da ƙwai sai da bread ya aje mata a gabanta.


"Ki cinye su yanzun nan tunda baki son cin abinci."


Kwaɓe fuska tayi kamar zata yi kuka tare da tura baki tana magana ciki ciki ba wanda ke jin me take cewa


Shagala yayi da kallonta yadda take yi sai ji yayi ta burge shi, murmushi kawai yake yana kallon bakinta yana tuna ranar da ya sumbaci bakinta da irin yanayin da ya shiga, da daɗin da baƙin nata ke da shi,gaba ɗaya ya shagala da kallonta yana cin wani nishaɗi a tattare da shi, ji tayi a jikinta ana kallonta tana ɗaga kai sukayi ido huɗu da shi ɗauke idanunsa yayi daga kallonta, abun mamaki sai yaga ba Sumayya a ɗakin ba alamarta, juyawa yayi gabas da yamma Kudu da arewa ba alamarta, sai a lokacin idanunsa ya sauka akan Jabeer dake ta dariya, itama Jabeer take kallo Muhdeen ya ce,


"Kai kuma lafiyarka?


Ba tare da ya kalle shi ba ya ce,


"Lafiya lau nake"


"Ina Sumayya ta shiga ko tana toilet ne?"


Tsagaita dariya Jabeer yayi tare da cewa


"Mallam ka warware ba abunda ke damunka ka tattara kabar Asibitin nan"


"Pls Ina take?"


"Kai da kake zaune tare da ita baka sani ba sai ni? naga lokacin da ka shagala da kallon tauraruwarka ita kuma lura da hakan yasa baƙin cikinku ya kore ta dana na lura ba zata iya jurewa ba"


Ya ƙarasa maganar yana mai ƙara keta wata dariyar ya tashi ya fita yana cewa


"Kada na dawo na tarar da kai dan yanzun kam ba abuda ke damunka ba zaka tare mani rikicin wannan matar taka ba."


Daga nan Jabeer ya fita ya bar Muhdeen da Inteesar, yayin da zuciyar Muhdeen tayi fari fes dan a duka lokacin da suka keɓe shi da Inteesar sai ya dinga jin wani aminci ya lulluɓe shi, kallonta ya cigaba da yi don shi ba mai yawan kallo bane amma idan dai akan Inteesar ne baya taɓa iya ɗauke idanunsa daga kallonta, sam baya gajiya da kallonta.


Daƙyar ta iya cinye abincin da ya zuba mata kamar zatayi kuka, dan ita ba mai yawan cin abinci bane, dan haka kishingiɗa tayi a saman sofa ɗin, matsawa yayi kusa da ita da niyyar kai hannu ya taɓa ta yaji anyi knock bada izinin shigiwa yayi, Mannir ne riƙe da leda babba a hannunsa ya miƙawa Muhdeen tare da cewa


"Yallaɓai gashi"


Amsa yayi tare da cewa


"Nagode Mannir"


Mannir ya miƙa masa sauran canji da da suka rage, kai Muhdeen ya girgiza tare da cewa


"Na baka kyauta"


Godiya yayi tare da addu'a ga uban gidan nasu ya fice.


Miƙa mata ledan tayi tare da cewa


"Ki ɗauki daya kisa yanzun nan idan kin koma gida zaki cigaba da sawa."


Cikin sanyin Muryarta ta ce,


"Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allan ƙara huɗu."


.tsayawa yayi yana kallonta har cikin ransa ya ji daɗin kalamanta, janyo ta yayi tare da manna masa kiss a gishi.


Gwaggo ce ta turo ƙofar ta shigo, Mummy na biye da ita a baya.


Cikin so da kula suka gaisa da Muhdeen, kuma shi kansa yaji daɗin yadda suka saki fuska da shi ba sun daina fushi da shi,yanzun Dady ne kawai ya rage bai daina fushi da shi ba.


Bayan awa uku su Gwaggo da Mummy suka tafi, Inteesar ma binsu tayi .


A rana r ne aka sallami Muhdeen ya tattara kayansa ya koma gidansa, bayan ya koma ko zama baiyi ba ya ɗauki wayarsa ya da nawa Jabeer kira, bayan ya ɗaga ne Muhdeen ya ce,


"Dan Allah ka shirya ka raka ni mu roƙi Dady ya bani mata ta dan Allah, dan bani da matsala da Mummy da Gwaggo dan naga sun sauka zasauyi sauƙin kai amma Dady kam har yanzu bai sauko ba, dan Alalh ka raka ni Jabeer, a shirye nake da na fuskanci kowane ƙalubane ne ."








*Daga alƙamimin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




*Don ƙarin bayani*




09065327995






Love you oll😍😘


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a








*INTEESAR*


Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.NT
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne




*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce bada niyyar yin hakan nayi barshi me mai kashe auren wawa




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page7️⃣4️⃣


"Dan Allah kanshirya ka rakani mu roƙi Dady ya bamu matata don Allah, dan bani da matsala da Mummy da Gwaggo dan naga sun sauka zasauyi sauƙin kai , amma Dady kam har yanzun bai sauko ba dan Allah ka rakani Jabeer a shiryau nake da na fuskanci bko wane ƙalubale ne"


Daga nan ya kashe wayar toilet ya shiga yayi wanka.


Sumayya kam tana can ɗakinta sai cika take tana batsewa, ita a tunaninta tunda ya dawo zai shigo ne ya lallaɓa ta, amma sai taji shiru bai shigo ba kuma ba alamar zai shigo, haka ta dinga saƙa da warwara ita kaɗai a ɗauki, zuwa can sai ta ƙyalƙyace da dariya har tana kwanciya saboda tsabar dariya, ita kaɗai ta fara magana


"Kwantar da hankalinki Sumayya komai zai tafi yadda kike so, kedai ki kasance mai juriya ki daure har sai kin kai ga nasara akan abinda kika saka a gaba, komai zai dawo maki dai-dai Sumayya da farko ki fara ajiye makaman yaƙinki a gefe."


Haka ta dinga magana ita kaɗai, daga ƙarshe ta fito ta nufi ɗakinsa, tana tura ƙoafar taji wani ƙamari ya ziyarci ta tsaye ta same sa yana saka hula a kansa, bayan ya gama shiryawa kamar wani ango yayi masifar kyau ta cikin mirror ya hango ta tana sakin murmushi, mamaki ne ya kama sa dan dai shi ya sani Sumayya fushi take yasan ba zata saurare shi ba dan haka ya fita harkarta, amma abunda ya bashi mamaki ganin yadda take murmushi kamar ba ita ba, kamar ba fushi da kishi ne ke damunta ba, juyowa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads