Showing 39001 words to 42000 words out of 149432 words
Chapter 14 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
Ba Wanda ya lura da Salisu shi kuma farfesun ya fara ci yana Kai naman bakinsa ya yamutse fuska,da sauri ya zaro hanki a aljihunsa ya saka naman da ke cikin bakinsa aciki ya dunk'ule a hannunsa Shima ruwa yasaha rabin kofi.Bilyaminu kuwa yana Kai cokalin abinci a bakinsa ya murtuk'e fuska Amma shi yayi k'arfin halin had'iye abincin Amma sai da ya rintse ido sannan ya Kora da ruwa.Sumayua kuwa duk Bata lura da abunda ke faruwa ba hankainta na Kan Mijinta da wayar da yakeyi.Jabeer ne ya kalli Salisu da Bilyaminu ya ce,
"Kunji abunda naji kuwa?"
Kai suka gyad'a masa ba tare da aunce komai ba.Ya cigaba da magana
"To Alhamdulillah ni kunga tafita."
Mi'kewa yayi suma suka mi'ke suka bi bayansa dai-dai lokacin da Muhdeen ya gama wayar da yakeyi,kallonsu yayi mamaki ya ce,
"Ya dai?har kun gama cin abincin ne?"
Wani irin dariya dariya Jabeer ya shek'e da shi Wanda sai da gaban Muhdeen ya fad'i,don yafi kowa sanin waye Jabeer idan yaji yayi irin wannan dariyar to tabbas ta mugunta ce.Jabeer ya ce,
"Eh mun gama cin abincin Alhamdulillah girkin Amarya yayi dad'i,kuje kuci naku aci dad'i lafiya.
Ya nufi k'ofar fita yayin da Salisu da Bilyaminu suka bi bayansa, kasancewar a motar Jabeer suka zo horn yayi Mai gadi ya bud'e masa suka fice daga gidan.Shiru muhdeen yayi yana nazarin kalaman Jabeer yasan ba banza ba, dinning area ya nufa abincin da Jabeer ya bari ne ya d'auki cokalin ciki ya d'iba tare da kaiwa bakinsa,da sauri ya tofar dashi k'asa ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in ya dafe kansa yana fad'in
"Sumayya kin kunyata ni a wurin abokaina,tunda nake ba'a ta'ba kunyatani irin na yau ba.kima mace ace baki San yadda ake gika abinci ba wannan want irin rayuwa ne?"
D'aga masa hannu tayi tana cewa
"Dakata haka nan dama ka auro ni ne don ka wulak'antani?,tunda nake a rayuwarta ban ta'ba yun'kurin shiga kitchen da niyyar gika komai ba,ko uwata da ubana basu ta'ba cewa na dafa masu Koda ruwan zafi ba Amma a Kan son da nake maka karon farko a rayuwat na shiga kitchen don na girkawa k'artin banza abinci baka yaba mani ba how dare you zaka ci mutuncina.Kuka ta saka masa,tunawa yayi da yanayin rayuwarta bata ta'ba yin girki ba Amma don ta faranta masa tayi hakan yasa ya rungumeta Yana rarrashinta.
Jabeer kuwa sai da ya biya gidajen abokansu ya sajke kowa a gidansa,Kai tsaye gidan Mummy ya nufa don hsky yunwa yake ji Yana driving yana dariyar gidan Muhdeen da suka baro a zuciyarsa Yana tausayawa Muhdeen wani 'bangaren zuciyarsa kuma baya tausayinsa, musamman idan ya tuna cin mutuncin da yayi masa lokacin da ya ce bai goyi bayan ya auri sumayya ba.
Da sallama ya shiga falon inda ya tarar da Mummy da Mufida a falon durkusawa yayi ya gaida Mummy, Mufida ta gaishe sa ya amsa.Kallon Mummy yayi ya ce,
"Gwaggo fa tana d'akinta ne?"
"A'a suma kitchen."
Dariya yayi tare da cewa,
"Dama yunwa nake ji bari na gyara zama naci girkin tsofaffo."
Mufida ce tayi dariya tare da cewa
"Ai ba ita ke girkin ba,Mai girki nayi ita kuma tana ta zuba mata surutu."
"Okay to wace ce ke girkin?"
"Inteesar ce ke girkin."
Take yaji wani farin ciki, mi'kewa yayi tare da cewa
"Bari na shiga kitchen d'in mu gaisa da Gwaggo."
Koda ya shiga kitchen d'in a ya samu Gwaggo akan kujera sai surutu take ta zubawa Inteesar,yayin da Inteesar ke tuk'a tuwon shinkafa.Gaida Gwaggo yayi ta amsa da cewa
"Jabiru kaine a tafe?ya jikin wannan lagwanin matar taka?"
Murmushi kawai yayi ya zubawa Inteesar ido fa take kwasar tuwo,ji tayi a jikinta ana kallonta d'ago Kai da zatayi suka had'a ido da sauri ta d'auke idanunta tare da cewa
"Yaya Jabeer ina wuni?"
"Lafiya lau ya kike?'
"Alhamdulillah."
Gwaggo sai surutu take zuba masa shi kuma duk hankainsa na kan Inteesar har ta gama kwashe tuwon ta bud'e miyar agushi da alaihun da takeyi taga ya nuna,kashe gas d'in tayi ta d'auki food flask da ta zuba tuwo takai dinning table ta dawo ta Kai miyar dama ta had'a juice d'in kwakwa da madara ta zuba a jug ta saka K'ank'ara a ciki ya d'auki sanyi bayan ta kammala shirya komai ne ta kalli Gwaggo dake ta zubawa Jabeer surutu ta ce,
"Bisimillah Gwaggo na kammala komai."
Wasshe baki Gwaggo tayi tana cewa
"Yauwa 'yar albarka gani Nan zuwa kwanan biyu da kika koma wajen Ummanki nayi kewar dadd'ad'an girkinki mai dad'i."
Mi'kewa tayi tare da janyo hannun Jabeer tana cewa
"Muje kaima nasan wannan matar taka ba iya girka maka abinci zata iya ba."
Dinning table d'in suka zauna inda suka tarar da Mummy da Mufida Mufida ce ta zubawa kowa nasa, ta tsiyaya masu juice d'in kwakwa da ta had'a nan kowa ya fara cin girkin Inteesar nan Jabeer ya dinga santi yana yaba dad'in girkin yana korawa na juice kundai san Inteesar a wajen girki wannan ne dalilin da yasa Mummy keson girkin Inteesar.Gwaggo kuwa har gidansu Inteesar take zuwa ta d'aukota don ta tayata girki,bayan kowa yaci ya k'oshi ne Mufida ta tattare kayan ta nufi kitchen dasu,Mummy kuwa d'akinta ta nufa inda Inteesar ta kalli Gwaggo ta ce,
"Gwaggo ni zan tafi gida ban gama aikin da nakeyi ba kika zo kika ce nazo mu tafi,zan koma na k'arasa."
"To 'yar albarka ki gaida umman taki ko na rakaki ne?"
Jabeer ne ya ce,
"Dama tafiya zanyi bari na ajiye ta kawai."
Sallama yayi wa Gwaggo da Mummy sannan yabi bayan Inteesar, kasancewar a waje yayi parking ne yasa yayi saurin bin Inteesar akan tazo ya kaita amma sam tak'i yarda don ta lura da shige mata da yakeyi kuma ita Bata da niyyar kula ko wane d'a namiji. Cikin k'osawa tayi magana
"Yaya Jabeer kada ka damu ba nisa ne damu ba da k'afa zan gangara ."
Kafad'a ya d'aga alamar baidamu ba,hakan yasa ta cigaba da tafiya abun mamaki sai taga ya jera da ita yana ta binta,hakan yasa ta tsaya ta zuba masa ido ya sakar Mata murmushi tare da cewa
"Kada ki damu zan cika alk'awarin da na d'aukarwa Gwaggo,na cewa zan raka ki."
Bata sake ce masa komai ba har suka Isa k'ofar gidansu.Kwatsam sai ganin Usman tayi a k'ofar gidansu ya Kara waya a kunnen sa ya cire yana dube-dube da alama wayarta yake kira.Ido hud'u sukayi da Usaman ya zuba mata idanunsa take ya gane Jabeer shine wannan mutumin da yaga Inteesar dashi a super market,Jaber ma ya ganesa.Ganin haka yasa Jabeer ya kalleta ya ce,
"Dama wannan shine aikin da kika ce zakije gida kiyi?to gashi nan sai kije ki sameshi,daga nan ya juya ya tafi cikin wani irin yanayin da mai wuyar karanta.
Washe gari ranar juma'a da misalin k'arfe goma da rabi na safe Gwaggo ta matsa akan cewa lallai cewa sai an kaita gidan Muhdeen,Mufida ce zata rakata inda Ishaq ya kaisu har gidan Muhdeen.
Koda suka shiga gidan Sumayya suka samu a falo, sanye take da wando 3 quarter da singileti ga tulin k'arin gashin da akayi mata a sake shi a tsakiyar bayanta.Da sallama Gwaggo suka shiga falon kallo d'aya Sumayya tayiwa Gwaggon ta kauda Kai gefe hakan baisa Gwago ta damu ba,ta ce,
"Amarya baki amsa sallama ne ko kuma baki ganni bane?"
Yamutse fuska tayi tare da cewa
"Na ganki mana Gwaggo ko so kike na goyaki ne ko?ki kuma na tashi nayi rawa da tsalle saboda kinzo?"
Mufida ce ta kalleta ta ce,
"Haba Aunty Sumayya wannan fa kike gani itace ta haifi Baban mijinki fa?"
Hannu Sumayya ta d'aga ta ce,
"To sai me matar da ba k'aunata take ba,a gabanki taci mutuncina Wai banida tarbiyya,to yau zata ga rashin tarbiyya muraran.Idan kuma ba so take na nuna mata ba to tattara tsummar rayuwarta tabar Mani gida.
Gwaggo cikin 'bacin rai ta ce,
"Ina Muhammadu yake Ina son ganinsa yanzun Nan."
"Barci yakeyi kuma bazan tayar dashi ba."
Cikin kakkausan murya ta sake magana ta ce,
"Yau nine zanzo gidan jikata a wulak'antani ba ruwan sha ballantana abinci?"
Dariyar rainin hankali tayi sannan ta ce,
"Kinga mijina barci yakeyi bana son ya farka da hayaniyarki fita kibar mani gida,dama tun ranar da kika ci mutuncina Dan naje gaisheki na sakawa raina cewa sai na rama duk randa na auri Muhdeen kika zo gida na.Dama ni haka nake ba'ayi mun ban rama ba ko waye a duniyar nan yayi Mani sai na rama,naki ma na raga maki saboda albarkaci jikanki."
Gwaggo tayi dariya tana fad'in
"Yarinya kin d'ebo ruwan dafa kanki,wallahi sai kinyi Danasanin abunda kikayi Mani kuma zaki ga matakin da zan d'auka akanki wallahi matakin bazai maki dad'i ba."
"Babu matakin da zaki d'auka akaina,don mijina yana sona Baya son 'bacin raina."
Daga Nan Gwaggo tana fita Mufida tabi bayanta,suka shiga mota Ishaq yajasu suka tafi.
Tun akan hanya Gwaggo ta kira Dady ta sanar dashi duk abunda yake ya bari yazo ya sameta a gida.Jin yanayin Muryarta yasa yasa hankain Dady tashi ba shiri ya kamo hanyar gida.isowarsu ba gida ba jimawa Dady ya iso nan Gwaggo ta basu labarin rashin mutuncin da Sumayya tayi mata nan ta nuna masu cewa yarinyar nan bata da tarbiyya shiyasa tun farko na hana auren nan amma baku saurareni ba.
"Innaillahi wa'inna ilaihir rajiun"
Kalmar d Dady ya furta kenan
Gwaggo ta ce,
"Sani!"
Dady ya kalleta da sauri Jin yadda ta kira sunansa ,ta cigaba da cewa
"Idan har ni na haife ka kuma na Isa da kai to a yau d'innan ina son Muhammad Muhdeen ya k'ara aure."
Dady da Mummy da sauri suka kalleta Jin kalamanta,Dady ya ce,
"Amma Gwagg...
Dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu ta cigaba da magana
"Ba shawara na kawo ba,umarni na bada."
Kai Dady ya gyad'a tare da cewa
"Yadda kike so haka za'ayi,amma wace ce zamu aura masa?"
"INTEESAR"
Da mamaki ya kalleta ya ce,
"Ita Inteesar d'in tana sonsa ne?"
Bata bashi amsa ba ta shiga d'akinta ta fito da handa bag ta kalleshi ta ce
"muje"
sannan ta kalli Mummy ta ce
"sai mun dawo "
Mamaki ya hana Mummy magana Dady yabi bayanta basu tsaya ko Ina ba sai k'ofar gidan su Inteesar.
Daga alk'alamin✍️
Maman Ihsan
09065327995
Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni, bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page2️⃣8️⃣
Mamaki ya hana Mummy magana,Daddy yabi bayanta basu tsaya ko ina ba sai k'ofar gidansu Inteesar.
Dady ya tsaya a k'ofar gida yayinda Gwaggo ta kutsa Kai cikin gidan tana kwad'a sallama.Umma ce ta fito daga d'akinta,ganin Gwaggo yasa ta fad'ad'a fara'arta tana yiwa Gwaggon sannu da zuwa,Gwaggo Bata ita take ba ta bud'e baki ta ce,
"Allah dai yasa Mai gidan yana nan?"
"Eh yana nan,yana d'akinsa bai fita ba kinsan yau juma'a sai bayan an dawo sallar juma'a yake fita."
Gwaggo tayi murmushin Jin dad'i ta ce,
"Ai zuwan nawa na wannan lokacin wajensa nazo,ayi Mani magana dashi."
Ummma ta shiga da sallama ta sanar dashi sak'on Gwaggo,kusan a tare suka fito ya gaida Gwaggo cikin girmamawa ta amsa masa da fara'a sannan ta sanar dashi tare da 'Danta suke tafe,magana Mai mahimmanci ya kawosu.Jin haka yasa Abba ya buk'aci Umma ta kawo masa tabarma,bayan ta kawo ne ta shimfid'a masu sannan ta koma cikin d'aki ta sanyo hijab,yayimda shi kuma Abba yayiwa Dady jagora suka shigo kan tabarma suka zauna yayinda Gwaggo kuwa tana zaune a kan gujerar tsugunno,Umma kuwa tana daga gefe itama akan kujera.Gaggaisawa akayi yayinda Gwaggo ta kalli Abba ta ce,
"Nazo wajenku da k'ok'on barata ne,Allah yasa zakuyi Mani alfarmar da nake nema daga gareku."
Murmushi Abba yayi tare da fad'in
"Haba Gwaggo don Allah ki daina fad'in haka,wani k'ok'on bara Zaki nema daga wajenmu?ai kimfi K'arfin ki nemu alfarma a wajenmu sai dai ki fad'i duk abunda kike so muyi maki, matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba zamuyi maki shi."
Kai Umma ta jinjina tare da cewa
"Insha Allah"
Shiru tayi na d'an lokaci kafi ta cigaba da magana
"Alfarmar da nake nema a wajenku shine,ina son a d'aurawa jikana aure da 'yarku."
Umma da abba ba k'aramin mamaki furucin tsohuwar ya basu ba,Umma Kam tsabar mamaki Bata San lokacin da ta mi'ke tsaye zunbur ba,tana kallon Gwaggon da mamaki.
"Nasan zaku yi mamaki kwarai da Jin furucina amma Dan Allah ku amince Mani kada kuce bazakuyi ba."
Abba da har lokacin bai daina mamaki ba ya ce ,
"Gwaggo wanne jikar naki kike magana akai?"
"Muhammadu Muhdeen"
Mamaki ne ya k'ara cika Abba.
"Bashine aka d'auraurensa a kwankin baya ba?"
"Eh shine "
Abba ya cigaba da cewa
"To Mai zaisa..."
Gwaggo ta dakatar dashi ta ce,
"Kun yarda dani?"
Abba da Umma suka ce eh sun yarda da ita.
"To Alhamdulillah tunda kun yarda dani,kunsan yadda nake masifar k'aunar Inteesar bazan ta'ba aikata abunda zai zama Mai cutarwa a gare ta ba,don haka Ina son a masaallacin juma'a a d'aura auren Muhdeen da Inteesar."
Shiru sukayi suna nazarin maganar Gwaggo da irin k'aunar da Gwaggo da Mummy suke nunaw Inteesar.dakyar dai suka fahimci Gwaggo inda suka amince za'a d'aura auren.Nan murna kamar ya kashe Gwaggo ta ciro kud'i dubu d'ari daga ciki kakkarta ta ce ga kud'in sadaki,daga baya za'a had'a Mata kayan lefe anjima a d'aura auren a masaallacin juma'a bayan idar da sallar.
'Baengaren Muhdeen kuwa Yana taahi daga barci k'arfe d'aya saura kwata Yana Shirin shiga wanka Kiran wayar Dady ya shigo wayarsa.bayan ya amsa kiran ne Dady ya sanar dashi ya biyo ta gida idan ya biyo sai suje masallacin Juma'a a tare.
Hakanan kuwa akayi,bayan ya shirya sai ya biya ta gidan Mahaifin nasa gaba d'aya falo ya tarar da su Falo ,ya gaida Dady ya amsa masa ba yabo ba fallasa haka ma ya gaida mahaifiyarsa Nan ma ta amsa masa fuska a sake.Kallon Gwaggo yayi da niyuar bud'ar baki ya gaisheta ta d'aga masa hannu rltare da cewa
"Ri'ke gaisuwarka mijin Hajiya,Wanda baida kata'bus a gidansa sai abunda matarsa ta ce,yanzun kamar Ni ne zanje gidanka har wannan matar taka Mai ka da busasshen crayfish d'in zata ci Mani mutunci kana ciki gida."
Kallonta kawai muhdeen keyi don baisan zancen da take fad'a,don har yanzun baisan da zancen ba.
Dady me ya kalli muhdeen ya ce,
"Kai kana cikin gida Amma a wulakantani Mani mahaifiyar da ta haifeni a gidanka?"
Shiru yayi don baisan lokacin da Gwaggo ta je ba kuma Sumayya Bata sanar dashi ba.Muryar Dady yaji ya ce
"A yau d'inman ana idar da sallar juma'a za'a d:aura aurenka da Inteesar."
Waige-waige Muhdeen ya farayi don yaga waye za'a d'aurawa aure da Inteesar,ganin shi kad'ai ne yasashi cewa
"Dady Wai waye za'a d'aura auren Nan yau?"
"Kaine"
A zabure ya mik'e tsaye tare da firgici a fusakarsa ya Fara magana
"Dady yaushe nayi aur...
'Daga masa hannu Dady yayi
"Ba shawararka muke nema ba Umarni ne koma ka zauna."
Hakan yasa ya koma ya zauna zuciyarsa na masa k'una sosai,shi kad'ai yasan bakin cikin Amma dayake namijin Duniya be shi sai yayi kamar hakan baidamesa ba.har suka Fara Jin dad'i a ransu ganin bai damuba bazai basu matsala ba.
Bayan an idar da sallar juma'a ne dubban jama'a suka sahida d'auri Auren muhdeen da Inteesar.Muhdeen kuwa kamar zai mutu don bak'in ciki.
Daga nan Muhdeen gida ya tafi ransa na k'una,duk yadda Sumayya tayi ya fad'a Mata abunda ke damunsa k'in sanar da ita yayi.Tabishi ta nace Amma Sam yak'i fad'a dole ta hak'ura ta kyaleshi.Da aka Kira sallar la'asar yaje yayi ya dawo,haka da aka Kira sallar magariba ya fita yaje masallaci,Nan ya zauna sai da akayi sallar isha'i bayan sun idar ne yaje restaurant ya siyo masu abinci.Tana zaune yazo ya ajiye Mata a gabanta Kai tasaye d'akinsa ya nufa,Nan ya zaro wayarsa number Jabeer ne ya kira,bugu biyu Jabeer ya d'aga tare da cewa
Ango ango ango ran Muhdeen ya 'baci da yaji ya ce ango ango ango,shi a tunaninsa Jabeer yasan komai don haka cikin 'bacin rai ya Fara magana
"Ka bani mamaki Jabeer wato hada Kai za'a had'a baki a d'aura Mani aure ko?sannan ki ka sanar Dani ko?kawai Dady ya kirani a waya Wai nazo bayan naje Wai yau za'a d'aura Mani aure inaji Ina gani yau aka d'aura Mani sabon aure Alhalin ki wata d'a....."
Baikai K'arshen maganar sa ba yaji k'arar fad'uwar Abu tiff da sauri ya juyo yaga Sumayya ce,ashe ta biyoshi Bai sani ba kuma taji komai da ya fad'a
*PLEASE KUYI MANAGE DA SHI*
Daga alk'alamin✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
09065327995
Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa, ce don a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne banyi,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, Idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashine mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page2️⃣9️⃣
Baikai K'arshen maganar sa ba yaji k'arar fad'uwar abu tiff,da sauri ya juyo yaga Sumayya ce,ashe ta biyoshi bai sani ba kuma taji komai da ya fad'a.
Baisan sanda ya saki wayar ta fad'i k'asa ba ya k'arasa bakin k'ofar ya durk'usa a gabanta tare da tallabota zuwa cikinsa,ganin ta suma ne yasa ya nufi fridge da hanzari ya d'auko robar ruwa 'balle murfin yayi tare da 'balle murfin ya yayyafa mata, shiru bata farfad'o ba,ya sake yayyafa mata a karo na biyu nan ma shiru bata bata farfad'o ba, hankainsa ba k'aramin tashi ya yi ba a karo na uku ne ya guntsi ruwan a bakinsa ya fesa mata a fuska da k'arfi sai gashi ta saki wani ajiyar zuciya tare da fashewa da wani kuka.Ahankali kalamansa da taji ya yi a cikin waya suka soma dawo mata cikin k'wak'walwarta,wani kuka ta fashe dashi mai cin rai tana fad'in
"No no no bazai yuwu ba wallahi babu kishiya a zamana da kai, bazan ta'ba zama dakishiya ba wallahi bazan iya shererin d'inka da kowace mace ba