Header Ads
Showing 135001 words to 138000 words out of 149432 words

Chapter 46 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1399

Ads at the middle of Article

yayi yana kallonta yayin da ta ƙaraso wajensa wajensa tare da riƙe hannunsa biyu cikin murmushi ta ce,


"Masha Allah ka ga yadda kayi kyau kuwa kamar sabo ango?"


Murmushi yayi tare da cewa


"Nagode"


"Ina zuwa wannna kwalliya haka?"


"Zamu je wani waje ne ni da Jabeer"


"To idan kun je ku gaishe mani da ita"


Da mamaki yake kallonta


"Wace ce zamu gaisar maki da ita?"


Dariya kawai tayi tayi sannan ta ɗora da cewa


"Nasan zaka tafi wajen ƙanwata ce, shine na ce ka gaisar mani da ita."


Tsayawa yayi yana kallonta yayi mamakin jin maganar daga bakinta, dan idan da ba don shine da kansa yaji ba wata ce ta faɗa masa zai ƙaryata, don ko a mafarki ta nuna masa wannan yanayin idan ya farka zaiyi sadaka.


"Ke Sumayyata da na sani ce ko kuma an canza msni ke? ban taɓa tunanin jin hakan daga bakinki ba, sai nake ga kamar ba ke bace."


Murmushi tayi yayin da ta ƙara matse hannunsa cikin nata


"Kada kayi mamaki nice, na canza daga yadda ka sanni ne ka ɗauka waccan Sumayyar da ka sani a baya ta sauya, wanna ta banbanta da waccan."


"Da gaske kike yi?"


"Eh mana baka yarda da ni bane?"


"Ba wai ban yarda da ke bane,kawai mamaki nake canzawarki lokaci guda, anya ba wata munaƙisa kike shiryawa ba?"


Murmushi tayi tare da girgiza kanta


"Dama nasan ba zaka yarda da ni ba amma da sannu zaka fahimci komai, yau da gobe."


Shikenan na ji, amma mutuƙar wani abu mara kyau ko mara daɗi ya biyo baya to da ki sani bazan saurara maki ba ko kaɗan, dan wallahi sai kin ɗanɗani kuɗarki."


"Allah sarki bansan me yasa kake mani mugun fahimtar nan ba"


"Ai Sumayya kin wuce sani na, duk mutumin da zaiyi yinƙurin kisan kai da ba abunda bazai iya aikatawa ba."


Dafe goshi tayi tare da rintse ido


"Dan Allah ka daina dawo da abinda ya wuce, mu mance da shi kawai mu rungumi gaba, amma matuƙar zaka dinga tuna aibu na ba zaka taɓa ganin haske na ba, nayi nadamar abinda ya faru a baya dan Allah a daina tuno mani da shi, insha Allahu itama Inteesar zan roƙi gafararta ta yafe mani."


Farin ciki ne ya lulluɓe shi ya rungume ta yana godiya ga Allah da ya sa Sumayyarsa ta gane gaskiya.


Kiran wayarsa ne ya sa ya sake ta tare da ƙarasawa jikin gadon ya ɗauki wayar, sunan Jabeer ne ya fito, ɗagawa yayi tare da cewa


"Ka fito ne?"


Jabeer ya ce,


"Mu haɗu a ƙofar gidan kawai"


"Okay I'll be on my way"


Kashe wayar yayi tare da kallon Sumayya ya ce,


"Sai na dawo"


"Oky tare da ita zaku dawo?"


"Bani da tabbas ki taya ni da addu'a Allah yasa ya amince"


"Ameen, thank you so much"


Daga nan ya nufi ƙofar fita ta riƙe hannunsa tare suka fito ta raka sa har wajen motarsa, wannan karan ba shine Aiyi driving ba Ishaq ne ya ja shi suka tafi, tana ɗaga masa hannu har mai gadi ya wangale masa gate suka fice, sannan ta koma cikin gidan.


Dady zaune a falo shi da Gwaggo suna fira yayin da Mummy da Inteesar suke cikin kitcheen suna aiki.


A ƙofar gidan kuwa Jabeer ne yayi parking, yana jiran ƙarasowar Muhdeen, bayan Muhdeen ya ƙaraso ne Jabee yayi horn mai gadin ya buɗe masa gate, bayan ya shiga ne shima Muhdeen yabi bayansa da tasa motar parking suka yi sannan suka fito a tare suka shiga gidan, bakinsu ɗauke da sallama, Dady da Gwaggo suka amsa sallamar yayin da Muhdeen da Jabeer suka ƙaraso suka durƙusa tare da gaishe su, bayan sun gaisa ne suka zauna akan Centre carpet kowa yayi shiru Gwaggo ce ta katse shirun ta hanyar cewa


"Muhammadu ya jikinka har ma warware ne da zaka fara yawo?"


Murmushi yayi jin Gwaggo tayi magana kuma yasan kuma ta sauko dan haka ya samu ƙwarin gwuiwar yin magana


"Dama nazo ne ina mai roƙonku a karo na biyu da kuyi haƙuri ku gafarce ni ku bani mata ta mu kom..."


Tsawar da Dady ya daka masa ne yasa ya kasa ƙarasa maganar, wanda har Mummy da Inteesar da suke kitchen sai da suka jiyo tsawar, dan haka suka nufo falo dan ganin meke faruwa.


"Muhammad ka kiyaye ni ka fita a ido na me ka maida mutane ne? idan ma kana tunanin cewa Inteesar zata koma gidanka ne? to kayi kuskure babba tunda Allah yasa ka zo yanzun nan ba sai anjima ba kamar yadda na umarce ka da ka aure ta ba tare da ka shiryawa hakan ba, to yanzun ma na umarce ka da ka sake ta ba tare da ka shiryawa hakan ba, kada kayi mani musu ko gardama kuma ba shawara bace umarni ne ka sake ta yanzun nan."


Muhdeen da Inteesar jin kalaman Dady yayi masu tsauri ne lokaci ɗaya suka fara zubar da hawaye, Muhdeen ya durƙusa akan gwuiwar ƙafarsa biyu yana zubar da hawaye yana roƙon Dady da ya amince da nadamarsa.


"Dady tun ranar na baku haƙuri na roƙe ku da ku yafe mani, ku amshi tuba na sannan kuma ku kafa mani kowace irin sharaɗi ne indai akan Inteesar ce zan cika su, idan har na sake aikata wani abu mara kyau a gare ta na amince ku raba ni da ita har abada, yanzun dai na gane kuskurena, wallahi bazan iya rayuwa ba Inteesar ba."


Jabeer ya dora da cewa Dady zan faɗa maganar nan ne badan na bi son zuciyata ba kuma badon Muhdeen yana amini a gare ni bane a'a zan faɗi haka ne dan..."


Dady ne ya ɗaga masa hannu alamun dakatarwa ya ce,


"Kai Jabeer kayi magana kai tsaye bana son nuƙu-nuƙu."


Kai ya jinjina alamar to sannan ya ɗora da cewa


"Dady wallahi yanzun Muhdeen yayi nadama da gaskiya yake son Inteesar, nabtabbata idan kuka basa matarsa suka cigaba da zamansu, na tabbata ba zaka taɓa dana sanin hakan ba, kuma..."


"Kai Jabeer wato ya ɗauko ka ne dan kazo ka wakilce shi ko? to daga kai har shi ku fita kubar mani gida na, kuma kada na sake ganinku kunzo nan da makamancin wannan zancen."


Kuka ne ya ƙwace masa kamar ƙaramin yaro ya dinga roƙon Dady amma yayi biris da shi ganin Dady baida niyyar saukowa yasa Jabeer yaja hannun Muhdeen suka nufi hanyar fita, kuka ne ya ƙwacewa Inteesar da mamaki Dady yake kallonta dan yasan ko kukan ne takeyi, kafin yayi magana yaji muryar Gwaggo na cewa


"Wai kai Sani wani irin taurin zuciya ce da kai, yazo na farko ka kore shi ya je yayi hatsari Allah yasa kwanansa na gaba, yanzun kuma ka sake koransa so kake ya je ya sake wani hatsarin ya mutu ko?"


Ƙara sawa tayi bakin ƙofar ta janyo hannun Muhdeen suka dawo .


Ajiyar zuciya Dady ya sauke tare da cewa


"Gwaggo mu muka aura masa ita da kanmu a bisa umarnink, mun kai ya gidansa akan muna da yaƙinin cewa bazai watsa mana ƙasa a ido ba, amma ina muke a lokacin da suke zaune ya dinga azabtar da ita? ina muke lokacin da ya dinga ƙuntatawa rayuwarta ya maida ita baiwa? ina muke lokacin da uwar gidansa Sumayya ta mayar da ita tamkar baiwarta, ita ce yai mata wankin toilet gyaran ɗaki shara ta bata umarnin ta dafa mata abincin da ranta keso, ina muke lokacin da take rayuwar rashin ƴanci? ina muke lokacin da matarsa Sumayya tayi yunƙurin kashe ta?"


Kaga ba wannan nake so naji daga gare ka ba, yaro ya gane kurensa ya kuma kowa ya fahimci yanzun yana son matarsa, abu ɗaya ya rage a nemi jin ta bakinta idan ta amince zata koma ɗakin mijinta kuma tana sonsa ai shikenan sai ku binsu da fatan alkhairi."


Jinjina kai Dady yayi ta ce,


"Shikenan Gwaggo yi adda kika ce haka za'ayi"


Kallon Inteesar dake goge hawaye Gwaggo tayi tare da cewa


"Zo nan ƴar albarka"


Cikin sanyin jiki ta ƙara so ta durƙusa a gabansu, Dady ya kalle ta tare da cewa


"Inteesar"


Cikin sanyin murya ta ce


"Na'am"


"Kina son Muhammad kuma zaki iya cigaba da zama da shi matsayin mijin aure?"


Gaban Muhdeen ne yake dukan uku uku yana fargabar ta ce bata sonsa, Mummy ma da ta kasa magana kallon Inteesar take tana addu'a Allah yasa ta amince, dan yasan cewa tayi sa'ar suruka.


Tsawon mintuna biyar batayi magana ba sai da Gwaggo ta tambaye ta a karo na biyu ta ce


"Eh zan zauna da shi"


Daga haka ta ruga a guje zuwa ɗakin Mufida cikin jin kunya, dariya sukayi Muhdeen ya ɗaga hannu yana godiya ga Allah.


Muryar Dady suka ji ya ce,


"Akwai sharaɗi guda ɗaya, har sai ka raba masu gida da Sumayya, bazan taɓa bari ka haɗa su gida da Sumayya ba, dan kafi kowa sanin abunda ta aikata, dan haka zama da ita hatsari ne ga rayuwar Inteesar."


Nan dai Mummy da Gwaggo suka amince da maganar Dady, dama yana da wani gidan da ya siya har Jabeer ya bashi shawara yakai Inteesar gidan ya nuna gida ɗaya zai aje su, an gama komai na gidan hatta fenti anyi saura a goge gidan kasancewar yayi ƙura a kuma zuba furniture's.


Kai ya jinjina tare da cewa


"To insha Allahu nan da gobe za'a goge gidan a zuba furniture's sai ta zauna a ciki."


Nan sukayi masu fatan alkhairi farin ciki a wajen Muhdeen ba'a magana.


A ranar yasa akayi fenti aka aka gyara gidan aka wanke, washe gari, washe gari kuma yasa aka saka labulaye da furnitures.


Ɓangaren Sumayya kuwa taso ace gida ɗaya aka haɗa su da Inteesar, dan ko da ya sanar da ita yadda sukayi da Dady bata so araba masu gida ba, dan magana tayiwa Muhdeen akan ya koma ya roƙi Dady kan cewa su zauna tare ya nuna mata cewa Dady da Gwaggo ba zasu yarda ba, amma idan komai ya tafi dai-dai zuwa nan gaba zai haɗa su gida guda hakan yasa ta ɗanji sanyi a ranta.


Mummy ta Kira Aunty Abla tare da ƙawarta Aunty Bilkisu, suka je gidan da Inteesar ta zauna da Sumayya suka tattaro kayan Inteesar duka aka zuba a mota suka nufi gidanta na yanzun.


Matsakaici gida ne dan bai kai wancan gidan da Sumayya take ciki girma ba, don shi 3 bedrooms ne kowane ɗaki yana ɗauke da toilet sai wani toilet da akayi shi a falo saboda baƙi, sai kuma dinning room da kitcheen.


Tsarin gidan yayi kyau komai nasa madaidaici ne gwanin ban sha'awa.


Ana gobe Inteesar zata tare farin cikin da Muhdeen yake ciki baya misaltawa, sai wani rawar ƙafa ya ke kamar sabon angon da za'a kaiwa Amarya gobe, farin cikin da yake ciki ya kasa ɓoyuwa duk wanda ya kalle sa yasan yana cikin farin ciki.


Ɓangaren Inteesar kuwa wani sabon gyara Hajiya Bilkisu ta yi mata a cikin kwana biyun nan, tun daga kan na wanka na shafawa na sha da na turara jiki da na tsugunno, sai wani ƙamshi na musamman take fitarwa a cikin kwana biyun nan ta sauya Sosai.


Duk yadda Muhdeen yaso su haɗu da Inteesar Mummy ta hana, dan ko yazo bata bari ta fito su haɗu, yau da ya ƙagara da ya ganta ne ya nunawa Mummy cewa yana son zaiyi magana da ita ne, amma ta nuna masa cewa ya faɗawa Mufida abunda zai faɗa sai Mufida ta sanar da Inteesar, haka ya hakura ya koma gidan a zuciyarsa yana cewa ai daga gobe ne, ƙarshen tika-tika tik.








*Daga alƙalamin*✍️


Zainab Abdullahi K N.T
(Maman Ihsan)






*DON NEMAN ƘARIN BAYANI*


090 65327995




Love you oll😍😘


Comments &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






Idan kinsan cewa kina cikin group ɗin Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne.




*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page7️⃣5️⃣


Duk yadda Muhdeen yaso su haɗu da Inteesar Mummy ta hana, dan ko yazo bata bari ta fito su haɗu, yau da ya ƙagara ya ganta ne ya nunawa Mummy cewa yana son ya ganta ne, amma ta nuna masa cewa ya faɗawa Mufida ta sanar da Inteesar, haka ya haƙura ya koma gidan a zuciyarsa yana cewa ai daga gobe ne, ƙarshen tika-tika tik.


Rana bata ƙarya yau ne ta kama ranar da Inteesar zata tare a sabon gidan Muhdeen, musamman Mummy ta sa aka kawo mai lalle da kitso, inda aka tsantsare ta da ado da kwalliya, tun safe ya kira Mummy yake tambayarta wai zaizo ya ɗauki matarsa, ta sanar da shi cewa ba sai yazo ba su da kansu zasu kawo masa ita, godiya yayi tare da mata sallama.


Da misalin karfe takwas na daren Inteesar tana zaune a ɗakin Gwaggo, bayan anyi mata kwalliya tana zaune cikin riga da zani na atamfa ta lulluɓe jikinta da mayafi, sai ƙamari ke fita daga jikinta, Gwaggo na ƙara mata nasiha Mummy ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Gwaggo ce ta amsa mata sallamar Inteesar sai kuka da take yi.


Gwaggo ce ta ɗaga kai ta kalle ta tare da cewa


"Sanin ya dawo zaku tafi ne?"


"Eh Gwaggo ya ce mu fito"


Kai Gwaggo ta gyaɗa alamar gamsuwa


"To gata nan ku tafi, Allah ya sanya alkhairi, ya kaɗe duk wani sharri da fitina dake tunkarar rayuwarsu, Allah ya basu zuri'a ɗayyiba".


Murmushi Mummy tayi cikin jin daɗin addu'ar da Gwaggo tayi tare da cewa


"Ameen ya rabbil izzati, Allah ya amshi addu'ar ki."


Jan hannun Inteesar tayi dan ta miƙe amma Inteesar bata miƙe tsaye ba ta cigaba da zamanta tana kuka, jin muryar Gwaggo suka yi tana cewa


"Ki tashi ki tafi ɗakin mijinki bana son munafurci, kukan me zakiyi anan wa zakiyiwa kuka? lokacin da aka ce ba zaki koma ba aka kore sa ba ƙofar kitcheen kika rakuɓe kinawa mutane kuka ba?kika nuna kina son komawa ɗakin mijinki ba? sai yanzun za'a kaiki inda kika kika nuna kina so zaki dinga yiwa mutane kukan munafurci."


Mummy ce ta dinga rarrashinta taja hannunta suka fice, bayan ta daina kuka.


Dady ne da kansa yayi driving nasu yayin da Mummy ke zaune a gefensa, Inteesar na bayan Motar, har Dady yayiwa motar key zai ja sai ga Mufida ta ƙaraso a guje ta buɗe murfin motar ta zauna gefen Inteesar.


Kafin Dady yaja motar wayarsa ya ciro tare da lalubo number Muhdeen.


Muhdeen ya gama shiryawa kenan zai fito daga ɗakinsa wayarsa ga soma ruri, ganin Dady ne yasa ya saki murmushi dan yasan akan Inteesar ne, ɗaga kiran yayi tare da cewa


"Assalamu alaikum, barka da dare Dady"


Daga can ɓangaren Dady dake zaune a motarsa ya ce,


"Yauwa barka dai, kana gidan ne?"


"A'a Dady yanzun dai zan tafi gidan."


"To kayi sauri mu haɗu a can gidan dan yanzun zamu kama hanaya."


"To Dady gani nan zuwa."


Bayan Dady ya kashe kiran ne ya ya ja motar suka bar gidan.


Bayan Muhdeen ya gama waya da Dady ne ya nufi ɗakin Sumayya, domin yayi mata sai da safe tunda ba gidan zai kwana ba, tura ƙofar yayi tare da yin sallama.


Kwance take akan gado tayi ruf da ciki, goga fuskarta tayi a jikin filon, tashi zaune tayi tare da ƙaƙalo murmushin yaƙe, ta ce,


"Wa'alaika salam"


Kallo ɗaya yayi mata ya gane tasha kuka, ƙara sawa yayi jikin gadon ya zauna tare da kiran sunanta


"Sumayya"


Kallonsa tayi yadda yasha kyau sai annuri yake fitarwa, take taji wani tuƙuƙuƙin bakin ciki da ya taso mata, zuciyarta sai tafarfasa take sunkuyar da kanta tayi ƙasa tayi dan bata don yaga halin da take ciki, magana ya soma yi


"Kinga dan Allah ki..."


Kafin ya kai ƙarshen zancensa ne ta ɗaga masa hannu alamar dakatarwa, ta kasa magana ƙofar fita kawai ta nuna masa alamar ya fice, mamaki yake kamar ba ita ce ta nuna masa rashin damuwarta game da zancen ba, amma yau gashi yana magana ta kasa jure sauraronsa sai korarsa take,hannu yakai zai taɓa ta sai ta ja da baya ta haɗa hannayenta biyu alamar riƙon sannan ta nuna masa ƙofar fita, hakan yasa ya fita tare da mata sai da safe duk da yasan na amsawa zata yi ba.


Bayan ya shiga mota ya tayar mai gadi ya wangale masa gate ya fice, kai tsaye ya nufi hanyar gidansa, yana driving yana tunanin halin Sumayya bayan ta nuna masa ta sauya ba komai, amma yanzun yaga alamar ba abunda ya canza a tattare da ita, amma ko ma dai mene ne da sannu zai gano komai."


Sumayya kam Muhdeen na fita ta saki kuka mai sauti, pillows dake kan gadon ta kwashe ta dinga jifa da su a ƙasa, bedsheet ma ta yaye shi tayi jifa da shi, idanunta ya sauka akan babban hoton da ke manne a bango ita da Muhdeen suna dariya, tashi tayi ta ciro photon tayi jifa da shi ya tarwatse a ƙasa


Haka duk wani abun fashewa da ke ɗakin dangin su kwalabe da gilashi sai da ta tarwatsa su ta kwanta a saman katifar tana rera kuka.


Kasancewar gidan Muhdeen baida nisa da sabon gidansa, hakan yasa ya riga su Dady isa gidan, ko da yayi horn mai gadin ya buɗe masa gate ya shiga kai tsaye cikin gidan ya nufa, shugarsa falon keda wuya sai yaji horn alamaun Dady sun iso, farin cikin da yake ciki ne ya ninku.


Bayan Dady yayi parking ne suka gaisa da mai gadin dama yasan Dady shi ya kawo sa gidan, bayan sun gaisa da Dady ne suka gaisa Mummy da Mufida Inteesar dai ba magana.


Shiga cikin gidan sukayi Mummy na riƙe da hannun Inteesar, Muhdeen ya buɗe masu ƙofar tare da yi masu iso zuwa cikin falon


Dady da Mummy suka zauna kan kujera, yayin da Muhdeen da Inteesar da Sumayya ke zaune a ƙasa, Muhdeen da Inteesar da Mufida suna zaune a ƙasa , cikin girmamawa ya gaida iyayen nasa suka amsa masa kafin Dady ɗaura da cewa


"Muhammad"


Ɗago kansa yayi ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads