Showing 108001 words to 111000 words out of 149432 words
Chapter 37 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
sai da na farka na ganni a asibiti tare da Mufida."
Daga nan suka saka salati suna jimamin abuda ke faruwa, Dady ne ya ce,
"Anya kuwa Sumayya kanta d'aya?"
Murmushin takaici Jabeer yayi ya ce,
"Kafiyarta k'alau Dady ba abunda ya same ta haka take dama ba k'aramin aikinta bane ta illata mutum, shiyasa na sanar da Muhdeen kada ya had'a su gida d'aya bai saurare ni ba."
Sakin baki Gwaggo tayi tana kallonsa cikin mamaki
"Au dama yasan halinta shine ya had'a su gida d'aya dan ta illata 'yar mutane?"
Dady ne ya kalli Mufida ya ce,
"Tashi ki raka ta d'akinki tayi wanka ta ci abinci."
Mik'ewa Mufida tayi taja hannun inteesar suka shiga cikin d'akinta.
Jabeer ne yayi musu sallama zai koma wajen aikinsa, har ya kai bakin k'ofar ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa
"Koda kun had'u da shi kada ka sake ka sanar da shi tana nan gidan."
Kai ya jinjina alamar to, sannan ya saka kai ya fice abinsa.
Koda Jabeer ya isa asibitin ne ya sallami Umma inda ya ce zai jira su gama tattara kayansu ya kaisu gida, a motarsa ya zauna jiransu, Umman Inteesar ce sai k'anwar ta Mama Huraira, inda ya d'auke su a mota ya kaisu har k'ofar gida sannan ya juyo.
'Bangaren Muhdeen kuwa tunda ya koma gida sai faman safa da marwa yake yi, gaba d'aya ya rasa hankalinsa da nutsuwarsa, ganin yanayin da yake ciki da kuma tunawa da kalamansa da take ne yasa ta kama bakinta tayi shiru bata sake ce masa komai ba, wayarsa ya d'auka ya kira Jabeer, lokacin Jabeer na tuk'in mota ne yayi parking a gefen hanya tare da amsa kiran Muhdeen.
"Assalamu alaikum"
Muhdeen da ke tsaye a falo cikin tashin hankali ya fara magana
"Jabeer ka sallami su Umma ne?"
"Eh na sallame su, yanzun nan ma na kaisu gida na ajiye ina kan hanyar komawa ma yanzun nan"
"Ok su nawa ne ka kai gidan?"
"Su biyu ne"
"Wace da wace?"
"Umma ce sai k'anwar Umma wacce take jinyarta."
"Babu Inteesar a cikinsa?"
"Gaskiya bata tare da su."
"Jabeer akwai matsala wallahi, bansan inda Inteesar take ba na neme ta banganta ba."
Shiru Jabeer yayi kamar baisan komai ba ya ce,
"Ikon Allah, to Allah yasa ka ganta."
Daga nan ya katse kiran, yana shirin tada motar ne ya kuma jin wani kiran .
D'agawa yayi yaji muryar Muhdeen na cewa
"Jabeer magana fa nake maka mai mahimmanci, amma naga baka d'auki maganar serious ba."
"To banda addu'a me zan maka bayan wannan?"
"Haba Jabeer ai da sai kazo ka tayani nemanta muyi duk wani fad'i tashi da zamuyi ko Allah zaisa a ganta, dan Allah kazo gida na gani nan ina jiranka."
"Okay gani nan zuwa"
Daga nan ya katse kiran ya d'auki hanyar zuwa gidan Muhdeen.
Koda ya k'arasa gidan a falo ya same shi kallo d'aya tayi masa yaga har ya fita hayyacinsa, yana ganin Jabeer ya fare magana yana cewa
"Jabeer bata gidan nan kuma na je wajen Ummanta bata can bata je na na je gidanmu ko ta je wajen Mummy da Gwaggo duk sun tabbatar mani da bata nan, ta ina zan fara nemanta, Jabeer inacimin tashin hankali."
"Kallonsa yayi tare da cewa
"Kada ka damu kanka tunda dama ba wai kana k'aunar ta bane, to meye naka na damuwa tunda gaka ga Sumynka abar sonka da k'aunarka, ka manata da waccan kucak..."
Kafin ya kai k'arshen zancensa yaji Muhdeen ya kai masa naushi a baki har sai da bakinsa yayi jini, hankici ya ciro daga aljihunsa yakai wajen sai kuwa ga jini ya gani dariya yayi yana kallon Muhdeen da ke ta huci.
Kasan irin maganar da zaka fad'a mani a bakinka, dama na lura da kai tunda na kira ka nake sanar da kai abunda ya faru da ni naga kai ko damuwa baka yi ba,ina cikin tashin hankali amma kai hankalinka a kwance, yaushe ka zama haka wannnan sam ba d'abi'arka ba ce, ko dabba na ajiye ai ta 'bata zan neme ta ballantana kuma mata ta, wacce nake jinta a yanzu tamkar wani sashe ne na jiki na."
Kallonsa kawai Jabeer yake yana gano irin soyayyar da yake wa Inteesar da zallar k'aunarta a cikin idanunsa, bai ce da shi komai ba illa ya nufi hanyar fita ya kai bakin k'ofar sannan ya juyo ya kalle shi ya ce,
"Akan wannan kalmar da na fad'a akan Inteesar ne ka fad'i haka idan kuma a ce ranar da ka gano cewa wata tayi yunk'urin kashe ta zanso ganin wani irin mataki zaka d'auka akanta."
Sumayya da fitowarta kenan daga d'akinta jin kalaman Jabeer yasa gabanta fad'uwa, zufa ce ta fara keto mata ta fara tambayar kanta me kalaman Jabeer ke nufi, ko dai yasan abunda ya faru ne da Inteesar yasa yayi wannan maganar? me zaisa ya fad'i haka idan baisan komai ba? sannan kuma ina Inteesar take tana raye ko ta mutu? da dukkan alamu Jabeer yasan komai bisa la'akari da kalamansa, gabanta ne ya tsananta fad'uwa musamman da taga Jabeer ya zuba mata ido yana watasa mata wani irin kallon da bata ta'ba ganin ya mata makamancinsa ba, dawowa yayi ya kalle ta ya kalli Muhdeen yana murmushi kafin ya bud'e baki yana ya fara magana.
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DON K'ARIN BAYANI*
09065327995
Love you oll😘😍
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6️⃣2️⃣
Gabanta ne ya tsananta fad'uwa musamman da taga Jabeer ya zuba mata ido yana mata wani irin kallon da bata ta'ba ganin ya mata makamancinsa ba, dawowa yayi ya kalle ta ya kalli Muhdeen yana murmushi kafin ya bud'e baki ya fara magana.
"A gaskiya ina matuk'ar tausayinku daga kai har ita Sumayyar, domin dukkanku ababen tausayi ne."
Daga nan yasa kai ya fice ya barsu suna masa kallon mamaki, yayinda gaba d'aya hankalin Sumayya a tashe yake, tasan dole akwai abunda Jabeer ya sani, shi kuma Muhdeen tambayar kansa yake mai Jabeer yake nufi? dole akwai abunda ke faruwa, Jabeer da idan ya ganni a damuwa shima sai ya shiga damuwa? farin ciki na shima nasa ne bak'in ciki na ma nasa ne, amma yanzun ina cikin damuwa amma shi ko a jikinsa, lallai akwai wani abu a k'asa.
Har k'arfe goma na dare yayi ba Inteesar ba alamunta, Muhdeen kuwa hankalinsa ya fi jirgin sama tashi, ko ruwa bai saka a cikinsa ballantana abinci, ya kira Mufida fiye da sau biyar yana cewa ta kira duk wasu k'awayensu ta tambaye su ko sunga Inteesar, itama Mufidar sai ta nuna masa tashin hankalinta akan rashin ganin Inteesar kamar bata bata san komai ba.
Wasa-wasa har k'arfe sha biyun dare yayi yana nan zaune a falo lokaci ne yaji yunwa ta dame sa tun safe rabonsa da abinci tun na safe, hakan yasa ya nufi fridge ya bud'e robar yoghurt ya sha.
D'akinsa ya nufa ya d'auro alwala tazo yayi sallar nafila, tare da addu'oi Allah ya bayyanar masa da Inteesar, wajen k'arfe uku na dare ne ya yana zaune akan sallaya ya d'an jingina jikinsa da jikin gado a haka barci ya d'auke shi.
Da misalin k'arfe biyar na asuba ya farka daga barcin, toilet ya shiga yayi wanka tare da d'auro alwala, bayan ya saka jallabiyarsa ne ya nufi masallaci.
Misalin k'arfe shida na safe ya fito daga masallaci, yana shigowa kai tsaye ya d'akinsa ya nufa key na motarsa ya d'auka ya fito, motarsa ya tada kai tsaye sai gidan iyayensa, horn yayi mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga yayi parking, dai-dai lokacin da Dady ya dawo daga masallaci, kallonsa Dady yayi ya kauda kansa ya shige cikin gida, tsayawa yayi yana bin Dady da kallo, don iya saninsa idan dai ya shigo gidan nan Dady ya gansa yana tsayawa ne har ya k'araso su gaisa, amma sai yaga yau yayi tafiyarsa, bai kawo komai a rai ba ya nufi cikin gidan shima a falo Dady na k'ok'arin haurawa sama ne ya ji muryar Muhdeen na cewa
"Barka da safiya Dady"
Dakatawa yayi da tafiyar har ya k'araso gabansa, durk'usawa yayi ya gaishe shi
"Ina kwana Dady?"
Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa masa
"Lafiya lau, kai ne da sassaden nan lafiya dai ko?"
"Gaskiya Dady ba lafiya ba har yanzun fa ban ganta ba."
"Wace ce baka gani ba?"
"Dady fa tun jiya na sanar da ku zancen rashin ganin Inteesar, ko ka manta ne?"
"To ka tafi ka cigaba da nemanta har Allah yasa a dace."
Daga nan ya haura sama abunsa ya bar shi nan tsaye sake da baki, mamaki yake yadda mutanen da ya kamata ace sun damu da damuwarsa amma sukayi masa biris da zancen rashin ganin Inteesar d'in.
Zama yayi akan kujera don yasan mutanen gidan ba su kai ga tashi daga barci ba.
B'angaren Sumayya kuwa tunda taga yanayinsa ta da abunda yayi wa Jabeer ta tsorata da yanayinsa, ta kuma shiga fargabar idan Inteesar tana raye ta sanar da abunda ta mata bata san matakin da zai d'auka akanta, zullumin da take kada ya d'auki mummunar mataki akanta na rabuwa da ita, domin kuwa Allah ya sani ita ba zata iya rayuwa babu shi ba, don tana masifar sonsa da kishinsa, wanda hakan yasa ta aikata abunda ta aikata a kansa, kuma yanzu ta gama tabbatar da kanta cewa lallai Muhdeen ya kamu da son Inteesar, Wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba, wani irin sake tayi da har hakan ya faru, haka ta kwana sak'e-sak'e da tunanin yadda zata 'bullowa lamarin.
A can gidansu Mummy kuwa Muhdeen na nan zaune har yaga k'arfe bakwai da rabi yayi ba motsin mutum ko alamar fitowar kowa.
Haka ya cigaba da zama har k'arfe takwasa tayi, Gwaggo ce ta fara fitowa daga d'akinta tana masifa wai har yanzun ba wanda ya fito ballantana ayi haramar shiga kitchen a d'ora breakfast, ganin Muhdeen tayi zaune ya tafka tagumi kallonsa take tana yamutse fuska ta ce,
"Kai kuma lafiya zaka zo ka wani zaunawa mutane gida da sassaden nan lafiya? ka fad'i abunda ya kawo ka ka tafi ka bar mana gida?"
Da mamaki ya tsaya yana kallonta, dan dai baiga abun fad'a ba, daga ganinsa ta fara sabibi bayan tasan halin da yake ciki, tunawa yayi da abuda yayi mata jiya kila shiyasa take masifa, Dan haka ya share ta kamar baiji me take fad'i ba.
"Nace ka tashi ka fita ko?"
"Ni da gidan uba na kike kora ta? to wallahi naki isa ki kore ni na fita sai dai ke ki fita kibarni"
Sakin baki tayi tana kallonsa ta ce,
"Ni da gidan d'a na zaka ce na fita, ni na haife shi da kaina ba wata ba."
"Ko ke kika haife shi baki fini iko da gidan nan ba gidan uba na ne, nine magajinsa."
Cikin d'aga murya ta ce
"Sannu magaji, na ce, sannu magaji, to bari kaji gidan uban da kake tak'ama da shi to zansa yanzun uban naka ya fitar da kai, idan kuma kana musu ne ka zuba ido ka gani."
Dai-dai lokacin Mummy ta fito daga d'akinta, ganin Muhdeen yasa ta d'aure fuska, tsayawa tayi ta zuba masa ido.
Durk'usawa yayi ya ce,
"Mummy ina kwanan?"
"Lafiya lau"
"Mummy baki ji labarin ta ba?"
",Labarin me kenen?"
"Mummy kada dai ace kema kin manta da maganar 'yar ta ki."
"Ban manta ba ya ake ciki ne? An ganta me?"
Girgiza kai yayi cikin damuwa kafin ya ce,
"Mummy ina cikin tashin hankali sosai, Na kasa cin abinci na kasa barci, yanzun ta ina zan fara nemanta?na sanar da Mufida tayi cigiyarta wajen k'awayensu bata nan in zan same ta?"
Mummy dai zuba masa ido tayi tana kallonsa, ganin bata ce komai ba ne yasa ya ce,
"Ko na koma na sanar da Ummanta halin da ake ciki ne? sai ta tayamu bincikawa wajen 'yan uwanta, a binciko ta."
Girgiza kai Mummy ta tayi tare da cewa
"Kada ka sanar da Ummanta ka d'aga masu hankali."
Kai ya jinjina alamar gansuwa sannan ya ce,
"To shikenan zanje gidan kaaai na gaishe ta, idan tana nan shikenan idan bata nan banganta ba sai na sallame su kawai na nar gidan."
Kai kawai ta jinjina masa ba tare da tayi magana ba ta nufi kitchen.
Hararar Gwaggo yayi tare da yin tsuki ya mik'e ya nufi k'ofar fita, kallonsa tayi tare da cewa
"Kayiwa uwarka gata can ta shiga kitchen, mara kunyar banza mai k'irar yahudu da nasara."
Duk maganar da suke a kunnen Inteesar dama ba barci take ba, tunda ta idar da sallar asuba tayi azkar bata kwanta ba fitowa tayi da niyyar shiga kitchen sai, sai ganinsa tayi zaune a falo da sauri ta juya ta koma cikin d'akin Mufida ba tare da ya ganta ba, bayan shigarta ne ba jimawa Gwaggo ta fito.
Bayan ta ji fitarsa ne ta fito faga cikin d'akin, zata durk'usa ta gaida Gwaggo sai Gwaggo tayi sauri jan hannunta ta mik'e tsaye,
"Kinga 'yar albarka ta shi ba sai kin wahalar da kanki ba, fatan kin tashi lafiya? ya jikin naki?
Cikin sanyin muryarta ta ce,
"Lafiya lau da sauki' naji muryarsa ya zo gidan nan Gwaggo dan Allah ka da ku maidani gidansa"
Ta k'arasa maganar cikin rawar murya kamar wacce zata saka kuka, dafa kafad'arta Gwaggo tayi tare da cewa
"Ki kwantar da hankalinki ba mai maida ke gidansa kinji."
Jinjina kai tayi alamun gamsuwa ta ce
"To nagode"
Daga nan ta nufi hanyar kitchen.
Jin muryar Gwaggo tayi tana cewa
"Ina kuma zaki je?"
"Zanje na gaishe da Mummy ne"
Daga nan ta nufi kitchen d'in inda ta samu Mummy na fere dankalin turawa, Mummy na ganinta ta sakar mata murmushi ta ce,
"Daughter kin tashi"
Itama murmushi ta sakar mata zata durk'usa Mummy tayi saurin cewa
"A'a Daughter tashi dan Allah"
"Ina kwana Mummy"
"Lafiya lau Daughter ya jikinki"
"Naji sauk'i Mummy"
"Ina ke maki ciwo yanzun?"
"Bakomai Mummy, ba wurin da ke mani ciwo?"
"Kin tabbata"
"Eh Mummy"
"To alhamdulillah haka nake son ki"
K'ok'arin karb'ar wuk'ar take ne sai Mummy ta hana ta tace
"Daughter kije ki kwanta ki huta"
"Mummy kinsan ban saba kwanciya da safe ba idan ba aiki mayi ba, dan Allah ki kawo zan iya."
Mik'ewa Inteesar tayi ta nufi wajen gas don duba ruwan shayin da ta d'ora, Gwaggo ce ta shigo kitchen d'in ganin Inteesar na aiki yasa ta saki salati.
"Fatima saboda rashin tausayi yarinyar da d'anki ya gama azabtar da ita daga fardad'owarta kuma sai ki sakar mata aiki? wannan ai rashin tausayi ne muraran."
"Gwaggo ba laifinta bane ta hanani nice na matsa mata dole ta barni."
"Saboda baki tausayin kanki da kanki ko?"
"Gwaggo wallahi zan iya kibarni nayi."
"Sai kiyi tayi ai"
Daga nan ta saka kai ta fice, Mummy dai uffan bata ce ba don inda sabo ta saba da halin Gwaggo.
Muhdeen kuwa da ya d'auki motarsa ya bar gidan, kai tsaye gidansu Inteesar ya tafi, koda ya shiga a zaure ya samu Abba yana karatun al'qur'ani mai girma, bayan ya kai k'arshen ayar da yake karantawa ne ya rufe tare da ajiye shi gefen tabarmar da yake zaune, durk'usawa yayi bayan yayi sallama
"Ina kwana Abba"
"Muhammad kai ne da safen nan? ka tashi lafiya?
"Lafiya lau Abba"
"Masha Allah, ya kwanan iyali?"
"Lafiya lau"
"Masha Allah"
Shiru yayi ya kada magana, har abba yayi magana ya ce,
"Bari na shiga na duba ko Umman ta tashi sai ku gaisa."
"To Abba"
Daga nan Abba ya mik'e ya nufi cikin gidan, ya tarar da Umma ta fito daga d'akinta kenan zata hura huta,kallonsa tayi tace,
"Mallam ka shigo ne"
"Eh ga Muhammad nan zai gaishe ki."
"Wani Muhammad d'in"
"Surukinki mana"
"Murmushi tayi tare da cewa
"Tare da Inteesar suka?"
"A'a shi kad'ai na gani"
Daga nan ya koma zaure inda suka shigo tare Muhdeen na bunsa a baya, suka tarar har Umma ta shimfid'a masu tabarma, durk'usawa yayi ya ce,
"Ina kwana Umma?"
"Lafiya lau Muhammad"
"Ya k'arfin jiki?"
"Jiki Alhamdulillah naji sauk'i"
"Masha Allah Allah ya k'ara lafiya"
"Ameen ka zauna mana"
Zama yayi gefen tabarmar kansa a k'asa, muryar Abba ya ji yana cewa
"Sannu da k'ok'ari fa mungode da d'awainiyar Asibiti, Allah ya saka da alkahiri."
"Bakomai Abba addu'a da sanya albarka kawai nake nema daga gare ku"
Murmushi kawai Abba yayi tare da cewa
"Ai kullun cikin yi maku addu'a muke Allah ya albarkaci rayuwarku ya kare ku daga sharrin abun k'i yasa ku gama da duniya lafiya."
Murmushi yayi tare da jin dad'in addu'a da Abba yayi masu Umma ce ta amsa da Ameen, shiru ne ya biyo baya, inda muryar Umma ta katse shirun da cewa
"Halan Inteesar bata san zaka zo nan ba?"
Zuciyarsa ce ta tsinke ya rasa me zai ce, amma tuna zancen Mummy da tayi masa da gudun kada hankalin iyayenta su tashi yasa ya k'ak'alo murmushi ya ce
"Bata sani ba Umma"
"Ayyah nasan da ta sani zata dame ka, ka kawo ta."
Fira suka d'an ta'ba daga nan yayi masu sallama ya tafi.
Yana driving gaba d'aya hankalinsa a tashe yake ya rasa inda zai saka kansa yanzun ya gama tabbatar wa da kansa cewa bata gidan Ummanta, kai tsaye gidansu ya koma.
Suna kitchen sun kammala aikinsu dai-dai lokacin da Inteesar ta fito daga cikin kitchen d'in d'auke da faranti da aka jera foodflask a ciki tana fitowa daga kitchen d'in ta nufo falo, dai-dai lokacin da Muhdeen ke shigowa ya juya falon ya maida k'ofar ya rufe.
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*DON K'ARIN BAYANI*
09065327995
Love you oll😘😍
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6️⃣3️⃣
Suna kitchen sun kammala aikinsu dai-dai lokacin da Inteesar ta fito daga cikin kitchen d'in, d'auke da