Showing 102001 words to 105000 words out of 149432 words
Chapter 35 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
tare da yin parking suka fito, mai gadin ya gaishe su basu ma tsaya kula shi ba suka nufi cikin gidan.
Da sallma suka shiga ba kowa a falon, d'akin Inteesar suka nufa nan ma bata nan, suka duba kitchen bata nan, wayar Muhdeen Mummy ta Kira a kashe don haka ta d'an jira tsawon mintuna goma ba alamar motsi yasa Mufida ta ce
"Kodai basu nan be?"
Mummy ta kalle ta ta ce,
"Ina inteesar zata je da safen nan?"
Mufida ta mik'e tare da cewa
"Bari na duba d'akin yaya ko yana ciki."
Kai kawai Mummy ta gyad'a mata, yayi da ta nufi d'akin Muhdeen, knocking tayi har sau uku shiru, kawai sai ta tura k'ofar ta shiga idanunta ya sauka akan Inteesar dake kwance a sume kanta na zubar da jini, K'ara ta saki Wanda ya razana Mummy ta nufi d'akin da sauri, idanunta ya sauka akan Inteesar k'araswa tayi tare da tallabota idanunta na zubda hawaye tana kuka tana jijjiga ta Mufida ma kuka take yi tana Kiran sunanta bata motsi bata numfashi, ruwa ta umarci Mufida da ta kawo mata da sauri ta k'arasa ta bud'e fridge dake cikin d'akin ta d'auko goran ruwa ciki ta kawowa Mummy, kar'ba tayi ta yayyafa mata mata shiru ba numfashi,sau hud'u tabna zuba mata ruwa shiru.
Wayar ta ta duba ta laluno number Jabeer tare da kiransa, fitowarsa kenan daga d'akin tiyata yana kunna wayar sai ga Kira Mummy, d'agawa yayi ko jira batayi yayi magana ta ce
"Jabeer kana ina?"
"Ina asibiti Mummy"
Kayi sauri kazo ka same ni a gidan son kuma kada ka sanar da shi kazo kawai yanzun nan ba sai anjima ba."
Kashe wayar yayi ya nufi motarsa yana tambayar kansa ko me ke faruwa yaji muryar Mummy kamar tana kuka, figar mota yayi tare da barin asibitin, gidan Muhdeen ya nufa, Mummy ce tayi wani tunani ta ce kada ya shigo ciki ya tsaya d'an nesa da gidan gasu nan zuwa, sai kuma ta share hawayenta tare da k'ok'arin dai daita nutsuwarta sannan ta fita waje ta umarci mai gadin da ya je bakin titi ya siyo mata bottle of water mara sanyi na gidan duk sunyi sanyi yaje can bakin tati ya siyo a can, tunda yasan Mahaifiyar mai gidansa ne yasa ya tafi yabar gidan.
Yana fita ta umarci Mufida ta taimaka mata su d'auki Inteesar su tafi da ita, haka kuwa suka kama ta suka fita Direban Mummy ne yana ganinsu yayi saurin bud'e masu bayan motar suka kwantar da ita.
Komawa sukayi cikin gidan suka share fasassun kwalbar suka zuba a mazubin shara suka goge wajen suka tsaftace shi sannan suka janyo k'ofar suka fito suna fitowa sai ga Direban Muhdeen wato Ishaq ya dawo tare da Mai bawa fulawoyin gidan ruwa, gaishe da Mummy sukayi ta amsa cikin nitsuwa kamar ba abunda ya faru, dai-dai lokacin da mai gadin ya dawo, ya kawo mata ruwan ta ce ya barshi suyi amfani da shi an Kira ta suna sauri zasu tafi, shiga motar sukayi direbanta yaja suka bar gidan akan hanya suka had'u da Jabeer yana ganin su ya fito daga motarsa ya k'arasa wajen motar,Mufida ce a gefen dieban Mummy ta zauna baya ga Inteesar kwanace a gefenta, ya bud'e baki zai gaida Mummy idanunsa suka sauka akan Inteesar zaro ido waje yayi tare da cewa
"Shbhanallah, me ya same ta haka?"
"Shine dalilin kiranka, yanzun ba lokacin bayani so nake ka kaimu wani waje da zaka kula da ita kayi abunda ya dace ko Allah zaisa a samu kanta."
"Gaskiya sai dai mu kaita asibiti"
"Wane asibitin?"
"Asibitin mijinta mana."
Kai Mummy ta girgiza alamun a'a sannan ta ce,
"Ba za'a kaita asibitinsa saboda bana son yasan halinda da take ciki."
Da mamaki Jabeer yake kallonta
"Saboda me Mummy?"
"Yanzun ba lokacin da zamu tsaya dogon magana bane, ina son wajenda bazai san halin da take ciki ba."
Shiru yayi tare da nazari sannan ya ce,
"To mu kaita asibitin aboki na"
Ciro wayarsa yayi daga cikin aljihu sannan ya kira Doctor Salim, bayanin abunda zai kawo yayi masa sannan ya kalli Direban Mummy tare da bashi umarnin ya biyo shi a baya, daga nan ya shiga motarsa tare da yi mata key yabar wajen, Direban Mummy ya bi shi a baya suka bar unguwar.
Suna isa Asibitin da Doctor Salim yake aiki suka tarar da shi a harabar asibitin yana jiran k'arasowarsau, cikin k'anka'anun lokaci aka shigar da ita d'akin da Doctor Salim ya umarce su, nan ya kwantarwa da su Mummy hankali ya ce su jira tukunnah.
Nan suka tsaya suna jira har tsawon awa biyu kafin Doctor Salim ya fito ya same su, ya sanar da su cewa sunyi duk k'ok'arin da zasuyi amma har yanzun bata farfad'o ba, doguwar suma tayi zata iya fardad'owa ko wane lokaci.
Dai-dai lokacin Jabeer ya fito tare da wani Doctor d'auke da kayan aiki, Jabeer ne ya kalli Mummy ya ce,
"Mummy ki kwantar da hankalinki, insha Allah zata dawo hayyacinta,anan za'a kula da ita zaku iya tafiya gida anjima kundawo, koda kun tafi akwai nursess d'in da zasu kuka da ita."
Girgiza kai tayi tare da cewa
"Jabeer bazan iya tafiya nabarta ba."
"Mummy ba yanzun zata farfad'o ba gara ki tafi tukunnah idan yaso sai kibar Mufida ta tsaya, don nima zan koma can Asibiti zuwa d'an anjima zan dawo."
Yana kaiwa k'arshen maganarsa kafin Mummy tayi magana wayarsa ta soma ruri, cirowa yayi yaga Muhdeen ne, don haka ya kalli Mummy tuna cewa ta ce bata san yasan da zancen, hakan yasa ya d'aga wayar tare da cewa
"Doctor ya akayi ne?"
Daga can 'bangare Muhdeen ya fara magana yana cewa
"Wai ina ka shiga ne tun d'azun ka fita daga Asibiti baka dawo ba kuma naka sanar da ni ba."
"Am not sure zan iya sanar da kai inda naje, amma dai gani nan zuwa yanzun nan."
Tsuki Muhdeen yayi tare da katse kiran ya cigaba da duba patient d'insa."
Jabeer ne ya kalli Mummy bayan sauran Doctors sun tafi ya ce,
"Wai garin yaya akayi hakan ta faru?"
Girgiza kai tayi tare bawa Jabeer labarin komai da ke faruwa kamar yadda Mufida ta sanar da ita.
Ransa yakai matuk'ar'baci da jin zancen don kwata-kwata baiyi tunanin hakan ba, ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"To waye ya dake ta akai haka?"
"Allah masani sai dai idan ta farfad'o ta sanar damu."
"To Allah yasa haka"
Daga nan yayi masu sallama akan anijima zai dawo, ya tafi zuwa Asibiti.
Wayar Mummy ce tayi ringing ta duba taga Dady ne ke kiranta, d'agwa tayi tare da cewa
"Assalamu alaikum"
Daga can 'bangaren kuwa Dady ne da Gwaggo zaune a falo, jin Mummy ta d'aga wayar ne ya ce,
"Wai ina kika tafi ne tun safe gashi har k'arfe goma sha biyun rana, kuma kun fita baku sanar da kowa inda zaku tafi ba."
'shiru tayi tana nazari idan ta sanar da shi cewa ga abunda ya faru da Inteesar anya zai giyi bayan hukuncin da tayi niyyar d'auka akan Muhdeen kuwa? kada tazo ta sanar da shi yazo yak'i bin bayan hukuncin da zata yanke akai, hakan kuma zai iya bata matsala, don hukuncin da tayi niyyar yankewa k'arshenta bazaiwa kowa dad'i ba, kuma tasan Dady yana da sauk'in kai, zai iya lalata mata k'udirinta don haka ta ce,
"Yanzun zan dawo na tafi dubiya ne"
"Okay Mahaifiyar Inteesar ko?"
"Eh ita"
"To ki gaishe ta nima jiya daddare naje, Allah ya bata lafiya"
Daga nan ta katse kiran ta kalli Mufida ta ce,
Zan tafi gida yanzun duk abunda ake ciki ki kirani a waya ki sanar dani, sannan naga restaurant a nan kuda da su yakamata ki nemi abunda zaki ci, koda take bari nasa Direba ya kawo maki takeaway."
Daga nan ta tafi Mufida ta samu wuri ta zauna.
A 'bangaren Muhdeen kuwa yana zaune a office d'insa gaba d'aya kewarta yake, yana tunanin daren shekaranjiya da ya fara kusantarta yana farin ciki da nishad'i shi kad'ai, don Allah Allah yake ya koma gida ya ganta, gaba d'aya tunaninta ya addabe shi, ji yayi gaba d'aya bazai iya hak'uri ba sai yaje gare ta, don haka ya mik'e don komawa gida ya ganta ko zai samu nutsuwa.
Sai da ya fara zuwa d'akin da aka kwantar da Umman Inteesar d'in, shiga yayi ya gaishe ta a karo na biyu, daga nan ya nufi motarsa don komawa gare ta
Yana k'ok'arin bud'e motar ne sai ga Jabeer ya k'araso wajensa, kallon Jabeer yayi tare da cewa
"Daga ina haka?"
Dariya Jabeer yayi tare da cewa
"Naji kewar matata ce shine zanje naganta."
Dariya Muhdeen yayi lokacin da shima ya tuno da Inteesar d'insa
"Kaidai ka sani sauk'in abun ma nima Ina da tawa, yanzun haka wajenta zanje don gaskiya yanzun nasan dad'in aure wallahi don haka da na tuno da ita naji na kasa hak'uri sai naje na d'an kwashi gara tukunnah, wata kila ma sai gobe dan bana jin zan samu lokacin dawowa."
Murmushin takaici Jabeer yayi don a tunaninsa akan Sumayya yake magana baisan akan Inteesar bane, don haka sharesa kawai yayi yabar wajen, bunsa da kallo yayi tare da ta'be baki yaja motarsa yabar wajen.
Koda ya isa bakin gate horn yayi mai gadi ya wangale masa gate, shiga yayi bayan yayi parking ya fito fuskarsa d'auke da annuri, duk Wanda ya kallesa yasan yana cikin farin ciki.
Kai tsaye d'akinsa ya nufa ganin ba kowa a falon, ba Sumayya ba Inteesar, kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet don yin wanka, bayan ya fito ya ya shafa turare mai dad'in k'amshi, k'aramar riga ya saka da wando 3 quarter.
Shikad'ai yake magana kamar yanayi da wani yana cewa
"Bansan yaushe ne ki kuma wani lokaci bane na kamu da sonki, bani da burin da ya wuce na ganni gani gaki, ina jinki tamkar wani sashe na jiki na idan na kasance tare da ke har farin ciki nake ji a cikin raina."
Haka ya dinga magana shi kad'ai har ya gama shirinsa ya fito don zuwa d'akinta, yana fitowa ne yayi kici'bis da Sumayya tana dawowa daga waje, kallo d'aya yayi mata ya kauda kansa ya nufi d'akin Inteesar, ganin haka yasa Sumayya ta k'arasa da sauri ta rungume sa ta baya tare da d'ora ha'barta a kafad'arsa cikin kirsa ta fara magana tana cewa
"Washh baby nagaji wallahi tun jiya da na fita ban dawo ba sai yanzun duk a gajiye nake baby yunwa ya addabe ni me yarinyar nan ta girka muna ne?"
Baice da ita komai ba illa ya janye ta daga jikinsa yayi tafiyarsa, murmushin mugunta tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya nufi d'akin Inteesar.
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love you oll😘😍
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by ✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page5️⃣9️⃣
Baice da ita komai ba illa ya janye ta daga jikinsa yayi tafiyarsa, murmushin mugunta tayi ta nufi d'akinta, shi kuma ya nufi d'akin Inteesar.
Da sallama ya shiga d'akin bayan ya tura k'ofar, bata cikin d'akin dan haka sai ya zauna a bakin gadon yana jiranta don a tunaninsa tana toilet ne, har tsawon mintuna goma bata fito ba kuma baiji alamun motsin mutum ba, dan haka ya tashi ya k'arasa k'ofar toilet d'in bata ciki tsayawa yayi ya k'arewa d'akin kallo komai tsaf abun sha'awa sai k'amshi ke tashi, murmushi yayi sannan ya fita d'akin.
Kai tsaye kitchen ya nufa nan ma bata ciki har store ya duba bata nan, mamaki ne ya kama sa ina zata je ita da bata zuwa ko ina kullun tana gida to ina ta shiga ne?
Haka ya dinga duba cikin gidan nan duka d'akunan gidan lungu da sak'o ba inda bai neme ta ba amma bai ganta ba, haka ya bincike gidan nan gaba d'aya ba Inteesar ba alamarta, fita harabar gidan yayi ya samu mai gadi da Ishaq Direba da mai bawa filawa ruwa suna fira.
"Cikinku akwai wanda yaga fitar matar gidan nan?"
Girgiza kai mai gadin yayi tare da cewa
"Hajiya Babba dai tun jiya da ta fita yanzun ta dawo, amma Hajiya k'arama banga fitarta ba gaskiya."
Shiru Muhdeen yayi yana nazari duk ya bincike gidan nan amma bata nan, kuma mai gadi baiga fitarta ba, juyawa yayi ya kalli sauran ma'aikatan gidan ya tambaya su ko akwai Wanda yaga fitarta kowa ya ce bai gani ba, dubansa ya maida wajen mai gadin ya ce,
"Kuma ba wanda yazo gidan nan yau?"
"Eh to Mahaifiyarka tazo ita da k'anwar ka da safe."
"Akan idonka suka fita?"
"K'warai kuwa akan Ido na suka fita."
"Basu fita tare da ita ba?"
Nan sauran ma'aikatan gidan suka tabbatar da suna dawowa Mummy zata fita kuma ita kad'aice suka hangeta a bayan motar, sai Mufida dake gefen Direban.
Haka ya juya ya koma cikin gidan, kai tsaye d'akinsa ya nufa ya shige tare da zama a bakin gadon, zamansa kenan sai ga Sumayya ta turo k'ofar ta shigo, zama tayi gefensa tare da rik'o hannunsa cikin nata ta fara magana
"Ya naganka haka kamar kana cikin damuwa?"
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce,
"Wani lokaci kika dawo gidan nan?"
Kwantar da kanta tayi a gefen kafad'arsa ta zagayo da hannunta d'aya ta bayansa ta rungume sa d'ayan hannun kuma tana rik'e da hannunsa ta fara magana
"Dawowa ta fa kenan naganka kana k'ok'arin shiga d'akin Amaryarka, gashi naga bata girka muna komai ba yau kuma yunwa nake ji."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Nima tunda na dawo nake nemanta bansan ina ta shiga ba."
Gaban Sumayya ne ya fad'i jin maganarsa don ita dai ta san da cewa ta barta kwance matacciya kodai bata mutu bane? ko kuma dai ta rayu ne, to idan bata mutu ba ai da anganta a cikin gidannan amma shiru? meke faruwa ne? haka take ta tunani tare da anyyana abubuwa dayawa a cikin zuciyarta, ganin yadda ta fad'a duniyar tunani ya tambaya ta
"Tunanin me kike yi ne?"
Murmushi tayi tare da k'ara narkewa a jikinsa ta ce
"Bakomai, kada ka damu maybe wani uzurin ne yasa ta fita."
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Ba uzirin da zaisa ta fita kai tsaye ba tare da sani na ba."
"Ok to Allah ya dawo da ita lafiya."
"Ameen"
"Baby nayi missing naka fa, amma kai naga kamar ba kayi missing d'ina ba, ada baka iya kwana biyu baka neme ni ba amma yanzun kwana biyu shiru baka ma damu da ni ba, ko a jikinka ni gani nake ma kamar ba kai ba wallahi, ka canza mun."
Zura hannayenta tayi cikin rigarshi ta fara shafar kwantaccen gashin k'irjinsa tana shafawa, wani yarrr yake ji a jikinsa take yanayinsa ya sauya, ganin hakan yasa ta saki wani shu'umin murmushi, ganin tana son sashi cikin wani yanayi ne yasa ya ce mata,
"Pls ki bari, bana cikin yanayin a yanzun so nake nasan halin da Inteesar take ciki."
"Kada ka damu ita ba k'aramar yarinya bace, duk inda ta je zata dawo mana cikin k'oshin lafiya."
Ya bud'e baki da niyyar magana kenan tayi saurin saka bakinta cikin nasa ta fara tsotsa kamar ta samu sweet, hannunta na cikin rigarsa tana masa tafiyar tsutsa, baisan lokacin da ya fara maida mata da martanin abunda take masa ba,dama ba wata rigar arziki ce a jikinta ba, nan danan ya raba ta da kayan jikinta anan ya k'ara tabbatar wa da kansa cewa lallai mata suna suka da kafin ya fara ganin surar jikin Inteesar idan yaga jikin Sumayya burge shi take amma tunda yaga suffar jikin Inteesar sai yaga yanzu jikin Sumayya ba komai bane, dan fatarta bai kai na Inteesar laushi da shek'i da santsi ba, haka breast d'inta ma bai kai na Inteesar girma da laushi ba uwa uba tsayuwa don breast d'in Inteesar a cike suke kamar an hura balon-balon kuma a tsaye kem basu rankwafa ba bare su zube, ita kuma Sumayya nonuwanta k'ananu ne irin masu tsawon nan dan har sun d'an rankwafa.
Haka suka dinga wasanni da junansu daga nan suka afka duniyar ma'aurata, ya d'an samu gamsuwa d ita amma bai kai gamsuwar da ya samu da Inteesar ba, dan ko baiyi sex da Inteesar ba iya wasa kawai yana samun gamsuwar da ko yayi sex da Sumayya baya samunta, lallai Allah ya mata baiwar ni'ima.
Bayan sun samu nutsuwa ne ya tashi ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa.
Ita ko kwanciyarta tayi don dama sai yayi fama da ita kafin tayi wanka kullun haka suke ya zama jiki.
Bayana ya canza kaya ne ya kalle ta tare da cewa
"Ki tashi kije kiyi wanka lokacin sallar la'asar tayi, daga masallaci zan tafi asibiti naji ki ta tafi wajen Ummanta ne, idan kuma bata nan zanje gida ko ta tafi wajen Mummy da Gwaggo."
Bayan an idar da sallar la'asar daga masallaci asibiti ya koma, kai tsaye ya nufi word d'in da aka kwantar da Umma a can, Jabeer na k'ok'arin fitowa daga d'akin shi kuma yana k'ok'arin shuga ciki, komawa baya yayi don yana son magana da Jabeer d'in, kallonsa Jabeer yayi tare da cewa
"Har ka dawo ne angon Sumy?"
Kauda kansa yayi kamar baiji shi ba, Jabeer ya cigaba da cewa
"Kazo ganin surukanka ne ko? jikin nata da sauk'i insha Allah gobe za'a sallame ta."
"Ni duk ba wannan ba, a cikin nan da ka fito kaga Inteesar a ciki ne?"
Kallonsa Jabeer yayi tare da cewa
"Wata Inteesar d'in?"
"Ya ina tambayarka kana dawo mani da tambayar rainin wayo, wace Inteesar kasan zan tambaya bayan matata."
"Au haba dama kana da mata Inteesar ce?ai na d'auka Sumayya ce kawai matarka Inteesar kuwa 'yar aiki ce a wajenku."
Baida lokacin jurara maganganun Jabeer d'in don haka sai ya shige cikin d'akin dan bazai iya jurar maganganunsa ba.
B'angaren Mummy kuwa koda tabar Mufida a Asibiti gidan ta nufa, inda ta tarar da Dady da Gwaggo suna zaman jiran dawowarta, koda Gwaggo ta ganta ta fara sababi tana cewa
"Wannan wani irin mugun hali ne kike so ki d'auko Fatima? kibar gidan nan tun sassafe ko abinci na baki