Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 149432 words

Chapter 13 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1363

Ads at the middle of Article

suka amsa masu.Nan dai akayi siyen baki inda abokan ango suka wuce da k'awayen amarya.Ko rakiya bai masu ba suna ta tsokanarsa suka wuce.haurawa yayi Kan gadon ya yaye mayafin yadda zai ga fuskarta dakyau.Murmush take tayi domin burinta ya cika na auren Muhdeen kullum fatanta kenan tana sonsa sosai.kitchen ya nufa ya d'auko plata da kofuna guda biyu ya k'araso ya bud'e ledar, kaji ne bank'ararru guda biyu sunji gashi Mai kyau kuwa.d'aya ya d'auka yasa a plate d'in ya tsiyaya fresh milk a baki ya dinga bata tana ci tana shan fresh milik d'in har ta k'oshi.ya kwashe kayan ya Kai kitchen sannan ya dawo ya umarceta da ta shiga tayi wanka ta d'auro Alwala suyi sallah daga nan ya fice zuwa d'akinsa.


Zuciyarta cike da farincikin mallakarsa a matsayin mijinta, mi'kewa tayi ta cire kayan jikinta ta fad'a toilet don yin wanka.Bayan ta fito ta goge jikinta ne da k'aramin towel,ta shafa lotion da turare ta saka riga da wando na barci don dama ta d'auro alwala hijab kawai ta saka ta shimfid'a masu sallaya tana zaman jiransa


Zamanta bada jimawa ba ya shigo sanye da farin jallabiya a jikinsa.Jansu sallah yayi inda sukayi raka'a biyu,bayan sun idar ya dad'e yana masu addu'a kafin suka shafa.Goshinta ya rik'e tare da addu'a kafin suka nad'e sallayar.Zama tayi bakin gado yayimda shi kuma ya haura saman gadon light d'in d'akin ya kashe kafin ya cire jallabiyar jikinsa.


"Bakyajin barci ne kika zauna?ko gadina kike yi?"


Kwanciya tayi daga d'an nesa dashi,janyota yayi zuwa jikinsa kai tausassun le'b'bensa yayi a kan goshinta ya sunbaceta a goshi.Lumshe Idanuwanta tayi sakamakon jin tausasan le'b'bensa a goshinta tsintan kanta tayi cikin wani irin yanayi na nishad'i.Shafar gefen fuskarta yayi har zuwa kan wuyanta a hankali ya fara 'balle boturan gabar rigarta kasa hanashi tayi cikin hikima ya rabta da komai na jikinta tare da sumbatar kowane sashe na jikinta.A hankali yake shafa sassan jikinta tare da yi Mata tafiyar tsuka, wani abu Sumayya takeji tun daga tafin hannunta har tsakiyar kanta,la'b'banta kuwa sai tsotsonsu yake kamar ya samu sweet.A daren dai sai da ya mayar da Sumayya cikakkiyar mace.








Daga Alk'alamin✍️


Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)






09065327995










Love u oll😘😍




Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*






Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)












*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta cowace siga.






Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa.








Page2️⃣6️⃣




Wani abu Sumayya takeji tun daga tafin hannunta har tsakiyar kanta, la'b'banta kuwa sai tsotsonsu yake kamar ya samu sweet.A daren dai sai da ya mayar da Sumayya cikakkiyar mace.




Bayan awa d'aya ya samu nutsuwa ne ya janyota ya rungume yayinda take ta matsan k'walla.Toilect ya shiga ya had'a mata ruwan wanka sannan ya taimaka mata ta tashi ya kaita toilet inda sukayi wanka.


Shi da kansa ya yaye zanin godon inda ya shimfid'a masu wani.ya janyota jikinsa nan da nan barci ya d'aukesu.


Kiran sallar asuba ya farkar dashi daga barcin da yakeyi.Tashi yayi ya nufi d'akinsa, toilet ya shiga ya sake watsa ruwa ya Sanya jallabiya ya biya ta d'akin Sumayya ya tayar da ita domin tayi sallah.Masallaci ya nufa,sai da aka idar da sallah ya dawo.Kai tsaye d'akinta ya nufa ganinta yayi tana barci da dukkan alamu ma bata tashi tayi sallah ba.Tashita ya sakeyi domin har gari ya fara haske dakyar ta tashi ta shiga toilet,Don bata saba sallar asuba ba ko a gidansu idan tana barci ba'a tashinta idan tana barci ko lokacin sallah ne kuwa,don sallar ma sai taga dama takeyinta idan bata ga dama ba kuwa sai dai Allah ya kar'ba.


A can gidan Mummy kuwa tunda su Inteesar suka idar da sallar asuba su Mufida da Azeeza suka koma suka cigaba da barcinsu, Inteesar kuwa azkar tayi sannan ta mik'e ta nufi kitchen don tasan akwai bak'i a gidan hakan yasa taje don had'a breakfast.Kasancewar tana da zafin nama wajen aiki a cikin k'ank'anin lokaci tayi rabin aikin,don Koda Aunty Maryam k'anwar Dady ta shigo k'araso kitchen d'in k'amshi kawai ke tashi kusan a tare Aunty Maryam ta shigo tare da Mummy.sunji dad'in ganin Inteesar a kitchen tana aiki cikin girmamawa Inteesar ta gaishesu,suma suka amsa mata cikin jindad'i.Lokaci d'aya Inteesar ta shiga ran Aunty Maryam.Had'a hannu sukayi su uku zuwa k'arfe takwas sun gama shirya breakfast kala-kala Inda aka jera wasu a dinning table sauran kuma aka kai d'akunan da Bak'i suka sauka inda Aunty Maryam ta jera wasu a basket tace akai gidan Muhdeen.Mummy ce ta kalli Inteesar ta ce,


"Ina Mufida ce tazo direba ya kaiku,gidan Amarya ku Kai masu breakfast."


Inteesar ta ce,


"Suna can suna barci bari naje na tayar da ita."


Fita tayi daga kitchen d'in Kai tsaye ta nufi da'akin Mufida.koda ta shiga duk suna barci tayar da Mufida tayi ta sanar da ita sak'on Mummy.Yamutse fuska sannan ta sanar da Inteesar cewa bari tayi wanka ta shirya.


"Har sai kinyi wanka?nima fa banyi wankan nan ba dogon Hijab kawai zan saka mu tafi."


"Ke da Zaki iya lullu'be jikinki da hijabi kenan ba Wanda yasan ya kayan jikinki ya ke ba,amma ni da ba hijab zan saka ba fa?haka zan fita a ganni da rigar barci ba."


Daga nan Inteesar ta fita ta sanar da Mummy cewa Mufida zatayi wanka ta shirya in da Mummy ta ce,


"Ba ta yi wanka ba dama?ita da take dad'ewa a bathroom ne zamu tsaya jira?"


Kallon Inteesar tayi tare da cewa,


"Daughter Kinga bari in sanar da Ishaq direba ya kaiki,don nasan har zaku je ku dawo bata gama wanka ba."


Gaban Inteesar ne ya fad'i jin cewa wai ita kad'aice zata je gidan wancan mugun da sassafen nan,domin ita a rayuwarta ba mutumin da ta tsani ganinsa sama da Muhdeen,gashi kuma ba zata iya yiwa Mummy gardama ba ki ta kawo Mata wani uzurin.Bata da za'bi dole haka ta kar'bi basket d'in breakfast hannun Aunty Maryam inda Mummy ta rakata har harabar gidan.Nan ta sanar da Ishaq cewa yakai Inteesar gidan Muhdeen idan ta shiga ya jirata har ta fito kafin su dawo.




Can cikin bacci yaji k'arar k'ofa,a zuciyarsa yace waye haka da sassafe?tashi yayi yabar Sumayya a kwance tana ta barci don ko k'arar k'ofar ita bataji ba.


Falo ya k'araso ya bud'e k'ofar,ganin Inteesar yasa ya murtuk'e fusak kamar Wanda Bai ta'ba dariya ba.Itama 'bangarenta haka ne don ba Wanda ta ysani haninsa a rayuwarta sama da Muhdeen.Cikin sanyin Muryarta ta ce,


"Ina kwana?"


Bai amsa ta ba sai cewa yayi


"Lapiya?"


Bata kula shi ba ta mi'ke masa basket d'in,baice komai ba kar'bi basket d'n tare da shigewa cikin falon ya barta nan tsaye.


Juyawa ta yi don k'arasawa wajen Ishaq koma gida.








******* ********


Har Muhdeen Sumayya suka cika sati d'aya da aure,Kullun sau uku Mummy zata Aiko masu da abinci safe da Rana da dare.Aranar ne kuma ta sanarwa muhdeen za'a daina kawo masu abici,sai dai matarsa ta cigaba da yi masu girki.


Bak'i kowa ya tafi gidan an watse daga Dady, Mummy,sai Mufeeda.Asiya dama tunda akayi biki ta koma Gwaggo ce kad'ai ba ta tafi ba.


: Bangaren ango da ameya kuwa suna shan soyayyarsu son ransu.Abunda ya tayarwa Sumayya hankali shine jin wai zata Fara girki,don ita a rayuwarta ba ta ta'ba shiga kitchen da sunan girki ba don ko ruwan zafi bata ta'ba d'orawa a wuta ba Babu abunda take a gidan iyayenta,komai 'yar aiki ke Mata ko kauda tsinke Bata iya ba.Nan dai ta nunawa Muhdeen cewar ya Nemo masu Mai aiki don ita ba zata iya aikin komai ba,nan ya nuna Mata cewar gsky bazai iya cin abinci wanda 'yar aiki ta girka ba,haka tsarinsu yake ko gidansu Mahaifiyarsa ce ke girka abinci,don haka bazai iya ba gsky.nan hankain Sumayya ya tashi don bata ma san ta Ina zata fara ba kuma Bata San yadda zatayi ba.nan take sanar da ita abokansa ma zasuzo gobe zasu zo suci girkin amarya.Nan dai ta cire d'an kwalin kanta tana goge zufa duk da sanyin A C daga ratsata








Daga Alk'alamin✍️


Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)




09065317995




Love u oll😘😍




Comment &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*






Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.






Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,Idan suna ko hali yazo daya to gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe arashi ne mai kashe auren wawa.






*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*




Page2️⃣7️⃣


Nan take ya sanar da ita abokansa zasu zo gobe zasu zo su ci girkin amarya.Nan dai ta cire d'an kwalin kanta,tana goge zufa duk da sanyin A C dake ratsata.


"Me ya faru ko akwai wata matsala ce?"


Kai ta girgiza tana tunanin ta yadda zata fara,domin kuwa wannan Abu ne mai matuk'ar wahala a gare ta.Bata ta'ba tunananin wannan ranar zata zo ba.Ita da rayuwarta daga taci tasha ta kwanta ba abunda takeyi,Mai mata aiki ce take komai sai da ta tashi barci ta yi wanka tayi kwalliya ta fita Koda zata shigo d'akin sai sai ta tarar an kimtsa mata komai ko kitchen idan ta shiga sai dai idan akwai abunda taje d'auka,sau tari ma tana zaune zata bada umarnin a kawo mata duk abunda ranta keso gashi yanzun mijinta da tayi tunanin zai bi ra'ayinta amma ya ce wai bai yarda da 'yar aiki a gidansa ba.Kukar shagwa'ba ta saka ta ruga a guje ta nufi bedroom d'inta.Shima ya ta shi ya bita a guje kamar sharukhan🤣


Koda ya shiga d'akin kwance ya sameta tayi kwanciyar rubda ciki,janyota yayi jikinsa ya rungume yana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi.Cikin kwantar da murya ya fara magana.


"Haba Baby kukan me kike yi?kinsan na tsani naga kina kuka hankalina tashi ya ke."


Cikin shagwa'ba ta fara magana


"Haba ya zanyi wallahi bazan iya ba,sai kace jaka?nifa bana aiki a gidanmu kafi kowa sanin ma'aikata ke mana aiki ban iya ba kuma ban saba ba,sannan nayi aure bazan huta ba sai nazo na zama banida banbanci da 'yar aiki?"


Cikin sigar rarrashi ya fara magana


"Kinga ba wai ke zakiyi duka aikin gidan nan ba,girki ne dai bazan iya cin na 'yar aiki ba.kuma ai tunda kika zo gidannan bakiyi aikin komai ba,nine nake yin gyaran d'akunanmu na share na goge na wanke toilet na gyara kitchen,duk da Mummy ke aiko muna da abinci ko wace rana ni nake wanke kwanoni .Aikin komai ban baki ta'ba yi ba,kuma dama ranar Monday zan koma asibiti wajen aiki, kafin ranar zan nemo wacce wacce zata dinga yin aikin Amma iyakar ta dai ta yi wanke-wanke da ta gyara kitchen da falo da d'akinki Amma ban yarda 'yar aiki ta shigar mani d'aki ta gyara ba.Zanyi da kaina kuma ban yarda 'yar aiki ta shiga kitchen ta girka mani abincin da zanci ba sai dai matata,sannan akwai Wanda zai dinga wanki da goga fatan kin fahimta,girki kawai ne aikinki a gidan nan Zaki iya ko?"


Kai ta gyad'a masa alamar Eh.Daga nan salon ya canza aka lula duniyar ma'aurata.




Gidan Jabeer kuwa,Matarsa kuwa ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba.Tun ranar da taga ya shigo da Inteesar gidan kuma taga yadda taga Jabeer ya na ta rawar jiki da Inteesar a wurin reception d'in bikin Muhdeen,ta kuma tambayi Mufida wace taga tayi posting a status d'inta ta fito daga Motar Jabeer?sannan washe gari ranar dinner haka taga Jabeer ya d'aukota a motarsa sai wani kallo yake mata mai cike da shauk'i sannan cikin pic d'in ga bugu da k'ari taga photon da Mahaifiyar Jabeer d'in ta rungume Inteesar da su Azeema.Tayi ta sak'a da warwara musamman da ta tambayi Mufida cewar meye dangantaka su da Inteesar ta sanar da ita cewa ba dangantaka sai dai suna mata kallon ita wata sashe ne daga garesu, bata kuma da wata aminiyar da ta wuce Inteesar barci kawai ke rabasu.Nan ta d'aura da cewa wai me yasa da Inteesar zata shiga motar Jabeer ita Mufida bata shiga ba,Mufida ta sanar da ita cewa shi Jabeer d'in ne ya ce su biyu zasu tafi.Har Jabeer d'in ta tsare da tambayoyi ya nuna Mata ba komai a tsakaninsu.




Washe gari ranar da abokan Muhdeen zasu zo, Sumayya na kitchen tana shirya masu girkin tarbar su.Waya ta d'auka ta hau internet don ta samu tasan yadda zata girka masu lafiyayyen jallop.da Farfesun naman kaji.wayar na gabanta tana kallo kuma tana had'a abubuwan girki,a zuciyarta tana ayyana wahalar da akeyi a yayin da ake girki.ta kwashe awa biyar a kitchen tana girka jallop d'in shinkafa da Farfesun kaji.Muhden ne da dawowarsa kenan daga masallaci ya shigo kitchen d'in Jin k'amshi na tashi kitchen d'in sai yanon girkin yakeyi tun baici ba.


Kira ne ya shigo wayarsa, Jabeer ke sanar dashi sun iso,fita yayi ya masu jagora suka shigo.Su uku ne suka zo Jabeer, Salisu, Bilyaminu.A falon gidan ya sauke inda ya d'an tsaya suka gaisa sannan ya nufi cikin kitchen d'in ya sanar da ita zuwansu.Fridge ya bud'e inda ya kwaahi gorunan ruwa da na lemuka ya Kai masu.Ba jimawa itama ta fito daga kitchen d'in d'auke da tray an jera food flask a kai, dinning table ta nufa inda ta jera su,sannan ta k'araso wajensu tana fad'in


"Manyan bak'i sannunku da zuwa"


Suka amsa mata cikin fara'a har suna tsokananta da cewa wai ta rik'e masu aboki gana d'aya tunda yayi aure basu sake ganinsa ba.murmushi kawai tayi,don dama ita ba Mai damuwa mutane bane.Hira sukan tan ta'ba kad'an inda Jabir ke ce masa ya dawo bakin aiki don aiki ya masa yawa,kusan sati d'aya yana hutu.Dariya yayi Yana cewa


"In dawo ina?"


Jabeer ya sake maimaitawa da cewa


"Bakin aikinka mana "


Dariya yayi tare da cewa


"Haba Bross idan ka ce na dawo yanzun ai bakayi mani adalci ba,ina laifin ma nan da wata d'aya kaga lokacin na d'an more amarci ."


Dariya suka yi gaba d'ayansu.


Salisu ya d'aura da cewa


"Allah idan baka dawo nan da one week ba a kunnensa Dady don sai na fad'a masa,ba gara kai ba naka da sauk'i ba,Ni tawa matar Bata da lafiya laulayin ciki take kullun ba lafiya ga kasala da amai ga ciwon Kai da jiri,haka nake fita naje Asibiti ballantana Kai.Ta'be baki muhdeen yayi tare da cewa


"Allah ya bata lafiya,idan saboda lailayin mace ne ba zaka je aiki ba kuwa ashe zaka dad'e kana zaune a gida."


Gayara zama Jabeer yayi Yana kallon Muhdeen ya ce,


"Yauuwa Bross tunda naga tana jin maganarka kaje ka shawo mani kanta mana."


Kallon mamaki Muhdeen ke masa yana cewa


"Kayi mata laifi ne?sannan Kai baka san yadda zaka shawo kan mace ba har sai na shawo maka kanta?karka bani kunya Mana."


"Kai dai bari kawai,abun ya wuce tunaninka,kishi ne kad'ai ke damunta akan abunda bata da tabbas akai."


Gyad'a masa kai Muhdeen yayi ya ce,


"Kamar ya kishi kuma?dududu watan ku nawa da auren?"


"Kishin zance mana kawai don ta ganni da naje gidan tare da Inteesar shine fa..."


Bai Kai karshen maganar ba Muhdeen ya ja tsuki tare da watsawa Jabeer harara yana cewa,


"Aikin banza ai ta burgeni da tayi maka haka,na lura tun randa ka k'yallara ido akan wannan kucakar yarinyar sai wani rawar k'afa kake akanta sai kace a kanta ka fara ganin mace."


"Kar ka sake kiranta kucaka don ita ba kucka bace,kuma da kake cewa akanta na faraganin mace kusan haka ne,domin akanta na fara ganin mace da ta had'a komai da komai da komai 💯 abunda nake buk'ata daga wurin mace.Kuma mata irinta basu da yawa sai ka tara mata d'ari dakyar zaka samu guda uku irinta.Duk namijin da zai kalli Inteesar bai hango qualities d'in da ke tattare da ita ba tabbas idonsa a makance yake.


Dariya Salisu da Bilyaminu suka yi yayin da Muhdeen da Sumayya kuwa suka tsuke fuska.Salisu ya d'aura da cewa,


"Maganarka gaskiya ce,domin domin yarinyar kan Bata da makusa son kuwa k'in wanda ya rasa."


Bilyaminu ya d'aura da cewa,


"Gaskiya kam ku duba ranar da muka dawo daga reception muna jiran K'arasowar Jabeer, sai gashi da ita kunsan dai neman matan banza a wajen Bashir kamar d'an akuya baya ma zancen aure sai lalata da 'ya'yan mutane amma ranar da yaga Inteesar ya fara furta maganar aure Wai ya samu matar da zaiyi rayuwar aure da ita."


Muhdeen ne ya ya'be baki ya ce,


"Kun zauna kuna ta maganar wannan yarinyar idan shi ya kawo ku ta ki tafi can ku k'arata da zancenta amma ba gidana ba."


Jabeer ya ce,


"Au korarmu kake ko ruwa bamu sha ba?"


Sumayya ce tayi magana cikin jin dad'in kalaman mijin nata akan Inteesar ta ce,


"Kuyi hak'uri ga Abinci can da abunsa na shirya maku a dinning table."


Jabir ne ya fara mi'kewa ya na cewa


"Dama yunwa nake ji ne wallahi kasan mai dafa mani abincin ba lafiya,idan ma rowa yasa kake korarmu sai munci.Lokacin da mukayi aure gidan kowannenmu nan sai da kaci abinci sannan munzo gidanka bazamu ci ba?ai wallahi sai munci."


Muhdeen yayi dariya yana cewa


"Au abun ma bin bashi ne?."


Salaisu ya ce,


"K'warai kuwa bin bashi ne kaci na amaryar mu don haka muma sai munci."


Dariya sukayi gaba d'ayansu yayinda suka nufi dinning area.Bayan sun zazzauna sumayya tayi serving d'insu ta ajiyewa kowa a gabansa,ta zuba masu ruwa da lemu ta ajiye masu.Dai-dai lokacin wayar Muhdeen tayi ringing tashi yayi domin amsa kiran, Mummy ce ke kiransa falo ya k'arasa ya zauna Kan kujera.Bayan ta ajiye masu komai a gabansu ta zuba masu farfesun ne ta zauna tana jiran mijinta ya gama wayar ya k'araso.Jabeer kasancewar a yunwace ya ke ya Fara dibar jallop d'in yakai bakinsa tare da bisimillah,rintse ido yayi tare da ya mutse duska sakamakon uban gishiri da yajin da ya gigita k'wak'walwarsa ga shinkar duk karfi da sauri ya tofar da abincin k'asa tare da d'aukar kofin ruwa sai da ya shanye sannan ya ajiye.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads