Header Ads
Showing 129001 words to 132000 words out of 149432 words

Chapter 44 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1392

Ads at the middle of Article

ta gama komai, murmushi tayi


"Daughter yau da sammakon aiki kika tashi? baki gajiya ne?"


Murmushin tayi tare da sunkuyawa ta gaida Mummy, ta amsa mata cikin farin ciki buɗewa ta fara yi tana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci Inteesar ta gama ayyukan nan.


"Sannu da ƙoƙari Allah yiyi maki albarka"


Murmushi kawai tayi inda ta ɗauko basket ta fara shirya wanda za'a tafi Asibitin dasu, kallonta Mummy tayi tare da cewa


"Waɗannan da?"


"Mummy na yaya ne da za'a kai masa Asibiti."


Murmushin jin daɗi Mummy tayi don taji daɗin jin hakan har cikin ranta, don yanzun ta lura tun lokacin da Muhdeen ya durƙusa a gaban Inteesar yana kuka yana riƙe rigarta tare da roƙonta tayi haƙuri ta koma gidansa, tun a lokacin Mummy ta hango soyayyar Muhdeen acikin idanunta, amma duk da haka zata gwada ta dan ta tabbatar da abinda zuciyarta ke faɗa mata, kallon Inteesar tayi tare da cewa


"Oh yanzun abincin nasa ne kika haɗa? saboda shi kikayi wannan sammakon?"


Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta, ba tare da ta ce komai ba Mummy ta cigaba da cewa


"Idan kin kammala ki bawa Direba ya kai masa kiyi zamanki ki huta, ba wanda zai je."


Da sauri ta kalli Mummy tana so tayi magana kuma tana jin nauyin Mummy dan haka ta nufi ɗakin Gwaggo, kallo ɗaya Gwaggo tayi mata taga yanayinta ya sauya, dan haka ta ce,


"Lafiya kuwa?"


Girgiza kai tayi ba tare da ta ce komai ba, Gwaggo ta ce


"Akwai abunda ya faru naga duskarki ba walwala, daga ina kike?


A takaice ta ce,


"Kitcheen"


Miƙewa Gwaggo tayi tare ta nufi kitchen, ta samu Mummy ta ce,


"Fatima lafiya naga Inteesar ta fito daga nan kitcheen duk yanayinta ya sauya?"


Dariya Mummy tayi tare da cewa


"Dama ina son na tabbatar da hasashe na ne, yarinyar nan sammakon zuwa kitcheen tayi tana girkawa mijinta abinci, kuma inda zaki tabbatar saboda shi tayi duk abincin da yafi so shi ta girka masa, saboda na ce, Direba ne zai kai ba wanda zai je shine fa ta shiga wannan halin, nima na faɗa ne kawai dan naga yadda zatayi."


Murmushin kawai Gwaggo tayi ta fita daga kitchen ɗin zuwa ɗakinta kallon Inteesar tayi tare da cewa


"Kiyi wanka kiyi breakfast sai kibi Direban ku tafi ko?"


Bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba,tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta, Gwaggo dariya itama tayi tare da cewa


"Wato dama can kina son mijinki kike nuna baki sonsa ko? to anyi walƙiya na ganki kina so kina kaiwa kasuwa, har kina roƙo kina kuka akan cewa baki sonsa a raba auren, to yanzun da an raba auren wa kika cuta idan ba kanki ba? don nima nasan cewa idan kika rasa miji irin jikana Muhammadu kinyi babban rashi, samun miji kamarsa sai mai Sa'a irinsa basu da yawa a wannan duniya, bawai ina faɗa maki haka a matsayin yana jikana bane a'a ina baki shawara ne a matsayi na na babba a gare ki wacce ta hango abinda ke baki hango shi ba, ki riƙe mijinki hannu biyu da kyau, kinga har kusan kashe kansa yayi a dalilin an hana sa ke yana masifar sonki fiye da yadda nake zato, don banyi tunanin cewa yana sonki har haka ba, shiyasa nima na sauko daga dokin fushin da na hau da shi, dan na fahimci irin son da yake maki, yanzun mahaifiyarsa ma tasan da hakan, mutum ɗaya ne nake tunanin zaku fusƙanci ƙalubale daga wurinsa wato Mahaifinsa, dan naga yadda ya ɗauki abun da zafi sosai, ni kuma bazan ce masa komai ba duk shawara da ya yanke akai Shikenan."


Da sauri Inteesar ta kalli Gwaggo ta ce,


"Idan bai amince ba fa?"


"Sai kuyi haƙuri bana son nayi saurin saka masa baki, wannan karon zan barshi yayi iko akan ɗansa, ba kamar kwanakin baya ba da nake masa katsalandan na hana shi aiwatar da hukuncin da yayi niyya, amma idan naga abun yayi yawa zan taka nasa birki ne."


Cikin sanyin jiki ta nufi toilet don yin wanka, Mufida ce ta shigo take tambaya ina Inteesar Gwaggo ta sanar da ita yadda sukayi tun daga kan girki har zuwa wankanta zata je Asibiti, dariya Mufida tayi tare da cewa


"Lallai kuwa bari nayi mata kwalliya ta musamman, ina zuwa."


Ta fita zuwa ɗakinta kasancewar Inteesar da ta farfaɗo daga Asibiti aka taho da ita nan, so ba kayanya ko ɗaya a nan kayan Mufida take sakawa tunda kusan jikinsu ɗaya duk da cewar akasarin ɗinkunan Mufida suna matse ta cif ita kuma bata cika son ɗinkuna da suka matse mata jikinta ba.


Sai da Mufida ta zaƙulo wani wani leshi milk colour da broun yana da ratsin golding color, sai ta fito mata da mayafi golding colour sai hakka da takalmi broun ta kwashe su tare da kayan kwalliya ta nufi ɗakin Gwaggo, lokacin Inteesar har ta fito daga wanka tana shirin zuwa ɗakin Mufida sukayi karo da juna, komawa baya Inteesar tayi Mufida ta kalle ta ta ce


"Kayan da zaki saka na kawo maku, dan so nake ki burge mijinki fiye da waccan matar tasa, dan naga juya da ta ganki kamar zata haɗiye zuciya ta mutu dan baƙin ciki, yau so nake ki kece raini ki fito kamar wata Amarya."


"Kinga Mufida meye abun wani kwalliya a cikin zuwa asibita?ni ba shi zai kaini ba kibarshi kawai."


"Wallahi sai kin saka."


Bata jira sawarta ba kawai sai ta fara ƙoƙarin zura mata kayan, ganin haka yasa Inteesar ta karbi kayan tare da cewa


"Bari nasa da kaina."


Bayan ta saka kayan ganin yadda siket ɗin kayan ya matse ta tam a jikinta hatta hips nata sai da suka bayyana, kallon Mufida tayi tare da kwaɓe fuska kamar zata yi kuka ta ce,


"Bazan iya fita da kayan nan ba."


Dariya tayi tana kallon Inteesar ta ce,


"Wow gaskiya Allah yayi halitta a nan kinga yadda kikayi kyau kuwa?"


Yamutshe fuska Inteesar tayi


"Kinga ni ban damu ba nafi son saka abaya gaskiya, wannan kayan takura Ni zaiyi baki ga yadda suffar jiki na suka bayyana ba?"


"To meye?"


Girgiza kai tayi


"Nidai gaskiya bazan iya ba."


"Wajen mijinki fa zaki"


Bata saurare ta ba ta fara mata makeup duk da ta ce bata so amma sai da akayi mata na dole, sarƙa da ɗan kunne na gold ta saka mata duk yadda Inteesar tayi sai da Mufida tayi mata kwalliya ta fito kamar ba ita ba, wani kyau da kwarjini ta ƙara sai fitar da annuri take, kallon Gwaggo tayi tare da cewa


"Gwaggo ni da zan tafi Asibiti meye na mani kwalliya kamar wacce zata je gidan bikin?"


Taɓe baki Gwaggo tayi tare da cewa


"Kunfi kusa Ni bani da lokacinku bari naje na cika ciki na."


Daga nan ta fita Inteesar ma tabi bayanta, suka nufi dinning table, ruwan tea kawai Inteesar ta sha sannan ta ce, ta ƙoshi, hakan yasa ta miƙe ta kalli Mufida ta ce,


"Ki bani hijabi na tafi."


"Gyale na ɗauko maki ki saka?"


"Haba kema kinsan bana son saka gyale"


" To ni bani da hijabi gyale nake da su hijabi na guda biyu ne na sallah kuma yanzun na saka su cikin washing machine na zuba ruwa da sabulu zan wanke."


Kallon ta kawai Inteesar tayi ta nufi ɗakin Mufida, kai tsaye toilet ta wuce ta duba cikin washing machine taga duka hijaban ta saka su ta jiƙa, daga gani tasan da gan gan Mufida tayi haka dan yasan dole zata nema ita kuma ba zata so ta saka ba, takaici ne ya ishe ta dole ta ɗauki mayafin ta saka ta zura takalmi da ɗauki hand bag ta fito, kallo ɗaya idan kayi mata sai ka sake sha'awar kallonta, tayi kyau sosai, ɗakin Mummy ta shiga ta sallame ta itama ta yaba da kyaun da Inteesar tayi, sannan ta nufi kitchen ta ɗauki basket ɗin ta nufi harabar gidan dan ta sanar da Direba ya Kaita Asibiti.


Direban Mummy ya buɗe mata bayan motar ta shiga bayan ya saka abincin, sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar gidan








*Daga alƙalamin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




*DON NEMAN ƘARIN BAYANI*


09065327995




Love you oll😍😘


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, duk abu ɗaya ne, sannan idan kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, dan ko kin shiga idan baki comments zan fitar da ke ne.




*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo ɗaya to a gafarce, bada niyyar yin hakan nayi ba arashi ne mai kashe auren wawa.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page7️⃣2️⃣


Direban Mummy ya buɗe mata bayan motar ya shiga, bayan ya saka abincin sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa ya tada motar suka bar gidan.


Ɓangaren Sumayya kuwa bayan sun gama abuda sukayi ne suka kwanta rungume da juna a haka barci ya ɗauke su, kiran sallar asuba ne ya tada Bashir ya janye ta daga jikinsa don yasa ko ya ce, ta tashi tayi sallah ba tashi zatayi ba, sai ta gama barcinta, buɗe ido tayi jin ya janye ta daga jikinsa ta ce,


"Ina zaka je?"


"masallaci zanje, tashi muyi wanka lokaci na tafiya"


Gyara kwanciyarta tayi tare da cewa


"Idan na tashi da safe zanyi wanka da sallar."


Girgiza kai kawai yayi ya nufi toilet don yin wanka, bayan ya fito ne ya saka kaya ya nufi masallaci.


Ana idar da sallar ya dawo ya kwanta ya cigaba da barcinsa, ƙarfe bakwai ta farka ta tayar da Bashir ya tashi zaune tare da kallonta


"Lafiya Summy?"


"Ka fita ka nemo Mani kayan da zansa idan nayi wanka, kasan banzo da niyyar kwana ba kuma ban ɗauki komai ba so kane ka siyo man.."


Kafin ta kai ƙarshen zancenta ya ce,


"Kwantar da hankalinki Baby akwai kaya ana sababbin waɗanda na tanada saboda irin haka, ke dai kawai kije kiyi wanka."


Tashi tayi ta nufi toilet bayan kamar mintuna ashirin sai ta fito kanta na ɗaure da towel, ba tare da jin komai a ranta ba ta warware towel d'in ta shafa mai shaf-shaf t gama shiryawa ta ɗauki doguwar riga ta material da Bashir ya ajiye mata ta saka ɗan ƙaramin mayafinsa ta saka ta kwashi wayoyinta da jakarta ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin ƙofa ta jiyo muryarsa yana cewa


"Bako sallama?"


"Sorry Dear may be na dawo ta nan, amma ba tabbas ko na koma gida sai shawarar da na yanke."


"Okay sai munyi waya kenan?"


"No kada ka kira waya ta idan ba nice na kira ka ba kada ka kira ni, idan ma akwai wani abu ne to kayi mani text message idan da yiwar nayi magana zanyi maka magana ta waya, idan babu kuma zaka ga text message ɗin a."


Daga nan bata jira amsar da zai bata ba tayi ficewarta har ta kai tsakiyar falo ta ji ya ce,


"Ba zaki tsaya muyi breakfast?"


"Kai ta girgiza tare da ɗaga hannunta na hagu tana kaɗai yatsarta manuniya alamar a'a."


Daga nan tayi ficewarta gurin motarta, shigewa tayi tare da tada motar ta bar gidan.


Kwance yake bayan Jabeer ya taimaka masa yayi wanka, ya dawo ya zauna, Jabeer ne ya shigo hannunsa ɗauke da kayan Muhdeen, kasancewar dama a cikin office ɗin Muhdeen akwai bedroom da toilet don haka ya je ya bedroom nasa cikin wardrobe na kayan Muhdeen ya ɗauko masa wasu ƙananan kaya ya kawo masa ya saka, yana gama sakawa Jabeer ya fita da waɗanda ya cire shi kuma ya kishingiɗa, idanunsa ya lumshe kamar mai barci alhalin ba barci yake ba.


Sumayya ce ta turo ƙofar ta shigo, shi dai ya ji motsin shigowar mutum amma baisan ko wace ce ba, kuma bai buɗe idanunsa ba, ƙamshin turaren da ya ji ne yasa ya yayi magana ba tare da ya buɗe idanunsa ba ya ce,


"Bashir kaine da sassafe haka?"


Gaban Sumayya ne ya faɗi jin abunda Muhdeen ke faɗa, cikin rawar murya ta ce,


"Nice kuma Bashir yau?"


Da sauri ya buɗe idanunsa ya sauke a kanta, ganin ita kaɗai e yasa ya ce,


"Bashir kaɗai nasan yana amfani da wannan turaren shiyasa nayi zaton ko shine, don naji ƙanshin turarensa ne, amma ke me ya haɗaki da irin turaren nan?"


Murmushi tayi tare da zama dab da shi inda yake kishingiɗe, tashi zaune yayi ta ƙara matsawa dab da shi, tana shirin yin magana ne sai ga Inteesar ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama


"Assalamu alaikum"


Jin muryarta yasa ya zubawa ƙofar ido idanunsa suka sauka akanta, subhanallahi, ai mutuwar zaune yayi sakamakon wani ƙayataccen kyau da yaga tayi, din tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin tayi nasa kyau irin na yau ba, ko lokacin aurensa da Sumayya da aka mata kwalliya a lokacin kallon arziki bata ishe shi ba, ko lokacin aurenta da shi ma bai ko kalli fuskarta ba, tabarakallu ahsanal khaliqin, shine kalmar da ya furta a zuciyarsa, ita kanta Sumayya sai da gabanta ya faɗi ganin irin kyau da kwarjini da cikar haiba irin ta Inteesar, don ko mace ƴar uwarta ta kalle ta sai ta sake kallonta ballantana namiji, tsananin kishi ne da baƙin ciki suka cika mata zuciya.


Ita kuma Inteesar ganin basu amsa mata sallama bane yasa ta sake cewa


"Assalamu alaikum"


Daƙyar Muhdeen ya iya amsawa da


"Wa'alaiki salam"


Shigowa tayi hannunta ɗauke da Basket da aka jera abincin a jiyewa tayi a gefe ta sunkuya ƙasa ta gaida Muhdeen.


"Ina kwana yaya?"


Tsayawa yayi yana kallonta, don tun da yake a rayuwarsa ba mahaluƙin da ya taɓa durƙusawa har ƙasa ya gaishe sa sai ita, farin ciki ne ya lulluɓe masa zuciyarsa don haka ya ce


"Kin tashi lafiya"


"Lafiya lau ya ƙarfin jiki?"


"Alhamdulillah"


Miƙewa tsaye tayi tare da cewa


"Allah ya ƙara sauƙi"


Ya amsa da


"Ameen"


Kallon Sumayya tayi tare da cewa


"Aunty Sumayya ina kwana?"


Ganin Muhdeen ne yasa ta amsa mata da


"Lafiya lau ya kike?"


"Alhamdulillah"


Zama tayi a ɗaya daga cikin kujeru da ke cikin room ɗin, Sumayya ganin Inteesar zaune yasa ta ƙara shigewa jikin Muhdeen musamman da ta lura ya mida hankalinsa ga Inteesar ita kawai yake kallo, sajensa ta shafa da hannayenta cikin kirsa ta ce




"Nayi missing ɗinka sosai wallahi"


Gajeren murmushi yayi tare da cewa


"Nima haka".


"Da gaske"


Kai kawai ya ɗaga mata alamar eh, amma gaba ɗaya hankalinsa na ga Inteesar, ya mace a kallonta abubuwa dayawa yake ayyanawa a zuciyarsa game da ita, lura da hakan yasa Sumayya tayi ƙoƙarin ɗauke hankalinsa dan ya manta da Inteesar dake wajen.


Bakinsu ta daɗe wuri guda ta tsotsansa, zaro ido yayi yana kallonta da mamaki, sanin cewa Inteesar na wajen ne yasa ya fara ƙoƙarin zame jikinsa daga nata amma ina sai ƙara ƙanƙamesa tayi a jikinta, hannu tasa cikin sumar kansa kamar maiyi masa susa.


Inteesar tana ganin haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita da sauri ta fice.


Fitarta daga ɗakin ta nemi wani waje da aka tare kujeru ta zauna a harabar wajen, akwai 'yar tafiya tsakani, tagumi tayi tana tuna yanayin da ta barsu take taji wani ɗaci a zuciyarta ƙwalla ne suka taru a idanunta sai tayi saurin mayar da su, tsuki tayi tare da furtawa a fili.


"To me yasa ma naji haushin abunda suka yi? ina ruwa na da su? me yasa nake jin kishinsa a raina?."


Ita kaɗai take magana sanin ba wanda zai amsa mata yasa tayi shiru.


A can ɗakin kuwa Jabeer ne ya turo ƙofar ya shigo,turus yayi yana masu kallon mamaki, kafin ya ɗaga masu murya da cewa


"Meye haka!?"


Sai a lokacin suka dawo hayyacinsu kallon Jabeer sukayi da yake kallonsu shima.


"Nan Asibiti be meye haka? wai mara lafiya kenan, tashi ku tattara kayanku ku tafi can ku ƙarata."


Kwanciya Muhdeen yayi ita kun Sumayya dama ba kunya ce da ita ba, dan haka ko a jikinta.


Tsuki Jabeer yayi yayin da idanunsa suka sauka akan Basket da Inteesar ta kawowa Muhdeen breakfast.


"Wannna basket na abincin fa wa ya shigo da shi, tunawa Muhdeen yayi da Inteesar dan haka ya miƙe da ƙyar tare da cewa


"Inteesar ce ban ma san lokacin da ta fita ba."


Da mamaki yake kallonsu


"Kana nufin tana zaune a nan a gabanta kuke wannan abun?ko kunya baka ji ba wannnan ai cin fuska ne."


Sai a lokacin shi kansa Muhdeen yaji kunyarta ya rasa yadda akayi ya biyewa Sumayya, duk da baiso biye mata ba amma shu'umancinta sai da tasa ya biye mata.


Hanyar fita yayi ko zai ganta a wajen amma ba ita ba alamarta, to ko dai ta tafi ne, juyawa yayi yaga wayarta a inda ta zauna sai ya tabbatar da cewa bata bata tafi ba.


Ɓangaren Inteesar kuwa tana zaune a inda take ne sai taga mutum tsaye a kusa da ita, da sauri ta ɗaga kai dan ganin waye sai ganin Auwal tayi tsaye a kanta murmushi yayi tare da cewa


"Assalamu alaikum"


Itama murmushi tayi tare da amsa masa sallamar da yayi mata.


"Wa'alaika salam, Malam ina wuni?"


"Lafiya lau Inteesar me kike ana ?"


"Bakomai ina dai hutawa ne"


"Ok masha Allah, classmate ɗinki ce ba lafiya"


Miƙewa tsaye tayi tare da cewa


"Subhanallahi wace ce Malam?"


"Lokacin da nake teaching naku ba S.S 2 ba akwai wata yarinya da na kawo ta class naku ba,na ce cousin ɗita ce ba?"


Shiru Inteesar tayi tare da yin nazari kafin tayi murmushi ta ce,


"Maryam Kabir ko?"


"Ƙwarai kuwa ita"


"Ayyah to mu ƙarasa na gaishe ta."


Yana gaba tana binsa a baya har zuwa inda aka kwantar da Maryam, suna zuwa ma tana barci bata samu gaisawa da ita ba, sai dai ta gaida mahaifin Maryam da mahaifiyar sannan ta juyo don komawa, Mallam Auwal ya bita dan mata rakiya suka jera suna fitowa.


Muhdeen da ke tsaye ta hango Inteesar tare da Mallam Auwal, suna tafiya a hankali suna magana, zuciyarsa ce ta fara tafarfasa musamman da ya kura Jama'a da yawa masu kai komo da waɗanda suke zaune sai kallon Inteesar suke, sai ta zama kamar zara a cikin taurari, itama kanta bata sake ba saboda kayan jikinta da suka ɗan kama ta ga gyale da ta yafa bata saba sakawa ba, ta saba da hijabi don haka sai take jin kanta wani iri.


Mallam Auwal ya ce


"Wa kika

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads