Showing 96001 words to 99000 words out of 149432 words
Chapter 33 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
aurenka a kaina, zaman da nake a gidan kurkukukun gidanka k'addara ta ce kuma tazo k'arshe da yardar Allah, dan zama da kai ya zama tsautsayi da k'addara, jiranka kawai nake ka sauwak'e mani naje na auri masoyi na mai son farin cikin rayuwa ta ba irinka ba mugu azzalumin mutum mai bak'ar zu..."
Kafin takai k'arshen maganar da tayi niyar fad'i sai ta ji saukar mari tass a gefen fuskarta, idanunsa gaba d'aya sun rikid'e sun koma jajir kamar garwashin wuta jikinsa har rawa take ya ma kasa magana sai kallonta take, itama dafe kumatunta tayi tana kallonsa sam bata ji zafin marin da ya mata ba, saboda bak'in ciki da ta k'unsa masa lokaci guda ya gusar da zafin marin, ko ba komai zuciyarta tayi fari tunda ta zama sanadiyar 'bacin ranta, fita yayi a fusace kai tsaye ya nufi office d'in Jabeer.
Bayan fitarsa itama ta nufi k'ofar fita ta janyo k'ofar ta jita a datse, ya rufe ta ya tafi da key d'in, komawa tayi ta zauna kan kujera mai zaman mutum uku tare da fashewa da kuka.
Jabeer na k'ok'arin fita da file a hannunsa Muhdeen ya shigo, ganin yanayinya yasa ya koma ya ajiye file d'in tare da k'arasawa kan kujerar da Muhdeen ya zauna, dafa kafad'arsa yayi tare da cewa
"Bross ya akayi ne? wa ya ta'bo ka ne?"
Uffan baice masa ba, shima yasan bazai tanka masa ba, don yasan halinsa dama idan har aka 'bata masa rai baya iya magana duk juyin da za'ayi kuwa bazai ta'ba magana ba idan ransa ya kai k'ololuwar 'baci, ba abunda yake tunawa kamar kalamanta da take cewa jira take ya sake ta ta auri wanda yake son farin cikinta ba irinsa ba mugu azzalumin mutum mai bak'ar zuciya, rintse idanunsa yayi tunawa da kalamanta, shi kansa ya yarda cewa yana jin son yarinyar a cikin zuciyarsa,bawanda baisan sanda son nata ya samu gurbi a cikin zuciyarsa ba.
Haka Jabeer ya dinga lalla'ba shi da kwantar masa da hankali har fushin nasa ya d'an sauka, Jabeer ne ya fita yayin da shi kuma ya d'an kishingid'a akan kujerar.
'Bangaren inteesar kuwa tana nan sai da taci kukanta ta k'oshi tukunna sannan ta tashi ta fara dube-dube ko zata samu key ta fita amma ina bata samu ba, ganin akwai bedroom a ciki ne yasa ta shiga, toilet ta fad'a ta d'auro alwala tazo ta yi sallah, bayan ta idar da sallar ne ta d'an jingina da jikin gadon ta lumshe ido kamar mai barci bayan ba barci take ba idanunta biyu, bata san lokacin da ya shigo ba k'arar ajiye abu taji ta bud'e idonta da sauri, ganinsa ta yi tsaye a gabanta fuskarsa ba yabo ba fallasa, kallon ledar da ya ajiye mata tayi takeaway ne yayo mata, fridge ya nufa ya bud'e ya ciro mata lemo da ruwa masu sanyi ya ajiye mata tare da zama bakin gadon ya ce,
"Ga abinci nan kici, na tuna tun tea da kika sha da safe baki ci komai ba gashi har yamma tayi."
Duk da itama kanta masifaffen yunwar take ji sosai amma sai ta dake ta ce,
"Bazanci ba?"
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Kinsan irin 'bacin ran da kika saka ni ciki kuwa? tunda nake a rayuwa ta ba wacce ta ta'ba tsayawa a gaba na ta fad'a mani irin munanan kalaman da kika fad'a mani ba, kece mutum ta farko da kika gaya mani maganganun da suka matuk'ar sosa mani zuciya, kuma na kasa d'aukar matakin da ya kamata na d'auka akanki, saboda kece kawai amma wallahi da wani ne ko wata ce da abinda zanyiwa mutum bazai ta'ba mantawa ba."
Murmushin takaici tayi tare da cewa
"Ni me yasa ka kyale ni?"
"Saboda yadda nake jinki a raina, bansan yaushe ne ko kuma a ina be ba, amma kuma abunda na sani shine ina sonki a yanzun."
Da sauri ta kalle shi cikin mamaki ta ce,
"Wallahi baka sona ka tsane ni, In banda abunka me zakayi da kucaka? ko ka manta ne?"
Dafe goshinsa yayi don ko ya mata bayani ba yadda zata yi ba.
"Ki bani daman a karo na biyu zan gayara kuskure na."
Bata ce komai ba ta had'a kanta da gwuiwa kamar ba da ita yake magana ba.
"Waye wannan Usman d'in tsohon saurayinki? akan me zai dinga kiranki a waya kina matar aure?"
"Bai san cew nayi aure bane?"
"Me yasa baki sanar da shi ba bayan kinsan hakan ba dai-dai bane a matsayin matar aure ta dinga waya da wani namiji da ba muharraminta ba a waya suna soyayya?"
Ta'be baki tayi
"Ni wannan ban d'auke shi aure ba, shiyasa ban fad'a masa ba don banyi kama da matar aure ba."
Dariya yayi tayi sosai kamar ba shi ba, duk da cewar bai cika dariya ba shiyasa ta zuba masa ido tana kallonsa, ganin yadda dariyar tayi masa kyawu sosai har wushiryarsa sanda suka fito, kwantaccen sajen da yayiwa fuskarsa k'awanya ta zuba ma ido suman fuskar bak'i wulik ya kwanta luf akan kyakkyawar fuskarsa, kansa ma a cike yake da suma Wanda ke shan gayara kwanta tare da d'an kanannad'ewa sai shek'i suke, gaba d'aya ta shagala da kallon kyakkyawar fuskarsa, sai da taji ya tsagaita da dariyar sannan ta d'auke idanunta akansa.
"Wato kina nufin baki d'auki kanki a matar aure ba ko? saboda abu d'aya ko? wanda ake aure dominsa, dam ci da sha da sutura da lafiya duka an d'auke maki shi a gidanku ba sune aure ba saduwa tsakanin miji da mata ne kad'ai ya rage wanda matar aure zata nuna maki ko? to kada ki damu Dan wannan shima daga jiya ai kin zama cikakkiyar matar aure ko? to kada ki damu yanzun aka fara, dama bawai ya isheni bane gani nayi kin suma yasa na barki haka nan, kuma yau naga kamar baki warke ba ko kin warke ne yanzun ma na d'ora daga inda na tsaya?"
Ya k'arasa maganar yana zare mata hijab tare da janyo ta a jikinsa, kiciniyar k'wace kanta tayi amma ta kasa, kuka ta saka masa kuka tana cewa
"Ni wallahi ba abunda nake nufi ba kenan, kuma idan wannnan ne aure to na hak'ura da auren tunda ba farilla bane auren."
Daiya yayi
"Matsoraciya ko ba farilla bece aure ai sunnah ce mai k'arfi, kuma wahalar da kika sha ranar ma saboda na farko ne a rayuwarki, dole zakiji wannan zafin amma yanzun ba zaki ki ba."
Sake ta yayi ya d'auka kedar tekeawa ya bud'e, cokali ya saka ya d'ebo abincin da niyyar kaiwa bakinta ta juyar da kanta gefe, naman kazar ma bata ci ba ba yadda bai lalla'ba ta ba ga yunwa tana ji amma tak'i ci, haka ya k'yale ta ya maida ya rufe sannan ya ajiye.
Janyo ta jikinsa yayi tare da yin kissing nata ta ko ina, bata yi aune ba kawai ji tayi ya raba ta da kayan jikinta, k'ok'arin cire mata bra yake yi ta rik'e da k'arfi tare da fashe masa da kuka, ganin ta rik'e bra d'in da k'arfi bata da niyyar sakewa kawai sai taga ya yaga mata bra d'inta, haka ya dinga tsotson breast d'inta kamar ya samu sweet, haka ya dingayi yasha wannan ya luguiguita wannan, haka ya dinga tsotson la'b'banta tare da zura harshensa cikin bakinta, haka ya fara rikita ta da salonsa, tun tana kiciniyar k'wacewa har itama jikinta ya fara amsa sak'onsa, wani yanayi ta tsinci kanta Wanda bata ta'ba tsintar kanta cikinsa ba sai yau cikin wani irin murya ta ce,
"Yaya ka bari wallahi bana so, akwai zafi ban warke ba wallahi idan ka k'ara mutuwa zanyi."
Dak'yar maganarsa ke fita cikin wata kasalalliyar murya ya fara magana
"Ki kwantar da hankalinki ba abunda zan maki, ina son ne na samu relief a jikinki, idan kuma kika nemi mani gardama to zan maimaita abunda anyi a daren jiya da kika ce da zafi, jin hakan yasa ta k'yale shi sai da ya luguiguita ta son ransa sannan ya k'yaleta ya mitgina gefe yana fitar da numfashi mai k'arfi.
A can d'akin da aka kwantar da Umma kuwa Gwaggo ce da Mummy suka tashi tafiya, Mufida ma ta ce zata bisu ta dawo da safe, tunda Mama Huraira ce zata kwana da ita, Abba ne ya shigo da sallama, suka gaisa da su Mummy lokacin ya dawo daga kasuwa ya zo, bayan sun gaisa ne su Mummy sukayi masu sai da safe don k'arfe shida na yamma tayi, Mufida ce ta ce,
"Mummy ina son naga inteesar kafin mubtafi"
"Mufida kenan yanzun Ina zaki ganta, tunda son ya fita ta bishi ai bata dawo ba"
"Eh Mummy sun dad'e tun k'arfe biyu yanzun k'arfe shida awa hud'u fa kenan, yakamata ace sun dawo."
Kallon mamaki Umma tayi mata ta ce,
"To ke ina ruwanki ba suna tare ba ai ba abun damuwa."
Girgiza kai tayi tare da cewa
"Mummy ki kira shi ya dawo da ita mana."
Gwaggo ce ta kalle ta da mamaki ta ce,
"Yau naga d'ibar albarka, ke wace irin jidalalliyar d'iya ce? ance suna tare da mijinta ki damu ya dawo da ita, idan ya dawo da ita uwar me zata yi anan d'in? ita fa yanzun matar aure ce ke da baki son kiyi auren sai ki ta galbaro akan titi, so kike ta bar mijinta tazo ta zauna dake kuyi ta karad'in banza?"
"Haba Gwaggo daga nayi magana sai ki dinga zaro zance haka? kamar dama kina jira na ne? "
Haka dai suka tafi amma Mufida taso taga inteesar kafin su tafi, dan haka da suka kawo dai -dai office d'in Muhdeen Mufida ta kalli Mummy ta ce ,
"Yauwa ga office d'insa nan ko mu d'an tsaya ne zan bawa Inteesar sak'o."
Gwaggo tayi saurin cewa
"Yauwa kira shi dama maganin ciwon k'afa sun k'are ya bani wasu."
Knocking Mufida ta dingayi ba'a bud'e ba,yana cikin bedroom nasa yana ji amma yak'i bud'ewa ita kuma inteesar tana ta addu'ar ya bud'e k'ofar ta fita, ganin ba shi da niyyar bud'ewa ne yasa ta ce,
"Knocking ake fah"
"Inaji ai bani da niyyar bud'ewa ne."
Daga can waje kuwa Mummy ce ta kalli Gwaggo ta ce
"May be baya ciki ne amma bari na kira wayarsa naji ko yana ina."
Wayar ta ta ciro ta laluno number sa ta danna masa kira.
Yana kwance sai numfashi yake saukewa don ba abunda yake da buk'ata illa Inteesar, tun jiya da ya d'and'ani zumarta gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa ba shi da wani burin da ya wuce ya sake jinsa a cikin wannan kogin zumar da bai ta'ba tunanin jin irinsa ba, burinsa ya sake shiga wannan kogin dad'in amma ina dolensa ya barta sai ta warke raunin da yayi mata.
Wayarsa ce ta soma ruri, bai duba ballantana yasan wa ke kiransa, sai da aka kira sau uku bai d'aga ba, kallon Gwaggo tayi tare da cewa
"Son fa bai d'aga wayar ba mu tafi kawai Gwaggo, idan ya kira sai na sanar dashi ya kawo maki maganin ciwon k'afa."
"Saboda ba k'afarki bace kuma baki san ya nake ji ba shiyasa kike fad'in haka ko? to ina nan har ya dawo ya tarar da ni a nan ya bani maganin."
Mummy dai bata ce komai ba sai ta k'ara kiransa.
Mik'a hannu yayi tare da duba wayar ganin Mahafiyarsa ce yasa ya d'aga tare da cewa
"Barka da yammaci Mummy"
Jin muryarsa wani iri yasa Mummy cewa
"Son kana lafiya kuwa?"
"Lafiya lau Mummy"
"Ok to kana ina ne yanzun?"
"Ina office d'ina "
"To gamu a k'ofar office d'in"
Daga nan ya katse kiran, k'ok'arin dai daita nutsuwarsa yayi ya gyara zama rigarsa sanna ya kalli inteesar da ke zaune ta had'e fuska ya kalla sannan ya mik'e ya fita, bud'e k'ofar yayi duk suka zuba masa ido, idanunsa sunyi ja na jaraba ga gefen bakinsa da inda janbakin inteesar ya shafi la'b'bansa, zuba masa ido sukayi yauinda Mufida ta ce,
"Yaya ina Inteesar?"
"Cikin sark'ewar murya ya ce,
"Tana ciki, ina ganin kamar barci take yi ne."
Mummy ce ta ce
"Gwaggo tazo ka bata magani"
Daga nan ya juya ya koma cikin office d'in Mufida tabi bayansa, Gwaggo ma haka ganin haka ne yasa Mummy ma ta shiga.
Anya ma akwai maganin anan?bari na kira a kawo mani na baki, Kiran waya yayi ya fad'i sunan magungunan da za'a kawo masa, Mufida ce ta ce
"Yaya banga Inteesar ba"
Tana cikin bedroom barci take, karaf kuwa Inteesar taji maganar Mufida bata ma san tare da su Mummy take ba, da sauri ta diro daga kan gadon ta mane cewa kanta ba d'an kwali rigarta duk ta cukuikuye gashin kanta a yamutse zif d'in rigar ma a zuge take, haka ta k'araso wajensu ganin irin kallon da suke mata na zargi musamman Mufida da ke watsa mata kallon gargad'i,tunawa tayi da yadda ta fito sannan ta kalli fuskar Muhdeen taga shatin jan bakinta a bakinsa sai ta kwa'be fuska cikin shagwa'ba kamar zatayi kuka, Mufida ta ce
"Ina nan ina ta jiranki ke miji dad'i kinzo kin tare a office nasa ko? Wato bakiji magana ta ba to kije ke kika sani duk abunda ya biyo baya."
Mummy ce ta kalle ta ta ce
"Me ke faruwa Mufida?"
Kallon Muhdeen Mufida tayi tare da cewa
"Komai ma ya faru."
*Wash hannuna ya gaji*
*Daga alk'alamin*✍️
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don k'arin bayani*
09065327995
Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page5️⃣7️⃣
Kallon Muhdeen Mufida tayi tare da cewa
"Komai ma ya faru."
Kallon rashin fahimta Mummy tayi mata tare da cewa
"Ina komai ya faru me kike nufi?"
Kafin Mufida ta bud'e baki tayi magana Jabeer ya shigo office d'in a gigice wata nurse na biye da shi a baya, hannun Muhdeen ya janyo tare da cewa
"Pls kazo da sauri an kawo Emergency ne, suna buk'atar taimakon gaggawa."
Fita office d'in sukayi cikin hanzari, yayinda Mummy ke cewa
"Allah ya basu lafiya ya tashi kafad'arsu."
Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen, idanun Mufida na kan inteesar kafin ta maida dubanta ga Gwaggo ta ce,
"Kinga anyi masa kira gaggawa, gashi yamma tayi yakamata mu tafi tunda bamu San lokacin dawoarsa ba."
Dai-dai lokacin da wata ta shigo da leda da magungunan Gwaggo a ciki Mufida ce ta kar'ba tare da mik'ewa Gwaggo
"Kinga magungunaki an kawo."
Kar'ba Gwaggo tayi tare da kallon Inteesar ta ce
"Ke kuma abunda ya kawo ki kenan ko? Ko kunya bakiji wai kinzo duba jikin Mahaifiyarki kenan ko? cikakken mintuna talatin bakiyi ba tare da mahaifiyarki taki, da kika kwanan biyu baki gane ta ba ko?amma shi mijin da kullun kina ganinsa kullun tare kuke kwana amma a asibitin ma ba zakuyi hak'uri ba saboda tsabar jaraba irin..."
Kuka inteesar ta sake tare da nufar Gwaggo zata fad'a jikinta ne ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ta ce,
"A'a ni kada ki k'araso waje na ki shafa mani najasa nasan ko wankan tsarki ma bakiyi ba."
Jin kalaman bakin Gwaggo yasa Inteesar komawa jikin Mummy,rungume Mummy tayi tare da saka kuka, Mummy ma rungume ta tayi tare da d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi, tana shafa sumar kanta ta ce,
"Kema kinsan halin Gwaggo ba tun yau ba, haka take kada maganarta ya dame ki."
"Wallahi Mummy ba haka bane ba abuda mukayi."
"Ba komai ba sai kin rantse ba koda ma kunyi ba laifi kika aikata ba mijinki ne."
Tafa hannu Gwaggo tayi tare da cewa
"Yau ni kuluwa naga abun mamaki, 'yar albarka yaushe kika zama haka da rantsuwar k'arya? ko makaho ya kalle ki yasan da walakin goro a miya."
Mummy ce ta kalli Gwaggo ta ce,
"Kinga Gwaggo don Allah kibarta haka nan baki ga yadda taji bane, ai ba komai zakiyi magana aka..."
Kafin takai k'arshen maganar da zatayi Gwaggo ta ce,
"Dalla ni rufe mani bak, dan na fad'i gaskiya zaki ce me yasa? Yarinyar da tazo dubiya na uwarta ko mintuna talatin batayi ba amma ta tare ta k'unshe a cikin ofishin miji sama da awa uku, tun lokacin da suka dawo sallar azahar fa gashi yanzun k'arfe biyar suna nanik'arki juna, 'yar k'aramar yarinya da ita sai jaraba, ni nasanta ko da naje gidansu nayi wata d'aya akwai ranar da na aike ta ta Kira mijinta muyi Karin kumallo tare, tunda ta shiga bata fito ba har yunwa taci ta cinye ni, sannan suka fito yamutsai yamutsai da ita, tunda yanzun an masa Kiran gaggawa ai sai ki koma wajen Ummanki kafin ya dawo."
"Gwaggo nifa ba da son raina na biyo shi ba, cewa yayi yayi mije naci abinci da nak'i zuwa Mama ce tasa na biyo shi, kuma shi ya rufe office d'in da key ya hanani fita."
Rarrashinta Mummy tayi har ta daina kukan sannan ta shaida mata cewa ta shiga toilet ta watsa ruwa ta kimtsa jikinta ta koma wajen Umma, idan ya dawo sai su tafi gida, sallama sukayi suka tafi suka barta.
Bak'in ciki da takaici ne suka ishe ta,ga yunwa da ya addabe ta duk ta rasa yadda zatayi gaban dressing mirror ta tsaya ta gyara dogon sumanta tare da tufke shi, rigarta ta gyara zamansa ta rufe zif d'in rigar tayi bra d'inta da ya ya yaga gida biyu ta kalla d'agawa tayi taga ba yadda za'ayi ya moru, tsuki tayi tare da d'aukar hijabinta ta saka, ficewa tayi daga office d'in ta nufi hanyar da zara sada ta da d'akin da aka kwantar da Ummanta.
Tura k'ofar tayi ta shiga da sallama Abbanta da Mama Huraira ta gani sai Ummanta da ke kwance amma ba barci take ba, koda idanunta ya sauka akan Abbanta farin ciki ne ya lullu'be ta, dama tunda tayi aure bata k'ara ganin Abbanta ba, saboda ranar da suka je Muhdeen cewa yayi ya bata mintuna talatin ta gaishe su ta fito,hakan yasa bata ga Abbanta ba sai yanzun a asibiti.
Cikin farin ciki ta k'arasa gabansa tare da fad'awa jikinsa ta kwantar da kanta a kafad'arsa ta ce,
"Abba na nayi kewarka wallahi sosai."
Murmushi yayi tare da d'aga ta ya ce
"Kina lafiya?"
"Lafiya lau Abba na."
"Masha Allah ko na kira wayarki bata shiga ko kin canza layi ne?"
Tunawa tayi da tun ranar da Muhdeen ya kar'be mata waya bai bata