Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 149432 words

Chapter 16 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1385

Ads at the middle of Article

san mahimmancinta a gare shi."










Daga alkalamin ✍️


Maman Ihsan






Don K'arin bayani


09065327995






Love U oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*






Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa shi ta kowace siga.




Wannan kagaggen labari banyi tunanin rubutashi shi dan cinzarafi kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to ku garface ni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.




Page3️⃣1️⃣


"Sani akan me zaka bada kud'in kayan kaya lefe? bazaiyuwu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta ta?shi da kansa ya siyo,to haka ma Inteesar shine da kansa zai siya,saboda hakan zaisa yasan mahimmancinta a gare shi."


Kallon takaici Muhdeen ke yi wa Gwaggo sai da ta Kai K'arshen maganarta sannan ya ce,


"Banda kud'in da zan siya mata wani kayan lefe yanzu,dududu Yaushe nayi auren?sati biyu kenan fa kinsan miliyoyin da na kashe a lokacin auren nan kuwa?banda wani kud'in lefe yanzun keda kika had'a auren sai ki siya mata kayan lefen."


"Dan k'aniyarka ba gata nayi maka ba?"


Bud'e baki yayi da niyyar maida Mata da martani Dady ya daka masa tsawa.


"Kai Muhammad ka shiga hankainka , Mahifiyar tawa ce kake maidawa magana a gabana?"


Sunkuyar da kansa yayi k'asa yayin da Gwaggo ta d'ora da cewa


"A'a Sani ba ruwanka da shi ai wannan tsakanin kaka da jika ne ka kyalemu kawai."


Jinjina kai Dady yayi tare da kallon Muhdeen ya ce,


"To na dai sanar dakai sati mai zuwa Zata tare a gidanka,sannan batun kayan lefe Kai da kanka zaka had'o mata ne ko kuma kud'i zaka bayar?"


Hannu ya saka cikin aljihun wandonsa ya ciro A.T.M card d'insa ya mik'awa Mummy.


"Ga shinan duk abunda kuka siye sai ku cire ku biya tunda kinsan pin d'in."


Amsar A.T.M card d'in tayi tare da sa masa albarka.Dady ya mik'e don dama Shirin fita yayi,daga nan yayi masu sallama ya fita.Mummy ce ta ce,


"Bari na shiga ciki na d'auko waya ta na kira Aunty Abla ta shirya gobe zamu je mu had'o kayan lefen."


Daga nan Mummy ta mi'ke ta nufi d'akinta,Gwaggo ce ta kalle Mufida ta ce,


"Ke 'yar nan tashi ki d'auko Mani magani na nasha don anjima zamuje mu d'auko Inteesar"


Cikin zumud'i Mufda ta Fara magana


"Gwaggo anjima za'a d'aukota?"


"K'warai kuwa anjima za'a d'aukota mu kawota gidannan idan sati d'ayan yazo sai a kaita gidan mijinta."


Cikin farin ciki ta nufi d'akin Gwaggo yayin da Muhdeen ya mik'e ya fice, Gwaggo na ce masa


"Asauka lafiya"


Ko kallonta baiyi ba ya daka Kai ya fice.


Inteesar ce zaune a gaban Abba da Umma a tsakar gidansu,Abba ya kalleta cikin nutsuwa ya ce,


"Inteesar"


Jin yadda yadda Kira sunanta cikin wata irin murya yasa ta zuba mada ido tana jiran Mai zaice.


"Kiyi hak'uri na yanke shawara akanki ba tare da na tuntu'be ki ba,banyi shawara dake ba naji r'ayinki ba kiyi hak'u..."


Idonta ne ya ciko da k'walla cikin rawar murya ta fara magana


"Abba don Allah ka daina bani hak'uri akan koma meye,nice ya kamata na baka hak'uri ba Kai ba,duk shawar ko hukuncin da ka ga ya dace ka yanke akaina dai-dai ne Abba.Ni Mai biyayya a gare ka na ka daina bani hak'uri idan kana bani hak'uri ji nake kamar ban cika 'ya Mai biyayya a gare ka ba."


Shiru yayi cikin alfahari da 'yar tasa ya fara magama


"Na aurar da ke"


Da sauri ta d'aga ido tana kallonsa da mamaki,ganin irin kallon mamamkin da takeasa ne ya sashi fad'in


"Kiyi hak'uri"


Sunkuyar da kanta tayi k'asa hawayen da suka taru mata ne suka samu nasarar zubowa,cikin rawar murya ta ce,


"To Abba "


Hawaye ne suka cika idanun Umma Don bata ta'ba kowa wa a ranta cewa Nan kusa zata rabu da 'yarta tilo ba,Amma gashi k'addara tasa lokaci guda ba zato ba tsammani zasu rabu ba,ita da ganinta sai ranar da tazo gaishesu.Abba ya cigaba da cewa


"Ki kasance Mai biyayya ga mijinki yi nayi bari na bari duk abunda ya umarce ki da kiyi masa to kiyi masa matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba.sannan ki zauna lafiya da abokiyar zamanki ki bata girmanta a matsayinta na wacce take gaba dake,ki zama mai kauda kai akan al'amarin mijinki da abokiyar zamanki,kiji kik'i ji ki gani kik'i gani ki zama Mai kyautatawa ga kowa mijinki da danginsa da kowa da kowa.Ki zama Mai nutsuwa da kamun kai a duk inda kike,ki girmama mijinki kibi shi sau da k'afa kindai ga irin zaman da mukeyi da Mahifiyarki a cikin gidan nan kiyi koyi da ita."


Nan dai ya cigaba da Mata nasiha masu ratsa jiki Umma ma ta d'aura da nata, Inteesar dai kanta a sunkuye yake sai kuka da takeyi.Ganin kukan nata yayi yawa ne yasa Abba ya Umarce ta da ta tashi ta shiga d'akinta.


Bayan shigar ta d'akin ne,Abba ta kalli Unma ya ce,


"Dama kinsan munyi maganar kayan d'akinta akan zan siyar da dabbobi na a siya Mata kayan d'aki tunda auren ba shiyawa akayi ba."


"Eh na sani haka ne"


Cewar Umma dake goge hawayent,Abba ya d'aura da cewa


"Naje na samu kadintan nan dake bakin titi muna maganar kayan d'akin ne sai naga Alh.sani ,wato mahaifin Muhdeen ya tsaya da motarsa Yana horn,juyawa sai naganshi na k'arasa muka gaisa nan yake sanar Dani cewa kada muce zamu siye ki cokali domin su day kansu zasuyi Mata komai.Shi ya d'auki naiyin kayan d'aki komai zai siya matarsa kuma Hajiya Fatima zata siya Mata kayan kitchen,da na nuna cewa yayi yawa shine yake ce Mani Wai na manta cewa Inteesar 'yarsu ce?ko da ace ba d'ansu ne zai aure ta ba zasuyi Mata kayan d'aki ballantana tuwo na maina."


Cikin jindad'i Umma ta sanya masu albarka.




'Bangaren Muhdeen kuwa yana komawa gida Kai tsaye ya nufi d'akin Sumayya,yana Isa k'ofar d'akin kuwa ya samu K'ofar a wangale,Kai tsaye ya tura Kai cikin d'akin amma bata nan ga 'barnar da tayi kaca-kaca.Closet d'in ta ya duba kayayyakin da ta yayyaga kawai ke ciki, toilet ya nufa k'ofar toilet d'in ma a bud'e take,yana makin ina Sumayya ta shiga don dai bata shiga kitchen amma duk da haka ya kutsa Kai a cikin kitchen d'in ya duba bata nan.Gaba d'aya haka ya bincike gidan nan ko wane d'aki lungu da sak'o ba Sumayya ba alamarta,sai yayi dabarar tambayar Mai gadin ko yaga fitarta nan mai gadin ya sanar dashi cewa ta fita bayan fitarsa ba dad'ewa.Nan hankalinsa yayi masifar tashi har ya rufe mai gadin gidan da fad'a kamar zai rufe shi da duka shi dai hak'uri kawai yake bashi,don yasan bashida laifi amma yasa shi gaba da fad'a alhalin shi a matsayinsa na mai gadi ya isa ya hana matar gida fita?haka ya k'araci fad'arsa ya fice.


Gurin ajiye motocinsa ya nufa ya figi motar a guje Mai gadin ya wangale masa gate ya fice ya fice daga gidan.Parking yayi a gefen titi yana ta sak'e-sak'e ina Sumayya zata tafi?gashi Dad d'inta da Mum d'inta basa nan sun koma London,dama can suka fi zama ko sunzo Nigeria basa jimawa zasu koma.yanzun ta Yaya kuma ta Ina zai fara?


Kai tsaye gidan k'awarta Jumy ya nufa a k'ofar gidansu ya sameta tana zance da saurayinta a cikin mota,bayan yayi parking ne kasancewar Jumy ta hangi motarsa yasa ta fito,bayan sun gaisa ne ya tambayeta k'awar ta sanar dashi bata ga Sumayya ba ya sanar da ita cewa bata gida kuma wayoyinta duka basa shiga,daga Nan dai ya yi Mata sallama ya tafi,gidan Shila ya nufa nan ma bata nan k'arshe dai haka ya hak'ura ya nufi gidan Abokinsa Salisu,daga waje ya tsaya ya kira Salisu a waya ya sanar dashi cewaa yana gida ya shigo ciki.


Bayan ya shiga cikin gidan ne ya samu Salisu a fall da matarsa Saliha sai 'yarsu k'arama 'yar shekara d'aya mai suna Hidaya da sallama ya shigo falon.


"Assalamu Alaikum"


"Wa'alaika salam"


Salisu ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya k'arasa wurin Muhdeen ya bashi hannu sukayi musabaha tare da janyo shi ya zauna kan kujera.


"Abokina da alama yau dai kayi 'batan hanya ne ko?"


Murmushi kawai Muhdeen yayi tare da cewa


"Bari kawai"


Saliha matar Salisu ne ta gaida Muhdeen


"Ina wuni ango?"


Murmushin yak'e yayi tare da cewa


"Lafiya lau Saliha"


"Ya amarya?da Safen nan muka gama zancen zuwa gidanka naga amarya."


Murmushin yak'e kawai yayi tare da d'aukar Hidaya Yana Mata wasa.


Saliha ce ta nufi kitchen take ta kawo masa abun ta'awa,duk d yunwar da yake ji baya tunanin zai iya kai want abu a bakinsa.ganin Saliha na zaune ne kum ga shi magariba ta kusa yasa ya mi'ke yayi Mata Sallama ya nufi k'ofar fita inda Salisu yabi bayansa suka fice.
A Harabar gidan suka tsaya Salisu ya zuba masa idanu ganin yadda yadda gaba d'aya ya canza lokaci guda.


"Lafiya kuwa?naga gaba d'aya ka sauya me ya faru ne?"


Ajiyar zuciya Muhdeen ya sauke,sannan ya bawa Salisu labarin duk abunda ya faru.A jiyar zuciya Salisu ya sauke.


"Lallai kana cikin yanzun abuda za'ayi shine mu bari muyani Ko Sumayya zata dawo idan har takai dare bata dawo ba zuwa gobe da sassafe sai mu san abunyi."


Nan dai suka cigaba tattaunawa kafin sukayi Sallama ya tafi.


Washe gari ne ya kama ranar da za'aje a had'o ma Inteesar kayan lefe,kuma a ranar ne za'a d'auko ta a kawo ta gidan su Mummy.Da misalin k'arfe goma na safe ne Aunty Abla k'anwar Mummy da kuma k'awar Mummy Hajiya Ameera suka zo don siyowa Inteesar kayan lefe.su uku suka tafi Mummy da Aunty Abla da Aunty Ameera ne suka tafi,aka bar Gwaggo da Mufida a gida.


'Bangaren Inteesar kuwa kwana sukayi ita da Ummanta tana tayi mata nasiha Inteesar tasha kuka kamar ba gobe har idanunta sun kumbura,ita dai bata san waye mijinta ba abunda ta sani kawai ance mata an aurar da ita, kuma an sanar da ita cewa yau zata koma gidan Mummy da zama kafin ranar juma'a akaita gidan mijinta.Bayan wannan bata san komai ba.Haka dai dai tayi ta Addu'a tana Kai kukanta ga Allah akan auren nan yasa ya zama alkhairi a rayuwarta.


Da misalin k'arfe biyu na rana Mummy da su Aunty Abla suka dawo nik'i -nik'i da akwatunan da kayyaki a ciki akwatunan guda takwas ne da kayan da duk ake had'awa a cikin lefe,komai yayi kyau masha Allah.Nan dai aka bajewa Gwaggo kayan tana dubawa tana Sanya alkhairi da Addu'a Allah yasa shekara Mai zuwa ta Muhdeen da Inteesar.


'Bangaren Muhdeen kuwa ya yi neman Sumayya har ya gaji,ya Kira layin wayarta bila adadin shida Salisu tun safe suke ta nemanta Amma ba Sumayya ba labarinta,duk inda yasan tana da alak'a da mutanen wajen sun tafi wajen amma basu sameta ba. a cikin kwana d'aya muhdeen yabi ya zabge ya fita hayyacinsa domin hankain Muhdeen yafi jirgin sama tashi.








Daga alk'amin ✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




*DOMIN K'ARIN BAYANI*


09065327995




Love u oll🥰😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*


Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.




Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne mai kashe auren wawa.




Page3️⃣2️⃣


A cikin kwana d'aya muhdeen yabi ya zabge ya fita hayyacinsa, domin hankalin Muhdeen yafi jirgin sama tashi.




A yammacin ranar ne Gwaggo da Aunty Abla da Hajiya Ameera suka je gidansu Inteesar dan d'auko ta.Umma ce da k'anwar ta Huraira sai k'awayenta su biyo da kuma mak'ota da suka shigo Umma ta sanar dasu,duk da ba taron biki akayi ba amma za'ayi taron biki ranar juma'a a gidan Mummy.Mama Huraira k'anwar Umma ce ta shirya Inteesar cikin atamfa riga da zani da Ummanta ta d'nika mata sai mayafi fari da aka yafa mata ta lullu'be fuskarta da shi,idan ka ganta sai ka tausaya Mata idanunta duk sun kumbara sunyi jazir hatta fuskarta ma duk tayi ja ta kumbura saboda tsabar kuka.Ita dai gata zata rabu da Abbanta da Ummanta,zata je can wani gida inda zata shirya sabuwar rayuwa gashi ita kanta ba'a fad'a mata waye mikinta ba kuma itama bata tambaya ba, tambayar da taketayiwa kanta shine,shin shima mijin bai santa ba kamar yadda itama bata sanshi ba?shin wace irin rayuwa zata yi?yanzun shikenan ta rabu da Ummanta da Abbanta kenan sai randa yazo gaishe su?


Kuka ne yaci k'arfinta dakyar mama Huraira ta rarrasheta tayi shiru ta dakatar da kukan da takeyi.Nasiha sukayi mata Mai ratsa jiki sannan aka ja hannunta don tafiya,nan fa ta coge ta ri'ke hannun Umma tana kuka dakyar aka 'ban'bare hannun Umma daga nata,hakan yasa Umma itama hawayen da ta rik'e suka samu nasarar zubowa.A haka tana kuka suka nufi hanyar fita inda Mama Huraira ta tsaya da ita zauren gidan wajen Abba,shima ya d'ora da nasa nasihar sai kuka Inteesar take yi,haka dai aka ja hannunta suka nufi hanyar fita, inda aka jera motoncin.Motoci guda uku ne aka shiga da Amarya d'aya inda Mama Huraira da k'awayen Ummin suka shiga mota d'a ma'kotansu ma d'aya,yayinda su Gwaggo da Aunty Abla ma suka shiga d'aya.duk da cewar unguwa d'aya ce basu da nisa minti kad'an suka isa gidan,bayan Mai gadi ya wangale masu gate ne suka shiga nan aka firfito Mama Huraira ce ta rungume Inteesar ta gefen kafad'arta suka shiga cikin gidan.


Part d'in Muhdeen da ya zauna kafin ya auri Sumayya nan aka ajiyeta,duk da cewar ba dad'ewa yayi da barin d'akin ba sati biyu kenan,ba wani k'ura sosai dama Mummy ta sanya Mufida ta gyara part d'in.Da sallama suka shiga falon ba kowa sai k'amshi ke tashi,har bedroom aka shiga da ita inda aka zaunar da ita bakin gado.kasncewar lokacin sallar magariba ne yasa sukayi Mata sallama akan cewa zasu dawo ranar juma'a,waro ranar da za'a kaita gidan mijinta.


Har yanzun Inteesar Bata san waye mijinta ba ta d'auka saboda shak'uwar da ke tsakaninta da 'yar gidan su Mummy yasa aka ce ta zauna nan gidan kafi akaita gidan mijinta.


Bayan kowa ya watse ne ita kad'ai ta ragae a d'akin,ido ta zubawa d'akin tana k'are masa kallo a zuciyarta tana cewa d'akin wannan mugun aka kawo ni,mutum sai mugunta da da bak'in hali a haka dai ta nufi toilet ta d'auro alwala tazo ta shimfid'a sallaya ta tada sallah.


A can aibitin Muhdeen kuwa Salisu ne ya fito daga d'akin tiyata hankalinnsa a tashe, wayarsa ya ciro Number Muhdeen yayi dialing, Muhdeen na kwance a samam gadonsa ya lumshe idonsa kamar mai bacci tunanin Sumayya kawai yakeyi,ya rasa ina zai same ta faga k'arshe dai ya yanke shawarar zuwa London wata kila can take tafi wajen iyayenta,yana cikin wannan tunanin ne wayarsa ta fara ruri da sauri ya bud'e idonsa don kullun baya cire rai akan Sumayya zata kira sa,ganin Jabeer ne yasa shi sakin tsuki don dama haushin Jabeer ya ke ji akan bai goyi bayansa ba ya juya masa baya.Yana gani wayar ta katse bai d'aga ba,har aka k'ara kira still bai d'aga ba sai da Jabeer ya kira sau biyar sannan ya d'aga don yasan idan Jabeer ya matsa da kira akwai abu mai mahimmanci da yasa shi yawaita Kiran.Daga wayar yayi ba tare da yayi magana ba,ganin ya d'aga yasa Jabeer ajiyar zuciya ya ce,


"Muhdeen akwai matsala fa"


Tsaki muhdeen ya yi tare da cewa


"Kaine bak'on matsala ni tun jiya nake cikin matsala ka sani."


Cikin tashin hankali Jabeer ya cigaba da magana


"Kaga duk abunda kake ka bari ka taho nan Hospital Emergency ne..."


"Kamar ya duk abunda nake na bari nazo?Kai me kake yi da ba zaka yi abunda ya..."


Katse sa Jabeer yayi tare da cewa


"Ba lokacin dogon magana tunda kayi aure k'afarka bai lek'o Asibiti ba kullun kana gida,ban ta'ba kiranka ba sai yau to tunda kaga na kiraka abun yafi k'arfin mu ne don Allah kazo ba lokaci."


Katse wayar yayi tare da mi'kewa time ya duba k'arfe goma na dare wayarsa ya saka a aljihun wandonsa ya d'auki makullin motarsa ya fice don zuwa Asibit.




Inteesar kuwa tunda ta idar da sallar magarib bata tashi ba sai da ta idar da sallar isha'i.Bakin gadon ta zauna har mai aikin Mummy ta kawo mata abinci da abunsha,ruwa kawai tasha ta zauna tayi tagumi tare da fad'awa duniyar tunani.


Mufida ce tayi sallama


"Assalamu Alaikum"


Inteesar da ta kwanta akan sallaya ta amsa da cewa


"Ameen wa'alaiki salam"


Mufida madadin ta shiga sai ta tsaya daga bakin k'ofar tayi shiru,jin shirin yayi yawa ne yasa Inteesar cewa me haka Mufida ki shigo mana,cikin tsokana Mufida ta fara magana.


"Wace ni da zan shigo d'akin ma'aurata kai tsaye,na sani ko Angon na ciki?"


Ta shigo tana k'unshe dariya a bakinta,kallon mamaki Inteesar ke yi wa Mufida cikin takaici ta fara magana


"Nagode Mufida wato ma dariya kike mani ko?ina cikin k'unci ke kina farin ciki ko?me yasa kika canza mun ada tare muke kuka tare muke dariya Amma yanzun Ina kuka ke kuma dariya kike mani ko?"


"Ba haka bane Inteesar matsalarki tawa ce tawa ma taki ce, gaskiya ina farin ciki da wannan auren naku sosai ba kad'an ba."


Ran Inteesar ne ya 'baci sai ta fashe da kuka tare da fad'awa jikin Mufida ta fara magana cikin kuka.


"Mufida bansan yadda zanyi ba anyi mani aure ba tare da na shiryawa hakan ba,banida burin aure yanzun ban sakawa raina aure nan kusa ba,karatu naso nayi Mifida bansan dalilin da yasa lokaci d'aya Abba na ya aurar dani ba.banyi wani abu na rashin kyautatawa ba ko na rashin d'a 'a ballantana nace ko shine dalilin da yasa suka aurar dani kudun kada na kunyata su.Kuma wani abun takaicin ma ki Mijin da aka aura mani bansanshi ba Mufida."


Tausayinta ne ya cika Mufida,don tabbas tasan cewa Inteesar karatu tasa a gaba sai gashi Allahu yayi ikonsa sai dai abin da ya d'aure mata Kai yadda akayi Inteesar Bata san waye mijinta ba.


"To wai ke ya akayi baki san mijin da aka aura making ba?"


"Basu fad'a mani waye mijina ba nima bazan iya tambayarsu ba"


Shiru Mufida tayi kamar ta fad'a mata waye mijin Amma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads