Header Ads
Showing 141001 words to 144000 words out of 149432 words

Chapter 48 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1357

Ads at the middle of Article

matakin da batayi niyyar ɗauka ba.haka ta zauna tana jiran fitowarsu dan tasan baya wuce awa ɗaya ya gama.


"Shiru ta ji awa ɗaya ya wuce basu gama ba, tana duba agogo awa biyu nan ma shiru, hankalinta ya tashi sosai dan tunda take da Muhdeen 50 minutes ko 1 hour then ya gama sex, amma yanzun awa biyu ya ɗauka yana sex shiru bai gama ba, tana zaune har awa uku baƙin ciki dabtakaici duk ya ishe ta, kamar ta tashi tabar gidan amma ba zaiyiwa ba dan idan ta tashi ta tafi shirinta zai wargaje, dan haka ta samu wuri ta zauna.


A can cikin ɗakin kuwa sai da Inteesar ta gaji ta saka masa kuka sannan ya ƙyale ta yana rarrashinta, zuciyarsa cike da farin ciki da annashwa wani ƙaunarta ne ya ƙara ninkuwa a cikin zuciyarsa, da kansa ya ɗauke ta ya Kaita banɗaki, sukayi wanka, duk da bata saki jiki ba kunyarsa ne kawai ke dawainiya da ita.


Bayan sun gama wanka ne suka fito, gaba ɗaya Inteesar yunwa take ji, a daddare ta saka doguwar riga na atamfa bata ma tsaya wane makeup ba, shi kuma yana ɗauke da towal a ƙugunsa dan ba kayansa a nan ɗakinsa zai je ya saka kaya, ganin yadda take sauri ne yasa ya kalle ta lokacin da ta jona handryer tana busar da suman kanta, nan da nan ta gama ta tufke suman a tsakiyar kanta bayan ta nannaɗesa saboda tsawonsa, bata ma tsaya ɗaura ɗankwali ba siririn mayafinta ta ɗauka ta yafa gana ƙoƙarin fita ne ya ce,


"Saurin me ye wannan?"


"Kitcheen zan tafi"


"Me zakiyi a kitchen?"


"Ƙarfe ɗaya ya kusa fa kuma ni yunwa nake ji"


Da mamaki ya kalle ta dan yasan bata samu da cin abinci ba, murmushi yayi tare da cewa


"Kece da jin yunwa har kina sauri haka? ko da yake abincin da kika ci na zazzagar da shi ko?"


Ya ƙarasa maganar cikin tsokana, yayinda ita kuma kunyarsa ne ya sake dirar mata, dan hakan ta nufi ƙofar fita a guje ta buɗe ƙofar tana dariya, yayin da shima yabi bayanta.


Tana zuwa tsakiyar falon tayi turus, sakamakon ganin Sumayya zaune ta zuba mata ido, shima tsayawa yayi yana kallon Sumayya da mamaki a fuskarsa.


Murmushin ƙarfin hali Sumayya tayi tare da cewa


"Kun fito?"


Muhdeen dai bai bi ta kanta ba ya nufi ɗakinsa, yayin da Sumayya ta cigaba da cewa


"Ance ka girmama baƙonka, amma ni naga kamar bakiyi farin ciki da zuwa na ba ko? shikenan bari na tashi na bar maki gidanki."


Miƙewa tasaye tayi tare da kallon Inteesar, har ta kai baƙin ƙofa Inteesar tayi saurin binta ta riƙe hannunta tare da cewa


"Kiyi haƙuri Aunty Sumayya ba haka bane, mamaki ne ya hana ni magana"


"Mamakin me kike yi?"


Ta ƙarasa maganar da sakarwa Inteesar murmushi, itama martani murmushi ta maida mata ta janyo hannunta ta ce,


"Dawo ki zauna Aunty Sumayya nan ma ai gidanki na"


Zama sukayi ta kalli Sumayya da ke murmushi ta ce,


"Ina wuni Aunty Sumayya?"


"Lafiya lau ƙanwata ya kike ya amarci?"


Sunkuyar da kanta kawai tayi tana murmushi, yayinda Sumayya ke wata mata harara ji take kamar ta shaƙeta ta mutu.


Ganin Inteesar ta ɗago da fuskarta ne yasa ta yi saurin sakin murmushi


"Kunga ki saki jikinki da Ni kinji? ki ɗauke ni a matsayin ya a gare ki, ki mance da abubuwan da na maki a baya, nayi nadama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, ko makamancinsa ma na ɗauke ki tamkar ƙanwa ta da muke uwa ɗaya uba ɗaya da ita, haka nake so nima ki ɗauke ni, kinsan ba iya girki ba kuma mijinki baya son na masu aiki, saboda haka na yanke shawarar idan ba zaki damu ba zan dinga zuwa kina koya mani girki na tsawo sati ɗaya."


Kallonta Inteesar tayi tana tunani kafin ta ce


"Bakomai"


Kin amincewa shawara ta?"


Kai ta girgiza alamar amincewa ta ce


"Na amince bari na sanar da yaya."


Daga nan ta miƙe ta nufi ɗakinsa, ya gama shirinsa zai fita, murmushi ya sakar mata tare da cewa


"Nazo na tayaki girkin ne?"


Ya ƙarasa maganar yana murmushi


"Ka barshi kawai ba aikinka bane, zamu shiga kitchen yanzun tare da Aunty Sumayya."


Take fara'ar fysakarsa ya ɗauke ya ce,


"Kinga kada daɗin bakinta ya ruɗe ki, Sumayya tafi ƙarfin ki ta wuce sanin tunaninki, nasan wace ce ita haka nan awai ba zata zo gidan nan da sunan ki koya mata girki ba, domin yadda masana da jinkai hakan zai zama kamar ƙasƙanci ne a wurinta, matuƙar ta ajiye jin kanta da taƙamarta yazo gare ki da sunan koyon wani abu to ki tabbata da biyu tayi hakan, akwai dalili da kuma wani buri da take da shi akanki, ki bita a sannu dan ta fiki wayo da dabara kina da saurin yarda da mutane hakan zai bata damar samun abinda take so daga gare ki cikin sauƙi, shiyasa kika ji na ce ban amince da ita ba, ni kaina zanso zaman lafiya da haɗin kai da junanku, amma tunda na ce maki a'a akwai abunda na hango."


Murmushi tayi tare da cewa


"Ta nuna mani nadamarta naga sauyi a tattare da ita, bazan shige mata ba sai dai bazan iya ƙin amincewa da alfarmar da tazo nema daga gare ni ba."


Jinjina kai yayi tare da cewa


"Shikenan Allah ya ya kaɗe fitina a tsakanin ku ya haɗa kanku."


Murmushi tayi tare da cewa


"Ameen ya rabbil izzati"


Tare suka fito daga bedroom ɗin, suka tarar da Sumayya a falo, zama yayi a akan kujerar da ke kusa da Sumayya, ido ya zuba mata dan haka kawai bai yarda ba abinda ta zo da shi ba , dan yasan halinta sarai, ganin irin kallon da yake mata ne yasa ta ce,


"Wai Baby naga kamar baka so zuwa na gidan nan ba, ko baka son kaga kan matanka ya haɗu ne?"


Murmushi yayi wanda iya fatan bakinsa ya tsaya


"Idan akwai wanda zai so haɗin kanku da zaman lafiyarku a baya na yake, domin zaman lafiyarku shine kwanciyar hanakali na."


"To me yasa naga yanayinka ya canza?"


.Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa


"Sumayya Inteesar ƙaramar yarinya ce a gare ki, dan Allah ki riƙe ta amana da zuciya ɗaya, bata da matsala idan kika kama girmaniki nasan zata maki biyayya, ke kanaki shaida ce akan biyayyar ta ɗan zaman da kuka yi da ita, ki ɗauke ta ƙanwa ba kishiya ba ki riƙe girmaniki a matsayinki na babba."


Juyawa yayi ya kalli Inteesar tare da cewa


"Inteesar Sumayya ba tsararki bace ta girme ki a shekaru da kuma gidan aure, ki bata girmanta a matsayinta na babba a gare ki, bana son raini ya shiga tsakaninki da ita, kuyi haƙuri da junanku banda ɗaukar zuga, duk wacce ta batawa 'yar uwarta rai kata ce zatayi faɗa da ita, ta same ta ta sanar da ita abinda tayi mata wanda bata ji daɗinsa ba su fahimci juna, Allah ya haɗa kanku."


Amsawa sukayi da Ameen, daga nan ya tashi ya nufi masallaci, Inteesar ta kalli Sumayya tare da cewa


"Aunty duk da rana tayi bari na dafa mana ko Taliya ce ko?"


Murmushi tayi tare da bin bayanta tana cewa


"Muje muyi tare na fara koya tun yanzun ."


Tare suka shiga kitchen ɗin Inteesar na mata bayanin yadda ake komai, tana kuma yi a akace yadda zata gane, wani abun ma da kanta zata karɓa ta zuba, a haka har suka girka jallop ɗin taliya da yaji kayan lambu da busashshen kifi.


Jin an tada sallah ne ya sa Inteesar cewa


"Aunty bari naje nayi sallah ko?"


Kai Sumayya ta jinjina tana murmushi ta ce,


"To sai kin fito nima na je nayi"


Inteesar ce ya fita daga kitchen ɗin ta nufi ɗalibta dan yin sallah,tana fita Sumayya ta bita da harara tare da yin tsuki.


Bayan Inteesar ta shiga ɗauki ne ta faɗa toilet bayan ta ɗan gyara zanin gadon da ya yamutshe, ta kauda komai.


Alwala ta ɗauro yazo ta gabatar da sallar azahar, bayan ta idar tare da yin addu'a sannan ta bar salllayar a wajen tare da ajiye hijabin akan sallayar dan Sumayya idan tazo tayi amfani da shi, dan ba da hijab tazo gidan ba.


Bayan ta fita ne ta samu Sumayya a falo tana zaune a kujera.


"Aunty na idar kije kiyi sallar sai muci abinci ko?"


Jinjina kai tayi


"Okay to"


Miƙewa tayi ta nufi ɗakin Inteesar dan yin sallah, dan da ba don da Inteesar ta ce tayi sallar ba ba yi zata yi ba, sai da ta tsaya ta na ƙarewa ɗakin kallo yadda aka tsara shi, gwanin sha'awa, komai tsaf a mahallin da ya dace, taɓa baki tayi ta nufi toilet ɗin.


Muhdeen ne ya turo ƙofar falo ya shigo tare da sallama, Inteesar dake zaune a falo ya amsa masa sallamar, ƙarasowa yayi tare da zama gefenta ya riƙon hannunta cikin nasa .


"Ina Auntynki take?


"Ta shiga tayi sallah, bari ta fito sai muci abinci."


Yana rufe baki sai ga Sumayya ta fito daga ɗakin Inteesar, idanunta ne suka sauka akan hannun Muhdeen dake sarƙe a cikin na Inteesar, kauda kanta tayi gefe, Inteesar tayi ƙoƙarin zame nata amma sai ya sake riƙe hannun da kyau kallon sa tayi ya ɗaga mata gira ɗaya kauda kanta gefe tayi tare da miƙewa tsaye ta ce,


"Muje Aunty dame ke nake jira."


Jin hakan yasa Sumayya tayi saurin nufar dinning table dan ba zata iya sake kallonsu a haka ba, a haka suka nufi dinning room ɗin sai a lokacin da zai zauna ne ya saki hannunta.


Ta dauki plate da zuba ma Muhdeen ta ajiye masa, sannan ta zubawa Sumayya itama ta tsiyaya masu lemo da ruwa ta ajiye masu, sannan ta zuba nata itama, kallonta yayi tare da cewa


"Duk kiran yunwar da kike yi iya abincin da zaki ci kenan?"


Dariya tayi ta ce,


"Yaya wannan fa ya ishe ni."


Nan suka fara cin abincin a tare har suka kammala, Inteesar ta tattara kayan Muhdeen yayi falo kan kujera ya zauna, Sumayya ma ta biyo shi kasancewar a doguwar kujera ya zauna hakan yasa itama ta zauna kusa da shi tare da kwantawa ta ɗaura kanta a saman cinyarsa, wasa ta fara yi da yatsun hannunsa, shima bai hana ta ba, har Inteesar ta kammala wanke kwanonin ta dawo falo ta same su a haka, bata nuna ɓacin rai ko damuwa ba ta zauna kujerar da ke gafensu.


Sai yamma bayan sun kammala cin abincin dare ne sannan Sumayya ta shirya don zuwa gida lokacin da zasu raka ta wajen mota ta kalli Inteesar ta ce,


"To ƙanwata sai kuma gobe idan na dawo ko? ango ma da zai mana kwana biyu biyu to na ƙara maku kwanaki biyar, ku ɗauka yau ne aka kawo ki gidan mijinki a matsayin amarya."


Farin ciki a waje. Muhdeen ba'a magana dan har ya kasa ɓoyuwa, godiya yayi wa Suamya dan ya ji daɗin hakan da tayi, bayan ta ja motarta mai gadi ya buɗe mata gate ne ta bar gidan.


Haka rayuwa tayi ta tafiya Inteesar tana samun kulawa sosai daga wajen Muhdeen, kuma kullun Sumayya tana zuwa gidan dan koyon girki, dan yanzun ba girki kawai take koya mata ba, har da gyaran gado da ɗauki da duk wasu aikace-aikace na cikin gida. Idan Muhdeen ya kwanaki biyu a gidan Inteesar haka zaiyi kawanki biyu a gidan Sumayya, yana ƙoƙarin kwatanta adalci a tsakaninsu, sai dai matsayin Inteesar na musamman ne a cikin zuciyarsa, idan tana aiki a asibita da zaran ya samu sarari zai kira ta suyi ta fira da juna, ko suyi Video call tsabar kwanciyar hankali da ta samu da kula daga gare shi har ta ɗanyi ƙiba tayi kyau sosai.


Gidan iyayen Inteesar kuwa haka Muhdeen ya sa a rushe shi, a maida masu shi zubin na zamani, dama Umma tana shirin zuwa Gombe jikin mahaifiyarta ya tashi bata da lafiya, tana son zuwa ta gaida mahaifiyarta a Gombe, koda Inteesar ta ji labarin abinda za'ayiwa iyayenta tayi farin ciki sosai da jin wannan zancen taso ta bi Ummanta suje Gombe tare amma Muhdeen ya gama ya dai ɗaukar mata alƙawarin idan ya samu dama zasu je tare shima ya gaida danganta, a haka ya haƙura ana gobe Ummanta zatayi tafiyar ne daddare suka je ita da Muhdeen, inda ya kaiwa Umma sha tara na arziki, ya ɗaukar mata shatan mota da zai Kaita har Gombe tare da bata kudi masu yawa, sanan sukayi mata sallama, inda ta dinga saka masu albarka tare da godiya, Abba ma da ya shigo ya tarar da abinda Muhdeen yayi ya masa godiya sosai da tarin addu'oi.


Bayan tafiyar Umman Inteesar da kwana biyu, Inteesar tayi waya da Ummanta, inda Ummanta ke sanar da ita jikin kakar ta Inteesar yayi tsanani, Inteesar hankalin ta tashi matuƙa har ta samu Muhdeen da zancen zata je kila su gana kafin ta rasu, amma duk da haka bai barta ba, Sumayya ce itama ta saka baki ta matsa masa, wanda hakan yasa ya bata izinin zuwa Gombe ya haɗa ta da direba da zai Kaita ya dawo da ita, inda Inteesar ta ƙara ganin girman Sumayya a idanunta, mutuncinta ya ƙaru sosai a idanun Inteesar.


Ana gobe zata tafi ta je tayi sallama da su Gwaggo da su Mummy, haka nan kawai jikin Muhdeen ya bashi cewar akwai wani mummunan abunda zai faru da Inteesar, dan shi dama yakan ji a jikinsa indai wani mummunan al'amari zai faru da na kusa da shi jikinsa na basa, dan haka yaso hana amma Inteesar da Sumayya suka matsa dan haka yayi ta addu'a.








*Daga alƙalamin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI*


09065327995




Love you oll😘😍


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a






*INTEESAR*


Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_*
*_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_*
*_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_*
*_dama wadanda zasu ganki ahanya?_*
*_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_*
*_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_*
*_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_*


```ARZUQLANA GALLERY```


*_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_*
```Laces
Atampha
Shadda
Abayas
Materials
Gyale
Takalma
Jaka
Kayan Kitchen
Bangles n jewelries```
*And many more*


```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO```
*_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_*


*_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_*


*_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_*



*_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_*
https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ










*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGAƊI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shiga ta kowace siga ba tare da izina ba.




Page7️⃣8️⃣


Ana gobe zata tafi ta je tayi sallama da su Gwaggo da su Mummy, haka kawai jikin Muhdeen ya bashi akwai wani mummunan abunda zai faru da Inteesar, dan shi dama yakan ki a jikinsa indai wani mummunan al'amari zai faru da na kusa da shi, dan haka yaso hana amma Inteesar da Sumayya suka matsa dan haka yayi ta addu'a.


Ranar da Inteesar zata tafi dama ba ita ce da girki ba Sumayya ce, da n hakan Muhdeen a gidan. Sumayya ya kwana, da asuba ya shirya ya tafi masallaci, bayan ya dawo ne yake sanar da Sumayya zaije suyi sallama da Inteesar, itama ta dage sai ta bishi, ba yadda zaiyi dan haka ya barta suka fito tare da zumar zuwa gidan Inteesar,


Motarsa ya ɗauki ya tada suka tafi.


A ƙofar gidan ne ya tarar da direban da zai kai Inteesar Gombe, kasancewa Ishaq Direban Muhdeen baida lafiya yasa aka samo masa wanan, abokin Ishaq ne sosai, bayan sun gama gaisawa da Direban kai tsaye ya nufi cikin gidan bayan yayi horn mai gadi ya buɗe masa, bayan yayi parkinga ne suka fito Sumayya na biye da shi a baya.


Da sallama suka shiga falon zaune ta ke ta haɗa hannayenta biyu tayi tagumi, da alama tayi nisa a cikin tunanin da take ne, tsayawa yayi ya rungume hannunsa a ƙirjinsa, Sumayya ce ta ƙarasa ta zauna gefen Inteesar tare da cire hannun da tayi tagumi ta cire tare da zuba mata ido, sai a lokacin Inteesar ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula, dubanta ta fara kaiwa ga Sumayya da ta cire mata hannu, kafin ta maida dubanta ga Muhdeen, cikin sanyin muryarta bayan ta durƙusa cikin girmamawa ya ce


"Ina kwana yaya?


"Lafiya lau, kin tashi lafiya ya shirye shirye?


"Alhamdulillah"


Ta amsa masa, sannan ta maida dubanta ga Sumayya ta ce,


"Aunty Ina kwana?"


"Lafiya lau Inteesar ya shirin tafiya?"


Ganin yadda yanayinta ne yasa Muhdeen cewa


"Lafiya naga kamar akwai wani abinda ke damunki ko?"


Kai ta girgiza


"Ba abunda ya same ni, kawai dai ina jin jiki na wani iri, tafiyar ma ta fitar mani a rai, amma ba yadda zanyi dole na je, tunda suna can suna saka ran zuwa na ."


"Kinga nima fa ba son tafiyar nan nake ba."


"A 'a baby kada la kashe mata gwiwa, ka dai mata addu'ar dawowa lafiya."


Jinjina kai yayi tare da jan hannun Inteesar, inda yake cewa


"Zo mu shiga ciki muyi sallama da kyau ko?"


Sumayya ce ta bishi da kallo tare da cewa


"Baby ana jiranta a waje ga direban can yana jiran fiowarta,"


Murmushi yayi tare da cewa


"Kada ki damu da yanzun zamu sallami juna."


Daga nan bai sake magana na kuma bai daki hannun Inteesar ba.


Suna shiga ɗakin ya murzawa ƙoafar key ya rufe ta ciki.


Sumayya kuwa yana shiga da Inteesar tabi bayansa a hankali ta maƙale a jikin ƙofar dan ta dinga sauraron abunda zai faɗa ma Inteesar.


Shi kuma bayan ya zare key ɗin kawai sai ya zauna kan kujera, tare da janyo ta ya ɗauka ta samun cinyarsa ya fara magana


"Gaskiya zan ji kewarki sosai, dan kwanaki bakwai da zakiyi a can ji nake kamar shekaru bakwai zakiyi, dan rashinki a rayuwata babbar giɓi ce, amma ni naga kamar ke baki damu da ni ba ko? "


Murmushi tayi tare

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads