Header Ads
Showing 63001 words to 66000 words out of 149432 words

Chapter 22 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1396

Ads at the middle of Article

na rashin sabo da juna sai kin gane kurenki,kada ki nuna d'ari ko wani shakkata da kike idan kunne ya ji jiki ya tsira.
Bud'e murfin motar ya yi ya fito itama ta fito,inda ta tsaya gaida su Mallam Ibrahim Mai gadi da sauran ma'aikatan gidan,inda suka ta ya ta murna da Allah sanya alkhairi,sannnan suka gaida Muhdeen,nan suka nufi hanyar cikin gidan tana gaba Yana binta a baya saida suka k'arasa k'ofar falon sai ji kawai tayi ya rik'o hannunta cikin nasa da sauri ta kalle shi,ji kawai ya ja hannunta suka shiga falon bakinsa d'auke da sallama.


"Assalamu Alaikum"


Gaba d'ayansu suka amsa sallamar tare da kallonsu, Gwaggo,Dady, Mummy,da Mufida.


Kunya ce ta rufe Inteesar ta yi k'ok'arin zame hannunta cikin nasa Amma ina bai bata wannan damar ba, sunkuyar da kanta k'asa ta yi har suka k'araso wajensu,Gwaggo sai washe baki take tana cewa


"Lale marhaba da zuwa 'yar albarka,lale lale."


Zaunawa sukayi a saman center carpet kusa da Mufida, Mummy ma ta ji dad'in zuwansu sosai da yadda tagansu sai ta yi farin ciki matuk'ar jin dad'i ta nuna,har lokacin bai saki hannunta ba, Gwaggo ta ce,


"Dalla sake mani hannun yarinyar albarka mu gaisa,ka wani rirrik'eta kamar za'a k'wace maka ita."


Gwaggo ta janyo hannunta ta janyota gaban kujerar da take zaune ido ta zuba mata ma wasu 'yan mintuna kafin ta ce,


"Muhammadu haka aka aura maka yarinyar Nan?"


Kallon Gwaggon ya yi don ya san me zata ce,kauda kansa ya yi daga dubanta ya maida dubansa ga Dady.


"Dady ina wuni."


Cikin sakin fuska ya amsa masa da


"Lafiya kalau Muhammad ya iyalin?


"Alhamdulillah"


Dubansa ya maida zuwa ga Mummynsa


"Mummy ina wuni?"


Lafiya lau son kuna lafiya?"


"Lafi..."


Kafin ya gama fad'in lafiya lau Gwaggo ta fara magana


"Ba wani lafiya da kake k'ok'arin cewa,lafiyarce za'a da'auki 'yar mutane a baka da d'an kumarinta a cikin kwanaki takwas naga yarinya ta rame sannan ka ce wa mutane lafiya?to gara ma ka fad'i gaskiya don banga alamar 'yar nan tana cikin kwanciyar hankali ba, Muhammadu kalleni in kalleka nan ba k'aramar yarinya ba ce ni da zaka raina mani hankali nasan k'ugin ciki nasan na gwaiwa wallahi duk wanda yasan 'yar albarka a baya ya kalleta yanzun yasan ba farin ciki da walwala a tare da ita."


Dubanta ta maida kan Dady da Mummy ta ce masu


"Kuma da yake ba tsoron Allah kuke ba bakusan laifin d'anku,har zaku kalli Inteesar ya ce maku suna lafiya ku yarda?"


Girgiza kai Dady ya yi Dan ya Saba da halin mahaifiyarsa,inda Gwaggo ta cigaba da cewa


"Da na ce sai nan da sati d'aya zanzi gidan naku nayi wata d'aya amma yanzun na fasa,jibi zanzo gidan naku dan hankalina ya tashi daga ganinta kasan bata cikin kwanciyar hankali,Amma kuka yi shiru tunda ba 'yarku Asiya bace."


Muhdeen ya tanka Mata


"Wai ke wannan tsohuwar me ke damunki ne haba mana,kince Bata cikin kwanciyar haankali to ki tambayeta idan ina mata wani abun da bata so."


"Me kake ci na baka na zuba? ai ba sai ka fad'a mani ba,da kaina zan tambayeta nasan halin da kuke ciki."


Janye hannun Inteesar ta yi tare da cewa


" kinga tashi mu tafi d'aki kinji 'yar albarka."


'Daga Kai Inteesar ta yi ta kalli Muhdeen ya yinda shi kuma yi mata wani kallo Mai cike da gargad'i karaf kuwa a idanun Gwaggo.


"La'ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi salallahu alaihi wasallam kallon uwar me kake mata haka?wato kada ta fad'a ki?to kada ka damu sai nayi maganinka wallahi da mi kake zancen."


Daga Nan ta ja hannun Inteesar suka shiga d'aki don ta k'udurata niyyar sak ta gano tsakanins,dafe goshi Muhdeen ya yi yana ta addu'ar Allah yasa Inteesar kada ta fad'awa Gwaggo komai,muryar Mummy ce ta dawo dashi tunanin da yake.


"Son maganar Gwaggo fa gaskiya ne nima na gani kuma nasan ba auren aoyayya kuka yi ba,kana can kana k'untawa 'yar mutane da ba ruwanta fa."


Dady ya d'ora da cewa


Muhammad Inteesar amanace awuri ka indan kaci amama amana zata cika.




*LONDON*


Kwance ta ke tana kallon Pics d'in Muhdeen tana kuka,ita kad'ai take magana


"Baby me yasa kayi Mani haka?me yasa aka aura maka wannan tsinanniyar yarinyar ne mun tsaka da cin amarci?kasan irin son da nake bazan iya had'a soyyayar ka da wata 'ya mace ba."


K'arar shigowar sak'one ya shigo tana dubawa ta ga Shila ce bud'ewa yayi taga Muhdeen da Inteesar a gaban motarsa a bakin super market,wani gigitaccen k'ara ta saki Wanda ya ja hankalin Mum nata da Da wayar take kallo tabbas shine tare da Inteesar sun ci ado ya d'aukota a motarsa,jifa ta yi da wayar ta bugata da bango dai-dai lokacin da iyayen nata suka shigo d'akin,numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa.






Daga alk'amin✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




DON K'ARIN BAYANI


09065327995




Love u oll😍😘




Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.




Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ki hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.






*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*




Page4️⃣1️⃣


Numfashinta ne ke barazanar d'aukewa tayi luuu zata fad'i cikin zafin nama Dad d'inta ya tare ta ta fad'a jikinsa,Mum d'inta ce ta saki kuka tana fad'in


"Shikenan mun shiga uku 'yar da muke da ita k'wara d'aya ce muke neman rasa ta akan d'a namiji."


"Kinga ba kuma Zaki zauna kinayi mana ba,ki kawo mani ruwa."


Fridge d'in da ke cikin d'akin ta nufa ta d'auko robar ruwa ta 'balle murfin ta mik'a masa ya kar'ba ya watsa mata a fuska sau biyu,sai ga ta ta farfad'o da ajiyar zuciya tana cewa.


"Wallahi bazai yuwu ba Ni Muhdeen zai ci amana ta Ina nan ina tunanin yarinyar nan ba sonta ya ke ba ashe yana can tare da ita ya manta dani ko?"


Ajiyar zuciya Dad ya sauke tare da cewa


"Kada ki damu da kansa zaizo har nan da kansa ya same ki."


Cikin muryar kuka ta fara magana


"Dad wallahi yanzun aka turo Mani pic d'insa ya tafi shopping da wannan matsiyaciyar yarinyar Inteesar,Dad ban ta'ba kisan Kai ba amma Inteesar d'innan matuk'ar tana raye bazan ta'ba samun kwanciyar hankali ba,I will kill her matuk'ar ban kashe ta...


"Shut up kinyi hauka ne ko kuma kishi hauka ne? kada na sake jin wannan maganar ko makamancinta a bakinki,dole ne sai kinyi rayuwa da Muhdeen?


Cikin d'aga murya ta maida ma Dad d'inta da martani


"Yas dole ne!na ce maka dole sai nayi rayiwa da Muhdeen shine mahad'in rayuwa ta bazan ta'ba iya rayuwa babu shi ba da na rasa shi gara a ce na rasa komai a duniyarnan Dad Kai da kanka kayi mani alk'awarin duk abunda nake so a duniyar nan zaka yi mani shi, kuma nima shira ne tunda na tashi naga duk abunda nake so shi kake mani ban ta'ba neman abu na rasa ba duk abunda nake so shi kake so kuma shi kake mani,amma karon farko a rayuwa ta na samu abunda nake son amma yana barazanar su'buce mani."


Mum d'inta ce ta yi ajiyar zuciya sannan ta fara magana


"Tunda haka abun ya kasance da kake cewa ya za'bi d'aya ko'yarka ko wacce suka aura masa kasan dai yana wa iyayensa biyayya bazai ta'ba tsallake maganar iyayensa ya bi na wasu ba kaima kasan da hakan kuma kaji maganganun da kakarsa ta fad'a maka lokacin da ka kira mahaifinsa kake masa magana,indai zaka bi shawara ta tunda basu suka kori Sumayya ba kuma mijinta bai sake ta ba kuma bai wulak'anta ta ba da k'afarta ta bar gidan ta taho nan,to idan zaka bi magana ta ta koma d'akin mijinta tunda ba zata iya rabuwa da shi ba."


"Mum ke da kanki kike fad'in na koma da kaina na zubar da aji na a idonsa da danginsa?da wannan yarinyar da ya aura?."


Fashewa da kuka ta yi fad'aj ikin Dad d'inta tana cewa


"Wallahi Mum ba inda zan koma wato ma na fahimci baki so na baki k'auna ta baki kishi na,tunda har kike son na zauna da kishiya ke me yasa kike zaune ke kad'ai Dad bai k'ara aure ba?ai da Dad ya k'ara aure kika San zafin kishi ba Zaki ce na koma na zauna da kishiya ba."


Da mamaki Mum d'inta ke kallonta


"Sumayya ni kike fad'awa haka?"


Tura baki ta yi tare da cewa


"Ai gaskiya na fad'a kinsan zafin kishin ne?"


Mummy ta yi kanta da niyyar marinta Dad ya daka mata tsawa


"Ke dakata!"


Sumayya k'ara shiga jikin Dad ta yi don ta tsorata da 'bacin ran da ta gani a fuskar Mun nata.


"Kada ki kuskura ki ta'ba mai ita don wallahi kika mareta sai kinyi mamakin abunda zaki maki,k'arya ta fad'a ba gaskiya bane?sabida ance gaskiya d'aci ne da ita,da wanne zata ji da 'bacin ran mijinta ko da naki?kinzo Zaki saka yarinya gaba kamar ba kece kika haifeta ba,ke kanki kin sani bani k'aunar ki 'batawa yarinyar nan rai tun tana k'arama ballantana yanzun da tasan me yakamata tasan dai-dai da akasin haka,da ki ta'bata gwanda ki ta'ba ni,idan kuma kina musu da haka ne to ki ta'bata kisha mamaki."


Mum bata sake cewa komai ba girgiza kai kawai ta yi ta fice ta bar masu d'akin.


A nan k'asa ta kuwa bayan Gwaggo ta ja Inteesar sun shiga d'aki ta zuba mata ido bayan sun zauna ta kalleta ta ce,


"'Yar albarka ki fad'a mani gaskiya ya yanayin zamanki da Muhammadu ya ke?"


Shiru Inteesar ta yi tana nazari kafin ta ce,


"Ba komai Gwaggo muna zaune lafiya"


Kai Gwaggo ta girgiza tare da cewa


"Ba lafiya ba 'yar albarka akwai abunda kike 'boyewa,kina nufin baya cutarki baya zalintarki yana kyautata maki duk wani hakkinki baya tauyewa?"


Shiru Inteesar ta yi ba tare da ta ce komaiba,hakan yasa Gwaggo cewa


"Kiyi mani magana mana abunda yasa kika ji na ce ki fad'a mani ya zamantakewarku ta ke shine kinsan ba auren soyayya kuka yi ba,auren had'i ne kuma bawai yana sonki bane kada ya je ya dinga k'untata maki ba.


"Shiru Inteesar ta yi tana tunanin zamanta da shi Sam baya mata adalci burinshi kawai ya ganta tana wahal,amma Bata son ta zama sanasiyar 'batawansa da iyayensa don matuk'ar ta ce zata sanar da Gwaggo to tabbas zata sanar da su Mummy da Dady kuma zasuyi fushi da shi, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru ta k'udiri niyyar hak'uri da juriyar zama da shi,dan haka kallon Gwaggo ta yi tare da cewa


"Kada kisa tunananin komai a ranki muna zaune lafiya ba abunda kike tunani bane."


"Shine duk kika rame kika lalace?ba komai tunda kink'i fad'a,koma dai mene ne zan gano Allah ya kaimu jibi zanzo na gaishe ku,tashi to muje."


Mik'ewa Inteesar ta yi inda suka nufi falo,zaune suka tarar da su kamar yadda suka barsu, Mummy ce ta zubawa Inteesar ido tana karantar yanayinta,adai zaman da sukayi tare da Inteesar barci ke raba Inteesar da gidanta a tsawon shekaru uku zuwa hud'u kenan amma tabbasa yanayin Inteesar ya canza da ganinta kasan akwai abunda ke damunta.


"Gwaggo ta sanar da ke ko akwai wata matsala?"


Kai Gwaggo ta girgiza yayin da take zama a kan kujera


"Ba abunda ta fad'a itama 'yar nema tayi shiru tana rufa masa asiri badai namiji ba ki cigaba da rufa masa asiri shi zai tona naki ne,ba'a goyon bayan namiji don ba d'an goyo bane kuma tunda na tambayeki kika mani shiru to duk ranar da kika zo kika ce ga abunda ya maki na cutarwa ba abunda zance masa sai dai nayi maki dariya."


"Mummy ce ta yi ajiyar zuciya


"Son Inteesar amana ce aka baka don Allah kada ka cutar da ita kaga k'aramar yarinya ce ita sai kayi hak'uri da ita,idan ta yi abu ba dai-dai ba ka nusar da ita ta lallami da hikima ka yi hak'uri da ita kada ka zaince ta."


Kai ya jinjina tare da cewa


"To Mummy kada ki damu insha Allah ba zakiji komai na rash...


Gwaggo ta yi saurin katse sa da cewa


"Ai dole ka ce ba za'aji ba tunda ka hanata fad'a kayi mata barazana me kuwa zamuji?amma ni ba iya ji ba har gani sai na yi dani kake zance."


Kallon Gwaggon ya yi tare da fad'in


"Me kum zaki gani rigimammiyar tsohuwa?ai ba abunda zaki gani,zancen da kike ma na cewa zaki zo gidana kiyi wata d'aya ban gayyaceki ba kiyi zamanki,ko na wuni d'aya bana buk'atarki ballantana na wata d'aya ki yi zamanki mu zamu zo ki ganmu idan kina buk'atar ganinmu."


"Wallahi baka Isa ba sai nazo"


Murmushin gefen baki ya yi


"Aiko duka ranar da kika zo sai kinyi jinya kin gwammaci da baki zo ba."


Da mamaki take kallonsa


"To me zaka yi mani"


"Ba abunda zan maki amma ina Mai tabbatar making da cewa kika zo gida na sai karen gida na ya yayyaga maki fatar jikinki."


Salati Gwaggo ta saki tana tafa hannu tana ceqa


"Oh ni Kuluwa yanzun kare ka ajiye a gidanka?saboda me?"


"Saboda ke na ajiye duk randa kika saka k'afa gida na sunanki sorry."


"Muhammadu haka zamuyi da kai d'an jakkar uba?"


Mi'kewa ya yi tare da cewa


"Ni zan d'an fita anjima zan dawo na d'auke ta mu koma gida."


Mummy ce ta amsa masa da


"Adawo lafiya"


Dady ya kalli Inteesar ya ce


"Daughter ba wani matsala ko?


Kai ta girgiza tare da cewa


"Bakomai Dady"


"Ba wani abunda kike buk'ata ?"


"Ba komai Dady"


Mi'kewa ya bar wajen.


Wunin ranar Inteesar a gidan ta yi shi Mummy ta Kira ta har d'akinta ta yi mata dabara da lallami, ko zata fad'a mata wani abu na rashin kyautatawa da Muhdeen ke mata amma sam tak'i yarda ta sanar da su haka suka hak'ura suka k'yale ta, Mufida ta ji dad'in zuwan Inteesar sun yini suna fira.


Bayan sallar isha'i ne Muhdeen ya dawo gidan don d'aukar Inteesar su tafi gida,bayan ya ci abinci ne Mummy ke sanar da shi cewa ya je tana d'akin Gwaggo,da sallama ya shiga d'akin Gwaggo da kezaune kan sallaya tana jan carbi ta amsa masa,kwance ya samu Inteesar ganin Gwaggo ya sa ya fara magana mai dad'i


"Sweet heart har kinyi barci kenan tun yanzun?"ashe daren yau ba zamuyi fira ba kenan?"


Ita kuma Inteesar cikin barcinta da yanzun ta saba aikin wahala safe da yamma, kuma yaune bata yi ba sai ta mafarkin wai yana mata hukunci me yasa ba tayi ayyukan da ya ce ta dinga yi kowa ne yamma ba?a cikin mafarkin ta wai gata kwance tana barci shi kuma yana tsaye kanta zai dake ta ne ta fara magana,daga shi har Gwaggo suna kallonta tana mutsu-mutsu sai suka ji ta fashe da kuka tana cewa.


"Yaya dan Allah ka yi hak'uri wallahi narci ne ya d'auke ni banyi ayyukan da kake sani ba,dan Allah kada ka dake ni wallahi bazan k'ara b...


Dafe goshi Muhdeen ya yi tare da sauri ya k'arasa bakin gadon yana jijjiga ta tare da kiran sunanta.


"Baby lafiyarki kuwa wani irin mafarki kike yi ne ai mafarki ba gaskiya ba ce."


Tana bud'e ido ta ganshi a gabanta sai ta k'ara rikicewa tana girgiza kai tana ja baya idanunta na zubda hawaye,goshinsa ya dafe cikin takaicin abunda ya ke 'boyewa yarinyar nan na fiddo da shi,Muryar Gwaggo da Inteesar ta ji ne yasa ta dawo hayyacinta ta gane ashe mafarki take.


"Ba shakka! Ni tunda na kalle ki nasan baki cikin kwanciyar hankali,idan ba haka ba ace barcin mintuna Ashirin ne zaisa ki rikice haka?wannan tsoron da na gani a cikin idanunki da maganar ayyukan da ya ke saka ki kina kuka kina bashi hak'uri kad'ai na fahimci halin da kike ciki saboda abinda mutum yasa a ransa ne ya ke mafarkinsa,don haka tashi kibi mijinki ku tafi."


Mi'kewa ta yi tare da d'aukar posanta da wayarta suka nufi k'ofar fita tana gaba yana binta a baya,bayan fitar Inteesar Muhdeen na k'ok'arin fita ne ya jiyo muryar Gwaggo tana cewa


"Idan baka kashe ta ba to ba sunanka Muhammadu ba."


Kamar ya yi mata magana sai kuma ya fasa ya fice tare da buga k'ofar da k'arfi."


"Ai da ka dawo ka 'balle k'ofar gaba d'aya,mutumin banza."


A falo suka tarar da Mummy sallama suka mata suka fice.


Yana driving ransa a 'bace saboda yasan cewa Gwaggo ta gano halin da suke ciki.


"Wato ke bakijin magana ko?duk gargad'i da nayi maki sai da kika bari suka gane halin da muke ciki dake ko?."


Kai ya jinjina


"Zaki gane kuranki wallahi"


Hawaye ne ya fara fita daga idanunta cikin muryar kuka ta fara magana


"Wallahi ban fad'awa kowa ba duk yadda suka lalla'bani ban fad'a ba."


"Ni zaki raina ma hankali?kina magana a gaban Gwaggo har da kuka kina rok'ona Wai ayyukan da na saki ko?."


"Wallahi bansan na fad'a ba mafarki nayi."


"Kada ki damu mafarkin zai zama gaskiya idan muka k'arasa gida,bana buk'atata na sake Jin muryarki."


Daga nan ba Wanda ya sake magana har suka k'arasa gida,bayan Mai gadi ya wangale masa gate ya shiga ya yi parking need suka fito,yana gaba tana binsa a baya,suna shiga yaga tana k'ok'arin nufar d'akinta ya ce,


"Dakata


Tsayawa tayi tare da kallonsa,ya cigaba da magana.


"Yanzunan ki tabbatar da cewa duka falon gidannan kin goge share su kin goge,sannan duka d'akuna guda takwas dake gidannan ki tabbatar a daren nan kin sharesu kin goge su,duka toilets guda takwas ki wankesu a daren nan toilet na falon nan ma shima haka duka kitchen d'in ma haka fatan kin gana?"


Shiru tayi ta kalli time a wayarta ta ce,


"Yaya kafin na wuce da safe sai da suka ayyukan nan da ka lissafa na yi su,ba wanda banyi ba a cikinsu,bayan na gama ne muka rufe gidan muka tafi ba wani datti bamu zauna gidan ba kuma kaga yanzun k'arfe goma na dare ya kusa don Allah ka barni da safe sai nayi ba datti suka yi ba wallahi barci nake ji."


"Umarni na baki ba shawara na nemi ki bani ba, sannan bari na fad'a maki daga yau bana son uzuri."


Yana fad'in haka ya nufi parta d'in Sumayya,ita kuma ta nufi d'akinta idanunta tab da k'walla na tausayin kanta canja kayan jikinta ta yi zuwa kananun kaya yadda zata ji dad'in yin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads